kan kujera, da siririn farin medical glass a idonta, tayi jugum tana ta kallon jikan nata. lokacin da aka kawo Turaki da Zaytuna asibiti, lokacin ta kira wayar Baffa take sanar masa tana ta kiran wayoyin yaran bata samu, har ta babarsu Hajiya Madina ma ta kira bata samu ba, shine Baffan ke faɗa mata halin da suke ciki na cewar suna asibiti, Zaytuna da Muhammad duk sun suma, kuma for morethan 15minutes ba wanda ya farfaɗo acikinsu.
a lokacin Granny ta kira ɗanta tace a yanzu ba da ɓata lokaci ba tana son zuwa nigeria, kuma a awa biyar da minti hamsin da biyar sai gata ta a asibitin cikin tashin hankali tana ta kuka, sai dai ko lokacin da tazo ɗin duk sun farka, Zaytuna ma har ta miƙe, shine dai ke kwance saboda ciwon dake jikinsa.
Granny ta numfasa tace,"Ramla dai ta cuci kanta, dan ba zance ta cucemu ba...so do you know what i want from you Muhammad?".
Turaki ya haɗiye abu ya kalleta yana jiran cewarta. "Muhammad ka manta da Ramla, ka manta da ita da abinda ya shafeta, ka samawa kanka lafiya, ka samawa kanka kwanciyar hankalin daka rasa tun ranar da tasa ƙafa ta tafi ta barku...".
Turaki ya katseta da faɗin,"Granny do you know what you are saying?". ta jijjiga masa kai,"i know Muhammad, i mean you should forget Ramla in your life, just like she forget you".
sai ya kwantar da kansa yace,"Granny hannunka baya ruɓewa kace zaka yanke ka jefar". tace,"idan ta kama a yanke sai a datse shi a huta, komai ai kamawa take".
kansa ƙasa yace,"but karki manta duk lalacewar uwa uwa ce, how can i forget her?, na fa manta da ita da abinda ya shafeta kike cewa?, how?, ki daina faɗar abinda ba zai yiwu ba Granny".
yanayin yanda yayi maganar sai yay mugun bata tausayi.
sai kuma ya rumtse idonsa zuciyarsa na tafarfasa,"even though I was six years old at the time. Granny har yanzu ina ganin hoton komai tar acikin kaina, ina kallon lokacin da tasa ƙafa tayi tafiyarta ta barmu ba tare da ta ko waiwayi kukan da nake ba, bata dubi kukan Zaytuna dake naɗe aciki showel ba, tayi tafiyarta ta barmu, as if ba daga jikinta muka fito ba, as if ba ita ta tsuguna ta haifemu ba, kamar ba da auren sunnah ta samar da mu ba, inda ace wutar ta cinyemu fa?, da ace mun mutu fa?, da Allah bai kawo Maama a lokacin ba fa?".
lokaci ɗaya sai hawaye ya shiga sakko masa akan kuncinsa, cikin kunnensa yana jin sautin kukan Zaytuna da ta dinga tsalawa a lokacin, yana jiyo nasa sautin kukan dake fita da harufan sunan Mum. yana jin komai kamar yanzu yake faruwa, tana fa kallon yanda wuta ke ci a ɗakin, amma ta tankaɗasa ya koma ciki ta rufe ƙofar ta barsa daga shi sai jaririyar dake cikin gado kusa da inda wutar ke daɗa kamawa, tayi tafiyarta ko tausayinsu bata ji ba, me suka mata?, har yanzu tambayar da yake ta so yayi mata kenan, ya ganta ya tsuguna agabanta ya tambayeta zunubin da suka aikata mata, sannan sai ya roƙar musu yafiyarta, idan ta yafe musu sai ya bata labarin abinda yake ɓoyewa kowa, kowa banda Bello da Zaytuna.
to aina zai ganta?, yaushe zata dawo?.
_a dai ci gaba da haƙuri, da zarar mun kammala biki shikenan....ina godiya da kulawarku._
*Please Comment and Share and Vote.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_Please avoid any mistake._
*24*
"nima da nake mahaifiyarta na manta da ita, na manta na taɓa haihuwar ƴa me kamarta ko sunanta, na jima da cireta a sahun ƴaƴana. saboda haka kaima ka manta cewar ita mahaifiyarka ce tunda har ta iya manta da cewar tana da ƴaƴa, ka riƙe wadda ubangiji ya dubeku ya tausaya muku ya baku ita ta maye gurbinta...Allah ne kaɗai yasan hikimarsa akan hakan, wataƙila ba zaku sami tarbiyya da soyayya daga wurin Ramla ba shiyasa ya ƙaddara faruwar wannan lamarin".
jin maganan Granny ɗin yasa Turaki buɗe idanuwansa, ya buɗe su a daidai lokacin da Hajiya Madina ke shigowa ɗakin. kallo ɗaya yayi mata yaji tsananin tausayinta ya kamasa, ya ƙara jin ƙaunar matar a ransa, haka ne, basu sami soyayyar mahaifiyarsu ba, kuma basu samu tarbiyya daga wurinta ba, amma Allah ya basu wacce tayi musu dukkan waɗannan gatan, wanda iyakacin abinda wadda ta haifesu zata musu kenan.
hijab ɗin dake jikinta fuskarsa ma a karkace ta saka, ya bita da kallo har sanda ya sauke ƙwayar idonsa kan bayan hannunta. tabon ƙonuwar da tayi tsawon shekaru 25 har yanzu yanan bai ɓace gaba ɗaya ba, sai kawai yasa hannu ya goge hawayen da ya sakko masa a lokacin da bai sani ba, idan bai so Maama ba wa zai so?, idan bai ƙauna ce ta ba wa zai nunawa ƙauna?, idan bai kula da ita wa zai bawa kulawarsa?, wataran har yana jin yafi sonta fiye da wadda ta kawosa duniya, har yana jin tausayinta fiye da yanda yake tausayin Mum ɗinsa.
Hajiya Madina ta ƙaraso bakin gadon, Granny na amsa sallamarta, jikinta duk a sanyaye taja kujera ta zauna, ta dubi Turaki da muryanta da yay ƙasa tace,"sannu me Babban suna". ya amsa da,"yauwa Maama, thank you so much for your care".
ganin yanda ta ƙura masa ido sai ya sauke idonsa ƙasa, yana jin nauyinta na shigarsa, ya sani yayi mata laifi. laifi har guda biyu a rana ɗaya, ya saɓa umarninta na cewa duk inda zai ke tafiya yanzu suke tafiya tare da Khalil, sannan yazo yasa kansa a situation ɗin da ya shiga, saboda wannan condition ɗin da yake shiga ne a duk sanda ya shiga ɗakin mahaifiyarsa shi yasa ba'a so ya shige shi, yasa ma aka rufe ɗakin gaba ɗaya Baffa ya ɓoye key ɗin, ya gargaɗe shi da ko da wasa kar ya ƙara tunkarar ɗakin, tunda duk sanda ya shiga yana tunawa da komai da ya faru a ranar da Mum ta tafi ta barsu, sai ya dinƙa jin komai tamkar a lokacin yake faruwa, sai ya dinƙa ganin yacca wuta ta ke tashi da yanda ya dinga kuka Zaytuna ma tana yi, sai yake jin kukan a cikin kansa.
hakan sai yasa yake jin wani irin raɗaɗi, ya dinƙa jin wani irin abu a tare da shi da ba zai iya kwatantasa ba a yayin da yaga hotonta. idan yana ganin hotonta sai yaji kamar ya cirota daga cikin hoton ta zama a zahirance, yay mata kallo na zahiri sai ya rungumeta ta yanda ɗumin jikinta zai ratsa shi, taci gaba da rayuwa tare da su ko da ace ba zata so su ba, shi dai kawai ya dinga ganinta yana jin daɗi, yake yi mata duk wata kalar biyayya, ya kuma nuna mata zallar soyayyarsa, irin wannan soyayyar da ta ke only between child and his mother.
alƙawarinsa ne daga zarar da ya sami job ba zai dinga barinta tana zuwa office ba, ta gama yiwa gwamnati aiki, shi zai dinƙa biyanta da kuɗin da yafi wanda take samu ba tare da tayi aikin ko da rubutu a takarda ba, alƙawarinsa ne zai nema mata wacce zata dinga kasancewa tare da ita idan baya kusa da ita, zai nema mata yarinya kamilalliya kuma kimtsatstsiya, irin yarinyar da ta san darajar uwa, irin wacce tasan kalar soyayya da kulawar da ya dace a nunawa uwa, irin wacca yasan ko da a bayan idonsa ba shi da haufin ba zata bari ko da ƙuda ya taɓa mahaifiyarsa ba.
ya ƙara ɗago kai yana kallon Hajiya Madina, wacca a yanzu tayi ƙasa da kanta tana goge hawaye. sai ya rumtse ido sosai yana jin wani ɗaci a zuciyarsa. a hankali yace,"dan Allah Maama ki daina kuka a gabana, bana so, yana ɗaga min hankali...kiyi haƙuri ji nayi kamar idan na shiga room ɗin Mum zan ganta, naji ne kamar tana kirana a lokacin, dalilin da yasa na buɗe kenan...kuma dana shiga sai ban ganta ba, ban ganta ba ko da inuwarta sai hotonta".
ta ɗago tana daɗa goge hawayenta da cewar,"me Babban suna bana so naga wani abu ya sameka, bana so ko kaɗan. amma wannan hawayen ba naka bane, na Ramla ne, ina ji inama na san inda take naje na dawo da ita, ta dawo muci gaba da rayuwa tare. ta zauna tare da ƴaƴanta ko sa sami kwanciyar hankali, babban damuwata shine rashin sanin halin da take ciki".
Granny tace,"shekarun aka faɗa muku kwana 25 kacal, idan zaku yarda da ni ku yarda kawai, ko da ace zaku samu labarin Ramla, ina jin sai dai ku sami labarin mutuwarta".
Maama tayi shiru tasa handky tana ƙara goge hawayenta tace,"in Allah ya yarda tana raye, me Babban suna yace yana ji a jikinsa tana raye kuma in a safe place".
Granny tace,"ke komai aka faɗa sai dai ki faɗi view ɗin wani me Babban suna, to ai sai kuyi ta zaman jiran ganin dawowarta, haka zaku zauna har zuwa busa ƙaho, zai fi muku ku haƙura da ita kawai".
Turaki yace,"insha'Allahu zata dawo". ya faɗa da sautin murya mai matuƙar ban tausayi.
Hajiya Madina ta kallesa tace,"da ma da kanka ka buɗe ɗakin?".
sai ya ɗaga mata kai alamar ehh. lokaci ɗaya zuciyarta taji rashin daɗi, taji tana dana sanin abinda ta yiwa Fillo, taji tausayin yarinyar ya kamata, taji ta ƙara son yariyar a ranta, taji ta ƙara ƙwaɗayin auren yarinyar wa Turaki, her only beloved son Muhammad Turaki.
"Me Babban suna nayi zaton Fillo ce ta buɗe zata yi aiki a ɗakin, da ta kirani nazo naga condition da kake ciki sai na yanke mata hukunci me tsauri, tana ta faɗa min bata da laifi ashe gaskiyarta take faɗa min ni kuma naƙi sauraronta. Allah na gode maka da ban yanke hukuncin da zanzo ina da na sani ba, niyyata muna komawa gida zan sallamesu ita da Kakarta, a zatona duk itace silar halin da ka shiga, ashe dai ƙoƙarin taimakon naka take da gaske".
Maganar takeyi yana sauroronta, idanuwansa kuma na gane masa Fillo a lokacin, yana tuno yanda ta dinga roƙonsa akan ya daina jiwa kansa ciwo, da kuma yanda ya ƙanƙameta yana neman taimako daga gareta, da sanin cewar in ya faɗa mata abunda yake buƙata zata taimaka masa kamar yanda ta saba, kamar yanda ta saba taimakonsa ba tare da ta san cewar ya sani ba, wannan tight hug ɗin da ya mata ji yayi kamar idan ya faɗa mata Mum ɗinsa yake so ta dawo masa da ita, to zata ce masa ya buɗe idonsa gata ta kawo masa ita, amma sai lamarin ya kasance ba haka ba.
sai ya lumshe idonsa yana daɗa hasko Fuskar Fillo, ta ya zata dawo masa da Mum idan ya faɗa mata?, ta ina zata fara kamar yanda bai san ta yanda ta fara wancan taimakon akansa ba?, sai ya matse idonsa yana jin wani abu da bai san menene ba yana tsarga masa.
tsawon lokaci Granny da Maama suna jimanta rashin Ramla tare da su, Turaki duk yana jinsu har lokacin idonsa na a rufe, amma tunaninsa na can wani wuri na daban.
akayi sallama a room ɗin, Hajiya Madina ta miƙe da sauri daga kan kujerarta tana yiwa Fulani matar me martaba barka da zuwa. cikin takun ƙasaita da girman izza ta ƙarasa shigowa ta nemi kujerar da aka nuna mata ta zauna.
hular alkyabbar dake kanta ta ɗage tana duban Turaki kafin tace,"Allah ya ƙara lafiya". tai maganar kamar tana jin nauyin bakinta, kuma kamar bata so ba.
ya ɗan rissina kansa cike da girmamawa ya amsa mata,"amin ya Allah, na gode Mami".
Hajiya Madina ma tana rissinawa ta ƙara ce mata,"sannu da zuwa". sai da ta ɗauki minti ɗaya kan tace,"yauwa. ashe Muhammad bai ji daɗi ba, to Allah ya inganta lafiya, ina ganawa da baƙi Mai Martaba yake cewa mu shirya mu taho hospital... accident ya ƙara yi?".
Hajiya Madina tace,"aa ba accident ba ne, rauni ne ya samu acikin gida, amma yazo da sauƙi ma tunda glass ɗin da ya fashe ne ya soke shi a goshi, but Drs ɗin ma sunce babu wata matsala, zuwa safiya zamu tafi gida".
sai bayan wucewar sakanni goma sha biyar da maganar Maama sannan Fulani tace,"Allah kiyaye gaba. zamu koma".
ta faɗa tana miƙewa, su kai sallama da Granny, Hajiya Madina kuma ta tafi yi mata rakiya.
Turaki yabi bayansu da kallo, yana ji a ransa Hajiya Madina itace rayuwarsa.
hoton wancan lokacin ya shiga haska masa, yana ɗan ƙarami bai san mene mutuwa ba amma yasan me wutar dake ci a cikin ɗakin zata iya haifar musu shi da ƙanwarsa, kasancewarsa yaro me bala'in wayo, kuma tun yana buga ƙofa yana faɗin,"Mum please come and open us". har ya gaji ya daina faɗa.
ya shiga toilet da gudunsa ya ɗebo ruwa a ƙaramin cup yazo ya dinga watsawa labulen da ya kama da wuta amma wutar bata mutu ba.
ya ɗauko abu ya taka yana leƙa cikin gadon da Zaytuna ke kwance yana so ya kamo hannunta ya ɗaukota su fita a ɗakin amma ya kasa, ƙarfinsa da tsayinsa ba zai kai ba. idan ya juya yaga wutar ta ƙara kama wani wajen sai tsoro ya daɗa kamasa, ya ƙara zuwa ya buga ƙofa in ya kira Mum yaji shiru sai ya dawo ya kuma taka abu a ƙoƙarinsa na ɗauko Zaytuna amma sai ya kasa, sai ya ƙara saka kuka yana ta kiran sunan Mum.
daga ƙarshe kawai sai ya zauna a gefen gadon ya kifa kai da gwiwa yanata kuka, kuka mai ban tausayi, yana ta kallon hoton Mum acikin idonsa, yana ji a zuciyarsa babu daɗi, yaro ne shi amma ya san me ake nufi da laifi, dan haka ya dinƙa jin haushin kansa akan laifin da yayiwa Mum ba tare da ya sani ba, laifin da gashi har ya shafi ƙanwarsa da yake tsananin so.
lokacin da ya saddaƙar shi da ƙanwarsa sun mutu, saboda hayaƙin da ya gauraye ɗakin da ba a iya ganin komai ta yanda wutar ta ƙara yawa saɓanin da kaɗan take ci tunda gefen labule ta kama, amma zuwa lokacin har ta kama katifa ƙauri yana tashi, ɗakin yayi duhu, shi kuma sai tari yake yi yana ta so yaja gadon Zaytuna amma ba zai iya ba.
a lokacin ne kuma hayaƙin ya fallasu acikin gidan, mai gadi yaje ya sanarwa da Hajiya Madina cewa wuta ta kama a ɓangaren Hajiya Ramla, kuma ya ga ta fita tun ɗazu ita kaɗai babu yaran. jin wannan batu yasa Hajiya Madina barin ɓangarenta a rikice ta yo ɓangaren Hajiya Ramla, ta shigo ɓangaren tana taƙwala kiran Your Excellency, sai taci karo da wayarta a kan dining.
wannan yasa Hajiya Madina ƙara hargitsewa ta haye sama da sauri, garin hawan ta zame ta faɗi, amma bata kula da faɗuwar ba ta tashi tana ɗingishi ta wuce direct zuwa ɗakin Hajiya Ramla, tana zuwa ta murɗa handle taji ƙofar a rufe, gashi tana gani daga ɗakin wutar ke ci, sai tabi ta rikice ta koma ƙasa ta kira me gadi tana daɗa tambayarsa ya tabbata yaga fitar Her Excellency, yace ya gani tun kusan minti biyar ma kenan, amma ba da yaran ta fita ba, kuma bama da mota ta fita ba.
Hajiya Madina ta ɗora hannu aka tana salati, suka dawo saman ita da me gadi, kuma suna zuwa suka jiyo kukan Turaki yana buga ƙofa yana cewa,"Mum please come and open us, please Mum, the fire is coming closer to us".
jiyo muryarsa yasa Hajiya Madina yin tangaltangal zata kife a ƙasa, tana duban me gadi tace,"my children are inside Malam Hamisu. innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, taimaka min Malam Hamisu ƙofar a rufe take". ta faɗa tana fashewa da matsanancin kuka tana kama handle tana jijjiga door ɗin.
Malam Hamisu ya murɗa handle ya tura ƙofar yana duddukanta amma taƙi buɗewa, sai daga baya tunanin ɗauko spare key ya zowa Hajiya Madina. ta kira me aikinta tace tayi gaggawar zuwa side ɗin Baffa ta ɗauko duka keys ɗin da ta gani acikin bedside drower, kuma cikin mintuna kaɗan sai gata ta kawo. Malam Hamisu ne ya iya buɗe ƙofar don ita ba zata iya ba saboda yanda jikinta ke rawa gaba ɗaya.
jin an danno ƙofa da ƙarfi hakan yasa Turaki ya tsorata, ya buɗe bakinsa ya kira sunan Mum da ƙarfi yana ƙara fashewa da kuka, sai yaji muryar Hajiya Madina saɓanin wacce yayi tsammani. ba zai iya tuna abinda ta dinƙa faɗa ba amma ba zai manta yanda ta dinga lalubensu ba acikin hayaƙin har ta gansa, tana zuwa ta janyo shi zasu fita sai ya tirje yana ce mata,"Maama Jaishuna".
tsananin firgicewa da rashin sanin inda kanta yake bama tasan me yake faɗa ba har suka fito daga ɗakin, tari ya sarƙe shi maganarsa ta maƙale, Hajiya Madina ta dinƙa jijjigasa har Allah yasa tarin ya tsaya.
kuma sai a sannan ta gane me yake cewa, lokacin da ta rungume shi tana kuka sosai, ya tureta a jikinsa yana nuna mata ɗakin yana cewa Baby Jaishuna. ta na fuskantar abinda ya faɗa ta kunce goyon dake bayanta wanda ta manta ma da shi, ta koma ɗakin a sukwane tana kurma ihu tana zabga salati. within a minutes sai gata ta fito tana janye da gadon Babyn, don sai da ta fito ta ɗauko Zaytuna acikin bed ɗinta wacce a lokacin numfashin jaririyar ma ya ɗauke gaba ɗaya saboda uban hayaƙin da ta zuƙa.
Malam Hamisu dake tsaye da yara a gabansa cikin ɗimauta yana dubanta ya ƙwala ƙara yana faɗin,"wuta a rigarki Hajiya".
taji sanda ya faɗi cewar wuta a rigarta, amma ba zata iya cewa ga yacca akayi ta cire rigar tayi wurgi da ita ba, domin hankalinta gaba ɗaya baya jikinta, yayi kan jaririyar yarinyar da ta gama saddaqarwa ta rasu, ta saddaqar da sun rasata, kuma banda Malam Hamisu ya lura da wutar ya ankarar da ita da sai dai wutar ta babbake su, duk da cewar wutar ɗan kama jikin rigar tata yayi, to sai Allah dai ya taƙaita komai yazo da sauƙi.
ganin Hajiya Madina ta rage daga ita sai rigar nono sai zanen jikinta, Malam Hamisu yaja yaran suka sauka zuwa ƙasa. itama ta sauko daga benen a ruɗe cikin tsananin tashin hankali tana salati tana kuka tana jijjiga Zaytuna.
bayan mintuna biyar sai ga fire service sunzo, motar su tayi parking a compound tare da motar Baffa, ya fito shima a matuƙar razane yana kallon yanda hayaqi ke fitowa ta window.
ya nufa me gadi da mugun tashin hankali yana tambayarsa ina iyalinsa, ganin Baffan yasa Turaki kamo hannun Khalil suka fito daga ɗakin me gadin da ya saka su aciki, a lokacin Khalil shekararsa biyu dan ko yayesa ma ba'ayi ba kasancewar baida cikakkiyar lafiya an haife shi a bakwaini.
ganin yaran Baffa yayi kansu da gudu ya ɗauke su, idanuwansa a warwarje yake tambayarsu ina Madina da Ramla, Turaki na kuka ya girgiza masa kai alaman bai sani ba shima. sai Malam Hamisu ne yake sanar masa ai babu jimawa Hajiya Madina ta fita a mota tayi asibiti da Zaytuna. kuma ya kamata abi bayanta gudun kar a sami mummunan haɗari dan hankalinta ba'a jikinta yake ba.
"Her Excellency fa?". Baffan ya tambaya da tsananin ruɗu bayan jin abinda Malam Hamisu ya faɗa masa. "ranka ya daɗe ita bata gidan, fitarta babu jimawa wutar ta tashi".
Baffa yaja yaransa yana cewa da Malam Hamisu,"ka ji da fire service ɗin nan, zan bi bayan Madina".
da faɗar haka ya shiga mota yaja suka bar gidan yabi bayan Hajiya Madina, yana driving ɗin yana bin hanya da kallo har ya iso asibiti, shima motarta ya gani a wajen asibitin sanda zai wuce, bai tunanin wannan asibitin tazo ba tunda ba shi suke zuwa ba.
Samun Hajiya Madina yayi a ward ɗin tayi dirshen a ƙasa sai kuka take yi, tana ganinsa ta miƙe tayi kansa tana nuna masa emergency room ɗin da jaririyar ke ciki, gaba ɗaya ma ta kasa magana sai jan nunfashi take yi tana masa nuni da hannu.
Jikin Baffa sai ya mutu zatonsa ko sun rasa yarinyar ne, ya nufi ƙofar emergency room ɗin yana leƙawa ta glass, likitoci ne kusan biyar akan yarinyar ana ƙoƙarin ganin an ceto ranta, duk da suna ganin da kamar wuya yarinyar ta rayu, wannan furucin nasu ne yasa tunda Hajiya Madina ta zube a ƙasa bata motsa ba tai dirshen tana ta kuka tana roƙon Allah.
kuma cikin hukuncin ubangiji sai gashi numfashin yarinyar ya dawo bayan an shafe rabin awa akanta ana ta saka mata wasu machines, duk da likitan ya faɗa musu the Baby is now alive amma hankalin Hajiya Madina bai kwanta ba, har sai da suka shiga room ɗin da akai admitting Babyn taga idonta biyu an saka mata robat oxygen a hancinta sai wutsil wutsil take sannan ta dawo cikin nutsuwarta.
tukunna hankalinta ya kwanta ta daina kukan da Baffa ya shafe rabin awa yana lallashinta bata ji ba, a sannan ne kuma zafin ciwon jikinta ya ratsata, tana dubawa taga ashe ta ƙone ne a bayan hannunta da kafaɗarta, sai kuma targaɗan da tayi a ƙafa garin hawa bene.
Hajiya Madina tasha wuya sosai da ƙonewar da tayi, ba za'a kira ƙonewar da ƙarama ba dan round tayi babba, dan bayan sunyi 1week a asibiti na kwanciyar da akai da Zaytuna sai da suka ƙara 1week saboda caɓewar da ƙunuwar tata tayi, ashe ƙarfin hali take tayi. saboda tashin hankalin da suka ƙara shiga na ɓatan Hajiya Ramla, babu inda ba'a duba ba babu Hajiya Ramla, haka babu cigiyar da ba'ayi ba within that 2weeks amma babu amo babu labarinta, wannan ne ya ƙara firgitar da Hajiya Madina ta ƙara fita hayyacinta gaba ɗaya, ta mance ma da wani abu ciwo dake jikinta balle xafinsa, dan idan ma tace zata bi ta kan ciwon tausayin Zaytuna da Turaki ba zai barta ba.
cikin wannan hali da suke ne na jimamin ɓatan Ramla kowa ya ƙara tabbatarwa da Alƙali Dikko yayi sa'ar mata a duniya, situation ɗin da Hajiya Madina ta shiga a silar ɓatan Hajiya Ramla ba zai faɗu ba, yanda kasan wacce uwarta ta mutu, abinci wannan bata ci sai an mata da gaske, kuka kuwa da ace ruwan hawaye na ƙarewa tuni nata ya jima da ƙarewa.
Hajiya Madina macece ta gari, me kyawun zuciya, wacce babu algus a tare da halinta, wacce take zaune da kowa lafiya take kuma nuna kowa nata ne, bata ƙyamar kowa kuma bata munafurta kowa, dan sau tari akan cewa da Hajiya Ramla matsalar kishiyarki ɗaya ne, bata iya munafurci ba. ita kanta Hajiya Ramla tasan tayi sa'ar abokiyar zama, abunda kowa ke faɗa mata kenan tunda aka auro Madina, shi yasa suke zaune lafiya babu fitina, babu faɗa balle tashin hankali, kansu a haɗe kamar waɗanda suka fito ciki guda.
tunda aka haifi Turaki Hajiya Madina ta mayar da shi kamar ɗan cikinta, idan ba sani kayi ba ba zaka taɓa cewa ba ita ta haife shi ba, an aurota dalilin rashin haihuwar Ramla, to kuma sai Allah ya nuna ikonsa ko da ta shigo gidan itama sai da ta shafe shekaru masu yawa bata ko yi ɓarin ciki ba, har Allah ya bawa Ramla ciki ta haifi 2wins maza, ranar suna yaran akasa musu sunansu Muhammad da Lateef, Muhammad shine aka saka masa sunan mahaifin Ramla suke kiransa da Turaki kamar yanda ake kiran mahaifin nata, shi kuma Lateef shine yaci sunan mahaifin Dikko zasu ke kiransa da Abi, to kuma a ranar sunan da daddare sai Lateef ɗin ya rasu.
sai da Muhammad Turaki ya shekara huɗu ciff a duniya sannan Hajiya Madina ta haifi nata yaron wanda yaci sunan mahaifinta Ibrahim suke kiransa Khalil, shekararsa biyu shima Ramla ta ƙara haihuwar ƴa mace me suna Zaytuna. part ɗin kowacce daban amma baka ganinsu ba'a tare ba, in kuwa ka gansu separately to dare ne yayi za'a tafi makwanci, amma da zarar safiya tayi sun tafi breakfast side ɗin Baffa, har sanda wani acikinsu zai yi baƙo, ko kuma idan Hajiya Ramla zata tafi office, idan wannan tayi ba daidai ba ɗaya zata gyarawa ƴar'uwarta kuma su amshi gyaran cikin sauƙin kai.
wucewar sati da watanni anata saka ran ganin ko Hajiya Ramla zata dawo amma shiru kake ji, da haka har aka shafe shekara guda, kuma a lokacinne aka sallama
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 73