kai ta kawo ya koma kamar wanda ke aiki da battery, kuma duk saboda zama da Bello, Maama tayi ta tofa masa lahaula.
duk friday Bello a gidansu yake yini, kuma shi Bello babu abinda ya iya sai shegiyar fitina da dambe, sai suje can field Bello yay ta koya masa yanda zai ƙwaci kansa in wani yafi ƙarfinsa, har ranar ya gwada masa yanda zai shaƙe wuyan mutum, Bello ya shaƙe masa wuya har sai da numfashinsa ya kusa ɗaukewa, kuma kamar wani Malaminsa ko Babansa Bello yace yaje yay ta practical, tun da yana da ƙanne yay ta gwadawa akansu, ai kuwa da daddare ya shaƙi wuyan Khalil zai yi assignment ɗin da Bello ya ba shi, Baffa kuwa ya tarfa shi yay masa ɗan banzan duka ya kulle shi a store, aciki ma ya kwana dan sai da safe Maama ta sato key ta buɗe shi, kuma a washe garin da suka haɗu a islamiyya ya faɗawa Bello, sai yace zai koya masa yanda ake ɓalle ƙofa in an kulle mutum, ko kuma da an kaishi ɗaki za'a kulle ya fice a sukwance tun kafin a rufe, har haura katanga duk tsayinta sai da Bello ya koya masa, da yacca zai ɗauko key ɗin mota ya fice daga gidan, har yana ba shi labarin wai shi a gidansu sai da ya fasa glass ɗin mota har biyu, Abbansa yazo dukansa ya ɗafe wuyansa yaƙi sakinsa.
watarana sun tashi a school yasa driver ya wuce da shi gidan su Bello, ya koya masa duk kalar yanda zai tseratar da kansa, wata rana kuwa yaywa Granny laifi zata kullesa a ɗakinta yay sufa yabi ta ƙarƙashinta, garin kamo shi ta zame ta faɗi, Anty Sa'adah ta kama shi ta murɗe masa kunne har sai da ya saki fitsari a wando.
yay shiru yace,"kin san Bello har cewa yay inyi kashi a fo sai in dangwala in rubuta sunana ajikin bangon ɗakin Baffa, in dai yake ni to baya so na...ai ko in faɗa miki ina yin haka washegari Baffa ya kaini Europe wurin Granny".
Fillo ta dinƙa dariya har da riƙe ciki, shi ma ya shiga tayata dariyar kamar yanda take yi.
ta kama hannunsa ta ɗora a saman ƙirjinta tana rufe ido, yayinda dariyarta ke juyewa zuwa sanyayyan murmushi, a yanzu ta ƙara yarda cewa Turaki yana sonta har cikin zuciyarsa, kuma ba ta tunanin akwai abinda zai canja hakan, tana ganin zallar soyayyarta fal a cikin idanunsa a duk sanda ya kalleta, duk da har yanzu da bakinsa zuwa kunnenta dai bai furta ma ta kalmar i love you ba tun bacin wadda ta gani a takarda.
acikin kwanaki ukun nan kacal tana cikin wata duniya ne ta daban me cike tarin kulawarsa da tarairayarsa, ta daina jin tsoronsa dan ya bi ya kulle duk wata hanyar tsoronsa a gareta, ta saba da shi yanzu fiye da tunanin kanta ma, ta saba da hirarsa da yake cikin yi ma ta ko da yana cikin aiki ne, kamar yanda ta saba da jikinsa, dan duk wani motsi nasa cikin taɓata yake yi, ko akan laptop yake to hannunsa ɗaya na cikin nata, ko kuma ya ɗorata ajikinsa yay aikin a haka, haka in bacci ne tana manne a jikinsa.
kuma yanzu duk ta san abubuwan da yake so da wanda baya so, dan a kwanaki ukun nan duk ya lissafa ma ta halinsa, ya faɗa ko mai da yake so ta dinƙa yi masa, kuma sai a yanzu ta fahimci ashe shi mutum ne me sauƙin kai in har ka fahimce shi.
bayan sallar la'asar Fillo na zaune ita ɗaya a ɗaƙin Turaki, wayarsa ce riƙe a hannunta tana game, ta ajiye wayar tana ɓata fuska, Tunda Turaki ya fita masallaci bai dawo ba, wai Baffa yayi baƙi daga ƙauye sun zo ba su sameshi ba, shi ne yace yaje ya kula da su, gaba ɗaya bai fi minti goma sha biyar da fitar ba, amma duk sai take jin babu daɗi, ta san dai akwai ƴan aiki amma gidan duk sai taji yay ma ta girma, ba ta san ta saba da shi ba har haka ba, ji tai tana kewarsa sosai kamar tun safe ya fita ya barta, abu ɗaya kawai ta sani ba zata ji daidai ba har sai ya dawo.
tun ɗazu tayi wanka but ta kasa shiryawa, so take sai yazo yayi mata choosing kayan da zata saka, cikin kwana ukun nan duk shi ke zaɓa ma ta kayan da take sawa, and ta lura ya fi son ƙanan kaya, amma yanzu fita za su yi, ba ta san waɗanda zai so ta saka ba a yayin da fitarsu za ta zama karo na farko.
ta ɗau wayar tana jin kamar ta kira shi, sai dai bata so ta dame shi, duk da bai faɗa mata ba tasan shi ma hankalinsa na kanta.
miƙewa tayi ta koma ɗakinta, ta buɗe wadrobe ta watso da duka kayan ciki, ta kama ƙugu ta tsaya tana ƙare musu kallo.
ta ɗauki wata blue ɗin atamfa, tsaye tayi a gaban full body mirrow tana kara atamfar a jikinta tana kallon kanta, ta ƙara haske sosai alamun jin daɗi na ratsata, kuma idan tasa atamfar ma zata yi ma ta kyau sosai, sai tasa hannunta a kumatunta tana taɓawa, sai taga kamar ƙashin wajen ya fara komawa nama yana son cika wajen.
a lokacin taji ƙarar buɗe ƙofa, tana juyawa idanuwanta suka sauka akan Turaki da ke gyara zaman hula a saman lallausan gashin kansa, fuskarsa ɗauke da wannan murmushin da yake tafiyar da tunaninta, baƙin boyel ne acikinsa ɗinki boda, yayi kyau sosai, sai taji kamar ta ɗauke shi ta kaishi can ƙuryar zuciyarta ta adana, ta yanda babu wani da zai dinƙa ganinsa, sai ita ɗaya tallin tal.
Turaki ya gama gyara zaman hular tasa, ya ɗago ya kalleta, ya furta ya Ilahi a sanda ya lura da ƙwayar idonta.
ya ƙaraso ciki da sauri, ya tsaya a dab da ita yana kamo fuskarta cikin tafukan hannunsa biyu.
"Fulani nah me ya faru?, me ya same ki?, me ya taɓa ki?".
yayi tambayar duk a lokaci ɗaya, me shirin kaɗan kawai sai ta sa masa kukan shagwaɓa, cikin sheshsheƙar kuka tace,"ba kai ba ne ka tafi ka barni ni ɗaya, gidan duk babu daɗi yay min girma".
"shhh...". yasa hannu yana goge ma ta hawayen a hankali, ita kuma tana ƙara narkewa da shagwaɓe masa.
duk sai yaji zuciyarsa ta matse da tausayinta, ya san tunda ya sabar ma ta da zama tare da shi yanzu dole ba zata ji daɗin zama ba idan ba ya nan.
"i'm sorry Fulani Nah, ban san zan jima har haka ba da ban fita ba sai in aika Sameer kawai, sai da naje naga ashe wai wata gona za'a ba su, kuma ba su faɗa min ba har sai da na dawo gida na duba takardar gonar a cikin takardun Baffa, ina ta sauri but kin san lamari irin haka dole yana ɗaukan lokaci".
ya faɗa yana sa hannunsa a bayanta yana zagaye ɗan ƙaramin ƙugunta da shi, sannan a hankali ya ƙara raɗa ma ta,"am sorry, kin haƙura?".
har sai da ya tabbatar zuciyarta ta nutsu sannan ya a hankali laɓɓansa su ka sauka akan cheeks ɗinta.
sannan ya shiga tambayarta me yasa bata shirya ba, Mum na ta yi masa waya tun ɗa zu, idan ba su je yau ba za'a sami matsala.
ta ce,"ni ban san kayan da zan saka ba ai".
a lokacin taji sautin murmushinsa kafin ya saketa, closet yaje ya zuge ya buɗe ɓangaren da abayas suke jere a jikin hanger, ya ɗauko wata orange colour da tasha uban adon stones a jiki.
"na ɗi son abaya akan atamfa ko less".
ya faɗa yana ajiyewa akan gadon sannan ya kamo hannunta ya kaita gaban dressing mirro ya zaunar da ita kan stool, da kansa ya ɗauka body lotion ya shafa ma ta, ita dai kallonsa kawai take ta cikin madubin, kamar ba asalin Turakin da ta sani ba, ya ɗauka powder ya rambaɗa ma ta, taita dariya, ganin zai mayar da ita dodanniya tai saurin karɓar form ɗin ta gyara powdern.
ba ta yarda ya saka mata brezier ba kamar yanda taga yana ƙoƙarin yi, ta karɓa ta shiga toiler ta saka da kanta, tana fitowa ta tarar baya nan, sai ta ɗauki rigar ta saka, abayar ta ƙara haska fatar jikinta da tayi fresh, tayi rolling mayafinta, sai ta zama kamar balarabiya, kamar ba wannan Fillon da ke yawo cikin tsumman kaya ba shekarun baya da suka wuce, wannan wata Fillo ce ta daban, wacce ake rainonta cikin so da kulawa, wacca ake nuna ma ta babu wata tamkarta, wacca ta shigo cikin sahun masu ji da ado da ƙwalisa.
ta ɗauko ƙaramar jaka kalar kayan, duk sai taji ta ƙosa Turaki ya dawo ya ganta, tana tsaye tana ta kallon kanta a madubi, tana tunanin duk ranar da akace ta ƙara kumari kuma ya zata dawo kenan saboda tsabar kyau?, sai ta tuna irin wankan da Raudha ke yi a saudiya idan zasu fita, tafiya tayi ta ɗauko wani box ta buɗe ta ɗauko glass ta saka.
tana shirin fita yay daidai ta buɗewar Turaki ya sanyo kai, turus yay ya tsaya yana kallonta tun daga sama har ƙasa, laɓɓanta suka tsuke fuskarta na bayyanta murmushin jin daɗi.
tana jiran kalman yabawa su fito daga bakinsa sai taji yace,"ina za ki a hakan?".
ya faɗa annurin fuskarsa na ɗaukewa, bai bari tayi magana ba ya wuceta ya shiga ciki, binsa tayi da kallo taga ya ɗauko hijabi, babu shiri ta juya zata fita yay saurin damƙo hannunta.
"babu abin da za ki fita a haka, da igiyoyin nawa uku reras akanki za ki fita a haka saboda an faɗa miki bana kishinki?".
"to mene a wannan shigar?".
"abubuwa da yawa kuwa da zasu ja hankalin wani ɗan banzan a kanki, ko ba kiga yanda kika yi kyau ba ne?".
ta juya idanu tare da yin fari tana cewa,"ai baka ce nayi kyan ba".
ya ce,"idan nace zan tsaya faɗa miki yacca kika yi kyau ba zamu samu damar fitar nan ba, dan duk lokacin za su tafi ne ba tare da na gama fayyace miki irin kyan da kika yi ba. oya ta ina zan zan cire wannan pin ɗin?".
ta marairaice da cewa,"please ka bar ni a haka, wa ye ma zai ganni to bayan a mota zamu je?".
sai kuma ta ɓata rai tana cewa,"wai ma ba gidan su me wancan part ɗin za mu ba?".
ya kalleta yaga yanda ta wani ci kunu tamkar ba ita ba, yace,"can zamu sai aka yi ƙaƙa?, sai aka ce a gidan su babu maza ko babu masu idanu?".
ta ɗan murguɗa baki,"sai ba zan dankama hijab naje gidansu ba tayi tunanin ni ƴar ƙauye ce wadda bata waye ba, ka sa aita gulmana idan mun baro gidan".
"su waye za su yi gulman naki?".
"ko ba tayi ita da muƙarrabanta ba za tayi ita da zuciyarta, don Allah ka barni in je a haka kar ta raina ni".
dariya ta ba shi, but sai ya gimtse yana ɓata nasa ran shi ma, ta durƙusa tayi pleading hannayenta tana yi masa magiyar ita ya barta ta tafi a haka, a ƙarshe dole ya haƙura ya barta, sai dai bai yarda tasa glass ɗin ba ya zare shi yay jifa da shi, ya kama hannunta su ka koma ɗakinsa ya ɗauko facemask ya saka ma ta.
"kuma saura idan munje in ga kin wage baki kina dariya ko murmushi...".
tun bai ƙarasa faɗar abin da zai ce ba tace,"yanda zata ji daɗin cewa zaman ƙunci nake yi da kai ba, ni dai kawai babu ruwanka da ni ka bini da ido kawai".
ya buɗe. baki da mamaki fal yana cewa,"when?, where?, how?, duk a yaushe kika yi baki har kike magana haka?".
ta turo baki gaba, ta ƙwace hannunta ta ɗauko baƙin glass ɗinsa ta saka masa,"yana yi maka kyau sosai idan ka saka, amma ni ɗaya zaka ke sakawa, promise".
ya karyar da wuya,"i promise you".
hannunsa ta riƙe suka fita, tunda suka hau saman titi kuma duk sai ta koma masa kamar ba wannan ƴar Babyn ba sarkin daru da rigima, wacce ta ke hawar masa bori ya zauna zaman lallashi, wannan wa ta Fulani ta daban ya ɗauko, me faɗa kamar yaƙi, da kuma ba da instructions.
ta dage tana faɗa masa in sunje gidan bata yarda ya kalli kowa ba, bata yarda yay magana sama da sau biyar ba, bata yarda ya amsa gaisuwar kowa ba, bata yarda ya cire glass aga hasken idonsa ba.
shi ma ya tamke murya yace,"duk da wa kike?".
"da Muhammad Turaki".
ya saki hannunta ya ɗalli bakinta, ta ɗauke idonta da ga barin kallon titi ta juyo ta kalle shi.
"to ba sunanka ba ne?".
"a bakin mutane ba, amma ban da naki".
"to ni haka zan faɗa".
yay murmushi,"wai to duk wannan cin maganin na mene?, ba fa a haka muka fito ba, ko nayi laifi bisa kuskure ne?".
tayi narai narai da idanu ta ce,"ni kawai bana son zuwa gidan".
"me yasa?".
"bana so muje wannan matar ta ganka, na san dole zata kalle ka, na san dole sai taji wani abu akanka".
tai maganar kamar zata yi kuka.
yay shiru bai ce komai ba, sai da suka yi nisa a tafi sannan ta ƙara cewa,"kuma na san kaima zaka kalleta ko?".
nan ma dai bai ce ma ta komai ba, hakan yasa kawai ta kifa kanta a saman gwiwarta tana jin wani bala'in zafi a zuciyarta, idan ta san haka ne da tun farko tace bata da lafiya ba zata iya zuwa ba.
*_bari nayi amfani da wannan dama wajen miƙa godiyata da nuna jin daɗi gare ku masoyana, tank you so much lovlies for keeping up with this story, ga shi dai muna ta tafiya amma ko kaɗan baku ƙosa da ni ba, duk da inata ƙoƙarin ganin na yanke labarin an gama shi kwatakwata. Anyway don Allah kuci gaba da bani ƙwarin gwiwa ta hanyar yin warm comments ɗinku da ku ka saba, haɗe da yin voting, mun kusa hattamawa insha'Allah._*
*_ina son duk wani makarancin littafin nan tamkar yanda nake son ƴan group ɗina na Halima Hz palace, muaahh to all of you😘😘._*
wataƙila a samu sabon update duk dare, amma zai zo babu yawa ne🤕
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*53*
*Azima Tahir Lukman.*
ashekarun baya masu yawa da suka shuɗe, Azima Tahir Lukman wata matashiyar budurwa ce, wacce ke matuƙar ji da kanta a ɓangaren kyau, ilimi da kuma dukiya ta mahaifiyarta wadda ta kasance ƴar siyasa.
kyau irin na Azima ke tasirantuwa a zuciyoyin maza da dama, daga masu kuɗin har talakawa, a inda ta ware manyan masu kuɗi da masu mulki waɗanda su ne take ganin su kaɗai ne suka isa su mallaketa.
kuma a kaf mazan da tayi mu'amala da su babu guda ɗaya aciki da zuciyarta ke jin tana so ko kuma zata iya aurensa, no; zata mu'amalanceka ne kawai domin kuɗin da suke aljihunka, da zarar ta gama da kai shikenan, saboda ta mallaki kuɗi a wurin irin alahazawan da ke zuwa wurinta ta kashe rai ba ɗaya ba, ba biyu ba.
zuciyar Azima ta so mutum guda tallin tal ne a rayuwarta, wato Alƙali Habib Dikko, shi kaɗai zuciyarta ta so tsakani da Allah, wanda har take jin she can go to the extend akan taga ta mallake shi, alhalin kuma yana matsayin saurayi ne na aminiyarta da ta san cewa an saka musu rana.
Ramla Muhammad Turaki itace babbar aminiyarta da suka yi university tare anan london, duk wanda yasan Azima ya san Ramla, haka duk wanda ya san Ramla yasan Azima, su kwana tare su tashi tare, su ci abinci tare su yi yawo tare, haka zalika ba sa taɓa aiwatar da abu sai da shawarar juna.
Azima ta samu Ramla ne tare da Dikko, tare ta gansu, wanda shi ma kuma ya aminta da ita sosai, musamman da yaga Ramla ta ɗauki duk wata yarda da amana ta bawa Azima.
sai dai daga lokacin da Dikko ya fara shirin kai lefen Ramla, a lokacin Azima ta fara kunno wutar gobarar da zata lalata lamarin auren, ta fara ɓata Ramla a wurinsa, abubuwa iri iri da zai sa yaji ya tsani Ramla babu wanda ba ta faɗa masa ba, tun baya yarda har ya zo ya fara yarda da ita, saboda sauyin da yake gani a tare da Ramla a lokacin da bata ba shi attension ɗinta, sakamakon final exams da za su fara.
hatta vedion tsiraici na lesbian Azima ta ɗauka ta bayar anyi editing ɗinsa da fuskar Ramla ta bawa Dikko, daga wannan lokacin kuma yaji ya tsani Ramla kwatakwata, ita kuwa Ramla a lokacin bata kawo komai a ranta ba dangane da watsi da lamarinta da Dikko yay, ta ta'allaƙa hakan ne da space ya bata saboda ta samu tayi karatun exams sosai.
sai dai kuma a lokacin da Azima take tunanin tayi nasara, a lokacin Allah ya toni asirinta a ranar wata laraba, inda wanda yay ma ta editing vedion tsiraicin Ramla yaje ya sami Dikko ya faɗa masa gaskiyar komai, a lokacin soyayya ta riga tayi nisa tsakanin Dikko da Azima, dan saura ƙiris su shigar da iyaye cikin maganar, dan Azima ta gama tsara yacca zata shimfiɗar rayuwar aurenta da shi.
kuma duk wannan lamari da ke faruwa Ramla bata da labarin komai, yacca Azima ba ta bari ta fahimci wani abu ta ɓangarenta ba, haka shi ma Dikko bai taɓa tunkarar Ramla da irin abubuwan da Azima tayi akanta ba har kawo iyau da take matarsa, uwar gidansa, kuma uwar ƴaƴansa, wucewar shekaru sama da 20.
lissafi ɗaya Azima tayi a bayan da Dikko ya juya ma ta bayansa, shi ne ba zata taɓa yin nisa daga gare shi ba, zata bi wata hanyar da zata kusance shi har ta wanke laifinta, kuma har ya yafe ma ta yace zai aureta kamar dai yanda taci burin hakan.
dalilin da yasa ta shiga rayuwar Mai Martaba Hashim Latif kenan, saboda ta lissafa cewa ta wannan hanyar kaɗai zata iya samun damar kusantar Dikko, ta hakan ne ba zasu yi nisa da junansu ba, ta hakanne zata samu damar wanke laifinta gare shi, in ya so a sanda yace ya yafe mata sai tayi duk iyakar ƙoƙarin da zata yi ta raba aurenta da Mai Martaba domin ta mallaki Dikko, amma sai dai me!, lissafin da hasashenta duk sai ya tarwatse ya bi iskar da ta kaɗa tun a ranar da ta sanya ƙafafunta acikin gidan mai martaba.
kuma daga lokacin da ta fahimci cewa ba zata taɓa samun Dikko ba, daga lokacin ta ɗauki alwashin ƙuntata rayuwar duk macen da ke rayuwa tare da Dikko hatta kuwa da ƴaƴan da zai haifa ba tare da ita ba.
shigowarta cikin rayuwar Mai Martaba ta gane asalin menene mulki da kuma daɗin da yake cikinsa, wannan yasa ta dasa cin burika da yawa a rayuwarta, lokacin shaiɗan ya fara buga ma ta sabuwar ganga acikin kanta, akan aikata mugwayen abubuwan da ba zasu ɓulle ma ta ba, ya dinƙa rinjayar zuciyarta da cewa tayi duk fafutukar da zata yi wajen ganin ta mallaki kaso 70 cikin tarin dukiyar Mai Martaba kafin ta barshi.
shiyasa daga lokacin da ta haifi Ilham, sai tabi duk wata hanya da zai sa Mai Martaba ya koma ganin ƴarta kawai a matsayin ita kaɗai ce ƴar da ya mallaka, wannan dalilin yasa ta kama fufutukar bin bokaye kenan, wanda ya zama mafi muhimmanci a wajenta.
kuma tayi nasara akan hakan, domin kuwa cikin ƴaƴa goma da Mai Martaba ya mallaka Ilham kaɗai idanuwansa ke iya gani a matsayin wacca ya haifa da cikinsa, wanda hakan ya janyo rabuwar kawuna a tsakanin sauran ƴaƴan da ita Ilham ɗin, domin ya mayar da ita tamkar ɗa namiji, duk wani abu nasa da ya mallaka yana rubuta shi da nata sunan, har ya kan yawan buɗar baki yace _na so ace Ilham Namiji ce, da ta gaji wannan kujerar tawa tun ina raye._
sai dai babu wanda ya taɓa gane Azima na ɗauke da wani mummunan ƙudiri, kasantuwarta mace mai dabara, macen da ta ke lulluɓe da mayafai guda biyu, ciki baƙi waje fari, sai dai ba ta taɓa barin wani mahaluƙi ya ganta da wannan baƙin lulluɓin sai dai farin da ta yafa daga waye.
_"har yanzu mun kasa gano taƙaimemen ciwon da ke tare da ita. duk wasu injina da ya kamata muyi amfani da su sun gaza yin aiki wajen gano cutar da ke tare da ita"._
maganar da ɗaya daga cikin likitocin ke yi kenan acikin ofishinsa, acikin asibitin masarautar kaltungo, Mai Martaba ya miƙe cikin mutuwar jiki suka fito tare da Dr ɗin.
a sanda suka fito ya tsaya daga can nesa yana kallon matar tasa ta silin hanyar da ta buɗe ta ƙofar ɗakin da take kwace.
kallo ɗaya zaka yi mata tun daga nesa kaji zuciyarka ta motsa saboda tausayin mawuyacin halin da take ciki a yanzu, ka kuma ƙara jin tsoron ruɗin duniya, a yayin da zuciyarka za ta tuna ubangiji da dukkan irin ikon da yake zartarwa akan rayuwar kowanne bawa.
kwance take an ɗaureta ajikin gadon ɗakin asibitin da ke cikin masarautar saboda yawan girgiza da take yi yanzu, idanunta a tsaye suke sun ƙafe akan windon ɗakin da ta nan ne kowa ke iya samun damar ganinta, har kuwa da ƴarta guda ɗaya da ayanzu ita ma bata iya zama tare da ita saboda bala'in ɗoyin da take yi wanda kowa ke cutuwa da shi, hatta kashi idan tayi sai ta jima cikin su kafin azo a kula da ita.
gaba ɗaya ta gama lalacewa, ta koma ita da ƙwarangwal babu maraba, a halin da ake ciki yanzu, dukkan wani ɓangare na zuciyarta ya riga ya gama dagargajewa a ƙirjinta, tana jin ƙirjinta ne kamar Allah bai taɓa halittar komai a cikinsa ba, zuwa yanzu duniya gaba ɗaya ta gama yi mata zafi, babu abin da take fata sama da mutuwa, sai yanzu ta gane ka zalunci mutum Allah ya baka damar neman yafiyarsa, ko ka saɓawa Allah ka nemi gafararsa tun kafin ya damƙe ka, wata rahama ce babba daga ubangiji, atleast ka iya samun sassauci na daga bala'in da zaka shiga.
halin da take ciki a yanzu ta tabbata babu wani abu na awo a duniyar nan da za'a auna ya fitar da kalmar da zata fassara shi, a yanzu ta afka ne cikin wani rami na nadama, nadamar da ta ke kira da mara amfani.
ta kuma sa ni har ta mutu Allah ba zai bata damar yin magana ba, balle ta samu ta fayyace mugun abubuwan da ta aikata, balle har ta nemi yafiyar waɗanda ta cuta. ta sa ni wannan kaɗanne daga cikin hukucin da Allah zai yi mata.
_(Ya Allah ka kiyashe mu daga sharrin zuciya, ka rabamu da aikata aikin danasani.)_
Hajiya Ramla ta zo tayi tsaye a bakin windon ɗakin Fulani Azima, kallon junansu suke yi, idon Fulani Azima sai hawaye yake zubarwa kamar an kunna famfo, tana ta girgiza kan gadon da take, da alama so take yi ta sauko, kuma so take yi tai magana da Hajiya Ramla, so take yi a bata aron dama ko da guda ɗaya ce, ko da ta minti ɗaya ce.
in har Hajiya Ramla tace bata ji tausayinta ba tayi ƙarya, abu ɗaya ne kawai ta san da shi, shi ne ko akwai sama da abin da yafi tausayi ba zata taɓa yafewa Azima ba ko da ace zata shiga halin da yafi wannan muni.
ta sauke numfashi tana ƙara kallon Fulani Azima wacca har yanzu idonta ke maƙale akanta tana jijjiga gadon.
sai ta saka facemask ta fesa turare sannan ta fuskanci gaba ɗaya windon, tace da ita,"na san kina ta so ki buɗi baki ki nemi yafiyar abin da kika yi min ni da ɗana, kamar yanda kike so ki buɗe baki ki faɗi mugwayen abubuwan da kika aikata. ban da masaniyar ko Allah zai baki aron wannan damar, but ki sani ko da bayan raina kika sami damar magana, karki tsammaci za ki ambaci sunana da roƙon na yafe miki, karki saka sunana acikin waɗanda zasu yafe miki, Azima ba zan taɓa yafe miki abin da kika min ni da Babana ba, sai mun tsaya a gaban ubangiji ni da ke, sai Allah yayi mana hisabi. but just keep in mind da bakina dai ba zan taɓa faɗar abin da kika aikata ba, idan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 60 Chapter of 73