Inna".
tana rufe baki Nuratu da Mommi suka iso wajen, dai-dai kuma da miƙewar Turaki. yana tashi idonsa ya kai kan Mommi, ta ke idanuwansa suka firfito waje yana binta da kallo me ban mamaki da al'ajabi, me yake gani?, dama da gaske akwai fuska biyu a duniya?, wannan matar ai photocopy ɗin Fillo ce.
Mommi da ta iso gabansa ta ɗaga masa hannu alamar sannu. mamaki na bala'i ya ƙara kama shi, bai san lokacin da ya kamo hannunta ba ya jata zuwa room ɗin da Fillo ke ciki.
ganin hakan yasa kowa miƙewa yabi bayansu da kallo harta kuwa da Mum da taji su Umma na cewa,"ikon Allah wannan yaron na da lafiya kuwa". Nuratu tace,"ah wannan sai dai mahaukaci". ta faɗa tana bin bayansu da sauri.
Inna Wuro tace,"ah tou haka duk zaku yi ta gamuwa da gamonku, ance aljanu ku ka kwaso kun dage mutanene, ni dai da naga ba zan iya ba ai ta kaina zanyi, wa zai zo ya wahala, haka kawai a shanye ƙafa ko wuya banji ba ban gani ba".
Umma ta dafa kafaɗar Mum dake bin bayan Nuratu da kallo tana jin shigar wani al'amari me girma a tare da ita. a hankali Umma tace,"am sorry to say, amma ɗanki bai da lafiyar ƙwaƙwalwa ko?". Mum ta juyo da kallonta gareta tace,"ɗana kuma?". ta tambaya da mamaki.
Umma tace,"ehh fa, wanda ke zaune anan kusa da ke". kan Mum ya ƙara ƙullewa tace,"me kike son cewa ne?". ta tambaya tana jin ƙirjinta na bugawa.
jin ƙarar saukar mari ya tattara hankalinsu kan su Turaki gaba ɗaya, Nuratu ce a gabansa tana huci tana faɗin,"baka da hankali ne?, ya daga ganin mahaifiyata zaka kama hannunta, ko an faɗa maka mu kafirai ne kamarka?, shashashan banza da wofi, to wallahi in baka bar asibitin nan cikin gaggawa ba sai nasa ƴan sanda sun zo sun tafi da kai yanzu".
Turaki ya ɗago da fuskarsa yana dafe da kuncinsa, hoton fuskar tasa ya shiga cikin ƙwayar idon Hajiya Ramla da suka ƙaraso wajen da sassarfa. cikin zafin nama Turaki ya ɗaga hannu zai saukewa Nuratu zazzafan mari Hajiya Ramla ta zaro ido waje tana faɗin,"Babana". ta faɗa da ƙarfin sautin da yay amsa kuwa a wajen.
Turaki yaji saukar muryar a cikin kunnensa, yaji shigar sunan acikin kansa da cikin zuciyarsa, daga jin muryar kasan muryar babbar macece, amma hakan ba shi zai hana shi gane mamallakiyar muryar ba, ba shi zai hana shi gane muryar kowa ce ba a duk inda ya jita, tsawon shekaru da yawa ba tare da suna tare ba, hakan ba zai hana shi gane muryar wadda ta kawo shi duniya ba, da wayonsa ta tafi dan haka a ko'ina kuma a kowanne hali yaji voice enta zai shaida.
sai dai kafin komai dake cikin kansa ya gama wanzuwa sai ganin Hajiya Ramla yay a gabansa, ganin nata kuma ya firgita shi sau ɗaya yaja da baya, sai kuma ya dakata yana binta da kallo ƙwayar idonsa duk a waje.
an ɗauki tsayin shekaru da yawa, sai dai duk tsayin shekaru da dogon zamanin da zata ɗauka ba tare da ƴaƴanta ba, hakan ba zai hana tana kallonsu ta shaidacewar su ɗin jininta ba ne, kamar yanda shima ba zai taɓa manta mahaifiyarsa ba, babu tantama wannan ɗanta ne, haka shima yake jin babu tantama wannan wadda ta kawosa duniya ce, ɗanta ne wanda ta tafi ta barsa a lokacin da yake shakaru shida a duniya, kamar yanda shima yake ganin uwassa wacce ta tafi ta barsa lokacin da yake da shekaru shaida a duniya.
sai kawai ta fashe da kuka, Turaki ma da yay mutuwar tsaye ya fashe da kukan farin ciki, ya taho da sauri ya rungumeta yana faɗin,"Mum, Mum are really the one?, da gaske idona ba gizo suke yi min ba?, Mum ina kika tafi?, ina kika je Mum?, me yasa kika tafi kika barmu?, laifin me muka yi miki Mum?".
maganarsa ta katse, kukan tsananin murna da farin cikinsa ya ƙaru. ya janye daga jikinta yana daɗa kallonta, daga shi har ita babu wanda zai iya kwatanta irin abinda yake ji a tare da shi. kallonta yake sosai da irin wannan tsananin so da tausayin da Allah ya halicce shi na daban a tsakanin uwa da ɗanta.
Hajiya Ramla na hawaye ta kai hannunta ta kama fuskarsa, ɗayan kuma ta dungure masa kai fuskarta ɗauke da tarin murmushi, tace,"babu Alhamdulillah sai wannan tarin tambayoyin Babana".
bai iya cewa komai ba, haƙoransa duka suka bayyana a waje kamar yanda nata ma suka bayyana, ya kuma rumgumeta sannan yace,"to Mum na faɗa Alhamdulillah...then you too should answer my questions".
Hajiya Ramla ta ture shi daga jikinta tana cewa,"to ba zan amsa ba ɗin, in kuma ka zama Me girma Turakin Taraba sai in ji". ta faɗa da irin salo na wasa dake tsakanin uwa da ɗanta. ta kamo hannunsa tace,"where is Zaytun?".
ya kasa ce mata komai, kawai sai ya ƙara rungumota yace,"to Mum aina kika ɓuya?, there are alot of questions but ki fara amsa min wannan".
tace,"Babana muna gaban mutanene fa". ya zare jikinsa anata ya kama hannunta yaja ta zuwa wajen kujeru dake wajen ya zaunar da ita. shi kuma ya zube gwiwoyinsa a ƙasa tare da kwantar da kansa saman cinyarta yana kamo hannunta duk biyun ya riƙe su da kyau kamar wanda za'a ƙwaceta.
daga ita har shi babu wanda ya iya cewa komai, hannunta a sumar kansa tana shafawa, shi murmushi ita murmushi, haƙoranta a waje nasa ma a waje. jinsa yake kamar ya buɗe cikinta ya koma ciki, haka itama ji take kamar ta tsaga ƙirjinta ta sanya shi a ciki, kowanne da maganar da yake son yi amma tsananin farin ciki da murnar da suke ciki ya ha rufe bakinsu.
idon kowa dai tuni ya dawo kansu, aka bar batun Fillo da halin da take ciki, basu san tuni ta farka a lokacin su Dr Yusuf su kai kanta, kuma lokacin da zai shiga ɗin ne ya kama hannun Mommi ba tare da sanin kowa ba da hankalisu yay can kan su Turaki ba ya shiga da ita ciki ya tsayar da ita dai-dai saitin da idanuwan Fillo na buɗewa zasu sauka akanta.
Hajiya Ramla tace,"Babana am asking you where is Zaytun?". ya ɗago da kansa ya kalleta kawai sai ya ƙara rungumeta.
a lokacinne kuma wayarsa dake aljihu tayi ƙara, yace,"Mum ɗauko ki min picking ba zan iya sakinki ba".
ta zaro wayar daga aljihunsa tana bin sunan dake yawo a jiki, kamin tace masa,"Beta Half". yace,"pick". tace,"my daughter inlaw right?".
sai ya saketa ya karɓi wayan yana wani murmushin na daban, ya shafo kumatunta yace,"you will soon meet her". ya faɗa yana miƙewa tsaye still holding her hand ya juya yana kallon kowa dake kallonsu, idonsa ya sauka akan Inna Wuro da ta saki baki tana kallon film ɗin da zuciyarta ke raya mata shi take kallo. ya saki hannun Mum ya isa wurin da take bakinsa gaba ɗaya yaƙi rufuwa, yana zuwa da sigar tsokana yace,"tsohuwa aron ɗan kwalin kanki".
da sauri kuwa Inna Wuro ta kunto Farha dake bayanta ta jefa masa zanin goyon tace,"komai ma ai sai a baku girmaku ne".
ya karɓa ya juya bayan yace mata,"Thanku, zan baki tukwici after". ya isa wajen ya rufe fuskar Hajiya Ramla da zanin sannan ya zauna kusa da ita yace,"stay quite har inje in dawo kinji". tai masa knodding kanta kawai tana binsa da kallo da jin soyayyar nan ta ɗa na fizgarta.
ya miƙe kenan sai ga Hajiya Madina ta iso wajen hankali a tashe, tana ganinsa ta yo kansa a rikice, za tai magana expression ɗin da take gani a fuskarsa yasa ta tsaya tana ƙare masa kallo. kafin ta ɗauke idonta daga kansa da mamaki tabi mutanen wajen da kallo ɗaya bayan ɗaya, sannan ta ƙara kallonsa tace,"mene haka a fuskarka?, Fillon ta farka lafiya ne?". ya kamo hannunta yace,"insha'Allahu lafiya zata farka, yanzu just close your eyes i want to show you something".
tace,"in rufe idona?, ka nuna min me?".
ya zagaya ta bayanta yace,"suprise". sannan ya ɗora haɓarsa kan kafaɗarta yana fuskantar da ita wurin da Mum ke zaune yace,"gidan da kika gina a Ausburg nake so a matsayin tikwici". tace,"na ma baka Me Babban suna, amma ni dai barni in buɗe idona inga halin da yarinyar mutane ke ciki, ni ce silar condition ɗin da take ciki, so this is not time for joke, kaima ɗin mamakinka nake".
ya saketa yana faɗin,"indai kika buɗe ban ce ba isn't a suprise, kuma sai na doka miki yaji".
Hajiya Madina tai shiru ƙirjinta sai duka yake, Turaki ya ƙarasa wurin Hajiya Ramla ya ɗauke zanin daga saman fuskarta, sannan ya ɗora hannunsa a kafaɗarta ya kwantar da gefen fuskarsa a gefentata, Hajiya Ramla tabi Hajiya Madina da kallo tana jin wani irin shauƙi na kewar ahalinta da tayi, tana tuna irin rayuwar zaman lafiya, jin daɗi da kwanciyar hankalin da sukai da Madina.
Hajiya Madina na yin kalar tausayi har sannan idonta a rufe tace,"Me babban suna kai ka taɓa saɓa umarnina, amma ni ba zan iya saɓa naka ba, but ai na san kana jin tausayina ko?, to mu jingine wasa gefe kaji ɗan albarka".
muryarsa na fita da wani emotions yace,"gidan da ke Ausburg Maama". tace,"naji nace maka, muna komawa gida zan baka takardun".
yay murmushi me kama da dariya ganin duk yanda ta ƙosa yace,"promise?". tace,"i do, har ma da key ɗin sabbin motocina guda biyu duk na baka".
yace,"zanyi kyauta ne da su nima".
tace,"tunda na riga na mallaka maka ikonka ne kai duk yanda kaso da su, can i open my eyes now?".
yana dariyar jin daɗi ƙasa-ƙasa yace,"not now, untill i say".
kawai sai yaga ta buɗe idon, Hajiya Madina ta buɗe idon da niyyar kai masa duka ganin yau yana neman mayar da ita wata yarinyarsa abinda basu taɓa yi ba, ƙwayar idonta ta sauka akansa sai kuma ta mayar da kallonta kan fuskar da take ganin kamar gizau a kusa da shi.
in ace da abinda yafi mamaki tabbas ta shiga cikinsa, ta ƙara buɗe ido tana kallon Hajiya Ramla dake ta mata murmushi, ta ƙwala wata ƙara tace,"Your Excellency are you really the one?". ta faɗa bakinta na ƙin rufuwa tana ganin hakan kamar a mafarki. sai kawai tai sufa taje ta rungume Hajiya Ramla tana faɗin,"Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah". ta faɗa tana ɗagowa daga jikinta ta shiga duddubuta wai ganin dai kamar ba dai-dai take gani ba.
a lokacin ne kuma su Zaytuna suka ƙaraso wajen, abinda kowa ya gani yasa suka tsatstsaya da mamaki suna kallon Maama da tabi ta susuce saboda tsabagen murna. Maama ta waigo ta kalle su tace,"ubangiji yaji kukanmu ya amsa adu'armu ya dawo mana da Mum".
ai kan kace me wannan asibiti ya karaɗe da ihun murna, duk suka tafi da gudu suka faɗa kan Hajiya Ramla suna ta ihu, wanda in ace a tsaye ta-ke sai sun kaita ƙasa.
Zaytuna ce kawai ta tsaya taƙi zuwa wajen tana kaudar da fuskarta da gefe, dan ita bata ganin zata yi farinciki kamar yanda bata tunanin zata yafewa Mum. Ilham kuwa na tsaye daga gefen su tana ta kallon su cike da burgewa, musamman Turaki da ta kasa ɗauke idonta a kansa saboda yacca ta-ke ganin haƙoransa gaba ɗaya a waje, da irin tarin farin ciki da annurin da bata taɓa ganinsa ba aciki. a ɗazu hankalinta duk a tashe yake da bai dawo gida ba, haka da taji wurin kidnappers ya tafi hankalinta ya ƙara kaiwa ƙololuwar tashi, but a yanzu zata iya cewa kamar tana jin kanta ne a saman gajimare tana tafiya, ko ba komai tasan lokaci yayi da zata samu wannan gurbin da Turaki ke cewa ba zata same shi ba a zuciyarta, ta sani wuyarta mahaifiyarsa ta san ita matarsa ce, ita kanta bata san Mum ba dan ba'a haifeta ba lokacin, amma kallo ɗaya ta yiwa Mum ɗin tasan itace mahaifiyarsu da kowa ya taso a family yake jin labarin ɓatanta.
a taƙaice dai Maama da iyalanta duk sai suka manta da batun wata Fillo saboda tsabagen farin cikin da suke a ciki. kuma haka suka zama ababen kallo a wajen dan tuni akai caa akansu ana kallon ikon Allah.
gaba ɗaya sun cikwikwiye Hajiya Ramla sun kasa jin ma abinda ta-ke cewa na,"ina da patient kuyi a hankali". but inaa duk wannan batu da take yi babu wanda ya jita hatta Turaki dake manne a jikinta.
kuma a lokacinne Kaka suka shigo ita da su Yami da Khalil waɗanda yaje ya ɗauko daga asibiti, sai dai me?, zuwan su wajen kawai suka ga Fillo a guje ta fito tana ƙwala kiran,"Kaka ga Ummina, Kaka Ummina ta dawo".
_ayi haƙuri nayi late, azumi nai na kasa motsi after ansha ruwa._
*Vote, Comment, and Share.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_😂😂yau dai ina typing ina gyangyaɗi, so duk baragadar da ku ka ci karo da ita ku gyara da kanku kawai🤣🤣._
*37*
gaba ɗaya Fillo sai ta rikice ta firgice ta nemi fita a hayyacinta, ba don komai ba sai dan tsananin murna da kuma mamakin ganin mahaifiyarta a lokacin da bata tsammata ba, tsabar farin ciki ji take kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha. ganin komai ta ke yi tamkar mafarki ko kuma ba daidai take gani ba, lokacin da ta farka da matsanancin ciwon kai ta tashi, amma buɗe idon da zata yi ƙwayar idanunta suka sauka akan Ummi dake zaune a gefenta ta kama hannunta ta riƙe tana hawaye.
da farko tai zaton gizau idonta yay mata, dan haka tai saurin maida murfin idonta ta rufe sannan ta ƙara buɗewa, kuma a wannan buɗewar ne ta tabbatar da abinda ta gani ɗin gaskiya ne, Umminta ce a gabanta, wannan macen da tafi gwal, tafi zinare, tafi lu'u lu'u girma da daraja, wannan macen ce da bata da tamkarta a duniyarta, tauraruwar da ke haska duniyarta, mahaifiyarta ce mafi soyuwa a ranta, jarumar da tai fama da rainon cikinta tsawon watanni tara, jarumar macen da ta tsaya tsayin daka akan ibadarta da iliminta da kuma tarbiyarta, jarumar macen da ke sadaukar da farincikinta domin ƴaƴanta, jarumar dake ɓoye zafin ciwon rashin lafiyarta gudun tashin hankalin ƴaƴanta, jarumar uwar da ta kan iya haƙura da loma ɗaya na abinci da zata sa a bakinta ta rabarwa ƴaƴanta, tabbas itace, ba zata mantata ba ko da ace tana cikin ciwon hauka ne, har a naɗe duniya ba zata kasa gane ɗumin jikinta ba, ba zata manta wannan farar fuskar da bata iya bacci ba har sai ita tayi, abu ɗaya da ta san yake dahir shine uwa dabance, daban take da kowacce irin halitta a duniya, soyayyarta dabance da ta kowa, ƙaunarta ma haka, mahaifiyarta itace ranta itace jininta itace duniyarta.
hawaye ta dinƙa ji yana bi ta gefen fuskarta, dama tasha faɗawa Kaka cewar Ummi bata mutu ba tana raye, kuma da izinin Allah zamu gana da ita, sai ga shi yau ta ganta, sai ga shi ta ganta a ranar da wani macuci, azzalumi ya dasa baƙin ciki a zuciyarta wanda ba zai taɓa gogewa ba, to mai ma zai ci gaba da zamar da wannan baƙin cikin alhalin ga mahaifiyarta ta dawo a sanda take tunanin babu me iya share mata hawayen baƙin cikin da Amir ya haifar mata?, ai babu wani sauran baƙin cikinsa kuma, ta san in ace bata sami ganin mahaifiyarta ayau ba, to tabbas baƙin cikin abinda Amir yayi mata shi zai zama ajalinta.
zata iya cewa bata san lokacin da ta yunƙura ta miƙe zaune ba daga kwancen da take, jinta tayi kawai ajikin Ummi tayi mata wata tsatstsaurar runguma, Ummin ma ta kewayeta da dukkan hannayenta tana daɗa matseta a jikinta, Fillo taji saukar wannan ɗumin na daban wanda ajikin uwa kawai aka halicci yana ɗumama jikinta, tana jin wannan soyayyar mahaifiya ta daban tana ratsa jini da sassan jikinta, sai kawai suka fashe da kukan farin ciki a tare, babu wanda ya lallashi wani acikinsu har sai da suka yi me isar su tukunna.
cikin muryar kuka tace,"Ummina ina sonki sosai".
kuma abinda taji Ummin ta fara ce mata shine,"Auta wa ya kawoki nan garin?, me ya sa me ki haka?". ta tambayeta ɗin tana janyeta daga jikinta tana dubanta, tana yi mata kallo me cike da tausayi da kuma fargabar abinda bata fatan ya kasance a rayuwar ƴarta, domin tasan rashin uwa a tare da ƴaƴanta babu halin da baya jefa su, balle kuma su da basu yi sa'ar uba ba, wanda ko kallonsu ba yayi balle ya kula da rayuwarsu.
a lokacin sai kawai ta faɗa ƙirjin Ummi tace,"Ummi kullum sai nayi kukan rashinki, Ummi ko me nake yi tare dake nake yinsa a zuciyata, Ummi duk sanda naga ƴa da mahaifiyarta sai nayi ta kuka in kasa ko da cin abinci. Ummina me yasa kika tafi inda ba zamu ganki ba?, me yasa baki ci gaba da wannan haƙurin naki ba?, me yasa kika bari takaicin ɗa namiji da baƙin cikinsa yasa kika nesanta kanki da ƴaƴanki da kowa naki?, Ummi kin san kuwa tsananin son da nake miki?, muna fa yi miki so me zafi, Ummi kin san buƙatar rayuwar ƴaƴa shine mahaifiyarsu, amma mu sai kika ƙaurace mana na tsawon shekaru da yawa, Ummi ba kiyi tunanin in ta gayyara ba?, ba ki yi tunanin...".
bata ƙarasa ba Ummi tasa hannu ta rufe mata baki, hawaye na zubar mata tace,"tambayar da nayi miki daban, zancen da kike min daban".
Fillo ta ƙara matseta tace,"kiyi haƙuri Ummina". tace,"ban san amsar tambayata".
Fillo ta rumtse ido tace,"ai tun sanda kika tafi na dawo wurin Kaka. wannan halin da kika ganni a ciki kuma wanda zan aura ne sila".
lokaci ɗaya jikin Ummin ya hau kyarma ta ɗago Fillo ajikinta tana bin ta da kallo tace,"ya zamo silar me?, me yay miki?, ina Kakan?". tace,"garkuwa yayi dani Ummi after all na basa dukkan yarda".
ta faɗa tana fashewa da kuka sosai, muryar Ummin ta fita a hankali da cewar,"ina fatan bai cuce ki ba?".
bata iya amsawa da baki ba sai Kai da ta ɗaga kawai. anan taji Ummin ta sauke ajiyar zuciya me nauyi, kafin ta furta,"Allah ya daɗa kare min ke, ya kareki daga sharrin duk wani abin ƙi. dan Allah kiyi haƙuri ƴata da abinda nayi muku, ban da bakin ce muku komai domin nasan ni ɗin me laifi ce, amma yanzu na dawo gareku sai mutuwa ce zata raba mu, ina roƙonku dan Allah ku yafe min, ki yafe min Autata".
Fillo tace,"ni ba kiyi min komai ba Ummina".
sai ta ɗago kai tana kallon Ummin tace,"Ummi to ya akai...". kuma karantar fuskarta kawai Ummin tayi ta bata amsa ba tare da ta ƙarasa ba.
"Dr Yusuf, shi ya shigo da ni nan yay min nuni da ke, shine sabon ɗan da Allah ya bani wanda ya kula da ni shi da matarsa kusan shekara guda, ba ƙyama, ba hantara, sun ɗaukeni kamar mahaifiyarsu, duk da ni nayi musu laifi na ɓoye musu cewar ina magana tsawon lokacin da muka ɗauka, haka nayi ta wahalar da su da aikin rubutu a takarɗa kuma basu taɓa ƙosawa ba".
maimakon kallon Ummi sai Fillo ta koma kallon Dr Yusuf, babu ko ƙyafta ido, kenan shisa watarana da yazo hira wajenta yace mata yana ganin me kama da ita sak, in ace zata yarda da ya kaita ta ganta, tave masa ba wani nan wasa yake yi, ashe Umminta ce ma, Umminta ya taimakawa har yake kyautata mata da irin halin karamcinsa.
_"sun ɗauke ni kamar mahaifiyarsu"._ haka Ummin ta faɗa, ƙwarai yau ta ƙara tabbatar da cewa Dr Yusuf na musamman ne, kuma ya zama dole ta saka masa da taimakon mahaifiyarta da yayi, kamar yanda ta san cewa yafi ƙarfin duk wani abu da zata basa, haka bata san irin kyautar da zata yi masa ba domin nuna masa godiyarta, but zata tambaye shi kyautar da yake so tayi masa ko da ace za'a kai ga matakin da sai ta ɗaga zoben azurfarta ta siyar.
Dr Yusuf ya sakar mata murmushi, itama ta mayar masa tana sauke idonta ƙasa tace,"Ubangiji Allah yay maka sakayya da gidan aljannah akan taimakawa Mahaifiyata da kayi, Allah ya rabaka da iyaye lafiya"...haka ta dinƙa jera masa adu'a kafin tace masa,"dan Allah Dr a wurin da ku ka tsinto ni ba kuga wata mata ba?".
Dr Yusuf yace,"ai ba tsinto ki mukai ba, kawo ki akayi". ta ɗan dube shi da mamaki tace,"bai gudu ba?". yay murmushi kafin yace,"ƙanina ne yanzu haka yana waje tare da su Daddy nah, itama matar da kike magana tana waje, ƙila zuwa yanzu ma su Kaka sun iso dan anyi musu waya tuni".
ai rufe bakinsa kenan t a saki hannun Ummi ta diro akan gadon tana ce da Ummi,"ba inwa Kaka albishir".
bata jira cewarta ba ta fito da gudu daga ɗakin tana ƙwala wannan kiran sunan na,"Kaka ga Ummina". ba tare da ta lura da jama'ar da suke cike a wajen ba balle tabi ta kan dalilin da yasa akayi wannan dandazon.
kuma cikin sa'a tana fitowar tayi karo da su Kaka na shigowa, idonta a rufe ta doka wani uban tsalle ta ɗafe Kaka tana ihun murna tana faɗa mata Ummi ce.
Kaka lamarin sai ya nemi ya bata tsoro dan sai take ganin kamar ko Fillo ta samu matsala ne, ta tafi zata faɗi dalilin ɗafe jikinta da Fillo tayi sai taji an saurin riƙota ta gefe.
Kaka ta fashe da kuka tana cewa da Fillo,"Fillo ashe dama Amir ne ya ɗauke ki, ashe yaron nan ba mutumin arziƙi ba ne, ashe Amir azzalumin bawa ne, ashe duk wannan kyawun halayyar tasa yardararmu yayi saboda cimma wata manufa tasa, ashe baƙin *BIRI* ne shi ya *LULLUƁE* kansa ta yanda ba zamu shaida mugun ƙudurinsa ba, Allah ya isa tsakaninmu da shi, ko yafiyarmu kaɗai ta ragewa Amir shiga aljannah ba zan yafe masa ba, sai Allah yay mana hisabi da shi, kuma insha'Allah sai yaga sakayya, sai ubangiji ya bi mana hakkin cutarmu da yayi tun anan duniya. yanzu muna kan hanya Khalil ya ɗauko mu ance an kawoki asibiti rai hannun Allah muka ji sanarwar an kama waɗanda sukai garkuwa da ke, wallahi tallahi ban shaida muryar matsiyacin ba sai Yami ce ta shaida, sai kuma da naji an ambaci sunansa, yanzu haka ance gobe za'a kai su kotu Hajiya Madina tace sai yayi zaman gidan yari".
sai ta fashe da kuka sosai tana ƙara cewa,"yasa na siyar duk da wani abu da ku ka mallaka a wajen mahaifiyarku, sai da ya tsiyatamu tass Fillo, biyar ɗin kanmu bamu da ita a yanzu, yasa muka ɗauki dukkan yarda da amana muka ba shi?, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, gaba ɗaya tsoron kowa nake yi Fillo, ta ya yanzu zaka iya tantance fuskar mugun mutum da ta mutumin kirki bayan mugwayen na amfani da fuskar mutanen ƙwarai?, Allah ya tawarwatsa rayuwar mutane irinsa a duk inda suke, adu'ata ɗaya Allah yasa bai lalata miki rayuwa ba".
Fillo ta zame daga jikinta, tasa hannu ta goge hawayenta tace,"bai ida mugun nufinsa ba Allah yaɓullo min da hanyar guduwa, Kaka bana son kukanki dan Allah ki daina, ki manta da zaluncin da Amir yay mana ki barsa da Allah, indai duniya ce ga shi gata nan, yau ba ranar kukan baƙin ciki ba ce ranar kukan farin ciki ne, irin wannan hawayen nawa nake so kiyi ba irin wanda nayi a sanda na san cewar Amir Birin da ya lulluɓe kansa da mayafin da ba mai iya ɓata shi bane. Ummi ta dawo Kaka, Allah ya bayyana mana ita, dan haka ki kalla gabas ki yiwa jalla wa'azza godiya".
Kaka bata bar kukan ba tace,"ke wai kina hauka ne, a ina kika ga wata Ummi?".
Ummi dake riƙe da Kaka ta gefe ta kwanto a kafaɗarta tace,"gani Dada".
"Halimatu". Kakan ta kira Ummi da mamaki matuƙa. "na'am Dada". sai Kaka ta rungumeta tana hawayen farin ciki itama,"Halimatu ina kika je?, dama kina raye Halimatu?, ƴata na yafe miki domin nasan ba komai ya saki barin gida ba sai baƙin cikin mugun miji, amma tsayin wannan lokaci ina kika shiga Halimatu har na ganki haka lafiya ƙalau?, kai Allah maji roƙon bayinsa".
Ummi tace,"tashin farko Kawu Nasir ne ya bani goyon baya harma ya ɓoye ni a gidansa, daga nan labarin da yawa, amma waɗan can mutanen da kike gani ɗansu ne
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 39 Chapter of 73