Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kake cewa ba, ni waye yace maka na ɗauke asiri akanka?". yace,"bakinki". ta waro ido waje tace,"da yaushe?". yace,"ranar da kike bawa ƙawarki labari a asibiti, accident ɗinki na farko da na kaɗeki". tace,"da ma kaine ka kaɗe ni akace wani ne?". kan yay magana ta tari numfashinsa da faɗin,"shima kana sane ka kaɗeni?". ya galla mata harara da cewar,"ehhh sai ki haɗa duka har marinki ki rama, yanzu amsa min tambayata". ta tankaɗe shi daga gabanta ta bar wajen da sauri, tana zuwa bakin ƙofa ya isa ya fizgota ya haɗeta da bango yana faɗin,"Allah you are going no where sai kin amsa min tun yaushe kika sanni?, kuma me yasa kika min asiri?". hakan yasa ta sakin kuka sosai, tana rantsuwar,"Allah ni ban taɓa saninka ba sai da na fara aiki a gidanku, sunanka kawai na sani ajikin takardar da akai maka asiri, amma wallahi bani nayi maka ba, banma san su waye ba jinsu nai kawai suna faɗa, kuma ma ai saboda idan na faɗa ba za'a yarda da ni ba shisa ban faɗawa kowa ba, ina tsoron kar ace ƙarya ne ni nayi maka, amma na rantse da zatin Allah bani ce nayi maka asiri ba". tai maganar idanuwanta a rufe, dalilin ba zai iya jin kukan ba ya kwantar da ita a ƙirjinsa yana shafa bayanta yace,"na yarda daina kukan cry cry Baby, kanki zai ciwo za ki zazzaɓi". tana fizgar numfashi da ƙarfi tace,"wallahi Allah bani bace kuma ban san su waye ba". ya ƙara yin ƙasa da murya very calmly yace,"ohh nace na yarda, na yarda ba ke kika min ba shikenan daina kukan haka, ko ba kya so na barki ki tafi?". da sauri ta girgiza kanta,"ina so". yace,"to inji kinyi shiru sai in barki ki tafi". ɗiff ta ɗauke wuta kamar ba ita ta cika ɗakin da kuka ba yanzu, ta lafe a chest ɗinsa tana jin yanda heart ɗinsa ke bugawa ba irin yanda ta san ainihin bugun zuciya ba, shima fuskarsa kwance akan gashinta ya lumshe ido, wayarsa na ta uban ringing bai ma san anai ba. har aka turo ƙofar ɗakin aka shigo daga shi har ita ba wanda yaji motsin buɗe ƙofar balle kuma motsin mutum. Hajiya Ramla tai mutuwar tsaye daga inda take tana neman bango ta dafe, kafin dai tayi ƙarfin halin ɗaga ƙafarta da take jin kamar ta mutu ta dawo saitin inda zata ga fuskar wacce yake rungume da ita haka, bata san ba ko matar tasa ta dawo basu sani ba, sai dai tana zuwa ganin fuskar Fillo wacce idanuwanta ke lumshe yasa tai saurin ja da baya tana dafe bango da furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. wannan dogon salatin da taja cikin razani shi ya dawo da Turaki cikin duniyarsa, ya buɗe ido a tsoroce jin muryar Mum akansa, ya kalleta ya juya ya kalla ƙofa sannan ya juyo ya kuma kallonta, sai kawai ya saki Fillo yana ja da baya, lokaci ɗaya sai ya dawo kamar wanda ya kashe ɗan sarki aka gurfanar da shi a gaban sarki. Mum ta bi ɗakin nasa da kallo sannan ta tsayar da kallonta akansa, ta tattaro yawun bakinta da ƙyar tace,"Babana, me nake gani haka?, kai ne da kanka tare da wadda ba matarka ba?". sai kawai ta ɗaga hannu ta wanke shi da marin da ya kai fuskarsa ƙasa, da kanta ta ɗago da shi ta ƙara wanke shi da wani sabon marin da ya kaisa ƙasa gaba ɗaya gwiyoyinsa suka zube a gabanta. Zaytuna tasa hannu ta rufe bakinta tana fashewa da kuka, tun ɗazu take kiransa a waya bai ɗaga ba, abinda take ta so ta faɗa masa kenan ga Mum nan. Fillo dai tuni ta durƙushe a wajen tana kuka sosai kamar ranta zai fita, cikin ƙunar rai da zafin zuciya ta rarumi lamp zata buga masa Zaytuna tai saurin riƙe hannunta tana faɗin,"Mum ki tsaya kiji". tayi wancakali da ita gefe tai kansa tana kai masa ƙafa ta ko'ina. "mutumcin gidan namu zaka zubar mana?, dama abinda na haifarwa kaina kenan?, sheɗani na haifa dama ban sani ba?". ya saurin ɗagowa yana kallonta idonsa na hawaye yace,"Mum". bata barsa ya faɗi abinda zai faɗa ba tasa ƙafa ta daki gefen cikinsa. "kaico, kaico da haihuwar irinka, nayi dana sanin haihuwarka, me ma yasa na saka maka sunan da ba zan iya kiranka da shi kai tsaye ba na zazzageka, me yasa nake jin ba zan iya tsine maka ba kai tsaye, wallahi na tsani ganinka, kai ba ɗana bane, yau sai dai ko ni ko kai a gidan nan". ta ƙarashe maganar dai-dai lokacin da Hajiya Madina ke shigowa a rikice, tayi fatali da kwalbar da taga Mum ta ɗauka zata rotsa masa, ta riƙeta da kyau tana cewa,"me idanunki suka gane miki your excellency da har ba zaki iya excusing ɗinsa ba". Mum na huci sosai kuka na zuwar mata tace,"kin san i spent morethan 5minutes a bakin ƙofar nan ina jiyo kukan yarinyar nan tana roƙonsa akan ya rabu da ita, amma ɗan banzan yaron nan yaƙi barinta ƙarshe dana buɗe ɗakin ajikinsa na ganta rungume da ita tana sauke numfashin wahala, bai ma san na shigo ba tsabar ya riƙa a iskanci, ki barni kawai na kashe shi Madina ba zamu zauna da gurɓatacce ba wallahi". Hajiya Madina taja da baya tana neman faɗuwa, tai saurin dafe bango saboda daina gani da ta fara yi, ta shiga tashin hankali na farat ɗaya da take jin kamar zuciyarta na neman bugawa, batun hawan jini kuwa tasan tuni ya hau, tabi Fillo dake kuka sosai da ido, sannan ta dawo da kallonta kan Turaki bata san lokacin da ta zube ba a gabansa, nan da nan hawaye ya shiga sauko mata. tana magana da ƙyar tace,"this is not the background i gave you, ba foundation ɗina bane wannan, dan Allah na roƙeka ka ƙaryata abinda idanuwa da kunnuwa suka ji, me babban suna me ya sameka?, me kaje ka sha da har ka nemi ka aikata abinda baka taɓa aikatawa ba tsawon shekaru talatin da uku?, ina kaje aka baka wani abu kasha?, me yasa ɗazu baka ce min in barka kaje wurin matarka ba kana buƙatarta?, me ƙaramar yarinya kamila kamar Fillo tayi maka da zaka lalata mata rayuwa?, me babban suna me nai maka da zaka saka min da hakan?, so kake ka kashemu ko so kake kace mu mutu mu bar maka duniyar?, ashe da rabon kaine silar yanke farin cikin rayuwata?, ban yafe maka ba me babban suna, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". ta faɗa tana fashewa da kuka sosai, da ƙarin cewa,"ba tarbiyyata bace wannan me babban suna, ba haka na raineka ba, wannan sabon halin me muni daga ina?". Mum tace,"ki matsa daga gabansa kar na fallatso miki jini, ki matsa nace miki". ganin abinda take ƙoƙarin aikatawa Samha tai saurin doka tsalle ta dire a bayanta tana rirriƙeta. Zaytuna ta duƙe a wajen tana cewa,"Maama duk fa ba yanda kuke zato ba ne, dan Allah ku barsa yay muku bayani". a fusace Maama ta dunƙule hannu ta kai mata naushi ta baya tai mata wani mugun duka a hanci, tsananin zafi yasa tai shiru tana dafe hancin da take jin kamar ya cire. Turaki ya dinga kallon Maama dake ta kuka a gabansa, kuma irin mugun kallon da take masa in har ya bari ta miƙe akansa sai ta kaisa har lahira, ya ɗaga kai ya kalli Mum dake faman kokawa da Samha da Khaleel tana so ta ƙwace daga riƙon da sukai mata ta rotsa masa kwalbar hannunsa. ya rumtse ido sosai ya daki kansa da bango sannan ya buɗe baki yace,"Maama she is my wife, na bayar da sadakinta 5months da suka wuce, na damƙa sadakinta a hannun mahaifinta". "what?!!!". abinda Maama da Mum da Baffa dake shigowa yanzu suka faɗa tare. Bello ma dake zuwa yace,"ehh Maama ya aureta tunda daɗewa". *Vote, Comment and Share.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _Avoid error mistakes._ na kwana 3 ne🤐, ataimaka kar inji ana nemana🙏🏃‍♀ *41* with confusion Baffa ke kallon Turaki, kuma tashin hankali da damuwar dake tattare da Mum da Maama sai suka juye zuwa tsantsar mamaki. Maama ta dinƙa kallonsa babu ko ƙifta ido, so take ta tabbatar da idan a hayyacinsa yay wannan maganar, kamar dai ba ɗanta ba an sauya mata wani, kuma kamar dai yasha wani abu da ya juyar da tunaninsa. Mum ta jefar da kwalbar hannunta, ta mayar da ƙwayar idonta kan Bello wanda ganin zata kallesa ɗin yay saurin sauke idonsa ƙasa. Baffa yay ajiyar zuciya wadda babu wanda bai jita ba, muryarsa ta fito da amon da babu wanda bai sha jinin jikinsa ba acikinsu, ya juya zai bar ɗakin yace,"ku sameni a parlo". wannan sautin muryar tasa da kuma yacca ya juya ya fice ɗin Turaki ya tabbatar da ya gama shiga uku, Bello ma ya ɗora hannu aka ya furzar da wata iska daga bakinsa, ya san Baffa ya san ya faɗansa idan ransa ya kai ƙololuwar ɓaci, yana da masifar son ƴaƴa shisa ma ba ya iya musu faɗa, but baya tolerating shits, ya san ba zai taɓa ɗaukar wannan kwaɓar da Turaki yajawa kansa ba, bayan wannan ɗan guntun jawabin da yay bai kuma san ta inda zai fara yin wani ba in aka tsaresu. Mum tazo ta wuce ta kusa da shi fuuu kamar zata tashi sama, kallo ɗaya zaka mata ka san a fusace take. Turaki yabi bayanta da ido kafin ya maida kallonsa kan Maama ya buɗe baki zai yi magana, tayi saurin ɗaga masa hannu,"dakata, kar ɗan ƙwaya ya sake yace zai min bayanin da kaina ba zai ɗauke shi ba". sai kuma ta miƙe tai bakin ƙofa tana ƙara faɗa masa,"kar in jini a cikin lamarinka". ta fice tana jin ita bama tasan actual tunanin da zatai akan maganar tasa ba, dan magana ce yay ba irin ta waɗanda ke cikin hankalinsu ba. kowa ya fita a ɗakin aka bar Turaki da Fillo kawai, ya miƙe yana jin kansa na sara masa, Bello ya dawo yay tsaya jikin ƙofar yana kallon abokin nasa da tausayi yace,"ka taso muje tun wutar da sanyi sanyinta before ta balbala ta ƙona mu". Turaki ya kallesa ya ɗauke ido, ya mayar da kallonsa kan Fillo da har yanzu take a wajen a duƙe kowa ma ya manta da ita, kukanta take tayi bata daina ba, ya tafi yana jin jikinsa kamar mara lafiya ya isa inda take, ya ɗagota tsaye yana faɗin,"please stop this crying its hurts me alot, from today ba zan ƙara saka ki hawaye ba, i promise". ya faɗa yana ƙoƙarin ɗora kanta a ƙirjinsa, sai ta hana hakan tana ɗago da kanta ta kallesa tace,"me kace musu?". ya rufe ido ya buɗe yace,"ce musu nayi ke matata ce". ta kasa ɗauke idonta akansa saboda itama a shock take, and gani take kamar ya sha ƙwaya ne shisa yake wannan maganar da hankali ba zai ɗauka ba. "shi auren film ne dama?". yana kallonta yace,"ba film ba ne, namu ɗin ne dai ya zama kamar a film". ya faɗa yana matso da ita ta ƙwace daga riƙon da yay mata ta tankaɗa shi baya, cikin sheƙar sabon kuka tace,"leave me alone, Allah i hate you, ji a matsalar daka jefa ni alhalin ni babu wanda ya taɓa riƙe hannuna ma, shikenan yanzu zaka ja Ummina ta yanka ni". tai maganar tana wani kukan sosai. da damuwa sosai yace da ita,"muje". taƙi tafiya, ransa a ɓace ya doka mata tsawa,"nace muje ko". jikinta ya fara kyarma ya kama hannunta suka fito, tafiya suke kamar marasa lafiya, ji yake kamar babu komai acikin kansa, kamar babu yawun da zai yi musu bayani, taƙaimaimai ma bai san ta ina zai fara ba. Bello dake daga gefensu yace da Fillo,"ki ɗaga ƙafa dan Allah, acikin matsala fa muke". suka haɗa ido da Turaki yace masa,"kaita innalillahi ni inata yin hasbunallahu". sai da Bello yay adu'a sosai tukunna ya iya saka ƙafarsa cikin parlon, ƙafafun Fillo suka fara shiga sannan na Turaki, idon Maama ya sauka akan hannunsa dake riƙe da nata wanda da alama forcing nata yay ta ƙasa ƙwacewa, lallai me babban suna ya riƙa da yawa. bai yi gigin nufar inda Mum da Maama suke ba, still hannunsa na riƙe dana Fillo ya wuce ta bayan kujerar da suke suka zagayo ta ɗaya side ɗin, Fillo tayi-tayi ta ƙwace hannunta ya hana hakan har suka zo tsakiya ya zauna sannan itama ta zauna, duk akan idon Baffa dake jinjina ƙarfin hali irin nasa, sai da suka zauna ya saki hannun nata tayi saurin matsawa ta bar kusa da shi. Baffa ya ajiye wayar dake hannunsa yana girgiza ƙafa, sai da yaywa Turaki kallon tsab ya tabbatar ba ƙwaya ce ke aiki a jikinsa ba sannan yace da shi,"maimaita abinda kace ɗazu". Turaki yace,"Baffa...". ganin zai masa dogon jawabi ya dakatar da shi wajen ɗaga masa hannu. "ce nayi ka maimaita abinda kace ba dogon turanci nace ka min ba". Turaki ya sauke numfashi ya sunkuyar da kansa yace,"na aureta tun 5months da suka wuce". yana yin shiru Baffa ya maida kallonsa kan Bello yace,"ehen?". yay saurin ɗaga masa kansa,"ehh Baffa da gaske ne ya aureta". Baffa ya sake cewa,"kai ka zama waliyin right?". da sauri ya girgiza kansa ganin irin kallon da Baffa ke watsa masa yace,"a'a wallahi Baffa, ban ma san yay auren ba sai after yake faɗa min, wallahi ban san yanda auren...". tsawar da Baffa ya sakar masa ta dakatar da shi,"shutup, waye marainin wayonka anan da zaka faɗa masa ba da kai akayi komai ba, marasa mutunci banza ƴan iska marasa hankali, waɗanda baku ɗauka iyayenku a bakin komai ba, wato har kuna da bakin ma da kuke maimaita min ko?, gaku kun balaga bari kuyi gaban kanku, to tunda ka aureta sai ka saketa yanzu dan ni ba zan yarda da wannan auren iskar ba, ba'a gidana ba, ba'a zuri'armu ba, ka saketa yanzu nace sannan ka min bayanin uban da yasa ka kai ƴar mutane cikin ɗakinka". furucin Baffan na ƙarshe ya doka wata tsayawa acikin kan Turaki, bai san lokacin da ya ɗago yana kallon Baffa da wani bala'in tsoro ba, muryarsa na breaking yace,"saki kuma Baffa, dan Allah karka yanke min wannan tsatstsauran hukuncin ba zan iya ba". Baffa dai ya riƙe haɓa couldn't stop looking at him, dama saboda ya ƙara tabbatar da abinda yace shisa yace ya saketa ɗin, kenan da gaske yake ya aureta ɗin tunda ga tashin hankali nan ɓaro-ɓaro akan fuskarsa saboda yace ya saketa, ya dinga kallonsa da wani expression da shi kansa ya kasa fahimta, yayi aure kuma har 5months duk ba wanda ya sa ni, to waye ya ɗaura masa auren?, kuma when hakan ta kasance?. "kayi aure Muhammad?, wa yay maka auren?". Turaki ya ƙara yin ƙasa da kansa yace,"Baffa ni ɗaya naje, dama ina da niyyar zan faɗa muku". ran Baffa ya ƙara ɓaci yana jijjiga kansa yace,"kana da niyyar faɗa mana bayan kayi gaban kanka?, ka ɗaurama kanka aure ba tare da saninmu ba Muhammad?, kayi aure babu ni ubanka da nake raye, babu ƴan uwana, ka shiryama kanka aure kai ɗaya, yaushe ka zama ɗan iska har haka?, yaushe ka mayar da ni mutumin banza ban sani ba?". sai kuma yay shiru ya mayar da kallonsa kan Hajiya Madina yace,"dama har haka ku ka mayar da ni mutumin banza da wofi?". kan ya ƙara magana ta tari nunfashinsa,"ya dai mayar da mu ƴan banza da wofi, ko idan da haɗin bakina akayi kaga na bari anyi wannan zaman?, to ni wiwin ma da ya fara sha ban sani ba balle sanda yaje ya ɗaura ma kansa aure, saboda haka kayi jan idonka akansa shi ɗaya, inma ɗauresa zaka yi duk kayi ba damuwata ba ce". sai kuma ta kalli Fillo tace,"kema ashe tantiriya ce ban sa ni ba...". kuma bata ƙarasa ba Turaki yay saurin katseta da cewa,"Maama bata san komai ba itama". da mamakin da yafi na da Maama ta saki baki tana kallonsa, sai ya juya yay facing Baffa yay kneeling murya a hankali yace "Kayi haƙuri Baffa, na san nayi kuskure amma ka yafe min dan Allah, wallahi ba zan ƙara maimaita makamancin haka ba, ba zan ƙara aiwatar da abu ba da saninku ba, dan darajan Allah kayi haƙuri ka bani damar da zan maka bayanin da zaka fahimce ni". Baffa yace da shi,"ai na kawo ƙarshen komai, sakinta kawai zaka yi dan wannan gantalallan auren ba'a zuri'armu ba". Turaki ya rumtse idonsa yana jin kamar ya kurma ihu, ya dinga roƙon Baffa akan yayi haƙuri ba zai iya sakinta ba,"dan Allah Baffa kuyi min duk abinda zaku yi min amma karku ce in saketa ba zan iya ba, dan Allah ku bani damar da zan muku bayani ku fahimta". Baffa ya jinjina kai yace,"zo nan Muhammad". bai iya miƙewa ba ya dinga jan gwiwoyinsa har ya kai gaban Baffan, Baffa ya miƙa masa waya yace,"ka kirasa kayi masa bayani, ƙila shi ya fahimceka, dan ni ban da ta cewa dan lamarinka yafi ƙarfin tunanina". Turaki ya karɓi wayar hannunsa na rawa, tun bai kai ƙwayar idonsa kan screen ɗin ba ya san wa Baffa yake nufi da ya kira, yana kallo kuma yaga sunan Hakimi ne akai calling kawai zai yi, sai yaji kamar ya fashe da kuka sanin cewa in har Hakimi ya san wannan maganar tasa kuma ƙare, ina shi ina kiran wannan azababben mutumin ya faɗa masa laifin da yayi da bakinsa, he can't even imagine yanda Hakimin ma zai yi fata-fata da shi, abu mafi sauƙi ne a wurinsa yasa a ɗaure shi bayan ya raba auren, saboda haka sai yay switching wayar off ya riƙeta a hannunsa, ko giyar wake ya sha babu abinda zai sa yay ma Hakimi bayani da kansa, ba ma ya fatan maganar taje kunnensa, inma zata je gwara ace taje masa a sabon aure zai yi, ƙaramin laifi ma yana ɗaure mutum na tsawon shekaru balle wannan da shi kansa ya san bai kyauta ba, dan lamarin aure ba abinda wasa ba ne. Baffa ya ɗaga masa murya yace,"kana ɓata min lokaci Malami, ka kirasa kayi masa bayani da kanka nace, idan kuma ka bari na ɗau mataki da kaina zaka sha mugun mamakina, sai kayi zaton bani na haifeka ba Muhammad". Turaki ya kallesa hankalinsa a mugun tashe, ya marairaice yana haɗa hannayensa yace,"don girman Allah Baffa ba sai an faɗawa Hakimi ba dan Allah Baffa, i beg you kayi min hukuncin duk da zaka yi min amma karka faɗa masa". sai kuma ya juya wurin da Maama take yace,"dan Allah dan Annabi Maama kuyi haƙuri, idan nayi muku bayani Allah zaku fahimce ni, nima ban san nayi kuskure ba sai daga baya, kuma na rasa ta yanda zan maku bayani ne shisa aka ɗauka tsawon wannan lokacin". Maama ta kawar da kanta gefe ɗaya bata ko kallesa ba, ita aurar Fillo fa ba shi yay mata ciwo ba, ofcourse yayi ba daidai ba, but da auren ya ƙare akan Fillo abin yayi mata daɗi, takaicinta ɗaya da aurensa zai ƙare a unprepared marriage, shikenan mafarkinta akan aurensa duk sai ya tashi a banza?, bacin irin ƙwallafa rai da cin burin da tayi da aurensa mussaman da ta gama saka Fillo acikin lissafin ƙarin auren nasa?, wancan an yisa ba shiri wannan ma kuma sai azo mata da wani zance na daban da hankali ya kasa ɗauka. "Maama please". ya ƙara kiran sunanta dan ya san ita ɗaya yake da ita a wurin nan, roƙon Mum won't favour him shisa ma yake tsoron kallonta. tausayinsa ya kama Maama sosai amma sai ta kawar ta dake ta kalli Baffa tace,"ka yiwa tufkar hanci kawai, ka kira Hakimin da kanka ka faɗa masa komai, mu ba iyayen banza ba ne da zai ja mana magana a bakin duniya, inma sallamarsa zaka yi ka sallame shi ya tattara komatsansa ya wuce ya bar mana gida, dan ni ba zan ci gaba da zama da ɗan wiwi ba, rashin sanin darajar iyaye har ina haka?, ai cin mutumci da rashin sanin darajar tamu yayi yawa". ya miƙe daga gaban Baffa ya nufi Mum, tana kallon ya taho ta dakatar da shi,"karka sake kazo inda nake, banda hurumi da kai. su ma ɗin da suka gaza ɗaukar mataki akanka har yanzu lokacinka suke da, ni kuwa ka iso gabana banga abinda zai hanani shaƙeka ba". sai kuma ta mayar da kallonta kan Baffa cikin ƙunar rai tace,"kai har yarda kake da shi akan ya auri yarinya?, ta ina zai soma ɗaurama kansa aure babu iyaye, shege ne shi?, ko kuma shi uban yarinyar ba ƙwaƙwalwa akansa?, ai kawai ka zartar masa da hukuncin haikewa ƴar mutane da ya nemi yayi, ka bugasa a jarida ka yaɗawa duniya, ba wai ka tsaya sauraron zantukan kare kai daga bakinsa ba, mu zai rainama wayo saboda a rabu da shi shine zai ce ya aureta, ko ya taɓa ganin anyi haka a film da zai ce zai kwatanta?, to ka zartar masa da hukuncin da ake ma ƴan iska kawai, ka mance ɗanka ne kayi alƙalanci dai-dai da yanda kuke ma masu ɓata ƴaƴan mutane, batun ya aureta ma bai taso ba ƙarya yake yi kare kansa zai yi". hankalin Turaki ya ƙara tashi matuƙa, ya zube yana dafe kansa sosai yace,"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, wallahi tallahi na aureta, na rantse da Allah na aureta, idan ban mallaketa ba babu abinda zai sa ki samemu a yanda kika ganmu Mum, mahaifinta ma shaida ne shi ya karɓi sadakinta...kuma wallahi ni banyi auren nan domin rashin sanin darajanku ba ko kuma ci muku mutumci ba, wallahi na amince an ɗaura auren ne saboda tausayinta". ya ɗaga kai ya kalli Baffa yace,"Baffa tayi min taimakon da ba kowa zai iya yi min ba shisa na aureta saboda ina ganin hakan shine mafi cancantar sakayyar da zanyi mata". "Taimako?". Baffa ya tambayesa. ya ɗaga kansa,"ehh Baffa, kuma ka tambayeta kaji". Baffa ya kalli inda Fillo take kamar yanda Hajiya Madina ta buɗe ido tana kallonta, kar dai ta faɗa masa duk shirin da su Samha suke yi akansa, kuma tunaninta bai kai ga nisa ba taji Fillo na cewa Baffa,"ni bai aureni ba Baffa, bai ma san a inda Abbana yake ba, kuma banyi masa taimakon komai ba". Turaki ya saki baki yana kallonta da mamaki, sai kuma yace,"ehh Baffa bata san na aureta ba amma ƙarya take yi wallahi tace bata taimakan ba, taimakon da tayi min ko wanda muka fito ciki ɗaya ba lallai ya iya yi min ba, ku a bata ƙur'ani ta rantse da shi bata saka kanta a haɗari ba saboda ceto ni daga hallaka ni da aka nemi yi, wallahi Baffa asirin da akayi min ta dinga bi tana ɗaukewa". Mum ta riga Maama da Baffa furta kalmar asiri, Fillo ta ɗago kanta a rikice tana kallon Baffa tana girgiza masa kai,"Baffa ba haka bane, ni ban san abinda yake faɗa ba". kwarjin dake tare da Baffa yasa bata san sanda ta fashe da kuka ba tace,"wallahi Allah bani nayi masa ba, waɗanda ma suka binne asirin ban sansu ba, jinsu nayi kawai suna faɗa, ni kuma nasan bai yi musu komai ba shisa na dinga lalata musu aiki". Baffa ya kalli Hajiya Madina yace,"kira min Kakar yarinyar nan". abinda take shirin yi kenan dama, dan ta fara tunanin anya ba aljanu a jikin Fillo, ta ɗauka waya ta kira Kaka wadda taji ta ruɗe jin tace suzo yanzu cikin gaggawa. Mum ta dinƙa kallon Fillo cike da nazari, muryarta kaɗai ta isa ta shaida maka abinda ta faɗa gaskiya ne balle kuma ka kalli fuskarta da gaskiyar ta fito ɓaro ɓaro, to waye zai ma Babanta asiri?, akan wanne dalili?, lokaci ɗaya kuma cikin kanta da zuciyarta suka haska mata sunan Fulani Azima, take ta furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un wanda yaja idon kowa kanta. kawai sai ta fashe da kuka tana jin wani zafi da tashin hankali, me sukai ma Azima haka a rayuwa?, cutarwar da tayi mata bai isheta ba sai da ta biyo ta kan ɗanta?. kukan nata kuma shi yasa Fillo hargitsewa ta fashe da kuka sosai tana girgiza kanta tana cewa,"wallahi Allah Mum bani nayi masa ba na rantse da Allah". Baffa yace da ita,"in har ba ke bace me yasa baki sanar ba?". tace,"Baffa ai nasan idan na faɗa ba lallai a yarda dani ba, kuma wataƙila ma ace ni nayi masa

Chapter 44 of 73