rayuwa da shi har a bada. da wannan buƙatar ta biya sai a raba auren Ilham da Turaki, kuma ta yanda nake so mutuwar auren ta kasance Dikko yaje gidan da kansa ya umarci Turaki da ya saki Ilham".
Boka ya bushe da wata mahaukaciyar dariya yana ɗaga hannu sama yace,"buƙata taki ta biya Azima, duk yanda kika nema haka za'ai, kuma komai da kika nema zai faru tabbas, angama da wannan buƙata taki ki jira kwanaki biyu kacal".
Fulani Azima ta saki wani murmushi na jin daɗi da kuma nasara, sannan ta miƙawa Jakadiya hannu. cikin rawar jiki Jakadiya tasa hannu cikin jaka ta ɗauko yari da sarƙa da zobe ta saka a tafin hannun Fulani Azima.
har yanzu murmushi bai ɗauke a fuskar Fulani Azima ba ta ajiye sarƙar a gefen boka tace,"wannan kyauta ce na baka. kuɗinta kimanin miliyan goma ne, kyauta ce kawai ba kuɗin aikinka ba".
Boka na murmushi yace,"godiya nake".
tace,"sai muje ga lissafin abinda zan bayar akan aikin".
ya ɗaga kansa sama yana kallon reshen bishiyoyi na tsawon daƙiƙa kafin ya sauke yace,"da farko za ki bayar da miliyan goma, sannan za ki kawowa jikokin Aljanu baƙin jaki guda biyar, sannan za ki haƙa kabari ki yanko mana zuciyar jariri fari wanda ana haihuwarsa ya mutu, sannan kuma muna buƙatar yatsa ɗaya na ita mahaifiyar Dikko".
rufe bakinsa kenan sai suka ga jan ƙyalle ya faɗo gabansu ɗaure da wani dunƙulen abu.
da tsananin mamaki yake kallon abin na tsawon daƙiƙa biyu kafin ya kai hannu ya ɗauko ƙyallen, ya ɗauko shi zaren da aka ƙulle shi na warwarewa.
mamakin dake tare da shi bai gama sakinsa ba yaga baƙar kurciya ta faɗo kan hannunsa a ma ce, sabon mamaki tsantsa ya kama shi.
ya ɗau kurciyar ya haɗe da wannan ƙyallan sannan ya juyo yana kallon Fulani Azima wadda idanuwanta ke a warwaje tana binsa da kallo.
taji yace,"ya akai haka?".
tace,"me ya faru?".
yace,"me na faɗa miki shekaru ashirin da biyar da suka wuce kafin nayi miki aikin Ramla?".
cikin saurin baki da rawar murya tace,"kace kar na kuskura inyi sakacin da asirin nan zai karye, domin duk ranar da ya karye ba zanji da daɗi ba".
tana yin shiru yay wani guntun murmushi na tayata jimami sannan yace,"ban labarin yanda aka yi bayan barinta gida".
jikinta na rawa tace,"lokacin da ta bar gida can ƙasar china ta nufa kamar yanda ka faɗa, bayan wata uku na bi sahunta zuwa dajin da kace anan aka jefa kurciyar domin na tabbatar da taje can ɗin. kuma ko da naje na ganta ɗin a gefen wata bishiya tana cin ganye, itama kuma ta ganni dan har ta dinƙa roƙona akan in taimaka mata bata san ta yanda akayi tazo wurin ba, ta bar Muhammad da Zaytun acikin ɗaki wuta tana ci bata san ba ko Madina ta kula kar yaran su cutu. sai nayi mata dariya nake faɗa mata cewar ni ce silar zuwanta wurin kuma ita da ƙara komawa wajen ƴaƴanta har abada. to muna cikin haka da ita ne sai ga wasu turawa sun zo, suna zuwa suke tambayata cewar nasan wannan mahaukaciyar ne?, da farko har zance musu a'a sai kuma nace ehh, sai ɗaya daga cikinsu yace min to suna da buƙatar siyanta idan zan siyar musu zasu yi tsafi da jininta, ni kuma jin hakan yasa ba tare da wani tunani ba na amince musu dan har inda suke da zama ma muka je tare suka min bayanin cewar zasu ajiyeta aɗakin tsafi tsawon shekara ashirin da shida cif kafin nan sai su zuƙe jinin jikinta suyi tsafin da zasu yi da shi, kuma tare da ni suka sakata a wani ƙaton ɗaki ko taga babu suka kulle suka ce za'a ke bata abinci ne kawai tana ci, don har sarƙoƙi suka saka suka ɗaureta saboda kar ɓacin rana yasa ta gudu, kaji abinda ya faru Boka, ko ɗaya ban saɓa ƙa'idar aikinka ba wallahi".
Boka ya ƙara murmushi sannan yace,"Azima aikinki ya lalace, domin kuwa maganar da nake miki yanzu asirin da yake kan Ramla ya barta kuma ba da jimawa ba za ki karɓi sakamakonki saboda aljanin da yay wannan aikin ba me yafiya ba ne".
Fulani Azima ta dafe ƙirji cikin bayyanuwar tashin hankali a tare da ita tace,"kamar ya Boka ban gane ba, me kake so kace min?, ta ya hakan zata faru?".
yana ɗago matacciyar kurciyar da jan ƙyallen yace,"waɗannan sune asirin da ke kan Ramla, wannan kurciyar da kike ganinta tun ranar da ta ɗauki Ramla bata ƙara zuwa nan ba sai yanzu, wanda ke tabbatar da cewa Ramla ta baro inda ta ke ta dawo cikin garin nan, kuma mutuwar kurciyar nan shine zahirin cewa babu wani abu da ya sami Ramla".
sai ya jefar da kurciyar sannan ya ɗauko ƙyallen yaci gaba da cewa,"wannan kuma shine ƙyallen da muka ƙulle ƙwaƙwalwar kifaye acikinsa saboda Ramla ta manta komai, dan haka faɗowar wannan da kuma warwarewarsa ya shaida mana Ramla ta dawo cikin tunaninta".
ya jefar da ƙyallen ma sannan ya juya bayansa yana kallon akuyar dake tahowa tana kuka yace,"idan za ki iya tunawa wannan itace akuyar da kika kawo muka ɗaurewa baki saboda rufe bakin Ramla, tsawon wannan shekarun tana nan tare da ni bata taɓa kuka ba sai yau kuma ayanzu, hakan ke tabbatar da cewa bakin Ramla ya buɗe duk inda ta ke yanzu tana can tana magana".
Fulani Azima ta ɗora hannu akanta tare da kurma ihu tace,"na shiga ukuna".
Boka yace,"ba ki shiga uku ba tukunna sai kinga yanda reshe zai juye da mujiya".
ya faɗa yana sa hannu ya daki ƙasar dake gabansa sannan yace,"kar hankalinki ya tashi sosai, ke ko garin da kike ba za ki bari ba, amma sai dai za ki kwanta baƙar jinyar da za ki ji gwara ace haukacewa kika yi ko kuma ɓatan kika yi da wannan ciwon da zai kamaki. domin za'a zo har kan gaɓar da hatta ƴarki ba zata iya zuwa kusa da ke ba".
Fulani Azima ta fashe da kuka sosai tana cewa da boka yay mata rai. cikin wata razananniyar tsawa yace da ita,"Azima ta shi ki bar mana wuri". ya faɗa yana nuna mata hanya.
suka miƙe tare ita da Jakadiya jikinsu sai rawa yake suka fita daga wajen tana ta uban kuka. suna fitowa tayi wani kukan kura ta shaƙi wuyan Jakadiya tana girgizata tana faɗin,"wallahi ba ki isa kin tona min asiri ba, ba zan kwanta cuta ba kibi ta bayan fage kije ki fallasa ni, zan kasheki sannan zan je in kashe Ramlar ma".
haka ta dinƙa sambatun magana bata saki wuyan jakadiya ba har sai da ta tabbatar ta mutu tukunna ta jefar da ita a wayen, ta bar wajen kamar ana tankaɗata har ta fito daga cikin jejin, tana zuwa ta buɗe mota ta shiga Driver yaja su, sai da suka shigo cikin gari sannan tasa ɗankwalinta ta shaƙo wuyan driver shima tana faɗar,"ba zan barka a raye ba kaima ka tona min asiri, ba zan barka kaga ciwona baka tona min asiri".
bata sake shi ba sai da ta tabbatar ya mutu, kuma kamin Fulani Azima tayi wani ƙoƙari na karɓar kan motar, motar ta gangara ta faɗa gefe, nan ta-ke glass ɗin motar ya tarwatse da yawa suka soki cikin kanta, ta kurma ihu tana neman ɗauki tana ƙoƙarin fitowa a motar, bata ankara ba ta kai fuskarta saitin wani glass da yay kamar kibiya ƙwayar idonta ɗaya ta soki glass nan take ruwan idon ya shiga tsiyayewa.
*A dai-dai wannan lokacin.*
*Yanda Abin ya kasance da kuma yanda abin ke faruwa.*
sanda Turaki ya ƙaraso wurin da kidnappers suka buƙaci da ya ajiye kuɗin, yay parking motarsa ya fito ɗauke da dumin jakar kuɗin.
ya tsallako side ɗin da suka ce yay tafiya me nisa sannan ya ajiye jakar a wajen, ya ɗauko wayar Maama dake aljihunsa ya ɗaga calling ɗinsu dake shigowa.
daga can ɓangaren yaji ance,"kai ne kasa coffee yadi?".
yace,"ehh ni ne". ya faɗa yana duddubawa ko zai ga ta inda mutumin yake. sai yaji mutumin na dariya yace,"ai ba zaka taɓa ganinmu ba ka bar wahalar da kanka da waige-waige, ka juya ka bar wajen ka koma bakin motarka ka jira yaronka zai zo ya sameka".
jin haka yasa Turaki saurin juyawa ya bar wajen, for the next 5minutes sai ga mutumin yazo ya ɗauki jakar shi kaɗai, cikin sauri yake tafiya don barin wajen, a lokacin Turaki ya fito daga jikin wata rila da ya laɓe.
yasa hannu a bayan wandonsa ya zaro bindigar da bai taɓa riƙeta ba sai a yau, ya saita ƙafafun mutumin ƙwayar idonsa na hasko masa yacca ake harbi acikin film, bai taɓa ganin bindiga ido da ido ba sai a yau da ya shiga office ɗin DSP ya ɗauko ba tare da sanin kowa ba, kazalika bai taɓa riƙe bindiga ba balle har yay attempt na harbi, but today bindiga tazo hannunsa, and zai gwada amfani da ita ko da ace wannan itace dama ta ƙarshe da yake da ita a duniya.
ya saita ƙafar mutumin ba don yana tunanin dai-dai ya saita ba, kuma babu ɓata lokaci kai tsaye ya saki bullet, kuma cikin sa'a bulle ɗin ya shige ƙafar mutumin, hakan kuma bai sa Turaki ya haƙura ba ƙara sakin bullet ɗin wanda a yanzu kai tsaye ya wuce zuwa kaɗar mutumin daidai sanda ƙafafunsa ke durƙushewa a ƙasa yana sakin jakar kuɗin ya riƙe kafarsa dake zubar da jini.
abinka da wanda bai san kan lamarin ba kawai sai ya jefar da bindigar a wajen ya kwasa a guje ya ƙarasa gaban mutumin, ta baya ya damƙi kwalar rigarsa ya ɗago da kansa, ya zagayo ta gabansa yasa gwiwar ƙafarsa ya daki haɓarsa, ta-ke jini da ƙwaƙwalwarsa suka haɗu waje ɗaya, ƙwayar idonsa ta firfito waje yana buɗe su da ƙyar saboda azabar harbin da ya shige shi ya kalli Turaki, cikin zafin nama Turaki yasa hannu ya fizge facemask ɗin dake fuskarsa.
yana faman huci kamar mayunwaci za ki yace,"ina yarinyar ta ke?". ya faɗa cikin ɗaga murya sosai.
sai kuma ya sassauta muryarsa yace,"zaka tsira da ranka, kuma zan kai ka asibiti sannan zan barka da wannan jakar kuɗin ka tafi safely, but first tell me ina yarinyar ta ke?".
shirunsa ya haɗe da ƙarasowar ƴan sanda wajen, suna zuwa ɗaya daga cikin ƴan sanda yasa ƙafa ya daki gabansa atake ya ƙwalla wata razananniyar ƙara saboda yacca yaji kamar za'a zare masa rai, babu shiri ya ɗaga hannu yana yi musu nuni da katangar gidan dake can gabansu.
Turaki is the first one da ya bar wajen a cikin gudu, wasu cikin ƴan sanda suka mara masa baya, yayinda wasu mutum biyu suka ɗauke wannan wanda Turaki ya harba sukai mota da shi.
harbin farko da Turaki yayi su Amir sunji a lokacin suna laluben Fillo acikin gidan, kuma rashin tabbatar da cewar harbin bindigar suka ji da gaske yasa basu bi ta kai ba sai a harbi na biyu, anan hankalinsu ya tattaru wuri ɗaya saboda haka duk sai suka dakata da batun nemanta suka koma ta yanda zasu tsira.
Amir yace,"duk yanda akayi shegun mutanen nan da police suka zo".
wani me kama da shi yace,"tabbas kuwa, but har ta ya mu kayi sakacin hakan ya faru?".
sai ya juya yana kallon mutumin da ya taimakawa Fillo yace,"hau katanga ka duba mana".
yana hawa katangar ya ƴan sanda daga can nesa kamar cinnaku sun baibaye faɗin wajen, hakan yasa da ƙarfi yace musu,"police ne mota har guda uku".
yana faɗar hakan ya dirge ta baya dan ba ya tunanin zai iya bari a rutsa har da shi.
su kuma nan suka fara neman hanyar guduwa ta ƙofar baya da Fillo ta bi, sai dai cikin rashin sa'a suna buɗewar suga police tsaitsaye a wajen riƙe da bindigu, kuma babu wata-wata suka shiga sakar musu harbi ratata, harbin ya sami kusan mutum huɗu su kuma sauran suka koma ciki da gudu don tsira da ransu, sai dai ko a lokacin tuni wasu ƴan sandan ma sun cika gidan.
"raise your hands up".
su shidan da suka rage ba'a harba ba suka ɗaga hannayensu sama time ɗin da Dsp yay arresting ɗinsu.
Turaki kuwa tun shigowarsu babu ta kan wanda yabi sai laluben inda zai ga Fillo, haka ya koma kamar wani zautacce ya shiga can ya fito ya faɗa can ya leƙa can, kaf babu inda bai duba acikin gidan nan bai ganta ba, sai ga shi ya faɗo parlon kamar an jefo shi yana zazzare ido ko zai ganta anan duk da perlon ya fara dubawa.
jiri ya ɗebe shi ya tafi ya faɗa kan wata kujera dake wurin, yasa hannu ya dafe kansa da yake jin yana barazanar tsage masa, ya rumtse idonsa sosai yana rasa me ke masa daɗi a duniyarsa, wucewar daƙiƙa ɗaya ya ɗago kai ya buɗe idonsa wacca ƙwayar ta kaɗa tayi jawurr ya sauke kallonsa akan Dsp yace,"yallaɓai banfa ganta ba, bata cikin gidan nan yallaɓai".
muryarsa ta fito cikin bala'in rauni kamar zai yi kuka.
Dsp na tsaye daga gefe yana kallonsa bai ce masa komai ba, har sai lokacin da wasu ƴan sanda guda uku zo, waɗanda sune aka saka su nemo Fillo a sanda suka shigo gidan.
"yallaɓai babu wurin da bamu duba ba acikin gidan nan kaf babu yarinyar".
Dsp ya kalli tawagar su Amir da suke tsaye hannaye a sama idanu duk sun raina fata, ya sakar musu wata uwar tsawa yace,"ku faɗa min ina ku ka ɓoye yarinyar?".
da farko duk shiru suka yi sai da ya ƙara doka musu tsawar da tafi ta farko tukunna ɗaya acikinsu yana karkarwa yace,"mu ma bamu san inda ta ke ba".
yana rufe baki yana jin saukar harbi a gwiwarsa, ba shiri ya saki ƙara ta azaba yana duƙe a wajen, tuni zufa ta shiga haɗo masa yana faɗin,"wallahi bamu san inda tayi ba ta gudu tun ɗazu, muna cikin nemanta ne ma ku ka zo".
furucin nasa yasa Turaki miƙewa daga kan kujerar da yake a kiɗime yana faɗin,"what!, ta gudu?, baku san ina tayi ba?".
ya furta yana jin kamar zuciyarsa zata buga.
Dsp ya ƙara harbin ƙafar wanda yay maganar, azaba ta ƙara ratsa shi ya kuma ihu wajen faɗin,"dan Allah kayi haƙuri". Dsp ya ƙara sakar masa wani a hannu, a wannan karon ko motsawa bai yi ba don tsabar azaba, maganarsa ta fito a hankali yana cewa,"na rantse da Allah ta gudu tun ɗazu".
Turaki yana shirin sauke ƙwayar idonsa kan mutumin kawai sai Allah ya kai idonsa kan Amir, yay saurin maida kallonsa kan Amir gaba ɗaya yana ƙare masa kallo da son tabbatar da abinda ƙwayar idonsa ke gani.
cikin kansa ya haska da hoton lokacin da yake tsaye gaban Fillo har yana riƙe ma ta hannu har zuwa lokacin da ya juya ya bar wajen.
"You!". Turaki ya faɗa in shock. sai kuma ya nufi wurin Amir gadan gadan kamar zakin dake cikin yunwa ya ga abinci.
yana zuwa yasa hannu ya shaƙi wuyan Amir, ya dinga tura shi da baya har sai da ya kaisa bango ya gwara kansa a jiki. "waye kai?". Turaki ya tambaya .
tun Amir bai basa amsa ba ya dunƙule hannunsa ya bawa fuskarsa wani mahaukacin naushi wanda yay sanadiyar ɗaukewar ji da ganin Amir na wucin gadin, hakama haƙorinsa ɗaya ya tsinke ya fara lilo.
Amir ya ɗago kansa a galabaice sai dai tun bai gama buɗe idonsa ba Turaki ya ƙara sakar ma fuskarsa mugun naushin da yafi na farko, kan Amir yayi ƙasa jini na zuba ta hancinsa. Turaki ya ƙara yin kukan kura ya ɗago da fuskar tasa ya kuma naushin fuskarsa a gefen ido, take jini ya taru cikin idon Amir, haka ma jini ya shiga fita ta hanci ta baki.
Amir yay yunƙurin ƙwatar kansa amma inaa lokaci ɗaya Turaki ya damƙi hannu da wani irin ƙarfin da bai san yana da shi ba barƙala hannun har sai da hannun Amir ya ɓalle.
a taƙaice dai Turaki sai ya koma kamar mahaukaci wajen dukan Amir, ya koma tamkar zakin da ya shekara ba abinci ya kuma samu abinci a daidai lokacin da yake so, naushi yake ta kaiwa fuskar Amir hagu da dama cikin ƙaraji yana tambayarsa,"who are you?".
sai da fuskar Amir ta kumbura tayi suntum babu kyan gani, ko'ina ya farfashe banda uban jini dake zuba ta gefen idonsa, tukunna Turaki ya bar fuskar tasa ya kai shi ƙasa yana tattaka ruwan cikinsa, yasa ƙafa ya dako shi ta can ya doko shi ta can, yay fatali da shi ta can, ya jefa shi ta can ya gwaru da bango, haka Turaki yayta ball da shi kamar wanda ya samu ball ɗin gaske.
tun Amir na iya ihu har yazo ya daina, tun yana buɗe baki yana uban nishi da son yin magana har ya kasa, shi kansa so yake yace da Turaki who is he, dan wannan dukan da yake masa ko uwarsa ya kashe sai haka.
da Dsp yaga dai Turaki na ƙoƙarin yin kisan kai yace da ƴan sanda dake tsaye,"ku dakatar da shi".
amma me ƴan sanda uku akansa sun kasa ƙwace shi daga kan Amir, suma ɗin duk sai da ya watsa su gefe yana miƙewa cikin huci da cewar duk wanda ya ƙara zuwa kusa da shi sai ya haɗa da shi.
bai ma san sanda yasa bayan hannu ya kwaɗe police ɗin dake ƙara yowa kansa ba, ya fizgo shi gabansa ya zare bindigar dake gaban wandonsa ya koma ya haye ruwan cikin Amir, ya cije fuska yana ɗaga bindigar ya bugawa Amir a kansa, ta-ke jini da ƙwaƙwalwar Amir suka haɗe wuri guda yaji kamar kansa babu komai, tukunna Turaki ya saita ƙirjinsa da bindigar yana bala'in huci yace,"for the last time i will ask you, tell me who are you?, in ba haka ba wallahi sai na sakar maka harbi a zuciyarka".
in ace da damar magana Amir zai yi, to amma ankai stage ɗin da yatansa ɗaya ma ba zai iya motsawa ba, balle kuma ya buɗe bakinsa da uban jini ya taru aciki yana tsiyayowa ta waje, shi da wannan mahaukacin dukan da Turaki ke yi masa ma da harbe shi ɗin yayi da ya huta, kuma baya jin ba zai mutu ba muddin Turaki ya ƙara dukansa, azzakarinsa kansa jini yake saboda Turaki ya daki wajen ya kuma ya daka yasa hannu ya kama ya murɗa, to ko da iyaka haka aka barsa ai yana jin sun gama ɗaukarwa Fillo fansa dan yasan ko ace ya tsira da ransa to tabbas a hoto zai tashi dan yana da yaƙinin Turaki ya gama kashe masa gaba, bai da burin da ya wuci a yanzu irin ya buɗe baki ya bawa Turaki haƙuri, kuma yaga Fillo ya nemi yafiyarta.
Turaki na ƙoƙarin sakin bullet a ƙirjin Amir B
Dsp ya taho da sauri ya bige hannunsa bullet ɗin ya sauka a kafaɗar Amir, Amir ya saki wata gigitacciyar ƙarar da shi kaɗai yaji kayarsa babu wanda yaji, don hatta wurin fitar sautin muryarsa Turaki ya gama kashe shi.
Dsp ya fizge Turaki daga kansa yay gefe da shi yana faɗin,"wa ya baka izinin yin harbi?, are a police?, to ko mu ba'a bamu umarnin yin harbi kai tsaye ba".
Turaki da duk ya gama ficewa a hayyacinsa yana ta uban huci yace,"yallaɓai na taɓa ganinsa a ƙofar gidanmu tare da ita, yafi ƙarfin rabin awa awajen kafin ya ƙyaleta ya tafi, and am sure shine ya ɓoyeta ma a yanzu, ka tambayesa inda ya ɓoyeta tun ban ƙarasa shi ba wallahi".
Dsp ya dafa kafaɗarsa yana faɗin,"calm down mana, yanzu idan muka kashe shi waye zai faɗa mana inda ta ke?, to dole mu bi komai a hankali ba wai mu ɗauki mataki mai gaba ɗaya ba".
Turaki ya dunƙule hannayensa duka biyun yaja da baya yana zaunawa kan kujera tare da fesar da zazzafar iska daga bakinsa.
ya rumtse idonsa sosai yana ɗaga kansa sama, ba komai yake hangowa ba sai sanda Amir ke tare da Fillo, muryarsa na fita a hankali yace,"Fulani where are?, bana ce miki zan zo ba yanzu, why did you leave?".
sai ya rumtse idonsa yana tunawa da maganar da ta faɗa masa,_"wai sai sunyi amfani da ni"._ bai san lokacin da daki hannun kujerar ba har sai da ƙashin hannunsa yayi ƙara.
ya kifa kansa a hannun kujerar yana faɗin,"ina kika tafi?, Fulanii why?, why Fulani?, how do you think i will survive without you by my side?, please tell me where you are zanzo na ɗauke ki ko da ace daga na ganki zan mutu".
ya faɗa a sanda wannan jarumtar tasa ta karye, raunaninsa ya wanzu, kukan dake can ƙasan zuciyarsa ya ɓalle, hawaye ya sauko masa ƙwayar idonsa na haska masa hotunan faruwar abubuwa kala-kala a tare da Fillo.
"idan kika tafi da wa zanyi rayuwar farin cikin gidan aure irin wadda na tsara mana ni da ke kaɗai?, wa ye zai tayani nemo Mum idan ba kya nan?, dan Allah karki min nisan da ba zan saka miki da ceton rayuwata da kika dinƙa yi ba".
sai kawai ya cije leɓensa na ƙasa ya kuma yin kukan kura yay kan Amir a fusace, da hanzari police suka ruƙo shi akai waje da shi.
*A dai-dai wannan lokacin.*
gudu suke sosai babu waige babu tsayawa har sai da suka ga cewar sun shigo cikin gari, kuma a lokacin ne Fillo ta faɗi tana kuka tace,"Mum ba zan iya ba na gaji".
tausayin kansu ya kawo zubar sabon hawaye saman fuskar Hajiya Ramla, ta duƙa ta kamo Fillo tace,"ki daure mu ƙara yin gaba, kinga nan wajen ma ba kowa zasu iya kama mu anan".
Fillo tace,"Mum ki barni ke ki tafi, su Adda Zaytuna suna can suna jiran dawowarki, Turaki kullum sai yayi kuka akan rashinki, dan Allah ki tafi Mum ƴaƴanki na buƙatar ganinki a raye".
Hajiya Ramla ta dafe kanta da ta-ke jin wani abu na mata yawo aciki, so ta-ke ta ɗauki magangun yarinyar ta saka su a ɓangaren tunaninta ko Allah zai sa ta gane abinda ta-ke cewa.
kuma kamar gimlawar Jinnu haka Hajiya Ramla taji maimacin furucin da Fillo tayi acikin kanta. ta dafe ɓarin kanta tana ta ambaton Allah har sanda taji wani abu na tafiya acikin kanta yana fitowa yana barin jikinta. lokacin kuma ta saki ƙara tana dafe kan sosai tana ƙara ambaton Allah.
wucewar daƙiƙa biyu ta buɗe idonta ta sauke su a wurin da ta-ke, hankalinta da tunaninta da suka dawo dai-dai suka fara tambayar a ina ne nan ɗin?.
magana ta farko da ta fara tunawa kamin gushewar hankalinta itace,_"ni Fulani Azima ni ce nayi miki asiri Ramla, saboda kin aure min farin cikina, dan haka kamar yanda na rasa Dikko kema kin rasa shi har abada domin asirin dake kanki har ki mutu ba zai barki ba, ƴaƴanki kuma zan saka su a tafin hannu dan suma sun shiga gonata tun da har ubansu yay kuskuren haifarsu da wata ba ni ba"._
wannan furucin na Azima shine furuci na ƙarshe da zata iya cewa ta tuna kafin hankalinta ya bar jikinta gaba ɗaya, ta rufe idonta tana tuna amintar dake tsakaninta da Fulani Azima tun suna Oxford University.
sai kuma tayi hanzarin buɗe ido ta maida kallonta kan Fillo wacce wahala tasa tayi laƙwas sai nishi kawai ta-ke saukewa. ta kamo hannunta jikinta na karkarwa tace,"ina ne nan ɗin muke?, kuma ke wacece?, sannan ina Babana da Zaytuna?, aina zan gansu?".
Fillo tace,"Mum suna gida ki tafi kije ki samesu, ni ƴar aikin gidan ce". tayi maganar da ƙyar tana jin ƴaƴan cikinta kamar zasu fito saboda masifar yunwa da ƙishiryawa.
Hajiya Ramla ta ɗagota jikinta tana faɗin,"ta ya zan tafi na barki bayan kin taimake ni, ke ya akai kika tsinci kanki a wannan halin?".
tambayar ta kawo zubar hawaye me zafi akan kuncin Fillo tace,"kidnappers ne suka ɗauke ni".
Hajiya Ramla tace,"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yi haƙuri ki daure ki tashi muje kinje, kin san hanyar da zamu bi muje asibiti?, domin kina da buƙatar ganin likita ƴata".
Kuka ya kubcewa Fillo tace,"Mum ai ba zan gane hanya ba, ban san nan ɗin ina bane dare yayi sosai".
Hajiya Ramla tace,"kamar kin ban waya ɗazu ko?".
kai kawai Fillo ta iya ɗagawa dan ƙarfinta ya ƙare bata jin akwai sauran yawu da ya rage a bakinta da zata yi magana.
tasa hannu a rigarta ta zaro wayar Hajiya Ramla ta karɓa, ta danna 0 tana ƙoƙarin tuna lambar Baffa ko ta Maama amma sai taji ta kasa, tai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 37 Chapter of 73