Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shi ya miƙe zai fita karaf idonsa ya sauka akan tiles inda take kwance, wajen duk ya ɓaci da jini, yay saurin rufe ido yana girgiza kansa, lokaci ɗaya amai ya taso masa babu shiri yay hanzarin ficewa, amai sosai ya yi da ya shiga toilet, bayan ya fito ya tsaya yana tunani, yana jin zuciyarsa duk babu daɗi. yay ta so ya tuna sunan abin da ya gani a ƙasa, ya dai san Nihal ma na irin haka wanda har suma take yi ita, sai kawai ya ɗauki wayarsa yay dialling lambar Zaytuna, tana ɗagawa ko sallamar bai amsa ba ya ce,"mene ma sunan wannan abun da kuke yi every month?". ta ji yay tambayar kamar a rikice, ba ta fuskance shi ba sai daga baya sannan tace,"oh menstruation". yay ɗan jim sannan ya ce,"wanne irin magani ake sha?". ta ce,"zan maka text ɗin su yanzu". yay ɗan guntun tsaki ya ce,"babu a gida?". ta ce,"akwai". ya ce,"to ki kawo yanzu, idan ana allura ma ki taho da ita". ya koma bakin gado ya zauna ya kulle idonsa yanata girgiza kansa, yana da ƙyanƙyami sosai fiye da tunani, ko Zaytuna da yake cin abincinta idan tana period ko ruwan hannunta ba ya sha, har yanzu zuciyarsa ba ta bar tashi ba, so kawai yake ya ƙara yin wani aman ko zai ji daɗi, kansa har wani ciwo yake yi. ya na nan zaune yana ta aikin jera tsaki kamar aikin farilla, wayarsa ta yi ringing, yana ɗagawa bai ko jira abin da Zaytuna zata ce masa ba ya ce,"ki sameta a ɗakinta". "Hammah ai ban san ɗakin nata ba, ban taɓa shigowa ba". a daƙile ya ce,"zan kashe fitilar ɗakina". ta ce,"tom". Sanda Zaytuna ta shiga ɗakin, samu tayi ta kyala amai yafi guda huɗu duk wuri daban daban, sai dukan tiles take yi tana ambaton innalillahi, tana faɗin azo a taimaka ma ta, ta kira sunan Kaka ta kira na Yami. Zaytuna ta ƙarasa da sauri, ta ɗauki jarkar ruwan da ke wajen ta buɗe ta tuttula a cup ta bata magani ta sha, sannan tayi ma ta allura, tsabar wahala ma bata san wa ke kanta ba, a hankali a hankali kuma taji ciwon yana ɗan sauƙi. sai lokacin da iya buɗe ido ta kalli Zaytuna ta ce,"Adda". ta amsa ma ta tana cewa,"sannu". Zaytuna ta riƙeta ta kaita toilet ta ce ta daure ko ba tayi wanka ba ta ɗauraye jikinta, haka tayi wanka a daddafe ta fito, zata kuma kwanciya a ƙasan tiles ɗin Zaytuna ta hanata, ta buɗe wadrobe ta ɗauko ma ta riga ne ɗan kauri iyaka gwiwa ta bata, sannan ta kwanta akan gado, tana kwanciya baccin wahala ya ɗauketa. Zaytuna da kanta ta gyara wajen tas, har kayan da ta cire ta wanke su a machine, ta kunna turaren wuta sannan ta kira Turaki a waya tace masa zata tafi, toh kawai yace ma ta, before ya kashe wayar tayi saurin ce masa,"kar ta sha ruwan sanyi, da abu me zaƙi, da cocumber". bai ko ce ma ta ƙala ba ya kashe wayar kawai. tafiyar Zaytuna babu jimawa ya fito a ɗakinsa ya tafi ɗakin Fillo, fitila ya kunna ya hangeta kan gado, yanayin yacca tayi kwanciyar kaɗai zai shaida maka kwanciya ce ta wahala, dan hatta yanda numfashinta ke fita ma ba ta daɗi ba ne, hasken fitilar yasa ta yin juyi tana sa hannu ta kare idonta duk cikin baccin, lura da hakan ya sa ya kashe light ɗin ɗakin ya kunna ta wayarsa, ya mayar da ƙofa ya rufe sannan ya ƙarasa ciki, a bakin gadon ya zauna ya kai hannu ya taɓa wuyanta da kanta yaji still jikinta da zafi. wayarsa ya ɗauko ya kira Zaytuna, ta ɗaga tana sallama da alama ma ta fara bacci, yace da ita,"zazzaɓin bai sauka ba fa". ta ce,"da ma akwai zazzaɓi ne Hammah?". bai amsa ma ta ba kawai yaja tsaki ya kashe wayar, ya haska torch ɗin wayarsa ya ɗauko ledar maganin ɗazu yaga bata sha ba, ya zazzage ledar ya ɓallo adadin yacca zata sha, ya zuba ruwa a cup sannan ya ɗago Fillo zuwa jikinsa, ba tare da yay magana ba ko ya tasheta ya kafa cup ɗin a bakinta ya zuba ruwa sannan ya tusa ma ta drugs ɗin duka, ya ƙara zuba ruwa tare da toshe hancinta, take drugs da ruwan suka wuce maƙogoronta. tsabagen baccin na cin sosai buɗe ido kawai tayi ta mayar ta rufe tana gyara kanta a ƙirjinsa, ajiye cup ɗin ruwan yay tare da mayar da ita ya kwantar, yasa hannunsa ciki nata mara ciwon ya haɗe da nasa, yay ta kallonta wucewar wasu ɗaƙiƙu tukunna ya buɗe blanket ya rufeta, yana me kamo ɗayan hannun dake da ciwo, ya kalli ciwon ya kalli fuskarta, ya tuna jiya haɗe da yin ɗan guntun tsakin da shi ɗaya ya san dalilin yinsa. ya ƙara ɗaukar waya ya kira Zaytuna, sai da ya kira sau uku sannan ta ɗaga, lokacin bacci yaci ƙarfinta sosai, dan kamar zata yi kuka ta ambaci sunansa. ya ce,"wannan ciwon na ta when suka ce za'a kunce?". ta ce,"Hammah ai ba da ni aka je hospital ɗin ba". sai ya hauta da faɗa yana cewa,"kuma ke ba ki san yanda za'ai masa ba za ki ce wani ba da ke aka je ba. mene amfanin karatun da kika yi?, ko haka kike yiwa patients ɗin da su ke asibiti?". faɗan ya fara hawan ma ta kai ta tari numfashinsa,"a bar shi ya ƙara kwana biyu tukunna". yaja tsaki yace,"ki fita ki bawa me gadi first aid". yana faɗa ya kashe waya ba tare da yace komai ba, ya fita da ga ɗakin cikin sauri, zuwansa gidan yay daidai ya isowar Zaytuna bakin gate ɗin sai tangaɗin bacci take yi. kusan fizgar firstaid ɗin yay daga hannun na ta ya juya ya tafi bai ko tanka mata ba, abun da bata taɓa yi masa ba kawai ta harari bayansa ta koma sai masifa takeyi. yana komawa ya tarar Fillo har ta tashi ta shiga toilet, zama yay bakin gadon yana jiran fitowarta, can sai ga ta ta fito tana jan ƙafa ɗaya, ya bita da kallo ta ƙasan ido, ita kuma ganinsa sai tai saurin juyawa zata koma toilet ɗin saboda rigar da ke jikinta, ƙafafunta tun daga gwiwa duk a waje, ga shi babu brazier a jikinta kuma ana hango shatin breast ɗinta. muryarsa a sama yace,"wallahi kika koma sai naji miki ciwon da yafi na jiya". cak ta tsaya ta manne a jikin bangon tana sakin kuka, ya taso ransa a ɓace ya figeta suka wuce, yana kallonta fuska ɗaure ya ce,"ban hannunki". za ta tsaya gardama ya bige hannunta daga kan fuskarta da take goge hawaye, ya kamo me ciwon ya shiga warware bandage ɗin, ya jawo stool ya zauna ya shiga ƙara dressing ciwon. tana kallonsa murya gwanin ban tausayi ta ce,"don Allah ka kira min Ummi". shiru kamar bai ji me ta ce ba, ta ƙara maimaita masa ya ce,"kin gyaro wayar ne?". tana kallon saman kansa da ke duƙe tace,"wacca wayar?". ya ce,"wadda kika fasa". a shagwaɓe ta ce,"to ai bana sa ne". ya ce,"to sai ki jira sai randa kika gyara". kukan da ya tsaya ma ta ya dawo, ta dinga roƙonsa akan ya kira ma ta Ummi ko Kaka, bai ko bi ta kanta ba yana gama naɗa bandage ɗin ya ɗauki first aid ɗin yay ficewarsa. around biyu na dare Fillo ta kasa bacci saboda tsoro, duk yanda ta so ta dake tai bacci ta kasa, sai tayi ta jin kamar ana motsi a ɗakin, a imagination ɗinta ma kamar kukan wani abun take ji, ta buɗe ido a hankali ta diro akan gadon tana tafiya saɗaf saɗaf sai adu'a takeyi ta fita daga ɗakin, da gudu kuwa ta kwasa ta ƙarasa ɗakin Turaki, tana shiga ta tura ƙofa ta jingina da ƙofa tana sauke a jiyar zuciya. motsinta ya sa Turaki buɗe ido ya ƙaro hasken bedside lamp, ta kusa ba shi tsoro ganin gashin kanta duk a barbaje, takaici ya cika shi ya buga mata tsawa lokaci ɗaya kamar wadda aka ɗauko sai gata a bakin gadon tana kyarmar jiki. "don Allah ka yi haƙuri, wallah tsoro nake ji ɗakin sai kuka ake yi a cikinsa". ta faɗa a cikin muryar kuka me tattare da rauni, har ya ƙara haɗe rai zai korata sai kuma ya tuna matsalar da ke tare da ita ta aljanu, saboda haka ya fasa ya kamo hannunta ya zaunar da ita a bakin gadon kusa da shi. calmly ya ce,"idan ba ki daina kukan ba sai na kore ki". ɗiff tayi shiru tana ƙanƙame jikinta. tausayinta ya kama shi sosai, ya sauko yace ta haye kan gadon, ta kalle shi zata yi magana sai ta fasa ganin irin kallon da yake watsa ma ta, tai saurin hayewa ta ƙudundune a tsakiya, yace,"matsa can". ta matsa inda ya nuna ma ta, sannan shi ma ya hau ya kwanta bayan ya kunna karatun alƙur'ani. yana kwanciya yaji ta kamo hannunsa ta riƙe, ya ce,"what?". ta ce,"don Allah ka barni a haka". "to yi bacci kar in ƙara jin motsinki". ta ce,"to". har tsawon wani lokaci yaji alamun dai ta kasa baccin, kawai tayi shiru ne kamar tana baccin, zai zare hannunsa a nata tayi mugun firgita ta ƙwalla ƙara tana yowa kansa gaba ɗaya. yay saurin tattarota jikinsa ya kewayeta da duka hannunsa yana cewa,"shhhh ba ihu ba adu'a za kiyi kinji". ya ƙara maimaitawa,"kin ji". ta fizgi numfashi ta ce,"wani abu ne yake bin jikina yana kuka". ya ɗora hannunsa a gashin kanta yace,"ta ina kike jinsa?". a hankali ta ce,"a ƙafata". ya miƙa hannu ya daɗa ƙaro hasken lamp, ya ɗaga blanket ɗin yana bin ƙafarta da kallo, yau da yaga duka ƙafarta a zahiri sai yaji ya tsorata da irin sirantarta, ya sauke numfashi yana tunanin anya ba sai ya kaita anyi ma ta general check up ba kuwa?, shi idan ma ana ƙara nama a jikin mutum tsab zai kashe ko nawa ne a saka mata, sirantar tayi yawa sosai. ya sunyo da kansa yana kallon fuskartata, ta rumtse idanuwanta gam kamar ko ance ta buɗe ba zata buɗe ba. a hankali in a cool voice ya ce,"za ki ci abinci?". ta ce,"a'a". ya hurar da iska a bakinsa ya ce,"cikin ya daina ciwon?". ta ɗaga masa kawai. ya ƙara cewa,"me kike so yanzu?". ta ce,"babu komai". "har yanzu kina jin motsin abun?". ta girgiza ma sa kai kawai tana ƙara ƙanƙame shi. a kunnenta ya ce,"ki yita ayatul kursiyyu". ta ce,"ina yi". "to yi bacci". ta knodding kanta kawai. ya girgiza kansa yana jin tsananin tausayinta, a hankali yaji ta sauke numfashi hakan ya shaida masa tayi bacci, sai ya kwantar da ita kusa da shi sosai, duk yanda ya so ya zare hannunsa daga riƙon da tayi masa ya rasa yanda zai yi, saboda ba ya so yay ƙwaƙwƙwaran motsin da zata farka. kuma baccin da bai iya yi ba kenan, yay tayi ma ta karatu a cikin kunneta, har aka kira sallar asuba, sai lokacin ya zareta daga jikinsa ya rufeta gaba ɗaya ya shiga toilet yay alwala, sai da ya yi raka'atanul fajr sannan ya wuce masallaci bayan yasa key ya rufeta a ɗakin. *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _Kar mu manta da karanta suratul kahf tare da yawaita salatin manzon Allah(SAW), a cikin wannan rana me albarka ta juma'a🙏🏽. Allah ya sadamu da alkhairan da ke cikinta._ *50* sai ƙarfe goma sha ɗaya Turaki ya farka da ga baccin bayan asuba da ya kwanta, lokacin da ya tashi bai ga Fullo a ɗakin ba, bai yi mamaki ba ya san da ma tsoro ya kawota, ba don haka ba ya san ba zata taɓa zuwa ba. yana kunna wayarsa ya ci karo da messege ɗin Sectery na sa, da yake tuna masa appointment din da yake da shi da wani company na lemu by 3pm. saukowa yayi akan gadon ya shiga toilet yayi wanka, bayan ya fito ya shirya cikin shigar manyan kaya na kufta black colour da tayi masa masifar kyau. yana cikin fesa turare yaji cikinsa yayi ƙugi sosai alamar yunwa, dan daren jiya ma bai ci komai ba, yay gajeran tsaki na ƙorafi da takaici, ga shi da aure amma bai da matar da zata dafa masa abincin da zai ci, shin wai sai yaushe zai san yayi aure ne?, when zai fara jin wannan daɗin da ake cewa akwai shi a gidan aure?, wannan farin cikin sai yaushe?, ga shi ta bakin Bello da gaske rainon Fillo zai yi, rainon da baya jin cewar zai iya, ya ƙara yin tsaki yana dire perfume da ke hannunsa, yanzu ba abin yaje gida ba da sunan zai ci abinci a fara yi masa tambayar ƙwaƙwaf. jakar laptop ɗin sa ya ɗauka ya fita a room ɗin, daidai bakin ƙofar room ɗin Fillo ya tsaya, ƙofar a buɗe take, ya tsaya yana tunanin ya shiga ko kar ya shiga, a ƙarshe zuciyarsa ta yanke masa yay tafiyarsa kawai, tun da har ta iya barin ɗakin nasa taji sauƙi kenan. yana saukowa parlo ƴan aiki suka fito da sauri da ga kitchen, suka durƙusa suka gaida shi, hannu ya ɗaga musu ba tare da ya amsa da fatar baki ba, har ya kai bakin ƙofa idonsa ya sauka akan dining, flask ne guda biyu a ajiye sai na tea flask, ya kalli Sakina da ba ta koma kitchen ɗin ba ya ce,"ta sakko ne?". kanta a ƙasa ta ce,"a'a ranka ya daɗe bata sakko ba kwatakwata". yay ɗan jimm sai kuma ya ce,"ita tace kuke yin girki?". ta ce,"a'a ranka ya daɗe, mun ga dai hakan na cikin aikin mu ne". ƙaramin tsaki kawai ya yi ya zuge glass ya fi ce, Sakina ta bi shi da kallo tana riƙe haɓa da jinjina kai. Hannatu na ganinta ta ce,"lafiya?, me kika guntso?". "uhmm ke wannan me gidan bai da sauƙi ko kaɗan, babu ma alamar mutunci a tare da shi, ni da ma tun ranar farko naji bai yi min ba sam, gaskiya matarsa na haƙuri da shi, irin mazan nan masu shegen girman kai da izza, fuska gaba ɗaya babu annuri". Hannatu ta ce,"wani abu kika gani hala". tayi maganar da irin suffa ta ƙwanƙwararrun munafukai. "ke kin ji yacca yake tambayar wa ya saka mu yin girki, kamar fa zai kawo min duka, babu wani irin taushi girmamawa ta ɗan adam acikin muryarsa". sai kuma ta taɓe baki,"ni da ma na faɗa miki tun ranar da muka zo na san ba zaman lafiya ake a gidan nan ba, ba ki ga ita kanta kamar ba ta da miji ba, sai dai ta sauko tayi kallo taci abinci ita ɗaya ta koma, tabɗijam ni kuwa dai duk kuɗin namiji wallahi ba zan yarda da rashin mutuncinsa ba, ke ni ba zan ma yarda da wani auren dole ba, ba zan iya namiji ya takani ba gaskiya". "ke ma dai Sakina ai da ma da gani ba auren soyayya akai ba, ni itace ma ta ke bani tausayi tun da naji ance tayi aiki a gidansu, wataƙila ƙarfi aka nuna musu aka aura ma ta shi dan anga ba su da hali, ni tausayi ma take bani kina kallonta kin san bata jin daɗin zaman, ko da yake babu komai zamu ɗaurata a hanya, naga ba ta da girman kai za ta sake da mu, zamu ba ta shawarwarin da zata saita mishi zama". Sakina ta nufi cooker gas tana faɗin,"ke yanzu dai buɗe firinjin nan ki ɗauko mana kazar nan da naji ta ɗan fara yami, mu gyara muci abarmu in ba haka ba a banza za'a barta ta lalace, naga matar gidan ba wani wayewa tayi da cin kayan daɗi ba, duk gata nan a ƙanjame ai. Allah na tuba ni ina da wannan uban kayan daɗin ma me zai sa in damu da takaicin ɗa namiji, ai ɗaukarka zanyi in bawa banza ajiyarka, kai ita ma dai wallahi anyi lusara, ko da yake wasu sun ɗaukaki soyayyar namiji fiye da jin daɗi, kuma kin san Allah duk yanda akayi ganinta ƙashi da rai yasa yake ma ta wulaƙanci, babu gaba babu baya kyace me cutar S, kai Allah dai mun gode maka, kuma banza da ita ma kawai ta jefa shi a kwandon shawara ta bawa jikinta ingantattun kayan da zasu farfaɗo da ita, ba dai gidan jin daɗi da hutu ta zo ba, wallah wata guda yay ma ta yawa ta murmure". Hannatu tai ƴar dariya tana fito da gasashshiyar kaza a freezer,"Sakina ko dai ko dai, kawai...". bata ƙarasa ba Sakina ta juyo tana yi ma ta wani kallo,"ko me?, ni da wannan miskilin mijin?, ba dariya ba murmushi babu fara'a?, azaba!, Allah ya kiyaye wallahi, ai ranar farko zan bakawa gidan nan wuta dan ba zan iya da mugun halinsa ba, dukanta fa yake yi". Hannatu ta riƙe baki,"kai don manzon Allah?". "mtswww ke sai shegiyar gulma ba kya sa ido a abu, jiya baki ganta tana kuka ba?, to da daddare ma lokacin da ya shigo na hau saman ina jinsa a ɗakinta yana zazzaga ma ta masifa ita kuma sai kuka takeyi, ke Allah yasa ma ba sakinta yay ba dan naga yau gaba ɗaya fa ba ta sakko ba". Hannatu tayi dariya,"wallahi yana sakinta zan shiga da ga ciki, wa ye zai so rabuwa da wannan gidan da aka aje daula, aljannar duniya, ita ma ɗin dai shashasha ce kawai, ni fa yana burge ni sosai saboda yana da kyau kamar ka sace shi ka gudu, kuma da yardar Allah sai ya zama rabona". ta faɗa tana jujjuyawa,"kalle ni fa da kyau, kissar ƴan aiki zanyi kawai a wuce wurin". buɗar bakin Sakina za ta yi magana suka ji sallama a parlo, da sauri suka fita a tare, ganin Yami yasa suka ƙarasa da sauri su na yi ma ta sannu da zuwa, Yami na yi musu fara'a ta amsa musu, ta zauna akan kujera tana tambayarsu ya aiki. "ina matar gidan fa?". Yami ta tambaye su. Sakina ta yi saurin cewa,"bari a hau a kirawota yau ba ta sakko ba gaba ɗaya, ƙila ba ta tashi ba". Maijidda ta cire hijab ɗinta ta ajiye tana cewa,"ƙyale ta bari na hau na sakko da ita". ta faɗa tana nufar upstairs, kuma duk da haka Sakina sai da ta bi ta saboda taje ta yo munafurci. “Aa lafiya dai?” Maijidda ta tambaya lokacin da take ɗora ƙafafunta akan steps. Sakina ta ɗan sosa gefen fuskarta ta ce,“Aa da ma wai...”. dakatar da ita Maijidda ta yi kana ta ce,“Aa Kika ce bata sakko ba ko, na ce miki to zan je na gani ko lafiya, ina ga ai babu kuma buƙatar sai kin biyo baya na ko kuwa?. Kije kiyi aikin gaban ki”. Haka kawai ta tsinci kanta da fad’a mata wad’annan maganganun ba tare da sanin dalili ba. but still sai da Sakina ta bi ta ɗin bayan ta haye, kuma tana hawa ɗakin Turaki ta buɗe a hankali ta shiga, tai tsaye daga bakin ƙofa tana yi masa kallon tsab, ganin kan gadon ba'a gyare ba yasa ta riƙe baki tana jijjiga kai, ko me ta saƙa a ranta oho, da sauri kuma ta fito tana barin wajen ta nu fi ɗakin Fillo. Maijidda kuwa tana isa ta ga ƙofar d’akin Fillo a bud’e, bata yi mamaki ba sanin cewar Turakin baya nan, kai tsaye ta saka kanta ciki d’auke da sallama. Bata ji alamun za'a amsa ma ta ba don haka kawai ta kutsa kanta ciki, a karo na biyu ta ƙara yin sallama saboda son ta samu izini kamar yadda Manzon Allah (SAW) yay mana umarni da mu yi. Sai da tayi sallama uku babu amsa hakan ya sa ta ƙarasa ciki tana kuma ƙara yin sallama, rufe bakinta ke da wuya sai ta jiyo kamar shesshek’ar kuka, hakan ya bata damar yin sauri ta isa bakin gadon tana fad’in,“hasbunallah wa ni’imal wakil, na shiga uku ni Hauwa, Ke! Meye ka faruwa meye damuwan?, Wani ya mutu bani da labari ne?.”. kawai sai itama ta fashe da kukan, da ma itama gwanar hawaye kamar Fillon, ganin hakan Kuwa ya ba ma Fillo damar ‘kara fashewa da wani matsanancin kuka cike da shagwab’a da iya shege gami da zallar wawta. Sakina dai na laɓe bakin ƙofa ta kasa kai da kunne, ta rufe baki tana fito da idanu waje. Maijidda tayi saurin kai hannu ta janyo Fillo jikinta, da tsantsar kulawa da damuwa irin ta ƴan'uwantaka take fad’in,“wai don Allah me aka yi maki?, don Allah ki sanar da ni meye wai ni don Allah?”. Da k’yar Fullo ta bud’e baki ta fara magana, leb’en sama da na k’asa su na had’uwa su na faman luguden kuka,“wai wai ni fisabilillah haka kawai..”. Maijidda ta zabura tana k’ara fad’in, “wai Ke me?, don Allah ki min bayani inji?, kin san kuwa duk yanda gabana ke faɗuwa?". “to wai ba Turaki ba ne haka kawai shi kullum ya gagara ya fahimce ni sam, sai yay ta faman ji da kansa, kullum sai yay ta ƙin kula ni yana share ni, ko kallona ma ba yayi, sai dai fa yay ta hararata, kuma idan nayi magana sai yay ta min tsawa yana ɗaga hannu zai mareni, ni sai yay ta min abu kamar ba mijina ba, da ma sai da na faɗa muku ba ya so na, ni kawai gida zan koma, ki kira min Ummi a waya please". kukanta ya ƙaru a san da take ƙarasa maganar. damuwa ta bayyana fal a fuskar Maijidda, cikin sanyin jiki da murya ta ce da ita,"kuma kina yi masa biyayya?, kina sauke duk hakkinsa da ke kanki?, kuma ba laifi kika yi masa ba?". tasa hannu tana goge hawayenta ta ce,"ai ni bana kula shi ma". Maijidda ta ware ido,"ba kya me?, kwatakwata ba kya kula shi kike nu fi ko kuwa da ku ka yi faɗan ne?, ni ban gane rashin kulawar ba". "ni kawai ba na kula shi ai baya so na?". Maijidda ta raɗa ma ta abu a kunne, Fillo ta ɗago daga jikinta tana faman ɓata rai,"ni nace miki komai ma bana kula shi, sai jiya ma na fara ganinsa a gidan, ni dan Allah ki kira min Ummi a waya azo a tafi da ni". "Allah me girma da ɗaukaka, yau ina ganin iya shege, da ma Fillo har haka kika kai ba kiyi hankali ba?, mijin naki za ki ce sai jiya kika gansa bayan sati guda da aure?, kuna cikin gida ɗayan?, to wa kika barwa shi?, ɗaya matar tasa ko kuma ƴan aikin?". kuka ya ƙara zuwar ma ta,"to ai shi ne baya zuwa inda nake, kuma da yazo sai ya fara min tsawa alhalin ya san bana so". Maijidda ta ce,"tabɗijam, to wallah sai yau na tabbatar da ke ɗin nan dai ba ki da wayo sam, a iya ɗauke asiri kawai kika fi wayo. yarinya Allah ya tausaya miki ya ba ki miji kamar Turaki, mijin kece raini, mijin wuce sa'a, amma ki gantalar da shi da lamarinsa saboda shegen taurin kai da miskilanci irin naki. to ai ni dai a iya nasiha da faɗan da naji an miki ba'a ce sai ya zo inda kike tukunna za ki saurare shi ba, kuma ba'a ce lallai sai ya zo inda kike ba sannan kema za ki je inda yake, yo to da ma wanne miji ne zai kula matarsa alhalin ita ba ta kula shi?, da kike batun ma ba ya sonki, ai ko jikina duka kunnuwa ba zan yarda da wannan zancen ba, dan idan ba ya sonki babu abin da zai sa ya aureki, don billahi irin waɗannan mazan masu aji da ilimi ya ratsasu ta ko'ina ba sa auren macen da basa so, haba Fillo ki yiwa bawan Allahn nan adalci mana, wannan mutumin dai zuciyarsa babu mugun nufi ballantana kice saboda ya wulaƙantaki ya aureki, kuma da ma akan mene ba zai ke shareki ba, shariya ma ai dole dan wallah me iyawa da halinki sai me kai zuciya nesa, in wani ɗan wiwin ma kika aura Allah da tuni kin sha kutufo, to da yake ma kin samu wuri ne shiyasa kike abin da kika ga da ma. kuma idan gidan za ki tafi da gaske ai haɗa kaya za kiyi kibi hanya ba sai kin kira waya anzo an tafi da ke ba". sai kuma ta kwantar da murya ta shiga ba wa Fillo shawarwari masu kyau a matsayinta na aminiya kuma ƴar'uwa, tare da ƴan nasihohi wanda ta san idan har ta ɗauka tayi amfani da su ba zata yi danasani

Chapter 56 of 73