Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da yake jin su har cikin ransa tamkar ana hura huta a zuciyarsa. ya kamo hannunta ya riƙe cikin nasa, sai taji ta kasa ƙwacewa, kawai ta kifa kai akan gwiyarta, tayi kewarsa har bata san iyaka adadinta ba. Cikin kwantar da murya ya soma magana yana faɗin,"na san ban kyauta miki ba akan canjawar da nayi miki, tsawon kwanaki tara kenan ina ƙuntata miki, ba zan hana ki jin haushina ba, amma ki yi haƙuri don Allah, ni ma nawa ranne babbu daɗi, tilasta min da aka yi akan mayar da auren nan duk shi ya dagula min lissafi ". tsabar tuƙuƙi da ɗacin dake tasowa a ƙarƙashin zuciyarta, tun da ya fara magana har ya kai ƙarshe bata ko kulasa ba, haka bata ɗago kai ta kalle shi ba, sai ma zame hannunta da tayi a nasa. Turaki ya gyara zamansa, ya matsa kusa da ita ta yadda numfashinsu yake gauraya da na juna, ya riƙo hannayenta duka acikin nasa yana murza lallausan tafin hannun nata, ya kifa goshinsa saman kanta yana sauke numfashi. baya jin a duniya akwai wata mace da zata kama zuciyarsa kamar ƙaramar yarinyar nan, kullum cikin adu'a yake yi Allah kar yasa sai ya rigata mutuwa. cikin hikima da iya tsara zance na miji ya shiga bata baki, yayi amfani da duk wasu kalamai da za su kwantar mata da hankali da shigar da nutsuwa cikin zuciyarta, har sai da yaga alamar hucewa a saman fuskarta. but hakan duk bai sa Fillo ta samu sauƙin zafin kishin da take ji ba, abu ɗaya kawai ta sani mijinta yana mata tsananin so, kuma yana sonta fiye da ɗayar matarsa. da kansa ya sauƙa ƙasa ya dafo mata indomie, ya zo ya sakata a gaba taci da ƙyar saboda lallamar da yake yi mata. tamkar ɗacin magani haka ta dinƙa cin indomie ɗin, but babu yanda ta iya sosai take buƙatar abinci, dan zata iya cewa rabonta da wani abu a ciki tun kunun gyaɗar da ta sha a gidan Yusuf. sai da ta kwanta sannan Turaki ya bar ɗakin, tana jin fitarsa ta ƙara fashewa da kuka, ba wai don tana so ba sai dan bata ma san lokacin da yake zuwar mata ba ɗin. washe gari da sassafe kuwa sai ga text ɗinsa akan ta shirya ta tafi gidan na su. tsabar farin ciki da jin daɗi bata san lokacin data tura masa da reply ɗin thank you ba. lokacin da ta fito zata tafi yana hangota ta balcony, fuskarta ta gaza ɓoye jin daɗin da take ji, yay murmushi kawai tare da juyawa ya koma ciki domin ya sanarwa da Ilham ita ma ta shirya ta tafi, tun da kusan yaune yinin bikin gidan. da rana taro yay taro, cikin taron mutanen da ake ta ɗaukar hoto Fillo ta yanke jiki ta faɗi. cikin tsananin tashin hankali Hajiya Madina da Hajiya Ramla suka sureta aka yi asibiti. zuwan su babu jimawa sai ga Turaki shi ma ya ƙaraso, cikin matsananciyar damuwar da ta kasa ɓoye kanta ba. ya zauna kusa da Maama, ta dafa kafaɗarsa tace,"ka kwantar da hankalinka insha'Allahu ba wata matsala ba ce babba". Mum ta kalle shi rai a ɓace tace,"na jima da fahimtar kana ƙuntatawa yarinyar nan. to wallahi kaji na rantse maka muddin silar ɓacin ranka take kwance anan sai ranka yayi mugun ɓaci". wucewar mintuna ashirin su na zaune jungum jugum sai ga likita nan ya fito, ya buƙaci cewar wani acikin su ya biyo shi. Hajiya Madina tace da Turaki ya tashi yaje, ya shiga office ɗin Dr jikinsa a matuƙar sanyaye, duba da yayin da yake gani akan fuskar likitan. "Bismillah zauna". ya faɗa yana yi masa nuni da kan kujera. Dr ya ɗauko file ya buɗe, ya dubi Turaki ta cikin glass ɗinsa sannan ya ce,"Halima Borkinɗo right". Turaki yay saurin jijjiga masa kai,"yes". Dr ya sauke numfashi, ya furzar da iska daga bakinsa sannan ya ce,"kun san cewa ta kamu da heart failure?". "mun sa ni Dr". "to amma ya akayi ku ka yi sakacin da har damuwa tayi mata yawa haka?, tana fa ƙoƙarin barin matakin farko da take ciki ne ta shiga na gaba". Turaki ya sauke doguwar ajiyar zuciya bai iya cewa komai ba. haushin kansa yayi matuƙar kama shi. "anyway ga wannan drugs ayi gaggawar siya mata, gudun samun matsala babba. and a kiyaye sosai da duk abin da zai haifar mata da damuwa kar a kai stage ɗin da Babynta zai cutu". idanuwan Turaki suka ƙanƙance yace,"Baby?". ya tambaya da mamaki sosai. Dr ya jinjina masa kai,"ƙwarai Baby, ko ba ku san tana da ciki ba ne?". bakin Turaki ya buɗe, duka haƙoransa suka yo waje,"i din't get you clearly Dr, wanne irin ciki wai?". Dr ya faɗaɗa murmushin sa, yana kallon Turaki yace,"zauna da kyau kar ka faɗi". sai ya ɗebo sauran takardun da ke cikin file ɗinsa ya zubewa Turaki a gabansa ya ce,"ashe kamata yayi in fara yi maka congratulations, so you are expecting a baby in the next five months Insha'Allah, a test ɗin da aka yi mata ya nuna mana cikinta yana cikin wata na huɗu ne, but how comes duk baku yi noticing ba?" Turaki ya kasa amsa tambayar Dr, sai ɗaga hannu sama da yay yana godewa ubangiji. ya daɗe a hakan kafin ya mayar da hankalinsa kan doctor ɗin yace,"thank you very much, ga wannan kasa mai a mota". ya ajiye masa kuɗi saman table ɗinsa, hakan kuma yayi wa Dr daɗi sosai, nan da nan ya shiga bawa Turaki shawarwari akan yacca za su kula da cikin. Turaki duk ya ƙosa ya miƙe akan kujerar, hannu ya miƙawa Dr ɗin su kai shaking, tukunna ya fita a office ɗin bakinsa sam yaƙi rufuwa saboda tsabar farin ciki. kai tsaye room ɗin da Fillo ke kwance ya wuce, a ciki ya sami Maama da Mum, lokacin ta farka tana zaune, sun sakata da tambayar me take son ci, ita kuma duk ta narke tana faɗawa Mum wai Mangoro take so me warin gawasa. kallo ɗaya Mum ta yiwa Turaki ta zunguri Maama suka fita suka bar ɗakin, su na fita ya rungume Fillo da farin cikin da ba zai iya misaltuwa ba. ta ture shi daga jikinta tana turo baki gaba tare da ɓata fuska. "ni ka matsa daga kusa da ni". yay murmushi me sauti yana zura hannunsa cikin rigarta, cikinta ya shiga shafawa yana faɗin,"ta ya zan barki alhalin akwai ajiyata anan?. congratulations very soon za ki zama Mother". ta yi masa wani kallon mamaki, ya ɗaga mata gira duka biyu,"am serious Angel". sai ta kulle idonta tana jin wani daɗi na tsarga mata, ta kai hannayenta duka biyu ta dafa cikin tare da hannunsa da yake kai. "Allah ka azurta ni da zuri'a ɗayyiba". ta faɗa hawayen farin ciki na sakko mata, Turaki yay kissing ɗinta a goshi tare da faɗin,"amin summa amin uwar ƴaƴana, i love you so much". lokacin da suka fito su Maama har sun wuce, duk kunyar da yake ji, bai iya haƙuri ba sai da ya ɗaga waya ya kira su Maama ya sanar musu. bayan sun gama wayar ya kira Bello, yana ɗagawa yace da shi,"Bello ai na zan sami Mangoro me warin gawasa?". Bello ya ce,"yanzu na mayar da farantin tallan gida, ya ƙare tass da yake yau anyi ciniki". Turaki yay tsaki,"kai dai kana da matsala". "to MT haka kawai sai ka kama wani kirana kana tambayana in da zaka samu mangoro, hanyar kasuwa ne baka sa ni ba ko me?. ni don Allah kace a bani matata yau wallahi duk na gaji a matse nake". Turaki yaja dogon tsaki ya kashe wayar, ya kamo hannu Fillo dake dafe da ciki yace,"sorry Angel, duk in da mangoro yake zamu samo shi yanzun nan, ki tayani bawa Baby haƙuri". sai ya kuma ya fara ce mata,"yanzu idan namiji ne wanna suna zamu saka masa?". "ai kai kake da wannan alhakin". "to in dai namiji ne sunan Abba zamu saka, idan kuma macece zamu sa sunan Maama, in kuma twins ne duka maza zamu sa sunan Abba da Baffa, idan twins ne duka mata sai mu sa Maama da Ummi". "Mum kuma fa?". "ita ma zamu saka nata idan kin ƙara haifar wasu twins ɗin". "wai haka Doctor ɗin yace maka twins ne?". "hakan nake fata Angel". sai ta marairaice fuska, idonta ya ciko da ruwan hawaye, ta damƙe hannunsa ta ce,"Jannaty ina tsoron haihuwa, an ce akwai wahala". tausayinta ya kama shi,"kar ki damu Angel insha'Allah ke kalar taki haihuwar zata banbanta da ta su, cikin sauƙi zata zo miki". "Allah yasa. amma Jannaty ka dinƙa yi min adu'a kullum na haihu da raina da lafiyata, ina so na raini yarana da kaina domin in ba su ilimi ingatacce tare da ba su kyakykyawar tarbiyya, ba na so na mutu a lokacin dana san ƴaƴana za su buƙace ni". sai kawai ya gangara motar gefe yay parking, yacca jikinta yay sanyi haka ma nasa, ya juyo ya kalleta yaga tana zubar da hawaye, ya janyota ya rungumeta. ta fashe da kuka sosai tana faɗin,"Jannaty bana so su tashi acikin maraicina, ina so su ma suji wannan daɗin na uwa". lokaci ɗaya Turaki yaji idonsa ya ciko da ruwan hawaye, yana shafa bayanta yace,"mene kuma na zancen mutuwa Angel?, don Allah ki daina, da izinin ubangiji da ranki da lafiyarki za ki haihu, kuma insha'Allahu ubangiji zai ba ki aron tsawon ran da har auran ƴaƴanki za ki gani". ita dai bata iya cewa komai ba, kuma har suka ƙarasa gida jikinsu duk yay sanyi. Fillo kuwa tana shiga bedroom ɗin Mum ta rufe fuskar ta, saboda haɗa ido da su da tayi, don samun su tayi zaune su ma duk cikin farin ciki, kuma ganinta kowa ya shiga mata adu'ar Allah ya raba lafiya. Zaytuna da Samha sai tsokanarta suke yi wai ta zama uwar biyu. tun daga wannan ranar kuma Fillo sai ta koma rayuwar gidan su Turaki, don ƙememe Maama taƙi barinta ta koma can gidanta tace sai cikin yayi ƙwari, duk ranar kwananta nan Turaki yake zuwa sai su tare a ɗakinsa na gidan. sosai Fillo ke jin daɗin yanda Mum da Maama ke tarairayarta, musamman a wajen Hajiya Madina, don rainon cikin take yi cikin kulawa ta musamman daga wurin Kakarsa Hajiya Madina. macen da kullum cikin siyan kayan jarirai take yi, hatta gadon Baby tana zuwa saudiyya ta taho da shi, motsin Fillo kaɗan ta tambayeta me take so. Rayuwa ta cigaba da tafiya, a yayinda wasu abubuwan rayuwar kan sauya, lokaci yana tafiya a kullum kuma a ko da yaushe. wani lokacin cikin farin ciki wani lokacin baƙin ciki. A duk lokacin da agogo zai motsa, lokaci ne yake wucewa, lakacin da baza a sake maimaita irinsa ba, lokacin da ba zai taɓa dawowa ba. Sau da yawa ɗan Adam ya kan ƙagauta akan lokaci ya zo masa, musamman idan ya ƙosa akan cin burin wani abu da ya saka a ransa, sai ya gaza fahimtar irin saurin da lokacin yake yi, har sanda zai ankare da zuwan wannan abin da ya saka a ransa, anan ne zai ga tamkar ansa igiya ne ana janyo wannan lokacin. hakan take a ɓangaren Fillo, tun daga ranar da likita ya ƙayyade musu watanni biyar a matsayin watannin da zata ɗiba kafin ta haife abinda ke cikinta, daga wannan ranar ta ƙosa da zuwan lokacin, zuwan ranar, sai ta koma ko da yaushe cikin kallon kaɗawar agogo take, cikin lissafa kwanakin kalanda, cikin haddar kwanakin da muke shiga muna maimaita su, cikin lissafi da hasashen irin soyayya, kulawa, ilimi tare tarbiyar da zata bawa abin da ta haifa. sau tari mu kan yiwa kanmu lissafin tanadin abubuwa, sai dai abubuwa sukan zan zo mana ne a yacca ubangiji ya tsara mana ba yacca muka tsarawa kanmu ba. wani lokacin ɗan Adam kan iya ƙirga sautin fitar numfashinsa, ba tare da ya san lokacin da numfashin nasa zai daina fita ba, fitar da ba zai ƙara samun damar ƙirga shi ba. buri wani abu ne da kowanne ɗan Adam ke cin sa, sai dai ba duka burin ɗan Adam ne ke cika ba, kuma sau tari cin buri na katsewa ɗan Adam ne a lokacin da numfashinsa ya daina fita. Rayuwa babbar nasiha ce ga kowanne ɗan Adam, akan ya gane cewa ba komai ba ne yake da tabbas ba a rayuwa, idan aka cire lokaci, lokaci ne kawai yake da tabbas, sai dai ɗan Adam ba shi da tabbas ɗin zai kai kowanne lokaci na bugawar agogo, ko tabbas ɗin lokacin da yake ta lissafawa rayuwarsa. ubangiji ya riga ya ƙayyadewa kowanne bawa iyakacin lokacin da zai ɗiba a duniya, numfashin wani zai daina fita ne a bugawar sakan, yayin da numfashin wani zai daina fita ne a bugawar minti, kowanne bawa na tafiya ne kawai akan lokacin rayuwarsa. a rayuwa ba ko da yaushe ne ɗan Adam yake yin murmushi ko dariya ba, ba kowa ne yake samun damar rayuwa tare da wanda yake ba, ba kowa ne yake samun rayuwa a irin yacca yake so ba, babu wani bawa da ke samun ɗorewar farin ciki a rayuwarsa, fa ce wataran sai yayi kuka. *MUTUWA*, ita ce tabbatacciya, kuma ita ce abar dake kan kowanne rai, wacca bata da wani banbanci a tsakanin me kuɗi da talaka, babba ko yaro, me mulki ko mara mulki, ita ce wacca bata barin wani don wani yaji daɗi. sau tari ɗan Adam kan zauna yay ta tunanin yaushe ne zai mutu?, kuma ai na?, taya zai mutu ɗin?, mene zai iya zama ajalin nasa?, sai dai waɗannan tambayoyi babu wani mahaluƙi da yake da amsar su, mutuwar ce kawai take zuwa da kanta, walau ɗan Adam ya shirya mata walau bai shirya ba, ko ana so ko ba'a so, da zarar ta zo tafiya kawai ake yi, ta datse wannan numfashin da bawa yake fitar da shi, acikin jin daɗi wa ko akasin hakan. mutuwa ita ce kaɗai abar da ke iya yanke ƙaunar da ke tsakanin uwa da ɗanta, ko miji da matarsa, ko masoyi da masoyiyarsa, ko aboki da abokinsa. ta kan zo ne bagatatan ba tare da ta sanar ba, sau tari mu kan kasance tare da mutum, kuma a yayin da aka sami giftawar wani lokaci bayan rabuwar mu sai muji ance wane ya rasu, ko kuma wane ya mutu, a lokacin ne zamu yi tunanin me ya sami mutum?, taya za'ai ace ya mutu bayan muna tare a ɗa zu muna hira cikin wasa da dariya?, to ita mutuwa haka take, ta kan ɗauki bawa ne da lafiya ko ba lafiya, kuma a lokacin da wani ke kan hanyarsa ta zuwa duniya, a lokacin mutuwa ke ɗaukar wani ta raba shi da wannan duniyar duk son da yake yi mata kuwa, hakana duk son da ake yi masa. in ace mutuwa zata bar wani don wani yaji daɗi, da tabbas bata raba ɗa da mahaifiyarsa ba a lokacin da yake zuwa duniya ba, wata uwar kan samun damar ganin yaronta kafin mutuwar ta ɗauketa, yayin da wata yaron na fito ita kuma zata yi sallama da duniyar. a lokacin da aka ce mutuwa ta raba mu da wani mutum da yake sashi na jikin mu, ruɗewa da tsananin shiga tashin hankali tare da fitar hayyaci kansa mu gaza yarda da cewar an mutu ɗin, anyi tafiyar da babu dawowa, har ta kai ga ba ma gama yarda da cewar tabbas mun rasa wannan da muke jinsa wani ɓangare na jikin mu, har sai lokacin da aka ɗauki gawarsa acikin makara, aka tafi da ita zuwa maƙabarta, aka kama gangar jikin aka zura acikin ramin ƙabari, har a jera tukwane akan gawar, da ƙasar da za'a zuba akan tukwanen, sannan a shafe hasken farin likkafanin dake lulluɓe da gawar. a sannan ne zamu yarda da tabbas an tafi, an yi tafiyar da ba za'a sake dawowa ba, tafiyar da ba zaka ƙara ganin mutum ba sai a lahira, har ko da yaushe fatan guda ɗaya ne, mu mutu muna masu aikata alkhairi, mu zama masu cikawa da imani, mu zamto mun mutu ana yabon mu. a lokacin da kumburarrun ƙafafuwanta ke sakkowa daga matattakalar benen a hankali, a lokacin take jin wani baƙon yanayi yana ziyartarta, a lokacin take jin wani abu da bata saba jinsa ba, wani irin yanayi ne take jinta a ciki, wanda ya ke zarcewa har can ƙasan zuciyarta, ya motsa zuciyar tare da abin da ke cikinta. sai a lokacin da ta isa parking lot, tasa key ta buɗe motar, sannan ne ta fahimci kamar kewa ce take kamata, kamar dai zata yi kewar wani abu me muhimmanci a rayuwarta. sai dai abu guda ɗaya take so ta sani, menene dalilin da yasa take jin jikinta yayi sanyi sosai?, irin wannan sanyi da bai taɓa ji ba. wayar da ke riƙe a hannunta tayi ringing, duk irin farin cikin da take shiga a sanda taci karo da kira daga gare shi, yau sai taji wani mix feeling ya kamata, taji kamar tana tausayin shi me kiran ba ita kanta ba da take zama da ƙyar tashi da ƙyar. ta ɗaga kiran ta kara a kunne cikin jin sanyin jikin da ya ƙaru a gareta. "uwar ƴaƴana ina kewar ki, kullum idan bana tare da ke sai in ji ina kewarki kamar zan mutu, na kasa yin aiki yau gaba ɗaya, tun da na shigo office na zauna nayi jugum, sai nake jin kamar ban taɓa kewar ki ba sai yanzu ne zan fara, gabana yana faɗuwa, zuciyata ta kasa samun nutsuwa, yau jina nake tamkar maraya, kuka zan yi Fulani Nah, ina jin kamar zan yi kuka irin wanda ƙanan yara ke yi, Fulani Nah in taho gare ki yanzu?, in zo in kwanta akan ƙijinki in dinga jiyo sautin bugawar zuciyarki a yayinda kike lallashina?, jikinki kawai nake buƙata ayanzu Fulani Nah, ina ji daga yau ba zan ƙara matsawa daga kusa da ke ba, zan daina fita aiki saboda ke, kina lafiya Fulanin Turaki?". maganganun da suka fito daga bakinsa kenan, kuma maganganun da suka haddasa wata muguwar faɗuwar gaba a ƙirjin Fillo. bata san lokacin data shiga motar ta zauna ba. "ki shirya yanzu kije wurin Maama, yanzu zan taho, ba zan iya zaman office ɗin ba, ina so yau mu yini tare, hira nake so muyi sosai, ɗa zu ta kira ni tace min faten tsaki take sha'awar ta sha". Fillo ta dafe goshinta,"Laaa ƙwara da Allah yasa ka yi wannan zancen, kamar na sani na dafa mata shi tun ɗa zu, kuma kaga har na fito zan tafi na kai mata ashe na barsa ban ɗauko ba". "ki bata ta ci da yawa Fulani Nah, duk yawansa kisa ta ta cinye shi kin ji, tana sonsa, shi ne favorite ɗinta, ta ce me kifi take son ci, in few minutes zan iso gare ku, ki kula min da kan ku, zan siyo miki mangoro, Maama kuma zan siyo mata gwanda". "tom Jannaty sai ka dawo, nima yau kewarka da nake yi ta banbanta da ta ko yaushe". "Fulani Nah saura 20days mu zama Mum and Dad ko?". "insha'Allahu Jannaty". "Allah yasa ki haihu da ranki da lafiyarki". bayan gama wayar ta su Fillo to koma ciki, tana shiga kitchen ɗin ta kira lambar Hajiya Madina. daga ɓangaren Hajiya Madina ta ce,"Daughter yanzu nake shirin kiranki, ina ta jin kewarki na damu na, idan babu abin da kike yi ki taho yanzu, in Me Babban suna ya dawo sai ku tafi tare". Fillo ta ce,"Maama faten tsakin me nama nayi, kina so ko nayi miki me kifin?". fuskar Hajiya Madina ta washe da murmushin jin daɗi, duk duniya tana bala'in son souls ɗin nan guda biyu, Turaki da Fillo. "kar ki wahalar da kanki, ba sai kin ƙara ɗora wani ba, zanci wanda jikana ya ci". "to Maama idan na zo ba zan dawo ba, yau ba'a ɓangarena yake ba". "to shikenan. ki hanzarta ki zo Daughter, ina so zan yi wasa da jikana, ina so yau nayi ta kallon fuskar ki". Fillo na murmushi ta kalli cikin da ke jikinta, haka Hajiya Madina take yi, aikinta yanzu bai wuce tasa Fillo a gaba ba tayi ta magana da cikin tamkar a gaske, in anyi dariya sai tace ai ita tana jinsa su ne basa ji, kuma idan ya fito zai ba su labari ne. haka ɗaya yau zuciyar Fillo taji tana so ta yafewa wannan mutumin da ta manta a rayuwarta, kamar ta yafewa Amir, sai ta rumtse idonta ta hura iska a bakinta ta fita daga kitchen ɗin. tana tayar da mota kiran Ummi ya shigo wayarta. "Auta kina lafiya?". "lafiya lau Ummi". "masha'Allah, ina zaune naji ina kewar ki". "wallahi nima Ummi jira nake naje gidan su sai muyi vedio call da ke, yau kawai ina ta kewarki sosai fiye da da. Ummi na yi mafarkin Abba ma, yace in gaida ke, sai naji kamar na bi shi Ummi". *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *59* idan mu ka duba fuskar rayuwa, zamu ga gaba ɗaya tana tafiya ne based on yanda Allah (SWT) ya tsara mana. rayuwar mu na tafiya ne daidai da yanda ubangiji ya rubuta mana tun kafin zuwan mu duniya. duk hasashenmu, duk lissafin mu, duk yanda muke so, duk yanda muka tsara, duk yacca muke tunani, duk yanda ba ma so, duk yanda muke gudu, duk yanda muka yanke, to haƙiƙa yanda ubangiji ya rubuta mana hakan ne zai kasance, kuma na ubangiji shi ne daidai. sau tari idan muka duba fuskar rayuwa, zamu ga duniya tana yiwa wanda ya jima yana aikata laifi talala, zai ta aikatawa yay ta aikatawa, kafin ya ankare sai ya farga lokacin tuba ya ƙure masa, wani Allah zai iya nufar sa da tuba kafin mutuwa, wani kuma ba zai sami wannan damar ba, haka zai wuce lahira da tarin ɗumbin zunubi. haka sau tari zamu ga rayuwa ta rufta da wanda zai aikata laifi sau ɗaya tal a rayuwarsa, nan da nan sai ya fuskanci hukunci abin da muke tunanin me aikata babban kuskuren shi ya kamata ya karɓa. haka zalika idan mu ka ƙara duba fuskar rayuwa, abin da duk mu ka sani shi ne asiri gaskiya ne, tun da har yaci shugaban mu fiyayyan halitta Annabi Muhammadu (SAW), kuma tasirin adu'a ya warka da shi, har aka gano wanda yay wannan sihirin. sai dai abun da yake da akwai a tamu rayuwar, ba ko da yaushe Allah ya ke tona asirin waɗanda suka zalunci wasu bayin Allahn ba, sai dai ubangiji yay wa bawansa sakayya kawai. idan mu ka ɗauki ɓangaren masu aikin asiri ga wani wanda bai ji ba bai gani ba saboda son zuciya da tsantsar zalunci. zamu ga a yayin da suka yi asiri sun yi nasara, sai dai ƙarfin adu'a kan karya wannan asirin na su komin tsayin shekarun da za'a ɗauka, yayin da wasu za su sami waraka suci gaba da rayuwar su ta yau da kullum, yayin da wasu kuma warakar zata zama ajalin su. sai dai fa abin da yake da akwai ko da asirin ya karye to bai zama tilas dole ba a san wanda yay wannan asirin har kuwa duniya ta naɗe, duk da cewa a yanzu ubangiji ya daina barin wannan ladan gabar, sanda za'a barka kayi ta yawo da hakkin mutane har ka mutu sai anje ƙiyama tukunna. a'a! a wannan rayuwar da muke ciki ta yanzu, tun a duniya Allah yake wulaƙanta mutum, rayuwa tayi kacakaca da shi, tayi masa ɗaurin goro, wataƙila ma ya faɗa tsananin wuyar da ta fi ta wanda ya jefa a ciki, har sai ma ubangiji ya so ka da rahmarsa sannan zai baka damar roƙon yafiyar wanda ka zalunta, idan kuwa aka yi rashin dace ubangiji bai baka damar fallasa kanka ba, balle har ka nemi yafiya, to lallai wata shari'ar sai dai a yi ta kuma a lahira. a lokacin da motar tata tayi parking a compound ɗin gidan, ta fito daga ciki riƙe da babban flask na abinci a cikin basket, ta jingina da jikin motar domin numfasawa, saboda yanayin nauyin cikin jikinta. Auwal ɗan me gadin gidan ya ƙaraso wajenta cikin sauri, bayan sun gaisa ya karɓi flask ɗin domin taimaka mata, bata hana shi ba saboda ita ma tana buƙatar ataimaka mata ɗin, duk da flask ɗin ba wai nauyi ne da shi ba, kawai dai ko ƙaƙa abu yake yana yi mata nauyi a yanzu. part ɗin Mum tana fara nufa, a parlo ta sameta tana kallon news da ake yi, ta zauna suka shiga gaisawa Mum na tambayarta yanayin jikin nata. a lokacin da Fillo ke kallon Hajiya Ramla tace,"Mum lafiya dai ko?". tayi tambayar duba da yanayin Mum ɗin da ta gani, fuskarta

Chapter 67 of 73