tafi da wayar kwa haɗu da shi acan. mu ba mutanen banza bane da sai da aka tsayar da maganar aure tsakaninku sannan ki nuna mana ba haka ba, ƙarya kike yi kinyi kaɗan".
Kaka tace,"ni dai kawai in har na isa dake to komai da ya faru tsakaninku ya wuce daga nan inda kike, in kuma ban isa dake ba zan gani. kuma insha'Allahu nima zan juya miki baya ata dalilin hakan, wallahi sai na nuna miki ban taɓa saninki ba, kallo wannan sai ya daina shiga tsakanina dake balle har ki samu ikon ci gaba da zama tare da ni".
jin furucin Kaka yasa Fillo ta dinƙa kallonta babu ko ƙifce, ji take ina ma ta haɗiyi zuciya ta mutu, anya ma Amir bai asirce mata Kaka ba?, ko da yake babban asirin da zakai wa mutane akan suƙi ganin bad side of you shine ka zama mutum na ƙwarai a idon duniya. ta tashi ba tare da tace komai ba tai fuuu ta fice daga ɗakin tana ƙara sakin kuka.
a ƙofar ɗakin taga Maijidda a tsaye tana hawaye, tai mata kallo ɗaya ta ɗauke kai tayi gaba abinta, Maijidda tabi bayanta tana kiranta, Fillo ta juyo a fusace tace da ita,"da kika iya zuwa kika faɗawa Yami na butulce masa why can't you ki faɗa mata shi irin wulaƙancin da yay min, why not ki faɗa mata ya kira ni da ƴar zina ko sa nuna masa kuskurensa, amma sai kika karesa kika bar laifin akaina ni ɗaya. babu komai, thank you for that, ko yanzu kin nuna min matsayina wurinki, kin nuna min ni ɗaya zan iya fighting akanki ba dai ke kiyi akaina ba".
Maijidda ta riƙo hannunta tana so tayi mata magana amma Fillo cikin ƙunar ran da take ji ta fizge tayi gaba abinta. Maijidda nace mata,"wallahi ni bancewa Yami komai ba, ita ta fuskanta da kanta shine ta ɗauko wayar ta kawo miki amma wallahi ni ko ɗaga wayar Amir ban ƙara yi ba tunda kika faɗa min abinda yay miki".
Fillo dai ko tsayawa bata yi ba balle ta tsaya sauraron abinda Maijidda ke faɗa, dan tuni ta toshe kunnenta daga jin abinda ma zata ce mata wanda bata ganin she can believe her.
har ta shiga parlon Hajiya Madina bata daina zubar da hawaye ba, da tarin tunani fal cikin ranta a game da Amir da kuma Kamal, mutumin da ta fara haɗuwa da shi lokacin da ta gudo daga gida, kuma mutumin da yace ba zai iya auren ƴar gaba da Fatiha ba.
ganin babu kowa a parlon kai tsaye kitchen ta wuce, tana shiga ta kunna tap ta wanke fuskarta acikin sink, jin motsi kamar an shigo kitchen ɗin tai saurin saita natsuwarta tana daɗa komar da hawayen dake ƙoƙarin sake sakkowa.
"menene Fillo?". taji muryar Hajiya Madina a bayanta, hakan yasa ta juyo da sauri tana durƙusawa ta gaida ita.
Hajiya Madina ta ƙarasa shigowa cikin kitchen ɗin, tace da ita ta miƙe. tana kallonta sosai tace,"kukan me kike?, wani abin aka yi miki?".
Fillo ta girgiza kai,"a'a Maama, kaina ne ke ciwo".
"kuma shine kike kuka haka, baki san zaki ƙarawa kanki ciwon ba ne?". tayi shiru bata ce komai ba.
Hajiya Madina tasa hannu ta taɓa kan nata sai taji zafi rau. "subhanallah, kin sha magani?".
ta girgiza kai tana so ta riƙe sabon kukan dake ƙoƙarin zuwa. "ya haka Fillo, banda abinki ba sai da lafiya ake yin komai ba, sai kisha magani kiyi kwanciyarki tunda ga Ɗausiyya. maza jeki bedroom ɗina akwai magani cikin drowern madubi, ki buɗe ki ɗauka sudrex ki sha. sai kije ki kwanta zuwa anjima".
tace,"tom na gode Maama". sai tasa hannu a gefen zanenta ta ciro key na mota. Hajiya Madina tasa hannu ta karɓa tana faɗin,"thank you very much". kan Fillo a ƙasa tace,"kiyi haƙuri ranar ban sami damar faɗa miki ba, naga idan nace sai nazo na faɗa miki before muyi taking any action zasu cimma burinsu ne, thats why na tafi ɗakin Hamman kai tsaye".
Hajiya Madina ta dinƙa kallon key ɗin babu ko kifta ido, cikin idonta haskowa take yi wai Turaki na driving ga babban mota yayo kansa kuma babu burkin da zai taka ya ƙwace, wanne kalar mummunan haɗari ne zai faru?, wataƙila shikenan rayuwar Turaki ta ƙare kenan kamar yanda suke so, ina alƙawarin kula da su data ɗauka?, tai saurin rumtse ido tana girgiza kanta da kawar da abinda ke cikin kanta.
ta dafa shoulder ɗin Fillo ta ƙara ce mata,"na gode, ina miki godiya da ƙoƙarinki wajen ganin rayuwar ɗana ta kuɓuta, insha'Allahu a wannan shekarar da ke za'a yi aikin hajji, ƙafata ƙafarki zuwa saudiya Fillo".
Fillo na kallon fingers ɗinta tace,"Na gode Maama Allah kuma ya amsa".
sai taji kawai Hajiya Madina ta janyota jikinta tayi mata side hug, tana jin ruwan hawayen da ya fito daga idonta ya sauka akan kafaɗarta. muryarta da rauni tace,"yanzu ba don ace Allah ya nufeki da jinsu ba shikenan komai da suka shirya sai ya faru ko?".
Fillo dai tayi shiru bata ce komai, illa iyaka tsananin tausayin Hajiya Madina dake acikin ranta. ta janye a jikin Maama tasa gefen mayafinta ta goge mata fuska tace,"please Maama stop crying, adu'a kawai zaki ci gaba da yi, Allah ya ƙara kare Hammah su kuma Allah ya shirye su".
Maama tace,"insha'Allahu, je ki sha maganin. hope kinci abinci?". tace,"zanci yanzu sai na sha maganin". Maama tace,"akwai sauran breakfast a dining, ki ɗiba ki wuce da shi ɗakina sai kici acan, ki tabbata fa kinsha maganin".
Fillo bata wuce ba ta sunkuyar da kanta tana wasa da gefen mayafinta, Hajiya Madina ta fahimci tana so tayi magana, hakan yasa ta kamo hannunta tace,"do you have something to say?". ta ɗaga kai tace,"ehh Maama, dama ce zanyi hope ba wanda ya san zaiyi tafiya?".
da mamaki Hajiya Madina ke kallonta, ai tayi zaton daga ita sai Bello suka san da batun tafiyar Turaki Hong kong. kan tai magana Fillo tace,"dama naji yana waya da Hammah Bello ne akan tafiyar". Maama tace,"ehh babu wanda ya sa ni, na kuma hana Khalil yay maganan ma if muna tare. je ki sha maganin bana son ciwonki".
Fillo ta fito a kitchen ɗin, Hajiya Madina tabi bayanta da kallo, tana ƙara jin yarinyar na shiga can cikin ranta.
a dining Fillo ta zuba chips da awara da souce, ta hau sama ta ɗauko maganin sannan ta dawo ta ɗauka abincin da wuce ɗakinsu, kamin ta fito Khalil da ta samu a parlo yana kallo yana ta tsokanarta da acici. kaɗan ta samu taci abincin saboda bakinta da take jin babu taste, tana shan magani ta kwanta a wurin, ko da teacher ɗinsu yazo ma bata samu ta iya zuwa ba, Ɗausiyya na tashinta tace ta faɗa masa bata da lafiya.
bata tashi ba sai 12, shima ƙarar wayar ɗakinsu ce ta tasheta. daga ɓangaren Nihal tace da ita,"Fillo please if you are not doing anything zo ki taimaka min da gyara closet ena".
Fillo tace,"toh". ta ajiye wayar ta shiga toilet ta wanko fuskarta sannan ta fito ta wuce.
tana shiga parlo ta tarar da Zaytuna zaune, sai taji gaba ɗaya ta kasa ɗaga ƙafarta saboda azaban kunyar Zaytuna ɗin. sim sim kanta a ƙasa ta ƙarasa shiga ta durƙusa har ƙasa ta gaida Zaytuna.
Zaytuna dai data san komai kuma ta fahimci komai sai tayi murmushi sannan ta amsa gaisuwar. tace da ita,"sai yanzu kika shigo?".
still kanta na ƙasa tace,"na shigo tun safe, Maama tace na kwanta saboda kaina dake ciwo".
"ayyah Allah ya sauƙe, ko ayi allura?".
cikin azama Fillo ta miƙe tayi upstairs bayan tace,"a'a na warke".
Zaytuna ta rakata dariya, ta jima bata ga me tsoron Allura kamarta ba, duk zafin ciwo aka ambaci allura sai tai firgigita ta taashi wai ta warke, ko da ace ciwon cinta yake.
a ɗakin Neehal tare suka gyara kayan closet ɗin, Nihal sai labari taketa bata, mostly duk akan school ne wanda hakan ke ƙarawa Fillo jin kwaɗayin tayi karatu sosai, har itama ta kai matakin university, dama Maama tayi mata alƙawarin indai lesson teacher ɗinsu ya bada good perfomance akanta to zata zana private waec, in yaso idan zata je malasia course na phd nata sai su tafi tare, wanda hakan ya ƙara mata ƙaunar Hajiya Madina.
sosai Nihal ke burgeta saboda sauƙin kanta, ita da Khalil sune kaɗai suka yo halin mahaifiyarsu.
after azhar Fillo na parlon Boɗejo tana yi mata tausa, Boɗejo sai labarai take yi mata kala-kala. kuma labarin sosai yake yi mata daɗi, wani wurin tayi dariya wani wurin kuma tai murmushi, wani wurin kuma ta jinjina irin tuggu da ke cikin gidan sarauta, cikin ranta tana godiya ga Allah da yasa bata da haɗi da sarauta.
can sai taji Boɗejo tayi shiru, ta ɗago kai ta kalleta, sai taga hanyar bedroom ɗinta take kallo, Fillo ta waiga taga Turaki ne ya wuce, gabanta taji ya faɗi, da sauri ta juyo tana ci gaba da matsawa Boɗejo ƙafarta, fatanta ɗaya Allah ya kawo abunda zai tasar da ita daga wurin nan yanzu, kuma Allah yasa kar Boɗejo tace zata aiketa ɗakin nata, dan sam bata so ta haɗu da Turaki.
Boɗejo tace,"ina faɗa miki to haka ake yi fa idan biki ya tashi, in kika ga yanda ake kashe kuɗi sai kiyi zaton ko ba'a san ciwonsu ba ne. to da yake al'adar gidan sarauta ce hakan, indai za'a yiwa Yarima aure ko kuma Gimbiya to zaki ga yarda ake ɓarin kuɗi kyace ba'a talauci a nigeria, musamman ma ace bikin sarauta da sarauta ce ta haɗu, to ina faɗa miki in aka tashi kai lefe hatta bayin gidan sai an yi musu sutturu an kuma basu kuɗaɗe. kinga lokacin bikina dangin Mamana sai da suka dinƙa cewa ko dai siyar da ni akayi. yanzu dai ai zaki ganewa idonki tunda muna tare, in bikin Ilham ya tashi uban kayan da zaki samu sai kinsha mamaki, har sai kin kyautar kema".
tun farkon fara labarin Fillo batai magana ba, har Boɗejo ke cewa ko tana ciwon baki ne, amma haka kawai da taji ta ambaci sunan Ilham sai ta sami kanta da tambayar,"Boɗejo wacece Ilham?".
Boɗejo tace,"kul Gimbiya za ki ce, ita ɗin ai ƴar me martaba ce, yanzu in a gaban fadawa kika faɗi sunanta haka gatsal ai kin shiga uku, ƙila ma Fulani tasa a ɗaureki...ita aka sakawa sunana ai shiyasa nake masifar sonta, baki taɓa ganinta ba?".
tace,"ban ma taɓa jin sunanta ba".
Boɗejo tace,"kika ce kuma shekararku biyu a masarauta kafin a ƴanta ku ayo nan da ku...ko da yake zai yiwu ɗin ki kasa saninta, tunda uban ita kaɗai ce baya so, tun tana ƙarama ya kaita can ƙasar arna bata dawo ba sai da ta shekara biyar".
Fillo tai shiru ita dai ƙirjinta sai bugawa yake haka ɗaya babu gaira babu daɗi, wayar Yami dake soke a gefen zanenta tayi ƙara, tai banza da kiran har ya katse, lokaci ɗaya taji sabon ɗaci da ɓacin rai a zuciyarta. sanda kira na biyu ke ƙara shigowa sai taji kamar ta rotsa wayar, Boɗejo dai nata zuba labari tausar ƙafa yayi mata daɗi.
can dai ta gaji tana kallon Fillo tace,"ki ɗaga wayarki mana, anata kira kin sha re, yanzu fa idan samuwa ce shikenan kin yiwa kanki. haba ƙila ma ba lafiya ba tunda kika ga kiran yayi yawa haka, kusan sau shida fa ina jin ma ko bakwai".
Fillo ta ciro wayar hawaye na sakko mata, tabi sunan Amir dake jikin screen da kallo. maganar Kaka ta ɗazu ta haska acikin kanta,_"ni dai kawai in har na isa dake to komai da ya faru tsakaninku ya wuce daga nan inda kike, in kuma ban isa dake ba zan gani. kuma insha'Allahu nima zan juya miki baya ata dalilin hakan, wallahi sai na nuna miki ban taɓa saninki ba, kallo wannan sai ya daina shiga tsakanina dake balle har ki samu ikon ci gaba da zama tare da ni"._
ba don waɗannan maganganun da Kaka ta faɗa mata ba, da idan ta ƙara sauraron Amir a rayuwarta shegiya ta ke, ai me zuciya akewa gori ba mai dukiya ba.
tana ɗaga wayar ba tare da ta amsa sallamarsa ba tace,"ba ta gate ɗin ɓangarenmu ba, main gate na gidan". tana faɗar hakan ta kashe wayar ta cillar tana ɓata fuska.
ta yunƙura zata tashi tana cewa da Boɗejo,"zanje Yayana ne yazo yana ƙofar gida".
Murmushi ya sauka a fuskar Boɗejo tace,"Allah sarki, to gaida shi dan Allah. ki buɗe friedge ki tafi masa da fura tana cikin gora, jiya Nihal ta dama min ita da daddare, akwai inibi ma duk ki haɗa masa da shi, ko kuma zaki shigo da shi ciki ne?, ko can ɓangarenku ɗin zai je?, a'a kinga ma kawai shigo da shi nan ɗin mu gaisa, yanda kike da mutumci ai dole a mutunta baƙonki".
ta girgiza kai tace,"a'a Boɗejo sauri ma yake ai, ba zai shigo ba na sani".
Boɗejo tace,"to ɗaukar masa abin sawa a baki ki kai masa, ba kyaje haka ba gaskiya hannu na dukan cinya".
ba yanda Fillo ta iya haka dole ta ɗauka Furan da inibi saboda takurawan da Boɗejo tayi mata, amma tana fitowa ta bawa me gadi, dan da dai ta bawa Amir gwara ta zubar a kwata, hakan kuma babu kyau.
ta jima tsaye bakin ƙofar gate ɗin kamin tasa ƙafa ta fita saboda bala'in zafin da zuciyarta keyi mata, dole ta fara controlling kanta kamin ta fita.
daga can ƙarshen katangan gidan ta hangosa tsaye jingina akan machine, ta tsaya taƙi ƙarasawa wajen sai shi ya ƙaraso inda take. bata jin zata iya ɗaga ido ta kallesa hakan yasa yana kusantota ta rufe ido da hannunta tana ƙara yin ƙasa da kanta.
Amir na ƙarasowa gabanta sai ya zube a gabanta yana sa dukkan gwiwoyinsa a ƙasa, ya haɗa hannayensa wuri guda alamar roƙo, cikin muryar dake bayyana dana sani da ɗumbin nadama yace,"dan darajar Allah da manzonsa kiyi haƙuri ki yafe min abinda nayi miki, nasan nayi kuskure kuma na karɓi hukuncin da kika min. amma horarwa ta isa haka, da nisanta ni da kanki da kike wallahi tallahi gwara kice na kwanta a akan titi mota tabi ta kaina, and am giving you full assuarance of zanyi hakan domin ba zan iya ci gaba da rayuwa babu ke a tare da ni ba...i know halina ba zai sa ki yafe min ba, but ki ji tausayin Uwar da ta mallaki ɗa guda ɗaya, wannan ɗan nata kuma ya kamu da son mace guda ɗaya, wanda son nata zai iya zama ajalinsa, ita kuma uwar bata so ta rasa ɗanta, ki kwatanta yanda wannan uwar dake son ɗanta zata ji in har ta rasa shi...kiyi haƙuri, kiyi haƙuri, dan Allah da Annabinsa Halima".
kuka ya kubcewa Fillo, ta sauke hannunta daga fuskarta, ta buɗe idonta a hankali tana sauke su akan Amir, da tsananin mamaki ta ɗan ja da baya saboda ganinsa durƙushe a gabanta yana hawaye, kallonsa take sosai tana ganin yanda hawaye ke sauka kamar an kunna famfo.
bata san sanda tace,"na fa yafe maka". ta faɗa tana turning around gudun kar wani ya gansu.
Amir bai motsa ba still duka gwiwoyinsa na ƙasa yana hawayen so, jin zuciyarsa yake kamar zata faso ƙirjinsa, anya zai iya ci gaba da rayuwa babu Fillo?.
tana kallon gefe tace,"ka tashi kar wani yazo ya ganka".
acikin muryar da ta jiƙu a maye na so yace,"mene aciki dan wani yazo ya ganni durƙushe a gaban wacce nake ƙauna duk duniya bayan uwata?, ko ban miki laifi ba ni me zube gwiwoyina gabanki ne balle kuma na aikata laifi. Halimatuna ba zan taɓa miƙewa daga nan ba har sai kin dubi hawayena, ko da zaki shiga gida ki barni haka".
Fillo ta ƙara waigawa ko'ina bata ga kowa ba, muryarta a ƙasa tace,"Amir na haƙura, in ban haƙura babu abinda zai fito da ni wajenka".
ya ɗago da sauri yana kallonta, yana ganin yacca hawaye ke sunturi akan kumatunta, sai yaji zuciyarsa ta ƙuntata sosai, yaji wani mugun sonta ya ƙara kamasa, ji yake ina ma there is chance ɗin da zai iya hugging nata da yayi hakan, sai dai babu wannan damar, but he will use another chance yaga ya tsayar da zubar hawayen, to make sure ya goge wannan dattin baƙin cikin da ya haddasa mata.
dan haka sai ya dinƙa jan gwiwoyinsa akan ƙasar wanjen har zuwa gabanta, yasa hannu ya riƙe siraran ƙafafunta da suka shige cikin tafin hannunsa, yace,"kiyi haƙuri don Allah, na tuba ba zan ƙara aikata kuskure makamancin haka ba".
a hankali tace,"Amir na haƙura fa". ya girgiza kansa da cewar,"zubar hawayenki na shaida min baki haƙura ba, kuma baki yafe min ba, kiyi min rai ki daina bari hawayenki na zuba a ƙasa, wallahi tallahi ina jin kamar za'a zare raina ne".
tasa hannu ta goge hawayenta tace,"na haƙura Allah kuwa". ya miƙe yana murmushi, suka haɗa ido tana jin kamar ba zata iya sakin nata murmushin ba, sai dai kuma ƙwayar idonsa da ta shiga cikin tata ta dagargaza alwashinta, taji ba zata iya yi masa komai ba, dan haka ta sakar masa sanyayyan smiling ɗin da sai da Amir ya nemi bango ya dafe.
tai masa harar wasa tana faɗin,"duk ka wahalar da ni".
ya kafeta da ido murmushin kan leɓensa yaƙi ɗaukewa, ya bar jikin bangon ya matso kusa da ita sosai har tana jiyo numfashinsa da bugawar zuciyarsa, yay ƙasa da murya sosai saitin kunnenta yace,"please can i hug you?, just a little, don't say no plsss".
da sauri Fillo ta ɗago kanta ta kallesa, taga yanda idanuwansa suka sauya kala, tai saurin juya masa baya tana jin wani irin kunya na rufeta. ganin zata gudu yay saurin riƙo hannunta ya janyota yace,"in baki juyo ba da gaske zanyi hugging na...". ai bai ƙarasa ba ta juyo da sauri tana kulle idanuwanta.
rufe idon nata kuma ya bawa Amir damar ƙare mata kallo tas, ji yake kamar ya ɗora lips ɗinsa a nata, kamar ya tsaga ƙirjinsa ya ɓoyeta aciki, kamar a barsa daga shi sai ita a wannan duniyar, he can't even imagine kalar soyayya da tarairayan da zai nuna mata idan suka yi aure.
a hankali yace,"buɗe idonki ki faɗa min ni dake wa yafi wani wahala da har kike faɗin duk na wahalar da ke".
cike da kunya ta buɗe ido tana tura baki gaba tace,"ka sakar min hannu a waje fa muke".
ya ɗaga shoulders ɗinsa yace,"and so?, hannun matar fa da zan aura na riƙe shi kuma munafiki ina ruwansa?...kinga bar batun ma na sakar miki hannu dan ba zan iya ba, watanni bakwai ɗin dana ɗauka bana tare dake Allah ɗaya yasan baƙar wuyar dana sha, dube ni fa kiga yanda duk na fige na lalace, duk wanda ya ganni ya ga wanda yay jinya ba ƙarama ba, cin abinci da ƙyar bacci kuma sai ɓarawo. but you". ya faɗa yana sa ɗayan hannunsa ya ɗago fuskarta,"hankalinki kwance har da wani kumatu kinyi, kinyi haske abinki alamun baki da wata matsala balle damuwa. lallai yau na yarda ni ɗaya nake kiɗa da rawata, Allah sarki ni Amir ashe son maso wani nake yi".
Fillo ta kauda fuska gefe tace,"ai kaima kasan abinda kayi min baka kyauta ba, da farko na rame sosai saboda jin ciwon abinda kayi min, amma da na cireka daga raina gaba ɗaya sai na sami salama, in yi baccina hankali kwance ba tunaninka balle na damu. kuma ni ka sakeni kar wani ya ganmu, this is not a privacy place".
Amir ya ware idonsa sosai akanta yana kallonta da mamaki yace,"Halimatuna am i hearing well?, english fa naji kina yi".
ta juya ƙwayar idonta tace,"da ka barni ai ba wulaƙanta nayi ba, yanzu haka lesson teacher na bai jima da tafiya ba".
mood ɗin Amir ya sauya, yana niyyar fizgota jikinsa ta cije tana ƙwacewa daga hannunsa har sai daya saketa.
ta bisa da kallon sauyawar mood ɗinsa tace,"lafiya?". without looking at her yace,"please and please, i beg you for the sake of Allah, let by gone be by gone. bana son tuna baya, karki ƙara cewa na tafi na barki, if not kuma Allah zan miki tafiya me gaba ɗaya, dan zanje na tunkuri mota gaba da gaba tabi ta kaina".
tayi far da ido tana haɗe hannayenta a ƙirjinta tace,"tom ba zan ƙara ba insha'Allah. am sorry, ina Innah?".
ya ɗan kalleta yay mata harar wasa, harar da tasa Fillo ƙyalƙyalewa da dariya sosai wanda duka haƙoranta na gaba sai da suka bayyana.
cikin nishaɗin da take jin kanta aciki tace,"ɗan ƙara yi na gani". fuskarsa na washewa da dariya ya kai yatsansa zai ɗalli fuskarta tayi saurin kauda fuska still tana dariya.
Amir yay ƙwafa yace,"zaki bayani, nima sai na rama kukan da kika sa na dinƙa yiwa Innah". ya sauke numfashi yace,"Innah na gaida ki, ƙila gobe tazo ko jibi, zasu zo da kayan sa ranarki. Halimatu nan da next 2months nake so na mallakeki matsayin matata. na sami aiki a wata makaranta yanzu haka ni ne Director a school en, last month ma na saya wancan machine ɗin da kike gani".
tace,"wow congratulations". yanda ta faɗa kace wata baturiyar gaske, kawai sai ya waigo yana kallonta da burgewa da sha'awa. yace,"Halimatu yanda kike da kyau da burgewa haka komai naki yake, kinji ko in kika yi english kamar a bakinki aka yisa, ina irin americans ɗin nan na cikin tv masu news?, wallah fa kamar haka, taya hakan ya kasance?".
ta basa labarin komai tare da cewan,"kuma Adda Zaytuna da Maama ma totally bama hausa da su yanzu, wurin da nayi mistake zasu gyara min".
Amir yace,"masha'Allah, Allah sakama mutanen gidan nan da alkhairi, but".
tace,"but what?". ta tambayesa ƙwayar idonsa na shaida mata kishin dake ransa, tai murmushi tace,"teacher ɗin ma fa inyamuri ne, duk ya zama jagwal, shi ko kallo ma bai da shi".
ya lakuce mata kumatu yace,"time ɗin da zai kalle ki ai ba sani zaki yi ba. gwarama muyi auren ni naci gaba da koya miki".
ta ware ido,"Maama ai tace zan zana waec na wuce UNI".
ya fincikota gabansa yace,"UNI ɗin da zaki je ta wuce gidana".
sai da suka kusa 1hour tsaye a wajen suna hira kafin hankalin Fillo ya dawo jikinta, don gaba ɗaya Amir yayi amfani da salon soyayyarsa ya kawar da duk wani fushi da take yi akansa, kuma ita kanta bata san sanda salon soyayyar ya ɗebeta ba ta manta da komai, har ta sake da shi suka koma kamar ba suyi faɗa ba.
tana leƙen agogon hannunsa tace,"Amir time, tausa fa nake ma Boɗejo na taso. kuma haka nace yanzu zaka tafi, ni duk naji ma ina jin kunya dan wannan tsohuwar sai ta ɓaro ni".
yay murmushi me sanyi yace,"shikenan ki koma ciki, amma zan dawo da daddare bayan kin koma aiki, ban gaji da ganinki ba gaskiya".
su kai sallama zai tafi yace,"i love you so much Halee". tace,"thank you, bye bye. ka gaida Inna". ta faɗa tana juyawa don barin wajen.
ai da sauri ya riƙo hannunta ya koma gabanta yana faɗin,"Allah sai kin faɗa".
ta shagwaɓe fuska tana cewa,"zan faɗa but not now, not 2day". yace,"ai kinji na rantse". sai da ta kulle idonta tukunna ta iya cewa,"i love you too". ta faɗa Amir na jin wani mugun daɗi acikin ransa, ya kama hancinta ya ɗan ja sannan ya saki hannunta asking her me take so ya taho mata da shi anjima, tace duk abinda yaga ya dace da ita.
ya juya ya tafi yana ɗaga mata hannu, itama cike da kunya take ɗaga nata.
sai da ya hau machine ɗinsa ya tafi sannan ta nufi gate.
daga Amir har Fillo cikinsu babu wanda ya lura da motar da tai parking daga can gefensu, tun fara hirarsu ba jimawa, haka yanzu ma da ta zo shiga gidan bata kula da motar ba, so tana zira ƙafarta cikin gate taji an mugun danna horn kamar za'a tashi duniya, ta juyo a tsorace tana kallon bayanta.
ba tare da gama tantance motar waye ba ƙarar horn ya kuma shiga kunnenta tana jin kamar dodon kunnen zai mutu.
ta ɗan yatsine fuska tana shigewarta tunda ba huruminta bane na me gadi ne, bata taɓa ganin kalar motar ba acikin gidan balle tace ta gidan ce.
ta shige da saurinta, kiciɓis suka yi da mai gadi ya fito daga banɗaki riƙe da buta a hannunsa sai sauri yake yi. yace,"ƴar nan Allah sa ba Alhaji bane".
Fillo tace,"wallah ban sani ba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 73