Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ɗaura ɗankwali. Tana ɗaurin ta ke cewa Yusuf. "Yaya ashe ka shigo. Ɗazu Ammi ke cewa ƙila har ka koma ba lallai ta ganka ba...idan ka gama abinda kake naji dai tana batun zuwa abuja yau". Ya ɗago da ido ya kalleta yace,"me zai kaita Abuja?". Time da ta ke gama ɗaura ɗankwalin tace masa,"biki mana...daughter ɗin ƙawar nan tata da aka haɗaku kaƙi, itace zata auri ɗan gwamnan jigawa". Ya maida idonsa kan wayarsa yace,"When will she come back?". Tace,"I don't know. but i heard her saying sati guda za'ai ana bikin". Karo na biyu ya ɗago ya sake kallonta. "kuma Daddy ya barta?". "kai dai Yaya babu ruwanka. Ka barta taje tai hidimanta ta dawo". Still yana kallonta yace,"ki shirya ku tafi tare". Tayi saurin kallonsa da cewa,"niii babu inda zanje. Haka kawai na bita Ammi ta dinga cusa ni cikin yaran nan masu shegen ji da kai suna min kallon raini". Ya ƙara cewa,"you mean ita ɗaya zata tafi?". "kamar dai hakan. Amma ƙila Nabla ta bita kasan ita amara ƙirjin biki ce". Bai ce komai ba ya miƙe tsaye yana zuba hannayensa cikin aljihu. Yana cikin saka takalminsa Inna Wuro ta dawo parlon, tayi kasaƙe tana kallon Yusra dake yafa ɗan yalolon mayafinta a kafaɗa. "kuma fita zaki yi a haka?". Inna Wuro ta tambayeta tana kuma ƙarewa shigar jikinta kallo. Yusra ta jefa cingom bakinta ta amsa mata."yesss mun koma school yau...na manta ma ban faɗa miki ba, ko da yake jiyan na shigo ai na tarar kinyi bacci, an kafe mana result and i don't have any problem". Inna Wuro tayi mata wani kallo, kamar ba zata ce komai ba sai kuma ta juya ta dakatar da Yusuf dake shirin fita tana ce masa. "wai kuwa kana kallon a yanda yarinyar nan zata fita shine ba zaka tsawatar mata ba, kana babba amma kai sam baka san abinda ya kamata ba, da kai da hoto duka ɗaya. Kalla fa gantalallan ɗinkin dake jikinta, wuya duk a buɗe kusan rabin nono a waje, amma a haka ta ke ikirarin zata fita har makaranta salon ta jawa Amadu zagi". Sam Yusuf bai lura ma da kayan dake jikin Yusra ba balle ɗinkin, sai bayan daya gama saka takalmin ya kalleta, sai aikin zumɓura baki gaba ta ke yi tana ƙunƙuni, da gaskiyar Inna Wuro dole tace gantalallan ɗinki, shi a wurinsa ma wannan ɗinkin asarar kaya ne. "ke karki kuskura ki fita a haka". Ta ƙara kumbura kamar zatai kuka ta ke nuna kayan jikin nata. "fisabilillahi me wannan ɗinkin yay, ni gaskiya babu abunda zan sauya tunda ko Ammi ta ganni da su kuma bata ce komai ba". Inna Wuro tace,"yo wannan Uwar taki sanin ya kamata tayi da zata hanaki fita tsirara". Yusuf ya wurga ma ta wani mugun kallo. "yaushe na fara wasa da ke? Ki wuce ki sauya su babu inda zaki fita a haka". Yana rufe baki Aliyu ya miƙe daga kwancen da yake, shima yana mata wani banzan kallo irin na baya son raini yace,"Uban waye sa'anki anan da ana yi miki magana kina ke ba haka ba. Kin wuce kinyi abunda akace ko sai na saka miki ƙafa". Yusra ta fashe da kuka tana bige-bigen ƙafa a ƙasa, ta wuce Inna Wuro tana faɗin ba zata ƙara zuwa site ɗinta ba sai dai idan sauya mata suna akayi. Inna Wuro ta bita da cewa,"ai dama bani ke gayyato ki ba, ke kike kawo kanki". Ta dubi Yusuf tace,"yau zaka koma kano ɗin?". Yace,"may be". Ta taɓe baki tai ciki abinta. "kai kasan abunda kace, ni dai nafi ƙarfin zagi da yaren bature. Na ɗauka yau ɗin zaka tafi na baka saƙo ka kaiwa Nuratu". Jin ta ambaci abar ƙaunarsa yay saurin cewa,"ki bada yau zan koma". Tace,"na fasa ai". Sannan ta dubi Aliyu tace,"kai kuma ɗan zaman kashe wando idan zaka tafi karka bar min tv a kunne ka kashe min". Yusuf na fitowa yay part ɗin Ammi mahaifiyarsa, har ya shiga parlon sai ya fito sakamakon murɗawa da cikinsa yay, ya koma part ɗin Hajiya Falmata da suke kira da Umma. Step sisters ɗinsa ya tarar a parlon su biyu, Salma da Kursum. Ya ƙarasa shiga ciki ya zauna kan kujera suka gaishe shi, Salma ta miƙe tana faɗin,"bari na kira Umman". Tare suka dawo da ita, Salma na gaba ita tana baya da waya kare a kunnenta tana bada sallahun da za'a taho mata da shi daga kano. "yanzu ka shigo?". Ya kalli Umman da tai masa magana yace,"na ɗan jima ina wajen Inna Wuro". Tace da shi,"aiko ga breakfast ɗinka can ina ga ma yay sanyi". Ta kalli Kursum tace,"je kiyi warming abincin Yayanku". Within 3mints Kursum ta dawo ta janyo center table ta ɗora plate ɗin abincin a kai. Yana ci suna magana da Umma, tana sanar masa tafiyar Nameer da yay a ɗazu, ya samu aiki a wani company dake can taraba state. Bayan ya sauke spoon daga bakinsa yace,"Nameer ɗin yace min Daddy bai yarda da zuwansa can ba". tace,"da ƙyar Alhaji Saleh yay conviecing ɗinsa ai, shine Nameer ɗin ya wuce yau da wuri". "to Allah ya taimaka ya bada sa'a". Umma ta amsa da amin. Sauri sauri Yusuf ke yi wajen cin abincin dan gaba ɗaya hankalinsa na can wurin Ammi, fatansa ma Allah sa Yusrah bata faɗa mata ya shigo ba. Yana gamawa ya miƙe yana yiwa Umma Sallama. Ta tambaye shi,"when zaka koma?". Yace,"may be da yamma ko kuma gobe". Umma tace,"Nuratu tai min complain jiya da mukai waya...". Tun Umma bata ƙarasa maganar ba yay murmushi tare da cewan,"tare zamu tafi insha'Allahu". Itama tai murmushin tana cewa,"sai ka dinga haƙuri da rigimar Nuratu, musamman yanzu da ba ita kaɗai bace". Fitowarsa daga part ɗin Umma na Ammi ya wuce, a parlo ya tarar da ita suna magana ita da yaranta, ya ƙaraso ciki kansa a ƙasa gabansa sai faɗuwa yake. Ammi kam ko iskar da ta ɗebo shi ta kawo shi bata kalla ba, maid ɗin dake riƙe da trolley ɗin Ammi ta durƙusa ta gaishe shi ya amsa. Sai da ya bari Ammi ta gama magana da yaranta sannan ya gaisheta, tai banza da shi tamkar bata ji shi ba. ta zo fita ne ma ta tuna da ƙararsa da Yusrah ta kawo mata sannan ta dakata daga fitan, ta dawo tai tsaye akansa. "idan ka wulaƙanta ni nayi maka shiru ba zan yarda ka dinga saka min yara kuka ba ka aje wannan a ɓangaren tunaninka...idan ba haka ba wallah ba zamu kwashe ta daɗi da kai ba, ba ruwanka da sabgar ƴaƴana ka fita a harkarsu". Ya ɗago ido ya kalleta ta ɗauke nata daga kallonsa, muryarsa a ƙasa yace,"ita Yusran me tace miki dama?, babu wanda ya duketa balle zagi, kayan da zata fita da su ne basu dace ba akace ta sauya shikenan sai ta ɓare baki...". Ammi ta wurga masa wani kallo tare da cewan,"ni rufe min baki, ina ruwanku da shigar da tayi, ina ce ai ba tsirara zata fita ba ko?...da ƴaƴan waccan Matar ne da kake kallonta da gashin ido ai ba zaka ce da su ƙala ba, sai nawa ƴaƴan da aka raina shine za'a bi a takura musu...to da gatansu tunda ban mutu ba saboda haka a bar takura musu, na faɗa maka. itama kuma Kakar taka ka faɗa mata...shima Aliyun zai shigo ya same ni". Ya girgiza kansa kawai, kamin yace,"kiyi haƙuri". Tana ƙoƙarin fita maganarsa ta tsaida ita,"Ammi dan Allah ki kwana ɗaya kawai". Tace,"tunda takarda aurena a hannunka ta ke me zai hana". "dan Allah Ammi, wallah idan ki kai nisa da yawa gidan baya daɗi". Tai murmushin takaici,"har yaushe asirin da ke kanka ya kunce daka fara sanin muhimmancina acikin gidan nan?...kaima ka zama mace ka iya makirci kenan, to ni ba zaka yaudaren ba, ko ɗazu baka san ina kallonka ka shigo ka fita ba ne saboda kana tsoron kada uwarka ta tsine maka...". Yusuf yay saurin katseta da cewan,"Ammi don Allah ki daina irin wannan maganar...". Itama bai ƙarasa ba ta katse shi da faɗin,"an riga an shanyeka ai duk gaskiyar da zan faɗa a iska zaka dinga jinta". Yay shiru bai ce komai ba, ta ƙara cewa,"ka tashi ka kaini airpot". Yay saurin miƙewa yana karɓan jakar hannunta suka fita tare. Tunda suka shigo motan babu wanda yay magana, har ga Allah Yusuf naso yay hira da mahaifiyar tasa amma yana tsoron ta balbale shi da faɗa, dan yanzu da abunda yake na faɗa da wanda ba na faɗa ba duka na faɗa yake zamar mata indai tsakaninta da shi ne. Tunda yazo ma yake son mata albishir da cikin Nuratu amma yana tsoron abunda hakan zai haifar, dan bata ƙi ma tai muguwar adu'a ba tunda ba son auren nasu ta ke ba, ita duk abunda ya shafi Falmata to shikenan ta ɗaura gaba da shi, yasan da ace Nuratu ba jinin Falmata bace Ammi zata ɗan rangwanta masa akan ƙin zaɓinta da yay. Maganarta ta kutsa cikin tunaninsa. "yarinyar da na so na haɗaku ce za'ai bikinta. Da yake Allah ba azzalumin bawansa ba ne sai ya haɗata da wanda ya fika. Ɗan governor ɗin Jigawa ne, yaron ance a ƙalla ya mallaki sama da miliyan 200. Shi ɗaya ne a wurin mahaifinsa, babarsa ita ɗaya ce for morethan 35years da suke tare da mijinta...ba irin Babanka ba da shekara 15 muka ɗauka tare yaje ya ɗauko min annoba". Yusuf yace,"Allah sanya albarka a auren nasu". Aciki ta amsa masa, yana kallon yanda ta ke hararsa ta cikin window, tunda yake da ita basu taɓa fita tare ba ta shiga back seat ba sai yau, tunma bayan auren nasu dama bata yarda ta shiga motarsa, hanya ma bata so su haɗa da shi. "Ammi Nuratu ta kwan biyu bata da lafiya". Ya faɗa cikin kwantar da murya. Ammi ta dakata daga danna wayar da ta ke yi ta ɗago ta dube shi, kamar ba zata ce komai sai can kuma a hankali tace,"bata da ƴan'uwa ne?". Ya rumtse idonsa sosai kamin yace,"tana da su mana Ammi". "ohh tou kuma kazo kana faɗa min bata da lafiya, ai su zaka je ka sama bani ba da ban haɗa dangi da ita ba". Bai ƙara cewa komai ba yay shiru, Sani Abacha International Airport ya ajiyeta, bai baro wajen ba sai da jirginsu ya tashi tukunna. Yana kan hanya abokinsa Dr Huzaifa ya kira shi, saboda haka ya yanke hanya ya biyo ta shongo estate. Slowly yake driving ɗin, Idonsa na kallon left side yana kallon wani gini da ake ƙarasawa, idonsa ya sauka akan yashin da tifa ta juye yanzu ta bar wajen. Kamar wanda ya tuna wani abu sai ya waiga yana daɗa kallon wajen daya bari, hoton wannan yarinyar ya haska acikin idonsa a wancan lokacin daya taɓa wucewa ta wajen. Tana zaune a gefen yashi ta ƙudundune tana rera kuka a hankali, ta riƙe siririyar doguwar ƙafarta tana kallon wajen da taji ciwo cike da tashin hankali. Gaba ɗaya ciwon ba wani babba bane, amma kace wadda akace ƙafartata ce ta ruɓe za'a yanke saboda kawai jinin daya fito a wajen ɗan kaɗan. sai yaga kamar yanzu ne abun ya faru, dan bai san lokacin da leɓensa ya tale da murmushi ba tunawa da yay da irin dramar da suka sha da ita akan kawai ta bari ya saka mata bandage akan ciwon da taji. _"jinina zai ƙare"._ Haka ta faɗa masa a lokacin daya tsuguna gabanta yana tambayarta me ya faru, cikin muryar kuka, kuma duk da cewar muryar tata ɗauke ta ke da kukan da tasha, hakan bai hana daɗin muryarta fitowa ba. Ta runtse ido ma ta kasa kallon ciwon, ya koma mota ya ɗauko first aid amma ko da ya dawo sai ya tarar bata wurin, abun yay matuƙar bashi mamaki a sannan, dan zatonsa ma ko aljana ya gani ko kuma aljanu suka buɗe masa ido yau, saboda kyan yarinyar ma yafi kama dana aljanu. Kuma sai can zai bar wajen ya hangeta ta ɓoye a bayan bulo, ashe first aid box ɗin daya ɗauko ne yasa ta guduwa. *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *6* Yau ya kasance juma'a. Ƙofar gidan na Judge Dikko Habib cike yake da ɗumbin mutane masu zuwa karɓan sadaqa, yara da manya musamman ma magidanta marasa ƙarfi, haka gidan yake kasancewa a duk wata juma'a, zaka ga mutane babu masaka tsinke tun an idar da sallar asubahi sun bi layi suna jiran fitowar Mai gidan. Judge Dikko Habib babban alƙali ne wanda ake damawa da shi a manyan shari'ar da ta shafi cikin ƙasa da wajenta, kuma alƙalin da gwamnatin tarayya keji da shi. Dattijon ƙwarai mai halin dattako da nagarta, Yawancin zamansa a america yay, karatunsa ma tun daga secondry har matakin phd duka acan yayi. Matansa Biyu Hajiya Ramla da Hajiya Madina amma ainihin sunanta Aina'u, Ƴaƴansa 6, uku maza uku mata. Kuma kaf cikinsu babu wanda ke karatu a nigeria duka waje yake fitar da su. Turaki ne ma kawai yayi secondry a nigeria kamin ya fita US yay degree da masters ɗinsa acan. Idan yazo zai bawa kowa sadaqa zai bashi kuɗi dubu uku, sai ma'aikatan gidan maza su bika da kwanon shinkafa, taliya guda biyu da kwalaban farin mai da manja. Judge Dikko baya taɓa barin wajen har sai ya tabbatar da kowa ya samu, duk kuwa da uban yawan da mutanen ke da, baya gajiyawa kuma baya ƙosawa, hakana duk nisan tafiyar da yayi duk irin muhimmancinta zai katse kome yake yi ya dawo alhamis dan kawai waɗannan mutanen da Allah ya ba shi ikon taimaka musu. Ya faɗa saveral times gani yake idan har ba shine da kansa ba to ba za'a riƙe amana kamar yanda ya bayar ba, saudiya kawai yake tafiya ya iya haƙura, shima kuma sai ya kira Muhammad Turaki a duk inda yake ya dawo ya tsaya akan ragamar abun, dan shi kaɗai yake ganin zai iya kwatankwacin abinda shi zai yi da kansa. Kuma a wannan juma'ar ne ma'aikatan gidan basa samun hutu ko kaɗan, dan tun daga safe har dare suna rabon abincin sadaqa. Ƙarfe goma da rabi Baffa ya dawo cikin gidan daga rabon sadaqar daya fita, Khalil dake ƙoƙarin shiga motarsa zai fita ya hange shi, hakan yasa ya rufe motar ya taho da sauri. Ya rissina a gaban mahaifin nasa cike da girmamawa yana faɗin,"Barka da dawowa Baffa". tare da miƙa hannu don karɓar jakar hannunsa, wadda yake zuba kuɗin sadaqa ya fita da ita. Baffan ya dube shi yace,"ba fita zaka yi ba?". "fitar ba wata mai muhimmanci bace". Ya faɗa yana ƙara miƙa hannu don amsar jakar. Baffan ya miƙa masa, shi kuma yana masa sannu tare da adu'ar Allah ya bada lada a irin ayyukan alkhairan da yake yi. Tare suka jera suna tafiya, suna entrance na shiga parlo Baffa yace da Khalil. "Muhammadu ya dawo ne?". "a'a bai dawo ba". "amma ɗazu sai naga motarsa". "ai dama ba da ita ya tafi ba, da GLK ya tafi". Baffa bai ce komai ba ya shiga katafaren parlonsa bayan Khalil ya buɗe masa ƙofa. Hajiya Madina coming down from stairs take welcoming nasa. Khalil ya miƙa mata jakar hannunsa tace ya wuce ya kai bedroom ɗin Baffa. Tana gyara dining area ta ke cewa Baffa, "yau ka dawo da wuri, hala ba'a taru ba yanda aka saba". "ba haka bane, jikina nake jinsa babu daɗi". "subhanallahi". Ta faɗa a sanda tayi saurin barin abinda ta ke yi ta dawo kusa da shi ta zauna. Tana taɓa jikinsa looking worried tace,"i hope ba ciwonka ne zai tashi ba". Tai maganar tana ɓalle maɓallin gaban rigarsa. Sannan ta miƙe tana cewa,"let me reduce the AC". Kayan breakfast ta ɗauko ta dawo da shi gabansa ta aje saman wani medium glass table. His favorite dish kunun gyaɗa da awaran ƙwai, da kanta ta ke feeding nasa tana jera masa sannu, bayan ya gama ta bashi drugs sannan ta buƙaci daya tashi ya koma bedroom yace a'a ta barshi nan. Ƙasa ya sauko ya zauna kan tattausan carpet ɗin dake malale, haɗuwar parlon da tsaruwarsa kace turakar sarki, ya kishingiɗa da tum tum ɗin dake gefensa, in a state of misery yace. "ban san me ya riƙe yaron nan ba". Yay maganar yana sosa gashin gemunsa. Hajiya Madina ta sauke nunfashi kamin tace,"yace yana hanya ai...ka kwantar da hankalinka please ba wani abun damuwa ba ne. Duk yanda akai aiki ne yayi masa yawa". "to Allah yasa". Ya faɗa fuskarsa na nuni da damuwar dake ransa, na rashin dawowar Turaki gida tun a ranar daya dawo ya kirasa ya sanar masa ya dawo gida yana da buƙatar ganinsa. Suka ci gaba da magana akan rayuwa, a haka har ya fara samun relief na ciwon kan daya fara gallabansa ɗazu. yay nisa yace,"yaran nan basu tashi ba ne?". Hajiya Madina tace,"what is the time now?". Ta faɗa tana duban agogo tukunna ta ƙara cewa,"masu baccin dama Zaytuna da Nihal ne, Samha ta tashi yanzu...itama tana tunanin baka shigo ba ne thats why baka ganta ba, tunda time ɗin dawowanka bai yi ba". Yay murmushin manyace yace,"da asuba da naje gaida Boɗejo ina jinta ita da Zaytuna". Ya ƙarasa maganar yana ƴar ƙaramar dariya, yayinda Hajiya Madinan ke taya shi dan lamari indai aka ammabaci Boɗejo aciki to za'a dara. fararan haƙoransa a waje yake faɗa mata cewar,"da asubar nan fa ko lazimi bata gama ba take mitan Allah kaimu safiya ta bar gidan ita ba zata iya da gorin da akeyi mata ba". Hajiya Madina ma tai dariya sosai, lokacin kuma hankalinsu ya karkata kan yaransu dake shigowa parlon bakunansu ɗauke da sallama. Shigar jikinsu kaɗai zata shaida maka ƴaƴan wani ƙusan ne, ballanta azo ga kallon fatar jiki da zata tabbatar maka da hutu, jin daɗi da gata ya zauna. Baffa ne ke amsa sallamar tasu yana miƙewa zaune daga kishingiɗar da yay ajikin tumtum. Samha, Zaytuna da Nihal suka zube a gabansa, cike da tsantsar girmama da ladabi suka gaishe shi cikin taushin murya. ba sai an faɗa ba, irin zaman ma da sukai a gabansa shi zai baka tabbacin an gina tarbiyarsu bisa bigere na addini, duk da Judge Dikko ɗan boko ne hakan bai sa yay watsi da koyarwar addini da al'ada ta fulani ba ya ɗauki ɗabi'ar bature ya gina iyalinsa akai. Idanuwansa na bin kowacce da kallon so da ƙauna dake tsakanin uba da ɗansa yake amsa musu cikin farin ciki da annashuwa. Adu'a yake jero musu iya adu'a su kuma suna amsawa da amin, Zaytuna wadda ke da idon hawaye tuni idanuwanta suka ciko da ƙwalla, haka ma muryarta tayi rauni wajen amsa albarkar da mahaifinsu ke saka musu. Da yake shi mutum ne me barkwanci acikin iyalinsa ya kalla Nihal cike da zolaya yace,"Auta ya naga kinyi fari har kinfi Boɗejo, saura ƙiris ki koma Zabiya". Babu shiri Nihal tai dariyar da duka haƙoranta suka bayyana a waje tana rufe bakinta da hannu. Baffa ya ƙara cewa,"ki sammawa Mamanki abinda kike shafawa ko ta ƙara yin kyau ta koma ƴan mata". Yay maganar cike da barkwanci. bata bar dariya ba tace,"Baffa ni babu abinda nake shafawa tsabagen hutu ne kawai". Yay murmushi, Hajiya Madina tace,"yo Allah na tuba ni wa zai ganni ma yace na ajiye maka waɗannan yaran...ni jikina ma ai yafi na wata budurwar, man bature kuwa ai sai dai mu barwa wasu danmu da namu farin Allah ya halitto mu". acikin amon yanda tayi maganar zaka tsinci tsagoron kishi duk da cewar maganar anyita ne for raha becouse of ayi dariya. "Zaytuna naga hannun naki". Hajiya Madina tace tana duban inda Zaytuna ke zaune, gefen mahaifinta tamkar zata shige cikinsa. ta taso ta dawo kusa da ita tana nuna ma ta hannun. "ya fara sauƙi ai...da zafi har yanzu?". "ehh Maama yana zafi". "sannu, did you take your drugs?". Tace,"ehhh". "Allah ya sauƙe". Baffa yace,"to wai ba za'a nemo wata ƴar aikin bane?, kuma ke har kina shirmen me da kika bari ruwan zafi ya taɓa ki". Hajiya Madina tace,"tsautsayi dai da baya wuce ranarsa, ita kasan kamar inji ba son zama take yi ba tai aiki ba ko masu aikin suna nan...amma idan yau Jamilar bata dawo ba sai nayi magana da Yami ta samo wata, ai dama sati ɗaya Jamilar tace zata yi". Sahma tace,"ai Maama a nemi wata kawai, dan bana tunanin Jamila zata dawo, don naji Sha'awanatu na cewa kamar aurenta za'ai". "ai da hakanne zata faɗa, ko ta kira waya ta sanar". Baffa na riƙe da hannun Zaytuna yake cewa da ita,"please Babyn Baffa a daina shiga kitchen kinji, bana so wani abu ya dinga taɓa min lafiyarku". Sameer da suka shigo shi da Khalil yace,"to wai a yanke hannun mana". Zaytun tayi masa wani kallo tace,"sai kazo ka yanke ai". yace,"karki bari a barmu daga ni sai ke a gidan nan kiga aiki da cikawa". Baffa with full of smile on his face yace,"ƙyale shi haushi yake ji hannunki yafi na budurwarsa kyau, kuma nan gani nan bari...". tun bai ƙarasa ba Samha da Nihal da ita Zaytunan suka ƙarashe faɗin,"ɗumamen mayya ba". sukai maganar suna dariya. Sun ɗau tsawon lokaci suna hira kafin yaran su tashi su tafi, suna fita Baffa ya kamo hannun matarsa yana cewa,"haba ƴar shawalwalata ɓata fuskan kuma na menene?". Bai jira me zata ce ba yaci gaba,"kema dai ai kin san waɗannan idanun tsufan nawa kallon jaririya ma suke miki ba ma budurwa ba, me za'ai da wata ƴan mata ina dake ƴar shila, kin fa riga kin rufe ƙofar tuntuni, to mene kuma wani batu zai sa ki ɓata fuska ummm Babyn Baby, please saki ran karki ɓatan kwalliyan da akayi mani nake kallo ina jin daɗi". ya ƙarasa maganar yana shafo fuskarta ita kuma tana ƙoƙarin danne murmushin jin daɗin dake neman suɓuce mata, yanda yake yi mata kamar ƙaramar wata yarinya, har sai da yayi nasarar sakata yin murmushin daya haɗe da dariya. "yauwa ko ke fa gimbiyata, sarauniya a fadar zuciyata, ina sonki fa, ina sonki da yawa wallahi...kai Allah dai ya ƙara miki kyau". Ya faɗa yana kamo dogon hancinta. sai kuma ya kai bakinsa saitin kunnenta yana cewa,"wai yaushe zamu ƙara tafiya honey moon ne?". Hajiya Madina tace,"da gaske fa nai zaton ko ka ƙyalla ka gano wata ƴar baturiyar ne". Yace,"waa nii rufani ki saya". Yana nuna idanuwansa yace,"ai wannan idanuwan babu abunda suke gani sai ke, ke ɗaya tallin tal Aina'u ta Habibullahi". "to yanzu tashi mu koma ɗaki ka samu ka rama baccin asuba da baka koma ba...nima na samu na tafi guest parlo kasan yau ranar amsar kukan mata ne". Suka miƙe tsaye tare yana faɗin,"ai nai zaton idan munje ɗakin soyayya zamu sha". tai murmushi ta kama hannunsa. "to kai dai muje mana Your Excellency". Da haka suka haura stairs. **** "ni kuwa na godewa Allah, wai ko Allah Fillo ba za ki daina wannan kukan alluran haka ba". Kaka ce ke maganar tana daga cikin ɗaki tana gyara, dan yau tun before 7 ta tafi kai Fillo asibiti, dalilin ma daya sa suka dawo da wuri saboda Amir ne ya kaisu, acan asibiti suka tarar da shi dan da wuri yaje ya kama musu layi, tun daren jiya ya kasa zaune ya kasa kwance saboda yanayin yanda ya tafi ya barta da jikinta. tun wancan ranar da Fillo ta ƙona asirin nan shikenan ta kwanta ciwo, har sati guda tana kwance jiki sai dai yay ta tsamari ba sauƙi. Sai ma yau ɗin da ta ɗanji daɗi. A yau ɗin ne Kaka ta ƙara ƙudurtar cewar Fillo bata da wani miji a wannan duniyar sai Amir, saboda samun namiji a wannan zamanin kamarsa babu shi, yau ta daɗa yabawa da hankalinsa, yana da duk wasu good qualities da ake buƙata a wurin ɗa namiji, ga uwa uba ilimin addini. ko sisinta bata kashe ba shi ya biya komai da akai bill, duk da ba kuɗi ne da shi ba, amma akwai zuciyar nema da kuma kyauta, babu yanda ba tayi ba akan ya karɓa ya ƙara amma yaƙi. dai-dai da ruwan sha wannan sai daya siya mata na Faro da suka dawo, da kayan marmarinsa iya koƙarinsa. tana lure da shi banda tayi masa da gaske a ɗazun bai so tafiya ba. Fillo dai kukanta ta ke rerawa da ƙarfin sauti ba kaɗan ba, da Kaka ta gaji da halinta tayi mata banza. Har ta gama duk abinda take Fillo dai bata daina kuka ba, kukan da bana komai ba ne sai na allurar da akayi mata. allurar da taja akaita fushi da masoyin da ake ji da shi, dan har Amir ya ƙaraci zamansa a parlon

Chapter 4 of 73