nemi kujera ta zauna tana rufe fuskarta da duka hannunta biyu, Allah ɗaya yasan abinda take ji a zuciyarta, kuma ta lura in bata yi da gaske ba zuciyartata na gab da bugawa.
Turaki ya kalleta ya kalli Baffa wanda ko juyowa bai yi ba ya kalli inda Maama take, dan haka abin sai ya ɗaure masa kai ya dinƙa kallon su 1 by 1, abinda zai iya rantsewa bai taɓa gani ba a tsakaninsu ba kenan tsawon rayuwarsa, fushi da junansu dai, shi ko irin wannan saɓanin da ake cewa ana samu tsakanin Mata da Miji ma bai taɓa gani ba ko da a fuskokinsu. to me yake faruwa ayau ɗin?, duk akan ɓatan yarinyar ne ko ya?, me Maama take son faɗa masa ne ɗazu da bai fahimta ba?.
sai ya sauke ƙafafunsa ƙasa ya zauna daga gefen kujerar da Maama take, ya kai hannunsa ya ɗora akan yatsun ƙafarta yana jin wani abu na tsarga masa. tunaninsa ɗaya ne me ya saka masa Maama zubar da hawaye irin haka?. bai san lokacin da ya haɗe yatsunsa ba ya dunƙule, banda akan ƙafar Maama yake babu abinda zai hana shi nausar koma menene.
sai da ya rufe idonsa ya buɗe tukunna ya buɗe baki yace,"Barka da Rana Baffa". a sannan ne Baffa ya gyara zamansa yana kallonsa yace,"yaushe ka sauka?". yana kallon mahaifin nasa da son gano abinda ke faruwa yace,"ban jima ba. na baro Bellon acan zai ƙarasa projects na jiya da kayi magana".
tun ajiya da suka yi waya da Khalil yaso ya taho amma sai Baffa ya kirasa yace zai yi representing nasa a wani program da yake da shi da safe, dalilin da yasa ya zauna ɗin kenan, kuma ayau ɗin ko Bello bai san ya taho ba saboda daga can airpot yayi.
Baffa yace,"an dawo lafiya?". yace,"lafiya lau".
shi dai jikinsa duk a sanyaye yake, musamman da har yanzu yaji Maama na kuka kuma Baffa ko kallon inda take zaunen bai yi ba. baya so yayi saurin interfering shi yasa yay shiru, amma sai yaji ba zai iya jurar jin kukan Maama ba, hakan yasa idonsa a ƙasa yace.
"Baffa da akwai wata matsala ne?".
Baffan yace,"ita Babar taka bata faɗa maka ba ne?".
Turaki ya ɗago ido ya kalli Hajiya Madina sannan ya kwantar da kansa gefen gwiwarta yace,"a'a, bamu zauna da ita ba tukunna".
Baffa yace,"to gobe bayan an idar da sallar juma'a insha'Allahu za'a ɗaura maka aure, kai da ƴar uwarka Ilham, dan haka sai ka zama alert".
da wani bala'in shock Turaki ke kallon Baffa, maganar na maimaituwa acikin kansa. bai san sanda ya furta,"aure kuma Baffa?, dama ana irin wannan auren?, Baffa aure ban shirya ba kuma bada yarinyar da nake so ba?".
kamin Baffa yay magana Maama ta buɗe fuskarta da tayi shaɓe-shaɓe da hawaye tace,"kaji ai zancen da nake maka ba. yanzu tsakani da Allah idan har aka yi masa hakan an masa adalci kenan?, ina aka taɓa yiwa mutum aure ma bai san da zancen ba sai kace wani gantalalle, and beside ita kanta matar da aka lalaƙa masa bai ce yana sonta ba, haba Baffa ka dawo cikin hayyacinka mana, ɗanmu fa da gatansa taya za'a ce za'a masa irin wannan auren da ko mara gatan ma ba'a yiwa irinsa, abar ta batun ma ni a sanar da ni tunda dama ni ba kowa bace, amma dai at first ai ya kamata shi a sanar da shi in ya amince sannan, idan ma kuma dolen ake so ayi masa sai a sanar da shi tunda wuri ba wai sai a ƙurewar lokaci irin haka ba, kawai tsakani da Allah dan anga yaro yana da biyayya sai ake zaluntarsa duk ta inda aka so, wannan ba daidai bane wallahi, kuma Allah ko kotu muka je sai an ƙwatarwa ɗana hakkinsa".
Baffa ya ɗago ido ya kalleta da kyau yace,"you are free to go there Madina, ki shigar da ƙara gaba da kotu kinji. abu ɗaya kawai nake so in sanar miki shine babu mahaluƙin da ya isa ya hana wannan auren. duk fitinar da zaki tayar wallahi sai dai ta ƙare miki ke ɗaya, wannan batu na aure magana ce ta mahaifiyata, saboda haka babu uban da ya isa ya hana, ɗa nawa ne ba na wani ba, kuma tun a jiya na faɗa miki muddin kika nemi ki ɗaga min hankalin ki tada fitina akan wannan batun, to tabbas zai yanke tsatstsauran hukunci akanki".
Hajiya Madina ta ƙara fashewa da kuka sosai. Turaki dai na zaune kamar gunki sai kallon Baffa yake kamar yana kallon sabon mutum. sai da Hajiya Madina taci kukanta sosai tukunna ta ɗago tace,"muddin ina raye, muddin da lafiyata babu wanda ya isa yaywa ɗana auren dole, sai kace wata mace. abunda ko ada can ba'a yi ba, idan ma auren dolen ake so ayi masa a fara faɗa masa mana, ba wai aje a ɗauko ɗiyar matar da ba ƙaunarsa ta ke ba a haɗasa da ita".
sai tai ta ɗauke idonta daga kan Baffa ta maida kan Turaki, tasa hannu ta ɗago fuskarsa daga saman cinyarta da ya kwantar, ta kalla cikin idonsa tana ganin yacca ƙwayar ta sauya kamar bata shi ba, taji wani bala'in tausayinsa ya kama shi, yana da mugun haƙuri kuma yana da tsananin biyayya ga iyaye ko da ace zai cutu, tana kallonsa tace,"kana da ni Hammah, ni mahaifiyarka ce da ba zan iya zuba ido naga ana cutarka ba, saboda haka ka faɗa min zaka iya auren Ilham ko ba zaka iya ba?, ka shiryawa wannan auren ko baka shirya masa ba?".
Turaki ya haɗe murfin idonsa ya rufe yana jin wani abu na taso masa daga ƙasan zuciyarsa, dama har yanzu shi under 20years ne shi bai sani ba?, dan a ganinsa yaron ma da yake 20years ba za'ace zaa masa irin wannan auren ba, me yasa Baffa?, me yasa zai biyewa rikicin tsufan Boɗejo?, ofcourse baya san wannan auren, kuma ko da ace zai iya so ɗin kukan Maama kaɗai na iya sa shi ya ƙetare umarnin Baffa da bai taɓa ƙetarewa ba tunda aka haife shi, to amma sai dai Baffan ya karya shi da furucisa guda ɗaya, ya sagar da shi daga duk abinda yay niyyar yi.
dan shi tanadin da yake Baffa na gama zancensa daga nan sai ya miƙe yaje ya sami Ilham ɗin yay mata cin zarafin da ko da gawarsa ba zata yarda a ɗaura mata aure ba, to sai dai a yanzu Baffa ya gama da shi tunda har yake batun zai ɗauki tsatstsauran mataki kan Maama, bijirewar tasa ba zata haifar da komai ba sai ɗa mara ido.
dan haka zai amince ya auri yarinyar, amma ya tabbata da kanta zata bar gidan, dan ba zata taɓa samun fuskar zama da shi ba, ya sa ni ita ta amince tana sonsa tunda har aka yarda da auren, but she will regret.
yanzu baida lokacin yi mata komai saboda ba abinda ke gabansa ba kenan, neman Fillo ne a gabansa yanzu.
yasa hannu ya dafe kansa yana jin zafin dake kansa na ratsawa a jikinsa. ya buɗe ido ya kalli Hajiya Madina da har yanzu hannunta ke kan goshinsa tana kallonsa kamar ba zata ƙifta ba.
ta ƙara ce masa,"karka cuci kanka, sai in har ka yarda za'ai auren nan, idan baka yarda ba yanzu ka miƙe in kai ƙara gaban Babban Alƙali, dan yau daga uban har ƴaƴan sai na maka su a kotu dan ba zan ci gaba da zuba ido ina kallo ana zaluntar min kai ba wallahi, ko zaka yi aure ba'a cikin shiri ba na yarda amma sai in wadda kake so".
bata ma san sanda tai furucin daga uban har ƴaƴan ba. Turaki ya kalla mahaifinsa yace,"Baffa ni fa ba yaro ba ne".
Baffa yay saurin ɗaga masa hannu yace,"sanin hakan yasa muka haɗa aurenka da ƴar'uwarka, ka shirya gobe after salatul juma'a za'a ɗaura aurenka. haka muka zauna muka yanke ni da mahaifiyata da ƴan'uwana, and that is our final decision, idan har kuma ka bijire min to tabbas zan sallamaka a cikin ƴaƴana sannan in sallami itama Babar taka dake ɗaure maka gindi".
Hajiya Madina tayi hanzarin miƙewa daga kan kujera tace,"in har zan cika alƙawarin dana ɗauka na riƙe yaron nan bisa amana, to Alƙali Dikko dan ka sakeni ba zanji wani ɗar acikin raina ba. so barazanar sakinka ba ita zata sa in sauka akan bakana ba, aure in kaga anyi tabbas to da amincewar yarona".
tana gama faɗar haka tace da Turaki,"Hammah ta shi muje, inga wanda ya isa yayi maka auren dole, ko da kai yaro ne ba'a isa ba balle kuma da hankalinka".
cikin ɗaga murya Baffa yace,"Madina wai me yasa baki da mutumci ne, auren nan na faɗa miki mahaifiyata ce ta shirya shi, shine har kike so in ta ke umarninta?".
Maama ta taɓe baki tace,"cikin ku huɗu da Allah ya bata kaf ɗinku wa aka yiwa auren dole?, kuma jikoki nawa gareta?, sauran ƴaƴan nata rasa ƴaƴa suka yi da ba zata yiwa ƴaƴansu ba sai nawa ɗan da aka sawa ido dan an gansa yafi kowa haƙuri, yafi kowa biyayya. to daɗin abinda ƙasa bata cika bakina ba balle a cuce shi...Me Babban suna ta shi ka ji, aure sai in bana numfashi, kaf ƴaƴana ba wanda aka isa aiwa auren dole".
Turaki ya riƙe kansa da ke neman barazanar fashewa ya riƙo hannun Maama yace,"zan aureta Maama, zanyi auren na amince. adu'a kawai zaki yi min".
ƙyam idonta ya tsaya akansa tana hango tsananin ƙarfin halin dake tare da shi wajen ganin ya furta hakan. ta maida kallonta kan Baffa tana kallonsa, ko a jikinsa, bai damu da halin da ɗansa zai shiga ba ma?.
ta ɗauke kanta tace,"babu komai akwai Allah, idan ma saboda wata manufa aka haɗa auren nan Allah ya saka maka ya kareka daga sharrin mugun mutum...and ko banza ƴarsu ce zata wahala wallahi tunda babu sonta a zuciyar mijinta. kuma sai in dai bai ga wadda yake so ba, abu da Allah ya halasta masa auren mace huɗu, yana ganin wadda yake so zan ɗaura masa aure da ita wallahi kuma banga wanda ya isa ya hana faruwar hakan ba, in masa auren gatan da ko ƴaƴan masu mulkin ma ba'a yi musu".
taja hannunsa,"tashi muje Allah yayi maka albarka ya baka ladan biyayya, idan ba me tarbiya ba waye ma zai yarda da wannan kalar cutarwar".
ta mayar da kallonta kan Baffa tana cewa,"Allah ya bawa mutum ƴaƴa amma baida burin da ya wuci ya ƙuntata musu, duk wai ace mutum shi yana bin maganar manyansa, Allah na tuba yayye ba iyaye ba har sunsa na baƙantawa ɗan cikina, ita kanta yarinyar nasan ba kai tsaye akai komai ba sai da ubanta yaji ta bakinta, amma kai wai me biyayyar yayye ka yanke hukunci kanka tsaye, sai anyi magana ka dafe ƙirji kana nishi hawan jininka zai tashi, inga me zaman jinyarka yau".
tana gama faɗar hakan ta kama hannun Turaki, kamar wani ƙaramin yaro haka ta ja shi suka fita daga parlon Baffa na bin bayanta da kallo, ko kaɗan bai mamakinta ba dan dama yasan za'a rina, in ace dai Turakin yana son yarinyar yasan babu abinda zata ce balle har ta tada jijiyar wuya haka, amma akan hakan yau ɗaya har tana faɗar wai yana ƙuntatawa ƴaƴansa, when akai haka?.
acan parlonta ta tarar da duka yaranta zaune sunyi jungum-jungum, Khalil da Nihal da Zaytuna, Samha da Sameer basa nan dan basu dawo daga ƙasar da suka tafi ƙulla mugun nufinsu ba.
ta shigo tana ta masifa, Khalil ma yay tsaki yace,"gaskiya, gaskiya abinda Boɗejo tayi bata kyautaba sam. wannan wane irin aure ne tsakani da Allah?".
Nihal ma na turo baki tace,"yanzu dan Allah duk burin da muka ci akan auren Hammah sai azo mana da shi a irin haka?, shirin me muka yi tsakani da Allah, ni wallahi wannan tsohuwar dama ta mutu".
Zaytuna dai ba tace komai ba illa kallon Turaki da take tayi ƙwayar idonsa kamar ba nasa ba. Nihal ta miƙe ta isa kusa da shi tana ɗora hannunta akan nasa tace,"Hammah kai kace kana son auren da har tai mana wannan shirmen?".
bai ce komai ba, lokacin Hajiya Madina ta ƙaraso wajen riƙe da cup a hannunta da ruwan sanyi aciki, ta zauna tana tallafo kan Turaki ta bashi ruwan ya sha. bayan ya sha ta ajiye cup ɗin tana faɗin,"suje can suyi bikinsu su kaɗai, ni da ƴaƴana dai babu mai zuwa, wanda ya fasa cewa ina baƙinciki ba ɗan halak ba ne. kuma kaima ana ɗaura auren kayo kwana ka dawo gida".
Nihal na matsar ƙwalla tace,"yanzu Maama sai kace bamu da gata sai ayi bikin Hamman'mu a haka babu shagalin komai?, duk fa ina ta cewa friends ina idan Hammanmu zai yi aure kowa zan gayyace shi. shi Baffan dan tana babarsa kawai kuma sai ya wani kama biyewa rikicin tsufanta, ni taja ma wallahi har Ilham ɗin na tsaneta, ƙilan ma harda wannan munafukar Babar tata aka haɗa baki".
Hajiya Madina tace,"kwantar da hankalinki Nihal, shi da yake da ikon auran mata har huɗu, Allah ya kaimu nan da ranar da zai hango zaɓin ransa. anan za'aga inda ake aure, lokacin zamu yi namu shagalin bikin akan matar so, kuma ko a yanzu ina da arziƙin da zan iya yin bikin da zaici uwar nasu acikin kwana biyu cal, sai dai ba zan ɓarnatar da dukiyata ba akan auren matar shige".
ta kalli Khalil tace,"kaima uban ƴan ladabi da biyayya, ka sake nai kiciɓis da kai zaka je wurin ɗaurin aure gobe babu abinda zai hanani sa maka kafa na fyaɗeka a ƙasa, in taka ƙafar in karya banza".
Nihal tace,"dama ni wallahi babu inda zanje dan ɓuya ma zanyi ko Baffa ya kira wayata Allah ba zan ɗaga ba. dan dana hau whatsapp naga Marfu'a(Yayar Ilham wadda itace ta farko a ƴaƴansa mata), ta ɗora invitation card na dinner da cocktail ranar saturday da sunday".
Hajiya Madina da har yanzu ta ke a fusace tace,"sa ji uwar kunya kuwa, dan gobe ma zamu bar ƙasar ni da shi, sai su nemi uban da zai yi replacing angon, ai insha'Allahu duniya sai ta gane auren cusa kaine, ango ba so yake ba".
tana kallon Zaytuna tace,"kema uwar rawar ladabi da biyayya, Allah sa inga kin shiga lamarin bikinsu kiga asalin ɓacin raina".
ta faɗa tana maida hannunta kan goshin Turaki da take jin zafin kan na ratsa fatar hannunta, a lokacin Turaki ya buɗe idonsa yana kallonta muryarsa a raunane yace,"Maama da gaske ne kun fito da yarinyar nan ta ɓata?".
ta ke Hajiya Madina ta fashe da kuka tace,"ko dan wannnan dalilin tashin hankalin da nake ji ai yaci ace a tsayar da maganar auren ɗana?. banda ma dai Baffan Baffa ne ai sai ya miƙe tsaye yace ko za'ai a bari aga yarinyar mutane dana fita ta ɓatar tukunna, amma har shine yana min tsawa yana cewa babu ruwan auren ɗansa da ɓatan yarinya. yanzu fisabillah me Kakar yarinyar nan zata ɗauke ni?, ba sai su koma min kallon matar banza ba azzaluma na ɓatar musu da ƴarsu nazo ina shagalin bikin ɗa, wallahi ni dai sanyin Baffanku ba komai bane fa ce cutarwa".
ya rumtse idonsa ya buɗe tukunna ya ƙara cewa,"garin ya akayi ta ɓata?".
nan ta kwashe labarin komai ta ba shi.
"to su police ɗin suna cewa wai sun fi tunanin kidnappers, ka faɗa min Hammah idan kidnappers ne tuni basu kira waya ba, amma fa shiru shiru har zuwa yau babu wanda ya kira waya, ko'ina an duba babu ita kamar ɓacewar aljani, har yanzu dana sanin fita nake da yarinyar nan, dan Kakarta da wanda zata aura zasu ga kamar da gangan hakan ya faru, kasan zuciya bata da ƙashi". ta faɗa tana kuka sosai.
Idonsa a lumshe yace,"ki daina kuka Maama, insha'Allah an kusa a ganta".
dukansu suka amsa da amin. sannan ya miƙe yace,"zanje in kwanta, kaina yana ciwo sosai".
tace,"tafi ɗakina, kuma ka cire damuwar komai a ranka. yanda kake da gatanka zakai auren gata nan da wani lokaci insha'Allah. Dikko ne yay sirika ba Madina ba".
Turaki ya wuce ya hau upstairs yana jinsa kamar ba shi ba, yana jin komai kamar a mafarki. kuma kafin ya kwanta sai da ya kira Bello ya sanar masa, tsaban shock Bello ashar ya ɗura a lokacin, har bai san sanda yay formating document da yake haɗawa ba.
kuma Turaki bai jira cewarsa ba ya kashe wayarsa.
*Washe gari, Juma'a, Masarautar Kaltungo, Ƙarfe Ɗaya da rabi na rana.*
ana idar da sallar juma'a a masallacin aka ɗaura auren Muhammad Habib Lateef da Rumana Hashim Lateef akan sadaki dubu ɗari uku. ɗaurin auren daya samu halarta manya manyan ƙusoshin ƙasar nan, dan duk wanda yake da faɗa aji a ƙasar nigeria da wajenta sai da Mai Martaba ya gayyace shi ɗaurin auren, kuma cikinsu babu wanda ya turo wakilinsa duk da kansu suka zo.
duk girman masallacin fada sai da mutane suka cika shi taf, ciki da wajensa babu masaka tsinke, ango dai yana tare da mahaifinsa dan babu abokinsa ko ɗaya, Bello ma da yace zai biyo jirgin safe Maama ce tayi sai taci ubansa matsawar yazo. ango dai kamar ba ango ba dan fuskarsa babu walwala, ga shi dai acikin mutane kuma inda ake ɗaura aurensa, amma hankalinsa gaba ɗaya na can kan Fillo, ina take? da kuma halin da take ciki.
bayan gama ɗaurin aure aka tafi reception, inda ɗumbin jama'a suka ci sukai hani'an, dan babu wanda zai ce bai goge haƙori da naman kaza ba. ana dawowa daga reception kuma aka koma can gidan mai martaba, cikin masarauta kenan, duk ta yanda Turaki yaso ya zame ya zille ya tafi gida abin yaci tura, dan Baffa na riƙe da hannunsa sai nunawa jama'arsa shi yake cike da tsantsar farin cikin da ba zai misaltu ba, shi kansa Turakin sai da yaji tausayin mahaifinsa, bakin Baffa sam yaƙi rufuwa, da zarar sun gaisa da mutum zai nuna masa Turaki yace,"shine babban ɗan nawa, asa masa albarka". haka ya dinƙa yawo da shi yana nunawa jama'arsa da jama'ar mai martaba.
Turaki kam ya koma kamar yaro, bai sami salama ba sai da suka dawo fada, dan iyakar wanda suka dawo fadan duk ƴan'uwa ne, yana jin wayarsa na ta buga ringing daga Maama sai dai babu ta yanda za'ai ya ɗauka.
acikin fadar Mai Martaba ne zaune daga tsakiya akan royal chair, sai Hakimi a kusa da shi ta hannun dama, sai Baffa a kusa da shi ta hannun hagu, sannan Falmata a kusa da shi sai Boɗejo daga kusa da hakimi ta wani hakimci ƙafa ɗaya kan ɗaya cikin alkyabba me ƙallin bala'i, sai ɗaukar idon jama'a take, bakinta yaƙi rufe haƙwaran makka ɗinta guda huɗu duk a waje.
Mai Martaba ne ya fara doguwar nasiha ga amarya da ango akan zaman aure, bayan ya gama ya damƙa amanarta a hannun mijinta, ya kuma yi musu addu'ar samun zaman lafiya da samun zuri'a ɗayyiba. bayan ya gama Hajiya Boɗejo ta ɗora da nata, tayi doguwar nasihar aure da babu wanda jikinsa bai amsa ba a wajen hatta Turaki, daga ƙarshe kuma sai ta fashe da kuka tana zuba musu adu'oi iri-iri.
bayan ta gama Hakimi ma yay nasa, bayan ya gama Baffa yay musu tasa, sai a sanda yake yi musu nasihar ne kawai Turaki sai jin hawaye yayi ya sauko masa ba tare da sani ba, daga ƙarshe Inna Falmata ma tayi nata.
bayannan kuma aka rarrabawa ƙur'ani da littafan adu'oi. daga nan kuma aka ɗauki amarya akayi cikin gida da ita ana batun gobe idan Allah ya kaimu za'a shiga sauran hidiman taron biki.
Turaki na fitowa daga fada ya fice bai bari sun haɗu da Baffa ba, iyakar kyau dai yayi kyau kowa ya gansa yaga sabon ango amma sam babu wannan annurin na farin ciki a fuskarsa.
Gimbiya Ilham kam tun sanda tai ƙoƙarin kama hannun Turaki taji yanda ya make hannunta taji jikinta yyi sanyi, musamman da ta kalla fuskarsa taga ya murtuke kamar wanda aka yowa aiken mutuwa, kace bai taɓa dariya ba a duniyarsa.
Turaki na isa gida Hajiya Madina tasa key ta kulle side ɗinta dan bata ma so wasu ƴan bani ka iya ɗin suzo mata, ko kuma Baffa ya dawo yace zai shigo.
hakan ko sai data faru, mutane suka dinga zuwa gidan suna juyawa, Mai Gadi na faɗa musu abinda Hajiya Madina tace masa na cewar basa nan, a same su acan masarautar.
to haka dai ranar Hajiya Madina da yaranta suka yini cikin ɓacin rai, iyakar yin Baffa ya gana da matarsa da yaransa Hajiya ta toshe duk wannan ƙofar, sai haƙura yayi dole, dan ko a washe gari sai gidan Hakimi ya tafi yay breakfast dan shima irin Turaki ne bai iya cin abincin restaurant ba.
kuma a ranar da daddare Boɗejo tazo ta tayar da wuta a gidan, kamar zata cinyesu saboda masifa akan Turaki sai yaje Dinner, har da cewa,"aini Madina ban san ke fitinanniya bace sai yanzu, ashe kin ma fi Fulani Azima haɗari, to wallahi dai akan auren jikana da jikata aniyarki ta koma miki".
Maama dai ɗaga kai bata yi ta kalla Boɗejo ba balle ta tanka mata, har ta gama zazzaga masifarta da yaɓa magangunta.
Boɗejo ta tasa ƙeyar Turaki a gaba tace,"wuce motar Nasiruddeen na waje suyi maka rakiya, in an hana ƙawayenka zuwa ai kana da ƴan'uwa".
sannan ta juya kan su Zaytuna tace,"ku kuma ku wuce muje, haka kawai za'a tusa muku baƙin hali a zuciyarku, tsakani da Allah mene abin baƙin ciki a wannan aure banda ma dai zuciyar mutum ba ta da ƙashi. to kuyi gaba muje ba sai kunyi wata kwalliya ba, idan ban isa da wasu ba ku ai na isa da ku. ƙulla auren zumunci kuma yanzu na fara, kuma inga uban da zai sa Turaki ƙaro aure dan naji ana ƙishin ɗin haka, in ban ba'asa naje na bankawa ƴar mutane wuta ba".
haka ta saka su a gaba har Khalil da su Samha da suka dawo a yau suka wuce suka tafi. wajen dinner dai iyakar haɗuwa ya haɗu, amarya da ango sun haska guri, amma ko kaɗan fuskar ango bata murmusa ba, MC ma da yay batun liƙi sai Khalil ne ya fito ya wakilce shi ya watsa bandir ɗin ƴan 500 har guda biyu.
kuma fuskar ango kaɗai zaka kalla ka hasko tsantsar rashin son auren a tare da shi, Gimbiya Ilham kam da ƙyar ta iya controlling hawayenta ta dinƙa yaƙen ƙarya, saboda gaba ɗaya ta fahimci Turaki ba auren ne baya so kaɗai ba ita kanta ba sonta yake ba.
bata tabbatr da hakan ba sai after an tashi daga dinner sunzo shigo mota yace,"ki bar cusa kanki gare ni, domin ni ba sonki nake ba, cusa min ke akayi. idan kuma wancan son kike tunani har kika iya amfani da shi kika sa aka ƙulla wannan auren to kinyi babban kuskure, domin ni son ƙanwa nake miki ba shirmen so irin naki ba. and again ki san da cewar baki da matsuguni a zuciyar Turaki dan already wata da ta fiki komai ta cike wannan gurbin".
wannan maganganun nasa yasa tayi kuka ta gode Allah a wannan daren, kuma sai ta dasa zarginta akan Gimbiya Aisha.
washe gari ma kamar ba zata je Cocktail party ba amma haka dole taje, shima kuma taga abinda yafi na jiya a wurin Turaki, don opalli ya nuna kowa ba auren so suka yi ba.
ranar lahadi da za'a kaita tamkar ta shiɗe haka taji, tunanin ta inda zata fara zama da shi kawai take yi, Mai Martaba da Fulani Azima su suka kaita gidan anan Estate ɗin su Turaki, daga gidansa zuwa nasu babu nisa, gidan ya gaji da haɗuwa kamar a turai, bai san sanda Baffa ma ya gina gidan ba.
shima Turaki Baffa da Maama ne suka masa rakiya, kuma banda cewar ɗanta za'a kai babu abinda zaisa taje. ko kula Baffa bata yi ba har suka je, yana ta janta da hira tai banza da shi sai Turaki da take kulawa, tana faɗa masa ya cire damuwa saboda yanda duk ya rame.
acan gidan Amarya da Ango ma Hajiya Madina kallon inda Mai Martaba yake bata yi ba balle wata Fulani Azima, bata san ita Fulanin ba so take ba. haka suka gama yiwa ma'auratan nasiha da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 34 Chapter of 73