take yi masa gani yake kamar tana masa kallon tuhuma ne, me yasa yazo nan?, me yasa ya biyota?, me yasa bai tambayi izininta ba?, ai tun kamin yazo ɗin sai daya shiryawa amsa waɗannan tambayoyin, ya kuma san zata yi masa rangwame ko da zata hukuntasa.
ya rumtse idanuwansa tare da ƙara riƙe hannunta sosai yana murzawa sannan yace,"kiyi haƙuri, na kasa ci gaba da jurewa shi yasa na biyo ki".
cikin sanyayyar murya tace,"hannuna".
sai taji yace,"ba kuma zan iya sa ki ba Halimatu, wallahi ba zan iya ba. dan Allah ki barni".
ba tare da ta ɗago kanta daga sunkuyen ba ta raba hannayen nasu, sannan tace,"me yasa to baka tambayeni ba kafin...".
bata ƙarasa ba ya katseta,"naga zan mutu shi yasa, kuma bana so na mutu ban mallakeki ba, ba kuma na so na mutu ba muyi sallama ba...ina ta son ganinki, ina ta so nayi magana dake, amma wannan aikin yabi ya toshe kowacce ƙofa, ita kuma zuciyata sai zafi take tana kukan rashinki, shisa yau nace babu abinda zai min shamaki da ganinki ko da ace fadar sarkin gombe kike aiki yau sai na shigeta na ganki, daga nan kuma nima sai na nemi taimakon a ɗaukeni aikin muke yi tare ina rage miki, ta yanda zanke samun ganinki ko da yaushe...nazo da complete takarduna, please kiyi min iso ko Allah zai sa a dace".
ta kalleshi tana murmushi, da gaske yake babu wasa a maganarsa neman aikin yazo. ta kalli takardun ta ƙara kallonsa tukunna tace,"ni babu takardun komai aka ɗauke ni".
yace,"arziƙin Kaka kika ci shine dalili".
ta juya idanu sannan tace,"ko da babu Kaka ni banga ana ɗaukan me wanke-wanke da shara da takardu ba".
yace,"kuma dama na iya wanke-wanke sosai ba".
ta saki dariya sosai tana ɗora bayan yatsunta akan bakinta. yana kallonta har yanzu fuskarsa bata gama saki ba yace,"dariya na baki?, Allah da gaske na iya wanke-wanke, kuma ki tambayi Inna kiji, idan na wanke kwano har ƙyalli yake ya dawo kamar sabo, kuma na tabbata na fiki iyawa...saboda haka nasan idan suka ɗaukeni a kwana ɗaya zasu bani ɗaki a gidan nan, wataƙila ma ke su kore ki, kuma dama haka nake so dan wallahi bana ƙaunar wannan aikin".
tayi wani murmushin tace,"kaga ni kuma ina sonsa, tunda da kuɗin muke rufawa kanmu asiri...yanzu haka ma Kaka ta kusa siya min ƙaramin fili da kuɗin da ake ajiyewa".
ya ɗan kauda kai gefe sannan ya dawo yana ƙara fuskantarta. "sau nawa kike aikin ruwa?". ta juya idanu sannan tace,"ummm ya danganta, ina wanke kwanuka kuma zanyi girki idan Adda Zaytuna bata yi ba, sannan kuma in wanke banɗaki 6, shikenan".
"shikenan!, wannan yawan aikin shi zaki kira da shikenan Halimatu?". ya maimaita kalmar da mamaki.
ta ɗaga gira,"eh, ai babu wahala tunda ba ɗauda suke yi ba, nan da nan nake kammalawa na tafi ɗaki na huta...saboda haka ka bar damuwa watarana sai labari".
yace,"balle ma kin kusa ki daina, very soon insha'Allahu...nayi mafarki na zama ɗangote".
ta waro ido tana kallonsa, ya ɗaga kai yace,"da gaske, wai na koma Ɗangoten Gombe, na aureki mun bar ƙasar gaba ɗaya, muka ajiye Inna da Kaka a saudia mu kuma muka wuce London Honeymoon".
tayi far da ido ta maimaita kalmar, "Honeymoon, kamar na taɓa jin wannan kalmar amma na manta aina".
"zaki ma santa ne lokacin da mukayi aure, Allah Halimatu na aureki da Uwar kuɗina a yawon shaƙatawa kawai zamu ƙare rayuwarmu, wani banzan aikin gida duk ba za kike yi ba".
tasa hannu cike da kunya ta rufe fuska,"ni fa yarinya ce nace ka daina faɗa min kalmar aure".
yay mata harar wasa yace,"kin manta ɗazu kika zo duniyar...ai na tabbata a karatun aure babu wanda ba ki sani ba sai dai ki raina min wayo, sai kace ba aminiyar Maijidda ba".
ta danne dariya tace,"me kake nufi da Maijiddan?". yace,"oho".
haka sukai ta hira ba tare da sun san lokaci ya tafi ba, Fillo sam ta manta ma a inda suke, sai da mai gadi ya ankarar dasu. cike da kunyar mai gadin ta bar wajen dan idan ta biye ta Amir ba zasu tafi haka ba, yana faɗa mata wai yau subscription zai yi.
bin ta yayi a baya yana ta murmushi, tsaye ya sameta a gate ɗin da zai shigar da kai ɓangaren ma'aikatan gidan, tana ta jan yatsun hannunta kamar yanda hakan yake sabonta ne.
ya jingina da ƙofa yana kallonta yace,"wai kuɗi kike lissafawa a jan yatsun nan ko me?".
idonta na ƙasa ta jinjina kai,"ehh kuɗin ɗangoten Gombe nake ƙirgawa".
yay murmushi yace,"Allah ya amsa". itama tace,"amin". sannan ta kalli yanayin garin da magriba ta ƙarato tace,"muyi Sallama su Hajiya na kan hanya, kuma akwai sauran aiki gabana".
yace,"aikin me?". tace,"Adda Samha ta bar min guga kuma tana da yawa, gata bata da sauƙi mafaɗaciya ce".
"barkono ce ita?". tace,"kafi barkono in kaji ana faɗa".
ya kalli agogonsa yaga har ƙarfe shida da minti goma, ya sauke numfashi sannan yace,"to sai yaushe?". daga yanda yay maganar sai yay mugun bata tausayi, itama ba dan tana so zasu yi sallamar ba, lokacin da bata fara aikin ba ai babu ruwanta da wani kallon lokaci, ko zasu kwana suna shan soyayyarsu babu mai katse su.
"kawai zance banda lafiya kaga zan huta ranar". ya ɗan zaro ido waje yace,"a'a bana so kiyi ƙaryar ciwo, kawai dai zan ƙara dawowa".
ya faɗa yana jan ɗan cif-cif ɗin gemunsa. "a'a ni kam ban yarda kazo ka ban kunya ba". ta faɗa tana kama gefen hijabinta.
yace,"ohh kina jin kunyar kar suga saurayinki ba ɗan gayu ba kuma talaka ko?, alhalin ke me kyau ce".
tayi saurin girgiza masa kai yanayin fuskarta na sauyawa,"ko kaɗan ba haka bane, dan Allah karka ƙara wannan tunanin Amir, ba zanji kunyar nunaka a koma ina ne ba wallahi, kai nake so ba gayunka ko kuɗinka ba, kuma so nake maka na tsakani da Allah". tayi naganar kamar zata yi kuka.
"bance ki zubar min da hawayenki ba, kin san suna da tsada...na faɗa ne dan na zolaya, kiyi haƙuri".
tai knodding kanta kawai, kamar ba zasu yi sallamar ba, sai da tayi da gaske tukunna sukai sallamar ta juya ta tafi, kuma tana cikin tafiyar ne ya dakatar da ita da tambayar me ya sami ƙafarta, dan a ɗazu bai lura ba sai yanzu. tace masa babu komai tsayuwar da sukai ne yasa ƙafar yin tsami, ba don ya yarda ba sai dan karya takura mata ya ƙyaleta.
sai bayan isha'i mutanen gidan suka dawo, bata ma san sun dawo ba saboda lokacin tana ɗakin ƴan aiki zaune cike da kewar Kakarta, yanza basa yini tare ko kaɗan, da dare yayi sai safiya ta taho aiki.
tayi zurfi cikin tunani taji wayar ɗakin na ƙara, tana ɗagawa taji muryar Zaytuna na cewa da ita,"kina ina ne?".
tace,"laa Adda kun dawo, banji ƙarar mota ba". Zaytuna tace,"to kizo". ta ajiye wayar ta miƙe tana jan ƙafar dan sam bata so a gane ciwon dake ƙafarta.
Boɗejo kawai ta samu a parlon, ta ƙarasa ta tsuguna ta gaisheta. sannan ta tashi zata hau upstairs, Boɗejo ta tsayar da ita.
"kinga ke ƴar nan zo kai min idon baturen nan nawa ɗakin kwana na". Fillo ta rissina ta karɓa, Boɗejo ta kalleta tace,"ke kuma zuwan yaushe?". tace,"ban jima ba". "Allah sarki, to sannu Allah yayi miki albarka". Fillo tace,"amin". Boɗejo tace,"to ɗakin nawa kin sa ni ne?". Fillo ta girgiza kai alamar a'a.
Boɗejo ta ɗora ƙafarta kan tumtum ɗin dake ƙasan carpet tace,"can ɓangaren ƙarshe nake kusa da su Turaki, nan suka wullani wallahi daga ni sai halina, kamar ba saurauniya ba ada".
ta jefa wata choculate a baki ta ƙara cewa,"ai da mijina shine sarkin garin nan, to daya rasu ne kuma ɗana Habibu ya hau kan kujerar...kin ganni kamar ban haɗa jini da sarauta ba ko?, wallah bata dameni ba in faɗa miki ƴar nan, banda ma dai Allah ya ƙaddara da hakan ai bata faru ba, shi yasa ko ƴar izzar nan ma ta masu sarauta banda ita, sha'anina kawai nake ba zan iya takura kaina ba wallahi, ina dalili. me gidan nan aini ya biyo, idan kika gansa ba kyace Yarima ba, shi dai Habib ɗin dama da kin gansa kinga wanda sarauta ke yawo a jininsa, aishi wannan Yaron na gidan nan yayo, umm Turaki ba wallahi kam...sauran yaran Ibrahimu da Samir za ki gansu kamar ƴaƴan tsintuwa".
Fillo dai murmushi take tayi, taji sosai tsohuwar ta burgeta. "ba kya magana ne?". Fillo ta girgiza kai tace,"a'a ina yi Hajiya". Boɗejo tace,"auyo ni fa nace ai da an banu...ba ki da magana dai ina ce ko?, dama ai ba kiyi kama da sauran ƴan aikin ba iyayen zuba kamar tsohuwar kanya, wallah na faɗa miki su nan suke zubewa su sakani gaba inta basu labarin masarauta wai suna so, ita surukar tawa tayi ta jin haushina, itama wannan ƴar Samha taita ɓata rai wai ita ba haka ƴan sarauta suke ba, to ni dai basu isheni kallo ba ma dan bana bi ta kansu, ina dalili ka takura kanka akan wata banzar aba sarauta".
Fillo tayi murmushi me sauti still dai bata ce komai ba, haka kawai taji tana so ta ɗauki lokaci tare da tsohuwar suna hira. sai yanzu Boɗejo ta bata glass ɗin dake cikin box ɗinsa tace,"idan kinje sai kin kunna fitilar ɗakin dan ba lallai bane an kunna min, tunda me ta'adin Sameer baya nan can muka baro shi gidan Hakimi...akan mudubi kawai zaki ɗora min shi kinji ki riƙe da kyau kar ya fashe, na huɗu kenan da Habib yasa akayo min shi daga dubai, da yake acan ake duba min lafiyar idon".
Fillo tace,"to Hajiya". Boɗejo tana kallonta sosai tace,"a'a wallahi sunana Rumana ko kuma kice min Boɗejo kamar yanda jikokina ke kirana. ina wani batun Hajiya anan salon dai a ƙarawa mutum jin kai, ai da Hajjah suke ce min, Mai Martaba na rasuwa na rufe ido nace ko Rumana ko wani sunan, to shine fa baturen yaron nan ɗan gidan sarki Habib ya saka min Boɗejo, da ike shi ne jikana na farko, kai izza acikin yaron nan kamar ba zai taka ƙasa ba".
tana faɗar baturen yaro Fillo ta gane Yarima Abbas take nufi. "kema ɗakin kwanan masu aikin kike?". ta girgiza kanta,"a'a wurin Kakata nake". "can da nisa ne kenan?". "a'a Boɗejo nan ɓangaren ma'aikata, nan muke da zama".
Boɗejo tace,"auyo ce min zaki tsaffin bayina ne ku, to ai shikenan dama ce nake nan kike kwana nace to kizo ɗakina mu kwan tare dan sosai na yaba da hankalinki wallahi".
Samha ta faɗo ɗakin rai ɓace, tana jifan Fillo da wani irin kallo tace,"ke dan Uwarki ina aikin da na saka ki?". maimakon bata amsa sai kallo da Fillo ta bita da shi, cikin ranta tana maimaita dan uwarki, kalmar da ta jima bata ji an faɗa mata ba.
"ba magana nake miki ba?".
Fillo ta rufe ido tana jin zuciyarta na suya sannan ta buɗe tace,"Adda Samha ai nayi". "kika yi a gidan uban wa?. bance miki acikin trolly za ki jerasu ba, gobe da asuba zan bar ƙasar". sai taja tsaki tace,"ni ba'a taɓa bagidajiyar ƴar aiki ba sai akanki wallahi, to minti uku na baki kije ki kammala shiryan kaya tun ban nuna miki other side of me ba".
a sanyaye Fillo tace,"kiyi haƙuri don Allah, zan gyara yanzu". ta faɗa tana barin parlon, guntun hawayen dake maƙale a idonta ya sauko, a rayuwar nan ko mene zaka yi mata kayi amma karka sako mahaifiyarta aciki, bata so, bata so ko kaɗan.
kuma ɗazun sha'afa tayi gaba ɗaya, ta gama gugar sai ta zuba cikin wadrobe tana ta sauri saboda ƙafarta da ke mata zafi, amma tana ta alla alla kafin su dawo taje ta gyara.
Boɗejo ta kalli Samha tace,"ki dai dinga bin duniya a hankali, ni wallahi duk kece me ɗaukan duniya da zafi su dai su Zaytuna basu ɗorawa kansu wannan masifar ba...yo Samha kuɗin ubanki ɗin me?, shi ya bawa kansa?, to in gaya miki nan da kika ganni kafin Babana ya zama wazirin Sarki kika ganmu sai kin tsartar da yawu, to amma yau fa?, matar wa na zama kuma yanzu uwar su wa na zama?, kuma wane irin matsayi na taka?...to wallah kaɗan daga cikin ikon Allah kiga ƴan aikin nan da kike narkawa uwar tsawa kullu yaumin sun lula sama ke kuma kina nan ƙasa".
"wallahi ba amin ba, wannan ai mugun baki ne Boɗejo". Samhan ta faɗa tana wucewa ta haye sama.
a bakin side ɗin su Turaki, Fillo tazo wucewa zuwa part ɗin Boɗejo, Khalil dake balcony a tsaye yana waya idonsa ya sauka akanta, ya lura da yanda take ta ɗingisa ƙafa tana tafiya da ƙyar.
ya sauke wayar daga kunnensa ya kalli adadin minutes ɗin, sannan yace,"please hold on 2minutes". daga haka ya aje wayar nan kan table ya fito.
"Fillo". kiran sunan nata ya dakatar da ita daga tafiyar, muryar Kalil taji, amma ko da ta juyo maimakon ta gansa sai taga Turaki na tunkaro inda ta ke.
*Please comment, Share and Vote pls.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_nace muku i love you ko na bar kayata?...kai aradu sai na faɗa ko me xaku yi sai dai kuyi😏, idan na faɗa sai na ruga da gudu yanda ba zaku iya kamani ba😝...nace ba *I LOVE YOU MY FANS* 🏃♀._
*15*
tunda taga Turaki ne ke tunkarota tayi ƙasa da kanta, ta shiga wasa da hannunta, haka kawai kuma sai ta tsinci kanta da mugun faɗuwar gaba, saboda haka a hankali ta shiga karanto innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, hasbunallahu wani'imal wakil.
_laifin me ta aikata?._ shine tambayar dake yawo acikin ranta, dan ita dai ta sa ni tsawon lokacin da ta ɗauka a gidan nan bai taɓa ambatar sunanta ba, to amma yau kiran nata na menene?.
tana cikin wannan saƙe-saƙen yazo ya wuce ta gefenta, ta ɗaga kai tabi bayansa da kallo tana ganinsa har ya shige part ɗin Boɗejo, sai a sannan ta sauke ajiyar zuciya me nauyi.
maganar Khalil da ta ƙaraji a gabanta ita tasa ta baro da kallonta daga entrance na boɗejo.
"ina za ki?". Khalil ɗin ya tambayeta yana kallon hannunta dake karkarwa tana ƙara damƙe box na glass din, ya lura kamar tana so ta hana hannuwan nata karkarwa ne amma hakan ya gagara.
tace,"Boɗejo ce ta aikeni ɗakinta zan ajiye mata idon baturenta".
Khalil yay murmushi yace,"kema ta koya miki idon bature kenan...to amma me ya samu ƙafarki?".
ta ɗan kallesa da mamaki amma sai ta kawar, bayan ta kalli ƙafartata tace da shi,"babu komai".
sai kawai ya jinjina kansa yace,"to shikenan tunda babu komai je aiken".
ya faɗa yana tsare ƙafafun nata da ido, sai ta tsaya bata tafin ba, ya ɗago ido yaga shi take kallo, da murmurshi ya ɗaga mata gira ɗaya yace,"ehen je ki mana". ya faɗa ba tare daya nuna mata so yake ya ƙureta ba.
ta juya zata tafi sai kuma ta ƙara juyowa ta kalle shi, ya ɗauke kansa yana kallon sama as in idonsa ba'a kanta yake ba. tana fara tafiya taji yace,"babu komai?, to shi wannan jan ƙafar na menene?, ko wani laƙanin ne nima a sammin?".
ba tare da ta juya ba ta girgiza masa kai bata ce komai ba, ta rumtse ido tana so ta ɗaga ƙafar ya ƙara cewa,"to jan ƙafa dai babu kyau, idan ma dai da kyau to kika ci gaba da janta ƙafarki faso zata yi ki rasa mijin aure, dan babu me kaiki gidansa kina yaga masa ledar ɗaki".
bata san lokacin da ta saki dariya ba, ta ɗan waigo tana kallonsa tace,"Hammah Khalil kana da ban dariya".
hannayensa a aljihu yace,"ke kuma kina da ban mamaki".
tace,"mamaki kuma?".
yace,"yes, banda haka ace mutum na ciwon ƙafa kuma yaƙi faɗa kuma a tambaya ya mu sa...to faɗa min, magani kike tsoro ko kuma allurar?".
ita kam bata san taya akai ya lura da ita ba tun farko, duk yanda ta dinga ɓoyewa ashe sai an iya ganewa. fuskarta tayi narai-narai kamar me shirin kuka, yana lure da ita da hakan, ya fiddo da hannunsa daga aljihun sannan yace,"je ki kai aiken kizo mu wuce asibiti". ta ɗago ido ta kallesa sai dai bai bata damar magana ba ya ƙara cewa,"ina jiranki a mota".
yana faɗin haka ya juya ya bar wajen, ita kuma ta juya ta ƙarasa part ɗin Boɗejon.
Khalil ya kira Hajiya Madina a waya ya sanar mata zancen ciwon ƙafar na Fillo wanda itama bata san da shi don tunda suka dawo bata ganta ba.
a parlon Boɗejo Fillo ta tarar da Turaki hakimce akan kujera ya zubawa tv dake kunne ido, kallo ɗaya zaka yi masa ka gane kallo kawai yake amma ba don yana fahimta ba, dan gaba ɗaya hankalinsa baya wurin.
tunda tayi masa kallo ɗaya bata ƙara ba, a iyakar wannan kallon ta gane cewar yana ɗauke da damuwa, wata damuwa da yake so ya rabu da ita.
dole ta gabansa zata wuce kafin taje bedroom ɗin Boɗejo, ta durƙusa a gabansa tace,"ina yini". bata sa ni ba ya amsa ko ba amsa ba, ta tashi ta bar wajen.
tana ajiye glass ɗin ta fito, zata fice daga parlon taji muryarsa yace,"ban ruwa".
sai kawai ta tsaya tana kallonsa da mamaki, anya kuwa da ita yake?, ba shine rannan yace ko ruwan goran da zai sha ba karta ƙara ɗora hannunta akai ba.
"ba kiji bane?". maganarsa ta katseta daga tunaninta, ta ɗago suka haɗa ido da shi, tayi saurin ɗauke nata ta nufi hanyar kitchen, lucky kawai tayi amma ba don tasan nan ne kitchen ɗin ba, har ta shiga kitchen ɗin tana jin idonsa akanta.
ta dawo ta ajiye masa ruwan akan table ɗin dake gabansa, har ya zuba ruwan ya sha bata miƙe daga tsugunawar da tayi ba, kamar wadda yace mata tayi ta zama karta ta shi.
ƙwayar idonta ta jima akan yatsan ƙafarsa, sai can ta ɗan ɗago kai ta kalle shi, yasha ruwan amma still cup ɗin na riƙe a hannunsa, idonsa a rufe, haka kuma ya kwantar da kansa jikin kujera ya tusa ɗayan hannunsa cikin sumarsa yana yamutsawa.
kawai sai taji tausayinsa na gaira babu dalili ya tsarga mata, ta jima tana kallonsa ba tare da saninsa ba sannan ta tashi ta fita daga parlon.
zata shiga ɓangaren Hajiya Madina fitilar mota ta hasketa, tasa hannu ta kare tana kanne ido. sai sannan ta tuna ma da maganar Khalil na zasu asibiti, ita kam ai ko me za'ai ba zata je asibitin nan ba. ai dama ta gama ayyukanta, wurin Kaka zata gudu wadda ba zata takurawa ciwonta ba, dan haka da sauri ta ɗau hanya zata tafi sai ga Hajiya Madina ta fito.
"au baku tafi ba?". Hajiya Madinan ta tambayeta tana tsareta da ido.
tace,"ehh Maama yanzu dai zan tafi, dama nazo zan miki sallama ne".
Hajiya Madina ta tsaya tana kallonta, kamin tai tambayar da zata mata sai ga Khalil ya ƙaraso wajen, yana zuwa yace,"ɗauko mayafinki".
kamar zatai kuka tace da shi,"Hamma Khalil ai naji sauƙi".
baice komai ba Hajiya Madina tace,"me ya samu ƙafar taki dama?".
idanuwanta suka yi narai-narai tace,"gurɗewa nayi ɗazu da zan sauko daga bene".
Hajiya Madina tace,"ki dinƙa kulawa Fillo, je ki shirya kuje ya kaiki asibiti, duk ƙanƙantar ciwo bama barinsa sai anga likita".
ba don tana so ba sai dan ba yarda zata yi, saboda bata son yi mata musu.
a mota ta sami Khalil na jiranta, ta buɗe baya ta shiga, nan ma sai shine ya buɗe mata don bata iya ba. ƙamshin cikin motar daya gauraye da sanyin ac ya bata da wani daɗi, ta buɗe ƙananun ƙofofin hancinta ta zuƙe ƙamshin tana jin wani sanyi a ranta.
Khalil nata bin waƙar turancin dake tashi a motar, ita dai tayi shiru sai bin titi take yi da ido tana kallon hanya, rabon da ta fito har ta manta, kullum suna wuri ɗaya idan ba wani taro za'ai a masarauta ba shine har da su ma'aikatan ake tafiya, Maijidda ma ta fita yawo itace Yami ke yawan aikenta, ita kam Kaka da ta aiketa ma gwara taje da kanta.
a harabar asibitin yayi parking, tayi ƙoƙarin ganin ta buɗe motar da kanta, ta fito sannan ya sakawa motar key. "idan munje ki faɗawa likitan harda ciwon baki na damunki".
ya faɗa da sigar zolaya, tai ƴar dariya bata ce komai ba, tabi bayansa zuwa cikin asibitin. wani babban likita ne ya dubata, sai dai tasha kuka sosai saboda matsa ƙafar da akayi, sunan Kaka kuwa ta kira yafi sau biyar.
a wani pharmacy Khalil ya tsaya ya siya magungunan da aka rubuta masu yawa harda allurai.
tunda suka ɗauko hanyar dawowa Fillo ke jin kanta na wani mugun sara mata, Khalil na kallon duk wani motsinta ta cikin mirrow, sai cije fuska take yi hawaye na sauka a saman kuncinta, bai ce mata komai ba don duk tunaninsa ko har yanzu kukan allurar ne.
ita kuwa kanta ke mata wani azababben ciwo, yayi mata nauyi kamar an ɗora dutse, ga shi sai take jin tsoron da bata san dalilinsa ba, ji take kamar ana tsoratata acikin kanta, kuma kamar kiranta ake ana tazo.
tasa hannu ta damƙe zanin jikinta, daidai lokacin da Khalil yayi parking a compound.
kusan tare suka fito daga motar, ya bata ledar drugs ɗin yana yi mata sannu. karɓa tayi tare da yi masa godiya sannan tayi masa sai da safe.
ɓangarensu ta wuce bata wani biya ta yiwa Hajiya Madina sallama ba, tana tafe tana haɗa hanya saboda ganinta dake neman ɗaukewa gaba ɗaya, a yanzu ta manta da ciwon dake ƙafarta, ta ciwon kan kawai take yi.
duk da uban hasken fitulu dake gauraye da harabar gidan amma ita wani duhu take gani na daban, ta damƙe kanta haka har ta kai ɗakinsu, kuma sai lokacin ne taji idonta ya washe, ta buɗi baki tai sallama cikin ɗakin.
jin yanda tayi sallamar Kaka ta kafe ƙofar ɗakin da ido har ta shigo, tabi ta da ido har ta nemi wuri ta zauna tana jefar da ledan tulin drugs ɗin. sannan ta ƙara fashewa da wani kukan.
Kaka ta katse lazimin da take yi tace,"ke Lafiya?". tayi shiru bata ce komai ba. Kaka ta ɗaga murya sosai,"kin san dai bana son shashanci ko Halimatu, menene ya faru?, wani kuskuren kika aikata?".
ta ɗago tare da girgiza kanta alamar a'a. Kaka tace,"to menene?, wadda kuka baya yi mata wahala". bata yi magana da baki ba sai nuni ta yiwa Kaka da ƙafarta.
Kaka ta kalli ƙafar da ta kumbura tace,"subhanallah garin ya?".
da ƙyar ta buɗi baki tace,"nazo saukowa a bene na gurɗe". Kaka ta kawo hannu zata taɓa tayi ƙara tana janye ƙafa tana cewa,"Kaka akwai zafi fa...yanzu ma daga asibiti muke sun ƙara karyani shine kika ga ta kumbura haka, saura kaɗan na mutu Kaka".
Kaka nayi mata wani kallo tace,"kice gata suka yi miki...to sannu sai ki daina kukan, ke idan ba'ai miki hakan ba kina zaton zuwa safiya za ki iya motsar kafar ne ma, Allahk dai ya sakawa Hajiya da alkhairi". sai sannan Kaka ta kai idonta kan ledar maganin da ta yasar can gefe, tace da ita,"ledar kuma ta mene?".
tana shaƙar majina tace,"wai magani ne". Kaka tace,"wai kuma haka za ki ta shansa ba har sanda Allah zai kawo miki sauƙi".
Fillo taiwa Kaka da maganin wani kallo ta wutsiyar ido, Kaka na ganin hakan ta miƙe ta ɗauka ledar tana faɗin,"jefar da magani a bola ai ba wahala yake miki ba, gwara na ɗauke nayi masa guri tun ba kisa anyi asarar kuɗi ba...dan na san kuɗi ne bana wasa ba aka kashe".
Kaka ta shige cikin ɗaki da ledar maganin dan yi musu wajen ɓuya. kuma tana shiga aka saki wata uwar tsawa a tsakiyar kan Fillo, ta buɗa baki zata yi adu'a da ihu sai taji ta kasa, ta ya zata kwatanta?, wani irin ciwo take ji acikin kanta da ba zai kwatantu ba, ita ɗaya tasan azabar da take ji, ga gefen cikinta ma da takeji kamar ana caccaka mata allurai.
kira kawai take ji acikin kanta, kira daga muryar da bata san ta ko waye ba, kuma muryar da bata taɓa ji ba. _"zo da nisa, maza zo da sauri"_. wannan kalmar ita ake ta faɗa mata, ta kai hannu ƙugunta ta damƙe wannan dunƙulallan asirin da ta ɗauko, kuma kamar wadda aka tsikara tayi zumbur ta miƙe ta fice daga ɗakin.
lokacin da Kaka ta fito daga ɗaki sai tayi tunanin ko ta shiga banɗaki ne, hakan yasa bata nemeta ba, har ta girgiza kai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 73