cinyar Turaki, ta buɗe idanuwanta da suka yi mata mugun nauyi, ƙwayar idonta ta sauka akan fuskarsa. a san da su ka haɗa ido sai tayi saurin runtse ido ta juyar da kanta gefe.
sabon kuka ne yake so ya ƙwace mata, so take ta motsa ta miƙe amma bata jin zata iya, every part of her body feels as if it is not her own, she is feeling pain everywhere, she wished ace bata yarda ta amince masa ba, kawai sai ta sa ki wani marayan kuka tana jin yacca take zugi ke ziyartar ƙasanta.
sautin kukan nata ya tafi ya zarce har cikin ƙuryar zuciyar Turaki ya matse zuciyarsa, zuciyar tayi rawa, da sauri ya ɗagota ya rungumeta yana shafa bayanta, shi kansa ya san dole tayi kuka, ya san bai yi mata ta sauƙi ba, bai ma san ta inda zai soma lallashinta ba, jinsa yake kamar babu wasu kalamai akan harshensa.
jin yanda hawayenta ke sauka akan fatarsa yasa ya dagota daga kafaɗarsa, sai kawai yasa harshensa yana goge ma ta hawayen, muryarsa na karyewa yake faɗin,"i am sorry wifey, you must pass this stage kafin kika zama cikakkiyar mace".
yaji ta ɗora hannunta akan ƙirjinsa, kafin muryarta ta fito cikin rauni tana faɗin,"mutuwa zan yi".
da sauri ya shiga girgiza mata kai yana faɗin,"not now, you will not die Wifiey, please don't say it again".
ta ƙara cewa,"jikina duk ciwo, ba zan iya motsawa ba".
ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka sosai, from the way tayi maganar za kasan a cikin ciwo take.
"zai daina ciwon yanzu insha'Allah, my only wish is you stop crying".
lallashinta kawai Turaki ke yi amma kamar yana tunzurata, Kukanta har cikin ransa yake ji, duk tausayinta ya lulluɓe shi, ji yake ina ma da damar da zai maida ciwon jikinsa.
duk ya rasa yanda zai yi ma ta, cikin kansa ya zama babu komai balle yay tunanin wata dabara, kamar bai san wa ni abu da zai yi ma ta taji sauƙin ciwon ba, ranar da ya kusancin Ilham tashi yay ya barta balle ya iya tuna wani abu guda ɗaya da yaga ta yiwa kanta ko kuma shi ɗin yay mata.
kuma kamar zai yi kukan shi ma, ya ɗauko wayarsa ya danna kiran lambar Zaytuna, har sau biyu bata ɗaga ba.
sai ya kira ta Bello, sai da kiran ya kusa katsewa sannan ya ɗaga, kuma sai bayan Bello ya ɗaga tukunna ya fara tunanin me zai faɗa masa?, yace masa me?.
yay guntun tsaki, yana jin Bello na ta hello hello MT lafiya a wannan daren, amma bai iya ce masa komai ba, sai kawai yay cilli da wayar ba tare da ya kashe ba.
sai a yanzu yaji ƙwaƙwalwarsa na karanta masa abin da ya kamata yayi, ya kwantar da ita cikin sauri ya shiga toilet ya kunna ruwan zafi, ya fito a daidai lokacin da kiran Bello ya shigo wayarsa, ya ɗauki Fillo sanna ya ɗau wayar ya kara a kunnensa.
ko abin da Bello ke cewa bai tsaya saurare ba yace masa,"after warm water then what?".
Bello yace,"Allah ya saka min kawai".
sannan ya kashe wayar bayan yaja dogon tsaki, Turaki na shirin ajiye wayar sai ga text ɗin Bello ya shigo. _sodium bicarbonate, salt and veniger._
yana karantawa ya mayar da Fillo ya kwantar, a wannan uban daren ya fita yaje part ɗin Ilham, dan acan ne yaga veniger da bakin soda, daga kitchen ɗinta ma ya ɗauko gishiri.
yana dawowa ƙarar text na ƙara shigowa. _just use salt and veniger is oak._
ya jefar da robar baking soda ɗin sannan ya shiga toilet ya kashe ruwan da ya kunna yake ta zuba, ya zuba abin da zai zuba ya sirka ruwan sannan ya fito.
yana kama blanket zai ɗaga ta damƙe tana girgiza masa kai,"please".
ya rufe ido ya buɗe,"babu abin da zan ƙara miki Angel".
sannan ta iya sakin blanket ɗin ya ɗauketa, yana sakata acikin ruwan ta fashe masa ta wani irin kuka tana riƙe shi, sai yaji kamar ya fito da ita, but he has no other choice.
"sorry Angel, i know it is painful but that will only make you feel better".
azabar duniya ta ishi Fillo, ta ƙara damƙo shi zata fito ya daɗa mayar da ita, kuka take sosai tana faɗin zata mutu, a sitz bath ɗin nan dai gaba ɗaya ta ruɗa Turaki ta gama gigita shi.
kuma duk uwar masifar da ta dinƙa masa akan ita ya fita ya ƙyaleta bata son ganinsa amma yaƙi fita, har sai da ya tabbatar ta ga su tukunna ya cirota yay mata wanka da kansa, anayi tana kai masa duka, bayan an gama sannan ya naɗota a towel kamar new born Baby ya fito da ita.
yana ɗorata saman gadon ta zabga masa harara,"ƙafana ba zai kuma iya tafiya ba".
ya zauna tare da kamo hannunta, zata ƙwace ya hana hakan, kissing forhead ɗinta yay kafin yace.
"Allah ya yi miki albarka, Allah yay miki sakayya da Aljannatul firdaus, na gode da kika kula min da kanki, yanda kika saka ni cikin farin ciki, ina roƙon ubangiji ya bani ikon faranta miki har ƙarshen rayuwata, insha'Allahu ba zan taɓa cutar da ke ba, wannan alƙawarina ne".
sai ya saketa yace,"kina jin ciwo a jikinki?".
ta ɗaga masa kai,"ai duk ka ɓalla ni".
"ban ɓallaki ba Hottie, yanzu ma zan ke baki abincin da zai sa kiyi ƙiba ba za ki ɓalle ba".
ta ɗaura kanta saman shoulder ɗinsa tace,"zafi nake ji".
ya ce,"ai na?".
sai tayi shiru, ya sauke numfashi yana shafo gefen fuskarta.
"zai daina, zai daina zafin kafin safiya".
sai kuma ya kira sunanta,"Fulani Nah".
ta amsa,"ummm".
ya ce,"I don’t have all of the words to express how much you mean to me. I can only say that you are the center of my life and everything else revolves around our love for each other. I will keep caring, adoring and loving you forever, during the easy times and the challenges we will face. I love you so much Angel".
ya shiga shafa fuskarta yana faɗin,"you deserve a gift from me in return of what you gave me".
"Bacci nake ji". ta faɗa da tsantsar shagwaɓar da ta motsa zuciyarsa, cikin murya me ban tausayi.
bargon ya ɗaga ya shigar da su ciki, da farko taƙi kwanciya a jikinsa saboda tsoronsa da take yi, kuma da ya shiga kalallameta sai ta lumshe ido ta lafe a ƙirjinsa lokaci ɗaya bacci ya ɗauketa.
shi kuma baccin da bai yi ba kenan har akayi kiran asuba, ya ƙura mata ido sai kallonta yake yi kamar tv.
ya zareta daga jikinsa a hankali ya tafi masallaci, har ya dawo bata ko motsa ba, yana taɓa jikinta yaji zafi rau kamar garwashi, yaji hankalinsa yay mugun tashi saboda zafin jikin nata ya wuce tunani.
tarkacen magungunsa dake watse a ƙasa ya kalla, ya duba kaf ciki babu pracetamol, sai can ya tuna akwai acikin maganinta da ke ɗaki, yana zuwa ya tarar babu, sai ya dawo ya ƙara taɓa jikin nata yaji ba wani sauyi.
ya ɗau waya ya kira Zaytuna bata ɗaga ba, sai ya kira ta Samha, tana ɗagawa yace,"kaiwa Zaytun".
jin muryarsa a rikice ta ce,"Hammah lafiya?".
ya buga mata tsawa,"nace ki kaiwa Zaytun".
da sauri ta diro akan gadon ta fita zuwa ɗakin Zaytuna, lokacin ta idar da sallah kenan.
ta karɓi wayar hannun Samha da ke yi mata alama da ido, ganin sunan Turaki ajikin screen ɗin taji mamakin kiran nasa a wannan lokacin ya kamata, ta haɗiye guntun yawu kafin tace,"hello Hammah...".
ai tun bata ƙarasa ya yarfa mata zagi yana yi mata masifa akan ƙin ɗaga waya.
baiwar Allah cikin sanyin murya tace,"na shiga uku, Hammah yau ni ɗin?, Allah ya baka haƙuri".
yaja tsaki, ba abin tayi magana ba ya ƙara yarfo mata wani zagin, don haka tayi shiru tana jiran cewarsa.
daki-daki taji yana karanto mata sunayen drugs ɗin da ta san nasa ne, daga ƙarshe taji yace,"wanne me zazzaɓi zai sha aciki?".
ta ce,"babu pracetamol ne?".
daga tambaya sai cibi ya zama ƙari, ya taso mata kamar zai rufeta da duka ta cikin wayar,"in akwai zan kiraki ne".
ta ɓata rai tana jin kamar ta kashe wayar.
"ibuprofen ko pracetamol zaka bata".
"duk babu anan, ki kawo min yanzu".
ta waro ido waje tace,"Hammah asuba ne fa".
yay tsaki,"kaiwa Sameer ki faɗa masa ya kawon yanzu, kar ya taho a ƙafa".
yana gama faɗa ya kashe wayar.
ba'ai 5minutes ba sai ga Sameer ya zo, yana fita ko gaisuwarsa bai amsa ba ya warci ledar maganin ya dawo.
ya ɗago Fillo ya zaunar da ita, ta buɗe ido a hankali ta kalle shi, zata sa kuka yay saurin cewa,"sorry Angel, sallah za ki yi".
jin ya ambaci sallah ta buɗe ido gaba ɗaya, taƙi yarda yay helping ɗinta sai da kanta taje toilet, duk taku ɗaya idan tayi sai zuciyarsa ta matse, yau rana ta farko da yaji kamar yay ihu saboda rashin samun damar maido da ciwon wani jikinka.
yana kallo ta fito tana dafe bango, ba zai iya jurar ganin yanda take takawa da ƙyar ba, kawai ya miƙe yaje ya ɗaukota, ya kunce towel ɗin ya saka mata jallabiyarsa, ya buɗe wadrobe ya ɗauko hiram ya yafa mata sannan ta tayar da sallah.
after ta idar ta kalle shi kaɗan tace,"ina so in kwanta".
ya taso ya ɗaukota ya dawo da ita kan gadon, sai da ƙyar ta buɗe baki ya zuba mata maganin ta sha, tun da ta sha kuma sai ta fara kukan ita Ummi ya kai ta wurin Kaka, tana jin zafi sosai ya kai ta su yi mata magani, acikin kukan kuma bacci ya ɗauketa.
ƙarfe goma sha ɗaya Fillo ta buɗe idonta a hankali, daki-daki ta dinƙa tuna abin da ya shiga tsakaninsu a daren da ya wuce, har yanzu a cikin kanta tana jin haskawar furucinsa na please help da ya ambata yafi sau a ƙirga, bin ɗakin ta dinga yi da kallo kafin ta iya miƙewa zaune.
karaf idonta ya fara sauka akan wani card da ya ɗauki hankalinta, ta ɗauko tana karanta rubutun da ke ciki, ɗauke da handwriting ɗin mutum ɗayan nan a duniyarta.
_i am proud of you wifey, very proud of you Angel, you are a precious girft to me from God, i love you so much Angel...Allah ya bamu ƴaƴa ma su albarka. Barka da tashi._
bata san lokacin da wani murmushi ya suɓuce ma ta ba, ta kai hannu zata taɓa cikinta idonta ya sauka akan kwalin waya dake kan blanket ɗin, Samsung W21, kamar ta so ta san wayar, sai ta tuna shekaranjiya ne su Nilfat ke browing suka ganta, ana lissafin kuɗin wayar 1.4something ML, ta ɗauka kwalin tana shafawa.
a lokacin ta ankare da farar takarda dake saman pillow daga gefen kanta, ta kai hannu ta ɗauko haɗe da maƙullan mota guda biyu da suke ajiki.
tana riƙe su a hannunta zuciyarta ta karanta ma ta,_another suprise, a huge suprise._
a sannan idonta ya kai kan wani gajeran rubutu ajikin ƙaramar papper,_Gratification of what you gave me last night._
cike da zumuɗi ta buɗe takardar, doguwa ce ɗauke da dogon rubutu acikinta, takardar shaidar mallakar gida ce da ke ƙasar Ausburg ɗauke da sunanta a jiki, *Halima Muhammad Barkindo.*, ta ɗauki keys ɗin guda biyu tana juya su a hannunta.
bata san lokacin da ta ƙwala ƙarar murna ba, daidai da shigowar Turaki ɗakin, ta kalle shi ta yunƙura zata miƙe sai taji ba zata iya ba, lokaci ɗaya hawayen tsananin farin ciki suka zubo mata.
ta buɗe hannayenta tana kallonsa tattare da so da ƙauna, sunan da bata taɓa ji ya shiga cikin kanta ba, sunan da bata taɓa alkintawa ba a mind ɗinta, sai a lokacin taji wanzuwarsa acikin zuciyarta da ma ruhinta.
"come to me Jannaty...".
tray ɗin hannunsa ya ajiye kan table ya taho gareta, a gabanta ya duƙa ya shiga jikinta kamar yanda ta buƙata, ta kewaye shi tana masa wata special runguma, ta ce,"thank you so much for the gifts, thank you Jannaty, love you more, i'm very proud of you, you made my world so beautiful, Ya Rahman ya saka maka da gidan Aljannah".
ta faɗa tana ɗora bakinta a wuyansa tayi kissing ɗinsa.
"Jannaty...". ta kira sunan nasa bakinta yaƙi rufuwa.
yaja hancinta ya ce,"yau ba Turakin?".
sai tace,"Turaki ina so zan ga motan".
"bakinki kawai ne ya iya faɗin sunan Turaki".
ya kamo hannunta ta tsaya akan ƙafafunta da ƙyar, kafin ya ɗauketa suka fita, a downstairs su ka wuce su Sakina dake zaune a parlon su na kallo.
a sanda Fillo taga motoci biyun, a lokacin ta nemi ciwon da ke jikinta ta rasa, ta doka uban tsalle ta maƙale wuyansa cike da tsananin murna.
godiya kawai take zabga masa tare da jero tarin adu'oi, ta nemi wannan kunyar tasa da take ji tun a daren jiya ta rasa.
"Maama tayi min kyautar su, ni kuma naga babu wanda ya dace da su sama da ke. ina sonki da yawa Angel".
sai da ta shiga duk mota biyun kafin ya ɗauketa su ka koma ciki, yana faɗa mata idan taji sauƙi zai fara koya ma ta driving.
ya sauketa a kan kujera, ta shaƙi iskar bakinsa da ta fita a lokacin, ta marairaice murya tare da faɗin.
"you have your breakfast without me?".
ya kalli yanda tayi narai-narai da fuska kaman zata yi kuka.
"ban yi breakfast ba Angel".
"but naji bakinka na ƙamshin mint leave and coffee".
ya ɗaga mata gira tare da miƙewa yaje ya ɗauko tray ɗin da ya shigo da shi ɗa zu.
"kurɓa ɗaya nayi, and am sorry for that".
"wa ya haɗa wannan?".
"ni ne".
"ummm".
"da gaske fa, i make this coffee for you, Zaytun na kira ta faɗa min yanda zan yi. tana ta min dariya da tambayar ƙwaƙwaf".
da kansa yay feeding ɗinta har ta ƙoshi, sai bayan nanne ya kira sunanta da Mrs Turaki.
abin da ya faru daren jiya ya dawo ma ta sabo, kunya ta lulluɓeta, ta yi saurin saka hannu ta rufe fuskarta.
"wallah you are so sweet Angel, you finished me yesterday night, shiyasa zan koma kiranki da Hottie, ƴar ƙarama da ke kin zautar da ni".
ba shiri ta ƙara ɓoye fuskarta a jikinsa.
da daddare su na zaune, kan Fillo na saman cinyarsa, yayin da wayarta ke riƙe a hannunta, tun ɗa zu take ta danne danne taƙi rabuwa da wayar, abinka da ɗan ƙauye yayi agogo, magana ma in yay sai ta ɗau lokaci kafin ta ba shi amsa.
"ba sabanban".
tayi murmushi kafin tace,"su Ummi su na gaisheka, Dada tace in ce ka gaida Boɗejo".
"yaushe ku ka yi waya?".
"ɗazun da kaje masallaci. Ummi na tayani godiya".
kallon da yay ma ta yasa tayi saurin rufe ido, ya kama hannun yana faɗin,"Don Allah Hottie, ɗan kaɗan fa".
tai saurin barin jikinsa ta ajiye wayarta ta dunƙule a waje ɗaya.
"ni a'a, har yanzu ina jin zafi".
Daga wannan ranar, sabuwar rayuwa ta *MH*(Muhammad & Halima) ta fara, sabuwar shaƙuwa, sabuwar soyayya, tarairayar juna da kulawa.
zuwansu ƙasar Ausburg ba ƙaramin daɗi yayi mu su ba, Fillo an waye an kile, mo re soyayya kawai suke yanda su ke so, kullum su na kan hanyar yawon shaƙatawa, a fita tun safe a yini a bakin beech.
wata irin soyayya Turaki yake nuna ma ta me ban sha'awa, yayin da ita ma anata ɓangaren bata ƙyale ba, don tuni Nuratu ta ɗorata a layin manya, ƙoƙari take yi sosai wurin ganin ta faranta ran Turaki, wajen ganin ta mantar shi kowacce mace a rayuwarsa, wajen ganin ta zama ita ɗaya a duniyarsa, gaba ɗaya rayuwar Fillo ta sauya acikin irin kulawar mijinta da tarairayarsa, this week su ne a wannan ƙasar another week su ne a wata ƙasar, acikin wata guda sun manta ma da nigeria gaba ɗaya.
su ci abinci tare, su yi wanka tare, su yi bacci tare, shi kansa aikin gida tare su ke yi, su shiga kitchen tare su yi girkin su a tare, don ba sa tsayawa wani bin order, goggling girki take da irin kayan abincin ƙasar su sarrafa abinsu, kuma in suka dafa kamar ma sun fi ƴan ƙasar iyawa.
a kullum idan su na tare sai su ke ganin tamkar lokaci a tsaye yake cak, tamkar babu kowa a duniyar nan sai su biyu kacal, rayuwa su ke yi acikin kwanciyar hankali da natsuwa.
wajen ƙarfe bakwai na safiya a ƙasar Australia, Fillo na tsaye ne gaban mirror tana tattare jelar gashinta ta tufke acikin ribom, tana sanye ne da ƙaramar riga armless milk colour da tayi matching da skin ɗinta, sai short skirt da ash color da ko gwiwarta bai kai ba.
kayan sawarta kenan a kullum tun da su ka baro nigeria, don su ne choice ɗin Turaki, ba ya son wata atamfa da danginsu, shiyasa ko da za su taho ko ɗankwali bai bari ta ɗauko ba banda kayan dake jikinta, sai da su ka sauka a ƙasar tukunna yaje ya rakito ma ta uban ƙanan kaya kamar wanda zai buɗe store.
tasa hannu a bayanta ta barƙala yay ƴar ƙara, a gajiye take gaba ɗaya, daren jiya su ka dawo daga saudia, bata taɓa jin rashin jin daɗin zaman jirgin ba sai a jiya.
madubin ya haska ma ta fuskar Turaki da ke tsaye a bayanta, wanda yasa hannu ya zare ribon ɗinta gashinta, ya baje a kafaɗarta.
"na fi son ganin gashinki a haka".
ya faɗa yana rungumeta ta bayan tare da ɗora fuskarsa akan gashin yana goga hancinsa akai.
"kullum ƙara kyau kike yi, tell me the secret".
ya faɗa yana kama hannunta, ya shiga tracing jan lallen da akayi mata da suka je india.
"hannun ya ƙara kyau da ya fara ƙiba yanzu".
sai ya ƙara cewa,"na ga twins ɗi na su na ƙara cika". ya faɗa yana zura hannunsa cikin rigarsa ya shiga shafa breast ɗinta.
ta lumshe ido kawai kamar me jin bacci, jinta take yi kamar bata da lafiya.
ganin yanda tayi wani collapse ya juyo da ita yana cewa,"what happened to my Angel".
da narkakkiyar shagwaɓa tace,"yaushe zamu koma gida, na gaji da zaman nan ɗin, yawon ma na gaji da shi, i want to see Mum, Maama, Ummi, Kaka, Dada, Adda Zaytun, Hammah Hamid, and Boɗejo, i am missing them alot".
ya rufe ido kafin yace,"not now".
ta riƙo hannunsa kamar zata yi kuka ta ce,"haba my soul, mu tafi gobe please, Allah na gaji da cin abincin ƙasarar nan, duk komai na ci babu daɗi, ina so inje in ci tuwon Kaka".
"haba Hottie we just spend only 3months fa, ai bamu gama honeymoon ɗin ba, ki bari mu cika 5months ɗin da Bello ya ban takardar hutu da ƙyar".
tayi shiru bata ce komai ba.
zai ɗauketa ta hana shi tana faman yamutsa fuska, ya waro ido yana cewa,"why?, wani abu na damunki ne yau?, duk naga kin yi wani iri kamar mara lafiya, tell me ina ne yake miki ciwo?".
ta wuce ta barshi bayan tace,"idan ka ɗauke ni zan iya yin amai".
ya bi bayanta da kallo, har sanda ta kwanta kan gado kamar wata mage, duk sai yaji tausayinta ya kama shi, may be har yanzu stress ɗin jiya bai rabu da ita ba.
ta buɗe lumsassun idanuwanta ta kalle shi kaɗan tace,"i want to sleep".
ta faɗa tana mayar da idonta ta rufe.
ya cire bluetooth ɗin dake maƙale a kunnensa ya ajiye akan mirror, tun da tace she want sleep tana nufin yazo ta kwanta a jikinsa, dan in dai ba dole ba bata taɓa iya bacci in ba ajikinsa.
ya hau gadon tare da kwantar da ita a jikinsa, a hankali yake shafa bayanta.
_tauraruwa ɗawisu, a Mata ni banga kamarki ba Fulani Nah. ke ce gaba domin kin ba su rata, tauraruwa ke ce me haska Mata, ko ince autar Mata don kina da gata, ba mai taɓaki in bar shi, me sonki dole in so shi...ehh ki yi ta farin ciki wurina kenan, in ga kina ta dariya shikenan, komai kike so zana zam yi miki sannan, abin da ba ki so in daina wannan, sannu sha yabo kece abar yabawa, Allah ya tsareki Mata ta kirki, Fulanin Turaki._
cikin golden voice ɗinsa yake rera mata waƙar a kunnenta, waƙar da a lokaci ɗaya ta kore baccin da take ji ɗin, wannan waƙar ta M Sharif da zata ce ita ɗaya ya iya a waƙar hausa, ita ma ɗin ya iya ne just becouse of her.
a kullum bai rera ma ta ita ba yay sama da sau biyar, su na aiki yana rerawa, in tafiya suke a mota, balle kuma ta lafe a jikinsa.
hatta bishiyar da su ke zama a ƙasanta in sun je beech za ta iya cewa ta haddace baitin.
Turaki yay ta ƙoƙarin da zai hanata baccin, don so yake yi ta tashi su yi excercise, ba ya so ta koyi lalaci tun da wuri haka, and ya fara ganin alamu 3days ɗin da suka wuce.
tana kuka kaɗan tace,"don Allah Jannaty ka barni in huta, shiru nake so ko da banyi baccin ba".
"idan kuma kika yi baccin fa?".
"zan so hakan, domin shi kaɗai ne abin da nake buƙata a yanzu".
"ki bari sai da daddare, yanzu kina kwanciya za ki cika ɗakin nan da minshari sai kace rago na kuka, duk ki cika min kunne ina tsorata".
babu shiri ta miƙe a jikinsa, ta sauka akan gadon tare da ɗaukar pillow, sai da taje bakin ƙofa sannan ta tsaya ta saita kansa ta jefa masa pillown.
"kai ne kake minshari ba ni ba, ɗakin nan ma shaida ne. ka sha zamanka kai ɗaya, bye".
yana dariya ya taso, ganin hakan tayi saurin jan ƙofar ta rufe tasa key, bata ko cire key ɗin a jiki ba gudun kar ma ya buɗe da spare, ta nufi ɗayan bedroom ɗin, don tana so ta huta ne sosai a yanzu, duk jikinta take jin ba ƙwari balle daɗi, ga zuciyarta da ke ta tashi, burinta tayi amai kawai ko ta huta, amma aman yaƙi zuwa.
*BAYAN WATA ƊAYA.*
*Nigeria.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*57*
*ƙarfe tara na safe.*
tun daga ƙofar gidan zaka shaida ana wani babban taro a gidan, taro irin na bikin aure.
motoci ne iri-iri daban danƙare daga wajen gidan, a yayin da gate ɗin gidan yake a wangale gaba ɗayansa, wasu mutanen na shiga ciki wasu kuma na fita.
Khaleel ne tsaye a bakin gate, wanda yake ango a yanzu, waya ce kare a kunnensa yana faɗa akan abin da ban san menene ba.
Sameer ya iso wajen a lokacin yana cewa da shi,"Hammah yace kaje gida ka same shi".
sai a yanzu na fahimci da wanda yake faɗan a wayar, amaryarsa ce suke rigima akan irin ɗan ƙaramin lamarin nan da ba'a rasa shi tsakanin kowanne ango da amaryarsa.
"to ba zan bayar ba, in za ki haƙura ki haƙura".
daga cikin wayar ɓangaren Rashida ta ce,"haka kace?, to zaka san kayi da ƴar halak, wallahi sai in ce ma ba za'a kawo ni gidan naka ba".
ita ma tayi maganar a fusace kamar yanda shi ma yayi.
"hakan zai sa ki burge ni".
ya faɗa yana kashe wayar ya jefa cikin aljihu, ransa a ɓace ya nufi mota ya shiga.
daga cikin gidan, idan ka shigo compound, zaka kutsa ne ta cikin tarin jama'ar da ke ta hayaniya su na kaiwa da komowa wajen aikace-aikace, wasu na wucewa da manyan kuloli na abinci, yayin da wasu ke tsaye akan babban kaskon da ake suyar nama a cikinsa.
idan ka lura da part huɗun da ke jere, za ka fahimci a ɓangare na uku daga ɓangaren dama, wanda shi ne ɓangaren Hajiya Ramla, anan ne taron mutanen yafi yawa, don ga takalman jama'a nan birjik daga wajen ƙofar parlon.
a yayin da ka shiga cikin parlon, zaka tarar da manyan mata masu ji da kansu, waɗanda suka sha ilimin boko, boko ta ratsa su ta ko'ina, waɗanda mafiya yawan su ma'aikata ne a ƙarƙashin federal government.
wasu na zaune akan kujera yayin da wasu ke zaune a ƙasan carpet ɗin da aka malale duka parlon da shi, kowa na hira da abokin zamansa, hayaniyar dai tayi yawa wacca ta kai ga har ba'a iya jiyo sautin muryar wata dattijuwa da ta shigo ciki tana kiran sunan Hajiya Ramla.
a lokacin ne kuma Hajiya Ramla ke sakkowa daga saman bene tare da ɗaya daga cikin amaren da ake aurarwa wato Samha.
magana suke yi yayin sakkowar ta su inda Samha ke ta ƙorafin hayaniyar.
"na nemi Nihal na rasa, ki lalubo min ita acikin taron jama'ar nan don Allah, ta zo driver ya kaita su karɓo mana ɗinkin mu. kina kallo ma Fillo bata sami saka ankon ɗaurin auren nan ba, haka Babana ya zo ya sakani a gaba yana ta kumbure-kumbure, ni ban san ya akai ku ka kaiwa ɗan shiriritar tela ba".
Samha
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 64 Chapter of 73