damƙi mayafin da aka lulluɓeta da shi, a hankali ya shiga adu'ar.
"Allah ba yanzu ba, Allah ko don waɗannan jariran, zuwan su duniyar kenan Allah, Allah ka sauya musu wannan ƙaddara ya zama ka ɗauke ni ba mahaifiyar su ba, sun yi kaɗan da irin wannan jarabawar, Allah don Allah ka dawo da Fulani ka ɗauke ni, Allah kar kasa Fulani ta tafi ta barmu, Allah ka tausaya mana ba zamu iya ɗauka ba,Allah ka tausaya mana don masoyinka fiyayyan halitta, Allah don son da kake yiwa Annabi Muhammadu SAW".
sai ya kalli jaririyar da kukanta ya fara yawa yace,"Allah'n mu ka tausaya mana, don Allah Allah ka juya wannan ƙaddarar, ka ganta Allah tana buƙatar nonon mahaifiyarta a halin yanzu, idan kace ka ɗauketa bata da me bata abincinta, Allah ko ba don ni ba, don jariran nan Allah ka tausaya mana, Allah jarabawar tayi mana girma, a sauya mana, a dawo da Fulani a ɗauƙe ni Allah".
sai yayi ƙarfin halin miƙewa ya hau kan gadon ya zauna, zama sosai har da miƙe ƙafa, ya ɗaga mayafin da aka rufeta da shi ya buɗe fuskarta, da farko daskarewa yayi a yanda yake, sai kuma yayi blinking idonsa, saboda ganin kamar likitocin sun yi makuwar saƙon da suka faɗa masa, domin wannan ba fuskar gawa ba ce, wannan fuskar ta me bacci ce, gata nan fess da ita, ta ƙara yin wani irin kyawun da bata taɓa yi masa ba, fuskarta ta ƙara yin doguwa, hakama hancinta kamar ba nata ba, ya ƙara yin tsaho sosai, fuskarta sai annuri take.
a sanda ya lura da rashin motsin bugawar zuciya a ƙirjin matarsa, a sannan ya kamo hannunta ya ƙanƙame a ƙirjinsa ya haɗa da jaririyar, yana jin irin yanda zuciyarsa ke huci tana huda ƙirjinsa tana neman fashewa.
shi musulmin ƙwarai ne ya san mutuwa, ya yarda da ita, so dole yay accepting jarabawarsa, dole ya yarda da ƙaddadararsa, yanzu ya tabbatar da likitocin ba ƙarya suka yi masa ba, ta mutu, ta tafi in da Maama ta tafi, ta tafi in da ba'a dawowa.
sai kawai ya kwantar kansa akan ƙirjin gawar tare da rufe idonsa, yana jin wani irin bala'in kaɗaici ya lulluɓe shi, yana jin mugun tausayin kansa, yana jin tamkar shi ɗaya ne ɗan Adam ɗin da yay ragowa yanzu a duniya, sai yaji ina ma shi ma tasa zuciyar ta daina motsawa tamkar ta Fulaninsa, shi ma ya koma gawar ko ya daina jin raɗaɗin da yake ji a zuciyarsa, yana jin kamar ya zama gawar ya bi bayan matarsa masoyiyarsa, ya bi bayan macen da ta dinƙa kasada da ranta domin ceto rayuwarsa.
a haka yay kissing ƙirjinta, tabbas wani tashin hankalin yafi gaban kuka, domin a yanzu ya kasa yin kukan, alhalin kuma kukan yake so ya yi.
wacewar mintuna ashirin da biyar, a lokacin ƙarfe ɗaya da rabi na dare, acikin parlon na Hajiya Ramla, gawar da aka rufe na shimfiɗe akan carpet, in da a hankali sautin wasu muryoyi ke fita da kuka wajen sanar da mutuwar da akayi.
a wannan lokacin Hajiya Ramla da Baffa da Boɗejo da Ilham na kan Turaki, wanda ya sume tun a dawowar su, tun a lokacin da suka dawo gida yake tsammanin zai ga Fulaninsa ta fito da ƙafafunta, amma sai yaga an fito daga mota wasu na ɗauke da gawarta, a lokacin ya san kallonta kawai yake yi, sai kuma yaji kukan jariran da ke hannunsa na tashi, kukan da ya ƙara haddasa bugun zuciyarsa, kukan da ya kaishi ƙololuwar tashin hankalin da har bai san lokacin da yanke jiki ya faɗi ba, ya san dai tare da yaran ya faɗi, amma bai san wanne hali shi da su suka shiga bayan faɗuwar tasa ba.
don haka tun bayan faɗuwar tasa tsawon minti goma kenan a yanzu, ƙoƙari ake tayi wajen ganin ya dawo hayyacinsa, kuma da taimakon Dr Yusuf ya farfaɗo, sai dai kana kallonsa kasan baya cikin hayyacinsa, idonsa na tsaye ne a waje ɗaya ƙyam ya zama kamar gunki, cikin ransa ji yake ina ma bai farfaɗo ba shi ma ya mutu, har cikin zuciyarsa ji yake ina ma yabi bayan Fulaninsa da Maama, duk da cewa baya so ya rabu da yaransa, to amma bai san ta yanda zai fara rayuwa tare da yaran ba alhalin mahaifiyarsu bata raye, yana tsananin tausayin su, don haka a yanzu babu abin da yake so illa ya mutu shi ma, baya so yaci gaba da rayuwar sam.
kamar daga sama mutanen parlon suka jiyo muryarsa na faɗin,"Wannan wacce irin jarabawa ce ubangiji yake yi min?, laifin me na aikata da za'a jarabce ni irin haka?...".
Baffa yay saurin saka hannu ya rufe masa bakinsa.
"kar ka yi saɓo Muhammad, kar ruɗani yasa ka fita daga imaninka, kayi haƙuri, ka yi tawakkali ka roƙi Allah ya baka dangana, kayi haƙuri komai muƙaddari ne, ka roƙi Alah ya baka ikon cinye jarabawarka".
Turaki ya shiga sauke numfarfashi, ya shiga jan mazaunansa har ya ƙarasa gaban gawar da yake gani, ya ɗaga mayafin ya ruƙo hannunta.
"Fulani Nah! don darajan Allah da Annabinsa ki tashi, na yarda ki tashi ni sai na tafi, ko kuma mu tafi tare, ba zan iya rainon yaranmu ba ni ɗaya, ban san me zan ce musu ba a san da suka tambaye ni ke".
sai kuma ya kifa kansa kan gawar yana ambaton,"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".
faɗa yake yana ƙara maimaitawa, yana girgiza gawar, gani yake tamkar idan yana hakan zata farfaɗo, kamar zata dawo duniyar su ci gaba da rayuwar su tare, su raini ƴaƴan da Allah yaba su ciki kyakykyawar kula da tarbiya, idan yaji yaran sun yi kuka sai ya shiga girgiza kansa yana faɗin Allah ka sassauta min, Allah tayi min tsauri, Allah kaji tausayina.
duk sai ya koma kamar wani taɓaɓɓe, sai maganganun kawai yake yi, idan aka ce yay haƙuri yay ƙoƙarin cin jarabawarsa sai yace ba zai iya ba, tayi masa tsauri, da farko an ɗauke masa Maama, mutuwarta bata gama sakinsa ba an ɗauke masa Mata, sannan an bar shi da marayu, marayun da ko nonon uwarsu ba su samu damar sha ba, to ta ina zai iya ɗauka?, ta ya ma zai iya cinyewa?
haka akaita rarrashinsa amma inaaaa, a lokacin da ya rasa Maama ganin yake idan aka cire Mum to duk wata mutuwa da zata zo masa zai ɗauketa, zai iya ɗauka, but a yanzu da ya rasa matarsa, uwar ƴaƴansa sai yaga abun ba haka ba ne, da wuya, da zafi, ba zai iya da wannan jarabtar ba me tsayawa a zuciya.
a wannan dare dai waɗanda suka sami yin bacci ƙailan ne, hatta Ilham sai ɓarawon bacci ne ya ɗauketa, domin sosai mutuwar ta taɓata, a ɗan sabon da suka yi Fillo ta shiga ranta, don tun bayan da Allah ya ganar da ita ta koma yiwa Fillo kallon ƙanwa ta jini ba wai kishiya ba.
Hajiya Ramla kuwa na kan ɗanta, idan tayi rarrashin tayi rarrashin sai taji tana taya shi kukan da ya kasa yi. haka suka kwana ba su runtsa ba, yana riƙe da hannun gawar, yayin da jariran ke jikinsa su na bacci, waɗanda aka rarrasa da ƙyar suka daina kuka har baccin ya ɗauke su, waɗanda har gari ya waye ana tunanin wanda zai shayar da su.
washegari ƙarfe goma na safe an gama haɗa gawar Fillo, gawar tana tsakiyar parlon na Hajiya Ramla cikin sutturarta, cikin wannan farin ƙyallan da ke jiran duk wani mai rai, mahaifiyarta da Yayanta da Kaka da Dada su na gaban gawar su na kuka, musamman Ummi wacca ake ta cewa su yi sallama, tayi mata adu'a domin wannan ita ce sallama ta ƙarshe da za su yi.
"Allah ya jiƙanki Halimatu, Allah ya yafe miki kurakuranki, Allah ya baki Aljannatul firdausi, Allah ya karɓi shahadarki, Allah ya karɓi ruhinki cikin daraja, Allah yasa Manzon Allah ya karɓi baƙuncinki, Allah yasa mutuwa ta zamto hutu a gareki, Allah ya lulluɓeki da rahamarsa da gafarsa, haƙiƙa ba ki yi min komai ba, na yafe miki duniya da lahira, abin da kika bari Allah ya kula miki da su, Allah ya basu haƙuri da juriyar rashinki. sai mun taho muma".
aka shigo da Turaki, ya zauna shi ma agaban gawar, yana jin sautuka na shiga kunnensa, sai dai a lokacin babu abin da ƙwaƙwalwarsa ke iya ganewa, har yanzu ya kasa karɓar mutuwar matarsa, ganin komai yake yi tamkar shirin wasa, tamkar shirin film aka haɗa don kawai a girgiza shi, don kawai a gwada irin ƙarfin soyayyar da yake yiwa Fulaninsa.
"Muhammad ka yi mata adu'a, kuyi sallama Muhammad kaji".
tun daren jiya, tun lokacin da labarin mutuwar matarsa ta riske shi, da zaman kwanan da yay agaban gawar, zuwa wayewar garin yau da ya ƙara tabbatar da ya rasata, sai a yanzu da ake cewa yay mata adu'a suyi sallama ya ji idonsa ya cika, saɓanin jiya da yake a bushe, har yana jin kamar ba zai taɓa zubar da ruwa ba, amma a yanzu tarin ruwan da ya cika a idonsa ba ya jin zai iya dakatar da su, saboda haka sai kawai ya kifa kansa akan ƙirjin gawar, hawayen ya ƙwace, kukan ya kubce, ya shiga rero kuka tamkar ƙaramin yaro, yana kukan jikinsa na girgizawa kamar yanda zuciyarsa ke yi.
adu'ar da ake ta cewa yayi ya kasa yi, sai da ƙyar aka iya raba shi da jikin gawar, aka miƙar da shi aka riƙe shi, yana kallo aka ɗauki gawar aka fita da ita, da sauri ya bi bayan su, ya tarar da su su na saka gawar a cikin makara.
abinda ya saka shi ƙara rikicewa, sai ya tsinci kansa da yiwa Allah godiya da ƴaƴansa ba su tsinci ganin wannan lokacin ba.
ƙarfe sha ɗaya dai-dai aka yiwa Fillo sallah, a cikin ƙaton compound ɗin gidan Alƙali Dikko, bayan gama sallar gawar aka ɗauƙi makarar aka fita da ita daga gidan, Turaki na sahun gaba, ƙafafunsa ke jansa ba shi ne yake tafiyar da su ba, yayin da hannunsa guda ɗaya yake cikin na Bello ya riƙe shi da kyau, saboda gudun faɗuwarsa.
a lokacin da aka isa maƙabartar, Hamid da su Yusuf da Baffa su ne suka fito da gawar daga cikin makara, Bello ya kama hannun Turaki ya kama kan gawar sannan aka sata a cikin ramin ƙabarinta, yana kallo ana fuskantar da fuskarta zuwa ɓarin gabas, yana kallo aka ɗauko fasassun tukwane aka jejjera a saman gawar, kafin daga bisani yaga ana zuba ƙasa ana toshe ko'ina, yana jin muryoyin da ba zai iya tantacewa ba na faɗin a toshe kowacce ƙofa, yana kallo bayan an gama rufe gawar ruf da ƙasa aka yayyafa ruwa a samanta, sannan aka ɗauko allon shaida aka dasa a wajen kan, allon da yake iya karantawa, komai yana faruwa kamar dai sati biyu da suka wuce.
sunan da ke jikin Allon ɓaro ɓaro, sunan matarsa, sunan abar ƙaunarsa, wannan Fulanin tasa, wannan Fulanin da yake jin ba zai iya rayuwa ba a duk san da babu ita a tare da shi, yau shi ne a gaban ƙabarinta, da shi aka kawota, yana kallo aka sakata cikin rami bai iya hanawa ba, bai iya buɗar baki yace a'a ba, bai iya motsawa ba balle ya riƙe gawar.
*Marigayiya Halima Muhammad Hayyo(Fulani), Allah ya jiƙanki da rahamarsa, 03/10/2022.*
kamar hakan allon ke ɗauke da rubutun cikin manyan baƙi, ji yake kamar ya fincike allon ya jefar.
a hankali ya dawo da tunaninsa ɓangaren da yaji ana doguwar adu'a, sai ya fara kallon kowa ɗaya bayan ɗaya, kowa a tsugune yake ya ɗaga hannunsa, sannan Dr Yusuf da Hakim da Khaleel idanuwan su na hawaye, sai Baffa da Daddy(Baban su Dr Yusuf) fuskarsu fayau, sai ya mayar da kallonsa kan ƙabarin, shi ma ya ɗaga nasa hannun, ya shigo jero tarin adu'a wa ruhin matarsa, yi yake yi yana maimaitawa, har zuwa lokacin da yaji takun tafiya alamu na ƙafafu sun fara barin wajen.
yana ji mutanen da ke kusa da shi su na tashi, kuma kafin kowa ya tafi sai an zo an dafa kafaɗarsa ance masa,"Allah ya jiƙanta, Allah ya bada haƙuri".
da haka da haka sai da ya tsinci babu kowa a kusa da shi, sai shi kaɗai da yake zaune yana kallon ƙabarin ya kasa sauke hannunsa, har sai da Bello ya zo ya dafa shi yace,"kayi haƙuri ka tashi mu tafi".
sai yaji Khaleel ma na ce masa,"Hammah kayi haƙuri".
kawai sai ya saki kuka me ƙarfin sauti, ya kai hannunsa ya ɗora akan ƙabarin, a hankali yace,"insha'Allahu zan yi duk abin da kika ce, zan kula da yaranmu, zan ba su tarbiyya, zan saka su a makarantar da kika faɗa, ba zan bari su yi kuka ba, ba zan sa suyi kuka ba, ba zan bari su shiga cikin ƙunci ba, ba zan bar su suyi maraici ba, zan riƙe amanar da kika bar min, nayi miki alƙawari, zan kuma cika miki shi tabbas. don Allah ki yafe min da duk laifin da nayi miki, don Allah Fulani Nah, ki ce ina gaida Maama".
Bello da Khalil suka kama shi ya miƙe. suka riƙe shi suka fara tafiya domin barin cikin maƙabartar, sai da suka zo bakin ƙofar fita ya juyo yana daɗa hango kabarin, yana faɗin,"zan dinga zuwa kullum ina gaishe ki, zan dinga zuwa kullum ina yi miki adu'a, idan Aayan ya girma zan dinƙa kawo miki shi kina saka masa albarka, na gode Fulani Nah, sai anjima kinji ƴar aljannah".
komawar su gida suka tarar da ɗumin dandazon jama'a acikin rumfunan tanfol ɗin da aka yi kusan guda biyar, kai tsaye cikin gidan ya wuce bai tsaya a waje ba, yana shiga ya fara karɓar gaisuwar ta'aziyya daga mutane, ba wani ganin su yake yi ba, don ba ya gani da kyau.
ya ratsa ta cikin falon Mum ya haye sama, daga ƙofar ɗakin nata ya tsaya yana kallon Nihal da Ilham da ke goye da marayun jariransa, sai ya shiga ciki ya kunto yaran daga bayan su da kansa, ya fito ya bar ɗakin, ya kuma ratsa mutanen dake parlon ƙasa ya fice daga sashin gaba ɗaya.
kai tsaye ɓangarensa ya nufa, ya buɗe ɗakinsa ya shiga, ya zauna akan gado tare da jinginar da kansa jikin gadon, ya kwantar da macen a ƙirjinsa, namijin kuma ya ɗora shi a kan ƙafafunsa.
"your mum is no longer with us, she is gone and she is never coming back, death have separated us, she wants us to pray often for her, tun kafin ta haife ku tace Allah yaywa rayuwarku albarka, kuma na san ta biku, Allah ya raya min ku. Allah ya bamu haƙurin rashin da muka yi, ina yi mana ta'aziyya".
ya faɗa ya ƙara maimaitawa kamar yaran su na fahimtar me yake cewa, kafin a hankali ya rufe idonsa. in da a wannan lokacin Ilham ta shigo hannunta riƙe da tea flask, jikinta duk a sanyaye sai idanuwanta da suka yi jawur.
ta ƙarasa ta zauna a bedside drower tana kallonsa, tana kallon yanda hawaye ke fitowa daga idonsa yana bin kumatunsa, yayin da bakinsa ke motsi yana furta abun da bata san menene ba.
ta jima kafin ta iya saka hannu ta taɓo shi tayi masa magana, ya buɗe idonsa ya kalleta bai ce komai ba, Baby ɗin dake saman ƙirjinsa ta motsa, yay saurin gyara zama yana ɗagota daga ƙirjinta ya kalleta.
"sorry little...". sai ya rasa da sunan da zai kirata, da Aina'u(Hajiya Madina) ko kuma Halima(mahaifiyarta)?
cikin wata murya me mugun rauni ya ce,"yanzu baza ki iya samun ruwan nono ba?".
ya jefa tambayar ga Ilham, kafin ta ba shi amsa sai ya ƙara cewa,"ki taimaka musu don Allah, tun jiya babu abin da suka ci, Mum tace min sun ƙi shan madarar, na san su na jin yunwa, don basu da bakin magana ne kawai amma da sun faɗa".
kuka ya taho mata tace,"idan akwai yacca za'ai nonon ya zuba sai ayi, duk nayi nayi su kama nonon ko zai zuba sun ƙi. amma ɗazu da ku ka tafi kaita Fauziyya ta ba su sun sha".
"wacece Fauziyya?".
"ƙanwar Bello".
sai ya ɗago da sauri ya kalleta yace,"don Allah kirawota tazo ta ƙara ba su, kin ga Maama ta tashi, bana so tayi kuka".
cikin sauri Ilham ta tashi ta fita, tana fita ya ɗauke Aayan daga kan ƙafarsa ya kwantar akan gadon, ya sauko yana jijjiga Maama a saman kafaɗarsa.
idanunsa na ƙara cika da ruwan hawaye, ya tuna jiya kamar yanzu ya na tare da mahaifiyar su, yana hasko san da Fillo ta ɗauko kayan da ke jikin yaran a yanzu, yana tuna sunan lukutar gombe, yana tuna irin dariya me faɗin da take yi a duk sanda ya faɗa mata hakan, yana tuna ranar da tayi fushi da shi ta kalle shi ta murguɗa masa baki, har tana cewa ko ta haihu yaranta da sunanta za su bearing ba nasa ba, sai da ace Muhammad Halima da Aina'u Halima, duk ba zasu saka Turaki ba, tana faɗin ai ita ta haifa, shi kuma yana faɗin ai dai shi ya bayar.
yanzu bata raye, komai nata ya zama tarihi, ta tafi ta barshi da memories masu matse zuciya, yaji hawaye masu zafi sun sauko masa, tashin hankalinsa ɗaya ne, damuwarsa ɗaya ce, tunaninsa ɗaya ne, nonon wa yaran za su dinƙa sha?.
*BAYAN SHEKARA GOMA SHA SHIDA.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*GAMJI WRITER'S ASSOCIATION*
_Home of exceptional writers._
*61*
Da gudu ta fito daga cikin ɗakin, isowarta falo suka yi karo da Inna Wuro ta faɗi a ƙasa, ita ma medical glass ɗin idonta ya faɗi, nan da nan ta shiga kokawar ɗauko shi daga ƙasan.
idanun sai ƙiftawa suke yi kamar an tsokane su, sai da ta saka glass ɗin sannan suka daina ƙiftawar, kuma kallo ɗaya zaka yiwa ƙwayar idon nata ta cikin glasses ɗin ka san ba lafiyayyu ba ne.
yanda jikinta ke rawa zaka ce ko bata da lafiya ne, nan kuwa zallar rashin gaskiya ne a tare da ita.
ta kalli Inna Wuro ta gefen ido, dariya ta taho mata tayi saurin sa hannu ta toshe bakinta.
"huhuhu, la'ila ha'ilallahu, waiwaiwai. to ni dai sai dai in ce Allah ya isa kawai".
ta buɗe baki zata yi magana Inna Wuro tayi saurin ɗaga mata hannu a sanda take girgiza kai.
"a'a fa ni ba sai kin ce min komai ba, ai na riga na kaiwa Allah ƙara, zai yi min sakayya da kansa, cuta ce dai kin gama yi min ita".
Aliyu ya shigo a lokacin, Inna Wuro ta ɗaga kai ta dube shi tana aikin rumtse ido, ta yarfar da hannu ta ce,"gwara da Allah ya shigo da kai Aliyu, hanzarta ɗauko mota ka kawo bakin ƙofar ɗakin nan nawa, gidan sarkin ɗori zamu tafi tun ban gama shiga uku ba, ta ɓalla min duk ƙafafun nawa biyu, kai baka ji irin azabar da ke ratsa ni ba. waiwaiwai, huhuhu Allah dai ya saka min".
Aliyu ya kai dubansa ga Maama wacca ke tsaye tana gyara zaman glass ɗin idonta, fuskarta ɗauke da siririn murmushin ƙeta, a yayin da dogwayen lashes ɗin sama da na ƙasa suka haɗe, kafin ta buɗe su kyawawan chocolate eye balls ɗinta masu ɗauke da ruwa su bayyana.
su na haɗa ido da ita tayi ƙasa da kanta tana haɗe pink lips nata, still tana ƙunshe dariyarta.
sim sim ta bar bayan Inna Wuro ta nufi hanyar fita Aliyu ya dakatar da ita, ta tsaya tana rumtse idanu kafin ta juyo ta kalle shi.
cikin siririyar muryarta me bala'in zaƙi tace,"Uncle ba na sane fa".
sai ya kalli Inna Wuro da har yanzu take dirshen a ƙasa, sai matsa ƙafafu take yi a lallai sun karye.
"Inna to kinji bata sane".
"to dama tsoron Allah take yi da zata faɗa maka gaskiya, ni dai tun da ta riga ta cuceni kaje ka ɗauko mota kawai mu tafi gidan sarkin ɗori tun ban koma amfani da sanda ba, dan ƙarshe dai asibiti su yanke ƙafafun, ni kuwa ina zan so naga ana tura ni a keken guragu".
tayi shiru tana girgiza kai alamun takaici ya isheta."sam yarinyar nan bata da mutunci wallahi, ka duba fa Aliyu ka gani an fi ƙarfin awa guda da watsar da ni da tayi a ƙasan tiles ɗin nan, amma kalmar haƙuri ta gagara fitowa daga bakinta. alhalin tun duku dukun safiya aka baro gidan uba aka taho gidan ɗana cin arziƙi, to da yake ma dai ɗan Adam butulu ne, amma babu komai akwai Allah ai".
Maama tace,"kiyi haƙuri Inna Wuro".
"a'a wallahi ba zai yiwu ki cuce ni ba ki bani haƙuri, ke dai je ki kawai da mugun halinki".
Maama ta fice daga ɗakin tana dariya.
Aliyu yazo ya kama Inna Wuro don ɗagata, ta miƙe tana faɗin,"ba abin nace zan bawa Zainabu shawara ba tace zata ƙullace ni, ko kuma ta zage ni, amma da sai in ce ku kai yarinyar nan gidan ruƙiya zance na domin Allah kenan".
Aliyu yay guntun tsoki,"zancenki kenan aljanu".
"to kaji ba, ina kuma ga uwarka na faɗawa. yanzu in ace jikar Falmata ce wallahi kaina tsaye zanje in bata shawarar nan. yanzu kai Aliyu ban da kai ma dai halin uwarka ka yo na rashin son gaskiya tsakani da Allah ai ka san wannan ƴa dai tana da iskokai".
yay mata wani kallo yana nufar kujera ya zauna,"babu wani zancen gaskiya tun da ba gani kika yi ta tayar ba".
"to Aliyu har sai ta tayar za'a san tana da aljanu, ina batun watsota da suke yi a guje fa?, haba a duba lamarin nan dai. ni ko da kaji na faɗi haka ba wai sonta ne bana yi ba wallahi".
Aliyu ya ɗauki remote yana dannawa yace,"to ba wasu aljanu, kije ki duba ɓarna tayi miki".
yana yin shiru tai hanyar ɗakinta cikin hanzari tana maganganu. kuma tana shiga ɗakin ta tarar da plastic bucket ɗinta yashe a tsakiyar ɗakin, murfinsa a tsakiyar gado yayin da aka yashe rabin dubulan da alkakin da ke cikin botikin.
ta ɗora hannu a saman ka kafin ta zube a gefen gado ta zabga salati.
"Jikar Zainabu ko masifa, to wallahi ba zai yiwu ba dole ma ƴar nan ta bar gidan nan yanzu babu ɓata lokaci, tun da dai gida Ɗana ya gina shi ba Zainabu ba, ina dalili jarabar sata har cikin ɗakina".
Aliyu na tsaye bakin ƙofa ta kalle shi tace,"ashe kasan hali shiyasa kace in zo in duba dukiyata, to kuwa dai ban yafe ba ka faɗawa Zainabu da shi uban yarinyar".
bai kulata ba ya sauke wayar kunnensa ya nufi gadon don tashin Farha, wacca ke ta bacci bama ta san wainar da ake toyawa ba. yasa hannu ya shiga tashinta, ta buɗe ido a hankali, ganinsa yasa ta miƙe zaune babu shiri tana murza idanuwa.
Inna Wuro da ke gyara bokitinta tana lissafa dubulan da alkakin da ke ciki tace,"da yake kai ne ai kaga ta tashi, ni kuwa da nake ƴar iska idan na tasheta ai sai dai ta yarfo min zagi. ba abin na bawa iyayenta shawara ba su ƙullace ni, amma wannan ƴa ai da gani ta narki ruwan mahaifa, ya kamata kuma a fita da ita ƙasar waje su fasa kanta su kwashe shi, shi Yusufun da ike karatun likitancin banza da wofi yay ai ya kasa gane ƴarsa ta kwankwaɗi ruwan mahaifa".
Farha ta sakko akan gadon tana ƙunƙuni ta fita daga ɗakin. direct part ɗin Ammi ta wuce, tana shiga parlo ta tarar da Ammi na cewa da Maama.
"wa ya faɗa miki ana taɓa kayan Inna Wuro, salon dai kija min jarfa. yanzu idan ta fara mita ta dinƙa yi kenan har sai an biyata kayanta, duk abin da kika ga tsohuwar nan ta ajiye a lissafe kayanta yake".
Maama ta turo ɗan ƙaramin bakinta, ta warware mayafin jikinta tana fito da uban dublan da alkakin da ta kwaso, ta buɗe leda tana zubawa aciki tana faɗin,"Ammi to ba ita bace nace ta bani sai ta ɗau guda ɗaya tal ta ban, ni kuwa tana fita na ɗauki rabona".
Ammi ta girgiza kanta,"to ai kuwa sai kiyi ki zuba a ledar ki ɓoye kafin ta biyo bayanki, don wallahi tazo wajen nan sai dai ku yi asararsa".
cikin sauri kuwa ta juye shi cikin leda ta saka a jaka. kuma kamar jira sai ga Inna Wuro ta faɗo ɗakin tana faɗin,"to ina Zainabun?".
su ka haɗa ido da Ammi da ke kan kujera tana danna remote wurin sauya channel. Inna Wuro
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 71 Chapter of 73