na tuƙa, ku sai ku tafi tare da wani acikinsu".
tana kama hannun Turaki ta riƙe tace,"a'a mu tafi dai taren, wani cikin nasu yaja wannan ɗin, sai ka faɗa musu key ɗin na jiki". da faɗin hakan taja hannun Turaki suka yi gaba, shi kuma Khalil ya shiga motar ya ɗauko wayarsa sannan yabi bayansu.
hakan akayi, cikin police mutum ɗaya yay driving motar Turaki.
sai da suka yi nisa a tafiya sannan Khalil yace,"Hammah kasan wa ka kaɗe?". Turaki bai ce komai ba, kuma sai a wannan furucin nasa Hajiya Madina tama tuna da wata halitta da aka buge, ta manta da wannan batun ta ɗanta kawai take, kuma tana ganinsa lafiya shikenan ta ƙara mancewa da batun gaya mata da yayi ya buge wani.
tace da Khalil,"koma wacece fatanmu ta rayu, idan ta dawo hayyacinta sai ta faɗi inda take ko kuma akai sanarwa gidan radio".
Khalil yace,"Maama ai wadda muke tare ce, Fillo ce". da maɗaukakin al'ajabi Turaki da Hajiya Madina suka waro ido a tare. tace,"wace kuma Fillo?". Khalil yace,"me aikinmu dai". Turaki dai bai ce komai ba, bai san ya zai kimanta yanda yaji maganar acikin kansa ba.
Hajiya Madina tace,"me yasa kace itace Khalil?". ya sauke numfashi yace,"idan munje asibiti za ki gani Maama".
*Taraba.*
ɗan ƙaramin tsakar gidan share yake tass, sai simintin yay haske kamar sabo. daga ɓangaren yamma wata ƙaramar ƙofa ce ta langa-langa, inda yake nan ne kitchen.
wata dattijuwar mata ta fito daga ɗaki wanda yake daga ɓarin yamma ta buɗe ƙofar kitchen ɗin ta shiga.
ta sunkuya ta sauke tunkuyar daga kan gawayin da take girki da shi. tana saukewa sai ga ƙaramin yaro da bai wuce shekara bakwai ba yazo wajenta yana faɗin,"Yaya ki zuba min abincin kar mu makara". sunan da suke kiran mahaifiyar tasu da shi kenan Yaya.
ta kalli yaron sannan tace,"to Yasir yanzu zan zuba maka, ai kaga sai yanzu na sauke". ta faɗa a sanda ta ke ƙoƙarin ciro farantan roba daga cikin kwandon wanke-wanke.
ta shiga zuba farar shinkafa da mai da yajin a faranti daban-daban, tana ta jin labarin da Yasir ke bata na yacca ake duka a islamiyar tasu.
bayan ta gama rabon abincin tace da shi,"kira su Maimuna su zo su ɗauka, wannan kuma riƙe namu ne ni da kai, ka riƙe da kyau".
ya karɓi filas ɗin abincin ya wuce yana ƙwala kiran Maimuna da Hindu kuzo ku ɗau abinci inji Yaya. yana shiga ɗaki Yaran suma suka fito suka ɗauki nasu, anan tsakargidan suka shimfiɗa tabarma suka zauna suna ci, Yaya na faɗa musu idan suka ɓata wurin sai sun share. hakan yasa Hindu tace da Yayarta Maimuna,"ni dai kinga ban ɓata wurina ba ko".
wani saurayi da bai fi 26 years ba yayi sallama gidan, dogo ne sosai kuma ɗan siriri kamar sandar kara, fuskarsa kewaye da saje wanda ya haɗe da gemunsa, ga kuma gashin bakinsa shima da yaywa fuskarsa kyau.
yaran suka amsa sallamar tasa suna yi masa sunnu da zuwa, ya amsa musu sannan ya shiga ɗakin kishiyar mahaifiyarsa da sallama a bakinsa.
ta gama cin abinci tana siɗe yatsu lokacin, ya zauna kan kujerar parlon da duk taji jiki. ta kalle shi da tausayi tace,"an dawo?".
sai dai ya sauke ajiyar zuciya sannan yace,"ehh Yaya sannu da gida". tace,"yauwa, ya wurin ɗinkin naku?".
yace,"ɗinki babu daɗi Yaya, yanzu ma gudowa nayi saboda kaina da nake jin kamar zai fashe, jiya kwana nayi ban runtsa ba ina kan ɗinkin ƴan bikin nan".
tayi murmushi tace,"to ya za'ai, neman halal da wuya, wataran kuma za'aji daɗi da izinin Allah...amma dai ka kammala musu ɗinkin nasu ko?".
Hamid yayi gajeriyar dariya yace,"yanzu ma da su muka gama rigima ai, Suhaila na cewa ba zata ƙara kawo min ɗinki ba balle ranta ya ɓaci, kuma dan nace idan tayi haka ta burgeni shine tayi fushi ta tafi, inaga da kuka ma ta wuce".
Yaya ta miƙe tana cewa,"an dai ji kunya wallahi, budurwar taka ma sai kayi mata halinku na teloli".
gajeriyar dariya kawai yayi baice komai ba, Yaya ta miƙe tace da shi,"ka ɗauko abincinka kaci ka koma ka ƙarasa aikin mutane, bana son saɓa alƙawari Abdulhamid".
ta shiga ɗaki don shirya Yasir, shi kuma ya wuce kitchen ya ɗauko abincinsa. yana cin abincin ne ƙannensa da suka shirya zasu wuce makaranta suka zo suka ce da shi kuɗin makaranta.
yana kallon Maimuna yace,"har lokacin biya ya yi?". ta ɗaga kai alamar eh tare da cewar,"shekaranjiya da jiya ma duk sai da aka fito da mu, bamu shiga aji ba".
yace,"kuma dan shirme shine baku faɗa ba".
tace,"Kawu ai ban sani ba ko baka da kuɗi".
yayi mata wani kallo yace,"ina ruwanki da rashin kuɗina, karki ƙara yin irin haka".
tace,"to Kawu".
Yaya ta fito daga ɗaki tana cewa,"ba laifinta ba ne ni nace su bari ba yanzu ba".
yasa hannu a aljihunsa yace,"a'a Yaya to ai zuwan nasu baida amfani kenan tunda ko sunje ba barinsu ake suyi karatun ba, kuma ni ai na sami kuɗi kwana biyun nan".
tace,"to Allah ya ƙara horewa dai". ya ɗauki dubu uku ya bawa Maimuna ƴar shekara goma yace,"ungo ki bawa Malam Ado, kice na Yasir da Hindu ne, dan Allah suyi haƙuri su ɗaga ƙafa jibi insha'Allahu za'a bayar da naki".
ta duƙa ta karɓa suna yi masa adu'a, sannan Yaya tayi musu adua suka tafi. fitarsu babu jimawa mai gidan Yayi sallama, sallamar da ta hassada faɗuwar gaba a zuciyarsu Hamid.
"Shema'u! Shema'u". kiran da me gidan keta ƙwalawa kenan, Yaya ta miƙe jiki a sanyaye ta fita tana cewa,"sannu da zuwa".
yay mata wani banzan kallo yana zuƙar tabar dake hannunsa sannan yace,"sai yanzu kika ji kiran nawa ko amsawar ce ba ki ga damar yi ba?".
bai jira cewarta ba ya ɗora da faɗin,"mutuniyar banza da wofi kawai, to ki gama rashin mutuncinki wallah idan banga dama ba aljannah dai ba za ki shigeta ba, tunda a ƙasan ƙafata aljannar taki take, kuma har saina ɗaga miki za ki shiga...kuma indai don ta ni ne na rantse sai da ki zama ƴar kallo, kina ganin mata na tururuwar shiga ke kina daga gefe can".
*Pls Vote, Comment and Share.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*17*
Yaya dai tayi shiru bata tankawa maganarsa ba, idan ma tace zata basa haƙuri wani sabon cin mutuncinne zai biyo ba, to shirun shi yafi alkhairi, but down deep in to her heart zafi ta ke ji, wannan halin na mijinta bata so, ƙaddara dai ta riga fata, ta ɗauki aurenta da Hayyo matsayin wata jarabawa daga ubangiji, kuma tana roƙon Allah ya bata ikon cinyewa.
ta mayar da tarin ƙwallar da ta cika idanunta. ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ɗago ta kallesa tace,"a ɗauko maka abinci?".
Hayyo yayi mata wani kallon banza yace,"mayya kawai wadda kare ya cinye zuciyarta, indai haƙuri ne naga Halima ma, dan haka kema muna nan wannan kafirin haƙurin naki zai kaiki maƙurar da za ki bar gidan nan da ƙafafunki. yo guda nawa kuma akayi?, saki dai kike so saboda ki tafi da hujja to ni ba zan sakeki ba dan bana yinsa, musulmin ƙwarai ne ni sam bana son al'arashin ubangiji ya girgiza".
Yaya ta girgiza kai kawai tana me cike da takaici, ita kanta ta sa ni haƙuri yayi kaɗan ya barka ka zauna da Hayyo, sai dai darajar ƴaƴa, tun bayan aurenta da shi daya sami biyan buƙatar kansa ya fito mata da asalin halinsa wanda yake ɓoyewa a lokacin aure, ta kuma san asalin waye shi wanda yake ɓoyewa idan yaje neman aure.
tunda ta haihu ta bar zamansa ta koma zaman ƴaƴanta, ba zata iya tafiya ta bar ƴaƴanta a wurin uban da bai san darajar ƴaƴa ba sam, ba zata iya tafiya ta bar ƴaƴanta su gantale ba, gwara ko Hayyo zai kasheta ta zauna ta kula da su, ko da ace sai dinga gutsirar naman jikinta ne, zatai ta haƙuri tana jurewa har Allah ya raya mata yaranta ta aurar da su, daga lokacin sai ta tafi ta bar masa gidan, ta bar masa Yasir tunda shi namiji ne, kuma tasan zai sami kulawa a wurin Yayansa Abdulhamid.
Hayyo ya zuƙi sigarin hannunsa ya feso mata hayaƙin yace,"a fito min da tabarma". ta juya cikin parlon tana sa hannu ta goge hawayenta. Hamid na zaune ya kasa ƙarasa cin abincinsa saboda baƙin cikin da takaicin rashin kyan hali na mahaifinsa, ya kalli Yaya da tsananin tausayi, ya sauke ajiyar zuciya yana tuno da tasu mahaifiyar, itama haka tasha fama, dan zai iya cewa ma har yanzu Yaya bata ɗanɗani baƙar kuɗar da tasa mahaifiyar tasha ba a wurin Babansa.
adu'a yake kullum, kuma yasan adu'arsu ta karɓu, lokaci kawai zasu jira sai dai idan ba'a raye, but dole-dole za'a zo time ɗin da mahaifinsu most regret all his past, lokacin da Allah ya shirye shi kenan.
ya miƙe tsaye jiki a saɓule ya karɓi tabarmar da Yaya ta ɗauko, yana kallon yanda hawaye ke bin kuncinta zuciyarsa na tsinkewa. muryarsa can ƙasa gudun kar Hayyo ya jiyo shi yace da ita.
"Yaya dan Allah ki bar kuka, komai lokaci ne kuma komai yana zama tarihi...kin san abinda zai kuma biyo baya idan yaga kina wannan kukan". ya faɗa tare da goge mata hawayen.
tace da shi,"na gode Hamid".
yace,"abincin nasa na kitchen ko?". ta ɗaga masa kai,"ehh yana ciki, cikin wannan filas ɗin daka siyo mana da azumi".
Abdulhamid ya fice hannunsa riƙe da tabarmar. Hayyo na jingine da jikin bango yana ta zuƙar tabarsa cikin ƙwarancewa da jin daɗi.
Hamid ya shimfiɗa masa tabar, Hayyo ya zauna har lokacin bai ko kalli Hamid ba.
"sannu da dawowa Abba".
kamar yanda ya tsammata dama babu amsa, dan shi zai iya cewa rabon da magana ta haɗasu da mahafin nasa tun azumi wata biyu kenan, haka ɗaya babu siɗi ba saɗaɗa, ko ya gaishe shi baya amsawa, hakana duk maganar da zai yi masa ba zai tanka masa ba. dan haka ya miƙe jiki a saɓule ya nufa soro inda ɗakinsa yake, ya ɗauko ƴar ƙaramar radio sabuwa ya dawo ya durƙusa gaban Hayyo.
ya kamo gidan radiyon daya san nan ne zaɓin Hayyo, ya ajiye a kusa da shi. lokacin kuwa ana labaran siyasa, cikin ran Hayyo yaji daɗi sosai, dan shi a rayuwarsa daka masa kyautar kuɗi ma gwara ka basa radiyo, tana saka shi nishaɗi musamman idan labaran siyasa ake. amma ba zai taɓa nunawa Hamid yaji daɗi ba balle ma har wata adua ko godiya ta shiga tsakaninsu.
jiya da shekaranjiya da bai saurara shirye-shiryen da yake ji ba duk jinsa yayi kamar mara lafiya, saboda tsohuwar radiyonsa taɓaci tun ranar da akayi wani mamakon ruwan sama, ta shige cikin ruwan daya cika ɗakinsa dalilin zubar da yayi. kuma babu kuɗi hannunsa dalilin ma da har ya ɗau wannan kwanakin babu ita.
kuma yasan Hamid ya siyo radiyon ne saboda shi, tunda akan ƴan ƙanan yaran ya sauke ɓacin ransa na lalacewar rediyon, dan duk sai daya bi ya zane yaran, ko yau da safe da zai fita yaga shatin wayar daya tsulawa Maimuna a fuska bai baje ba, amma bai ko bi ta kanta ba tunda ƴaƴa ne da basa gabansa, su rayu ko su mutu babu abinda yay masa zafi, haka suyi lafiya ko rashinta ko a gefen yatsansa.
ai yasha faɗawa ƴaƴansa da ku da shegu ɗaya na ɗauke ku, shi yasa bana wani ganinku da ƙima. zai fi muku ma ku nemi wani uban ko kwa ɗanji daɗi, amma a hakan dai Hamid yace masa a hakan kuma muke ƙaunarka Abba, muke alfahari da kai, duk tsanani ba zamu taɓa barinka ba, kuma zamu yi duk iyakar ƙoƙarinmu wajen ganin mun faranta maka, wajen ganin bamu saɓa maka ba. zamu maka biyayya, kuma zamu tsare mutuncinka.
acikin radiyon aka sako waƙar ɗan ƙwairo, Hayyo ya kama bin waƙar yana buɗe flask na abincin da Yaya ta aje masa. kamar wanda yaga kashi daya ga shinkafar, amma a haka ya cinyeta tas.
da yamma Yaran suka dawo daga makaranta, tunda sukai sallama suka ga Abban nasu a tsakargida suka kama raɓe-raɓe jikin bango. suna mugun tsoronsa, sunfi sakewa idan babu shi a gidan, idanma fita yayi sukan manta da shi. wataran Maimuna ta cewa Yaya ita gwara ma ace bata da Baba akan dai ta nuna Abba ace shine Babanta. a lokacin Yaya taita mata faɗa da cewar kata ƙara jin wannan zancen a bakinta, amma duk da haka Maimuna a makaranta bata amfani da sunansa, sai dai sunan Yayansu, Maimuna Abdulhamid haka ta ke using.
*VISION APARTMENTS, Zurich, Switzerland.*
a tsaye take a gaban windon parlon, windon dake ɗauke da manya manya gilasai, kalarsa ta haɗe da yanayin yanda hasken garin yake a lokacin. lokacin yammaci ne, yanayin garin na nuna cewa ruwan sama bai jima da ɗaukewa ba.
sanyin danshin ruwan na ratsowa ya shigowa cikin parlon, wanda ya gauraye da sanyin ac da kuma ƙamshin dake cikin parlon. hakan ya haɗu ya bada wani sanyayyan ƙamshi me daɗi, kalar komai na parlon ruwan toka ne.
sanye take da baƙin wando wanda ya ɗameta, hannayenta dake ɗauke da bangles acikin aljihun wandon, riga ce me ƙaramin hannu milk daga ciki sai ta ɗora rigar sanyi me kauri akai, irin rigar sanyin nan me gashi a hularta. hular ta rufe kusan rabin fuskarta. fara ce sosai, me kyan fuska, hancinta har baka, idanuwanta manya. jelar gashinta ta zagayo ta gefen wuyanta ta sauka akan kafaɗarta, hakan zai shaida maka kitso ne guda ɗaya tal a gashin nata.
kallon gilashin windon take tana ganin yacca sauran ruwan sama ke sauka akansa. sam ba haka taso ba, ba haka taso lamarin ya tafi ba, sai da ta rufe ido ta buɗe sannan tace.
"ba haka muka tsara ba, ba shirin da muka yi ba kenan. abunda muka tsara shine Turaki zai mutu a wannan ranar kuma a wannan lokacin cikin wannan dajin, lissafin da mukayi kenan, mun lissafa tarihinsa zai shuɗe ne cikin ƙanƙanan lokaci, zamu goge hotonsa da sunansa da duk wani abu daya dangance shi daga wannan zuciyoyin guda biyu...to amma me yasa komai ya rushe?, lissafin da mukai ya hargitse?".
da shi take magana, saurayin dake zaune akan kujera yana fuskantarta, fari ne shima, me kaurin jiki, me siririn saje. shekarunsa ba wasu masu yawa bane, ƙananun kaya ne jikinsa blue jeans and red t-shirt long slip, sai facing cap baƙa daya saka. tarin gashin girarsa ya kusa haɗewa, kallonta kawai yake tunda ta tsaya a gaban windon, har zuwa yanzu da take magana da shi.
"kina nufin laifina ne kenan?".
a zafafe ta juyo ta fuskance shi tana ɗage hular rigar sanyin ta koma baya ne. "ƙwarai laifinka ne, idan da ace ba lusaran mutane kaje ka samo ba me zai sa shirinmu ya ruguje?.". sai tayi shiru taja dogon tsaki sannan tace,"now what will happen next?".
har yanzu bai ɗauke ƙwayar idonsa a kanta ba, sai daya miƙe tsaye sannan yace,"shi zai kawo kansa garemu next ba sai mun wahalar da kanmu ba".
matashiyar budurwar tayi masa kallon baka da hankali sannan tace,"ta ya?". yay guntun murmushi yace,"rauninsa mana". tace,"like how?". ta faɗa fuskarta na nunawa da rashin fahimta.
"Mahaifiyarsa, Maama, Hajiya Madina. ita zamu ɗauke, ita ɗaya zamu ɓatar Turaki yazo garemu da kansa, da ƙafafuwansa ba'a mota ba, da wannan damar zamu yi amfani wajen ganin mun cimma burinmu akansa, burinmu kuma mafarkinmu na ganin baya raye".
kamar bata gamsu da hakan ba a yacca ya gani a fuskarta, hakan yasa yayo tattaki zuwa gabanta, ya zagayeta sannan ya tsaya a bayanta.
"karki ji komai, babu wata matsala...wannan karan babu kuskure ina da yaƙinin hakan...wancan matsalar da aka samu yaran sun ce unexpected suka ji syring ɗin motar police, banda haka tuni sun gama da shi. kuma kinga muma bamu tsammaci hakan ba, ba ki karanta min da cewar hakan zai iya faruwa ba, da tunda wuri za'a aiwatar da komai...Hajiya Madina itace matsalarmu a komai shi yasa ya zama tilas dole mu fara ɗauketa daga kusa da shi".
ta sauke numfashi tace,"kasan mene?, a rayuwa raunin Turaki mutum biyu ne, Hajiya Madina da kuma Zaytuna, saboda haka tunanina ya sauya. zamu fara gamawa da Zaytuna kafin zuwan komai...Zaytuna tana da saurin yarda, tana da saurin sakin jiki musamman ga talaka, dan haka na san ta inda zan ɓullowa lamarin...kaima bance ka tsaya da naka aikin ba".
tana faɗar haka ta ɗauki wayarta da ke kan center table, ta nufi hanyar bedroom tana faɗar,"gobe zan bar ƙasar nan".
"nima haka". shima saurayin ya faɗa yana me ɗaukar car key ya fice daga apartment ɗin.
****
ƙafafun Turaki suka fito daga parlon, sanye yake da wata dakakkiyar shadda aqua colour da tayi bala'in yi masa kyau, ɗinkin boda ne da aikin sama. kansa babu hula sai dai sumar kan tasha gyara sai ƙyalli take yi. duk ya rame, ya fige, fuskarsa ta ɗanyi duhu, idonsa yayi jaa kuma ya faɗa ciki kamar mara lafiya, saboda kawai saka abu a ransa da yayi, yarinyar nan daya kaɗe wadda tsawon kwana uku sai jiya ta farfaɗo, tun ranar da accident ɗin ya faru baya iya cin abinci, rashin bacci da kuma rashin kwanciyar hankali duk sun dabaibaye shi.
ya kalli agogon wrist ɗinsa yaga goma harda minti biyu.
"Khalil". ya kira sunan Khalil wanda ke daga cikin parlo, ya amsa masa yana faɗin,"gani nan fa". Turaki ya ƙara magana da muryar ƙorafi,"kai indai za'a fita tare da kai sai ka ɓata lokaci".
a time ɗin ne kuma Khalil ya fito, suka jera tare zuwa part ɗin Baffa, bakinsu ɗauke da sallama suka shiga parlon, Baffa yana zaune da mijin ƙanwarsa Falmata SS Ƙasim Kurfi.
Khalil da Turaki suka zauna ƙasa suka gaishe su. Alhaji Ƙasim ya shiga tambayar Khalil wurin aikinsa. after few minutes Baffa ya dubi Turaki yace,"ya jikin yarinyar da ka bige?".
kansa na ƙasa yace,"ban sa ni Baffa, amma dai jiya da daddare likitan yace ta farka after mun baro hospital ɗin".
Baffa ya jinjina kai, kamar ba zai ce komai sai kuma yace,"amma dai you supposed to go and check on her, kai ne sanadin halin da take ciki, so alhakin kula da lafiyarta ya rataya a wuyanka na faɗa maka hakan tun ranar dana dawo, bai kamata a tambayeka jikinta ba kai tsaye kace baka sa ni ba...idan ni ne kai ko asibitin ba zan ke iya bari ba".
Turaki yace,"dama can zan tafi yanzun". Baffa yace,"tou yayi, kuma idan kaje ka zauna da doctor ɗin nata kaji game da lafiyarta".
ya amsa da,"to Baffa". suka tashi zasu tafi Baffa ya tsayar da su, yace da Khalil ya ƙarasa ya buɗe drower dake can wajen tv ya ɗauko masa envlope. few seconds ya ɗauko ya kawo, Baffa ya buɗe ya ciro sabbin dollers ya bawa Khalil, ya karɓa yana jiran cewar Baffan.
already Turaki ya kai ƙofa, kiran sunansa da Baffa yayi ya dakata ya juyo, Baffan yace da shi,"kuyi changing nata before ku ƙarasa asibitin sai ka bawa Kakar Yarinya".
Turaki yace,"to Baffa Allah ya ƙara wadata".
da haka suka fice. bayan sun shiga ɓangaren Boɗejo sun gaisheta sannan suka wuce wajen Maama, a bedroom nata suka sameta, sun ɗan jima wurinta kafin su fito, itama ta bada nata saƙon dubiyar akaiwa Kaka.
motar Khalil suka shiga, Turaki ne ke driving, yayin da Khalil ke kujerar gefensa yana karanta jarida, news update ɗin da aka saki akan ASUU strike, tsaki yake taja saboda takaici, yanata ƙorafi akan strike ɗin, gami da tausayawa ɗan talaka da baida yanda zai yi.
ko jiya yana zaune Maama ta ɗauki nauyin karatun wasu yara su biyar zuwa turkey, maza uku mata biyu. tunda yake ta complain ɗinsa dai Turaki bai ce komai ba, hasalima tun shigowarsu motar bai yi magana ba, seems like hankalinsa ma baya cikin motar.
Khalil ya ɗaga wayarsa da call ya shigo, yayi taking 3minutes yana wayar before ya gama. kuma sanda ya gama ɗin Turaki ya juyo ya kalle shi a lokacin da yake ƙoƙarin yin U-turn.
"ina sketch ɗin ne?, jiya kace zaka nuna min muka manta gaba ɗaya".
Khalil ya juya baya ya ɗauko takardar, yana nunawa Turaki yanda akayi zanen sabon company nasu da Baffa zai buɗe. yana kallon sketch din yana kuma driving a hakan. yanda akayi sketching ɗin bai yi masa ba sam, hakan yasa shi cewa.
"wanne Arch ɗin ne yay wannan zanen?".
Khalil yace,"Yahya Ƙosa".
yace masa,"why zaka bawa daƙiƙi irin Ƙosa zanen abin arziƙi?, me Ƙosa ya iya?, kai baka ga irin haukan daya zuba ba ne a gidan Hakimi, har kwanan gobe Hakimi complain yake da wannan gidan".
Khalil yace,"ni fa Hammah is not my fault, Baffa da kansa ya basa, nawa karɓa ne kawai. Baffa ma so yayi ana kawowa a bawa engineer na faɗawa Maama ai baka gani ba tukunna".
Turaki yace,"ka yaga shi kawai dan ba za'ai amfani da shi ba, ji wani shirmen banza fa wai office na accounter a compound na Company...kuma a hakan degree holder yake ko?".
Khalil yay dariya yace,"kafa san komai Hammah".
tsaki Turaki yayi yace,"ka kira Lawan Shehu kai masa bayanin komai, shine zai yi mana aiki me kyau".
sai da suka tsaya a banka sukai changing doller tukunna suka ɗauki hanyar Miyetti Hospital.
Khalil ne ya fara wucewa ward ɗin yayin daya bar Turaki a mota yana waya da Bello Ƙaraye, zai biyosa daga baya.
kiran sallar da akeyi a masallaci ya fito da Turaki daga motar, yana waya da Zaytuna a lokacin bayan sun gama da Bello. cikin sauri yake tafiyar yana so ya fara zuwa ward ɗin da Fillo take sannan ya wuce masallaci dan baya son rasa jam'i.
yana tafiya yana wayar bai gani ba yayi karo da mutum, wayarsa ta faɗi ita kuma jakar hannunta ta faɗi kayan ciki suka zube kasancewar jakar ba me zip bace. Turaki ya kalla wayarsa daya tabbata ta fashe, tukunna yabi tarkacen jakar da suka zube da kallo, kayan makeup ne duka, sannan ya ɗago ido yana kallon wadda suka yi karon.
haƙuri yake niyyar bata, amma ganin yacca take faman cika tana batsewa sai ya ɗauke kansa ya fasa, laifinsa ne amma haƙuri dai ba zai bada shi ba.
ganin baida niyyar bata haƙuri kuma baida niyyar tsugunawa ya kwashe mata kaya yasa a gadarance tace da shi,"are you blind da kake tafiya baka kallon gabanka?, kuma hala baka gaji arziƙi ba shi yasa baka san yanda ake bada haƙuri ba. to ka duƙa ka kwashe min kayana ka miƙon jakata".
da wani irin ɗacin rai Turaki yake kallonta, imagine wadda yayi ƙanwa ta uku da ita take faɗa masa haka. yarinyar kyakkyawa ce, me hasken fata kamar madara, mai kyakkyawan jiki irin wanda yaji komai da ake buƙata a jikin ƴa mace. kallon farko ba sai ka ƙara na biyu ba zaka san macece da ta samu hutu, gata, da tarin ilimin boko. Kuma ba sai an faɗa maka ba, a maganarta da yanayinta zaka gane ƴar sarauta ce da mulki ya gama ratsa gaɓoɓin jikinta.
Turaki ya ɗauƙe idonsa akanta yana me fesar da iska daga bakinsa, matsawar yaci gaba da tsayuwa anan komai zai iya faruwa, saboda haka ya taka da niyyar barin wajen ba tare daya tsaya ya ɗauki wayar ba, baida buƙatarta domin ba zai rasa komai ba tunda yana ajiya a goggle, welcome back na line nasa kawai zai yi. sai dai yana niyyar barin wajen kawai yaga fadawa sun kewaye shi ta ko'ina, one by one ya kalle su, sannan ya ƙara kallon yarinyar, bai san lokacin da wani murmushi ya suɓuce masa ba har sautinsa ya fito. yasa yatsansa ya sosa girarsa, kafin ya shafo wuyansa still da smiling akan leɓensa.
a lokacin ne ɗaya daga cikin fadawan ke ce masa,"ka bawa gimbiya haƙuri sannan ka nemi yafiyarta, idan ba haka ba fushin Mai Martaba zai tabbata akanka, kuma zaka fuskanci hukunci daga masarautar kano".
shirun bafaden ya haɗe da tayar da iƙama a masallaci, muryar Turaki ta fito da wani amo mai taushi zuwa ga Gimbiya Aisha yace,"zanje nayi sallah, ki jira na dawo zan duƙawa izzarki kamar yanda kike so, zanta baki haƙuri har sai kin ƙoshi". yana faɗin hakan ya wuce ya ɗauki hanyar masallacin cikin sauri, tafiyar da ba zaka ce sauri yake ba saboda nutsuwar da ta shimfiɗu acikinta.
Gimbiya Aisha tabi bayansa da kallo tana jin wani malolon abu na tsaya mata a rai, _ta jira shi ya dawo._, haka ya faɗa mata fa, waye shi?, me yake ji da shi?, aina ya samo wannan isar?, ina ya sami ƙwarin gwiwar saka idonsa cikin nata bayan yaji wacece ita?. ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 73