ta banka ma ta harara kafin tace,"ban ce fa lallai sai kin gaishe ni ba. saƙon Amadu nazo isar miki, yace wannan aljanar jikar taki ta tattara komatsanta ta bar masa gida kafin ya dawo, idan kuma kika yi kuskuren da yazo ya sameta acikin gidansa to sai dai kotu ta raba shi da iyayenta, saboda shi dai bakin uwa bai bishi ba da za'azo har gida aci mutuncin uwassa".
Ammi tace,"ai dama ba kwana zata yi ba, anjima kaɗan za'a zo a ɗauketa".
"to shi yafi dai, yauwa ta bar gidan nan tun ba'a ƙure haƙurin ɗana ba, yo me ma na haɗa da ita da zata zo ɓangare na tayi min sata?, da ike ma dai ina da bala'in haƙuri shiyasa, don ma ban faɗa miki ba ne Zainabu, amma ƴar nan ƙafafuna biyu duk ta karya min, ban da Allah ya kawo Aliyu akan lokaci da ban san wa zai jona ni ba in samu in miƙe, amma dai na dai barwa Allah kawai".
Ammi tace,"kiyi haƙuri Inna".
"yo haƙuri ai dole tunda ni ba fitinanniya ba ce, kawai dai kija mata kunne kar ta ƙara zuwa gidan nan tunda batta da gado".
Ammi tace,"to".
"yauwa to sai anjima, zamu je wurin sarkin ɗori da Aliyu ne".
"Allah ya sauƙe".
"to amin Zainabu, na gode. amma ke ma dai sai kin rinƙa kulawa, in ba haka ba wataran tsaf zata jeho ki daga saman bene, tun naga aljanunta masu wurgi ne".
zata fita a ɗakin Maama ta buɗe baki, cikin ƴar ƙaramar muryarta tace,"a dawo lafiya Inna, Allah ya bada lafiya".
"amin in ma ba har zuci kika faɗa ba. ƴar banza da wofi me suffar ƴaƴan aljanu, kina fama da ƙaramar murya sai kace kukan mage, Allah ɗaya ma yasan manufar da yasa yayo ki a makauniya, sanyin tafiyar da aka ba ki ai ba'a banza ba, idan kin cuceni kin tsira kika cuci wani kafin kiyi taku biyu ai ya danƙo ki yaci ubanki. Allah dai ya jiƙan Uwarki ya gafarta mata, amma wannan halin dai ba nata ba ne sam".
ta fita tana ta zazzaga masifa, Maama da Farha kuwa sai dariya suke yi, bayan fitarta sai ga Ayan ya shigo, ya zauna kan kujera, bayan sun gaisa da Ammi take ce masa,"ni ai fushi nake da kai, yaushe rabon da kazo ka gaida ni?".
yana murmushinsa me kyau yace,"Ammi tare da Abie muke zuwa office shiyasa, kuma yau ɗin mun makara wajen zuwa gun Ummi ne shiyasa ban shigo ba a lokacin".
sai ya kalli Maama yace,"ki taso mu tafi".
Ammi tace,"da wuri haka?, ba zai bar min ku sai dare ba?".
"Ammi zamu je dubo Maman su Antynmu ne".
Ammi tace,"Allah sarki wannan mata dai tana shan wuya, Allah ya kawo mata sauƙi".
"amin".
Ammi ta rako su har bakin gate, Farha kuwa sai da ta raka su har bakin motarsu, har sai da suka gaisa da Turaki sannan ta juya ta koma gida, su na yiwa juna bye bye ita da Maama.
"Abie kun gaisar min da Ummin?".
Maama ta tambayi mahaifin nata a lokacin da motar su ke hawa kan titi.
Turaki ya dubeta ta cikin mirror yace,"mun faɗa mata Maama".
sai kuma yace,"Maama ko dai muje asibiti?".
ta bar abinda take yi ta kai dubanta gare shi tace,"saboda me Abie?".
yay ɗan jim kafin yace,"ina ga kamar ayi miki aiki a maƙogoronki, Maama muryarki tayi ƙanƙanta da yawa, wanda ya saba da ke ne fa kaɗai yake iya jin me kike cewa farat ɗaya".
tayi knodding kanta tare da cewa,"Abie idan hakan yana damunka ayi min duk abin da kake so".
ya numfasa kafin yace,"ba komai zamu ci gaba da zuwa gaban ka'aba muna roƙon Allah".
tafiyar tasu tayi nisa acikin motar, yayin da suke hira jefi jefi, har sanda Turaki ya tambaye su,"ina da ina zan kai ku?".
da yake duk friday haka yake kai su gidan ƴan uwa da abokan arziƙi ziyara, ko kuma wani lokacin su yini shi da Ayan a maƙabarta wajen Fillo da Maama, sai in yamma yayi yaje gidan su Yusuf wajen Ammi ya ɗauko Maama da suke sauketa acan tun safe.
Ayan yace,"Abie muje gidan Anty Maijidda, kwana biyu bamu je ba, kuma last zuwa da muka yi mun barota bata da lafiya".
Turaki ya amsa masa da to, sai da suka fara tsayawa a hanya suka yiwa ƴaƴan Maijidda siyayya kafin suka ɗauki hanyar gidanta.
Turaki ya ba su kuɗi masu yawa su kaiwa Maijidda kamar yanda ya saba duk sanda ya kawo su. sai da yaran suka shafe kusan rabin awa kafin su fito tare da Maijidda wacca ta rako su.
hangota yasa Turaki fitowa daga mota, ya ƙarasa ƙofar gidan suka shiga gaisawa da ita, tana ta yi masa godiya akan irin aiken da yake bayarwa akawo mata ita da yara.
Maama na kama hannunsa ta riƙe yake tambayar Maijidda yaranta, ganin yau bai ga ko muutum guda ya rako su Ayan ba, da kuma ɗan ƙaramin ɗanta da ya zama kamar abokinsa, kasancewarsa irin yaran nanne masu saurin sabo.
Maijidda tace,"wallahi kaga wata tahfeez aka buɗe a bayan layin nan, shine aka kaisu can".
"har friday suke zuwa kenan?". Turaki ya tambaya.
tace,"ehh juma'a zuwa lahadi, tun safe sai yamma".
"masha'Allahu, Allah ya bada ilimi me albarka".
ta amsa da,"amin amin".
"to bari mu wuce, a gaida min da abokina".
tayi ƴar dariya tana faɗin,"Musaddiq sarkin magana, zai ji insha'Allahu, da sun samu hutu ai zan kawo muku su, sai su yini".
sai ta saka hannu tana share ƙwallar fuskarta tace,"Allah ya jiƙan Fillo".
Turaki da Ƴaƴansa jiki a sanyaye suka amsa da,"amin ya Rahman".
tukunna suka yi mata sallama suka wuce, inda suka ɗauki hanyar gidan Me Martaba domin zuwa duba Fulani Azima, wacca har yanzu ta nan kwance rai a hannun Allah, gaba ɗaya halittarta ta sauya ta koma tamkar ta ƙadangare, sai ka rantse da Allah ba mutum ba ce tun asali, wasu gashi sun tsatstsafo mata a jiki, idanunta sun yo waje ƙwayar kamar zata faɗo ƙasa, bakin da hancin sun shafe a waje ɗaya, kai abun dai babu kyan gani da kwatance.
ga duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata ya zubar mata da hawaye idan bai san abun da ta shuka ba, wanda kuwa yasan me ta aikata muddin ya ganta sai jikinsa ya mutu gaba ɗaga, tsoron Allah ya ƙara shigarka, kaji gaba ɗaya duniyar ta fita a ranka, balle kuma kaji kana son sha'awa ko mallakar abun da ke cikinta.
Maama da ke kallon bakin titi tace da Turaki,"Abie don Allah zan bayar da sadaƙa".
Turaki yay parking a gefen hanya, ya zaro ɗari biyar a aljihunsa ya miƙa mata ta karɓa sannan ta buɗe mota ta fita. "na gode Abie".
ƴar tafiya kaɗan tayi daga inda motar tasu ta tsaya, ta tsuguna agaban almajirin ta saka masa kuɗin acikin robarsa tare da faɗin,"Baba kayi adu'a Allah ya kai ladan ƙabarin mahaifiyata".
tsohon ya shiga kwaranyo mata adu'a iya adu'a, daga mahaifiyartata har ita kanta da sauran ahalinta. ta ɗaga glass ɗinta tasa tissue ta goge hawayen da ya cika mata ido, kafin ta yunƙura ta miƙe jiki a sanyaye ta bar wajen nasa.
tana cikin tafiya tayi karo da mutum, ba wai don bata ganin gabanta ba, sai don hankalinta da ya bar jikinta a lokacin.
ta sunkuya ta lalubo gilashinta ta saka, sannan ta kalli mutumin da ta tsorata da ganin nasa, tayi saurin matsawa gefe tana ce masa,"kayi haƙuri don Allah".
muryartata ƴar ƙarama kuma ƴar siririya me zaƙi ta fito ta shiga kunnen Amir ta ratsa jikinsa, ya kasa ƙifta idonsa akanta, kallon mamaki kawai yake yiwa yarinyar gabansa, wacca gaba ɗaya yasan bata kai shekara sha bakwai ba.
abun da ya sani shi ne ya san wannan halittar, sai dai bai yi tsammanin zai sake ganinta a haka ba duba da tsawon shekarun da aka ɗauka, ya sani Fillo na da ƙaramin jikin da ba lallai shekarunta masu yawa su nuna a jikinta ba. to amma duk da haka abin da matuƙar mamaki ace ita ce a gabansa haka, babu wani alamar girma a tare da ita, after all shekaru goma sha bakwai ɗin da ya ɗauko bai ganta ba.
jikin Maama na rawa ta daɗa ce masa,"zan wuce".
Amir yay ajiyar zuciya bayan ƙare mata kallon tsab da yayi, tabbas wannan ba asalin Fillon da ya sani ba ce, wannan me kama da ita ce sak babu wani banbanci, sai dai in ace banbancin halayya, me hakan ke nufi kenan?, wata ce photocopy of her ko kuma ƴarta ce?.
lokaci ɗaga matacciyar zuciyarsa da babu tsoron Allah acikinta taji ta kwaɗaitu da yarinyar, yaji sha'awarta ta ratsa duk wani ɓargo na jikinsa, take kuma ya fara tunanin ta yacca za'ai ya shiga rayuwarta a irin matsayin da ya saba shiga rayuwar sauran ƴan mata?, ya shiga rayuwarta kamar dai yanda ya shiga rayuwar me kama da ita.
_(hmm Allah ya kyauta, ya kuma kiyashe mu daga sharrin zuciya, dama haka abun yake, ance wasu ko zasu je lahira su dawo halinsu ba zai taɓa canjawa ba, sai dai muyi adu'ar Allah ya tsare daga sharrin mugwayen mutane.)_
sai ya sauke idonsa akansa yana kallon jikinsa, wannan sam ba wancan Amir ɗin ba ne me ji da tashen ado da ƙwalisa a zamanin baya, wannan wani Amir ɗin ne na daban, wanda halittarsa ta sauya tun yana cikin prison, ya dafe ya zama mugun baƙi, yay wata muguwar rama kamar me cutar S, ya haɗa uwar ƙasumba a fuska kamar dodo, haka kansa ma ya tara uban gashi kamar mahaukaci, duk yayi duƙunduƙun kayan jikinsa duk a yayyage, ga uban ɗoyi da ke tashi a jikinsa kana ji kasan kwanan bola yake yi.
warin jikin nasa ya doki hancin Maama, take ta duƙa a ƙasa saboda aman da ya taho mata, ta shiga kyalaya amai kamar hanjin cikinta zasu fito.
Amir ya duƙa a gaban nata shi ma, zuciyarsa na harbawa kaɗan kaɗan, abu ɗaya yake tunani wanda yake jin har in ya rasa zai iya shiga wani hali, halin da yafi wanda yake ciki muni, muddin bai samu ya kusantu da yarinyar ba zai iya rasa lafiyar jikinsa.
don haka zuciyarsa na ingiza shi ya kai hannu zai taɓa Maama tayi saurin miƙewa tana ja da baya.
"mene haka?, na fa baka haƙuri".
ya miƙe yana lashe leɓe, a hankali yace,"Ki tsaya na taɓa jikinki don Allah ko ya ya ne, idan na taɓa zan haƙura na barki ki tafi".
Maama ta shiga girgiza masa kai tana ja da baya, yanzu kam ya gama tabbatarwa ba Fillon da ya sani bace, kuma ko da ace ita ɗin ce ma ba zata taɓa gane shi ba, don kwatakwata ya fita a Amir ɗin da mutane suka sansa, shiyasa har yanzu ma Ƴan sanda suka kasa kama shi bayan wani laifin da ya ƙara aikatawa lokacin da ya fito a prison.
"sau ɗaya yarinya, sau ɗaya kawai za ki barni in taɓa ƙirjinki, ki tausaya min wallahi a bola nake kwana".
yayi maganar da kana ji kasan ƙwaƙwalwarsa ta fara taɓuwa, lokaci kaɗan ya rage ya fara hauka tuburan.
san da Maama ta kai ƙarshe ajikin wani ƙarfe, lokacin Ayan da Turaki suka iso waje, tana ganinsu ta ƙwala kiran Abie, Ayan yasa hannu ya juyo da Amir, da yake irin tsayin mahaifinsa yayo sai ya zamana tsayinsa yay daidai da na Amir ɗin.
cikin zafin nama Ayan yasa hannu ya wanke fuskar Amir da zazzafan mari, ya damƙi ƙwalarsa yana jijjiga shi har sai da ya kai Amir jikin ƙarfen da ke bayansu ya buga kansa a jiki.
"kai ba mahaukaci ba ne zuciyata ta faɗa min hakan, ubangiji yayi min baiwar gane mutane a kowanne hali suke ciki. sai na kasheka tun da ka yi yunƙurin taɓa min ƙanwata".
ya faɗa yana ta buga kan Amir ajikin ƙarfen, Turaki kuwa na gefe rungume da ƴarsa a jiki zuciyarsa sai zafi take yi masa, idan har yace zai kai hannu ya taɓa Amir to bai san me zai ya faruwa ba, don wataƙila kafin ƴan sanda su iso wajen ya kashe shi.
ɓangaren Amir kuwa abu guda ɗaya ya sani, ba zai taɓa iya ƙwatar kansa ba a hannun Ayan, bai da wannan ƙarfin ko kaɗan, hatta ruƙon da yaron yay masa ji yake kamar an jona masa electricity.
zuwan police wajen suka ƙwace Ayan da ga kan Amir wanda yake ƙoƙarin kaiwa ƙasa. banda haki babu abin da Ayan ke yi, idonsa yay jawur kamar bana ƙaramin yaro ba, police suka kama hannun Amir suka saka masa ankwa, sai a yanzu idonsa ya kai kan Turaki, yaji gabansa yay mugun faɗuwa, ya wurga ido ya ƙara kallon Ayan, jini ba banza ba, don lokaci guda ya tuna da mugun dukan da ya sha lokacin da suka yi kidnapping Fillo.
don haka tsananin tsoro ya kama shi, ya tabbatar yanzu idan Turaki ya gane waye shi to sai dai waninsa, dan haka gwara yabi ƴan sandan, duk runtsi zai fito ya sani.
police su ka kama Amir suka saka shi a mota suka tafi. bayan su Turaki sun dawo daga dubiyar Fulani Azima, direct gidan ya wuce da yaransa, in da anan suke cin abincin dare duk friday.
ana jin tsayuwar motarsu Boɗejo tace,"to ga kajin nan sun iso".
Mum na zaune kan kujera, da jaririyar Nihal a hannunta ta gama yi mata wankan yamma, tayi murmushi da jin furucin Boɗejon.
Turaki ya shigo tare da yaransa, waɗanda sai da suka fara zuwa ɓangaren Baffa suka gaida shi.
jikokin gidan duk suka yi wajensa su na yi masa sannu da zuwa, ya ɗauki ƴar gidan Zaytuna me suna Aisha.
Maama tayi jikin Boɗejo tana cewa,"nayi kewar tsohuwa".
Boɗejo tace,"kinga ni kuwa yau ba wanda nayi kewa a cikinku, ko babu komai bakina da na Kakarku luff babu rabon faɗa".
"ai kuwa tun da kika faɗi haka ba zan ba ki abin da na taho da shi ba".
Boɗejo da a yanzu ta ƙara zama tsohuwa tukuff ta janyo Maama jikinta tana faɗin,"haba ƙawata ƴar mutunci yi haƙuri, ai yanda bana iya fita inci ni ɗaya ban rage miki ba haka kema na sa ni".
Maama ta dubi Turaki da ya zauna akan kujera su na gaisawa da Mum, tace,"Abie ka ɗauko min leda ta?".
ya kalli gefensa yay mata nuni da ledar, sannan ta miƙe taje ta ɗauko, tazo ta zauna ta buɗe ta ɗauko dublan ɗin ciki tana bawa Boɗejo, wacca ke tambayar aina suka siyo shi, ita kuma tana bata labarin yacca ta kwaso shi a ɗakin Inna Wuro.
da daddare bayan sun gama cin abincin dare, suka fara haramar tafiya gida.
Mum ta juye musu sauran teba da miyar gandar da akayi a flask tace su tafarwa da Ilham.
ko da suka koma gida Turaki ajiye su yay ya ƙara fita, ya tafi siyo magungunan da likita ya rubutawa Ilham, wacca likitoci suka yi iyaka bincikensu akan rashin haihuwarta, suka tabbatar da cewa da wuya idan ta haihu sai in kuma wani iko na ubangiji.
tana zaune a parlo tana kallo su Ayan suka shiga, tayi musu kallo ɗaya ta ɗauke kanta taci gaba da kallon film ɗin da ake yi a mbc action.
ganin bata kula su ba Ayan yace,"Anty daga wurin Maminki mu ke".
furucin nata yasa ta mayar da hankalinta gare shi tana jin cewarsa.
"ya ku ka ƙara samun yanayin jikin nata?".
Ayan yace,"ba sauƙi, sai tsanani da ya ƙara. yau da muka je jini yana ta zuba ta duburarta, sai botiki aka tara mata ma a wajen, ta ƙara motsewa babu kyan gani".
Ilham ta saka kuka sosai tana kifa kanta akan ƙafafunta, tsawon minti biyar tana kuka kafin ta ɗago tare da ɗaukar wayarta ta shiga kiran lambar Turaki, sau kusan sau biyar kiran yaƙi shiga, ana ta faɗa mata not recherble.
ta kalli agogo taga ƙarfe tara da rabi a lokacin, ta miƙe ta wuce ɗaki, ba jimawa sai gata ta sakko sanye da hijab. ta kalli yaran tace,"idan Babanku ya dawo kuce masa na tafi wurin Mami. ku faɗa masa ina ta kiran wayarsa taƙi shiga".
su ka amsa mata,"to, a dawo lafiya".
"Allah yasa". ta faɗa tana nufar ƙofar fita, maganar Maama ta dakatar da ita,"Anty ko za ki tafi da tebar?".
ta kalleta tace,"Mum ce tayi?".
"ehh".
"Maama ba zan iya ci ba, ku cinye idan kuna so. akwai pancake a kitchen na ajiye muku, ba kwa buƙatar wani abu?".
suka haɗa baki wajen faɗin,"ba ma buƙatar komai Anty".
ta kalli Ayan tace,"saura ka sakata kuka".
yay ƴar dariya yace,"Anty wai haka kawai nake sakata kukan?, sai fa tayi min ba daidai ba".
tayi murmushin ƙarfin hali kawai ta fice ba tare da ta ƙara ce musu komai ba.
sai wajen goma Turaki ya dawo gida, yana shigowa parlo ya tarar da Ayan akan Maama yana zazzaga mata masifa.
"dilla Malama bani abu na, na rantse da Allah daga yau ma kika ƙara taɓa min kaya sai na faffasa miki baki, kin dai ji na faɗa miki".
ya faɗa yana sakin ƙwafa me ƙarfi, sai kuma ya saka hannu ya dungure mata kai glass ɗin idonta ya faɗi, a rikice ta durƙusa tana neman glass ɗin.
ta lalubo shi da ƙyar ta saka, ta turo ɗan ƙaramin bakinta gaba tana hura hanci tace,"kuma wallahi idan Abi ya dawo sai na faɗa masa".
tana ƙoƙarin raɓawa ta gefensa ta wuce, ya fincikota yana faɗin,"ɗauko min kayana ki bani".
ta fizge tana faɗin,"ba zan ɗauko ba ɗin".
a zuciye Ayan ya ɗaga hannu zai mareta muryar Turaki ta dakatar da shi.
"Ayan!". ya kira sunansa da ƙarfin sauti wanda hakan yasa Ayan ɗin nutsuwa.
"me ta taɓa maka da ma?, kai da baka da haƙuri, na faɗa maka bana son wannan zafin zuciyar taka, idan ƙanwarka bata taɓa abinka ba na wa kake so ta taɓa?".
Ayan na faman huci yace,"to Abie ita ce komai ta ɗaukar min sai ta lalata, kalla fa yanda ta fasa min sabon bluetooth ɗina, kuma shekaranjiya da Uncle Bello yazo ya ban shi".
yay maganar yana nunawa Turaki.
"kuma shi ne saboda rashin tunanin akan abun duniya zaka ɗaga hannu kace zaka mareta?, ranar da bana raye a haka zaka kula da ita?".
Ayan yay shiru bai ce komai ba, ya kumbura yayi fam yana tunanin abin da zai yiwa Maama ya huce.
"garin ya kika fasa masa abun sa?".
"Abie ba na sane Allah, nazo sakkowa daga upstairs na zame shi ne ya faɗi daga kunnena".
Turaki ya jefawa Ayan key ɗin motarsa yace,"ka je mota ka ɗauko nawa".
yana rufe baki Maama ta ce,"Abie ni fa?, Farha ta karɓi nawa kuma ba zan iya cewa ta ba ni ba".
"ki bari zan siyo miki wani Maama".
washe gari da safe wajen ƙarfe takwas hayaniyar yaran nasa ta tashe shi daga bacci, ya tashi ya shiga toilet yay wanka, bayan ya fito yazo ya tsaya jikin window yana hango su.
a field suke su na buga basket ball, Ayan na ta yawo da ball ɗin yana dariya, ita ma Maama na ta yawo wajen ganin ta kare ball ɗin daga shiga cikin raga, sai dariya take yi tana cije leɓenta, motsi kaɗan sai ta gyara zaman glass ta karyar da wuya alamun ta fara gajiya.
duhun garin kuma ya fara hanata gani sosai duk da medical glass ɗin da ke sanye a idon nata.
ta durƙusa tana nishi, Ayan ya jefa mata ball ɗin ta ƙwalu a saman kanta, ya kwasa da gudu yana faɗin,"idan kin isa ki biyo ni ki rama ƴar makauniya".
haka yake yi mata sau tari, sai su na waje su na wasa sai ya tsokane ta ya gudu in dai yasan akwai hadari.
zafin ƙwala ball ɗin yasa Maama miƙewa ta ɗauka ball ɗin, ta ƙanƙance ido ta cikin glasses ɗin sannan ta saita Ayan da ya juyo yana yi mata gwalo, ta ɗaga ball ɗin ta jefa masa, ai ko cikin sa'a sai ga ball ɗin a fuskarsa, ta buga tsalle tare da ihu tana faɗin,"wooo ai dai na rama".
shi kuma ya dafe goshi yana faɗin,"yasin sai na faɗawa Abie ciwon idon ƙarya kike yi, ya daina asarar kuɗinsa a siyan glass kina gani tarr".
lokacin kuma hadari ya ƙara ɗinkewa, lokaci ɗaya garin yay baƙiƙƙirin, sai ya zamto Maama bata iya ganin komai hatta da gabanta, hankalinta ya tashi ta ɗaga hannu ta shiga laluben gabanta tana kiran Ayan.
"Ayan please ka zo, kar ruwan ya sauko, bana gani fa".
tana rufe bakinta taji ana yi mata cakulkuli ta baya, tai saurin juyowa don kama shi, sai dariyarsa ta jiyo yana ƙara yi mata cakulkuli ta bayanta da ya ƙara zagayawa.
"yarinyar ki bar min agogon da Ummi ta bar miki sai in taimaka in yi miki jagora".
"to ai tace nawa ne ni ɗaya".
"to shikenan sai ki taho da kanki".
taji yayi shiru babu motsinsa, taita ƙwala masa kira yana gefenta a tsaye yay mata shiru, sai kawai ta fashe da kuka tana ta ƙwala masa kira.
Turaki dake hango su yana murmushi, ya faɗa tunanin wani moment na su shi da Fillo.
kamar haka su na tare a field ɗin su na yin wasan ƴar burin burin, ya ɓace mata tana ta kiran sunansa yay shiru yaƙi amsawa, kuma a sanda ta kunce ɗaurin idon taga bata gansa ba sai ta saka kuka.
kamar dai yanda Maama ke yi a yanzu, sai ya tuna yacca ya dinƙa jin sautin kukan nata na dukan zuciyarsa a lokacin, amma duk da haka bai fito daga ɓoye mata ɗin da yay ba sai da ta shiga parlo.
ta hau upstairs ta gama lalubensa a can baya nan sai ta dawo ƙasa, shi kuma a lokacin ya shigo parlon, su na haɗa ido da ita ya kwashe da dariya sosai ganin yacca hawaye duk ya ɓata mata fuska.
kuma ganin nasa yasa ta ɗauki pillon kujera ta biyo shi, suka shiga zagayen kujerun parlon tana faɗin,"Allah ni ka tsaya in ƙwala maka".
ya tsaya daga bayan babbar kujera yana haki yace,"saboda me to?, wannan ai mugunta ce, kawai sai ki kama ƙwala min pillow bayan kin san da zafi".
"ni dai sai na ƙwala maka".
ta faɗa tana turo bakinta gaba cikin shagwaɓa, tare da dukan ƙafafu a ƙasa hawaye na sakkowa ta ido ɗaya.
sai ya kama ƙugunsa yana kwaikwayon yacca take yi da idanu, hakan ya daɗa tuzurata ta sa kukan shagwaɓa sosai.
cikin dabara ta dinƙa matsawa zata zagaya ta bayan kujerar da yake tsaye, fahimtar hakan yasa shi barin wajen da gudu dariyarsa na ƙaruwa sosai.
"to wai me nayi miki za ki ƙwala min abu?".
ta ɗage gira duka biyu ta ce,"ba kai ba ne ka gudu ka barni ka saka ina ta nemanka ban ganka ba".
"to sai ki bari naki turn ɗin yazo sai ki rama, amma ni dai ba za ki ƙwala min wannan pilon me zafi ba".
"ni dai Allah sai na ƙwala maka ko kuma ka ban haƙuri".
"tabɗijam sannu sara me baƙar takashi, kawai sai in kama ba ki haƙuri kina ƴar ƙarama da ke, bayan in da nayi haihuwar ƙauye da nayi jika da ke".
abin da ya faɗa yasa ta cije leɓe tana tunanin abun da zata yi masa, bata ankara ba taji ya ƙwalo mata pillow a saman ka.
ai kuwa sai ta ƙara fyallawa da gudu zata kamo shi, suka ci gaba da zagaye parlon cikin guje gujen su, shi yana ƙyalƙyala dariya ita tana cewa Allah sai ta rama, har sai da ta koma roƙonsa da Allah ya tsaya ta rama.
sai ya tsaya yana haki yace,"to naji za ki rama, amma kar kiyi min da zafi".
"ehh naji a hankali zan maka".
ta faɗa tana jijjiga ƙafa ɗaya.
sai ya sake yin dariya yace,"habawa yarinya ni za ki yiwa wayo".
yana faɗar hakan iska tayi blowing laluben parlon ya rufe masa fuska, kafin ya buɗe tayi tsalle ta dira akansa, ta cukwikwiye shi suka faɗa kan kujera tana ƙwaƙwƙwala masa pilon, sai da ƙyar ya iya kama hannayenta ya riƙe a cikin nasa.
"sai ance kin iya mugunta kice ke ba haka ba".
"ai har sai ka ban haƙuri zan ƙyaleka".
"ni fa ba zan bawa ƴar ƙaramar yarinya haƙuri ba".
suka shiga kokayawa har sai da tayi nasarar gantsara masa cizo a kunne, zafin cizon ya ratsa shi ya ƙwala ƙara yana faɗi,"i am sorry".
ta ƙara kai masa cizo a hanci tana cewa,"ba haka ba, sai kace don Allah".
ai kuwa ya ƙwalla ƙara da ƙarfi yace,"Don Allah kiyi haƙuri Fulani Nah, haba Fulanin Turaki ƴar albarka".
"waye yay nasara?".
"kece Anty Fulani".
ta ɗaga shi tana dariya sai haki take yi, tana tafa hannu tana cewa,"yau na zama Anty Fulani".
sai kuma ta faɗa saman ƙirjinsa ta tura hannu cikin rigarsa tana yawo da shi akan ƙirjinsa.
cikin muryarta mai sanyi da ratsa dukkan jijiyoyin jiki tace,"Jannaty idan muna wasa karka ƙara ɓace min irin haka, tsoro yana kama ni, bana so in ji
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 72 Chapter of 73