da taimakon da Hajiya Madina tace zata yi mata akan ta shiga jikin Samha ta dinga yawan bibiyar al'amuranta dan ta dinƙa jiyo mata plans ɗinsu akan Turaki. wannan dalilin yasa tace ta dage ta iya turanci saboda Samha bata fiya magana da hausa ba ko fulatanci sai dai english.
kuma ba tare da dogon nazari ba kai tsaye abinda Ummi tace mata shine,"duk abinda yaranta suka aikata laifinta ne, domin babbar illar da zaka yiwa kanka shine ka nuna banbanci a tsakanin ƴaƴanka, ka nuna soyayyar wancan tafi ta wannan a gareka, ka kasa ɓoye musu yanda kake jin matsayin kowannensu a zuciyarka, tabbas idan zuciyar wani ta ɗauka ta wani ba zata ɗauka ba, nuna banbanci tsakanin ƴaƴa kan haifar da matsala sosai, domin zuciyar wasu zata yi ƙoƙarin ganin yanda za ai su kauda wanda ake so ko kuma su illata shi".
Ummin tace mata,"dan haka yanzu shawara ɗaya da zaki bata tunda suma Allah yasa mahaifiyarsu ta dawo, to ta maida hankalinta kan waɗannan yaran masu raunin zuciya, karta ce zata fasa yiwa su Turakin abinda take musu dan hakan zai iya kawo gurɓataccen tunani a zuciyar mutane, ta mayar da son yaranta equal to yanda take son su Turakin, shine kawai samun kwanciyar hankalinta".
*Vote, Comment, and share.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*39*
*08:30am.*
acikin bedroom ɗin na Baffa, Hajiya Ramla ce tsaye gaban mirror ita da shi, sanye take da shadda golden colour tasha azababben aiki ajiki, anyi mata ɗinki bubun sai ƙyallin stones take yi, tayi masifar kyau kamar balarabiyar usuli, ita da Baffan iri ɗaya sak.
daren jiya tailor ya kawo musu ɗinkin su uku iri ɗaya, ita take taimakawa Baffa wajen shirin da yake yi, tana shirya shi ɗin suna hira cikin annashuwa da jin daɗi tare da alfaharin ƙara kasancewa da junansu.
turare ta ɗauka ta fesshe shi da shi tuni kuwa ɗakin ya ɗauka da wani daddaɗan ƙamshi, Baffa ya rungumeta jikinsa yana faɗa mata irin son da yake mata da kuma kewarta da yay a sanda bata tare da su, albarka kawai yake zunduma mata kamar yawun bakinsa zai ƙare.
wayarsa tayi ƙara ta zame daga jikinsa tai saurin isa kan gado ta ɗauko wayar, sai da tayi picking tukunna ta kara masa a kunne.
daga can ɓangaren Boɗejo tayi sallama suka gaisa da Baffa, tana kuka ta-ke shaida masa halin da Fulani Azima ke ciki, shi kansa Baffa da ya dawo a jiya jikinsa yayi matuƙar sanyi ya kuma tsorata ainun da yanda ya sami Fulani Azima, ya ƙara jin tsoron Allah da kuma tsoron sharrin duniya, saboda yanda ta dawo kamar ƙwarangwal halittarta dai babu kyan gani a yanzu, har ƙwalla sai da yay musamman da ya fahimci tana so tayi magana da shi, to amma shi har ga Allah ba zai iya bata wannan damar ba saboda ba zai iya zaman kusa da ita ba dalilin mugun ɗoyin da take yi, mijinta kansa sai ta window yake ganinta balle kuma shi, yana ji ma ana batun dawo da ita gida saboda su kansu asibitin sunce ba zasu iya da ita ba.
cikin sigar kwantar da hankali Baffa yace da Boɗejo,"kiyi haƙuri, adu'a zamu cigaba da mata Allah ya bata lafiya".
ta ƙara sautin kukanta tana faɗin,"Dikko ni ƴarta nake tausayi, a jiya yarinyar nan Ilham tayi suma yafi biyar, ko abinci bata iya ci Dikko, aljanun da bamu santa da su ba sai tashi suke, yau baka ga yanda suka farfasa mata jiki ba". ta faɗa tana kuka sosai.
Hajiya Ramla dake jiyo komai ta sauke numfashi tana jinjina al'amarin sakayya, ita dama tun can bata da niyyar tonawa Fulani Azima asiri akan abinda tayi mata, abunda zuciyarta ta yanke mata kawai shine zata barta da Allah sai kuma sun haɗu acan lahira, amma anan dai ba zata taɓa faɗar cewa ga wacca tai silar barinta gida ba, duk da cewar tunda ta dawo ta bada labari kowa ke cewa aikin asiri ne, to amma ko kusa bata yarda ta bar hakan a zuciyar mutane ba, duk da Hajiya Madina taso ta ɓaro komai ɗin dan har sunan Fulani Azima sai da ta ambata tana cewa wallahi sai taci ubanta zata kawo ƙarshen makircin matar, to da ƙyar dai ta tausheta ta bar maganar.
Boɗejo na kukan sosai tace,"Dikko ka bawa Ramla wayar ina so nayi magana da ita".
"tom shikenan, amma ki daina kukan hakan dan Allah".
tace,"Dikko ina ni ina daina kuka kuwa yanzu, ai ni da barin hawaye har sai Azima ta mutu, amma indai zanke ganinta a wannan halin hankalina ba zai kwanta ba kamar yanda hawayena ba zasu tsaya ba, wallahi ma ni daka ganni na yafe mata duk wani kalar rashin kyautawa da tayi min".
Baffa ya miƙawa Hajiya Ramla wayar, suka gaisa da Boɗejo, tai ƙasa da murya tana cewa.
"kiyi haƙuri Ramla ƙarar ɗanki na kawo miki, wallahi yaron nan azzalumi ne baya tsoron Allah kwata-kwata, kinga dai ko maƙiyin Azima yana zuwa ya dubata amma shi tunda ya kawo matar tasa ya yasar anan bai ƙara waigowa ba, tace min ko kiranta a waya ma baya yi, idan ita kuma ta kira shi suna gaisawa ɗan banzan yaron nan zai kashe wayar baya ko tambayar lafiyarta balle ta uwar dake cikin wani hali, to dan Allah ki faɗa min wannan mijin aure ne, kuma wallahi ƙarya yake yi yace baya son Ilham, dan dai kin ɓata ne lokacin yarintarsa amma da ko ke sai kin aura masa Ilham, to ni dai yanzu abinda nake so daga gareki tunda kin isa da shi kisa yazo wajen matarsa ko da ba zai zo duba Azima ba dan wataƙila sharrin da tayi masa ne bai manta da shi ba, ba haka ake ba sam wallahi, ya kamata yazo ya kasance da ita ya kwantar mata da hankali da irin salon ma'aurata, to da yake dai shi ɗin baida addini shisa, kuma rashin hankali da tunani ke damunsa, duk da nasan Madina ce take zuga shi wallahi, kuma zan dawo ne zata gamu da fushina da bata taɓa gani ba".
Hajiya Ramla ta tari numfashinta da cewa,"a'a Boɗejo Maamansa ai ba zata hanasa zuwa ba, ita kanta ina mai tabbatar miki da bata san da wannan rashin tunanin nasa ba da tuni ta tsawatar masa, amma zan faɗa mata insha'Allahu".
Boɗejo tace,"to ai dama Madina ta gama hanadameki ke da ƴaƴan, sai yanda tayi da ku. ke yanzu Ramla baki da ikon sawa da hanawa ga ƴaƴanki dake kanki sai dai Madina?, ni ko a tarihi ina na taɓa jin wannan yardar dake tsakanin kiahiyoyi, ai tun a auren nan na san Madina ba haka ta bar mutane ba, to ni dai wallahi tallahi zan baɗawa idona toka, in mance da cewar Turaki jikana ne in maka shi a kotu, Allah sai nayi ƙararsa akan zaluntar Ilham da yake dan ubansa, ina na taɓa jin kalar wannan auren me cike tsantsar zalunci da rashin adalci, wato yana nufin ma bai damu da ita ba ya huta da ƙaya kenanan tunda yanzu bata kusa da shi".
Hajiya Ramla ta kwantar da murya tace,"kiyi haƙuri Boɗejo zai zo insha'Allahu".
"ke ni rufe min baki sokuwar uwa kawai wacce wata ta fita iko da abinda ta haifa".
tai maganar a fusace tana kashe wayar cikin ɓacin rai, daga can ɓangarenta sai masifa take yi a asibitin muryarta ta karaɗe ko'ina, faɗawa me martaba take cewar yazo ya kaita kotu na ƙasar nan wallahi sai ta kai ƙarar Turaki akan wofuntar da matarsa da yay, sai taga ubansa Alƙali d ya tsaya masa.
Baffa ya dubi Hajiya Ramla dake riƙe da waya tai shiru fuskarta na bayyana rashin jin daɗi, ya karɓi wayar daga hannunta wannan yasa tayi firgigita ta dawo daga gajeran tunanin da ta lula, ta sakar masa murmushin da bai fito daga can ƙasar zuciyarta ba, Allah ma ya sani ko kaɗan bata farin ciki da wannan auren tun a ranar da ta san Ilham ƴar Fulani Azima ce, kuma in ace taso a ranar ko minti ɗaya Turaki ba zai ƙara ba da auren Ilham akansa, sai ta sa ya saketa, to amma babu yanda zata yi tunda har ubangiji ya riga ya shirya faruwar hakan, tsoronta ɗaya kar Ilham ta cutar mata da ɗanta tunda shi hali ana tsotsarsa a nono.
muryar Baffa na bayyana ɓacin rai yace,"a zatona tunda har an riga anyi auren kuma yayi haƙuri shikenan komai ya wuce, ashe ƴan banza ya mayar damu, to wannan yaron sai na saɓa masa, naga alamun sai mun saka ƙafar wando ɗaya da shi, sai nayi fatali da wannan son da nake masa in har bai riƙi matarsa da kyau ba, shikenan sai ace ni ne ban isa da yarana ba, ita yarinyar ba biyayya tayi ba ta haƙura da zama da shi har take kyautata masa, ko dan ubansa an faɗa masa ita so takeyi, zai gamu da fushina tabbas, zai haɗu da ni".
Hajiya Ramla ta sauke numfashi a sanyaye tace,"ai duk da kun aura masa wacce yake yaso da hakan bata faru ba, haka itama da kun bata wanda take so da hankalin ƴarku ya kwanta, da mijinta ya girmama halin da mahaifiyarta ke ciki. to amma ya zamu yi tunda me faruwa ta riga ta faru, wata matsalar dai muke ƙirƙirarta da kanmu yayinda ta zamar mana damuwa sai mu kirata da ƙaddara, kuma ma dai banda rashin adalci har ba'a ga biyayyar da Babana yayi ba ace za'asa ƙafar wando ɗaya da shi"...
Baffa ya katseta da cewar,"wait! mu kenan bamu isa da ƴaƴanmu ba sai mu bari suke juyamu?, wato bamu isa muyi musu zaɓi su karɓe shi ba kenan?".
tace,"a'a ai ƙarshen isa ai kun isa tunda har ya yarda aka ɗaura auren, ya kuma halarci ɗaurin aure har ya iya zama da matar, amma ko a musulunce ma auren dole dai bai halatta ba, ya kamata kuyi duba akan wannan, kun san irin cutuwar da zucoyiyin zasu yi kuwa?, ko baku taɓa cin karo da labarin auren dole yasa mata ta kashe miji ko kuma miji ya kashe mata?, duk abinda za'ai ake duba da yanda zamani ke tafiya ba yacca zamanin baya yake ba. kaga your Highness to tell you the truth, I personally do not like this marriage at all, kawai dan dai bani da yanda zanyi ne, bana son fitina sannan bana so yarona ya rasa kwanciyar hankalinsa, amma wallahi da sai Babana ya saki yarinyar nan, bana gudun maganar mutane, girgizar al'arshin ubangiji ne bana so".
"wait your excellency, me Madina ta kimtsa miki a dawowarki?".
ya faɗa yana dafa shoulders ɗinta. tai guntun murmushi tace,"ai ko Madina bata kimtsan komai ba, ba zan taɓa son auren nan ba, balle ma bata kimtsan ba, let me tell you this; i hate Fulani Azima with passion, hakama duk wani abu da ya shafeta, kamar yanda ƴarta ma ƙaunar ganinta bana yi balle kuma aurenta da ɗana, kawai dan banda yanda zanyi da abinda ku ka ƙadarta masa ne. but you keep in mind duk ranar da Babana sees his life choice no one will stop him from getting another marriage, ya zama dole a barsa ya auri zaɓinsa kamar yanda aka tilasta masa auren zaɓin wasu, yana da damar da zaiyi mata huɗu addini ya halatta masa hakan, so banga dalilin kuma da zai sa ace ita da ubanta ya zauna da mata huɗu ace ba zata zauna da kishiya ba, there is no such thing at all, Babana ba ƙaramin yaro ba ne".
da tsananin mamaki Baffa ke kallonta, tunda yake da ita bata taɓa rufe ido irin haka tana faɗa masa magana ba dake fitowa daga can ƙasan ranta, tafi Madina haƙuri nesa ba kusa ba, ta kan haƙura da duk kalar zaluncin da akayi mata ta barwa Allah, ansha cutarta ba sau ɗaya ba sau biyu ba tace ta haƙura ta yafe, sometimes ma sai dai Madina ta tayar da jijiyoyin wuya a madadinta. amma yau duk abinda yake jin tana faɗa daga can ƙasan ranta yake fitowa, and she means duk abinda ta faɗa ɗin.
ya buɗe baki yana so ya kawar da ɓacin ransa yace,"kin san kuwa Boɗejo ce ta shirya wannan auren?, kuma kin san ita tace bai isa ya ƙara wani auren ba sai in mutuwa Ilham tayi?".
ta kama maɓallin rigarsa tana saka masa tace,"idan har kai zaka bi umarnin mahaifiyarka to shima ka barsa ya bi umarnin tasa mahaifiyar". ta faɗa sanda take gama ɓallewar, sannan ta nufi saman mirror ta ɗauko glasses ɗinsa ta saka masa.
"yau dai ƙila gwamnati taci tararka dan ka makara da yawa". ta faɗa tana basa peck a goshi. shima yay mata peck a kumatun yana cewa,"yau ɗin rana ce ta musamman a wurina, dan haka office dole suyi min uzuri". ya faɗa yana kama hannunta su fito daga ɗakin, suka nufa downstairs, suna sauka daga steps Baffa yasa hannu ya rufe mata ido.
tace,"ah Your Highness so kake in faɗi ne?".
yace,"ta ina za ki faɗi bayan ina tare da ke, i want to suprise you with something shisa".
tai murmushi bata ce komai ba har suka sakko gaba ɗaga daga benen, Hajiya Madina da iyalanta na ƙasan sunja line kowannensu fuskarsa na bayyana farin cikin dake tare da shi, Hajiya Madina ta saka irin shaddar dake jikinsu da akai musu ɗinki iri ɗaya.
Turaki dake gaban layi ya matso ya rungume Hajiya Ramla, ƙamshin turarensa kawai taji itama tayi hugging nasa tana cewa,"Babana ya dai?, tunda na dawo kaƙi barina na huta, ko sai na mayar da kai ciki?, ko kuma sabon feeding zan fara ne?".
daga kunnenta Turaki ya raɗa mata,"If all mothers were like you, planet earth would be filled with such great families. I pray that you find happiness in every second of your wonderful life. Happy Birthday to the best Mother in the world, i so much loves you Mum".
ya faɗi hakan yana matseta sosai da jin wani irin shauƙi na ƙaunar mahaifiyarsa a tare da shi, nan da nan kuma duk sauran yaran suka yo kanta suna wishing ɗinta, sai da suka saketa sannan ta sami damar kallon Baffa da Hajiya Madina, sukai hugging each other suma suna mata prayers daga nan kuma ta ɗaga idonta ta kalla yanda sukai decorating parlon Baffa ya dawo kamar ba shi ba.
wani farin ciki mara misaltuwa ya mamayeta tana jin wata iriyar soyayya ta daban akan families ɗin nata na bin dukkan sassa na jikinta.
suka kama hannunta zuwa ƙaton center table ɗin da aka saka, an aje cakes kusan guda shida, kowanne an rubuta happy birthday to the special Mum, kallonta na ƙarshe ya sauka akan wanda akasa Happy Birthday your Excellency, tana kallo tasa hannu zata ɗauko suka tayata ɗaukowa suka kawo mata shi gabanta, da murmushin da ya kasa barin fuskarta tayi cutting cake ɗin tana cirowa ta kai bakin Hajiya Madina dake kusa da ita ta ɓarin hagu, Maama ta karɓa suna hugging each other da hawayen da ke sakko masu wanda basu san na menene shi ba.
daga nan kuma kowa sai ya shiga bata gift ɗinsa, Turaki ne na ƙarshe a wanda ya ajiye mata passport har guda biyu, ɗaya na zuwa saudiyya ɗaya kuma na zuwa agentina inda zata je ta huta taji daɗinta.
Hajiya Ramla ta dinƙa saka masa albarka da sambaɗa masa adu'a.
suna cikin yin breakfast ne Hajiya Ramla ke sanarwa da Hajiya Madina saƙon Boɗejo akan ɗanta, Maama bata san lokacin da bakinta ya suɓuce ba tace da Mum,"kinga manta da wannan tsohuwar da Allah, fitinarta tayi yawa wallahi, duk tsufa ya rikitar da ita, ta barsa da abinda har yanzu bai gama isarsa ba mana, idan yaje shi zai bata lafiya ne ko menene ake so kuma da ba za'a bar yaro ya sarara ba saboda dai an liƙa masa ƴar gwal, to shima ai ɗan gwal ɗin ne tunda Uwayensa na ƙaunarsa".
ta shiga zazzaga masifa ta inda take shiga bata nan take fita ba, har sai Baffa ya kira sunanta, a sannane ma ta tuna da batun zamansa a wajen ta manta tayi ɓarin zance irin haka akan babarsa.
yanda ya kira sunan nata tasan ransa ne ya ɓaci matuƙa, taci gaba da cin abincinta da ta ƙoshi ba tare da ta kallesa ba tace,"Allah ya baka haƙuri ya huci zuciyarka, yi haƙuri na annabi sarkin masu biyayya".
tukunna ta ajiye spoon ɗin ta miƙe tana kallon Turaki tace,"me babban suna duk sanda ta ka sami space sai kaje musu, ba qai ka matse kanka ba, sanda ka sami space nace, Allah ya baka ladan haƙuri da ladan biyayyar da kake yi".
har tai gaba zata fice sai kuma ta dakata, dan tasan muddin ta tafi ba abinda zai hana Baffa zazzagewa Turaki kwandon bala'i, kuma Hajiya Ramla babu abinda zata ce, ƙila ma yasa shi tafiyar da bai shiryawa ba ayau ɗin.
ta dawo ta koma dining ɗin ta tattara abincin gabansa tace,"tashi muje kaci acan, duk an bi an sa maka ido ka rame kana neman fita hayyacinka, ana aure ai ƙiba amma kai kai duk an tsabtareka". Turaki ya miƙe yabi bayanta suka fita, Hajiya Ramla tabi bayansu ta girgiza kai tana murmushi.
after sun kammala break fast ɗin yaran duk suka miƙe suka fita, Mum ta dakatar da Khaleel ya koma ya zauna sannan tace da Baffa,"Khaleel yaga yarinya yana so, yana da buƙatar aje a nema masa aure".
kunya ta kama Khaleel ya shiga sosa ƙeya, Beffa ya ɗan dube shi sannan ya dubi Hajiya Ramla yace,"ina ce ku keda ikon aurar da yaran ga waɗanda suke so, ai sai kuje ku nema masa ko".
yana faɗin haka ya miƙe yana cewa da Khaleel,"ka ɗauƙo key zaka kaini Government house, da sauri fa 11 muke da meating".
daga ɗakin Maama kuwa suna shiga ta dire masa abincinsa saman table tace,"ba inda zaka je wallahi, ai ba kai zaka bata lafiyar ba, in sunyi hankali sun dawo maka da matar shikenan, amma ba zaka bi sahunta ba wallahi ai ba mijin Hajiya bane kai".
ta bisa da kallo tana cewa,"nace fa babu inda zaka je daka wani bi ka damu".
ta wuce toilet ta barsa sai mita take yi.
ya ɗauki wayarsa ya kira Bello, daga ɓangaren Bello yace,"sai yanzu kaga damar waiwayata". Turaki ya sauke numfashi yace,"ba wannan ba Bello, i want you to find a solution for me, kaina ya ƙulle wallahi, i don't know how to inform them about the other marriage, ban san kallon da zasu yi min ba ban kuma san ta yanda zasu ɗauki lamarin ba, and i want to be with my wife now".
Bello ya shafa fuskarsa daga inda yake yana kwantar da kansa jikin kujerar office ɗin sannan yace,"explaining to them is not that difficult, yanda zasu ma yarda da zancen is the biggest tension, MT dole dai ka ja mana faɗan da ba zai ƙare ba at this age da muke da shi da muka wuce ai mana faɗa". yaja tsaki,"shikenan yanzu abinda kowa zai ce shine bamu da hankali, alhalin ni ban ma san sanda kaje kayi haukar taka ba, in ace ma kai ɗaya za'aiwa faɗan da sauƙi".
Turaki yace,"now you have a suggestion for me, ko kuma magana zaka ci gaba da gaya min in kashe wayata".
Bello yace,"gaka da masifa da gajen haƙuri, to haka kawai zan baka shawara ban gaya maka magana ba?, faɗan da zaka jawo min ni kuma fa?, mtswww where are you now?".
"i am at home".
yace,"are you coming to office?".
"not sure".
Bello ya sauke numfashi sannan yace,"I will come after I leave the office around six o'clock, kar ka fita kuma ka barni da zaman jiranka".
muryar Turaki a sanyaye da kuma ban tausayi yace,"Baffa can break this marriage Bello, i am afraid that will happen, ko kawai inci gaba da barinsa cikin sirri?, ita kanta yarinyar ma fa matsala ce".
cikin bada ƙwarin gwiwa Bello yace masa,"babu abinda zai raba aurenka insha'Allahu, ai da kyakykyawar niyya kayi, kuma rainonka akayi akan taimakawa, kuma karka manta kana da Maama, ita kaɗai in ka tuna kana da ita ya isa ka daina jin fargabar komai".
Turaki ya furzar da iska daga bakinsa sannan yace,"thank you friend".
Bello ya bushe da dariya yace,"ya da godiya tun ba'a sami mafita ba".
Turaki zai yi magana Maama ta fito daga toilet, yaga ta nufa wadrobe ta buɗe ta ɗauko hijab ta tayar da sallah, ya bi kiran Bello da kallo da ke tafiya, he have alot to say amma dole ya haƙura ya kashe wayar ya bari sai sun haɗu anjiman.
around 4 Turaki ya dawo yazo shiga da mota gate sai ganin Fillo yay ta fito daga cikin wata jar mota, kuma ta fito daga motar ta tsaya suna magana da na ciki ta window, yana kallon motar ya shaida ta Dr Yusuf ce, yaji kamar ya fito yaje ya bankawa motar wutar duk su ƙone. kusan 5minutes sannan Fillo ta bar wajen ta shige gida Dr Yusuf na ɗaga mata hannu ta glass ɗin da ya zuge.
motarsa na barin wajen Turaki ya fito kamar kububuwa ya shiga gidan, yanda yake tafiya kamar zai tashi sama, yana zuwa ya sha gaban Fillo ransa a haɗe kamar hadari yace,"juya muje".
tayi kamar bata jisa ba ta raɓa ta gefensa zata wuje ya wani fincikota ta dawo baya, idanuwansa a warwaje sun sauya kala ya ɗaga hannu ya wanketa da mari, babu shiri Fillo ta durƙushe a gabansa tana dafe kuncinta saboda wata hajijiya da taji tana neman ɗaukarta ta zubar. sai kuma kawai ta fashe da ku ka sosai tana jin zafi a ranta, ya dinƙa kallon yanda take durƙushe a gaban nasa tana kuka bilhaƙƙi, yaji kamar yasa ƙafa yay ball da ita saboda wani azababben kishinta dake sukar ƙirjinsa.
Fillo ta miƙe a harzuƙe tana ɗaga hannu sama zata rama marin sai taga ko kusa hannunta ba zai kai fuskarsa ba, hakan yasa ta kuma fashewa da kuka tana damƙar kwalar rigarsa tana jijjiga shi.
"ni me nayi maka?, Allah ba zan yarda ba sai na rama". ta faɗa tana dukansa da iyakar ƙarfinta a ƙirji sosai.
ya kama tsintsiyar hannunta ya damƙe da kyau ya wancalar da hannunta daga jikinsa ta tafi zata faɗi Zaytuna da ta iso wajen tai saurin tarota ta faɗa jikinta.
*Vote, Comment and share.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_Avoid error mistakes._
*40*
Zaytuna tayi matuƙar furgita da yanayin Turaki, hakan yasa ta riƙe Fillo da kyau ta jata sukai baya da shi saboda yacca yake faman uban huci kamar mayunwacin zaki.
ta shiga kaɗa masa kai tana kallonsa tace,"Hammah dan Allah kawai ka kawo ƙarshen komai a yau ko zuciyarka ma ta huta, ita mene laifinta?, ita me ta sani?, bafa ta san komai ba". ta faɗa ita kanta tana jin tsoronsa saboda yanda taga jijiyoyin kansa duk sun fito raɗau.
idonsa akan Fillo dake ta kuka yana binta da wani irin mugun kallo na tsantsar jin haushi yace da Zaytuna,"saketa, ki saketa ko na haɗa har da ke". ya faɗa yana raising voice ɗinsa sama, har sai da Zaytuna tayi masa alama da yay ƙasa da murya kar cikin gida su jiyo, dan ita bata so a san lamarin ɓoyayyan auren nan acikin tashin hankalin da zai sa aƙi fahimta. ya ƙara sakar mata tsawa yana zare mata ido yace,"nace ki saketa ko?".
taƙi sakin Fillon tace,"Hammah it is not her fault, me ta sani agame da hakan balle ta kiyaye, you just go and inform Maam about everything shikenan kai da ita duk sai ku huta".
yace,"tana haukar zan kawo ƙarshen komai, a hakan tana sauraron kowanne banza ya kulata, ita mahaukaciyar ina ce da bata san dai-dai da rashinsa ba?".
kamar zata yi kuka ta ƙara cewa,"please Hammah...". da ya yayo kanta kamar tashin iska babu shiri ta saki Fillo tayi gefe ɗaya.
me gadi yayo wajen da sauri yana bawa Turaki haƙuri duk da bai san meke faruwa ba amma da dukkan alama dai ba lafiyar. Turaki yay masa wani kallo shima yaja gefe, ya fizgi Fillo dake ta tirjewa tana faɗin,"ni ka sakeni babu inda zan bika, me nai maka da zaka tsaneni, kuma Allah sai na rama marin da kayi min ai ba abinda na maka, Allah ni ka sakeni sai na rama".
ganin yana ƙoƙarin duƙawa ya ɗauketa ba shiri ta saki jiki ta bisa suka fita.
suna fita bakin gate ta gartsa masa cizo a hannu babu shiri ya saketa, ta falla a guje zata juya cikin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 42 Chapter of 73