kanta yace,"waya farlanta miki hakan?". bata ce komai ba tayi shiru sai wasa da yatsun hannunta take ta duƙar da kai.
shi kam kallonta kawai yake, ta wani natsu kamar wadda taga mutuwa, kamar ba ita ta gama surutu ɗazu ba harda dukan wata.
ɗakin yay shiru Maijidda na daga gefe har yanzu a tsugune, ya maida kallonsa kan abincin da Maijiddan ta aje yace,"ki kawo mata abincin".
Maijidda ta ɗauko plate ɗin dake ɗauke da tuwon semovita da miyar agusi da naman ganda akai, ta miƙawa Fillo wacca tuni idonta ya cika da ruwa sai aikin ɓata fuska take.
da mamakin Maijidda babu tirjiya balle musu Fillo tasa hannu ta karɓa, kallon abincin kawai take ba don tana jin zata iya ci ba. bakinta babu taste ɗin komai hakan ne yasa ba zata iya cin komai ba, kuma bata ma jin yuwar.
wucewar daƙiƙa biyu Turaki yace mata,"wa kike jira yazo ya ci miki?". ba tsoronsa take ji ba, ita kawai yana yi mata kwarjini ne, ko bata kalle shi ba indai yana waje sai taji girman kwarjininsa ya cika wurin.
ba don tana so ba ta gutsiri tuwon da spoon ta kai baki, ta tauna ta haɗiye da ƙyar kamar me tauna magani, tana yin spoon huɗu sai ga amai ya yunƙuro, Turaki yay saurin ɗauke idonsa daga kanta ya kauda kai gefe yana jin zuciyarsa na tashi, Maijidda ta kamata suka wuce toilet, duka ta amayar da ɗan guntun abin da taci, ta wanke baki suka fito har sannan yana tsaye sai dai yanayin fuskarsa ya sauya.
sai sauke numfashi takeyi tana maida ƙwallar idonta, ta ƙasan ido take ta kallonsa, tana ce sannu yazo yi mata?, shi bai yi ba kuma bai tafi ba ya tsaya kamar wani sandar ba'are, Allah ya sani ji take kamar akanta yake a tsaye, da zata iya da ta buɗe baki tace masa ya tafi kawai.
a bakin gadon ta zauna. kuma tana zama taji ya ƙara cewa,"ki ɗauka ki ƙara ci, sai ki ƙara zuwa ki wani aman, ki dawo ki ƙara ci kije ki amayar haka har ki cinye shi".
wannan karon ba ita ta kalle shi ba Maijidda ce, tana masa kallo ɗaya ta ɗauke idonta ta koma can kan ɗaya gadon dake cikin ɗakin, room ɗin 2patient ake admiting acikinsa amma ko da Baffa yazo sai ya biya kuɗin ɗaya gadon dalilin da yasa take zaune ita ɗaya kenan.
jin an turo ƙofa Turaki ya kai idonsa wajen, Dr Yusuf ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. duk da cewar tun ɗazu da Turaki ya baro masallaci yana office ɗinsa hakan bai hana su daɗa yin musabaha ba. as usual fuskar nan tasa da murmushin da baya yankewa.
"ya me jikin ranka ya daɗe?". Dr Yusuf ya tambayi Turaki.
"gata nan maganin gardama ya rage ku bata before ku sallameta".
Dr Yusuf yay ƴar dariya yace da Fillo,"ya kike jin jikin naki?". tace,"naji sauƙi". yace,"to Allah ya ƙara lafiya. yanzu cin abinci yay miki saura shine zaki samu ƙwarin jikinki". tace,"to".
ya juya ya karɓi file daga hannun nurse ɗin da ta shigo ɗakin yanzu, yay rubuce-rubuce sannan ya rufe ya bata.
ya fuskanci Turaki yace,"insha'Allahu by wenesday zamu sallameta. komai normal babu wata matsala".
Turaki ya kalleta ya kalli tuwon yaga ko rabin cinsa bata yi ba, yace da Dr Yusuf.
"Allah ya kaimu. amma babu yacca za'ai a farke cikinta a dinƙa zuba mata abinci ta nan?, tunda bakinta nayi mata wahalar cin abincin".
da murmushi a leɓen Dr Yusuf yace,"babu matsala sai ayi hakan. bari yanzu sai mu fara preparation ɗin shiga da ita ɗakin tiyata...sai dai kuma fa idan za'ai irin wannan aikin dole sai a ɗinke baki gaba ɗaya ya zamana mutum ya dawo baya magana, wurin da za'a yanka a cikin nan nasa shine zai koma yagar bakinsa, abinci da ruwa ne kawai za'a dinga zubawa a ciki".
Turaki ya sosa girarsa sannan yaja kujerar dake kusa da shi ya zauna. "ayi abinda ya dace kawai Dr". sai ya kalla agogon hannunsa yace,"nan da minti nawa za'a shiga tiyatar?". Dr Yusuf yace,"in the next 5minutes, office kawai zan shiga na fito, ita dai yanzu a shiryata". Turaki yace,"alright a fito lafiya".
Dr Yusuf ya fita Nurse na biye da shi, wacca take ta dariya ƙasa-ƙasa da zancen da akai, ta lura sosai maganar ta tsorata Fillo. Maijidda ma na gefe a tsaye, itama dariya take ƙasa-ƙasa farkon da akayi zancen farka ciki, saboda yanda taga Fillo ta tsure tana raba idanuwa, amma daga baya da taga kamar maganar da gaske ne sai tai jugum tana dai ta kallon Turaki ta gefen ido, tana kuma jin tausayin Fillo na tsarga mata.
_"amma babu yacca za'ai a farke cikinta a dinƙa zuba mata abinci ta nan?"_ maganar ta Turaki ta daɗa maimaituwa acikin kanta. farko daya faɗa bata razana ba, amma da ta shiga bin fuskokinsu tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya sai ta tsorata ainun, dan ko ɗigo babu na alamar wasa a yacca fuskokinsu ke nunawa, hakan ya tabbatar mata lallai da gaske suke, farke mata ciki za'ai sannan kuma a ɗinke bakinta ta daina magana har a abada. idan da abinda yafi tashin hankali wannan maganar tasa ta shiga ciki, hangota take babu bakin magana kuma cikinta a yage, ta haɗe murfin idanunta da suke neman zazzagowa ƙasa, dan tunda aka fara maganar suke a waje.
jikinta rawa yake sosai, ƙatuwar malmalar tuwon take ta kallo, lissafi take yi, lissafin yanda za'ai ta cinye shi acikin miniti biyar kafin a shiga da ita tiyatar da suka ce. ta ɗago ido ta kalli Maijidda dake kallonta, yanda take a tsorace haka Maijiddan ma. cikinsu biyun kowa ya kasa cewa komai, tsoron Fillo ɗaya ne! tace zata basa haƙuri ya sakar mata wannan uwar tsawar da bata so, dan taga kamar hakan yake jira, dalilin daya sa bakinta mutuwa kenan.
Maijidda tayi sum sum ta fice zuwa kiran su Kaka, tana fita Fillo ta sakko a kan gadon ta wuce toilet, Turaki ya bita da kallo har ta dawo. ta koma gefen gadon ta zauna, ta saka hannunta da ta wanke ta fara cin tuwon tana kai ƙatuwar lomar data fi ƙarfin bakinta.
kana gani kasan tura tuwon kawai takeyi, bata ko tsayawa ta gama cinye na bakin zata ƙara saka wani, tunda take bata taɓa cin malmalar tuwo me girman wannan ba, kai abincin kansa bata cin da yawan hakan, shi yasa Yami kullum ke mata tsiyar taƙi ci tana ta bushewa.
yana zaune yana shafa wayarsa amma indonsa sam ba akan wayar yake ba akanta yake, tun lomar farko da ta kai baki. ba ƙaramin bashi dariya tai ba ya danna yana cije leɓe murmushinsa na fita saboda dariyar ba zata dannu duka ba, yanda take ta tura abinci cikin sauri, har yunƙurin amai tai amma tai maza ta maida shi, ga jikinta ma gaba ɗaya rawa yake kamar mazari.
cikin mintunan da ba zasu haura uku ba plate ɗin ya zama babu komai, ta cinye tas sai nishi take yi, ta sauko taje ta wanke hannu ta dawo. ta kalle shi taga ma hankalinsa bai kanta, wayarsa kawai yake dannawa, kamar tai magana ta roƙe shi suyi haƙuri sai dai tayi shiru, ta kama yatsun hannunta sai jansu take kace tana lazimi. idanuwan nan da suke loko sai ƙifƙiftasu take. Turaki duk yana kallonta, har maganar da bakinta ke sonyi yana kallon yanda ɗan ƙaramin leɓen ke motsawa. shi gani yake ma kamar ƙunƙuni take tana zaginsa.
suna haka aka murɗa ƙofa, tana jin hakan gabanta yay mugun faɗuwa ta haye kan gadon gaba ɗaya a zabure, ta takure ƙafafuwanta tana shirin sakin kuka. muryarta na karkawa ta cewa Turaki,"tun ɗazu na cinye abincin dan Allah kuyi haƙuri". tana rufe bakinta sai taga ashe su Kaka ne ba Dr Yusuf ba kamar yanda ta tsammata. hakan yasa ta saki ajiyar zuciya tana bin Kaka da ido, taga fuskar Kakan a haɗe alamar ɓacin rai.
"sannu fa me babban suna". Turaki ya tashi ya amsawa Kaka. "yauwa Kaka sannunku da dawowa. ya me jiki?". tace "da sauƙi...kayi zamanka mana". yace,"a'a Kaka dama ina niyyar tashi ai". tace,"ni dai daka zauna wallahi, bana jin daɗi idan kana ƙin zaman nan saboda mu". ya kalli tsohuwar da jin tausayinta a ransa, sosai suke kama da Fillo kawai dan ita ta tsufa ne. baya son musu da babba saboda haka dole ya koma ya zauna.
bayan ya zauna Kaka tace,"muna daɗa godiya fa me babban suna, babu abinda zamu ce sai Allah ya saka maka da gidan aljannah. kai da iyayenka kuna kulawa damu Allah ya biyaku da alkhairansa". yace,"amin Kaka na gode". ta sake cewa,"Maijidda ce taje take faɗa mana abinda ke faruwa na za'a shiga da ita tiyata, shine muka taho. nace ai hakan ma wani gata ne akai mata". Yami tace,"Allah yasa dai ayi a sa'a".
ya sosa girarsa leɓensa na fitar da murmushi yace,"ehh likitan ne dama ya bada shawarar hakan". karaf Fillo tayi saurin cewa,"a'a ba shi bane kaine ka fara faɗa masa. ni dan girman Allah Kaka kuyi haƙuri indai abinci ne zanke ci".
Kaka tai mata banza, Yami tace,"to ai magana ta ƙare tunda har likitan ma yayi shirinsa. kiyi adu'a kawai Allah yasa ayi miki a sa'a, hakan ai gata akayi miki Fillo kinga yanzu cikinki ga dinƙa samun abincin kirki. magana kuwa kya dinƙa nuna abunda kike nufi da hannu".
Yami na yin shiru Fillo ta fashe da kuka tana kifa kanta a gwiwarta, ta sani babu wanda zaiji tausayinta, kuma babu me jin kukanta tunda bata da uwa bata da uba a raye.
Turaki ya ɗauke idonsa akanta, zai fita Kaka tace,"a'a me babban suna tunda dai sa hannunka ne a yin aikin nan to ka ɗan jira likitan yazo a ɗauketa a gabanka. mu ba jin maganarmu take ba,". tana faɗin haka suka fice su duka suka bar Maijidda a tsaye, itama sai ta fara hawayen.
bayan fitar su Kaka ya jawo kujera sosai gaban gadon sannan ya zauna, ya aje wayarsa akan gadon, sannan ya sarƙe yatsunsa wuri ɗaya.
yace da ita,"haƙura za'ai da farka cikin ko kukan za ki ci gaba?".
kalmar farka cikin ita ke ɗaga hankalinta, tai saurin ɗagowa fuskarta tayi sharkaf. "dan girman Allah karka sa a farke min ciki, zan dinga cin abinci kullum, ai kana kallo ma cinye na ɗazu. dan son da kake yiwa Maama da Adda Zaytuna kace ba za'ai min ba".
mamaki yasa kawai ya tsareta da ido, taya akai tasan yana ƙaunar mutanen nan guda biyu?, taya tasan zai iya yin komai akansu?, waya faɗa mata ana roƙonsa da su ya aikata abinda bai niyya ba?.
ya sauke numfashi sannan yace,"an fasa". a hankali tace,"na gode, Allah ya kareka daga sharrin maƙiyanka". ta faɗa tana goge hawaye da ɗankwalinta daya zame. suka haɗa ido tayi saurin ɗauketa nata, ya kalli gashin kanta yace,"ɗaura ɗankwalin ki bani amsar tambayata". ta ɗaura ya ƙara cewa,"to ki cire tsoron ki nutsu". ta haɗiye wani irin yawu tana saita nutsuwarta. taji yace,"ɗago idonki ki kalle ni". tayi yunƙurin yin hakan amma sai ta kasa, yaci gaba da kallon siraran hannunta da suke ta karkarwa, sai kawai ya miƙa hannunsa ya haɗe hannayenta biyu ya riƙesu cikin nasa guda ɗaya, sai dai da mamakinsa duk da hakan basu bar karkarwar da suke ba kamar ma ƙaruwa abin yayi, cikin ransa ya ayyana duk yanda akayi wannan rawar da jikin nata yake yi bana lafiya ba ne.
jin yanda ya riƙe hannuwan nata yasa ta kulle ido wani abu na wucewa ta maƙogoronta. kuma kafin ta buɗe idon taji yace,"me ya kaiki wannan wurin a wancan ranar?".
ta buɗe ido ta sauke a saman sumarsa tana jin numfashinta na ƙoƙarin katsewa.
****
Yusuf na zaune a office yana operating computer wayarsa tai ringing, ya kai hannu ya ɗauki wayar, yana duba sunan me kiran yaga Inna Wuro, ya katse tukunna yabi bayan kiran.
Inna Wuro na ɗaga kiran ta maka salati,"innalillahii wa'inna ilaihi raji'una. Yusuf kana ina?, kaiwa Allah kazo da sauri babu lafiya".
tun salatin farko data ja ya miƙe daga kan kujerarsa, tana cewa babu lafiya bai jira komai ba ya kai bakin ƙofa, yabar office ɗin cikin sauri hankalinsa a tashe.
daga parlon Inna Wuro ta soke wayarta a gefen zani bayan kiran wayarsu da Yusuf ya katse. ta kalli Nuratu wacce ta tattare carpet ta kwanta a ƙasan tiles, sai yamutsa fuska take yi hannnunta riƙe da tulun ƙasa ƙarami da aka zuba yashi acikinsa, acikinsa take tofa yawu.
"ina dalili, gwara ya baro duk abunda yake yi yazo aiwa tufkar hanci, ba zan iya rainon wannan cikin nasa me shegiyar ƙazanta ba. ba ni nai ciki ba dan haka ba zanyi wahalarsa ba, azo duk abi a dinga tofe min ɗaki da yawu yana ƙarni...yanzu fa fisabillahi ji wani abu, anyi shara kin ɗage min carpet salon dai ayi baƙo a tafi anayi da ni a duniya bana gyara wajena, alhalin ba haka nake ba, kai da gara wani can da baku haɗa komai da shi ba yazo ya ɓata maka...kuma ni dai gaskiya nake faɗa miki kwanciyar ƙasar nan illa zata miki, inda rabon kin haifo ɗan da sanyi yayi ƙatutu a jikinsa ne to".
ta ɗau mayafinta dake kan kujera ta fita daga parlon, ɗan ƙaramin durstbin na shara ta ɗauka a ƙofar parlon sannan ta wuce ta nufi can inda incilerator yake zata zubar da sharar sai mita take yi.
"yanzu ni ba abin na faɗawa Amadu irin cin kashin da ƴaƴansa suke min ba yaga kamar ina tukura musu alhalin nazo ina cin arziƙinsa, Zainabu ta ƙullace ni tace zan haɗa ƴaƴa da ubansu. gwara nayi shiru na haƙura watarana sai labari, amma tsakani da Allah ni ba daɗin hakan nake ji ba, kawai dai dan babu yanda zanyi ne, amma cuta kam ana cutata".
ganinta mai gadi ya taso da sauri. "Inna ina za ki haka da kanki?". ta tsaya tana gyara mayafi tace,"ni ko wa nake da shi da zai min bacin na ƙarfafa jiki naiwa kaina". ta ɗaga ƙaramin durstbin ɗin sharar tace masa,"kaga dai yanda kwandon nan ya cika ko?".
ya ɗaga kai yace,"na gani". tace,"to billahi ina faɗa maka ko dattina ɗaya babu aciki, bar ganin daga ɓangarena ya fito".
Mai gadin yace,"to fa garin ya haka kuma Inna?".
tace,"karka tsammaci aljanu ne, wallahi ko ɗaya basu da hakki, mutanene marasa tausayin tsoho. Ƴaƴan Amadu ne wallahi, haka suke zuwa su cika min ɗaki alhalin ubansu yayi musu nasu, to ba zasu zauna a nasu ba dole dai sai anzo wajena an ɗauki magana. ni kuma bana biye musu kasanni da haƙuri, ban iya ɗaukar magana ba saboda bana son tashin hankali. kuma dai naga gidan na ubansu ne arziƙinsu nake ci shi yasa na iya zamana da su banda haka kullum sai anji kanmu...yanzu fa ka duba ka gani wannan sharar daga safiya zuwa yammacin nan aka tarata, da ci banza ci wofinsu aka mayar min da ɗaki kamar bola. yo ni kuwa me zanyi wanda ya wuci Allah ya isa".
Mai gadi yace,"a'a dai Inna haƙuri za'a ci gaba da yi, banda dai Allah ya isan kinga ai jikoki ne".
tace,"yo abunda ba ni na haifa ba balle bakina ya bisu su gantale, barni nayi kayata ni dai kam ai Allah ya isar min kawai. kai ai baka san wani abu ba ma, Allah ya isa ai sun saba da ita, dan jiya yaron nan Aliyu ce min yay wai babu wajen shigar tawa, daga nan na sallama nace Allah ya isa kam yanzu na fara har sai tawa ta sami shiga... yanzu ka duba ka gani banda dai rashin tausayi ina uwar me ƙaton gidan nan da kai shara, ko da yake rayuwa ce kowa yay na gari kansa...haka zanta haƙuri har dai Allah ya kawon mafita, ko kai haka iyalinka ke Uwakka?".
Mai gadin yace,"a'a Inna". tace,"kaga inda arziƙi yake, banda gidan Amadu inda Ƴaƴan ba kyau matan ba kyau".
Mai gadin ya karɓi basket ɗin yace,"kawo na zubar miki, ai ba kyaje wurin can da kanki ba yamma tayi".
ta sakar masa tana faɗin,"kai da yake ai kasan darajar babba. na gode Allah yayi maka albarka ya raya maka iyali, yasa ka gama da duniya lafiya, Amadu na dawowa zansa shi yay maka kyauta wallahi. ni ko zamu koma kanon ma ai ba zan bari a tafi babu kai ba, wa zai so ya rabu da ɗan arziƙi irinka".
nan ya barta tana ci gaba da surfa mita, ta zubawa gate ido tana ta Allah Allah motar Yusuf ta shigo. Mai gadin ya dawo ya bata basket ɗin ta wuce tana ta ƙara gode masa.
tazo wucewa ta ɓangaren Ammi ta saki basket ɗin ya faɗi ƙasa, babu shiri ta saki salati tana ɗora hannu aka. "la'ila ha'illallahu Muhammadu Rasulillahi". Ammi ta dakata da shiga parlonta ta juyo tana kallonta. kamar ba zaita magana ba, yanda taga Inna Wuro ta ɗora hannu aka yasa dole ta magantu har tana dawowa da baya don ganin lafiya.
"me ya faru?". cewar Ammin tana bin wurin da kallo. Inna Wuro ta sunkuya ta ɗauki durstbin ɗin tace,"a'a babu ruwanki, yaushe rabon da magana ta haɗani dake, tunda azumi ya fita kika ƙulla gaba da ni, sai yanzu ne da kika ga ina neman cutuwa sannan za ki kulani, to gaskiya matsa daga kusa da ni bana son munafurci...duk wanda yay na gari dai kansa, ni ɗin dai wallahi ba abar banza bace nafi ƙarfin wulaƙancin bawa tunda ni na haifin me ƙaton gidan nan".
jin haka Ammi tai tsaki a ƙasan ranta tai wucewarta, dama tasan ba wani abin arziƙi ba ne, bai wuce abinta da ta saba. Inna Wuro ta bita da ido ta taɓe baki, bata ce komai ba ta wuce side ɗinta, cikin ranta sai masifa take yi Yusuf bai dawo ba har yanzu.
tana shiga ta tarar da Kursum ta fito daga ɗakinta. tai saurin ajiye durstbin ta cire mayafinta ta aje. tabi hannun Kursum da ido har tazo ta zauna, idonta akan bowl da Kursum ta ciko da alkaki tace.
"babu masifar da ta wuce haihuwar ɓeraye wallahi. to ni Safiyya mene marabar ƴaƴan Amadu da ɓeraye?, ka ajiye aje a ɗauke babu neman izini. to ba zan iya ba, Allah ya dawo da shi lafiya, ko ya min gidana daban ko kuma ya katangeni a gefe ɗaya, ba zance haɗa mana ƙofar shigowa ɗaya da ku...ban son fitina ban iyata ba, Allah kuma ya rabani da ita, ku kuma naga tashin hankali kuka fi so".
tana cikin wannan sababin Nuratu ta miƙe tai hanyar ɗakin Inna Wuro da sauri tana rufe bakinta da amai ke shirin zubowa.
Inna Wuro ta koma da baya tayi wani zaman dirshen akan kujera, ta kama kanta ta riƙe tana girgiza shi. "wowowo, tashin hankali kala-kala a cikin gidan nan. tayi ta zabga amai babu ƙaƙƙautawa duk ta lalata min bandaƙi. to Yusuf ɗin yazo yau dai zamanki ya ƙare a ɓangarena, ya kwasheki ya mayar da ke gidanki ko dai yasan yacca zai yi da ke. banda ma dai kar yay min kallon mara mutunci ai kamin ya dawo zan kai miki kayanki waje".
sai kuma tai ta gumi,"wannan masifa duk ni na jawowa kaina da nace ki dawo wajena da zama, shegen shishshigi irin nawa dai...in nasan hakan kike laulayi wallahi da ban soma ba. gwara can Uwarsa ta riƙe ki, tunda ita ƙanwar Uwar taki tasa ƙafa ta bar gidan, ace aikin Umara har yanzu ba'a gama ba kusan sati uku...wa ma yasan inda ta kaɗa".
*Vote, Comment, and Share.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_Ina yi mana barka da sallah tare da fatan alkhairi a rayuwarmu🥰, mugun ji mugun gani Allah ka tsaremu da shi Amin Y Allah🤲...wayidi a miƙo, a miƙo naman sallah kar nai zuciya na hau bari a shop ɗin *BEST SHAWARMA & MORE*😫, idan kuwa na dira a shop ɗinn abin ba zai kyau ba dan ban fitowa sai asusun Yaya Nusaiba ya gane kurensa😂._
*19*
Yusuf na zuwa gida ko horn bai yi ba balle ya tsaya jiran wani abu shi buɗe gate, ya fito daga motar cikin sassarfa. yasan yana da patient, matarsa dake ɗauke da juna biyu mai wuyar laulayi, yau lafiya gobe babu lafiya, shi yasa duk hankalinsa ya tashi tunda yaji irin salatin da Inna Wuro ta zabga, duk wanda yaji wannan salatin ya san ba lafiya ba kamar yanda ta faɗa.
jinsa yake kamar ya ɗauki kansa ya dire a parlon Inna Wuro, ƙaramar ƙofar gate ɗin a buɗe take dan haka yana zuwa turawa yayi ya shiga. mai gadi dake daga cikin ɗakinsa a zaune yay masa sannu da zuwa, a sama ya amsa masa ya wuce kamar zai tashi sama gabansa sai faɗuwa yake.
hango Ammi yay zata shiga motarta, ya bita da kallo for some seconds, atleast dai zuciyarsa ta sami natsuwa ko ya ya ne, dan shi abunda yake hasashen ya faru daban ne, to kuma tunda yaga Ammi taci kwalliya kuma bai ga wani alamun tashin hankali tare da ita ba sai ya fara nutsuwa.
but still dai gabansa bai daina faɗuwa ba, ba zai yi la'akari da yanayin Ammi ba akan ba wata matsala bace babba, komai ma zai iya faruwa ba tare data sa ni ba, idan ma ta sani zata iya yin banza taci gaba da sha'aninta, ranar nan ma haka tayi da akazo aka ce mata Nuratu ta faɗi, baki kawai ta taɓe ciki-ciki tace Allah bada lafiya, Ko da aka kwantar da Nuratun bata je asibitin ta dubata ba, zallar ƙi take nunawa aurensa da Nuratu babu ɓoye-ɓoye ga kowa.
yana wannan saurin tafiyar ne dan ƙarasawa side ɗin Inna Wuro sai yaji wayarsa na ringing, yasa hannu a aljihu ya ɗauko. yana ganin sunan Ammi ƙirjinsa yay wani irin bugawa, da ƙyar ya iya ɗaga kiran a lokacin da yake dab da katsewa.
kasa cewa komai yayi daya ɗaga wayar but still bai daina tafiyar ba, sai dai ya rage saurin tafiyar tasa, jin bakinsa yake kamar ba zai iya cewa komai ba.
Ammi tace masa,"shawaran da zuciyar taka ta yanke maka kenan Yusuf?". mamaki ya kama Yusuf, taya akai ta gansa?, a hankali ya juyar da kansa gefe yana kallon inda take sai yaga bata wajen, ba abin yace mata ba shi bane tunda dai ta riga ta gansa ɗin.
ya buɗe baki zai yi magana ta tari numfashinsa,"yau da safe baka shigo inda nake ka duba ni ba sannan ka dawo kana ganina amma kasa kai ka wuce saboda banda mutunci yanzu a idonka. idan Falmata ce ka isa kai mata haka?, ko sallah kaga tana yi a compound ɗin nan ai sai ka jira ta idar tasa maka albarka tukunna zaka wuce. to ni dai Allah ya isa rabani da akai da kai wallahi, ba'a san irin baƙar wuyar dana sha kafin haihuwarka da lokacin haihuwarka ba, ba yafewa zanyi ba. kuma kaje duk wanda zai saka maka albarka wallahi bata kai tawa ba, a banza a wofi, kai da ka san darajar uwa ma da baka fifita kishiyata akaina ba, shashashan banza marar hankali kawai, idan baka sani ba ka sani uwa tafi gaban wasa".
muryar Yusuf a hankali kuma da ladabi yace,"kiyi haƙuri Ammi amma ba yanda kike tunani ba ne, yau da safe ko gidan nan banzo ba Allah".
taja tsaki tace,"aikin banza. to ka juyo ka kaini unguwa in ka dawo kaje duk inda zaka je".
yasa hannu ya shafa kansa tare da rufe idonsa bai ce komai ba kuma bai motsa daga inda yake ba. Ammi ta ƙara cewa,"baka ji me nace ba ne?".
yace,"naji Ammi". tace,"ba zaka kainin ba ne?, ko kuma izinin uwar taka zaka fara zuwa ka nema?".
ya ƙara sosa kansa yace,"ai Umman bata dawo ba Ammi".
da a kusa da ita yay maganar da babu abinda zai hanata buge masa baki, cikin zafin rai tace,"zan zauna zaman jiranka ne ko ya?".
yace,"Ammi dan Allah ki kira Aliyu, Inna Wuro ce ta kirani Nuratu babu lafiya zan ɗauketa mu wuce asibiti...". tun bai ƙarasa ba ta dakatar da shi,"ai nasan da Aliyun ban ce shi ba sai kai. Yusuf matarka ko mutuwa zata yi ba zaka je wurinta ba a yanzu sai ka kaini ka dawo, na faɗa maka in ba haka ba kuma zaka sha mamakina, zan maka abinda baka taɓa tsammani ba daga gareni".
ƙasan zuciyar Yusuf yaji
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 73