Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da damuwa sannan ga jikinta kamar a sanyaye. "babu komai Daughter, kawai yanayin garin ne na yau". tana faɗin hakan kuma sai ta ɗauki wayarta ta kira lambar Hajiya Madina, har kiran ya katse bata ɗauka ba. sai ta miƙe tana cewa da Fillo,"na bar ki anan ko zamu je tare?". "ina Mum?". "wajen Maaman ku. naga tun safe ban ji ɗuriyarta ba, ƙafana na ciwo ban sami damar leƙawa ɓangaren nata ba, ina ta kiran wayarta kuma bata ɗaga ba". Fillo tace,"ai ba mu jima da gama waya da ita ba Mum, ita ma ta kira ni ai". Hajiya Ramla ta sauke numfashi, tayi gaba yayin da Fillo ta bi bayanta. shigar su parlon Hajiya Madina kiran Turaki ya shigo wayar Fillo, tana ɗaga yace da ita. "Fulani Nah kin ƙarasa gidan?". "na je Jannaty, lafiya naji ka kamar a damuwa". "babu komai. yau ɗin ne kawai nake jinta duk babu daɗi, ina Maaman?". "yanzu ai na shigo ɓangaren nata, ban hau saman ba". "kowa a gidan yana lafiya?". "Jannaty wai...". "just answer me". "kowa lafiya lau, Mum ma muna tare da ita". ya sauke numfashin da ta jiyo har cikin dodon kunnenta. "ina kan hanya ne go slow ya tsare ni. amma insha'Allah yanzu babu jimawa zan ƙaraso gida". san da ta shiga ɗakin Hajiya Madina ta tarar da Hajiya Ramla na taɓa jikinta, a yayin da take yin magana da Nihal tana tambayarta,"kuma bata ce miki bata jin daɗi ba?". "a'a Mum, ba ma fa ta jima da kwamciyar ba ai, lafiyarta lau". "to masha'Allah, idan ta tashi ki ce ta kira ni a waya. zan je saboda baƙin Haɗeja da za su zo". "tom Mum". Hajiya Ramla ta fita, Fillo ta ƙaraso ciki ta zauna a gefen gadon da Hajiya Madina ke kwance tana bacci. ita ma tasa hannu ta taɓa ƙafar Maaman sai taji babu zafi kamar yanda kowa ke tunanin ko zazzaɓi ne ya sata yin baccin rana haka. "Allah yasa ba ciwon kai ba ne". Fillo ta faɗa tana cire mayafin jikinta ta ajiye, tare da naɗe ƙafarta ɗaya ta ɗora akan gadon gaba ɗaya. Nihal da ke kan kujera tana aikin project a system tace,"lafiyarta fa lau, ko 10minutes bata yi ba da kwanciya, tace idan kin zo ki tashe ta". "ta fita aiki ne yau?". "a'a haka kawai ta tashi da gyaran part ɗin Baffa yau, nace yau dai soyayya ake ji". Fillo tayi dariya tana faɗin,"amma dai kin tayata?". "ina zuwa ma ce tayi in bar mata ɓangaren miji ita ɗaya take so ta sami ladan". shiru ya gimla na kusan mintuna biyar, Fillo ta miƙe taje ta ɗauko basket ɗin abincin, a ƙasa ta zauna ta buɗe ta zuba iyakar wanda zata ci a plate, Nihal ta taso ta zo ta zauna su ka shiga ci a tare. "gaskiya yayi masifar daɗi, no wonder Maama tace ba zata ci komai ba sai kin kawo mata, bari na tasheta yasin tun zafin flask bai jiƙa shi ba". "no barta tayi baccinta please, abu da an kusa la'asar, lokacin sallah nayi za ki ga ta tashi". bayan wucewar mintuna goma hannayen Turaki su ka murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin, ƙafafuwansa suka shigo cikin ɗakin yayin da sanyin Ac ke ratsa shi. ƙwayar idonsa bata sauka akan kowa ba sai Maama da ke kwance kan gado tana bacci. A lokaci guda yaji jikinsa yayi wani irin sakayau tamkar an zare masa lakar jikinsa, abun da bai yi tsammani ba sai yaji yawun bakinsa ya bushe, Me ke shirin faruwa ne?. ya saki handle ƙofar da yake riƙe da shi, ya kasa ɗaga ƙafarsa yana jin wani abu ya wuce ta maƙogwaronsa, wani irin abu mai nauyin gaske, yana jin yanayin bugawar zuciyarsa na sauyawa, yana jin faɗuwar gabansa na ƙaruwa. ya san da cewa don mutum yayi bacci ba wani abu ba ne, dan bacci wani abu ne da ɗan adam ke yinsa a kowanne dare, to amma ba zai iya cewa ga ranar da Maama tayi bacci ba da rana, iyakar tsayin rayuwarsa zai iya faɗin hakan, ko da ace kuwa tana cikin halin jinya ne, baccin rana baya daga cikin al'amarin rayuwarta. to amma yau ɗaya, rana guda, rana ta farko kawai sai ta kwanta irin haka?, ƙarfe ɗaya da rabi na rana, har tayi irin baccin da bata ji buɗewar ƙofar tasa ba, kuma a lokacin da ya san tana zama tayi lazimin sallar azahar?. kawai sai ya ji wani abu ya motsa a ƙasan zuciyarsa, yaji kamar rauni na shirin kama shi, sai dai kamar ko da yaushe a rayuwarsa, yayi ƙoƙarin tattaro dukkan nutsuwarsa da dauriyarsa tare da dakiyarsa, ya maida ƙofar ɗakin ya rufe. "me ya sami Maama?". ya jefa tambayar ga Fillo da Nihal yana tsaye a gefe guda. "bacci take yi, aiki tayi ta gaji". "aiki!?, ina ma su aikin?". "part ɗin Baffa ne fa Hammah, ka san bata barin ƴan aiki su je can". "gajiya bata sakata baccin rana, tasha magungunanta?". "lafiyarta fa ƙalau Hammah, kawai muna zaune muna hira tace bari ta kwanta kafin ta gaban goshinta ta ƙaraso". ya shiga girgiza kansa, ƙafafunsa na ɗagawa da ƙyar, haka ɗaya Maama ba zata yi baccin rana ba, no matter what bata baccin rana, bai yarda da wannan baccin nata ba. "kar ka damu lafiyarta fa ƙalau, ban da yanayin ciwon kai da sai ka tashe ta". kunnuwan Turaki su ka tsinci muryar Fillo a cikin iskar ɗakin. ta karɓi ledojin da ke hannunsa tana ƙara faɗin,"Allah lafiyarta lau, amma idan kana ganin a tasheta ɗin to". "a ƙyaleta?". ya gyaɗa kansa kawai, sannan a hankali ya tafi zuwa gadon, da tafukan hannunsa guda biyu ya kama kan Maama ya gyara mata kwanciyar. ya zauna akan bedside drower yana kallon fuskarta, kamar tayi haske?, kamar kuma ta ƙara yin kyau?, sai yasa hannunsa a saman goshinta ya goge guntun gumin da yake ganin kamar idanuwansa na haska masa. wucewar minti ɗaya!, biyu, uku har zuwa biyar, zuciyarsa ta kasa samun natsuwa da baccinta, saboda haka sai ya kai hannunsa gefen filon, ya shiga dukan filon a hankali yana faɗin,"Maama, Maama, Maama". ya kira sunan sama da sau goma amma shiru bata buɗa idanunta ba. a yanda ya sani, duk tsananin baccin da Maamansa ke yi kiran suna ɗaya ne ya farkar da ita, balle ma ita bata da irin nauyin baccin nan, hasalima ko baccin take aka murɗa ƙofa aka shigo sai ta farka, ko kuma idan taji motsi. dan haka zai iya cewa bai san lokacin da ya miƙe daga kan drower ɗin ba. kuma maimakon zama a bakin gadon kamar yanda yayi niyya sai ya tsinci gwiwoyinsa da zubewa a ƙasa, kafin yaji wani nauyi ya ziyarci hannunsa, irin nauyin da sai da ƙyar ya iya ɗaga shi ya taɓata. "Maama". hannunsa ya sauka akan jikinta da yay sanyi, a yanzu da ya taɓata bai ga ta farka ba, haka bai ji ta motsa ba, sai yaji adadin faɗuwar gabansa ya ninku da kusan kaso tamanin da biyar. sai kawai ya tsinci kansa da shiga tashinta kamar ƙaramin yaro, babu abinda yake da buƙata a yanzu irin ta tashi, ta buɗe idonta, ta kalli cikin ƙwayar idonsa kamar yanda zai kalli tata, ta faɗa masa wannan maganar da tace zasu yi idan ya dawo, bai taɓa jin ya damu da baccinta ba irin yau, bai taɓa jin baccin wani ya tsorata shi ba irin yau, bai yarda da wannan baccin ba, bai yarda da shi ba sam. girgiza ƙafafunta kawai yake yi yana kiran,"Maama, Maama, Maama ki tashi na dawo, kin ce Papaya ta ƙare na taho miki da ita ga shi na siyo, ga takardar scaning ɗin jikokin naki ma na karɓo, su biyu ne kamar yanda kika gan su a mafarki. kuma mun yi magana da Baffan yace za'a buɗe makarantar islamiyar, idan ya so sai a haɗeta da boko, kuɗin da kika ce na kai gidan marayun na kai ga receipt ɗin, amma sun ce na faɗa miki akwai yara guda goma sha biyar da aka kwantar a asibiti, to sai naje asibitin na biya bill ɗin da ake buƙata, waɗan nan yaran ma da aka kai su sudan, sun kira ɗa zu sun ce na faɗa miki result ɗin su yayi kyau, gobe za su sauka a ƙasar nan, sun ce na faɗa miki su na sauka wurin ki za su fara zuwa, su na ta cewa ayi miki godiya su da iyayen su. gwandar a markaɗa ko yanka miki za'a yi?". gaba ɗaya a wani ruɗe yake maganar, kamar dai wanda ya susuce, ya juyo ya kalli Fillo da Nihal waɗanda ke tsaye a bayansa. "Nihal ɗauko wuƙa ki yanka mata gwandar". sai kuma yace da Fillo,"Halima taci faten?". a karo na farko da ya taɓa ambatar ainihin sunan Fillo. "a'a naga tana bacci shiyasa ban tasheta ba". "sauri ki zubo mata Halima, yanzu zan tasheta". kusan a tare Fillo da Nihal suka juya jiki duk a sanyaye, hannayen Fillo na karkarwa ta buɗe flask ɗin ta zuba faten tsakin da yawa, kafin ta yunƙura ta miƙe daga duƙen da take Turaki yazo ya karɓa, karɓar tasa tayi daidai da shigowar Nihal daga ɗauko wuƙar, ta ɓara ƙwallon gwadar ta yi masa wata iriyar rabawa, cikin sauri ta isa ta ajiye plate ɗin akan table ɗin da Turaki ya ɗauko ya ajiye a gaban gadon. har yanzu baya jin mazaunansa za su iya zama akan wani abu, don haka ko a yanzu ma gwiwoyinsa ƙara zubewa suka a gabanta, kafin yasa hannu ya juyo da kwanciyartata saitinsa, ya kalli fuskarta, ya kalli murfin idonta da yake a rufe, sannan ya kai ɗaya hannunsa ya kamo tsintsiyar hannunta guda ɗaya ya riƙe, tare da kai ɗaya hannun nasa ƙasan hancinta. jijiya bata motsi!, haka ma numfashin baya fita!, sai ya ƙara maida hannunsa wuyanta, nan ma beat ɗin dake wurin baya harbawa. ya san akwai suma kuma ya san akwai mutuwa, kamar yanda ya san banbancin kowanne, sai dai baya jin zai iya ɗaukar abin da yake ganin gaskiya ya ɗora Maama a wannan matakin, ba zai iya ba, ba kuma ya jin zai iya. don haka sai ƙafafunsa duka biyun suka tankwashe, yayinda da dukkan hannayensa ke riƙe da nata, a sanda kuma ƙwayar idonsa ta kasa ƙiftawa akan fuskarta. "ba ki taɓa yin bacci me nauyi ba irin na yau Maama, ba ki taɓa ba. tun ina ƙarami ba kya iya baccin rana kawai saboda mu, balle ma har ki sami damar yin me nauyi, amma yau zan bar ki ki huta, ki yi baccinki yanda ya kamata, na san kin gaji ne, zan zauna tare da ke har sai kin farka". a lokacin da yay shiru da maganar, a lokacin yaji tarin ruwan hawaye sun cika ƙwayar idonsa, zubowa suke so suyi ya sani, amma ba zai ba su damar hakan ba har sai abun da yake gudu akan farin cikinsa ya tabbata. shigowar Hajiya Ramla ɗakin yasa shi juyawa ya dubeta, sai ya ganta gaba ɗaya a rikice, cikin irin rikicewar nan da bai taɓa ganinta aciki ba. "Madam, Maaman yara, kar muyi haka da ke, kar kiyi mana irin wannan baccin, tashi haka don haka don Allah Madam". zantukan da Hajiya Ramla ke yi kenan a sanda ta sami zama a gefen Hajiya Madina, sai ta ɗagota zuwa jikinta, sai taji gaba ɗaya jikinta ya saki, jikin Hajiya Madina ya zame daga nata ya koma makwancinsa. ƙafafun Fillo suka tsuguna a kusa da Turaki, ta dafa kafaɗunsa hannuwanta na rawa, sai taji ɗan cikinta ya motsa a lokacin da ya riƙo nata hannun, ya juyo ya kalleta, suka haɗa ido tana ganin abun da bata taɓa gani ba acikin idonsa, ruwan hawaye!, ruwan hawayen da su ka sanya zuciyarta bugawa. lokacin da Hajiya Ramla ta tabbatar da baccin Hajiya Madina ba na farkawa ba ne, lokacin tayi ƙarfin hali da dakiyar kallon Nihal, wacce ke tsaye ta kasa ƙwaƙwƙwaran motsi, idanuwanta duk biyu a waje. "Mum Maama bacci take yi ko me?, suma tayi?, zata farka?, ana ta tashinta taƙi ta tashi". "idan baka saba aiki ba kayi to duk jikinka sai ya mutu, ina tunanin gajiya ce tasata wannan baccin me nauyi, ba sai mun tasheta bamu barta ta huta sosai". sai ta juya ta kalli Turaki, ta ƙara juyowa ta kalli Nihal ta ce,"ina wayata?". "Mum gata nan a hannun ki ai". tsabar ruɗewa ta manta ma da wayar na hannunta, ta shiga contact ta danna kiran lambar Family Doctor ɗin su. yana ɗaga tace da shi,"don Allah ka iso gida yanzu". bayan ta ajiye wayar Nihal ta ce da ita,"Mum wa kika kira?". "Dr Ibrahim ne". sai a sannan Turaki ya ɗago ya kalli Mum, mene na buƙatar likita kuma a wannan lokacin?, idan ya zo me zai yi?. su ka haɗa ido da Mum ɗin, tace da shi,"da yake tace min tana ciwon kai ɗazu, gwara ya zo ya dubata wataƙila BP ɗin ne ya hau ba mu sani ba". ta fita a riki ce, tana sauka ƙasa taci karo da Sameer da Khaleel, sai suka tsaya kallon juna. "da ma ba ku fita ba?". Khaleel yace,"dawowa muka yi, lafiya Mum muka ganki a haka?". "a'a babu komai, ko zaku koma kuga idan Baffa ya dawo?". Sameer ya ce,"yanzu ya kira mu, yace ya kira wayoyin kowa bai samu ba". "to ku tsaya anan ku kira min shi a waya". ta faɗa tana juyawa ta koma saman, Khaleel ya bi bayanta da kallo zuciyarsa cike da nazari da zurfin tunani. a san da Dr Khamis ya ƙaraso, idanuwan kowa na kansa a lokacin da yake wasu dube-dube a fuskar Hajiya Madina, da kuma gwaje-gwajen da yake yi. ban da Turaki da idonsa ke kan Maama kawai, yana jin wani bala'in ruɗani na shigarsa. cikin ƴan mintuna kaɗan Dr Khamis ya gama bincikensa, a sannan ne kuma idanuwan Turaki su ka koma kan likitan, yana kallonsa ya matsa kusa da Mum da Khaleel, wanda yake tsaye cikin ƙarfin hali. ya san dai likitan bayani yake yiwa su Mum, domin yaga bakinsa na motsawa, laɓɓansa na motsawa da harufan da riga ya san ma'anar su. kuma cikin sakanni uku sai ga Hajiya Ramla ta dawo kusa da Hajiya Madina, ta kamo hannayenta ta riƙe acikin nata, kafin a hankali laɓɓanta su tale da furta kalmar,"innalillahi ra'inna ilaihi raji'un, gare shi mu ke kuma gare shi zamu koma". furucin da ya haddasa motsawar zuciyar Turaki sannan ƙarfin bugunta ya ƙaru a lokaci ɗaya. idanuwansa su na kallo Mum ta ɗauki zani ta rufe Hajiya Madina da shi, ta rufeta har fuskarta, ta lulluɓeta da wannan zanin da ta ɗauko a jiya tace musu ta siyo shi ne saboda goyon jikanta. ba zai manta da wannan lulluɓin ba, ba zai manta da shi ba har a bada. sai kawai ya kifa fuskarsa akan ƙirjin gawar, hannunsa na dama kuma ya shige cikin sanyayyan nata hannun na dama. "Maama, Maama, don Allah ba yanzu ba Maama". yay maganar da wata karyayyar murya, a san da yay wannan furucin, a sannan ne hawayen da suka taru acikin idonsa suka sami nasarar gangarowa saman kumatunsa. idanuwansa suka runtse, hoton rayuwar su na tsawon shekaru 27 na haska masa daki-daki, a lokaci ɗaya kuma duk wani sauti na muryarta na amsakuwa acikin kunnensa da cikin kansa, sautin muryar da ya tabbatar ba zai ƙara jinsa ba. ya riga ya sani, faɗar ubangiji ce kullu nafsin zaa’iƙatul maut, Allah ya faɗi hakan har sau biyu a littafinsa me girma, duk wani bawa mutuwa tana kansa, duk wani me rai sai ya ɗanɗani zafin mutuwa, yaro ko yarinya, babba ko ƙarami, sabo ko tsoho. ya sani Mutuwa dole ce, ya san mutuwa akan kowa ta ke, ka aikata sharri ko akasin haka zaka mutu, kana kan aikata daidai ne ko akasin haka, baka san a wani hali za'a ɗauki ranka ba, za mu mutu a yau, ko gobe ko jibi, ko anjima ko yanzu, sai dai dukkanin mu babu wanda yasan a wanne hali zata riske shi, kai dai bawa baka sani ba! baki sani ba! ya sani yin mutuwa ko ambatonta bai da daɗi, amma dole ne sai mun mutu, dole za mu koma ga wanda ya halicce mu, wajibi ne mu amsa kiran ubangijin mu mai son mu, mai ƙaunar mu, mai jiran tuban mu a ko yaushe, dole ne zamu bar duniyar da aka ara mana, haka dole zamu tafi mu bar duk abin da muke so, haka dole zamu kwanta a ƙabari. kana tsaka da jin daɗin rayuwa mutuwa na iya zuwar maka, wani tazo mishi fuj’an, wani ta zo mishi idan yay fama da rashin lafiya, wani tari kawai zai yi, wani atishawa kawai zai yi, kuma da zarar ya furta Alhmadulillah sai Kaga a wannan lokacin an ɗauki ransa, wani yana sallah za'a zare masa rai, wani daga bacci shikenan za'a zare ran, sai dai ya farka ya gansa a ƙabari, gidan da yake na gaskiya, gidan kowa. duk irin son mu da duniya wallahil azim sai mun barta, duk irin so da ƙaunar da muke yiwa juna wallahil azim mutuwa sai ta raba mu, Ya Qadeer kai mana kyakkyawan ƙarshe, Ya Rabbi kasa mu dace duniya da lahira Ya'ilahi! Ya Hayyu Ya ƙayyum, kasa mu mutu muna matsayin mutanen kirki, ba waɗanda zamu mutu duniya da mutanen cikinta na tirr da mu ba, ya Rahmanu kasa kar mu mutu da hakkin kowanne bawa akan mu, don mun san cewa baka yafe hakkin wani akan wani, ya jama'atul musulim mu yafi juna!, mu yafewa junan mu!, kar mu dinga ƙullar junanmu domin ba mu san lokacin da zamu yi tafiya me gaba ɗaya ba. "ta mutu". Khalil yay ƙarfin halin furtawa sauran ƴan uwansa da kowannen su ke tsaye yana so ya fahimci abin da ke faruwa. "Kamar ya ya wai? Mecece mutuwa kuma?". Sameer yay tambayar a rikice. "da ma haka ake mutuwar?, ɗa zu fa muka gama hira da ita ko awa ɗaya ba'a yi ba, haba this is insane, wallahi Dr ɗin nan ƙarya yake, ya za'ai ma Maama ta mutu, me tayi?, laifin me ta aikata?, don Allah Mum a kira wani likitan ya dubata, don Allah a kira wani likitan ya zo ya tasheta". idan ace ba kallon fuskar Nihal suke yi ba, za su rantse da Allah cewa ba ita tayi wannan maganar ba, don kwatakwata muryar ba tayi kama da tata ba, ta fito ne cikin wani amon sauti na ƙololuwar tashin hankali, tana rawa tamkar iska na kaɗata. haka rayuwar take dama, hanya ɗaya ce da ita, ko kabi tafarkin gaskiya ko ka kauce duk dai ƙarshe waje guda kowa yake nufa, alkhairi ko sharrin da kayi kafin ka ƙarasa, shi zai zama shimfiɗa mai kyau ko mai muni a yayin da ka isa, sai dai fatan dacewa kawai. "ka kira Baffan ku ka sanar da shi, sai ka kira min Samha da Zaytun, amma ban ce ka faɗa musu ba". Mum tayi furucin ga Khaleel, wanda yake tsaye har yanzu hawaye sun gaza sauko masa. a wannan lokacin kuwa Nihal na kan gawar Hajiya Madina, tana girgizata akan sai ta tashi, tana roƙon su akan su kira likita me hankali ya tashi mahaifiyarta, ai hirar da suka kwana jiya su na yi baya nufin wasiyya ta bar mata, ita dai azo a tashi Maama, don tace mata a ƙarshen watan nan zata fara yi mata order ɗin kayan kitchen ɗinta. a wannan lokacin kuma Turaki ya iya ɗago da kansa, ya kalli Nihal ɗin sannan ya kuma kallon fuskar gawar, sannan ya ƙara kallon zanin da aka rufe gawar hannun Fillo ke damƙe da shi, sannan ya kai ƙwayar idonsa kan Mum da ke zaune kanta a ƙasa, hawaye na saukowa su na zuba akan kayan da ke jikinta, sannan ya kalli Sameer da ke duƙe ya rufe fuskarsa da dukkan tafukan hannunsa da alama kukansa yake so ya tsayar tukunna ya ɗago ya ƙaryata mutuwar, sannan ya kalli Khalil wanda ke jingine a jikin wadrobe waya riƙe a hannunsa ya ƙurawa gawar ido, gashin idonsa ba ya ko ƙiftawa. a wannan lokacin ne kuma hankalinsa ya fara gaya masa wataƙila zai sauya ma'anar rabuwa ta mutuwa a yau, don baya tunanin akwai abin da zai raba shi da gawar nan da yake riƙe da hannunta, Maamansa ba, babu me raba shi da ita. *BAYAN AWA BIYU.* a cikin wannan awannin, labarin rasuwar Hajiya Madina ya karaɗe cikin garin gombe, da sauran ƴan'uwa da suke na kusa da na nesa. lokaci guda tarin al'umma suka shiga ɓulɓulowa su na sauka a gidan Alƙali Dikko domin yin ta'aziyya, mutuwar da ta taɓa manya da ƙanan yara. cikin gidan ya ɗauki shiru, a zazzaune ake wasu na kukan fili yayin da wasu ke kukan zuciya, domin tabbas anyi rashi, an yi rashin mace mai tsanani son mutane da kyautata musu, mai kirki da sauƙin kai, macen da ke da tsananin kyautatawa marayu, macen da ba'a faɗa da ita acikin mutane in har ba ƴaƴanta aka taɓa mata ba, macen da a tsawon rayuwarta babu wanda ya taɓa buɗa baki yayi kuka da ita, ya kuma ya faɗi aibunta. a wannan lokaci ubangijin da ke da iko da zuciyar kowanne bawansa, shi kaɗai ya san adadin alhinin da ke cikin zuciyoyin ahalin gidan Alƙali Dikko, musamman yaran, waɗanda suka ruɗe da koke-koke, banda Samha da ke ta aikin suma tana farfaɗowa ta ƙara komawa. "an gama yi mata wankan, ku faɗa musu za'a shigo da gawar ciki su yi mata adu'a". "ina Hajiya Ramlan take?". "yanzu ta tashi, Samha ce jini ya yanke mata, ana tunanin ko ɓari tayi". a lokacin wani tsoho ya leƙo parlon yace,"to ina yaran su ke ne?". "Baba Musa gasu nan fa, ku shigo da ita ɗin". ya juya fuskarsa daga waje yana kallon mutanen dake tsaye yace,"sai kun ɗago makarar da kyau fa, yawwa kai ɗan karkata ta can". mutanen maza su huɗu suka shigo parlon da gawar, da yake acan part ɗin nata wasu Kakanninta mata da su Boɗejo suka yi mata wanka. su ka ƙarasa da gawar suka ajiyeta a tsakiyar yaran da ke zaune a ƙasan carpet, wacca Zaytuna ce kawai babu sai Samha da aka yi asibiti da ita yanzu. Baffa ya ƙaraso wajen ya zauna shima, zaman nasa babu wuya kira ya shigo wayarsa, daga can ɓangaren Zaytuna da ke ta kuka tace,"Baffa don Allah kar akaita sai na zo, ya tafi ya nema mana ticket yanzu zamu taso Baffa". "Zaytun kiyi haƙuri kinji ko, ki tayi mata adu'a kawai, idan aka ce za'a jira ku lokaci zai ƙure, kinga magariba na gabatowa". bayan gama wayar ya ɗaga kai yana cewa da Yayar Hajiya Madina,"Asiya kirawo Ramla don Allah, tazo su yi sallamar ƙarshe". "Baffa don Allah ku bar mana ita a haka ba sai an kaita wani wajen ba, mu zauna da ita a haka don Allah". Yayan Hajiya Madina Baba Nafi'u yace,"tun ɗa zu kake ta surutai Sameer, ya isa haka, kai musulmi ne ya kamata ka yarda da wannan mutuwar, batun a bar muku ita babu shi domin binne gawa wajibi ne". "don Allah Baba ku bar ta ko zuwa da safe ne, ƙila fa baccin ne yay mata nauyi da yawa, ko kuma shi likitan ne bai bincika da kyau ba, amma ɗazu mu ka gama hira da ita wallahi, wallahi lafiyarta ƙalau bacci kawai tayi tace idan Saamirawo(sirika Fillo) tazo to a tasheta". Nihal ke maganar duk a gigice. Baba Nafi'u ya ƙara cewa,"ku yi haƙuri kin ji Nihal, duk wani abu da ya ke faruwa tsarin ubangiji ne, namu tawwakali ne da addu'a, don haka ku yiwa mahaifiyarku adu'a". Baffa ya numfasa a hankali ya shiga kiran sunan yaran nasa da sirikan nasa ɗaya bayan ɗaya. "Khalil, Samir, Nihal, Halima, Ilham". sannan ya kalli Turaki daga ƙarshe yace,"Muhammad ku daure zuciyoyin ku, kuyi tawwakali ga Allah, wannan ita ce mutuwar, haka take, haka kowa yake haƙura da ita, haka take riskar kowanne bawa ba sai an shirya mata ba, mu ma nan duk jiranta muke yi. yanzu lokaci na tafiya, mutane na can a waje su na jiran a fita da ita, na san abin da kowannenku yake ji, na san raɗaɗin da zuciyarku ke yi muku. ku yi mata adu'a, wannan kukan da ku ke yi da musawar da ku ke yi ba gata bane a wurinta, zallar soyayyar da za ku nuna mata shi ne kuyi mata adu'a, wannan jinkirin kaita ɗin da ake ba alkhairi bane agareta". Maganar ta Baffa ta doki kunnuwan kowannen su, furucin da yay akan soyayya, sai kawai suka ji su na shuɗawa zuwa duniyar baya, wani lokaci me tsayi da ya shuɗe, kamar haka ne, kamar wannan lokacin su na zaune da ita take faɗa musu... _"ku nuna min soyayyar ku ko bayan raina Ƴaƴana, ina nufin kar kuyi kuka da rashina, adu'a za ku yawaita yi min"._ Turaki

Chapter 68 of 73