wannan koyarwa Kaka ce gareta, kwanukansu kullum sai sun wanke su ba iyaka wanda suka ci abinci ba kaɗai.
a hankali ta ke yin komai gudun kar ta fasa wani abun tunda komai tangaran ne. bayan ta gama gyara kitchen ɗin ta fito ta hau upstairs ta tambayi Zaytuna aina zata ɗauki lemun.
Zaytuna tace,"ki buɗe friedge za ki gansu aciki, amma karki manta ki haɗa da cup".
ta amsa da,"to Anty". sannann ta sakko ta koma kitchen ɗin, sai da ƙyar ta iya buɗe friedge ɗin saboda bata san yanda ake buɗe shi ba.
drinks ne kala-kala aciki da ruwa na jarka, ta san dai ruwan amma lemun idan aka cire fanta bata taɓa ganin duk sauran ba musamman five alive na kwali. kawai sai ta ɗauka ƙaramin tray ta saka kowanne guda ɗaya tare da faro guda biyu.
lokacin da ta iso wurinsu Turaki ya sauke hannun rigarsa na dama yana nunawa Bello yanda ciwon wurin yayi, babu wanda yasan da zuwanta wurin balle tsayuwar da tayi tana bin ciwon nasa da kallo ganin yacca yay rami, ita bata taɓa ganin ma irin ciwon da yay haka ba.
cikin kaɗuwar ganin ciwon ta sauke idonta ƙasa kawai tayi tsaye a wurin, tafi ƙarfin minti uku kamin Bello ya ankare da ita yace,"bismillah mana". ya faɗa yana kallonta.
ta ƙaraso ta aje tray ɗin saman table ɗin da ke tsakiya, sannan ta tsuguna ta gaida Bello cike da ladabi shima kuma ya amsa mata da fara'a.
tana durƙushe Zaytuna ta iso itama hannunta ɗauke da bowls guda biyu, duka snacks ne aciki.l ta aje kusa da tray ɗin.
idonta na kallon Bello tace,"Hammah Bello ina kwana". shima nasa na kanta yace,"lafiya lau Zaytun, ya kike ya hutu kuma?".
ta amsa mishi da,"lafiya lau wallahi, ya office?".
ya amsa da,"office babu daɗi, aminina ya gudu ya barni ni ɗaya".
Turaki yace da shi,"sai ka jira Maaman ta dawo tunda ƙorafi ya kawo ka gidan".
Bello yay murmushi bai ce da shi komai ba suka shiga taɓa hira shi da Zaytuna. idon Turaki ya kai kan Fillo dake durƙushe a wurin har yanzu, wani haushi ya kama shi, tunda ake ƴan aiki a gidan nan ba'a taɓa bagidajiyar yarinya irin wannan ba, shi bai san ba ma ko hankali ne bata da shi kwata-kwata.
"ke sai ance ki tashi ki tafi sannan za ki gurgura ƙafafunki ki tafi, ko kuwa kin zauna jin hirar da ba taki ba?".
kanta a ƙasa yake, kuma hankalinta ba'a garesu yake ba dan hirar da suke ma bata ji, banda yanzu da maganar tasa ta shigeta, tasan da ita yake, ba tare da ta ɗago ba tace,"ina jira a bani umarnin tafiya ne".
rai ɓace yace,"kiyi ta zama har a busa ƙaho".
ile kuwa yaga ko motsawa bata yi ba, wani sabon haushi ya turnuƙe shi, duk yanda akai ko aji bata taɓa shiga ba.
Fillo dai cikin ranta faɗi ta ke yi akan me zaisa ta tashi ba'ace taje ba salon ace tayi ba dai-dai ba, bata manta da wani lokaci ba lokacin da suka zauna a masarauta, Fulani ta bada aike a kaiwa Yarima Mansur, ita Kaka ta bawa ta kai, ta sameshi a wanjen shaƙatawa shi da abokinsa, data ajiye musu zata tafi ai cikin tsawa ya maido da ita da cewar uban wa ya bata izinin tafiya, akan haka har kusan horar da ita akayi, to dan dai Kaka na da matsayi ne a wurin Fulani.
to ita kuwa yanzu me zai sa ta kuma maimaitawa, ai jini ba wasa bane, shi da Yarima Mansur duk abu guda ne, balle shi wannan ɗin da ta ke ganin yana da girman izza.
"tashi kije kinji, ki zauna ɗakin baya inda abin buƙata za'a kiraki a waya". Zaytuna ta faɗa tana dubanta.
Fillo ta tashi cikin sanyin jiki ta wuce, Zaytuna ma ta fita daga part ɗin zuwa nasu.
Bello yana kallon Turaki yace,"Beb ɗin da ta tashi tana da hankali, itama ƴar'uwarku ce?".
Turaki yay masa wani kallo,"me yasa baka da hankali ne Bello?".
Bello yace,"tambaya fa nayi".
Turaki yaja dogon tsaki yace,"baka iya bambamce ƴan aiki ne kai, ko kaga tayi kama da Baffa ne ko Maama".
ganin yanda yasha murr Bello yace,"sorry maida wuƙar, ban zaci maid bace saboda surarta na kalla ba kayan jikinta ba".
Turaki ya jefa masa wani banzan kallo,"kana nufin muma a rame muke kamarta?".
"thats is not what i mean, kuma itama ai ba rama bace da ita, halittar jikinta ce a haka".
ba tare da Turaki ya sake kallonsa ba yace,"wataran sai ka rasa idonka akan kallon mutane".
Bello yay dariya sosai, daga haka kuma suka ɗora hirarsu ta abokai tare da ƙara tattaunawa akan batun aikinsa da Maama har yanzu ta dage akan ba zai koma ba.
*Dubai, 12:00am.*
Nuratu ce a ɗakin zaune kan kujera, gefenta tarin drugus ne sai ɓallo su take yi tana zuba su a hannu. ta miƙe ta ƙarasa friedge ta buɗe ta ɗakko ruwa mara sanyi ta buɗe, sannan ta ƙarasa wurin gado ta zauna a gefe.
zuciyarta fal da tausayin matar da suka ɗauko a asobiti suna kulawa da ita, ta kai hannu ta ɗago kan matar daga pillon da take kwance. sai a sannan matar ta buɗe nauyayyun idanuwanta ta zuba su kan Nuratu tare da sakar mata murmushi.
"sannu Mommi". Nuratu tace da ita tana sakar mata nata murmushin. kai kawai ta ɗaga mata alamar yauwa.
matar da suke kira da Mommi ta buɗe baki Nuratu ta zuba mata maganin, sannan ta kurɓi ruwan da shima Nuratu ta bata, ta haɗa ta haɗiye maganin.
lokacin Yusuf ya shigo ɗakin, ya ƙaraso ya zauna akan bedside drower, cike da girmamawa haɗe da ladabi ya gaisheta, yana tambayarta sauƙin jikin. kasancewar bata magana sai da ta amsa musu da kai.
Yusuf yace,"Mommi yanzu ina ke miki ciwo?". ya tambaya da tsantsar kulawa, ta kalle shi ta sakar masa murmushi tare da girgiza kai alamar babu komai.
ya ɗan lumshe idonsa sannan yace,"masha'Allahu, Allah ya ƙara miki lafiya". ta jinjina kai alamar ta gode, sannan ta kamo hannunsa ta riƙe cikin nata, tana shaking nasu alamar nuna godiya a gare shi mara iyaka.
ya dubi Nuratu yace,"Mar'atussaliha ki shirya Mommi mu fita outing ta samu taga gari, zaman wuri ɗayan zai isheta haka".
Nurata tace da shi,"tom ur excellency". har ya miƙe tsaye zai fita kukan da Mommi ta saka ya dakatar da shi, wannan fashewar kukan nata ya haifar musu da tashin hankali. inda ya koma ya zauna shi da Nuratu suna aika mata tambayar me ya faru.
sai dai shiru bata ce komai ba illah hawayen dake daɗa sakko mata, kuka biyu takeyi, kukan baƙin ciki da farin ciki. abunda Yusuf da matarsa suke yi mata iyaka abunda Ƴaƴan cikinta zasu yi mata kenan.
_su waye su?, aina suka tsintota?, ina ne nan wurin da ta ke sabuwar rayuwa?._ tambayoyin da suke yawo cikin kanta kenan tun daga ranar data farka a asibiti zuwa ranar da suka ɗaukota suka dawo da ita gidansu. so ta ke tasan amsar waɗannan tambayoyin sai dai ba ta da bakin da zata yi magana, haka kuma bata san ta yanda zata gwada musu ba har su fahimceta.
tunawa da wani lokaci yasa ta ɗora hannu a kunnuwanta ta toshe. domin tana jin faruwar abunne kamar a yanzu da ta ke zaune.
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*11*
"Mommi dan Allah kiyi shiru". Nuratu ta faɗa idanuwanta na kawo ruwa, zuciyarta cike da tsananin tausayin matar.
Yusuf yace,"Mommi hawayenki babban tashin hankali ne a wurinmu, dan Allah ki daina, ko menene kike tunawa zai zama tarihi da izinin Allah...and ina da yaƙinin 100% komai naki ya kusa daidaituwa duk da cewar bamu san me ya faru dake ba har kika zo ƙasar da babu wani naki acikinta, fatanmu Allah ya baki lafiya domin musan ta inda zamu fara".
shima ɗin maganar yake cike da tausayinta.
Mommi ta sake su daga rungumar da tayi musu, tasa hannu zata goge hawayenta Yusuf ya riƙe hannun nata tare da saka handky ɗinsa ya goge mata.
ta sakar musu murmushi, irin murmushin da ake kira na ƙarfin hali, sannan ta jinjina musu kai na ƙara godiya a gare su tare da nuna jin daɗin kasancewarta tare da su.
su biyun suka taimaka mata ta sauko daga kan bed, Yusuf ya fice ita kuma Nuratu tayi mata rakiya zuwa toilet. bata wani jima a wankan ba ta fito dafe da bango.
Nuratu na ajiye mata kayan da zata saka tai saurin bari ta taho tayi mata jagoranci suka ƙaraso ta zauna kan wata kujera.
Nuratu ce tayi mata komai, tun daga kan shafa cream har saka kayan. abaya ce white da adon stones masu ƙyalli. sai hijab ɗin peach ta ɗora mata akai wanda yake daidai ƙirjinta. kasancewar Mommi fara ce sosai sai kayan suka amsheta matuƙa, idan ba wanda ya sani ba sai ka iya rantsewa balarabiyar ƙasar ce dan tayi kama da su sak.
"Mommi ending this week zamu wuce Saudia muyi Umarah for 1 week daga nan sai mu wuce naija, Excellency ya gama gudanar da aikin daya kawo shi, aikinsa zai koma can nigeria gaba ɗaya".
Nuratun ta faɗa tana bata kubza a baki haɗe da black tea, Mommi taunar ta ke yi da ƙyar saboda jin wani nauyi a ƙirjinta kamar an ɗora dutse.
magana Nuratu ke tayi amma hankalin Mommi gaba ɗaya ya bar jikinta, tunaninta ya tafi can wata duniya ta daban, ita ɗaya ta san me ta ke tunani, kuma ita ɗaya tasan me zai iya faruwa. halin da mahaifiyarta ke ciki shi tafi so ta sa ni kamin azo kan kowa da komai.
ta rufe ido kaɗan ta buɗe ta ɗorasu kan Nuratu, sai tayi dauriyar maida ƙwallar data cika idonta sannan ta matso ta sumbaci Nuratu a goshi.
Yusuf na parlo zaune da waya kare a kunnensa yana sauraron maganganun da Umma keyi masa. tsawon lokaci kafin ya numfasa yace,"Umma please don't let Ammi knows munyi waya dake".
daga inda Umma ta ke ta galla harara kamar yana gabanta, tai shiru kamar ba zata ce komai ba, tana shirin yin magana ya rigata.
"please Umma". tayi hanzarin katse shi,"tana part ɗinta ina part ɗina how will she know?, ko da yake aini ce aku sarkin surutu".
yanda yaji muryata yasa shi sosa kai tare da cewan,"ba haka nake nufi ba Umma". dai-dai lokacin Nuratu ta ƙaraso wajen ta zauna saman cinyarsa tare da kwantar da kanta bisa kafaɗarsa, shi kuma ya zira ɗayan hannunsa acikin rigarta yana shafa cikinta, har zuciyarsa ji yake tamkar babynsa yake shafawa a zahiri. Nuratun ma ta ɗora nata hannun akan nasa suna shafa cikin tare.
komai na ubangiji ne, kuma komai lokaci ne, shekararsu biyu da aure Nuratu bata taɓa ɓatan wata ba, maganganu har sun fara tashin ai bata haihuwa, ya kamata ya ƙara aure tun kamin ya mutu baiga ɗansa ba. cikin masu maganganun harda Ammi mahaifiyarsa, da yake dama ita ba ƙaunar auren ta ke ba, kasancewar Nuratu ƴar Yayar kishiyarta ce wato Umma.
lokacin daya gama service ɗinsa ta aika shi har abuja yaje yayi kwanaki a gidan best friend ɗinta Hajiya Habiba don yaga yarinyarta. amma Yusuf na dawowa a lokacin ya tarar da Nuratu da tazo hutu shikenan sai yace shi fa ita yake so, duk yanda Ammi tayi yace shi Nuratu kaɗai zai aura, kuma da yake mahaifinsa ba mai takurawa ƴaƴa bane, abunda suke so shi yake so haka dole aka bi abinda Yusuf ke so.
Ammi tayi kamar tai hauka a lokacin, ita baƙin cikinta akan me zaisa ya auri jinin kishiya banda yana so ya tozartata a idon duniya.
to fa shikenan kuma sai ya jawo ta ɗauki fushin duniya ta ɗora akansa. dama can ana ƴar hakan saboda tana jin haushin shirinsa da Umman.
sam Ammi bata son Nuratu, kuma Nuratu yarinya ce me hankali. dan ko sau ɗaya ma bata taɓa nunawa Yusuf rashin jin daɗin tsangamar da ta ke samu daga wurin mahaifiyarsa ba. hasali ma idan yana bata haƙuri sai dai tace masa its matter of time hakan zai zama kamar ba'ai ba.
hatta wani lokaci da Ammin taje har gidansu Yusuf baya gari ta wanke Nuratu tass akan sun asirce mata ɗa, da kuma cewar Allah ya isanta da ta aure mata yaro alhalin tasan ita juya ce. Nuratu bata taɓa danasanin auren Yusuf ba sai a ranar, saboda wankin babban bargon da Ammi tai mata na maganganu marasa daɗi da tsayawa a rai.
hakanne ma yasa bayan tafiyar Ammin ta kira Umma tace ita kam tasa Yusuf ya saketa bata iya ci gaba da zama da shi, tunda dai haihuwar nan ba itane zata bawa kanta ba.
ta kwashe duk abinda Ammi tayi mata ta faɗawa Umman, silar inda faɗan gaba me tsanani ya shiga tsakaninsu kenan. Umma bata biyewa faɗan kishi na Ammi, amma akan wannan abin har sai da Daddy yace shi ba zai iya da jarabarsu ba sai ya maka su a kotu. dalilin samun sauƙi kenan shima kuma dan Umman tana bagararwa ne, amma da saboda Ammi ne har gaba da kotu sai dai akai su.
maganar Umma ta katse su Yusuf daga abinda suke ƙoƙarin yi, sai lokacin Yusuf ya farga ya amsa kiran sunansa da tai.
"ina Nuratu?". Umman ta tambaya da ɗaure muryarta.
"ga ta nan". "to bata".
ya cire wayar daga kunnensa ya ɗora akan kunnen Nuratu, ta wani narke tana shagwaɓewan Umman.
"ba dai ki da wata matsala ko?". Umman ta tambaya da tsansatar kulawa.
tayi kamar za tai kuka tace,"Umma ni so nake mu dawo, anan bana samun duk kayan kwaɗayin da nake son ci".
Umma tace,"kai Nuratu".
tace,"Allah Umma, nan fa babu irin su goruba, tsamin gaye, kuma fa har Farar ƙasa ma babu Umma, ga shi duk abunda naci ni ba sonsa nake ba sai ya dawo".
ta ƙarashe maganar tana fashewa da kukan taɓara.
daga inda Umma ta ke tai murmushi. "ai ke kika dage sai kin bisa, amma kiyi haƙuri kinji, haka ƙaramin ciki yake Nuratu. ai kun kusa dawowa, idan kun dawo ma nan gida za ki dawo ba zan barki ke ɗaya ba...yanzu dai zan san duk yanda za'ai na aiko miki abubuwan da kike so kamin dawowar taku, kiyi list sai ki turo min".
"tom Ummana. ina su Kursum?".
Umma tace,"suna bedroom ɗin su".
"kice ina gaida su kuma nayi fishi tunda basa nemana...kuma ko ɗansu yazo ba zan basu shi ba".
Umma tace,"ai kina da wayarsu ki kira su mana". sannan ta ɗaure murya tace,"ina Yusuhun?".
lokaci ɗaya Nuratu ta nemi hawa bori ajikinsa akan Umma tace Yusuhu, dan ita bata son sunan ana ɓata masa suna ya koma na ƴan ƙauye. ita kuma Umman duk lokacin da Yusuf ya ɓata mata rai ko ya ya ne sunan da take faɗa masa kenan.
"bana son iya shege Malama bawa mijinki".
tana ɓata fuska tace,"don Allah Umma ki daina cewa Yusuhu idan wasu suka ji sai su ɗauka".
Umma tace,"to sai kizo ki faɗawa ubansa ai yay masa sabon yanka".
sai around uku na yamma tukunna suka fita outing, Mommi nata jin daɗin fitar tasu saboda yanda suke ta ma ta hira su biyun, kowa so yake ya nuna bajintarsa na ɗebe ma ta kewa tamkar wasu ƴaƴanta. basu suka dawo gida ba sai after isha'i.
*Nigeria, Gombe, Dikko resident.*
kan Fillo duƙe tana yankan farce suna magana da Kaka, wadda ke ta yabon Turaki saboda mutumcinsa.
Fillo dai bata cewa komai, dan ita duk da halin kirkin daya nuna bata jin zai wani burgeta. saboda haushinsa ma ta ke ji gaba ɗaya, har ga Allah ta tsani mutum me ji da kai, wannan yasa tun a wancan ranar da ta fara zuwa aiki ɓangarensu taji ko kaɗan bata ƙaunar ma hanya ta ƙara haɗata da shi ko bisa kuskure.
ita bata ma yi tsammanin yana da halin ƙwarai har haka ba da zai iya taimakawa wani, tayi mamakinsa sosai. sai daga baya taga ashe tayi masa bahaguwar fahimta ne, bata san da yaje duba Kaka da jiki ba sai daga baya, tun ranar farkon aikin nan nata daya kira waya a ɗakin baya da akace ta zauna, bata ɗaga ba saboda baccin daya fara ɗibarta.
da kansa yazo ɗakin ya sameta tana bacci, yana shirin juyawa ne ta farka, ta tambaye shi akwai buqatar wani abu ne fuskarsa a tamke yace mata babu, sai kawai ya fice daga ɗakin. kuma babu jimawa ya ƙara dawowa ya tambayeta ina tsohuwar da ta samu anan, tace masa ai ko da tazo babu kowa a ɗakin.
kamar bai yarda da abinda ta faɗa ba lokacin, saboda ɗan jim yayi kamin ya fice a ɗakin. sai bayan isha'i da ta koma ne ta tarar da uban cartons jere a falonsu, maltina, madarar gwangwani da ruwa da kayan marmari kala-kala, ga kaza gasashshiya, abun ya bata mamaki sosai, duk da zuciyarta ta raya mata ko Amir ne ya kawo, to amma iya ƙoƙarinsa dai tasan baida kuɗin wannan uban sayayyar.
tana tambayar Kaka tace mata ai Zaytuna ce suka zo ita da Yayanta suka kawo mata, a lokacin bata kawo cewar Turakin ba ne dan haka kawai godiya tayi tana daɗa faɗawa Kaka kirki irin na Zaytuna da Hajiyarsu, Kakan itama na ƙara faɗar nata kirkin da ta san Zaytunan da shi a ɗan tsukukun zaman jinyar Turaki da tai.
Sai da Fillo ta shiga ɗaki taga ledar drip da tarin magani akan katifarsu sannan tai saurin fitowa daga ɗakin, tsayawa tayi kawai tana kallon Kaka kafin ta iya buɗar baki tace,"Kaka wa akaiwa ƙarin ruwa?".
Kakan tace,"ni ce, ai da suka zo dubani ɗinne sai shi Yayan Zaytunan ke cewa ina da buqatar asamin ruwa domin na samu ƙwarin jikina. yana zaune anan ya kira likita yazo ya dubani shine har ya biya kuɗin waɗannan magungunan, ina ji likitan yana lissafin kusan dubu takwas Halimatu...ai yaran nan sunyo halin iyayensu".
a lokacin hannu Fillo tasa ta goge hawayenta bata ce wani abuba. kuma tun daga ranar kullum sai Turaki yazo ya duba jikin Kaka sati guda kenan. ita bata ma san shine Turakin da tai kasada akansa ba sai ranar da Hajiya Madina ta aikata ɓangarensa tace tai gyara. anan ne tana shiga taga lafcecen enlergment ɗinsa a jikin bangon bedroom ɗin wanda daka shiga shi zai fara maka maraba.
kuma a sannan babu hoton abinda ya shiga haskawa a idonta sai na sunansa dake jikin wannan farar takardar da ta ƙona, kamar yanda akai rubutun manya ajikin hotonsa haka ma yake a jikin takarda. tarin tambayoyi da mamaki suka maƙale a kwanyar tunaninta.
tambayoyin da ta ƙudurcewa ranta son sanin su nan kusa bada jimawa ba in har taci gaba da zuwa aiki, tunda Hajiya Madina tace ko da Kaka taji sauƙi ba zata dawo ba ita zata ci gaba da aikin.
dan sosai Hajiya Madina ke sonta, tunda ko da akace za'a ƙaro wasu ƴan aikin tace a'a a barsu ita Halimatunta kawai ta isheta yanzu, inma zaa ƙaro to a ƙaro ɗaya saboda kar aikin yay mata yawa, kullum cikin yabonta take tace bata taɓa ganin yarinya me hankali da natsuwa ba irinta, hakan yasa ta ke jin daɗin aikin sosai.
ko a ƴaƴanta ma da Samha ne kawai basa wani ɗasawa amma ko Khalil idan ya ganta ya dinga tsokanarta da Sojan Rana. kuma sau tari indai Hajiya Madina na parlo sai tace itama ta zauna ayi kallon tare da ita, Turaki ne ma ta fuskanci kamar baya so talaka ya raɓe shi, shi yasa fuskarsa kullum ɗaure ta ke akanta, ko da yake ba ita ɗaya ya kewa hakan ba har ƙannensa idan aka cire Zaytuna da Khalil.
saurin da ta ke yanzu ta gama yankan farcen ta wuce don taji Hajiya Madina na faɗin yau zasu unguwa duka gida.
Kaka ta katse shirunta da cewar,"kin kuwa ɗauki namanki?".
ta ɗago tace,"aina?".
Kaka tace,"a'a na aje miki nama cikin farar robar nan, da za ki wanke-wanke ba ki gani ba?".
"ni banga komai aciki ba, ƙila Maijidda ta shigo ta wawashe shi...wa ya kawo miki nama dama?".
Kaka ta dire wani hijabi da ta ke linkewa tace,"Yayan Zaytuna ne ya shigo jiya da daddare, ba ki jima da kwanciya ba lokacin...nace masa ai ma na gama warwarewa lafiya ta samu dan jibi ma zan dawo aiki shine yace a'a nai zamana na ƙara hutawa tunda akwai me taimaka min, koma da babu a nemo wata".
Fillo ta miƙe ta ɗauko tsintsiya tana share wurin da ta ɓata tace,"an gode masa...yana ta abu na masu kirki alhalin ba haka yake ba".
Kaka dai shiru tayi, ita kuma ta ɗauki hijabi tana ce mata. "zan tafi Kaka. yau babu kula da buƙatun ɗan gwal da wuri zan dawo dan naji Hajiya tace zasu je unguwa".
Kaka tace,"sai kin dawo ki gaida Hajiyar".
tana fitowa haraba sukai kiciɓis da Maijidda, Fillo ta tsaya tana kallon yanda ta ke jera hamma daga gani kaga wadda ta taso a bacci.
Maijidda tace,"yauwa dama wajenki za ni". ta faɗa tana miƙa mata wayar hannunta tace,"Amir ne ke kira tun asuba".
Fillo ta kallesu ita da wayar kafin tace,"kuma ai sai kice masa bama tare". Maijidda tayi hamma sannan tace,"ai yaƙi gane wannan bayanin, ni dai ungo idan kin gama kya kawo wallahi mugun bacci ke idona".
ba tare da Fillo ta karɓa ba tayi gaba abinta da cewar,"sai ki faɗa masa kinzo ba ki sameni ba".
Maijidda tabi bayanta da kallo tana faɗin,"ni ban iya ƙarya ba, Allah haka zan faɗa masa kince idan yazo ya sameki acan".
a parlo ta samesu kaf ɗinsu, ita kam rayuwarsu na burgeta. ta durƙusa ta gaida Hajiya Madina. Hajiya Madina ta ajiye hisnul muslim ɗin dake hannunta a gefenta, sannan ta zare medical glass ɗin dake a idonta ta saka shi cikin box ɗinsa. ta kalli Fillo da fara'a tace,"Halimatu kin shigo?".
kan Fillo a ƙasa tace,"ehh Hajiya, Kaka na gaishe ki".
tace,"ina amsawa, jikin nata da sauƙi dai ko?".
"ehh taji sauƙi ai, tama ce zata shigo gaida ki zuwa anjima".
"a'a ita da ba ƙwarin jiki ba, zan shiga na dubata insha'Allahu...yanzu maza ki fito da break fast naga already Zaytuna ma ta kammala komai".
ta amsa da,"tou". sannan ta miƙe ta wuce kitchen din bayan duk ta gaida yaran.
a kitchen ta sami Zaytuna tana ɗauraye hannunta, ta ƙarasa tana yi mata sannu da aiki. Zaytuna tace,"yau kinyi late".
Fillo tai ɗan murmushi tace,"na tsaya yima Kaka aiki ne zata yi baƙi".
"oh Allah sarki, jikin nata dai da sauƙi ko".
"ehh taji sauƙi sosai".
"to Allah ya ƙara mata lafiya".
"amin ya Allah".
ta nufi drower ta taka kujera ta ɗauko babban tray, Zaytuna na goge hannu a towel tace,"na kammala komai fito da su kawai za ki...kiyi da jiki dan Allah zamu fita ne har da Baffa".
"tom Adda".
Zaytuna ta dakata daga fitar da zata yi ta tsaya tana kallonta, ta girgiza kai kawai sannan tace,"wannan jiki naki Fillo anya ba sai mun nemi magani ba, komai kike salalo salalo kamar mara jini ajiki".
tana faɗar hakan ta juya zata fita ta bar Fillo da ƴar dariya. Turaki ya shigo kitchen ɗin ko maganar da Zaytuna ma ke yi bai tsaya sauraro ba. ya wuce kai tsaye wajen drink trolly ya ɗauki mug, Fillo na shirin ɗaukar tea flask ta ɗora akai muryarsa ta tsayar da ita, ita bata ma san da shigowarsa ba.
yo ita me ta sani da wani wait ɗinsa da zai ce mata wani wait, mutumin da ba zai yi hausa zalla ba dole sai ya haɗa da yaren da ita bata iya shi ba, ko da yake taga duka haka suke, shi yasa wataran suke shanyata a tsaye idan suka faɗi abinda bata sani ba, banda late da Zaytuna ta saba faɗar mata shi har ta fahimci me hakan ke nufi to me ta sani bayansa.
dan haka kawai sai ta kuma yunƙurin ɗaukar tea flask ɗin, Turaki da idonsa ke kan hannun Flask ɗin da zata kama yace,"Wae ankam a iri 6iddo toi kam a nanako volwanego?". (wai ke wacce irin yarinya ce da ba'a faɗar magana kiji ne?)
kakkausar muryarsa a sama ya doka mata tsawar da ta saka ta ture flask ɗin ba tare da saninta ba, ya zamo zai faɗi ƙasa yay saurin isowa ya tare shi. kamar yasa hannu ya bibbigeta don haushi, shi haushinsa da yarinyar saurin rikicewarta akan abindai bai kai ya kawo ba. ga shi ya tsana yaga da anyi magana jikinta ya hau rawa, shi yasa ya cewa Maama su kaita asibiti a binciki lafiyarta.
ta ɗauki tsawon 2mints jikinta na rawa kamin ta daidaita, ta buɗe idonta da ta rumtse gam ta sauke kan dogayen yatsun ƙafarsa, sannan ta sauke hannunta daga
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 73