duka acikin kunnenta.
"say something Fulani Nah". ya faɗa yana yawo da yatsansa acikin kunnenta.
bata iya magana ba sai kewaye shi da tayi da hannayenta. hakan ya ba shi damar ɗago da fuskarta, ya ɗora goshinsa akan na ta iskar bakinsa ta fito ta sauka akan lips ɗin ta.
"say you love me Fulani". ta haɗiye yawu da ƙyar cikin mutuwar jiki tace,"i love you Turaki".
murmushi ya suɓuce akan leɓansa, a hankali yace,"Turaki ko?".
ta ɗaga masa kai tana daɗa mannewa ajikinsa.
buɗe lumsassun idawunsa yay, ita ma ta buɗe nata, ƙwayar idonsu ta sarƙe wuri ɗaya yana jin yanda jikinta duk ya mutu, sai ya ɗanyi murmushi yace,"can i?".
ta ce,"what?".
ya ce,"kiss your sweet lips".
ta ɗaga kanta kawai bata ce komai ba, sai ya ƙara sunkuyar da kansa a hankali ya ɗaura lips ɗinsa saman na ta.
lokaci ɗaya taji tana neman barin jikinsa zata faɗi ƙasa, sai ya koma ya zauna kan stool ɗin yana zaunar da ita saman cinyarsa, ya shiga tsotsar lips ɗin tamkar wanda ya sami alawar da baya so ta ƙare.
yana yi yana murza tafin hannunta, sai da yay kissing ɗinta sosai to his satisfaction tukunna ya ƙyaleta, ya saketa a sanda duk su biyun su ke mayar da numfashi, Fillo ta kalle shi da idanuwanta da kamar ba zasu buɗe ba, dan duk jikinta taji ya fara sauyawa, ta ɗan bugi ƙafafu a ƙasa kafin ta juya ta bar masa wajen, ya bi bayanta da wani irin kallo me cike da tarin feelings akanta, ya sauke numfashi yana jin yanda yanayin jikinsa ke daɗa sauyawa.
sai ya miƙe ya bi bayanta cikin mutuwar jiki, tana shirin hawa gadon ta kwanta taji ya rungumota ta baya, ya shiga yawo da hannunsa a jikinta gently,"Fulani Nah this smell makes me body weak". ya faɗa yana yawo da hancinsa a wuyanta yana shinshina humrar jikinta.
tuni jikin Fillo ya ɗauki rawa sosai, ta ɗan fara kuka tana faɗin,"Turaki let me".
cikin muryarsa da ta sauya gaba ɗaya yace,"nooo". ya faɗa tana jin yanda ƙirjinsa ke bugawa a bayanta sosai, ta juyo a hankali tana facing ɗinsa, hannayensa na karkarawa ya tallabi fuskarta ya ce,"please Fulani Nah let's make a love this night".
hawaye ya sauko a kuncinta ta ce,"what kind of love?".
yasa hannu yana sauke hannun rigar ya ce,"allow me to show you".
tayi saurin tura hannunsa tana faɗin,"no, i don't want".
"please Fulani Nah, please don't stop me kinji, promise you i won't go deep, please let us enjoy".
ya faɗa a sanda ya fara aika ma ta da wasu saƙonni, duk sai taji ya bata tausayi ganin ya koma kamar ba shi ba, kamar wanda bai da lafiya yake buƙatar taimakon gaggawa.
tuni ya fara tafiyar da ita cikin salonsa da ta fara jin ƙafafunta na neman gaza ɗaukarta, abubuwan da taji su na neman su rabata da duniyar da take ciki, wasu saƙonni da taji su na nema suyi raga-raga da tunaninta.
ta ji shi lokacin da jikinsa ya fara kyarma sosai kamar me jin sanyi, taji kuma lokacin da hannayensa duka biyu suka shiga cikin rigarta suna tafiya zuwa ƙirjinta, kuma taji san da yace,"can...?".
ba ta bari ya ƙarasa ba ta ɗaga masa kai da cewar,"yes, we can".
abin da bata sani ba shi ne lokacin da ya cire rigar jikinta yay wulli da ita, da lokacin da ya ɗauketa suka hau saman gadon.
abu ɗaya da ta san da shi shine tana mugun enjoying hot romancing ɗin da yake da ita, wanda ke dab da mantar da ita a duniyar da take. yanda ya fita a hayyacinsa haka ita ma, bata dawo cikin hayyacinta ba sai da taji yana neman wuce gona da iri, hakan yasa ta fashe da kuka sosai tana ture shi, ganin yaƙi yana ƙara maƙaleta ta tuna masa da period ɗin da take.
hakan ne ya sa Turaki dawowa cikin duniyarsa, yaja dogon numfashi ya sauke yana bawa katifar naushi, ya rumtse ido gam tare da rugumeta yana sauke ajiyar zuciya.
da ƙyar ya iya buɗe baki yace da ita,"i am sorry Fulani Nah, i am out of mind".
ƙirjinta sai bugawa yake sosai a jikinsa, ta jima tana kuka yana aikin lallashinta, da ƙyar tayi shiru sannan ta fara ƙoƙarin raba jikinta da nasa, ya hana hakan yana faɗin,"ba abin da zan ƙara yi miki, lets sleep to gether ok".
ta ƙyar da suɗin goshi ta yarda amma da tuburewa tayi ita ɗakinta zata koma, don gaba ɗaya a tsorace take da shi, yay ta begging ɗinta, yana lallashi da ban haƙuri tukunna ta yarda tayi bacci ajikinsa.
washe gari da safe kafin ta farka har ya haɗa ma ta kayan da zata tafi da su acikin trolly, sannan ya dawo ya tasheta, ko da ta farka ƙin yarda tayi ta kalle shi, ta sauko akan gadon kawai ta wuce toilet kamar dai tana fushi da shi.
da ta fito yana zaune a bakin gado, ta fita daga ɗakin ba tare da ta kalli in da yake ba. shi ma ɗin kuma bai bi ta ba balle ya takura ma ta, kuma yanda kowa ke da zuciya za su iya yin faɗa, sai ya miƙe ya shiga toilet yay wanka yazo yana shiryawa, dan Mum tuni ta kirasa ta faɗa masa sun ɗauki hanya.
yana zaune yana saka takalmi Fillo ta dawo ɗakin, tunaninsa duk shiryawa ta tafi yi sai ganinta yay ta dawo ɗauke da tray, ta wuce ta dire akan table sannan ta ƙara fita.
ɗaki ta koma don shiryawa, tuni ya fiddo ma ta kayan da zata saka, su na ajiye akan gadon, yau ma abaya ya ƙara ɗaukota ma ta blue colour kalar boyel ɗin da taga ya saka, da murmushi a fuskarta ta ɗauka ta saka sannan ta zauna duba iyakar kayan da ya haɗa ma ta, sai kace mace babu abin da bai saka ma ta acikin trolly ɗin ba, which he knows she will need.
sai da ta gama shiryawa tsaf sannan ta fita ta koma ɗakin nasa sai zuba ƙamshi take yi, samu tayi har ya zuba tea a cup, yau ƙin yarda tayi yay feeding ɗinta, ƙarshe ma bata zauna kusa da shi ba, ta ɗauki soyayyan bread da ƙwai ta koma ɗaya kujerar, shi ko yaƙi bi ta kanta.
ba su jima wajen yin breakfast ɗin ba saboda lokaci da ke neman ƙurewa, sannan ya kira Bello a waya ya sanar masa zai biyo ta office sai ya wuce ya kai su airpot, haka suka fito dai a gidan babu wanda ya kula wani.
cikin lokacin da bai kai awa ɗaya ba suka sauka a airpot na Taraba state, su na sauka Drivern gidan su Hajiya Ramla yazo ya ɗauke su.
gidan na su babban family house ne, parlon Granny cike maƙil da ƴaƴanta da jikokinta, kuma kamar zaman anyi shi ne domin tarbar su, su na shigowa aka yi kansu ana yi musu oyoyo kowa sai murnar ganinsu yake, Granny na faɗin a matsa a bawa kishiyarta hanya ta iso, Fillo sai so take yi ta ƙwace hannunta daga riƙon da yay ma ta amma yaƙi har sai da suka shigo tsakiyar parlon tukunna.
Kowa sai zuwa yake yana rungumeta, da ma kowa ita ke ta so ya gani musamman waɗanda ba su sami zuwa dinner ɗin su ba, kuma kowa sai yaba kyanta yake yi kamar za su cinyeta, ana faɗin Turaki yay dace da tsaleliyar mata, ita dai sai murmushi kawai take yi, musamman yacca taga kowa na farin cikin ganinta, tamkar ita ma da ma can a family ɗin take.
a kusa da Granny ta zauna wacca ta kama hannunta ta riƙe, tana yiwa wata tsohuwa bayanin ai yana da wata matar amma sun rabu, da alama tsohuwar ƙanwarta ce don sun ɗan yanayi.
Tsohuwar tace,"yo wannan Tuzurun ma ai mata huɗu ya kamata a haɗa masa, sa'anninsa su na nan kowanne da yara amma shi sai yanzu yake aure, al'adar bature duk ta ɓata mana yara suyi ta zama suƙi aure".
Fillo ta ɗaga ido yanda ba za'a lura da ita ba, ta sauke su akan Turaki da ke can cousin sisters ɗinsa sun baibaye shi, tayi dariya tana kallon yanda ya riƙe wata ƴar Baby yana cewa da Mamanta ta karɓi kayarta kar tayi masa fitsari ko kashi, ta karɓeta tana faɗin taga yacca zai yi ranar da aka haifa masa tasa, ba kashi ko fitsari ba tumbuɗi kaɗai ya ishe shi, Allah na tuba kwana nawa suka rage.
kuma kamar ya san Fillo na kallonsa a lokacin, sai ya ɗago karaf suka haɗa ido, ya langwaɓar da kai ta sakar masa murmushi, shi ma yay murmushin yana kanne ma ta ido ɗaya, yau duk sai yanzu tayi masa murmushi, dan tun tashinta take faman cin magani, shi kuma bai takura ma ta ba dan ya san abin da yay ma ta ne jiya.
gida dai sai ya koma kamar gidan biki, don har wata walima suka haɗa wai ta murnar zuwan Mum, wacca tun bayan dawowarta bata sami zuwa ba, Fillo kam sosai taji daɗin zuwanta, kuma nan da nan duk sai ta sake sosai, irin Family ɗin nan ne masu saurin sabo, kuma masu sauƙin kai da mutunta wanda ya shigo cikin su.
da yamma su na zaune a bedroom ɗin Granny wata me suna Nilfat ta shigo, ta kalli Granny tace,"duk kinga balarabiya kin maƙale ma ta".
Granny tayi ma ta daƙuwa tana cewa,"ungo nan".
Nilfat ta ce,"na gode, ai ba zan bari muyi faɗa ba, dan lallaɓaki nake na bi ki europe nima naje na samo irin wannan sulɓin fatar taki da bata tsufa".
ta wuce wajen Fillo tana cewa,"ki je inji mijinki".
Hajjah Yayar Granny ta ce,"kije kice masa ba zata zo ba, ashe shi ma irin Ahmad ne bai da kunya".
"yaran yanzu ne fa, ai sai adu'a kawai, amma kunya ina suka ganta". cewar Granny.
"to Hajjah tafiya fa zai yi, ai sallama za su yi ba wani abu yace zai yi ma ta ba". Nilfat ɗin ta ƙara faɗa.
Hajjah ta ce,"kije kice masa yay tafiyarsa, dole ne sai sunyi sallamar, kaji min mara kunyar yaro, ko wani abu zai bata".
Nilfat tayi ƙofa tana faɗin,"ni dai ban taɓa ganin inda akayi irin haka ba gaskiya, ya zai tafi ba tare da yay sallama da matarsa ba, wallah idan ni ce sai ince ta fasa zama, in ɗau kayata mu tafi, yo in ma ba sallamar zai yi ba ina laifi anan dan miji ya nemi matarsa".
Fillo dai na kusa da Granny kanta a ƙasa, har ga Allah so take taje ta gan shi, tun ɗa zu rabonta da shi wai sun fita shi da wani Baffayo ɗan gidan Anty Hajar.
Mum ta shigo a lokacin, ta zauna tana cewa,"wai Babana zai tafi, jirgin ƙarfe bakwai zai bi, daga masallaci zai wuce".
sai ta kalli Fillo tace,"je kuyi sallama". sai ta kasa sakkowa, duk kunya ta kamata, ga shi ita ba waya ba balle tayi masa text tace ya tafi kawai, sai da Mum ta ƙara yi ma ta magana sannan ta sauko akan gadon ta ɗauki mayafinta ta fita.
a compound ta tsaya tana kalle kallen inda zata gansa, Fareeda na zance daga can wajen flowers ta ƙwala ma ta kira,"Antee".
Fillo ta ɗaga kai da murmushi tana kallonta.
ta ƙarasa wajen na su, Farida tace,"ga wanda zan aura".
"masha'Allah". Fillo ta faɗa kafin su shiga gaisawa da Modi.
Farida ta ce,"mijinki ba?".
Fillo ta ɗaga ma ta kai.
"yana ɗakin Baffayo".
"ina ne ɗakin?".
"ki zagaya ta wurin shukokin nan, ɗaki na tsakiya me bishiyar ayaba a gabansa".
Fillo tabi hanyar da Farida ta nuna ma ta, tun daga ƙofar ɗakin ta san Turaki na ciki saboda ƙamshin turarensa da duk ya cika wajen, ta shiga ɗakin bakinta ɗauke da sallama.
Baffayo ne ya amsa sallamar, Turaki kuma ya ɗaga kai yana kallonta, Baffayo ya fita a ɗakin, ita kuma ta zagaya ta zauna akan kujerar da Turaki yake, ta shige jikinsa kamar yanda ya buɗe ma ta hannu.
"yau ni kike gudu ko?".
ta ɗago kai tana kallonsa ta ce,"kaima ai mantawa kayi da ni ka tafi wani wajen".
yaja hancinta,"munje gidan wani Kakanmu ne, ƙanin me sunana, da naje su na ta tambayarki nace za ku zo ke da Mum".
"to me ka siyo min?".
"ɗa zu ba gani nayi kin saka fura agaba kina sha ba, ko irin ma ki tuna da mijinki a kusa".
"to a gaban su Mum ɗin zance kazo ka sha?".
"ni ma shiyasa ai da naje Alhaji ya ban abin daɗi ban iya cewa zan ragewa Matata ba".
tai murmushi da kiran sunansa,"Turaki".
ya ce,"na'am Halima".
ta ɗan bugi kafaɗarsa,"sunan fa Ummi ne".
yasa hannu ya rufe bakinsa,"Allah na tuba ka yafe ni".
sai kuma ya kama kumatunta yana cewa,"to ni ma ai sunan Abba ne kike faɗa".
"to ai dai ba ainihin sunansa na faɗa ba, Turaki na ce".
"ehh haka ne afiruwa".
ta turo baki gaba,"mene afiruwa?".
"ɗan siririn mutum da za ki gansa kamar lamba ɗaya, kin san one bata da kauri kwatakwata".
ta shiga kai masa dukan wasa, shi kuma yasa hannu yana karewa yana dariya har sai da ya kama hannayenta ya riƙe.
"ai indai ƙiba ce zan yi".
yace,"ni ma na san da wannan, aikina kawai zanyi".
sai kuma ya kalli agogon hannunsa ya ce,"za ki sa nayi late, jirgi ya tashi babu ni, tun ɗazu na aika ki zo kika ƙi, da nayi tafiyata ai".
"da ni kuma yau banyi bacci ba nayi ta kuka, saboda duk yau nayi kewarka ban ganka sosai ba".
"ehh ba ke bace naga yau duk kina ta shareni, kawai saboda na saka kinji daɗi jiya".
ba shiri tasa hannu ta rufe fuska, ya ɗauke hannun yana faɗin,"idan kika tashi dawowa ki dawo da babban shiri".
"shirin me?".
ya goga hancinsa da nata yana jan haɓarta,"sai kin dawo ɗin dai, ke dai kawai kici tuwon dawar Innah kiyi ƙarfi".
ta cuno baki tana faɗin,"ni dai sai ka faɗa min shirin me?".
"shirin karatu".
"wanne karatu?".
"karatun manya".
"wanne karatun manya kuma?, ni ban sansa ba ai".
ya ɗora hannunsa saman cinyarsa ya tallabi haɓarsa yana kallonta ya ce,"karatun da zai mayar da ke cikakkiyar matar aure".
ta ɗan murguɗa baki bata ce komai ba.
ya lanƙwasa yatsanta ya ce,"ni dai kici tuwon dawa da yawa kiyi ƙarfi, don karatun ba na wasa ba ne, Mum tace 7days za kuyi, ni kuma 7days yay min yawa, dan haka ki dame ta ku taho jibi".
tai lamo da kanta a kafaɗarsa tana cewa,"kamar ma kar na koma ai, family ɗin ku su na da kirki sosai".
"ni ma haka suke ta ce min wai nayi sa'ar mata me hankali da mutunci, anyway yanzu dai faɗa min when zaku dawo?".
ta ce,"to ka zauna anan mana kaima".
"kije ki faɗawa Mum hakan".
suka miƙa yana manneta a jikinsa,"7days yayi yawa Fulani Nah, ki faɗawa Mum hakan".
ta ce,"7days yayi kaɗan Turaki, ina so zanje inga Ummi nah, kaga babu nisa daga nan".
bai ƙara cewa komai ba ya kama hannunta suka fita, lokacin Baffayo har ya tayar da mota, yay ma ta side hug yace,"please don't stress your self wajen yin aikace-aikace da zuwa gaishe gaishe, dan gidan nan da kike ganinsu aiki suke kamar injina. fita indai ba'a mota ba ne kice da Mum ba kya jin daɗi".
ta gyaɗa masa kai kawai tana jin babu daɗi, sam bata so ya tafi.
ganin hawaye a fuskarta yasa shi cewa,"ko in faɗawa Mum ba kya son zama?".
ta girgiza kanta alamar a'a tana riƙe hannunsa.
sai yaji ta ba shi tausayi sosai.
"daina kukan Fulani Nah bana son hawayenki". ya faɗa yana share ma ta hawayen.
sai ya ɗaga waya yana kiran babbar ƴar gidan Inna me su na Hamida, tana zuwa ya ce da ita,"ki kula min da ita kinji, less hayaniya a inda zata zauna please, tana son bacci ki kula da haka, sai an bata abinci tukunna take ci if not zata zauna da yunwa, bata da cikakkiyar lafiya, so duk wanda zai zauna kusa da ita ki tabbatar is not addicted to ɓatawa mutum rai".
tace,"insha'Allahu za'a kula me sunan tsoho".
yay murmushi yana maida kallonsa ga Fillo, wacce ta maƙale hannunsa tana hawaye, ya sunkuya yana ɗora kumatunsa kan leɓenta yace,"ummm 1 peck".
abin da bata taɓa yi masa ba, kuma shi ma bai tsammaci zata yi ɗin ba, tai masa peck a kumatu tare da kissing ɗinsa a goshi tana faɗin,"i will miss you".
"i will miss you too, take care...bye bye".
ta ɗaga masa hannu tana faɗin,"bye". ya sauke ajiyar zuciya,"ba ki min adu'a ba".
tasa hannu akan ido irin yacca yara ke kuka tace,"Allah ya kai ka lafiya, Allah ya tsare hanya, Allah ya kare ka da kariyarsa".
ya amsa da,"amin, thank you so much". kafin ya iya sakin hannunta ya wuce mota, ita kuma taji wani kuka ya taho ma ta but sai ta danne shi saboda Hamida, su na shiga ciki ta wuce ɗakin Hamida ta kwanta akan gado.
wajen ƙarfe goma na dare sun kwanta ita da Hamida sai ga Nilfat ta shigo ɗakin, ta kunna fitila ɗakin ya gauraye da haske, Fillo ta buɗe idonta don ba baccin take yi ba.
"au ashe baccin naku ma bai yi nisa ba, mijinki ne ya kira waya".
ta ƙaraso tana bawa Fillo wayar, sai taji wani daɗi ya ratsata, tun ɗa zu take ta tunaninsa, ta kasa ko baccin har Hamida tazo ta kwanta tayi nata, infact jinta take kamar mara lafiya, ta karɓi wayar tana kallon Nilfat da zata fita tace,"ki tsaya ki karɓi wayar".
ta ce,"wala, ba tawa bace ai ta Baffayo ce, yace da safe ya karɓa".
ta fita tana rufe musu ƙofar, daidai da shigowar kiran Turaki wayar.
tana ɗagawa ta saka kukan shagwaɓa,"tun ɗa zu sai yanzu ku ka je?".
"am sorry Fulani Nah, na dawo ne na tarar Maama babu lafiya, yanzu muka dawowa ma daga asibiti".
"subhanallah, me yake damunta?".
"Bp ɗin ta ne, but da sauƙi, ko in kai mata wayar?". ya tambaya jin ta damu sosai.
ta ɗaga kai kamar yana ganinta,"ehh".
yana zuwa ɗakin ya tarar Maama tayi bacci, Fillo tace da safe ya faɗa ma ta tana yi mata sannu sosai.
ya ce,"insha'Allah, tun ɗazu na kira Mum amma sai na kasa cewa ta baki. ba kiyi bacci ba ko tashinki aka yi?".
"ai na kasa yi".
"why?".
tayi shiru ta kasa cewa komai.
ya ƙara cewa,"why?, tell me".
"i am missing your warm body that make me fall asleep".
taji murmushinsa me sauti ya fito.
"sorry Fulani Nah, just close your eyes and go to sleep, I will come to your dreams, then you sleep like you used to".
a shagwaɓe ta ce,"promise?".
ya ce,"insha'Allah".
ba su jima su na wayar ba yace ta kwanta zai je Baffa na kiransa.
ta sauke numfashi tare da ce masa,"don't forget to Perform Ablution and recite Al'qur'an before you sleep".
ya ce,"i will not forget, good nite".
sam bata so wayar tasu ta ƙare, ta danne kukan kewarsa gudun karta ɗaga hankalinsa ta ce,"good nite, sweet dreams, please you take good care of your self".
"insha'Allah".
da ƙyar dai suka iya yin sallama, Fillo ta tashi ta kashe fitilar sannan ta dawo ta kwanta tayi lamo, ba don tana jin zata iya baccin ba, zuciyarta ta cika fal tare da tunaninka kala-kala, har ɓarawon bacci ya ɗauketa.
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*55*
kiran sallar farko a kunnen Fillo, tana buɗe ido ta ganta a inda saɓanin Mafarkinta ya nuna ma ta.
ta ɓata fuska tana jin kamar tayi kuka, wayar Baffayo da ke gefen pillow ta ɗauko, adu'arta ɗaya Allah yasa babu pin a jiki, cikin sa'a kuma tana dubawa taga babu, don haka da sauri ta shiga message tayi typing text kamar haka.
_I don’t just miss you, i miss the warmth in your breath, depth in your eyes, the touch of your fingers, and feeling your hands on my waist. I miss you truly and deeply._
after ta gama rubutawan kuma sai ta kasa sending, ta tsaya tana tunani, kunyar turawar takeyi, ta zuro ƙafafunta ƙasa daga kan gadon kamar wacca zata yi kuka, har sai da Hamida ta buɗe ido ta tambayeta,"Asiraawo lafiya?".
"yi haƙuri na tashe ki, ji nayi kamar wani abu na bina ne, ashe zaren jikin rigata ne".
Hamida tayi murmushi kawai tare da komawa ta kwanta, don ita kanta ta fahimci tana cikin kewar mijinta ne, duk da tana da nauyin bacci but tana jinta sai faman juyi take.
Fillo ta tura text ɗin sannan ta wuce toilet ta yo alwala ta fito, har ta idda sallar asuba bata ga reply ɗin Turaki ba kamar yanda tayi tsammani. duk sai taji babu daɗi, may be ko text ɗin ne bai yi masa ba, ko kuma abin da ta tura ɗin ne bai dace ba, duk sai taji ta kasa komawa baccin da yake so ya ɗauketa.
da safe wajen ƙarfe tara after sun gama breakfast, taji su na waya shi da Mum har take tambayarsa jikin Maama, tai ta jin kamar tace da Mum ta bata wayar, kewar muryarsa take yi kamar ta shekara dubu ɗari bata ji ba.
kuma bayan sun gama wayar da Mum a tunaninta ko zai kirata a wayar Baffayo sai taga har ƙarfe tara bai kira ba, sai taji kamar ta fara fushi da shi, but haka ta ƙara ɗaukar wayar ta ƙara tura masa text.
_The thought of you makes me smile, but the distance we share makes my heart ache. I am missing everything about you. I wish you were here Turaki._
ta tura da yaƙinin cewa a wannan lokacin zai dawo ma ta da reply tunda dai tasan yanzu wayarsa na hannunsa, but sai ta ƙara jin shiru, idonta ya ciko da ruwan ƙwalla ta ƙara tura masa text.
_kuma ba zan dawo gidan ba._
tana turawa ta ɗauki wayar ta fita ta kaiwa Baffayo, har ya tambayeta ta gama ne tace masa ehh ko ya kira ma ba sai ya kawo ma ta ba.
ta koma ciki ta shirya kamar yanda Mum ta umarceta don za su fara zagayen gaishe-gaishen ƴan uwa.
to acikin kwana biyu dai Fillo sai taji tamkar an sakata a kurkuku, mugun bala'in kewar Turaki take yi, har wata rama tayi ka rantse bata da lafiya, duk dare in zata kwanta sai tayi hawaye, ta riga ta saba da kwanciya a jikinsa, wannan ƙamshin jikin nasa, wannan ɗumin jikin nasa da ɗumin iskar bakinsa me ƙamshin min, wannan cairing ɗin nasa da soyayyarsa.
tun ranar da suka zo bata ƙara jin muryarsa ba, yau da safe ya kira Baffayo ya kawo mata waya amma da ta karɓa sai ta kashe kiran, yay ta kira taƙi ɗagawa ita alallai tayi zuciya tun da ranar nan duk yana kallon messges ɗinta bai yi ma ta reply ba.
wasa wasa dai sai taga ina ba zata iya yin har 7days ba, gida kawai take so ta koma, wurin Turakinta, tana missing late-night talk ɗin su, tana kewar precious smile ɗin sa, she want nothing except his presence around her, being away from him in this 4days she feels like being caged for a lifetime in misery.
a daddafe ta iya kwana biyar ɗin da suka yi, tuni ta fara cutar ƙarya me zafi ta yanda dole su tarkata su koma gida, hakan kuwa akayi, da Mum taga jikinta yay worst sosai musamman da taga kamar har da iskokinta dole suka ɗauko hanya a ranar.
sai ga su ƙarfe biyar na yamma sun sauka, don jirgi su ka biyo saboda Granny tace ba lallai Fillon ta iya jurar zaman mota ba, kuma su na dira a gombe taji ta warware daga cutar da ta fara kamata.
Zaytuna ce tazo ta ɗauke su a airport, duk tunaninta gidanta za'a wuce da ita but sai taga sun yi gidan su Turaki, ba haka ta so ba sam, yacca ta so ta koma gida ko da ace bata same shi yana nan ba, to da ya dawo ya zama yay tozali da ita.
san da taga Maama sai da gabanta ya faɗi, ashe ciwo take yi sosai dan duk ta rame, ta faɗa kamar ba ita ba.
sai taji ta kasa riƙe hawayen tausayinta a lokacin da Maama ta rungumeta tana yi musu sannu da zuwa tana sanya ma ta albarka.
yinin ranar gaba ɗaya tana tare da Maama, da ta motsa Hajiya Madina zata ce Daughter me kike so?, menene?, ko jikin ne mu tafi asibiti?.
haka ita ma ana ta ɓangaren, motsi kaɗan Hajiya Madina zata yi ta fara tmbayarta Maama me za'ayi miki?, akwai abin da kike so?, a ranar gaba ɗaya sai take jin Hajiya Madina acan cikin zuciyarta, taji tamkar tana tare da Umminta ne.
bayan isha'i su na zaune duk ɗin su a dining za su ci abinci, Hajiya Madina ta ce ita bata jin daɗin bakinta ta ƙoshi,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 62 Chapter of 73