nan ya tafi bata ko saurari duk kalar lallashin da yake yi mata ba.
"kinga yau burabusko akayi...Allah sarki su Yami sun sha aiki". Maganar Kaka keyi tana ɗiban burabuskon dake cikin kwano ta saka a baki. ta kalli Fillo tace,"tunda kina sonsa daure ki tashi kici".
Fillo taja majinar hancinta tana ƙoƙarin tsaida kukan da takeyi tace,"miyar mene?".
Kaka tace,"miyar ganye ce, kuma yayi daɗi sosai".
Fillo ta koma ta kwanta,"ki aje min zanci anjima". ta faɗa sannan taci gaba da kukan kamar ƙanƙanuwar yarinya.
"Allah ya shirya min ke...ni banga wani hankali a tare dake ba da Amir ya gani ya nace miki".
"ni daga yau ai babu ni babu shi, can yaje ya nemi wata ba dai ni Haliman Dada ba, dan ba zanje gidan da za'a kassara rayuwata ba".
Kaka ta taɓe baki,"to dama Fillo waya ɗauko shi ya kawo miki. Ke kika yayibo abinki".
Kaka na sauraron radio akai sallama daga bakin ƙofa, ta amsa tana cewa a shigo. Zaytuna ta ɗaga labulen ɗakin daya sha jiki ta shiga ta ƙara yin sallama.
"jaɓɓama lale". Kaka ta faɗa a sanda ta ke bin Zaytuna da ido da rashin gane wacece. Ita kuma ta nemi wuri zata zauna a ƙasa Kakan tace,"ah haba dai ga darduma yi haƙuri ki shimfiɗa hannuna da maiƙo".
Zaytuna ta karɓi darduman ta shimfiɗa ta zauna akai. Kaka tace,"sai dai ban gane wacece ba wallahi". Tai maganar fuskarta ɗauke da fara'a, tana so kuma ta gano a inda ta san kamannin dake fuskar.
"ehh ba lallai ki shaidani ba gaskiya. Daga cikin gida dai nake".
Kaka ta washe baki tace,"ƙwarai kuwa ga kamannin Alhaji nan...sannu da zuwa, baƙuwar tamu ashe babbace...bari na kawo miki ruwa".
Ta miƙe Zaytuna tace,"a'a wallah Inna ki barshi ai yanzu zan wuce". Kaka tace,"ai ko ba za ki sha ba saina kawo". Ta faɗa tana nufar inda kwandon wanke-wankensu yake ta ɗauko farantin roba, Allah ya taimaka akwai purewater wanda Amir ya siyo musu ɗazu mai sanyi kuwa, ta sako guda biyu ta ajiye agaban Zaytuna suna daɗa gaisawa.
Zaytuna bata da niyyar shan ruwan saboda a ƙoshe ta ke, amma gudun kar Kaka taji babu daɗi dole ta ɗauka tasha, tasan tsohuwar zata iya ganin kamar ko ƙyanƙyami ne ya hanata sha. balle ita bata ma ga rashin tsabta a wajen ba, komai fes-fes wajen ɗal-ɗal an share, shi kansa ɗakin sai ƙamshin turaren wuta ɗan tsinke yake, duk idon daya ga wajen dai ba zai ce wurin ƙazamai bane.
Ɓangaren masu aikin a haɗe yake, amma kuma kowa da gefen da yake.
kan Kaka a ƙasa tace,"ranki ya daɗe Allah sa dai ba wata matsala bace". Zaytun tace,"a'a Inna lafiya lau, kawai dai na shigo ɓangaren naku ne ina gaidaku". "Allah sarki aikuwa mun gode".
Zaytun ta miƙawa Kaka farar leda mai kauri irin ta store tace,"ga wannan, atamfofin marasa ɗinkin naki ne...akwai doguwar riga guda biyu sai a bawa yarinyar, banma san da ita ba ne sai da Maijidda ke gaya min...da yake Maijiddan kawai na sa ni sauran duk sai yanzu nake ganin fuskokinsu".
Kaka tace,"Allah sarki, ai Maijidda ita ta jima a gidan nan, su kam ai duk sai daga baya suka zo...itama ta wurin nawa bayan rasuwar mahaifiyarta na ɗaukota".
Lokaci ɗaya idon Zaytuna ya kawo ruwa, kewar tata mahaifiyar ya kamata, tai saurin danne hawayen dake ƙoƙarin zubo mata, wannan ciwon dake manne a zuciyarta ya taɓu.
Muryarta so cool tace,"Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu". Kaka ta amsa da amin, ita kuma ta yunƙura ta miƙe, dubu biyu ta ciro a purse ɗin dake hannunta ta ajiyewa Kaka. "gashi ai adu'a wa iyayenmu".
Kaka dake ta zabga godiya ta koma jero adu'oi kala-kala, ita kuma tana ta amsawa da amin cike da jin daɗi. Yayin da taji ƙaunar Kaka ta shiga ranta, dan ita a rayuwa babban abinda zaka yi mata a duk duniya ka burgeta shine kaiwa iyayenta adu'a, tabbas kai mata hakan zata girmamaka kuma zata mutuntaka. Kuma har gaban abadan ba zata taɓa mantawa da kai ba, kuma haka ta dinƙa maka alkhairi kenan.
Har ta fita bata lura da Fillo dake gefe ɗaya a rakuɓe ba, ta nannaɗe jiki da wani mayafin Kaka me kauri saboda sanyin da ta ke ji, fuskar nan tayi jajur tsabar ansha kuka an ƙoshi. ta haɗe rai babu annuri ko kaɗan. ƙememe tana ganin Zaytuna amma taƙi gaisheta kuma har haɗa ido sunyi, kuma tana lura da yanda Kaka ke aikin jefa mata harara amma tayi fuska, shi yasa itama Kaka ɗin taita adu'a a ranta Allah yasa kar Zaytuna tura da ita balle ta bata kunya.
Kaka da ta dawo daga rakiya tace da Fillo. "ke dai ki sauya hali dan gidan wani za ki je, kuma wannan halin naki dai ba halin zama uwa ta gari ba ne".
Maijidda ta shigo, tayi wajenta tana yi mata dariya tare da tsokanarta akan kukan allura. Bata kulata ba tayi mata shiru, ita kuma ta miƙa mata ƴar ƙaramar waya ƙirar nokia irin ta da can wadda aka fara sakawa sunan rakani kashi, wayar duk ta jeme tasha kyauraye, banda Yami babu ma me iya riƙe wayar.
"Amir ne ya kira yace na kawo miki. Wai ya kira ta Kaka a kashe".
Kaka tace,"ai ita ta tsinka cajar garin shirmen banzanta".
Fillo ta kalli wayar dake kan cinyarta, sannan ta kalli Maijidda da jajayen idanuwanta da suka sha kuka suka ƙanƙance tace,"kin ɗauke min ita a jikina ko sai na ƙarasa kasheta".
Sanin cewar zata aikata Maijidda tayi saurin ɗaukewa tana faɗin,"yanda Yami ke ji da wayar nan kika fasa aini za ki jawa faɗa".
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*7*
Acikin ɗan ƙaramin falon nasu, Fillo ce zaune ta takure daga jikin bango, jikinta gaba ɗaya a nannaɗe da babban mayafin da suke rufa da shi saboda sanyin da ta ke ji, kallo ɗaya za kai mata ta baka mugu mugun tausayi saboda yanda ta rame duk da cewar ita ɗin dama asali ba mai ƙiba ba bace, amma kana kallon ramarta a yanzu zaka san ta lalura ce.
Fillo cikin tuƙewar wani kukan ta kifa kanta saman gwiwoyin ƙafarta, kukan daya kusa yin rugu-rugu da zuciyar Amir dake zaune yana fuskantarta daga ɗan nesa da ita, yana jin zuciyarsa na matsewa da wani irin zafi.
Ya ɗauke ƙwayar idonsa daga kanta ya mayar kan magungunan daya ɓallo a hannunsa, sai kawai ya janyo ledar magungunan dake kusa da shi ya zuba su aciki ya ɗaure. Ya sauke numfashi very calmly yace da ita.
"ba saboda na takura miki ba, saboda lafiyanki Halima...but kiyi shiru ki bar kukan na zubar kin fasa sha".
zatonsa furucinsa zai yi tasirin da zai tsayar da kukan nata, amma sai yaji taci gaba da abunta kamar ba da ita yay maganar ba.
Sai ya duƙar da kansa a cikin damuwar da shi kaɗai yasan me yake ji, Allah ma ya sani, da ace yana da iko da har abada Halimatunsa ba zata yi ciwo ba, haka kuma da ace da yanda zai yi ciwon nan ya bar kanta ya dawo kansa tabbas da yayi hakan ko da hakan zai zama ajalinsa, shi dai ya ganta cikin ƙoshin lafiya da walwala.
ya ƙara ɗago kansa ya kai kallonsa gareta, ganin har yanzu kamar ba zata daina ba yace da ita,"Halima kin san kuwa irin zafin da nake ji a zuciyata?, ki yiwa girman Allah ki daina wannan kukan wallahi ko kaɗan bana sonsa, yana taɓa zuciyata...indai magani ne nace ba za ki sha inace shikenan ko?".
Fillo ta ɗago da kanta, idon nan ya ƙara yin loko yayi jawur, jijiyoyin kanta sun fito raɗau kamar idan kasa hannu zaka kamosu waje. Amir ya tsareta da idanu ita kuma tana saka hannu ta goge hawayen, amma da ike ita ɗin me ruwan hawaye ce tana gogewa wani na kuma sakkowa.
Ita ɗaya tasan irin azabar da ta ke ji a gaba ɗaya jikinta, ita ɗaya tasan me ta ke gani acikin barcinta tun daga waccan ranar zuwa yau.
cikin muryarta da ta disashe da kuka tace,"ni nace maka waɗannan magungunan naku babu abunda zasu yi min. ka daina asarar kuɗinka Amir, kawai a kira Malami yayi min adu'a".
Amir dai dubanta yake da mamaki, ita ba aljanu ba amma kusan sati biyu kenan da ta ke ciwon nan ta kafe akan ita dai a kira Malami yay mata karatu, ba maganin asibiti bane maganin ciwon da ke damunta.
kuma anyi anyi ta faɗa me ta ke ji tace ita babu komai zazzaɓi ne kawai. Asibiti kuma a duka test ɗin da suka mata sunce ma babu maleria.
Cikin kwantar da murya yace,"insha'Allahu kin daina shan maganin, amma ki bar kukan gaba ɗaya hakan kawai zai sa na kira Malam yay miki adu'a". Ta ɗan kafe shi da ido tana tunani cikin ranta, maganarsa da ta kutso cikin kanta ta katse abunda ta ke tunani.
"amma tunda nima kusan Malamin ne nayi maki adu'an ko Halimatu na?".
Kai kawai ta gyaɗa masa, ta sani ɗin in har ba'a kira Amir Babban Malami ba to ba za'a kira shi ƙarami ba, Babansa Malami kai kafatanin gidansu ma, kwatancen gidansu ma idan za'ai gidan malamai ake cewa, kuma kusan shi ya gado mahaifinsa 100% cikin yara 28 da Allah ya ba shi.
Ya taso ya matso kusa da ita, ya bar tazaran inches tsakaninsu. "me da me kike ji?".
Ya tambayeta yana kai hannunsa ya taɓa goshinta. Sai ta rufe ido tana jan numfashi, so ta ke ta tambaye shi abinda Kaka taƙi amsa ma ta, ta tambaye shi makomar wanda ya ƙona asirin da ba nasa ba, kuma so ta ke ta yi musu bayanin ta ƙona asiri, ko ta samu ta waraka daga wannan masifar da ta jawa kanta.
to amma ta ya?, ta ina zata fara?, da wanne irin bayani zata faɗa musu?, wacce fahimta zasu yi ma ta?, shin zama su yarda da ita ne?. Bama zata soma wannan katoɓarar ba, saboda idan Kaka ta fahimceta ba lallai Amir ya fahimta ba, kuma wataƙila idan wani yaji ta ɗaure kanta akan cewar ita ke da niyyar masa asirin.
Ita dai ta sa ni ko meke damunta a halin da take ciki yanzu yana da nasaba da ƙona asirin da tayi, ba zata iya tantance irin mummunar halittar da ta ke gani cikin mafarkinta ba, ita tayi hakan bisa tausayi da kuma son taimakawa wanda ake son cutarwa, to amma kuma shikenan daga taimako?.
Sai kawai ta rumtse idonta sosai, tabbas ba Muhammad Turaki kaɗai ba da akayi asirin saboda shi, tun daga kan wanda tunanin yin asirin yazo kansa, da mai zuwa ya amso asirin, da masu zuwa suyi aikin asirin, duka sun shiga uku, rubuce yake a tafin hannunta sai taci uwar uban duk wanda yay sanadin shigarta wannan mawuyacin halin.
"ya kike jin ciwon kan?". Amir ya tambaya with a look of concern and sympathy.
Ta haɗiye abunda ba zata kira shi da yawu ba, sannan ta buɗe ido takalle shi. "ina jin kan kamar ba nawa ba, kamar ma ba na mutane ba".
Ya sauke numfashi kamin yace,"sannu". ita kuma ta gyaɗa masa kai kawai.
Nan Amir ya kama kan nata ya shiga karanto adu'oi yana tofa mata, tsawon mintuna yana yin hakan kamin ya tsaya. Sannan ya miƙe ya ɗauko ruwan faro da yake siyo mata yanzu ya buɗe sabo ya tofa adu'ao aciki ya bata tasha, kana ya rufe ya aje mata sauran a kusa da ita.
Fillo ta rufe idonta ta jinginar da kanta ajikin bango, her breathing slows down, abu kamar almara sai taji ciwon kan daya addabeta tsawon sati biyu ya fara tafiya, har ma tana neman ta rasa shi gaba ɗaya. Hatta wannan nauyin da jikinta yay shima ya fara saki, to 10minutes sai taji komai yayi sauƙi kamar ba ita ba.
Maijidda tayi sallama cikin ɗakin daidai da buɗe idon Fillo, ta ajiye ƙwaryar furar dake hannunta tana zama kusa da Fillon.
"sannu". Tace da ita kamin ta juya gun Amir tace mishi,"sannu da zaman jinya Amir".
Yay murmushi kaɗan sannan yace,"yauwa Kuluwa".
Ya faɗa da zola dan bata son sunan, tace,"ni dai daga yau idan ka ƙara kirana da wannan sunan sai na rushe gwamnatin da ka kafa a zuciyar ƙawata".
"yaushe kika yi wannan isar?". Yay tambayar yana kallon inda Fillo ta ke, wadda ta samu relief a yanzu, dan har idanuwanta sunyi tangarau, tana kallonsu ne kawai bata cewa komai.
Maijidda tace,"ka dai bi a hankali kawai, ita masoyiyar taka ai tasan girman isar da nake da ita".
"ah lallai ne mai girma Kuluwa". Suka yi gajeriyar dariya su duka.
Amir yace da Fillo,"ya kike ji yanzu?". Idonta akan ledar magungunan dake can bayansa tace,"idan ka tashi tafiya ka tafi da waccan ledar ka jefar a bola".
ya waro ido waje yace,"haka likitan ya karanta mana dama?". ta ɓata rai tace,"koma me ya karanta ni dai a zubar da su kawai, ai naji sauƙin".
Maijidda tace,"ai sai ki bari idan Kaka tazo kyayi mata wannan bayanin".
Sai kawai Fillo tayi narai-narai da idanuwa, fuskar nan a marairaice tana duban Amir kaɗan tace,"dan Allah Amir...wallah idan Kaka tazo ba zata bari a zubar ba, ni kuma naji sauƙi".
Tana yin shiru ya ɗauki ledar ya saka a aljihunsa yana faɗin,"yanda kika ce ranki ya daɗe".
Wayarsa tayi ƙara ya ɗauka, ƙaramar waya ce ba wata babba ba, yayi shiru yana sauraron maganar dake cikin wayar kamin yace,"tom shikenan Bandirawo ina kan hanya insha'Allah".
ya ƙara yin shiru for seconds kan yace,"ahh mai jiki da sauƙi, yanzu haka ma ina wurinta".
"tom zata ji insha'Allah, mun gode".
Ya katse wayar ba tare daya dubi Fillo ba yace,"Bandirawo ne, yana yi miki sannu da jiki". Tace,"ina amsawa".
Sannan ya miƙe yana roƙonta akan ta daure taci abinci, gyaɗa kawai tayi, ta yunƙura itama zata miƙe dan yi masa rakiya yace a'a ta koma ta zauna.
Zuciyarta na harbawa da soyayyarsa ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, cikin sanyayyan muryarta da ciwo yaywa lahani tace,"na gode".
Ƙwayar idonsa akanta da tsananin shauƙinta yace,"da me?". Still idonta kan yatsunta tace,"ni dai kawai na gode, Allah ya bada lada".
Ya sauke numfashi yace,"amin". Sannan ya nufi ƙofa, ita kuma tana ce masa ya gaida su Inna.
Bayan fitarsa Maijidda tace,"ke kam Fillo kin mo re da miji aure, Amir mutumin kirki ne, ki ga fa tunda kika kwanta yake sunturi akanki". Fillo dai bata ce mata komai ba, don ita tunaninta ma na wani waje can na daban.
Dogon tsakin da Fillo taja na takaici shi yasa Maijidda saurin kallonta da mamaki. "shi kuma tsakin fa?".
Fillo tayi shiru tana jin wani ɗaci acikin ranta, tunda tazo gidan nan bata taɓa shiga ɓangaren masu gida ba, kai hasali ba matar gidan ma bata taɓa ganinta ba balle ƴaƴanta, idan aka cire wadda tazo ranar nan ta kawo musu kwancen kaya, abunda kawai ta san da bakin kowa na faɗa shine Uwar ɗakinmu Hajiya Madina.
Amma haka kawai ta ke jin bata son mutanen gidan, dan ta ra'ayinta da tuni sun bar aiki sun koma wani wajen to dan Kaka taƙi ne.
To dan me yasa ma ba zata ji zaman gidan nan ya fice akanta ba yanzu?, sanadin fa taimakon ɗansu ta shiga halin da ta shiga. sannan again tana kwance cikin wannan halin sunzo sun ɗauke mata Kaka sun mayar da ita aiki ɓangarensu, aikin da idan ta fita tun safe sai dare zata shigo, ta lura sam bata samun hutu da can ɗin.
Akan me ma zuciyarta zata so matar gidan?, tuwo ne a idonta da ta kasa ganin girman tsufan Kaka da har suke loda mata uban aikin da zai gajiyar da ita. Ko da yake in akace baka da shi dama shikenan taka ƙararriya ce, talaka dai na ganin rayuwa.
"salamu alaikum". Maijidda ce ta amsa sallamar da aka yi daga ƙofar ɗakin, Fillo kuwa aciki ta amsa, sai bin ƙofar ɗakin da tayi da ido.
Wata tsohuwar mata ta leƙo kai cikin ɗakin tana kiran sunan Kaka. Maijidda tace,"ki shigo bata nan". Ta shigo ɗakin tana faɗin,"bata nan?, ina lafiya dai ko?, kwana biyu banga gimlawarta ba acikin ɓangaren nan".
"lafiya lau, ta koma cikin gida da aiki ne shiyasa". Maijidda ta bata amsa.
Ta ƙara cewa,"Allah sarki shi yasa ashe, ni fa naga kwana biyu bana ganinta a wurin aiki. Kuma da yake ta saba leƙowa a gaisa ko da ba ranar aikinsu ba shi yasa ma nace bari na leƙo naga ko ba lafiya ba".
Maijidda ta ƙara cewa,"lafiya lau, idan ta tafi ne bata shigowa sai dare".
Matar tace,"to kwa sanar mata na nazo idan ta dawo, kuma kuce ina yi mata barka an samu ci gaba".
"to insha'Allahu za'a faɗa mata". Yanzu ma dai Maijidda ce ta amsa, dan Fillo ma babu alamar zata yi magana.
Matar har zata fita sai ta dawo tana cewa,"kinga na manta fa ashe Fillo babu lafiya, kusan ni ɗaya ce ban shigo dubata da jiki ba". Ta kalla Fillo dake kumbure ta haɗe gira duka biyu tace,"ya sauƙin jikin naki Fillo?".
Ba don taso amsawa ba tace,"naji sauƙi". tace,"to Allah ya ƙara lafiya...sai anjimaku".
Da haka ta fice tana fita Fillo taja uban tsaki tace,"har ga Allah haushin komawar Kaka aiki cikin gida nake, gaba ɗaya an riƙeta da aiki ba'a barinta ta huta. su ko tausayinta ma basa ji, ko basu da tsohuwa ne oho?, tun fa da ta fara aikin nan idan ta fita da safe bana ƙara ganinta sai wata safen, dan kamin ta shigo nayi bacci, jiya har kusan goma da rabi bata shigo ba...jiya da ta dawo ina ganinta tana miƙa tsabar gajiya, kawai don bana cikin hayyacina ne amma da sai naje gidan nace su sallamemu".
Ta gama ƙorafinta cikin masifa, Maijidda dai bata ce ma ta komai ba, sai ma ƙwaryar furar da ta janyo tana sha.
ruwan hawaye ya kawo idon Fillo, muryar in breaking tace,"ni ban san ba ko basu ga yanda Kaka ta tsufa ba ne...amma me suka ɗauki kansu?".
Maijidda tace,"masu kuɗi mana. kuma dai ba za ki ce suna sahun masu kuɗi marasa kirki ba. za ki so kanki ta wannan ɓangaren in kika faɗi haka...ke dai ki yiwa Kaka adu'a kawai, banda ke sanin kanki ne ba zata juri wannan bautar ba tunda ta tsufa da yawa".
Bata ce komai ba, Maijidda ta ƙara cewa,"ga furar kisha da sanyi".
"aina kika samu ƙanƙara?".
"Yami ta aike ni ɗazu na ganta shine na sayo, nasan za ki so".
Fillo tayi shiru, idonta na kallon yatsun ƙafarta.
"ni dai kici abinci kar naci amanar Amir".
"ba zan iya ci ba Maijidda sai Kaka ta dawo".
"haka za ki yini da yunwa kenan?".
"zanci amma idan ta dawo".
"Amma dai kin san sai dare ko?".
Fillo tai shiru, itama Maijiddan bata ƙara ce ma ta komai ba. For a while Fillo Let out a long sigh of despair, duka tafukan hannunta saman fuskarta tana ƙoƙarin danne kukan dake neman cin ƙarfinta.
"Maijidda tsawon yaushe idanuwana zasu ɗauka kamin Dada ta dawo gare su?".
tausayin Fillo ya kama Maijidda matuƙa, bata iya cewa komai ba sai hannu da ta saka itama tana goge nata hawayen.
****
Sakkowa yake daga stairs a hankali hannunsa riƙe da mug, three quarter ke jikinsa brown colour da white t-shir me coller dark blue. har yanzu ba'a cire masa bandage ɗin dake goshinsa ba.
yana sakkowa parlon direct kitchen ya wuce, ya zuba sugar acikin tea ɗin, sannan ya fito ya ƙarasa kujera ya zauna.
Kaka wadda ya barota a kitchen ta fito da sauri, ta ƙaraso inda yake, da rissinawa ta ke faɗin.
"sannu ya yallaɓai". Turaki ya amsa mata yana ɗan runtse ido saboda zafin ciwon dake kafaɗarsa.
Kaka ta saka masa pillo daga bayansa sannan ya jingina da kujerar.
"sai me kake da buƙata Yallaɓai?".
Ƙafafun Kaka a ƙasa lokacin da ta ke tambayar tasa. ya ɗan rufe ido yana jin tausayin tsohuwar a ransa, tukunna ya buɗe yana kallonta ta wutsiyar ido yace,"babu komai, kije ki huta haka don Allah".
tace,"to Allah ubangiji ya ƙara maka lafiya, ina bayan kitchen idan da buƙatar wani abu".
Tana faɗin hakan ta miƙe zata bar wajen, har tayi tattaki zata nufa kitchen ta fita ta baya sai ya dakatar da ita, tsawon kwanaki shidan da tayi a wurinsa sai jiya ya san sunanta a bakin Maama.
"Kaka". ta juyo idanuwanta a ƙasa, tun ranar daya dawo ta dawo aiki ɓangaren, ita ta ke ta lura da shi da ciwonsa, yana ganin ƙoƙarin tsohuwar sosai, yana jin tausayinta matuƙa a cikin ransa, sai dai bai taɓa jin tausayinta da yawa haka ba sai a yau da yake kallon fuskarta me bayyane da damuwar dake cikin ranta.
kullum zuciyarsa na gaya masa tsohuwar kamar wannan bata samun hutun rayuwa, to ina ƴaƴanta?, waye a ƙarƙashin kulawarta da ta kasa samarwa kanta hutu a wannan shekarun nata?.
Sai dai tambayar dake zuciyarsa yanzu damuwar dake fuskarta ta mene?, ya ƙara ɗaga ido ya kalleta, tana tsaye har yanzu bata motsa ba, ji yake kamar ya tambayeta menene matsalarta amma sai yaga wannan ba huruminsa ba ne.
Saboda haka sai yace,"Kaka tunda yau na sami sauƙi kije kawai ki huta kema".
Har yanzu kan Kaka a ƙasa tace,"to yallaɓai". ta faɗa tana sake juyawa ta nufi hanyar kitchen.
Kamar bata fahimci me yake son ce mata ba.
"Kaka ina nufin ki tafi ki huta sosai".
tace,"Yallaɓai ai kar na tafi kuma wata buƙatar ta tashi".
Kamin yayi magana sai ga Zaytuna ta shigo, ta wuce inda yake zaune tana kara masa waya a kunnensa, ya maida hankali ga wayar ita kuma tace da Kaka.
"ki tafi ɗin kawai babu matsala, zan zauna da shi".
da yake taji last conversation ɗinsu kamin shigowanta parlon gaba ɗaya.
Kaka tace,"to Zaytuna na gode, Allah ya ƙara masa lafiya. Kya sanar da Hajiyar".
"tom shikenan babu matsala". Da hakan Kaka ta bar wajen.
daga ɓangaren Bello Ƙaraye dake magana ta cikin wayar Turaki yace,"all this while ina ka bar wayanka, i have been calling tana ta ringing ba kai picking ba".
Zaytuna ta sauke cup ɗin tea daga bakinsa, bayan ya haɗiye tea ɗin daya kurɓa ya amsawa Bello da cewan,"Maama ce ta ɗauke wayan wai na samu na huta da kiran da ake mani, i though ma tayi switch off nata ashe kunne ta barta".
Bello yace,"anyway, how are you feeling now?". Cikin sanyin jiki yace,"Alhamdulillah".
Bello yace,"hope kana iya cin abinci yanzu ko?".
Yace,"yanzu haka ma am taking tea".
Bello ya ƙara cewa,"Good, batun drugs fa?". Yay tambaya cike da concern.
Turaki yay ɗan jim yana tuna yanda Maama tayi ta fama da shi akan shan magani ɗazu da safe.
jin shirunsa Bello yace,"i know, ba za'a sami matsala da kai ba a ko'ina sai a ɓangaren shan magani...you should have grow up by now gaskiya".
Turaki yace,"ka kira ka gaya min magana ne na kashe wayana?".
"yo tsakani da Allah ace ka girma amma kana gudun magani da Allura".
"ina ce ciwon jikina yake ko?".
"ai kuma da yake mun damu da kai...by the way zan shigo cikin satin nan".
"Allah ya kawo ka".
Bello yace,"ameen, Allah ya ƙara lafiya...and please ka dinga kulawa kaji"
Turaki ya amsa mishi,"toh".
Sallama Bello yyi masa ya katse wayar, ba'a ɗau lokaci ba Maama ta shigo parlon.
*Kuyi haƙuri da rashin update akan lokaci da kuma typing kaɗan. Rashin nepa ne ke damun ƙauyenmu, amma ku taimako da kuɗin solar kunji ƴan albarka☹️*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*8*
Idanuwan Turaki da Zaytuna suka ware akan Maama da ta shigo fuska babu yabo babu fallasa, suka bita da kallo har ta zauna kan kujera ta harɗe ƙafafu tana girgiza su. Dukansu suka sauke numfashi mai nauyi dan sun san tunda suka kalla fuskarta a haka to lallai akwai damuwa.
"ɗauki wayar nan ki kira min Bello". Muryan Hajiya Madina ta fito da wani irin amon sauti.
Zaytuna ta ɗauki wayar Turaki dake kan cinyarsa, tabi kiran Bello da suka gama waya da Turaki babu jimawa. ta miƙe ta isa ga kujerar da ta ke ta bata wayar, a kiran farko bai picking ba sai ana biyu, shima sai daya kusa katsewa tukunna.
Daga ɓangaren Bello yace,"Turaki ya dai?".
Hajiya Madina ta numfasa tace,"Bello ba shi ba ne".
Jin muryarta yay saurin gyara zama daga inda yake, ya gyara yanayin muryarsa, cike da ladabi ya gaisheta, ta amsa masa tare da tambayarsa ya aiki, yace mata aiki alhamdulillah.
Shiru na ƴan sakanni ya biyo baya, Turaki dai kallonta kawai yake, kiran Bello da tayi na menene?, me zata ce da shi?, to me ya faru ma tukunna?, dan yanayin fuskarta kaɗai yana shaida cewar there most be something
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 73