ba don tana jin yunwa sosai, ga shi kuma girkin ya burgeta, ƙamshinsa kawai taji tasan girkin Adda Zaytuna ne. tana cikin ci taji ƙarar buɗe ƙofa, tun da ta hangosa ta wutsiyar ido tayi mugun tsorata da sauri ta ajiye spoon ɗin ta kama jan yatsunta.
ya dawo ya zauna a inda ya tashi, ya kalla plate ɗin abincin tukunna ya kalleta yaga yanda take ta raba idanu, yaja tsaki cike da takaici. zai ɗaga murya sai kuma yay controlling kansa, calmly yace,"du ka za ki cinye, ke kika zuba ai ba wani ya zuba miki ba...finish eating and take your drugs".
ya faɗa yana jefata mata ledan magungunan.
ta ɗan kallesa taga baya kallonta tace,"idan na cinye to zaka barni na tafi?".
yace,"idan kin biyani abinda kika fasa min ba. ko an faɗa miki da kuɗin banza aka saya". tace,"insha'Allahu zan biyaka amma ba irin wancan ba, sai dai wani daban, Kaka bata da kuɗin wancan".
yay mata shiru, tana ɓata rai tace,"kuma ni lafiyata lau ai". ta faɗa tana ture ledan maganin daga kusa da ita.
sai da ta cinye abincin da ta zuba tass sannan ta miƙe ta wuce toilet ta wanko baki ta dawo, ta ɗauke plate ɗin ta ɗora akan table. kamar bada ita yake ba yace,"ba da kuɗin banza na sayo su ba, ɗauki kisha".
ba don komai ba sai saboda gudun kar ya sakar mata tsawa ko kuma yay mata wannan kallon da bata so tayi saurin ɗaukan maganin tasha, tana sha tana hawaye, bata miƙe ba sai da taci kukanta duk yana jinta amma bai ko kalli inda take ba.
bayan ta gama kukan ta zagayo ta gabansa ta zube duka gwiwanta biyu a ƙasa, ta haɗa hannayenta waje ɗaya alamar roƙo tace,"dan darajan Allah kayi haƙuri, kaga dare yayi Kaka na can tana jirana. kuma nasan Maama zata neme ni".
ta faɗa sabon kuka na taho mata, amma sai ta danne shi. Turaki yaci gaba da kallon wayarsa, kamar ba zai yi magana ba can sai taji yace,"thank you for saving my life which you have done so many times. but i want to ask you something and please you tell me truth".
furucinsa ya bata mamaki matuƙa, how does he knows that?, zuciyarta ta ambatar mata sunan Maijidda, ita kaɗai tasan wannan sirrin nasu.
to amma!...sai ta ɗago kai don kallonsa ƙirjinta na bugawa, gani take kamar maganar da yay ba da ita da yayi ba, ganin waya ce kare a kunnensa yasa ta sauke dogon numfashi, hakan ya shaida mata ba da ita yake magana ba.
cikin wayar da Turaki yake da Bello ta faki idonsa ta ƙarasa zaro key ɗin da ya leƙo ta aljihunsa ta yanda ba zai ji ba, ga mamakinta harta miƙe sai taji ya riƙe hannunta gam.
ta rumtse ido kamar zata yi kuka, ganin za tai magana yay saurin ɗora yatsansa saman lips ɗinsa alamar tai shiru. hakan yasa tai gum tana bo ne fuska. bayan ya gama wayar ya dubeta, tai tsaye ta rufe idanuwanta gam ko motsi taƙi yi tunda ya riƙetan. tsoronta Allah tsoronta kar yaga key ɗin motarsa da ta ɗauke, dan a second fitarsa ta ɗauke tasa acikin rigarta.
taji yace,"ni zan shanye sauran maganin?". ta buɗe ido ta ɗauki ledan da yay mata nuni da shi, cike da ƙaguwar ya sakar mata hannu.
tace,"wa zan kaima?". yana sakin hannunta yace,"ki wuce da shi". tace,"ina?". yace,"duk inda kika ga dama".
tana hararsa ta ƙasan ido tace,"ƙofan a rufe yake".
ta faɗa tana yamutsa fuska. ya miƙe yaje ya buɗe ita kuma ta fice da gudu, wannan gudun nata kuma yasa shi sakin gajeran murmushi yana girgiza kansa.
cikin sanɗa ta fita daga side ɗin nasu gaba ɗaya, ko tsayawa ba tayi ba a compound tayi ɓangarensu dan bama taso su haɗu da Maama a yanzu, sai safiya kuma.
sai after take jin wani mugun ƙamshi me shegen daɗi na binta, ta dinƙa jan hanci tana so taji daga ina ne, sai da ta shinshina jikinta taji ƙamshin a jikinta yake. tsabar daɗin ƙamshin nunfashinta har kusan sarƙewa yayi, tana tafe tana lumshe ido har ta kusa zuwa ɗakin Yami. aina ta samo wannan ƙamshin to?, ƙamshin da zata iya ce duk duniya babu ƙamshin da ya kaisa daɗi.
idanuwanta a lumshe ta ƙaraso ƙofar ɗakinsu, lokacin Maijidda ta fito daga ɗakin suka yi karo da juna. Maijidda ma taja hanci tana shaƙar ƙamshin tare da cewa,"kai Fillo wannan ƙamshin fa?".
****
Boɗejo dake zaune kan kujera a babban parlon Mai Martaba tace,"ah tou ni ɗin dai na gama magana...idan kuma kun lalace ne to sai naji, amma batun auren Ilham da Ɗan'uwanta wancan kumburarren babu wanda ya isa ya hana sai dai ko bayan raina, sai in kuma ikon me sama".
Mai Martaba ya sauke numfashi yace,"amma Hajjah...". da sauri ta katse shi,"Hashim kai kaɗai ne me shegen taurin kan da ba zaka tuba ka daina kirana da Hajja ba ko?, kasan Allah karka bari raina ya ɓaci akanka, ya nazo ina batun haɗa yara aure kana ce min ba haka ba yanzu kuma kana ƙara kirana da sunan da kasan bana so".
cikin kwantar da murya Mai Martaba yace,"kiyi haƙuri".
Boɗejo ta ƙara haɗe rai tace,"ka riƙe haƙurinka. muyi batun da ya kawoni wajenka, ba tun yau nake faɗa ba sai dai zan ƙara nanatawa ina so ku haɗa Muhammadu da Rumana aure, in kuma ban isa ba sai inji".
Baffa ya ɗago kai ya kalleta yace,"balle ma kin isa Boɗejo, sai dai kawai ya kamata ayi duba a lamarin, tunda bamu san ba ko su yaran nan zasu so haɗa su auren da za'ai".
Mai Martaba yace,"abinda nake so ki fahimta kenan Mama, zamanin yanzu ba ɗaya bane da na da, yanzu ba'a haɗa yara aure gudun abinda ka iya zuwa ya dawo a zamantakewar tasu muddin babu soyayyar junansu, amma kuwa idan aka tabbatar da yaran nan suna son junansu shikenan salamun alaikum mu kanmu ba ƙaramin farinciki zamu yi da hakan ba".
Boɗejo ta tafa hannu tana salati kafin tace,"na shiga uku, Hashim yanzu al'adar tamu zaka rushe?, kai kasan a yanda akayi aurena da ubanku kuwa?, tabɗijam, to da kasan ta yanda aka laliƙa min ubanka na aura da baka zo min da wannan ƙabali da ba'adin ba...shashashan sarki kawai, kai idan akai hakan ma ba ƙarfafa zumunci akayi ba, amma kana batun wani idan basa son junansu, a'a to da ƙiyayyar junansu suke yi?, ko an faɗa muku su irin ƴan'uwan mahaifinku ne kafin su tuba, kai gaskiya Hashim kana da gurɓataccen tunani, wai idan basa son junansu!, maganar nan naka har ga Allah yayi min zafi, to karka ƙara wallahi, don ni dai kaf jinina babu me mugun hali, kowa son ɗan'uwansa yake yi...tsakani da Allah ina Turaki zai ce baya son Ilham ƴar'uwarsa?, kuma itama ta ina zata ce bata sonsa yarinyar da kullum zancenta akansa yake, babu fitowar rana da faɗuwarta da ba zata ambaci sunansa ba, dan ma dai waccan uwar tata me baƙin hali da mugun nufi na hanata zumunci da shi, to a gaskiya indai ana so aga dai-dai abi umarnina kawai, auren nan yinsa za'ai babu wani zaman tuntuɓe-tuntuɓe balle asa jinina ya hau".
Mai Martaba zai yi magana ta ɗaga masa hannu,"a'a dakata, dakata ba sai kace komai ba. ɗaga waya kawai ka kira min Hakimi yazo yanzun nan, ban sani ba ko haɗe kanku kuka yi kuke so ku nuna min kune kuka haifi yaran nan, ni banda wani hurumi da su, in haka ne kuwa sai in kama gabana na barku da halin bijirewa maganata".
Baffa ya tausasa murya yace,"ba bijire miki zamu yi ba Boɗejo, zamani muke so ki duba. kuma muma fa bamu ce ba za'ayi hakan ba, ce muka yi a fara jin ta bakinsu tukunna, idan sun amince da junansu mu abin farinciki ne a wurinmu wallahi".
Boɗejo ta jijjiga kai ta harɗe ƙafafu tace,"to bara kaji Dikko, tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin Ubanku ba sai a ranar da aka kirani akai min zancen aurenmu da shi...ina zaune lafiya daga zuwa na gaida mahaifiyata zanyi kwana uku a wurinta sai Kakanku yasa Babana ya doka min kira wai inje fada ana nemana, kai kasan tashin hankalin da mahaifiyata ta shiga a dalilin wannan kiran kuwa?, saboda kiran fada bai cika zama alkhairi ba, ina zuwa ga Babana Waziri ga Mai Martaba ga Ubanku a zaune aka ce ga mijin da akayi min, kuma a gobe za'a ɗaura mana aure. yo da ike ni me biyayya ce ban bijire ba daga ni har shi uban naku, hasalima shi tausata yake yana cewa muyi haƙuri mubi umarnin iyaye zamu ga ribar hakan, to dana aure shi Dikko mutuwa nayi ko me?, gashi nan dai ku huɗu na haifa jeras tare da shi, idan bana sonsa zan bari a haife ku ne?. sai akan ƴaƴanku zaku ce ba haka ba, Turakin ma da wancan algungumar Azimar ta raine shi, Turaki fa har goya Ilham yayi, to banda dai rashin tsoron Allah irin naku ina ku ina cewa baya sonta?
ku dai ku ke kyautata zato akan abu, ba wai kowa yake hasashe mara kyau ba. na tabbata babu abinda zai sa yarannan suƙi amincewa muddin kun nuna musu kuna so, banƙi ba shi ɗan naka ya iya botsarewa to amma shima na san na ƴan mintina ne tunda yana da ladabi, kana cewa haka kake so ba zai ja ba zaice ya amince, sai dai idan kuma a munafurce ni a hure musu kunne".
daga Baffa har Mai Martaba babu wanda ya ƙara yin magana, Boɗejo ta tafa hannu wani bafade ya shigo parlon yana zubewa a ƙasa.
tace,"maza kira min sarkin gida". fitarsa babu jimawa sai ga sarkin gida ya shigo, ya zube agaban Boɗejo tace,"ɗau waya ka kira min Hakimi".
Sarkin gida ya kira wayar Hakimi da wayar Mai Martaba, bugu ɗaya biyu ya ɗaga. yay saurin miƙawa Boɗejo. ta karɓa tasa a kunne, bayan sun gama gaisawa tace,"kana jina?".
a ladabce yace,"ina jinki ranki ya daɗe, Allah ya ƙara miki lafiya da tsawon rai". tace,"amin, Allah yayi maka albarka...dama magana zanyi da kai".
kamar yana gabanta saboda tsananin ladabi yace,"tom shikenan, ɗazu ance min kin fita, gidan Dikko zanzo ko fada?".
tace,"a'a yi zamanka akan kujerarka. dama batu ne na aure nazo maka da shi, ina so a haɗa auren Turaki da Ilham, ba kuma na so ya wuce wata guda tunda da arziƙinmu, wata gudanma saboda zan gyara jikata ne banda haka cikin sati ɗaya za'ai komai a gama".
Hakimi yace,"tom shikenan ranki ya daɗe, za'ayi yanda kika ce. Allah ya tabbatar da alkhairi".
tace,"amin ya Allah". da haka suka yi sallama, da yake a handsfree ta saka duk conversation ɗinsu su Mai Martaba sunji.
"da akwai wanda zai ja ne?". ta faɗa tana kallon su duka. a tare suka haɗa baki wajen faɗin,"a'a, Allah yasa albarka ya kuma tabbatar da alkhairi". tana nuna musu fushinta na gardarma da suka yi mata a farko tace,"kai Dikko ka kira min Falmata yanzu a waya".
Baffa ya ɗau wayarsa ya kira Falmata ya miƙawa Boɗejo, sallamar Falmata kawai ta amsa tace da ita,"anjima za'a kawo Ilham gidanki, ki gyarata gyara na ban mamaki Falmata, gyaran da ba zai sa Turaki ƙara kallon wata mace da sunan sha'awa ba har mutuwarsa, irin gyaran da ba zai so Ilham ta matsa a kusa da shi ba".
Inna Falmata ta amsa da,"tom ranki ya daɗe".
Boɗejo ta dubi Mai Martaba bayan gama wayar tace,"sai kuma me?".
ya rissinar da kansa yace,"ya kamata a sanar da Fulani Azima da kuma Madina".
Boɗejo ta haɗe rai tace,"ashema ba so nake auren ya tabbata ba. gwara ma in Madina kace, amma wace wata Fulani Azima?...to maganar aure dai cikin sirri nayi ta, ko yaran ba zasu sani ba sai ranar ɗaurin aurensu, magana daga ni sai ku nayi ta, idan naji ta a wani waje kuma wallahi tallahi akwai Allah".
tana gama faɗar hakan ta miƙe. "Dikko tashi muje gidanka zan wuce".
*Comment, Share and Vote.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_not edited._
*27*
Fillo ce zaune akan dakalin bayan ɗakinsu, daga yanda ta zabga tagumi kasan tunanin wani abu takeyi wanda ke damun ranta.
ƙwayar idonta ta kaɗa tayi jajir, idon kuma ya ƙara girma. Maijidda ta ƙaraso wajen tana faɗin,"na tsani wannan tagumin naki wallahi".
Fillo ta ɗago ido tana kallonta, bata iya cewa komai ba saboda zafin da zuciyarta ke yi mata, tun ɗazu take so tayi kuka ko ta sami relief amma kukan yaƙi zuwa.
"kwana nawa kina kuka?, zatonki kuka na maganin damuwa?, to idan baki sani ba kuka baida amfanin komai, damuwarki ya wuci ki kaita gaban Allah, akwai me yaye miki sama da shi ne?, amma sai kiyi ta faman kuka kuma ayi tambayar duniya kiƙi magana, da me kike so Kaka taji?, bafa isassan lafiya ke gareta ba. kuma ke har me kika nema kika rasa a duniyar nan da zaki ɗau damuwa kisawa ranki kina ƴar ƙaramarki, salon dai jawa kai matsala".
Maijidda tayi shiru a sanda taji Fillo ta riƙe hannunta gam, tasan ba komai bane illa kukan da take so tayi, ta janyo Fillon jikinta ta kwanta a kafaɗarta, tuni kukan da Fillo ke jira tun ɗazu yazo mata, saida tayi me isarta tukunna ta yakice daga jikin Maijidda tana goge hawayenta.
cikin muryar kukan da bai gama sakinta ba tace,"Maijidda ke kike ganin ban rasa komai ba tunda Kaka ta tsaya min, amma a zahirance ni nayi babban rashi tunda har na rasa uba, ba wai don ya mutu ba, yana raye amma na zama kamar banda uba a raye, tunda uwata ta haife ni ban sami soyayyar uba ba irin wacce ko wanne ɗan halak ke samu, ban sami gata ba irin wanda kowanne ɗan halak ke samu daga wurin mahaifi, ban samu tarbiya ba daga wajen ubana, ban sami ilimi ba daga garesa, ban sami kulawarsa ba, ban sami farin ciki daga wurinsa ba balle naji daɗi daga garesa, ya kirani da suna shegiya, ya kirani da ƴar zina alhalin akan shimfiɗar sunnah ya samar da ni...".
muryarta ta harɗe tana kifa kanta akan cinyar Maijidda tana ƙara fashewa da sabon kuka.
"Maijidda banyi dacen uba ba, ni kaɗai ce nayi rashin sa'ar uba, ta dalilin baƙin cikinsa har yau ban san inda Ummina take ba, bamu san ina ta tafi ba, ki tayani adu'ar duk inda take Allah yasa tana cikin kariyar ubangiji, jikina na bani Ummina bata rasu ba tana raye, amma Kaka wai sai tayi ta ce min Ummi ta mutu".
kukanta ya ƙaru sosai, kuma daga ita har Maijiddan kukan suke yi. "Maijidda i wish ace ana sauyawa tuwo suna dana sauya Hayyo a matsayin ubana, i wish Hayyo is not my father, I wish I could take revenge for what Hayyo did to me and my mother. but i can't, i can't do that Maijidda, duk da lalacewarsa i still feel his love in my heart".
da ƙyar kukan Fillo ya tsaya bayan da ta ɗau tsayin mintuna tana bawa zuciyarta haƙuri da kalar tata ƙaddarar.
tana riƙe da hannun Maijidda tace,"ina key ɗin motar Turaki dana baki ajiya?".
Maijidda tace,"yana ƙasan kayanmu. amma Fillo ba kya tsoron garin mayarwa a ganki".
tana kallon wani side na daban tace,"idan ma an ganni there is no problem, and ba ma komawa ɗakinsa zanyi na ijje ba, Maama zan kaiwa".
Maijidda tayi ajiyar zuciya tace,"gaskiya Hajiya Madina ta dabance, ni tunda kika ban labari na rasa ma abinda zance, nayi matuƙar girgiza da lamarin".
Fillo tace,"ni kaina farko ban yarda ba sai da kunnuwana suka jiye min...kiji fa wai a tsinke burkin motar, wai sai ta kira shi tace yaje ya ɗaukota a anguwa motarta ta lalace, wai in ya taho sai me tirela ɗin yasha gabansa kawai yabi takansa".
Fillo ta rumtse ido gam tana jin kanta kamar zai buga. "Maijidda wannan masifa har ina?, ace ka dinga harin jinin ɗan'uwanka?, me ya yi musu?, Allah da ƙyar ƙafafuna suka iya ɗaukata suka kai ɗakinsa, ke yanda na tafi a rikice ko a hannunsa naga key ɗin motar sai nayi kokawa da shi na ƙwace, ko kuma na faɗa masa komai kowa ya huta, saboda Hajiya Madina yasa kawai ban faɗa masa ba amma wallahi nayi niyya, to kawai dai ina tausayin halin da Maama zata shiga ne. kuma nayi rashin dabarar na faɗa mata ma tun a daren, dan da wuya in babu spare key da zai ce zai yi amfani da shi".
Maijidda tace,"to Allah dai kar ya tsare shi daga dukkan shirinsu". "amin".
Sabira wacca itama jika ce a wajen iya Hanne abokiyar aikin su Yami tazo wajen ta zauna. taci kwalliya daga yanda ta riƙe jakar hannunta kasan shirin fita tayi.
tace da su Maijidda,"nan kuka yo ashe?". Maijidda tace,"ehh, nan ɗin yafi iska".
Sabira tace,"duk yanda akayi ba'a sanar da me gidan nan wutar ɓangaren nan ta lalace ba, ji fa kwana huɗu muna cikin duhu da zafi".
Maijidda tace,"ita kanta Hajiyan bata sani ba, kwana biyu basa zama. amma naji Yami tace sun faɗawa incharge zai bar mata saƙo". tace,"gwara haka, cikin daren nan duk sai ka kasa bacci wallah, ga zafi ga sauro".
cike da tsokana Fillo na kallon Sabira tace,"uwar yawo sai ina aka dosa?". Sabira ta ƙara turo ture kaga tsiyanta gefe ta tauna cingom dake bakinta, bayan ta karkaɗa ƙafa tace,"ni zan so ma ki rakani, dan wannan shirin nawa da kika gani bana wasa ba ne".
Fillo tayi ƴar dariya tace,"rufani ki saya, ke dai da yawonki amma ba dani ba, sai dai ko Maijidda gata nan itace uwar yawo irinki".
Maijidda tace,"balle ma ba zuwan zanyi ba".
Sabira tace,"ko zaki je ma ba zaki bini ba dan abinda zanje yi ba da irinki sanyi ƙalau ake zuwa ba, dan sai ki lalata min aiki. Fillon dai itace daidai da tafiyata".
Fillo tace,"wai ina zaki haka, naga sai wani faman cika kike kina batsewa".
Sabira tace,"ruwan masifa da bala'i zanje na juye". ta jijjiga kanta tana yin ƙwafa me ƙarfi,"ai na rantse yau idona idon kishiyar Anty Jummai sai na rotse mata kai".
sai ta karkato tana facing su Fillo da kyau ta shiga basu labarin kishiyar Yayarta. "wai fa kawai dan Anty Jummai tana da haƙuri, kuma ita ƴar talakawa ce shikenan kullum sai cin kashin da kishiyar taga damar yi mata. tayi ta zaginta wai ƴar matsiyata kyace ita ubanta haifarsa akayi da kuɗin, ga shegen haɗa makircin tsiya tayi ta jawa Anty Jummai Faɗa a wurin me gidan, jiya Allah ne ya taƙaita bai saki Anty Jummai ba".
Fillo da tausayawa tace,"kishiya dai kowacce kala ce bata da daɗi, Allah kai mana tsari da sharrin kishiya dan ni har ga Allah a duniyata inda abinda na tsana bai wuci kishiya ba wallahi".
ta ɗaga hannu sama tana roƙon Allah,"ubangijina na roƙeka ba don nafi kowa ba Allah karka sa mijin da zan aura yay min kishiya, ko na shiga na tarar ko a shigo a tarar da ni".
Maijidda tace,"ki dai roƙi Allah ya haɗaki da abokiyar zama ta gari shine kawai, ba wai batun kar a miki kishiya ba, in haka ne ina kike so akai sauran matan?".
zuciyar Fillo na sosuwa tace,"mu bar zancen nan kawai, zan iya haɗiyar zuciya a wurin nan. kishiya fa! ni Fillo da kishiya?, to ta ina ma za'a fara zaman?, in ke ganin abinda nake so tare da wata?, Allah karka nunan wannan ranar. Maijidda cewa fa kike wai kishiya ta gari, ke a duniyar nan har akwai kishiya ta gari?, hmmm yarinya baki san wace kishiya ba, amma kishiya babu ta kirki, ba sai na faɗa miki ba tunda kin riga kin san tarihin gidanmu, kin san baƙar wuyar da na sha hannun kishiyar uwa...ke Allah ya tsinewa kishiya kowacce kala ce ma".
Maijidda tace,"to Allah ya kyauta". Sabira ta miƙe tana faɗin,"bari naje, dan zuciyata azalzalata kawai take yi". Fillo tace,"je ki wallah ki ƙwatarwa Yayarki ƴanci, ki tsaya tsayin daka karki fito a gidan nan sai kin nunawa kowa Antynki na da gata, ke idan ta kama ma kiji wa Anty Jumman ciwo ki fito waje kina kururuwa, waye bai iya makirci ba ai sai in bai so ba, karki yarda ki taho sai an garƙame shegiya a cell, ke inta kama ma ki ɗau wuƙa ki saka a hannunta kafin akawo ɗauki, ana shigo kice gata can da wuƙa wai duk sai ta kasheku".
da gaske Fillo ke ta maganarta, bayan tafiyar Sabira Maijidda tace mata,"yau ba zaki je aiki ba?".
Fillo tace,"tun ranar dana fasawa Turaki turarensa nake shakkar komawa, so nake a bamu albashi tukunna sai na siyo masa tsiyarsa. shisa naiwa Maama ƙaryar banda lafiya".
Maijidda tace,"to yau dai Dr Yusuf yace zai zo, ki tashi mu san abinda zamu yi masa".
Fillo ta kalleta ta taɓe baki,"ni ba abinda zanyi tunda ba gayyatarsa nayi ba".
sukai shiru for some seconds sannan Maijidda ta katse shirun da faɗin,"Fillo Amir fa?, ya kamata ko me yayi miki kiyi haƙuri ke kam, tsakanin harshe da haƙori ma an saɓa, kuma shi dama zaman tare zo mu zauna zo mu saɓa ne. zatonki zaki samu masoyi kamar Amir?, karki zama butulu ki mance da irin halaccin da yay miki a rayuwa, ni dai dan Allah ko mene yayi miki kiyi haƙuri ki manta, tunda ni kinƙi ki faɗa min".
Fillo tai guntun murmushi na takaici,"shi bai faɗa miki abinda yayi min ba?".
Maijidda tace,"ni ba abinda yace min, kuma bana so na sani tunda har ke kika kasa faɗa min, abinda nake so kawai shine ku dawo daidai...".
Fillo tai saurin tarar numfashinta,"har gaban abadan, igiyar soyayyar dake tsakanina da shi na datseta har mutuwa, kije ki faɗa masa hakan, in ma yana wani lissafin rayuwa tare da ni ne to ya daina deceiving kansa, domin ni Halima na barsa har gaban abadan, wallahi ko Amir ne kaɗai ya rage namiji a duniya ba zan auresa ba".
sai kuma ta fashe da kuka,"idan har da gaske Amir sona yake tsakani da Allah ba zai taɓa goranta min ba, duk da banga laifinsa ba. laifin Hayyo ne da ya sheganta ni da bakinsa, in ace Hayyo bai kira ni ƴar Zina ba yau da Amir bai buɗi baki yace min ƴar gaba da fatiha ba...".
furucinta na ƙarshe yasa Maijidda tayi zumbur ta miƙe,"kika ce me?, Amir ɗin ne ya faɗi haka?".
cikin matsanancin kuka tace,"Allah shahida idan nayi masa ƙarya Allah kar ya ɗagani anan wurin, kije ki tambayesa. daga nace bana so naje gidansa babu kayan ɗaki gudun gori shine ya tashi ya juya min baya yana faɗa min wai kar na manta ni ƴar zina ce, saboda haka ko ba'a min gorin kayan ɗaki ba ana iya min gorin an haifeni without marriage. Maijidda wanda nake so da aure ya faɗa min haka tun ban auresa ba, just imagine anyi auren, waɗannan kalamai kike tunanin zai dinga gaya min?".
Maijidda ta sauke numfashi da matuƙar mamakin ace Amir ne zai faɗi haka. ta rasa abin faɗa saboda tayi matuƙar girgiza, idonta kawai Amir ɗin yake hango mata, bata taɓa tsammanin zai iya faɗawa Fillo haka ba saboda bala'in son da yake yi mata.
Fillo dai kuka kawai take yi babu ƙaƙƙautawa, har sai da wayar hannun Maijidda tayi ƙara ta ɗaga suka gaisa da Dr Yusuf yace musu ga shi a waje, sannan Fillo ta goge hawayenta ta shi suka tafi bayan ta wanke fuskarta.
***
A ɓangaren Bello, Turaki da Khalil. zaune suke a parlo bayan sun kammala breakfast, kowanne da takardu a gabansa da kuma biro, suna tattaunawa akan batun sabon company da Baffa yace za'a ƙara buɗewa.
Khalil na kallon takardar dake gabansa yace,"anawa tunanin gaskiya gwara a buɗe na sarrafa kayan miya a maida su na gwangwani ko leda. tunda shine kamfanin mafi ƙaranci da muke da shi a nigeria, kuma ina ganin hakan za'a sami abinda ake so fiye da tsammani".
Bello yace,"view ɗinka yayi kyau, sai dai yanzu mu fara kammalawa da wannan da Maama tace".
Turaki ya kalli Bello tace,"me Maaman tace?".
Bello ya duƙa yay rubutu jikin takardar gabansa tukunna yace,"Company ɗin dake Lagos da Baffa yace a siyar, tace ba za'a sayar da shi ba za'a maida shi na fulawa, Shine batun da nai muku jiya cewar zanje Hong Kong, saboda injinan da za'a siyo na yanda za'a sarrafa fulawan.
but ina ganin tafiyan ba ni ɗaya zanje ba da kai zamu tafi Turaki, zanyi convincing Maama mu tafi tare. tunda tafiyan jirgi ne ba wai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 73