Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ma dai Baffa ɗin ke kira da babu abinda zaisa ya ɗaga, daga ƙarshe ma sai ya fara ignoring call ɗin. Adda Samira ce ta fahimci yana so ya keɓe da matarsa hakan yasa taja su Adda Juwaira da su Kaka suka bar wajen, kamar ƙiris yake jira kuwa suna barin wajen yana saurin isa gaban Fillo da hazari ganin tana ƙoƙarin tashi ta bar wajen. ya kama hannunta ya maidota kan kujerar ta zauna, kawai sai ta ƙara fashe masa da kuka ita lallai ya saketa yanzu ba sai anje gida ba, ya dinƙa bata haƙuri da lallashi amma kamar yana tunzurata, ransa ya kai ƙololuwar ɓaci ya sakar mata uwar tsawa da tasa babu shiri ta faɗo jikinsa tana ƙanƙame shi, jikinta banda kyarma babu abinda yake yi. "ban san irin illar da zan yi miki indai kika ƙara ambatar min kalmar saki". sai kuma ya kwantar da murya gwanin ban tausayi yace,"wannan Kukan naki ba komai bane illa damuwa, muyi avoiding duk kalar wani abu da zai saka ki a damuwa muddin muna sonki da rai, haka Dr yace, bana so na rasaki Fulani nah ina so na rayu da ke, ki taimaka min, wannan kukan naki na faɗa miki baida amfani, in har za'a bawa Abba damar magana da yayi yace ki bar yi masa wannan kukan kiyi masa adu'a, so please ba kuka ba just pray for him". tayi ɗif tare da lafewa a jikinsa kamar ba ita ba, shashsheƙar kukan ma a hankali take yi yanda ba zai ji ba, ya kai bakinsa saitin kunnenta a hankali yace,"za ki bi ni mu tafi tare?". ta girgiza kanta da sauri alamar a'a, sai kawai ya rufe idanunsa tare da miƙewa ya kama hannunta itama ta miƙe. tana taka ƙafarta tace da shi,"zafi ƙafata". yace,"to in ɗauke ki?". ta girgiza kanta da sauri. ya riƙe hannunta suka koma office ɗin Dr, sai da Dr ya tabbatar masa ciwon ƙafartata babu damuwa ya kuma gamsu sannan ya kamo hannunta suka fito. su Kaka har sun tafi lokacin, tana wurga idanu a compound ɗin tace masa,"ina su Kaka?". yace,"sun wuce". ya faɗa yana nufar inda motarsa take, ita dai binsa kawai ta-ke yana riƙe da hannunta har lokacin, sai kallon baƙon asibitin ta-ke yi tunda ba nan aka saba kaita ba, suna zuwa bakin motar sai ga wani mutumi nan ya ƙaraso wurin da gudu-gudunsa. ya rissina yana cewa da Turaki,"ance in zo in tafi da ku ne". Turaki na kallonsa yace,"a'a ga motata ai, kaje kawai". mutumin ya ƙara rissinawa yana cewa,"umarnin Dada ne yallaɓai, Dottijo ma ya ƙara da nasa akai". Turaki ya kalla Fillo da ke ta kallon mutumin da rashin sanin sunayen da yake ambata. yace da shi,"kaje kawai babu damuwa". "tom shikenan ranka shi daɗe, A iso lafiya". ya juya ya bar wajen. Turaki ya buɗe front seat Fillo ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ɓangarensa, ya tada motar suka bar asibitin yana driving kamar baya so, ya maƙale hannunta a nasa kamar wanda za'a ƙwaceta ko wadda zata gudu. ita dai kanta na jingine da jikin kujerar, tana ta kallonsa ta gefen ido tana ganin yanda yake cije fuska yana matse goshinsa tare da dafe kai, har stearing ya kusa ƙwace masa, hakan yasa ya gangara gefe yay parking, ya kifa goshinsa akan stearing, Fillo dai sai kallonsa ta-ke yi, bayan wucewar daƙiƙa biyu tace da shi,"baka da lafiya?". yay shiru bai ce mata komai ba, har sai da ya ɗauki minti biyar a haka yaji ya ɗan sami relief tukunna ya ɗago, ɗagowar tasa tayi dai-dai da shigowar kiran Maama, yay picking yana magana da ƙyar. tace da shi,"me Babban suna na rasa yanda zanyi da Baffanku, kayi haƙuri kawai mu koma tare tunda Fillon taji sauƙi kaji, kasan dai yanda lamarin Boɗejo yake sai haƙuri". yace,"tom Maama". tace,"baku taho a asibitin bane?, su Kaka sun dawo tun ɗazu anata tambayar ko lafiya ku baku taho ba, ka san akwai ƴan uwan Babanta daba ƙasar nan suke ba suna so su ganta kafin su koma". yace,"ina kan hanya Maama". tace,"bana son damuwa Me Babban suna, karka zo min da ita ka jefar da ita tun a hanya kaji". ya amsa da,"as you wish". yaci gaba da driving ɗin, Fillo dai tsoro ya cikata duba da kamar ba'a hayyacinsa yake tuƙin ba, can yaji muryarta cikin ƙarfin hali ta ƙara tambayar,"baka da lafiya?". yay mata wani kallo yace,"kina da damuwa da lafiyar tawa ne?". idanuwanta suka yi narai-narai, ta kauda fuska gefe tana kallon titi tana jin zuciyarta nayi mata zafi, ita bata taɓa sonsa ba a rayuwarta, kuma bata taɓa jin zata so shi, abinda tayi masa taimakonsa kawai tayi, so how comes za'a ce shine mijinta?, me yasa ƙaddara zata yi mata haka?, ta ina zata fara zama da shi irin wannan zaman da taji su Ummi na faɗa wai zama na har abada?, taji ƙwalla ta cika idonta, wani dunƙulallan abu ya tsaya a maƙoshinta, in ace shima yana sonta wataƙila ta iya haƙurin zama da shi ɗin, but shima ba sonta yake ba, ya aureta ne saboda ya taimaketa da kuma tausayinta, sannan kuma ya aureta alhalin ya san ba zai iya zama da ita kaɗai ba?, shin ta ina zata fara zama da shi da bata sonsa da kuma kishiyar da bata ƙauna. ta rumtse idonta sosai cikin ranta tana adu'ar Allah ya ɗauki ranta kafin zuwan lokacin da za'ace an kaita gidansa. lokaci ɗaya hawaye ya shiga zubo mata, wataƙila da Abbanta yana raye da ya tsaya mata har sai an raba auren tunda bata so, ta kulle idonta tana jin wani bala'in zafi da ɗaci a ƙasan ranta, kishiya! ita Fillo da kishiya!, kuma kishiyar ma ƴar sarki yacce zata ji daɗin taka ta!, zata iya ɗaukar bull shits ɗinta kuwa?. kawai sai ta cije leɓenta na ƙasa, for some seconds ta buɗe ido a sanda motar ke ƙoƙarin dukan bishiya, da ƙarfi tace da shi,"kayi a hankali zaka ka bugi bishiya". yay saurin juya kan motar yana kaucewa bishiyar da ya kusa daka ba tare da ya sani ba, duk sai yaji dama ya bar wancan mutumin ya tafi da su, dan shi kansa ya san ba'a hayyacinsa yake ba, banda bala'in ciwo da kansa yake masa yana jin ƙirjinsa ma kamar zai bar jikinsa, ga idonsa ma ba sosai yake gani ba saboda azababben baccin dake cikinsu, ya ɗauka wayarsa zai kira Hamid yazo ya tafi da su sai kuma ya fasa, yaci gaba da lallaɓawa yana jan motar a hankali. sanda suka sauka akan titi ya shiga street ɗin da zai kai su gidan Barkinɗo, daga saman kansa yaji tana tambayar,"wai ina zaka kaini?, dan Allah ka kaini gida, ni ba wurin Maama zanje ba". bai ko waiga ya kalli inda take ba balle ya amsa mata. ta ɗauke idonta daga kansa taci gaba da kallon hanyar da bata sa ni ba, da irin ginin gidajen da zata ce in ba a tv ba bata taɓa gani ba, hanyar sam bata yi mata kama hanyar da ta taɓa bi ba, tunaninta ɗaya ne ta yanda zata buɗe murfin motar ta faɗa waje. sunyi tafiya me nisa a street ɗin sannan ya samu wuri yay parking, idonsa na manne da gabansa yace,"fita". Fillo ta ɗauke idonta daga kan symbol ɗin da take karantawa ta juyo tana kallonsa, kamar ba shine taji yayi maganar ba kuma sai taji ya cire mata tantama da ƙara maimaitawa. "fita". tace,"ai ban san ina ne nan ɗin ba, ba zan iya gane hanya ba". shirunta yayi daidai da doka mata tsawa yana ƙara cewa,"i said get out of my car". babu shiri ta buɗe motar jikinta na kyarma, ta fita ta tsaya tana riƙe da murfin motar, "dan Allah kayi haƙuri idan ka saukeni anan wallah ba zan iya zuwa gida ba, ban san ta nan hanyar ba". yana jinta dai bai tanka mata ba, ya ɗauko wayarsa ya danna kira a lambar Hamid, yana ɗagawa yace da shi,"kaine ka shiga mota yanzu?". Hamid yace,"ehh". yace da shi,"ƙaraso ka ɗauki wannan yarinyar, tana wajen symbol ɗin da akai addressing da sunan Hakimi". Abdulhamid yace,"ok tom gani nan". sai da ya hango motar Hamid ta taho tukunna ya figi tasa ya bar wajen, Fillo tayi saurin sa hannu ta kare idonta gudunta kar ƙurar da ya baɗeta da ita ta afka mata a ido. Hamid yazo ya ɗauketa kuma har suka ƙarasa gidan bata iya ce masa komai ba, sai magana yake yi mata tayi shiru bata amsa masa ba, tambayoyi ne fal a bakinta amma jin bakin nata take yayi mata nauyi. tunda ta fito a mota kuma sai ta zama ƴar kallo, idonta kamar zai faɗo waje saboda kallon gidan da ake nufa da ita da kuma mutanen dake ta tururuwa akanta, suka shiga gidan tana jin muryoyi da dama na faɗin,"ga ƴar gidan Hayyon, masha'Allahu ta sami lafiya". sai kuma taji wata dattijuwa na cewa,"ɗauko ruwan tofin nan a bata Malam yace tana shigowa ta fara shansa". idanuwanta suka sauka akan Ummi dake tsaye a bakin ƙofar ɗakin Hajjah mahaifiyar Hayyo, ta ƙwace daga hannun mutanen dake riƙe da ita ta tafi wurinta ta faɗa jikinta, Ummin ta kama hannunta suka wuce ɗakin Dada, kuma zuwan nasu ne ta samu duk amsar tarin tambayoyin dake cikin kanta tun kafin tayi tambayar a bata amsarsu. mutuwar iyaye bata daɗi, kuma ba'a farin ciki da mutuwarsu duk lalacewarsu, but a ɓangaren Fillo abu ɗaya da zata iya buɗar baki tace shine mutuwar mahaifinta tayi mata rana, domin ta dalilin mutuwarsa yau gasu cikin jin daɗin da basu taɓa hangar cewar zasu ji shi ba har su mutu, gatan da basu san suna da shi ba yau gasu acikinsa. sai nan da nan ake da ita da Hamid da sauran sisters ɗinta kamar wasu gwala-gwalai, tarairaya kace ƴaƴan wasu shegen ƙusan, motsi kaɗan a tambayesu me suke so. cikin satin mutuwar kafin ayi adu'ar bakwai haka aka dinƙa ɗaukarsu ana zagawa da su cikin dangi, babu inda ba'a kai su ba adai familyn mahaifinta da suke nan cikin taraba state, waɗanda basa ƙasar ne kawai ba'a kaisu wajensu ba amma suma sunyi vedio call da su. a hankali ta dinƙa jin damuwar mutuwar na tafiya tana barinta, sai in sun zauna ita da Hamid ne sai suyi ta tambayar junansu wai me yasa Abba ya tsiyatar da kansa haka har yayi irin wannan rayuwar ƙasƙancin bayan yana da gatansa, amsar da basu da ita har kullum kenan. *After 55days.* *Saudiyya, Jeddah, Sanabile, House no 08.* *13:00pm.* Rauda ta fito daga cikin bedroom ɗin hannunta riƙe da biro da jotter, yayinda Fillo ke biye da ita a baya nata hannun riƙe da laptop. suka ƙaraso parlo Raudha na cewa,"yanzu to ya kika ga lissafin?, tunda dinner ce kawai ai hakan yayi ko? sai dai ban san ba ko after an kaiki akwai abinda za'ayi". Fillo bata ce da ita komai ba ta zagaya ta side ɗin da Dada take ta zauna kusa da ita, taci gaba da operating laptop ɗin tana duba wata university acan Europe, dan tun bayan sati ɗaya da rasuwan Abbanta ta zana private waec tare da su Raudha da Amatullahi sauran jikokin gidan, aka kuma ce kowanne ya nemo university ɗin da yake so ya tafi, so ita taso ta zauna anan nigeria but due to haukar Asuu da ta sani yasa ta fasa cikewa ta-ke bincike akan Uni ɗin da Raudha tace su tafi can kawai, yanzu lissafin karatunta kawai take yi ba lissafin wani aure ba kamar yanda taga an mayar da hankali akai tun bayan adu'ar arba'in. Dada da ke shan tea ta ɗago kai ta kalla Fillo, ta girgiza kai tana yamutsa fuska kamar wacca taga kashi tace,"tirrrr, tirrr, tirrr da wannan mugun hali naki irin na Hayyo". Fillo kamar zata yi kuka ta shiga dukan ƙafa a ƙasa tace,"kai dan Allah Dada, Abba nah fa ya mutu ki daina min irin haka, duk in kin ambaci sunansa fa sai ya tashi a ƙabarinsa". Dada ta watsa mata wani kallo na ki shiga hankalinki da ni sannan tace,"an faɗa ko ba halin nasa ba ne, wani yace kar ya zama mutumin ƙwarai?, to in faɗa miki har duniya ta naɗe Hayyo dai bai da halin kirkin da za'a shaide shi da shi gwara ma ki daina nunawa duniya shi ubanki ne, ko kuma kike bari ana ambatarsa akai-akai ko ake masa adu'ar samun rahamar ubangiji. banda iskanci ke kenan baki da aiki sai faman ɓata fuska ki yita turowa mutane laɓɓa gaba kamar ganda, to wallahi ki kiyayeni tun ban ɓata miki ba, ana tausaya miki saboda rashin mahaifi amma kina yiwa mutane iya shegen da kika ga dama, to ni ubanki zanci ba kowanne iskanci nake ɗauka ba". ta gama faɗan tana harar Fillo kamar idanuwanta zasu zazzago, sannan ta juya kan Raudha tace,"ina jinki kin gama lissafin abinda na saka ki?, kuma kin duba shagon da yafi kowanne anan Jeddah ɗin?, ba sanin kan shagunansu nayi ba inda dai Riyadh ne can nafi zama". gaban Raudha ya faɗi, nan da nan ta shiga zare idanu kafin tace,"kiyi haƙuri Dada wallah na mance, amma zanyi yanzu". da muryar faɗa Dada tace,"in saka ki aikin tun yammacin jiya kice min ba kiyi ba?, to uban me kike rubutawa yanzu?". "Dada ai kin san can dangin mijin Fillo sunce za'ai events kafin ta tare, shine dama nake lissafin abubuwan da zamu yi, ƙanwar mijin tana ta yo waya ta tambaya ko mun gama shirya abubuwan da muke so kuma duk banyi ba, ita kuma inata tambayarta taƙi ce min komai kiyi mata magana dan Allah". ta faɗa duk a ɗarɗarce saboda irin kallon da Dada ke bin ta da shi da makafin idanuwanta. Dada ta gyaɗa kai ta juyo ta fuskanci Fillo tace,"ke ɗauko min sanda ta". sanin hali yasa Fillo miƙewa babu shiri ta wuce ɗakin Dada, in few seconds sai gata ta dawo tana miƙawa Dada sandar daga baya-baya. Dada ta karɓa ta saita kafaɗar Raudha ta muƙa mata, tuni zafin dukan ya ratsa Raudha idonta ya ciko da ruwa. Dada ta fara mata masifa,"uwaki da ubaki ke da lissafin bikin, wato har wani shirin bikinta kuke yi saboda ba kwa ƙaunarta ko?, saboda ubanta ya mutu shikenan sai ace bata da me tsaya mata?, to tana da ni Kakarta, ni ce nan gatanta, dan haka banga wanda zai ɗaukar min jika ya kaita inda ba'a ƙaunarta ba. ko za kice baki da labarin Kakar yaron bata sonta ba?, har tana faɗin wai ya sakar min jika, to dama ko bata sa shi ya saketa ba ai mu zamu buƙaci ya saketa tunda dama jikar tamu ba sonsa take yi ba, ni inama na taɓa jin anyi gantalallen aure irin wannan Allah dai ya gafartawa Hayyo, to in har ba so ake rai ya dinƙa ɓaci ba kar in ƙara ji an tada maganar auren nan". taja dogon tsakin da duk su Fillo sai da suka toshe kunne, ta doka sandarta akan table ɗin dake gabanta, fuskarta na bayyana tsurar ɓacin rai ta hau ruwan bala'i kamar zata haɗiye gidan. "wace ita da zata ce jikanta yafi ƙarfin jikata ba zai zauna da ita matsayin matarsa ba?, to me take ji da shi, kuɗi ko mulki ko kuwa sarauta?, idan tana ɗagowar cewa suna da Gombe a hannunsu to muma haka muke da Taraba a tafin hannunmu tun daga sama har ƙasa. ita wai ƴar wofi har wani kashedi take turo min kar in sake jikata ta tare a gidan jikanta saboda yana aurar ƴar sarki, to idan ban sa an ƙwace sarautar tasu ba Allah ya tsine, babu ƙulla ƙullar da ba zan iya yi ba akan a tsigesu a kujerar sarautar nasu sai inga ta tsiya, yo banda ma dai ƙaddara ina jikata ina jikanta?, ai wallah sam babu haɗi, jikata tafi ƙarfin wannan mummunan jikan nata, wani dogon banza ma da shi kamar basamude, ai Fillo matar larabawa ce ba matar mutumin da zuwansa saudia ma bai fi ƙirgen yatsu ba, yaron ma da bai ma san darajar mace ba, tun sadakar uku bai ƙara waiwayanta ba shi ga shi ɗan iska, iya haka ma ai ya shaida maka wannan yaro baida ilimin addini sam, mu kam kaf zuri'ar Barkinɗo babu wanda yake jahili babu kuma wanda ke auran jahili, babu ta inda aka barmu daga addinin har bokon, saboda haka can ta kwaɗa jikan nata ta cinye itace a yunwa ce, mtswww daga jin ma yanda take hayagaga akan sarautar tasu kasan ci akai aka rage musu". tai shiru tana faman huci sai girgiza ƙafa ɗaya akan ɗaya take yi, ta kuma jan tsaki ta kurɓi tea sai kuma ta zubar da shi acikin wata ƙatunwan silver me kama da sink. ta kama haɓa tana jijjiga kai na irin takaicin nan ya isheta, ta ɗora manyan idanuwanta akan Fillo tana faɗin,"to ni dai ban yafewa ubanki ba da yasa aka raina mu haka, banda yaja mana raini har ina wannan figaggiyar tsohuwar ta samu zarrar yo min aiken in raba jikata da jikanta dan yafi ƙarfinta, jikarta ƴar sarki ce tafi ƙarfin ta haɗa kishi da jikata ƴar aiki a gidan Alƙali yake ko uban me oho?, har ƙara faɗa take yi mu kuka da kanmu in har muka bari akayi tariyar auren nan". tai shiru tana cizon yatsa kafin ta shiga nuna kanta,"har ni ake yowa wannan baƙin aiken rashin mutumcin ban ɗau matakin komai ba?, ni ƴar sarkin taraba, uwar gwamnan taraba, uwar hakimin wurkum, Kakar soja, uwar macen da tafi kowacce mace kuɗi a nahiyar africa, yo ni kam yaushe nayi wannan saken?, dama har haka tsufan ya lalatar da ni?, ko da yake duk Hayyo ne yaja min ba kowa ba kuma yaje shi da Allah". cikin ɓacin rai ta ƙara buga sandarta akan table har saida glass ɗin ya tsage. "to billahillazi idan ban sa jikan nata yayi fatali da gimbiyar waje ba ya zauna da Fillo kaɗai ba shegiya nake, Hassana sunana na fita fitina da rigima wallahi, taje ta binciki tarihi taji ba'a taɓan ƴaƴa da jikoki a zauna lafiya". tai ƙwafa tare da miƙewa,"na rantse Allah ne ya rufawa Hayyo asiri bamu ƙara gamuwa ba da wallahi tallahi babu abinda zai hanani kai ƙararsa gaban alƙali, haka kawai yaja anai mana kallon ƙanan mutane har ana ci mana mutuncin da kare ba zai shinshina ba, akan jikarmu zata tare a gidan aurenta a kira waya ana mana gargaɗi, kashhh, amma babu komai idona idonta sai ta san tayi min aiken baƙaƙen maganganu, sai ta san tasa shegiyar matar tasa ta kira jikata ta zazzageta, zan nuna mata na fita ɗanyen kai, kowa ai shegen kansa ne, jikan nata da ta-ke ta haƙilo akansa zan nuna mata mune rayuwarsa, ba dai ance yana matuƙar ƙaunar Fillon ba, to aradu sai ya sakar min jika sai dai ya mutu, in ya mutu ita ke da asara bamu ba". zata bar wajen ta kalla Fillo taga tana kuka, ai ko ta ɗaga sandarta ta dinƙa bugun Fillo da ita tana faɗin,"saboda nace sai ya sake ki shine kike kuka, ke ko ace ma Kakar tasa bata kira taci mutuncinmu ba kya yarda ki koma wurinsa ne yanda yay fatali dake ɗin nan ya manta da aurenki dake kansa, to kuwa sai dai ki bi ubanki amma wannan aure sai ya mutu a yau-yau ɗin nan, dan ba zan yarda kije inda za ake miki kallon raini da ƙasƙanci ba duk da cewar ubanki yaja miki, kiyi kukan jini ba na ruwa ba, indai jikan wannan figaggiyar tsohuwar ne na rabaku bake ba shi, ya sakar min ke ki samu mijin aure anan kafin mu koma, babu abinda za kiyi da ɗansu, in ma saboda taimakon da suka yi miki ne gantalallar uwarki ta kasa cewa komai to ai kema kin masa taimakon da yafi nasu, ni na gode Allah ma da bai mayar dake saura ba". tai hanyar ɗakinta sai jaraba take yi, ta buɗe ƙofa zata shiga ta waigo ta kalla Raudha tace,"ɗau waya ki kira min Jagarɗo". sai kuma ta fasa shiga ɗakin ta dawo ta zauna, ranta ɓace take ta kallon Fillo dake kuka, banda tana tausayin karta ɓaɓɓallata da sai ta ƙara mummuƙa mata sandar ko ta shiga hankalinta. Raudha ta miƙo mata wayar tana cewa,"ga shi Dada". ta karɓa ta kara a kunne tare da saka glass ɗinta kamar ganinsa zata yi, bayan sun gaisa tace da shi,"kana jina?". daga ɓangaren Jagarɗo yace,"ina ji Dada". tace,"to ka saka Kakinka na sojoji ku ɗauki hanyar gombe yanzun nan, ka shiga har cikin gidan Alƙali wa yake oho, ka kamo ɗansa da yake auren Fillo kasa masa ankwa sannan ka basa biro da takarda kace ya sakar min jikata, in yaƙi kayi gidan gyara hali da shi da figaggiyar Kakarsa da ta yo min aiken rashin mutunci". Jagarɗo yace,"amma Dada inaga wannan fa sakin nan ba masalaha bane, kar a maida yarinyar nan bazawara tun tana ƙaramarta". ta fusata tace,"a mayar ai bata zama sauran wani ba, ya saketa yau ɗin nan in ba haka ba ai tashin hankalin da ba'a taɓa yi ba". tana faɗin haka ta kashe wayarta, ta kalli Fillo ta doka mata tsawa tace,"ɗago da kanki ki bani lambar mijin naki". Fillo ta ɗago kanta, hawaye duk ya wanke mata fuska, cikin muryar kuka tace,"ban san lambarsa ba". Dada taja tsaki tace da Raudha,"kira min AbdulHamid a waya". ko sallamar Hamid ɗin bata amsa ba sanda ya ɗaga wayar, tace da shi,"ka turo min da lambar mijin Fillo yanzu yanzu". sanin wace Dada yasa ko tambayar ba'asi bai yi ba, haka kuma bai jinkirta ba wajen turawar, dan duka 2 numbers ɗin ya tura mata, gudun ma kar ta ƙara kira ta zazzage shi tace ya tura mata ta ƙarya. Fillo ta miƙe tayi bed room ɗinsu tana jin zuciyarta kamar zata fito, har sau biyu kiran wayar Turaki na shiga bai ɗaga ba sai ana uku, lokacin suna tare da Bello a office, ganin lambar saudia ce yasa bai hanzarin picking ba dan bai san ko waye ke kiran ba. yana ɗagawa yayi sallama Dada ta amsa kamar abin arziƙi, daga can ɓangarensa ya kurɓi ruwa sannan yace,"wake magana?". Dada tana kalla Raudha tace,"munafuka mene ma sunan shi?". baki na rawa Raudha tace,"kamar Turaki naji suna faɗa". Dada tai gyaran murya sannan tace,"Turaki ne?". yace,"ehh ni ne". tace,"yauwa to suna Hassana Kakar Fillo ta wurin uba, Fillo uwar gidanka da bata tare ba har yanzu ka shaida?". Turaki ya gyara zamansa yana rissinar da kai kaman a gabanta yake yace,"Allah sarki Dada ina yini". tace,"lafiya". Turaki ya shafo wuyansa yana jin nauyi da rashin dacewar abinda yayi, tun ranar sadakar uku da ya baro Taraba bai ƙara waiwayar garin ba balle ta kan Fillo da ya san ya baro acan, ya sani tana da hakki akansa amma fushin da yayi da ita baya jin zai iya ƙara nemanta sai idan ita ta neme shi, shi ba lusarin namiji bane da zai bari son ƙanƙanuwar yarinya yake walagigi da shi, dalilin da yasa ya banzatar da ita da lamarinta kenan, kuma ya ɗau alwashin indai ba gajiya akai aka kawo masa ita ba shi dai da kansa ba zai nemeta ba, Maama tayi fama da shi har ta haƙura ta zuba masa ido, shi yanzu yaji ma da bala'in Boɗejo na kullum kullum, da fitinar da Ilham ta tsira ba dare babu rana, ta wanni fannin ma sai yaga barin Fillon acan shi yafi akan ya ɗaukota ya kawota nan ɗin, dan bai san abunda Boɗejo da Ilham zasu aikata ba. yace,"Dada dama...". tayi saurin katse shi da cewa,"riƙe dama ɗin ka, zatonka biko na zo?, a'a ko ɗaya wallahi ajinmu da girmanmu ya wuce nan, kiranka nayi dama in sanar maka da cewa Kakarka ta kira waya tayi mana kowanne irin kalar rashin mutunci, tace muddin Fillo bata rabu da kai ba to mu kuka da kanmu da duk abinda zai biyo baya, tace babu batun tarewarta a gidanka in ba haka ba zata cinnawa gida bom, tace ba zai yiwu daga auren ƴar sarki a ɗauko ƴar aiki ace za'a haɗata da ita a matsayin kishiya ba, itama kuma matar taka tace ba zata zauna da kishiya ba Fillo ta nemarwa kanta mafita tun bata yi mata lahani ba, to shiyasa na kiraka in faɗa maka cewa ka sakar min jika saki uku rasss domin tafi ƙarfinka ta kuma

Chapter 48 of 73