Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na mutunta ƴan'uwansa, Anty kamar fa zai duke ni, duk yadda na so da kar a fahimci ina cikin damuwa sai da Maama ta fahimta, da na dawo da daddare sai ce min yayi wai naje na kai ƙararsa ina so in shiga tsakaninsa da iyayensa, to wallahi zai yi min abin da ban taɓa zato ba, zamana da shi babu dole..." kuka ya ƙara kubcewa Fillo sosai,"kuma wallahi tallahi Anty ban kai ƙararsa ba, na san dai nayi iyaka ƙoƙarin da za'a fahimci bana cikin damuwa amma na gaza, shi ne har Maama ta gane ta tsare ni da tambayoyi, kuma ita ma ban ce mata ga dalili ba haka nace mata bana jin daɗi ne, kuma da ta san da ma ban da lafiya bata ƙara tayar da zance ba, amma shi ne har yake ikirarin wai sai ya rabu da ni in har na nuna bana son ƴar'uwarsa ko kuma na ƙara kai ƙararsa wurin Maama. tsakani da Allah Anty ko anan idan tazo ya nuna mata ta fini matsayi ba sai yaja min wulaƙanci daga wurinta ba, yanzu nan ƙunshi nace za'a yi min sai ce yay ba da yawunsa ba". Nuratu taji tausayinta sosai, ta dinƙa bata haƙuri da lallashinta, tare da yi mata nasihohi da kuma wasu shawarwarin da zata ji daɗinsu muddin tayi amfani da su. kafin nan suka yi sallama taja motarta. *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *58* dawowar Fillo gida ta tarar ana ta kai komo wajen shiga da kayayyaki ɓangaren Ilham, tun jiya ake wannan zaryar, ƴan'uwan mahaifiyarta ne kusan duk ɗin su, sai Boɗejo da Inna Falmata. sai dai bata san ba ko yau har da su tunda dai bikin ba ɗaya ba ne, duk da dai taga Boɗejo na nuna kamar bata da hurumi da auren su Zaytuna da Khaleel da Samha, kamar su ma ba jikokinta ba ne. ɗauke kai tayi daga barin kallon part ɗin Ilham ɗin, tayi wucewarta part ɗinta bayan ta tambayi Baba me gadi ko an kawo masa abinci, da shigarta kuma ta rufe su Sakina da faɗa akan rashin kaiwa Baba abinci da suke yi da wuri. ta kalli Maijidda da ke zaune a parlon ta haɗe rai, ta ce da ita,"yi haƙuri don Allah, sammako nayi gidan Yaya Yusuf, za su je taraba ne na bayar da saƙo akaiwa Ummi". Maijidda tace,"ba dai bikin Raudha ba". "shi ne ya taho wallah, next week in Allah ya kaimu". "kin ga da an kammala na su Adda Zaytun sai ki bi su ku tafi tare kawai". Fillo tayi murmushi me ciwo ta ce,"ni ma haka nace. ki hau sama ki jira ni bari na ajiye waɗannan kayan". ta faɗa tana wucewa kitchen, friedge ta buɗe ta zuba fruites ɗin da ta siyo, kusan kwana uku da ƙarewar na su amma Turaki bai kawo wani ba. fitowarta daga kitchen ɗin ta tarar da baƙi a parlon, fuskar farko da ta kalla ta shaida ƴan'uwan Ilham ne, don su na kama sosai da Fulani Azima. ta ƙarasa wajen su ta durƙusa har ƙasa, cikin ladabi ta shiga gaishe su, kuma ba tare da ta miƙe ta koma kan kujerar ba tayi zamanta akan carpet ɗin don bata tunanin zata iya zama kan kujera alhalin su na kai, hakan kamar da rashin ɗa'a. su uku ne manyan matan, kowacce sai da ta gama yi mata kallo a yatsine sannan suka haɗa baki wajen amsa gaisuwartata. Antyn Kano ta dubi Fillo da kyau kafin ta mayar da dubanta ga Mama Asabe ta ce,"wannan ce kishiyar Ilham ɗin?". Mama Asabe tace,"ina jin ita ce ko?". sai kuma kusan a tare suka jefawa Fillo tambayar,"kece matar nan ɓangaren ko kuma ƴar aiki ce?". kafin Fillo tayi magana Hajiya Zaliha ta amshe da cewa,"ita ce mana". "yanzu wannan ita ce wacce aka liƙawa Turakin da ma?, ai ce nake yi waccan da aka ce an ba shi a bushe take ko". Mama Asabe tayi maganar. Hajiya Zaliha ta taɓe baki ta ce,"yo ai dama saboda su taimakawa ƴar'su ta zama mutum kuma su ci arziƙi, shiyasa suka bi ta ƙarƙashin ƙasa suka kori Ilham aka liƙa masa ita, amma banda haka Turaki ai yafi ƙarfin tsummar ƴar aiki, ko da yake banga laifin iyayenta ba dan sun yi ƙoƙarin haɗa iri da mai dukiya kamar Turaki ba. hausawa suka ce bangon sukari a jingina da kai a lasa, yanzu ba gashi sun mayar da ƴar'su ta zama mutum ba, dama ai ƙwaɗayin dukiyar tasa ake ba wai saboda Allah suka nuna su na sonsa ba, yo ke daga jin labarin ɗauke asiri ai kin san ƙarya ne ma". Mama Asabe ta ce,"to ai ni a wata ruwayar ma ji nayi ance bata da asali, ance uwar na haifarta ta jefar da ita ta gudu, an ce ma bata san uban nata ba sai da zai mutu yazo neman gafarar uwar. to duk dai kin san harkar ta a haɗu a rufawa kai asiri ne shiyasa aka ɓoye gaskiyar zancen, amma dai tabbas an ce shegiya ce". Antyn Kano ta gyara zama tana duban Fillo, ta kama haɓa ta riƙe cikin izgili ta ce,"shegiya kuma?, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ashe abun har haka yayi muni, yanzu tsakani da Allah ina gamin haɗi tsakanin tsarkakke da gurɓatacce, shege ai sai ɗan uwansa shege, gaskiya wallahi an zalunci yaron nan, ko da yake aikin asiri babu abin da ba yayi. to ni su Mai Martaba ma mene na haɗa Ilham kishi da ƴar gaba da fatiha?. kai talaka dai akwai zubarwa da kai mutunci, da zarar an ce an rasa cin na yau da na gobe shikenan sai kiga an faɗa harkar karuwanci kuma. Allah dai ya kyauta yasa kar a haifi iri". tun a zancen farko zuciyar Fillo ta buga da ƙarfin gaske, ranta ya ɓaci sosai. a yanzu da Antyn Kano tayi magana ta ɗago da kanta tana kallon su, lokaci ɗaya idanuwanta suka cika taf da ƙwalla. Mama Asabe ta sake cewa,"um to mu yi dai abin da ya kawo mu". ta kai dubanta ga Fillo ta ce,"ga shi ba sanin sunanki muka yi ba, to ma dai in aka kira ki da shegiya ai ba'ai lefi ba sunan yanka ne irin naku na haihuwar kan titi. allura muka zo ki bamu idan kina da ita za'a cire sartse". a lokacin zazzafar ƙwallar da ke cikin kurmin idanun Fillo su ka gangaro saman kumatunta, wani irin baƙin ciki ya turnuƙeta, jin zuciyarta take yi kamar zata yi bindiga. she can't stay any more ana cin mutuncinta da na iyayenta. in ba haka ba za'a iya kaiwa gaɓar da wataƙila zaman aurenta ya ƙare yau a gidan nan. taji yo maganarsu su na ƙara faɗin,"ai Ilham ma tafi ƙarfin kishi da wannan wallahi, ta maishe da shegiya ƴar aiki kawai". cikin raɗaɗin zuciya Fillo ta miƙe zata bar wajen. Hajiya Zaliha ta dakatar da ita da faɗin,"ke figaggiyar kaza dama ba ki da tarbiyya, ina allurar da muka ce ki ba mu?, saboda kin mayar mu ƴan iska za ka kaɗa kai ki wuce ba ki ko tanka mana ba". Fillo ta runtse idanuwanta, ji take yi kamar ta tanka musu, kamar ta faɗa musu maganar da har mutuwa ba za su manta da ita ba, ta ci musu mutunci irin wanda ba za su ƙara sha'awar zuwa gidan nan ba har a tashi duniya, duk kuwa da cewar sun ajiye ƴa acikinsa. but ɗayan ɓarin zuciyarta sai ya haneta hakan, ba halinta ba ne, ba tarbiyar da aka bata ba kenan, tayi banza da su da maganar da suke yi ta haye sama tana goge hawaye. ba ta shiga ɗakinta ba sai da ta daidaita nutsuwarta tukunna, gudun kar Maijidda ta fahimci abin da ya faru. ko da ta shiga ba ta kalli in da Maijidda ke zaune ba tayi saurin shiga toilet ta wanko fuskarta, tana fitowa sai ga Hannatu ta shigo ɗakin, ta durƙusa tana faɗin,"Anty baƙi a ƙasa sun ce ki ba su allura". ta dafa kafaɗar Hannatu suka fita, su na tsaye ta wuce kitchen ta fito, ta tsaya tare da musu kallon banza kafin ta buɗi ba ki ta ce,"ban da zubar da mutunci ina ku ina aron abu?, anyway matar so bata da kayan faci a ɓangarenta balle tayi ajiyar wata allura". tana faɗar hakan ta haye sama abin ta, fiye da haka ta so ta faɗa musu, to gudun tashin hankali yasa ta rabu da su kawai. ko da ta koma ɗaki bata bari Maijidda ta fahimci komai ba, ta zauna suka cigaba da hira. "kin san Allah da tafiyata zan yi. ni kin san ba son ƴan aikin nan nake ba balle in zauna muyi hira da su. yanzu dai ina zamu je ƙunshin?". "to ai ma Maama tace wadda ta yiwa su Adda Zaytuna ita ce zata yi min, yanzu wurin saloon kawai zan je, mu bari sai da yamma ma je ko?". Maijidda tace,"a'a kin san halin lalle da cin lokaci, mu fara zuwa saloon ɗin tukunna". "to shikenan. bari naje na faɗa masa. kin san nace miki ina son zuwa gidan Yaya Yusuf, shi ne fa yau na buga musu sammako". ta yaye mayafin jikinta ta ajiye sannan ta fito ta nufi ɗakin Turaki, yana zaune kan kujera yana operating laptop, hannunsa riƙe da ƙaramin glass cup yana kurɓan coffee. yaji shigowartata amma bai ko ɗago ya kalli wurin da take ba, sai dai yayi mamakin ganinta ɗin, dan rabonta da ɗakinsa tun ranar da ya faɗa mata cewar zai dawo da Ilham, yau kusan kwana tara kenan. ko abinci idan ta gama a parlo take barinsa, ta ci nata ta bar masa nasa, ruwansa ne yaci ruwansa ne kar ya ci, yacca ya lura ma kamar girkin ma ba yi take ba sai dai ƴan aiki su yi, shiyasa shi ma baya shigowa sai yaci abinci a gidan su ko gidan su Bello. a ciki ya amsa sallamar da yaji tayi, ta ƙasan idonsa yake kallonta, tana tsaye daga jikin madubi ta maƙale, fuska sam babu annuri. yacca take fushi da shi haka shi ma yake fushi da ita, ranar da ya faɗa mata zai mayar da aure ta ƙona masa rai, yanda ta nuna ko kishinsa ba ta yi, irin ma ba sonsa take ba, kawai da ya faɗa mata ta kalle shi da fara'arta tace Allah ya sanya alkhairi, daga nan taci gaba da harkokin gabanta tamkar ba wadda kishiyarta zata dawo ba, shi kuma wannan nuna rashin kishin nasa ya ba shi haushi har ya ɗauki fushi da ita, kuma ganin bata bi ta kan fushin nasa ba ya ƙara hawa sama. ita kam tun da tayi masa kallo ɗaya ta ɗauke kanta, ba komai take tunawa ba sai ranar da ya sameta a ɗaki tana kuka. ba kamar yacca ya tsammaci kukan nata ba, kuka take yi akan ciwon mara da ya matsa mata kwana biyu, amma buɗar bakinsa a lokacin ce mata yay,"ya fi miki ki koyawa zuciyarki haƙuri da son zama da kishiya akan wannan kukan da kike yi mara amfani, domin kuwa dawo da matata babu fashi, Allah ya halasta min na zauna da irinki har guda huɗu, balle kuma matar da na fara zama da ita kafin ke, ki san da wannan". idonsa kawai ta kalla a lokacin ta san ya faɗa mata hakanne saboda kawai ya ƙuntata mata. ita sai a yanzu ta yarda da batun sauyawar da maza suke yi idan zasu ƙara aure, duk da bata ga yana wani rawar ƙafa ba amma ya sauya fiye da tunaninta, magana wannan bata haɗa su acikin gidan, kuma ba nata laifin bane, nasa ne, don ita ko kaɗan bata ma bari kishinta ya fito ƙarara ba yacca zai gane, tun tana ɗora hakan akan tilasta masa ɗin da akayi har ta daina, ta fahimci zallar bura'uba ce kawai irin ta ɗa namiji, don sosai ya tsiri wa su halaye da bata sansa da su ba, ko zata narke tana masa magana baya tanka mata, ban da jiya da yaci zarafinta. "Jannaty..." ta kira sunansa a hankali, taji ta gaza ƙarashe abin da zata faɗa saboda kukan baƙin ciki da ya taso mata. Turaki yay banza da ita kamar bai ji kiran da tayi masa ba, sai dai still bai bar kallonta ta ƙasan ido ba, yana duban kumbararrun idanuwanta, ga wanda bai sani ba zai ce ciwon ido take yi, but to him da yasan kayarsa ya san uban kuka taci ta ƙoshi har ta godewa Allah. sai ya ɗauke kansa ya sauke ajiyar zuciya, kamar ba zai bi ta kanta ba, sai kuma ya ɗan ji tausayinta a ransa, ya maido da dubansa gareta sannan yace,"ke ba kya gajiya da kuka ne, kin shigo min ɗaki kin min tsaye sai wani faman cin magani kike kina faman ɗaga hanci". Ya ida maganar yana yi mata kallon sama da ƙasa. Cikin sanyin murya ta ce masa,"don Allah kayi haƙuri ka bar ni in yi lallen". ya tamke murya ya ce,"na ce ba za'ai ba". "to ya zan yi da Maama fa?, ita fa ta ban umarni akan in je ayi min". yay ɗan jim kafin ya ce,"fita ne daga gidan nan zuwa gidan mu ba za kiyi shi ba, idan me lallan zata zo nan tayi miki ta zo, idan ba zata zo ba ki haƙura". ta haɗiye ƙullun abu a maƙogoronta na takaici, ta sunkuyar da kanta ta ƙara cewa,"don Allah ka bar ni in koma gidan ku in zauna har a gama biki, don Allah don Annabi". ɗago kansa yay ya bita da kallo, duk tayi sanyi sosai kamar mara lafiya. nazartar yanayinta ya shiga yi, so yake ya gano dalilinta na dagewa akan sai ta koma gidan su har an gama biki sannan ta dawo. yaga ta ƙara kawar da kai gefe tana goge hawaye. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce,"matsayina na mijinki wanda aljannar ki ke ƙarƙashin ƙafata, ina me ba ki umarnin ko nan da parlo kar ki bari ayau, har sai an kawo abokiyar zamanki tukunna". yay maganar cikin muryar ba da umarni. ta dube shi a sanyaye,"yan zu ba zan iya cin alfarmar Maama ba?". tayi maganar cikin wani irin rauni. yan da bai tanka mata ba haka itama bata ƙata cewa komai ba ta fita. tana fita ya ɗauki waya ya kira Maama yace mata wai sun fita ita da shi sai zuwa yamma za su dawo, a faɗawa me ƙunshin sai gobe ayi. ƙarfe bakwai na dare aka kawo Ilham, sai da aka fara kaita gidan su Turaki sannan aka yo da ita gidanta. lokacin da Fillo ta jiyo guɗa sai da zuciyarta tayi wani mugun matsewa, yunwa take ji a lokacin ta ɗauko abinci zata ci, amma lokaci ɗaya taji ta ƙoshi, bata buƙatar komai a wannan lokacin sama da tayi kuka. ɓangaren Ilham kuwa tana can tana shan mugwayen shawarwari, an cika mata kai fal da abubuwan da muddin ta ɗauke su ba zata jima ba Turaki zai ƙara saita mata hanya. wajen ƙarfe takwas da rabi na dare, Fillo ce a ɗakinta tana shirin kwanciya bacci, wayarta tayi ƙara, waƙar da ke tashi wajen ringing ɗin ya shaida mata Turaki ne, hakan yasa bata ko matsa daga inda take ba balle taje ta ɗauka. har sau biyu kiran na shigowa ya katse bata ɗauka ba, tana gama shiryawa ta haye kan gado ta kwanta, ta dunƙule a waje ɗaya, idanuwanta na ta hasko mata yacca Turaki zai kwana tare da wata yau ba ita ba. tayi nisa cikin wata duniya ta daban Turaki ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, ya kunna fitila ya bita da kallo, ƙarasawa yayi gaban dressing mirror da ya hangi wayarta akai, ya ɗauka ya kunna, sai yaga a silent take, hakan ya tabbatar masa da cewa ba da gangan taƙi ɗaga kiran nasa ba. ajiye wayar yayi ya shiga taɓa ƙafarta, tana jinsa amma tayi masa banza, ta rufe idonta kamar me baccin gaske. zama yay a gefen gadon kafin yasa hannu ya yaye blanket ɗin da ta rufa da shi, ya rumtsa idonsa a lokacin da idanuwansa suka sauka akan cikakkun breast ɗin ta da ya kwan biyu bai haɗu da su ba. Fillo ta buɗe ido a lokacin ta zabga masa harara tare da faɗin,"lafiya?". ta faɗa murya a sama kamar ba ita ba. ba tare da ya kalleta ba ya miƙe tsaye, ya zuba hannayensa cikin aljihu sannan yace da ita,"ki sauko ƙasa ki same ni, ina so zan yi magana da ku". taja blanket ɗin ta gyara kwanciyarta kamar bata ji me yace ba. ya juyo yana kallonta,"ba magana nayi miki ba kika koma ki kwanta?, me kike ji da shi ne yanzu?". ta ƙara jan blanket ɗin ta rufe har kanta, yana tsaye yana ta kallonta yana ƙoƙarin sarrafa ɓacin ransa, ya fi ƙarfin minti uku a tsaye Fillo bata ko motsa ba balle yasa ran ma zata tashi ne, ya jijjiga kansa ya fita ransa a mugun ɓace. yana sauka ya tarar Ilham ta shigo a lokacin, tana tafiyar yauƙi ta wuce ta zauna kan kujera, sai kallon parlon take yi tana taɓe baki kamar wacca taga kashi, mamaki take yi sosai har cikin ranta, bata taɓa zaton kaya masu shegen kyau da tsada ba ne aka zubawa Fillo. kusan zata ce kuɗi daidai ne da nata, kuma in har ba son zuciya ba colour ɗin funitures ɗin Fillo sun fi nata kyau sosai ma. sai da aka kwashi kusan mintuna goma kafin Fillo ta sauko, sanye take da hijab har ƙasa, fuskarta wasai kamar bata da damuwar komai, sai ma bacci da ya fara nuna alamarsa a fuskartata. tun da ta taho Ilham ke kallonta idanuwanta kamar za su faɗo ƙasa, zuciyarta tayi mugun bugawa da wani masifar kishi, ta haɗiye yawu da ƙyar a maƙoshinta, dama har haka Fillo ke da azababben kyau bata sani ba?, a yau dai ba zata so zuciyarta ba kam Fillo ta ci uwar ubanta a kyau, kyan nata har tsoro ya bata, yarinyar ta koma kamar ba ita ba, ta ƙara fresh da kyau me matuƙar ɗaukan hankali, sai ƙyalli take yi, ga shi kallo ɗaya zaka yi mata kasan tana ɗauke da ciki, bata san lokacin da wani uban gumi ya wanke mata wuya ba, ta damƙe hannunta a jikin kujerar tana ji kamar ta tashi ta bar parlon. Fillo ta wuce ta kashe tv, sarai ta san Turaki kallon news ɗin yake yi, ya bita da kallo, tun ɗazu yake a hasale da ita, ya lura ta ɗauki salon rashin mutunci, dole zai taka mata burki tun kafin akai ga nisa, don ba zai ɗauki wannan banzan halin ba, har ta dawo ta zauna kusa da shi bai ɗauke idonsa akanta ba, so yake ya karanci ma'anar murmushin da yaga tana yi tun da ta sakko. "i'm sorry Jannaty, haɗewa nayi da shaf'i da wutri shiyasa na ɗan ɓata lokaci, i hope hakan bai ɓata maka rai ba". tayi maganar tana kallon Ilham ta ƙasan ido, wacca ta cika tayi fam tana kallon yacca Fillo ta wani maƙale a kusa da Turaki. Turaki ya sauke numfashi ya dube su gaba ɗayan su, ba tare da ɓata lokaci ba ya shiga yi musu nasiha akan zamantakewar su, ya faɗa musu yacca yake so zaman su ya kasance, ya faɗa musu abubuwan da yake so su kiyaye gudun ɓacin ransa da na su. daga ƙarshe kuma ya tsara yadda kwanakin kowacen su zai kasance, sannan ya ba su damar jin ta bakinsu, Fillo na wasa da yatsun hannunta ta ce,"duk yanda ka yanke Jannaty ni kam yayi min". ya kalli Ilham, wacca ke kallonsa fuskarta na bayyana rashin amincewarta akan hakan, sai da ya ɗaga mata gira ya ce,"ehen, ko kina ciwon baki ne?". ta kawar da kai gefe guda tana cin nagani ta ce,"da dai ka ƙara, kwana biyu sai kace a zamanin da, ko gidan ƙawata kwana huɗu ake yi musu su da suka fi mu jimawa ma kenan". Turaki yay mata mugun kallo kafin ya ce,"to kwana biyun na yanke ba zan ƙara ba, nan gidana ne ba gidan ƙawarki ba ne". ya danne ɓacin ran da ke ingizo shi, ya ci gaba da yi musu nasiha sosai, irin nasihar da kowaccen su sai da taji a zuciyarta, bayan nan yay musu adu'ar zaman lafiya, kafin nan ya rufe taron na su da adu'a. cikin ƙarfin hali Fillo ta danne bala'in abin da ke taso mata ta ce,"Allah ya amsa dukkan adu'oin da kayi mana ranka ya daɗe, insha'Allahu ta ɓangarena ba zaka taɓa samun wata matsala ba, zan kiyaye dukkan abin da baka so, haka zan yi ƙoƙarin aikata duk wani abu da kake so domin farin cikinka, na yi maka alƙawarin hakan muddin numfashina". sai kuma ta kalli Ilham tace,"abokiyar zamana ina yi miki barka da dawowa, ina fatan zamu haɗe kanmu mu zauna lafiya kamar yanda mijinmu ke so, ni dai ta ɓangarena ba ki da damuwa na ɗauke ki tamkar ƴaruwa ta jini. bismillah gaisuwar musulunci". ta faɗi hakan tana miƙawa Ilham hannu don su gaisa, but sai Ilham ɗin taƙi miƙa mata nata, ta yi mata kallon sama da ƙasa tare da jefa mata wani irin wulaƙantaccen kallo. ɗan runtse idanun Fillo tayi tare da yin murmushin takaicin da babu wanda zai fahimta, bata san cewa ita ma ba har zuciyarta ba, yanda bata so ta haɗa hannu da ita haka ita ma, don ko ace ma ta amince su gaisa ɗin cikin dabararta zata aiwatar da abin da zai hana hakan, ai ba don Turaki a wajen ba kallo bata isheta ba. Ilham ta miƙe a zafafe zata fita ta bar parlon Turaki ya dakatar da ita. "ta wurinki zan fara samun matsala kenan ko?". Fillo ta miƙe ta ce,"zan wuce ɗaki, Allah ya bamu alkhairi ya tashe mu lafiya, sai da asuba ranka ya daɗe". tana faɗa ta wuce upstairs cikin natsuwa, Ilham ma ta bar parlon kamar wacca iska ke tunkuɗawa. tun da Fillo ta koma ɗaki taji bacci ya ƙara ƙauracewa idanuwanta, ta gaza danne abin da take ji a zuciyarta don ta samu ta saita kanta, gaba ɗaya zuciyarta a cunkushe take, bata taɓa zaton zafin kishinta ya kai har haka ba sai yanzu, tayi saurin faɗawa toilet tayi alwala tazo ta tayar da sallah. salloli tayi ta jerowa, gani take kamar idan tayi kuskuren sallamewa zata iya yiwa kanta rauni. bayan ta idar tayi zamanta akan dardumar tana tasbihi, lokaci zuwa lokaci sai ta sharce ƙwallar da ke sakko mata.. zuciyarta zafi take yi mata sosai, hatta kanta jinsa take yi tamkar zai rabe gida biyu, gaba ɗaya jin duniyar take babu daɗi sam, wataƙila in ace yau ba zata yi kwanan gidan nan ba da zata iya samun sassaucin raɗaɗin da take ji a zuciyarta. a can ɓangaren Turaki kuwa tun komawarsa ya tarar Ilham ta rufe ƙofa, bai ko bi ta kanta ba ya wuce ɗakinsa, sai dai tun da ya koma zuciyarsa ta gaza yi masa daɗi, tazara!, irin tazarar nan da bai taɓa zaton zata kasance tsakaninsa da Fillo ba, ko da sukai shariyar juna ya kan shiga duk dare yaga sleeping beauty face ɗinta. ya zata ji yau zata kwana a ɓangarenta ita ɗaya ba tare da motsinsa a sashin nata ba?, sai yay shiru kawai tare da rufe idonsa, haka kawai ya ji ya damu sosai akan halin da yasan babu makawa tana cikinsa yanzu. ya san yay mata rashin kyautawa, bai kamata ya shareta ba har ya canja mata ya zamar mata wani kalar mutum na daban da bai raineta akan hakan ba. tabbas tana buƙatar rarrashinsa ko ya ne, tana buƙatar kulawarsa da rarrashinsa a wannan daren ko zata samu bacci, don kamar yanda ya san kayarsa ne daren yau ba lallai ne ta iya bacci ba. wajen sha biyu saura aka turo ƙofar ɗakin a hankali, tun bata ɗago kai ba ƙamshin turarensa ya daki hancinta. ta ɗago domin ganin shigowar ko ta lafiya ce, kallo ɗaya tayi masa ta watsar. kallo ɗayan da tayi masa ya fuskanci tayi kuka ne har ta godewa Allah, don idanuwanta sun yi mugun kumbura, sai kawai ya tsinci kansa da matsanancin tausayinta a ransa. ƙarasa shiga yay, ya zauna a gefen dardumar, ya dinƙa kallonta yana ganin yacca taƙi ɗago ido ma ta kallesa, kenan bata ko ƙaunar ganinsa a yanzu?. kafin ya buɗe baki yay magana yaga ta miƙe, taja dardumar ta jefar da rabin ƙafarsa da ke kai, ta ninke sannan taje ta kashe fitilar ɗakin ta haye saman gado. ji tayi ya biyota kan gadon, tayi saurin miƙewa zaune tana cewa da shi,"ka tashi ka fitar min a ɗaki". ta faɗa murya a karye, yayin da hawaye ke sakkowa saman kuncinta, hawayen

Chapter 66 of 73