yin kyauta ga Fillo.
drivern ya buɗe mata back seat ta shiga, sai dai tun kamin ya zagayo ɓangarensa har Hajiya Madina ta kula da rashin Fillo cikin motar. hakan yasa ta buɗe motar ta leƙo kanta tana faɗin,"Ɗan Usaini ina ƴata?, ina Halimatu taje?".
Ɗan Usaini ya dakata da buɗe motar yace,"Hajiya ai taje kai miki waya ni kuma naje ɗan yin uzuri".
Hajiya Madina tace,"ban gane nufinka ba".
yace,"ruwa naje kamawa, to ban san ba gaskiya ko ta dawo na dai barta ta shiga ciki kai miki waya".
lokaci ɗaya Hajiya Madina ta fito a motar gaba ɗaya,"ka daina cewa ta kai min waya. kai wayar tun yaushe ne?, kusan fa minti biyar kenan, tana bani ta fito".
Ɗan Usaini na waige yace,"to ko ta zo ta tarar bana ciki sai ta koma, bari na duba cikin store ɗin".
ya faɗa yana barin wajen, Hajiya Madina tabi bayansa. lokacin hankalinta duk bai tashi ba amma dai ta tsorata, ina Fillon zata je?, idan cikin store ɗin ta koma ai tana shigowa zasu yi clashing tunda tana daga bakin ƙofa tana biyan kuɗi.
daga cikin store dai har wajensa babu Fillo, a wannan lokacin hankalin Hajiya Madina ya fara tashi, haka suka dinƙa zagayen arean wajen suna kiran sunanta suna dubawa amma ba ko alamarta.
Ɗan Usaini na tare da me gadin store ɗin yace da Hajiya Madina,"ƙilan ko da ta shiga kai miki wayar makuwar hanyar fitowa tayi".
Hajiya Madina dai tana tsaye ta kasa cewa komai, saboda yacca take jin numfashinta na neman yankewa, iska ce a wajen ke ta kaɗawa amma ita zata iya rantsewa hucin zafi take ji ajikinta, zata iya rantsewa kamar ji da ganinta ya ɗauke.
ƴar mutane ta ɓta ata sanadinta?, me zata ce da Kakar yarinya?, me zata ce da wanda ke shirin aurenta?. lokaci ɗaya kanta yay wani mugun sarawa kawai sai ta fashe da kuka, staffs dake cikin store ɗin suka fito dai anata ƙara lalube, tsawon kusan minti 30 inuwar Fillo ma ba'a gani ba.
da ƙyar Hajiya Madina ta iya picking call ɗin Baffa, ta faɗa masa halin da take ciki, sai dai kamin yace komai Hajiya Madina ta yanke jiki ta faɗi a lokacin, dalilin abinda taji Ɗan Usaini na faɗawa me gadin wajen.
"to ni dai bana ce hakan ba ne, zargi kawai nake da hasashe. kaga bakin bishiyar can anan naga motar tayi parking, kuma wallahi tun lokacin da zan tafi fitsarin naji hankalina bai kwanta da motar ba, to kuma sanda nake dawowa sai naga motar na barin wajen, sai na bita da kallo har ta ɓacewa ganina, kasan Allah ba wai don saboda ɓatan yarinyar nan ba, jikina kawai naji bai aminta da motar ba, Ya Rahmanu dai yasa ba ƴan garkuwa bane suka yi gaba da yarinyar nan".
da hanzari akai kan Hajiya Madina, da ƙyar aka iya kamata aka sakata a mota sai asibiti.
Tunda suka isa asibitin aka karɓe ta aka shiga bata taimakon gaggawa saboda yanayin yadda ta ke a sume, su na tsaye cirko-cirko a ƙofar ɗakin aka shiga da ita suna jiran suji me likitan zaice in ya fito, ba'a fi mintina biyu ba ya fito yana ƙarasa zare gloves ɗin hannunsa a lokacin ne kuma Baffa ya iso wajan da hanzarinsa.
ganinsa yasa Ɗan Usaini nufarsa, sai dai ko ta kansa Baffa bai bi ba yay wajen likita.
"Likita ya jikin matata?" Baffa ke tambaya yana kallon likitan da yake goge hannunsa da hand sanitizer.
ya kalla Baffa yace,"Patient ɗin ku jininta ya hau sosai, akwai abinda ya firgita ta lokaci ɗaya shiyasa BP ɗinta yayi high, wannan dalilin ya saka ta suma, but yanzu an saka mata drip kuma da izinin Allah da ta farka zata dawo dai-dai."
Ɗakin Baffa ya shiga ya tarar da ita a kwance tana bacci, ya zauna gefenta ya kamo hannunta yana ta kallonta, tausayinta yayi matuƙar kama shi, ya sa ni fiye da hawan jini ma za'a iya faɗa indai akanta ne, saboda ita macece da bata iya saka abu a ranta ba, tana da saurin ruɗewa nan da nan musamman akan ƴaƴanta, haka ma akan wanda ta damu da shi, ta kan kasa juriya da dauriya.
ya san tana matuƙar son Fillo, dan ko da yaushe suka zauna tana yawan masa labarin yarinyar, irin tarbiyar yarinyar da hankalinta da natsuwarta da kamun kanta, har ta kance masa ita ina ma ace yarinyar ta zama rabon wani acikin Khalil ko Turaki.
kuma sau tari tana faɗa masa insha'Allahu zata yi iyakar bakin ƙoƙarinta wajen ganin yarinyar ta samu wadataccen ilimi domin itama rayuwarta ta inganta, yarinyar ba kalar yaran da za'a banzatar da rayuwarsu ba ne.
Hajiya Madina bata farfaɗo ba sai bayan sallar isha'i, kuma tana farkawa idonta ya sauka akan Baffa dake waya da wani police yana shaida masa ɓatan Fillo, sai dai suna haɗa ido yay saurin sallama da police ɗin gudun kar taji a ƙara samun matsala.
ta kama hannunsa tana faɗin,"Baffa yarinyar mutane, ƴar mutane ta ɓata a hannuna Baffa, me zance da iyayenta Baffa?, me zan faɗawa mijin da zata aura Baffa?, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, wallahi wallahi banda masaniyar inda tayi, Baffa wallahi da nasan hakan zata faru ba zan fita da ita ba".
daga yanayin yanda take maganar kasan bata cikin hayyacinta.
sai kuma tayi shiru tana kallonsa kamin cikin sanyin murya tace,"Baffa an ganta ne?, Ɗan Usaini ya nuna motar mutanen?". ta faɗa tana sakin kuka me ban tausayi.
Baffa Ya kama hannunta sosai, ya kwantar da murya yace,"Please stop crying, Insha'Allahu za'a ganta very soon, ba wai ɓata tayi kamar yanda muke tunani ba insha'Allah".
tace,"Baffa ta ya?, Ɗan Usaini fa yace yaga motar da bai yarda da ita ba, kuma fa lokacin ne ta fito ta kawo min wayata, Baffa me kake tunanin ya faru?".
Baffa ya ƙara sauke numfashi sannan yace,"ki bar wannan tunanin Madina. kuma insha'Allah cikin daren nan zamu ganta, nayi report mawa police and zasu fara aikin nemanta yanzu".
sai ya ɗauko wayarsa yay dialling numbern Inspecter Sise, yana ɗagawa yace da shi,"ta farka, wanne irin bayani kuke buƙata daga wajenta?".
Inspecter Sise yace,"ka bata wayar muyi magana". Baffa ya kalla Hajiya Madina sannan yace da Inspecter,"tana da saurin ruɗewa, please a san irin tambayar da za'ayi mata".
tambayar kayan dake jikin Fillo da kuma yanayin yarinyar da kamanninta da yanda akayi ta fito duk su Inspecter ɗin yaywa Hajiya Madina, kuma duk ta ba shi amsa, sai dai daya tambayi hoto tace gaskiya bata tunanin yarinyar na da hoto ma.
daga nan kuma inspecter ɗin ya ƙara cewa da Baffa zasu yi arresting Ɗan Usaini domin shima zai iya zama suspect nasu.
motar police tazo asibitin cikin ƙanƙanen lokaci, aka sawa Ɗan Usaini handcuff aka wuce da shi, hankalinsa a tashe yana ta rantse-rantsen shi wallahi bai san komai ba akan ɓatanta, yaje kama ruwa lokacin, ai masa rai wallahi baida hannu.
To har wajen dai sha ɗaya na dare babu wani batu na ganin Fillo ko alamun ganinta, tun Baffa yana ganin ɓatan kamar da wasa har ya dawo ya ɗauke shi da gaske, a sannan kuma shima hankalinsa ya fara tashi. Hajiya Madina dai har lokacin banda kuka da ambaton Allah babu abinda takeyi, ƙememe kuma taƙi yarda aje gida a tambaya ko ta koma, sai Khalil kawai ta yarda Baffa ya kira ya gargarɗe shi akan kar ya bar kowa yaji zancen, kawai dai ya san yanda zai shiga wajen Kaka su gaisa ya gani ko yarinyar ta koma, shima kuma letter ya kira ya sanar musu bata nan.
a sanda waɗanda suka ɗauke Fillo suka fito daga cikin gari, lokacin ne kuma suka ƙara speed na motar, gudu na fitar hankali suka dinga shararawa akan titin da babu kowa, gudu na ganganci kamar basa son rayukansu. sai da suka yi tafiya a ƙalla ta awa guda sannan suka shigo cikin wata unguwa, daga nan kuma suka fara tafiya with normal speed gudun jan hankalin mutane zuwa gare su, har suka yi nisa sosai sannan suka sauka daga kan titi suka shiga wani layi, haka suka dinga wuce gidaje da shaguna, sai da suka zo kan wani incomplete building tukunna sukai parking motar, ɗaya daga cikin su ya fita ya buɗe gate suka shiga da motar ciki.
compound ɗin gidan ƙato ne, sai da suka je har entrance na shiga cikin gidan sannan sukai parking a wajen. na gaban motar shi ya fata fitowa yana cire face mask ɗin fuskarsa da ya dame shi, sannan wanda yay driving motar ya fito, sai ɗayan da ya rage a baya ya cicciɓo Fillo kamar wata jaririya, shima ya fito sannan suka nufi cikin gidan a tare da sauran. Babban parlo ne da ba'a gama ginasa ba but ansa tiles anyi filasta paint ne kawai ba'ayi ba sai ƙarashen wearing, suka wuce zuwa wani dogon corridor inda ananne zaka tarar da jerin ƙofafi na rooms, a ƙofa ta ukun ƙarshe suka tsaya, ogan nasu shi ya buɗe sannan wanda ke saɓe da Fillo a kafaɗa ya fara shiga, yana shiga ya kwantar da Fillo kan wani ƙaramin gado kamar gawa.
Madaidaicin bedroom ne da shi kaɗai akai completing gininsa acikin ɗakunan dake gidan kusan guda 7. ogansu ya ƙaraso gadon ya zauna daga gefe, yasa hannu ya mammari fuskar Fillo don tabbatar da nauyin sumanta, sannan ya ɗago kansa ya kalla ɗaya daga cikin yaransa yay masa alama da yazo.
mutumin da duk cikinsu shine ƙato yazo ya hau kan gadon riƙe da shimfiɗeɗiyar igiya a hannunsa, ya jirkitar da Fillo gefe ya ɗaure mata hannayenta ta bayanta, ya kuma haɗa ƙafafuwanta wuri ɗaya suma duka ya ɗaure, sannan ɗaya daga cikinsu ya miƙo masa masking tape ya nannaɗe bakinta da shi.
Sai da suka tabbatar ko da ta farka babu ta yanda zata iya wani ƙwaƙwƙwaran motsi tukunna duk suka fice daga ɗakin suka barta ita ɗaya suka rufe da key.
Fillo dai bata farka ba sai da ana tada iƙama na sallar asuba, a hankali ta buɗe idonta da ƙyar ta shiga bin ɗakin da kallo, tana jin kanta yay mata wani irin nauyi, ga warin wani abu a ƙofofin hancinta, gaba ɗaya wani irin ciwo jikinta keyi mata tamkar wadda aka ɗau kwanaki ana duka, ta rufe idonta ta rumtse sose sannan ta buɗe tana jin eyelid nata yay mata nauyi sosai, sai a sannan kuma ta fara bin ɗakin da kallo har ta sauke ganinta akan roof na ɗakin, sose take kallonsa da mamaki sannan ta ƙara juyar da ƙwayar idonta ta sauke akan ƙofar ɗakin, daga roof ɗin har ƙofar basa cikin irin waɗanda ta sani, ba ƙuma sa cikin inda tasan tana kwana. daga paint na ɗakin har kan gadon da take duk bata san su ba, to aina take?.
tana ci gaba da bin ɗakin da kallo tana so ta tuna a inda take, da kuma yacca akayi tazo nan ɗin amma ta kasa, ƙwaƙwalwarta gaba ɗaya ta cunkushe taƙi yin tunanin abinda take so. sai tayi ƙoƙarin motsawa don ta tashi amma sai taji ta kasa, ta ƙara yunƙurawa taji babu ta yanda za'ai ko da hannunta ya motsa balle ƙafarta, wannan ya tabbatar mata da cewar a ɗaɗɗaure ta ke gaba ɗayanta.
sai sannan tayi ƙoƙarin buɗe bakinta tayi magana shima sai taji bakin a liƙe yake, ta hanci kawai ta ke numfashi banda baki. sai ta rufe idonta tana juyar da fuskarta ɗayan side ɗin sannan ta buɗe idon, nan ta ƙara tabbatar da bata san ina ne nan ɗin ba, take ta fara kokawa da numfashinta saboda tsoro, dai-dai lokacin kuma taji ana sallamewa daga sallah a masallaci, sallar da ta fahimci sallar asuba ce tunda raka'a biyu taji anyi, cikin kanta taji ƙwaƙwalwarta na biyo mata innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, kuma a hankali cikin ikon ubangiji tunanin abinda ya faru da ita ya dawo mata.
sai ta rumtse idonta hoton komai na haska mata tarr tun daga ɗora wuƙa a maƙoshinta, da shigar da ita cikin mota, da kuma juyowa da akayi aka toshe mata hanci. take tayi ƙoƙarin ƙwalla razananniyar ƙara sai taji ashe fa bakinta a manne yake.
to Ina ne nan ɗin?, waɗanda suka ɗaukota su waye?, me yasa suka yi mata irin wannan ɗaukowar?, nan ɗin da suka kawota me zasu yi mata?, me yasa suka ɗaɗɗaureta haka har da toshe baki?. tarin tambayoyin da ta yiwa kanta kenan, kuma take ƙwaƙwalwarta ta bata amsa da,_"you have been kidnapped"._ take kuma zuciyarta ta ƙara maimaita mata innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
ƙirjinta ya dinga bugawa hawaye nabin kuncinta, tashin hankalinta ɗaya shin wanne hali Kaka ta ke ciki yanzu?, Wanne hali Amir yake ciki?, wanne hali Maijidda da Yami suke ciki?, ya Hajiya Madina zata kasance idan ta dawo taga babu ita?.
idan har kidnappers ne suka ɗauketa shin sunyi contacting da wani nata?, wa suka tuntuɓa?, adadin nawa suka nema kuɗin fansarta?, wa zai biya maƙudan da suka ambata?, sai brain ɗinta ta ƙara biyo mata innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Hasbunallahu wani'imal wakil.
ta buɗe idanunta ruwayen hawayen ciki na samun damar gangarowa, kuma a sannan ta fahimci hasken dake ta wajen window da take gani gari ya fara wayewa kenan?.
take kuma ta tuna da cewar fa bata yi sallar magriba da isha'i ba, ga asuba ma a kunnenta akayi amma bata yi ba.
taja ƙafafuwanta da suka sandare tana so ta lanƙwasa su sai taji kamar zasu karye idan tayi hakan, saboda azabar ciwon da suke yi mata. babu ta yanda zata iya miƙewa ta tashi ko da zaune ne, balle kuma ta iya sauka daga kan gadon, dan haka kawai sai ta fashe da kuka sosai, can bayan wasu awanni taji muryar mutane ƙasa-ƙasa a bakin ƙofar ɗakin.
Ta juyo da fuskarta tana kallon ƙofar, tana kallo aka turo ƙofar mutane uku suka shigo, Ƙaton cikinsu shi ya fara shigowa tukunna wasu sirara suka biyo bayansa bayan ɗayan cikinsu ya maida ƙofa ya rufe. tana kallo su suka ƙaraso bakin gadon, Ƙaton ya jawo wata kujera ya zauna yana facing ɗinta, tana kallo yaywa ɗaya daga cikinsu alama wanda shine duk yafi siranta a cikinsu, ya zagayo daga bayansa ya hau kan gadon ya ɗagata ya zaunar da ita, sai a sannan ta sami damar ƙarewa inda take kallo da kyau da kuma mutanen dake tare da ita fuskokinsu duka a rufe.
ƙatoton ya auna Fillo da bakin bindigar da take hannunsa yace,"zamu buɗe maka bakinka, idan har muka buɗe kayi wani yunƙuri na yin magana ko kuma ihu sai na fasa kanka da alburushi". Ya faɗa muryarsa da ƙarfi har tana amsawa a ɗakin, sai dai kana jin hausar tasa kasan riƙaƙƙen inyamuri ne.
hawayen Fillo ya ƙaru akan fuskarta, tana jijjiga masa kai alamar taji me yace cike da tsanin tsoro gami da tashin hankali.
Ƙaton ya kalli tsamurmurin dake kan Fillo tsaye yay masa alama da bakin bindigarsa. take tsamurmurin yasa hannu ya ɗaye masking tape dake manne da bakin Fillo, tsananin azaba yasa ta rumtse ido don ji tayi kamar ya haɗo da fatar bakin nata ne ta cire.
so ta ke tasa hannu ta shafa wurin ko ta sosa amma babu dama, tunda basu kunce mata hannu ba, saboda haka sai ta rumtse idonta sosai tana jinginar da kanta da bango har sai da taji zafin ya lafa tukunna ta buɗe.
ta buɗe ido ta sauke kan ƙaton mutumin dake latsa waya, rabin fuskarsa rufe take da hanky, tana kallo ya ɗaga hannunsa, ɗayan mutumin dake tsaye tun ɗazu a bayansa ya zagayo ya dire kwanon abinci a gabanta da pure water guda ɗaya. sai tabi kwanon abincin da kallo sannan ta ɗago ta kalli ƙaton dake saita da ita da bindiga, ya zare mata manyan idanuwansa yace,"buɗe kaci".
tana ƙoƙarin danne kukanta tace,"dan Allah zan fara yin sallah tukunna". mutumin ya sunkuyo da fuskarsa kusa da tata, a tsawace yace,"kaga nayi kama da wanda ke yin Sallah?, to nan wurin da kake gani ba'a sallah, ko adu'a muka ji kayi sai mun ɓula kanka da alburushi. adu'a ɗaya muka yarda kayi shine a biya kuɗin fansarka, daga wannan bamu yarda da kowanne kalan adu'a daga bakinka ba, do you hear me well?".
da sauri ta ɗaga kanta sai dai bata jin zata iya ta zama haka ba tare da sallah ba, don haka ta ƙara buɗe baki tace,"nayi muku alƙawarin wallahi ba zanyi wani motsi ba, ko adu'ar ficewata daga nan ma ba zanyi ba muddin ba zaku cutar da ni ba, amma don girman Allah ku barni nayi sallah, ko magriba da isha'i na jiya banyi ba".
tana rufe baki mutumin ya buga mata bindigar hannunsa a bakinta yace,"only when you are out of here shine zaka je kayi ta sallolinka, but not in this place, sallah acikin wurin nan is prohibited from you".
sai kawai ta fashe da kuka sose tare da faɗin,"to su waye ku?, Me nayi muku?, Me kuke so tare da ni?".
ƙaton mutumin ya bushe da dariya yace,"mu kidnappers ne, kuma ba zamu sakeka ba har sai an biya kuɗin fansarka naira miliyan biyar, idan kuma ba'a biya ba zamu yi gunduwa-gunduwa da namanka sannan muka aikawa da iyayenka".
cikin matsanancin kuka Fillo ta ambaci kalmar innalillahi a karo na babu adadi tun bayan farkawarta, suna batun miloyan biyar kafin a karɓeta. wa take da shi da zai biya waɗannan maƙudan kuɗin?, me Kaka zata ɗaga ta siyar a sami waɗannan kuɗin?, ta san babu me biyan waɗannan kuɗin a karɓeta kamar yanda babu abinda Kaka zata ɗaga ta siyar a sami wannan uban kuɗin.
saboda haka sai kawai ta rumtse ido tana jin tana sallamawa da duniyar, ita kuma haka kalar ƙaddarar take?, fatanta guda ɗaya ko da ace ba zata fita anan tana roƙon Allah yasa kar mutanen su cutar da ita su rabata da mutuncinta, a hankali yanda ba zasu ji me tace ba ta furta,"Ya Allah ka fitar da ni daga gurin nan cikin amincinka da salamarka".
Ƙaton mutumin ya ƙara sakar mata tsawa yana cewa,"buɗe abinci kaci". tana kuka cikin firgici da razanin da take ciki tace,"babu ta yanda zanci ai".
sai a sannan ya tuna da cewar a ƙulle take, ya daɗa kallon wanda ke tsaye kanta ya bashi umarnin kunceta.
cikin zafin nama tsamurmurin ya kunceta kamar zai wurgata ta faɗo ƙasa, sanda ya gama kunceta ɗin sai ta sauke ajiyar zuciya saboda relief da ta samu, ta kama hannun nata tana shafawa, jinin da ya daskare waje ɗaya na saki yana bin ko'ina, kamin a hankali taji dama-dama.
ba ta so ya ƙara yi mata tsawa don haka ta ɗauka pure water ɗin ta kuskuren bakinta ta zubar da ruwan a jikinta, sannan ta janyo kwanon abincin ta buɗe, taliya ce jallof babu kyan gani, lokaci ɗaya taji zuciyarta ta tashi, amma saboda babu yanda zata yi dole ta shiga cusawa a bakinta tana taunawa da ƙyar.
ganin ta fara cin abincin suka tashi suka nufi ƙofa zasu fita, tai ƙarfin halin cewa,"bani da kowa sai Kakata, ku taimaka min dan Allah".
suka mata shiru suka fice suna rufe ƙofar, sai kuma taji an ƙara buɗewa ƙaton mutumin ya leƙo yana faɗa mata,"if you dare try to make any sound, i swear I will fill your brain with this". ya faɗa yana mata nuni da bindigar hannunsa, kuma ta tabbata he means it.
taji alamun an saka key a jikin ƙofar which means sun ƙulleta kenan, sai ta ture kwanon abincin dake gabanta, tabi ƙafarta da kallo tana noticing yanda ta kumbura sosai, ta jawo ƙafar da ƙyar tana shafata sannan tayi ƙokarin zuro ƙofar ta sauko daga kan gadon tana tsayawa akanta.
da ƙyar taja ƙafarta bayan ta ɗauko pure water ɗin ta isa bakin wata ƙofa da ta gani acikin ɗakin, daban da wacce suka shkigo. ta kama handle ta buɗe ƙofar a hankali sai taga banɗaki ne, tai saurin faɗawa ciki tai tsarki sannan tayi alwala ta fito.
ɗankwalinta tasa ta tattare ƙasan wajen, bata san ina ne gabas ba, kuma lokaci ɗaya maganar Amir ta haska mata sanda yake cewa shi addini ɗan sauƙi ne, idan ka tsinci kanka a garin da ba naka ba, kuma babu mutane a wajen da zaka yi sallah balle ka tambaya, to kana iya fuskantar ko'ina ne ka tada sallarka, don haka ta fuskanci inda take jin yafi kwanta mata ta tada sallarta da babban mayafin dake jikinta, sai da ta rama sallolin jiya dake kanta tukunna tayi asuba ta kuma yi sallar wadha ɗin da bata wuceta.
Bayan ta idar bata yi saurin tashi a wurin ba sai da tayi dogayen adduoi sannan tai saurin miƙewa ta koma kan gadon gudun kar su dawo ɗakin su sameta.
ta zauna da yaƙinin duk sanda suka kawo mata abinci zata yi amfani da ruwan wajen yin ibadarta. kuma zamanta kenan cikinta ya murɗa, tasan ba komai bane face yunwa, kuma take sai amai saboda tuntuni take jin zuciyarta na tashi saboda wannan farar taliyar da ta ci mara ɗanɗano.
har yanzu tunaninta guda ɗaya ne, ta ina zasu fara neman wanda suke saka ran zasu biya kuɗin fansarta?, alhalin a wannan duniyar babu wanda ya san da su banda Allahn da ya halicce su.
a can ɓangaren kuwa tunda gari ya waye ƴan sanda suka ƙara tsananta bincikensu, har sannan kuma ba'a sallami Hajiya Madina ba don ita tace gwara a barta a asibitin har sanda za'a ga Fillo sannan ta koma gida ta iya haɗa ido da Kaka, amma banda cikin critical situation ɗin nan da suke ciki.
sai dai tunda ta farka ta tashi da zullumin ko zasu ji labarin cewar an ganta, amma police ɗin na daɗa faɗa musu shiru babu labarin yarinyar, sai dai sun sanar da Baffa cewa za su cigaba da bincike insha'Allah, kuma ganin har rana tayi still babu wani labari ya saka dole aka sanar da Kaka halin da ake ciki.
ba Kaka kaɗai ba, hatta ƴaƴan Hajiya Madina sai a sannan suka san abinda ya faru banda Khalil da ya san komai tun a jiya. dan Baffa ce musu yayi sun ɗauki hanyar abuja a lokacin Maama na da seminar a gobe ƙarfe 8.
Kaka dai mutuwar zaune tayi daga inda take, tabi Hajiya Madina da Baffa da Khalil da kallo, kamar dai bata fahimci zancen da suke mata ba, kamar ba dai-dai taji ba, kamar suna so suce Fillo ta ɓata tun daren jiya kuma har zuwa yammacin yau ba'a ganta ba, wannan mummunan labari ne, kuma bata tunanin waɗannan salihan bayin zasu iya zuwar mata da shi.
Hajiya Madina ta fashe da kuka ganin yanda Kaka ta daskare, tana cewa,"ki yafe min Kaka, wallahi ban san hakan zata faru ba da ban fita da ita ba".
Yami dake tsaye itama ta kasa motsi take kallon Maama da tausayawa tace,"ki daina kuka Hajiya, tsautsayi ne, kuma cikinmu babu wanda bai san ƙaddara ba me kyau ko mara kyau".
sai sannan hawaye ya sauko a fuskar Kaka, dai-dai take ji da gaske faɗa mata suke jikarta ta ɓata, tayi inda ba'a san ta nufa ba, kuma yini guda babu ita babu labarinta.
cikin muryar kuka tace,""Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, ya Rahimu ka bayyana mana yarinyar nan a duk inda take, ka dawo da ita garemu cikin amincinka".
ta faɗa tana mayar da idonta kan Hajiya Madina tace,"ki daina kuka Hajiya, ba ki da laifi ko ɗaya, dama ubangiji tuni ya shirya faruwar hakan, ko ace bata dalilin fitarku ba, ni musulma ce nayi imani da ƙaddara, saboda haka ki daina ɗorawa kanki laifi, ki share hawayenki don Allah, adu'a kawai ya kamata muyi Allah ya tsareta a duk inda take ya kuma dawo da ita garemu cikin amincinsa".
sannan Kaka ta ƙara maida dubanta ga Maijidda dake ta uban kuka, tace da ita,"ki kira Amir a waya ki sanar masa".
Yami tace,"a sanar masa kuwa?".
Kaka tace,"to ɓoyuwar ai babu amfani, gwara a faɗa masa ɗin sai su shigar da adu'a kafin tashin ɗalibai a makaranta".
Yami tace,"haka ne kuma, tunda su gidan malamai ne ko saukar ƙur'ani a iya yi cikin ƙaramin lokaci".
Maijidda ce ta kira Amir, kuma tun kamin ta sanar masa yasan babu lafiya tunda yaji muryarta tana kuka. kuma zata iya rantsewa da ta faɗa masa faɗuwa yayi a inda yake saboda yanda taji ya saki salati a gigice.
ƙarar salatin da kowa sai da ya jiyo daga cikin wayar, wannan yasa Kaka ta ƙara ruɗewa hankalinta yayi ƙololuwar tashi.
kowa dai a wajen yayi shiru,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 32 Chapter of 73