ta trying taji ba zata iya rubuta duk wata lamba da taɓa sani ba".
tace,"ƴata na mance lambar kowa da na sa ni, amma naji kina ta ce min Babana da Zaytuna banji kina min maganar Madina da Khalil ba, dan Allah suna ina?".
Fillo ta kasa magana kwata-kwata. Hajiya Ramla ta yunƙura ta miƙe tare da kamo hannunta tace,"yi haƙuri ki daure mu bar wajen nan, idan muka isa titi Allah zai kawo mana mafita". Fillo ta ɗaga kanta kawai.
"mu nufi gabas insha'Allahu sa'a ce zata fitar da mu".
Fillo ta daure da ɗan sauran kuzarin da ta-ke da shi suka ci gaba da gudu, sanda suka fara hango titi dai-dai lokacin ne kuma mota ta shigo layin da wani mahaukacin gudu irin tuƙin ƴan wiwi, tsoro yasa su kasa kaucewa gaban motar, haka ma Aliyu dake driving rikicewa yasa shi rasa yanda zaiyi, ganin motar tayo kansu gadangadan babu ta yanda zasu kuɓuta Fillo ta ture Hajiya Ramla daga kusa da ita, dai-dai lokacin kuma Aliyu yabi ta kan Fillo ta gangara gefe ɗaya.
cikin tsananin tashin hankali, ɗimauta da gigita Hajiya Ramla ta ƙwala ihu tana ɗora hannu akanta ta kurma salati, kafin tayi kan Fillo a guje tana ɗagota zuwa jikinta, ganin uban jinin dake zuba yasa ta fashewa da matsanancin kuka tana ƙara ambaton innalillahi.
Aliyu ya fito daga mota a hargitse yana furta,"innalillahi wa'inna ilahi raji'un".
Inna Wuro ma ta fito daga bayan motar ta taho da sauri tana faɗin,"shikenan ka shiga uku kai ɗaya Aliyu dan ban dani wallahi, yanzu ai kaga amfani jin maganata ni da kake ɗauka a watse, tuƙin mutuwar da nake hanaka kana maida ni gantalalla kana ƙara wani akai ga shi nan yau yaja maka masifa ka bige aljanu".
tayo wajen da Aliyu ke tsaye ya rasa abinyi, jinin dake zuba jikin Fillo ya rikitar da shi tashin hankalinsa ɗaya kar ace ya kashe rai.
ya zaro wayarsa a aljihu ya kira wayar Ammi, tana ɗagawa cikin dauriya da ƙarfin hali irin namiji yace,"Ammi ki fito na kaɗe wata yarinya, kuma kamar ta mutu Ammi".
Hajiya Ramla kuwa sai kuka take yi tana jijjiga Fillo akan ta tashi, Inna Wuro ta ƙaraso wajen da Hajiya Ramla ke zube a ƙasa da Fillo akan cinyarta, ta tsaya daga ɗan baya tace,"bayin Allah aljanu kuyi haƙuri dan Allah, ni wallahi babu ruwana, saukata kenan daga saudiya ko awa ɗaya banyi ba, aka tura wannan gantalallan yaron yaje ɗauko ni, alhalin tuntuni na faɗawa ubansa ya daina aika shi taho da ni tunda baida hankali, to da yake dai nayi rashin sa'ar haihuwar ɗa me jin maganata sai ta ƴaƴansa, in gaya miki sarauniyar aljanu tun daga iya fat Aliyu yake fafara wannan tuƙin mutuwar da ni, ina ta roƙarsa Allah Annabi ya tsaya yaƙi tsayawa saurarena saima ƙara wani da yake yi, yanzun ma ina ta ce masa zai buge mutane yaƙi jina ashe da rabon manyan zai shafce, rashin jin maganata yasa ya buge ƴar sarkin aljanu dan ba tsautsayi bane yana sane, dan haka wallahi kuyi masa duk abunda kuga dama baida kirki ko kaɗan, ko ƙafarsa ce ma ku shanye ta yanda zai daina tuƙa motar, kuyi haƙuri aljanu ni dai banda laifin komai Aliyu ne ku kumbura masa ciki wallahi tunda ya kashe muku ƴarku".
duk wannan maganar da take idonta rufe yake, sai yanzu ta ɗan buɗe ɗayan kaɗan tana kallon Mum, ita tsakaninta da Allah ta-ke maganarta aljanu suka bige, saboda yanda taga yalwataccen gashin Mum har kusa da ɗawawu, ga shi duk da uban dafewar da tayi hakan bai sa tsananin hasken fatar da ta-ke da shi ya dusashe duka ba, hakanne ya ƙara tsorata sosai ta-ke zaton aljanu ne musamman da taga dare ne yanzu, mai lafiya dai ba zai fito a yanda suke ɗin nan ba duka babu ɗankwali gasu a hargitse kamar sababbun kamu.
ta durƙusa a ƙasa tana yin alamar roƙo tace,"me girma aljana kiyi haƙuri ki daina tunanin yanke hukunci da ni, ki sunkuci ƴarki ku ɓace kuyi nahiyarku dan Allah. idan kuma ba za ki haƙura ba wallahi na goyi da bayanki kici uban Aliyu dan ko kaɗan baida mutumci, ga gidansu can ubansu shine ɗana ni na haife shi da cikina, amma ba kiga yanda ake wulaƙanta ni ba a gidan, matansa biyu ɗaya me mutunci ɗaya watsatstsiya, amma duk su ɗin sai suka haifi gantalallun yara ba kiga yanda suke bani wahala ba wallahi har kuka sai kin yi min idan kinga a yanda nake zaune a gidan, ni kuma kamar mayya na kasa barin gidan saboda duk cikin yarana gidan Amadu ne kaɗai kullum ake shan shayi da ƙwai da naman ganda da safe, sauran gidajen ƴaƴan ko daga ɗumame sai koko babu ko sikari aciki, to ba zan mutu a wahala ba na dawo gidan Amadu ake ban kayan daɗi ana gani min azaba".
Mum ta ɗago jajayen idonta tana kallon Inna Wuro, hakan yasa Inna Wuro zabura taga da baya tana faɗin,"wa'innahu min sulaimana wa'innahu bissimillahir Rahmanir Rahim".
Mum na kuka sosai tace,"yanzu ba zaku taimaka min ba sai na rasa ƴata?".
Inna Wuro na adu'a a bakinta tace,"ku kuwa kuna da taurin kai mutanen ɓoye, kawai kiyi siddabarunku ta tashi shine har sai anje asibiti salon dai aja kuɗin ɗana Amadu, kuma na faɗa miki indai Aliyu ne ku tafi da shi can nahiyar taku kawai kuci ubansa wallahi, ƴaƴan Amadu da yawa ba shi ɗaya ya haifa ba".
Mum na kuka ta kalli Aliyu da duk yake a ruɗe, shima tsoron ya fara kama shi yana ganin kamar ta bakin Inna Wuro aljanun ne.
adu'a kawai yake yana ƙara kiran wayar Mum da bata ɗagawa, Hajiya Ramla ta miƙe ta sunkuci Fillo da ƙyar zata goyata a lokacin ne Daddy da Ammi da me gadi suka iso wajen cike da tashin hankali.
Aliyu yace,"ban san garin ya ba Daddy, nayi ƙoƙarin ƙwacewa na kasa".
Daddy ya ɗago yayi masa wani kallo, sannan ya doka masa uwar tsawa yace,"dan uwarka baka da hankalin da zaka iya ɗaukarsu zuwa asibiti ne da har sai ka kira?, ko baka ga jinin dake zuba daga jikin yarinyar bane shashashan banza, comon zo karɓeta ku sata cikin mota".
Aliyu ya taho cikin mutuwar jiki suka kama Fillo shi da me gadi suka saka a mota.
cikin hanzari Daddy ya shiga driver seat sannan Ammi ma ta shiga gaban motar, Aliyu da Mum kuma sauka zauna da Fillo a baya, Daddy nata bawa Mum ɗin haƙuri, Ammi dai ta kasa cewa komai dan duk a ruɗe ta-ke.
Daddy yace,"kiyi haƙuri Hajiya ki daina kukan kiyi mata adu'a, insha'Allahu matsalar ba babba bace".
Inna Wuro ta ƙwanƙwasa glass tace da Daddy,"buɗen bus ina kwaso kayan jaririyar Yusuf da na yo mata tsarabarsu, datsada na siyo dubu shi biyar duk guda ɗaya".
Daddy yace,"kiyi haƙuri mu dawo tukunna kinga a condition ɗin da yarinyar nan ta-ke kar jininta ya ƙare".
ta zabga salati tace,"Amadu yanzu har ƴar sarkin aljanu ta fini matsayi a wurinka, saboda kana tare da aljanu ba zaka iya jin maganata ba, to kaje ni dai ba abinda zance wallah sai dai Allah ya saka min".
Daddy ya fito ya ɗauko jakar kayanta ya dire mata. ta kalli me gadi tace,"ɗaukar min muje, ni dai ba inda zan bisu, waye yake taimakar wasu aljanu, rabon ai su girgiza motar tasu akan titi ne suyi haɗari, in ko haka ta faru babu uban da zanyi jinya, suna gani aljanar da ta shiga jikin Yusuf akan son ɗaya daga cikinsu irin baƙar wuyar da suke ba shi. ɗazu ma ina bakin ka'aba har yana ce min wai in yi masa adu'a aga yarinyar nan da ta ɓata, kai baka ji ba kamar zai yi kuka da yana maganar, ni ko nace wallahi ba zan ba sai dai nayi adu'a Allah yasa su fofa daga jikinka".
Mum dai kuka kawai take yi har suka isa asibiti, suna isa Daddy ya kira Yusuf sai ga shi kuwa cikin hanzari ya ƙaraso, Allah yasa yana night duty, nan da nan aka shiga da Fillo Emergency room.
*A dai-dai wannan lokacin.*
Turaki na zaune acikin motar Dsp ya kifa kansa akan stearing, wayarsa dake aljihu ta shiga ringing cikin sauri yasa hannu ya ɗauko da dukkan fatansa daga gida ne za'a ce masa Fillo taje. sai dai ganin akasin lambar da yake tunani sai yaƙi ɗagawa ya aje lambar a gefe, kiran ya ƙara shigowa bayan katsewar na farko, cikin ransa yana tunanin me zai sa wannan me kiran ya kirawosa at this time.
kamar ya sha re sai kuma ɗayan ɓarin zuciyarsa yace ya ɗaga, yana ɗagawa kuma daga ɓangaren Dr Yusuf yace da shi.
"idan ba damuwa kuzo asibiti da gaggawa ga yarinyarku an kawo mana ita emergency, accident ɗin ma har yafi na da muni, jinin da ta ke buqata this time around yana da yawa, so please cikin gaggawa muna buƙatar kuzo".
ai babu wani batun ƙarashen jin abinda Dr Yusuf ke faɗa ya wurgar da wayar akan kujerar me zaman banza, ya duba jikin motar yaga da key ajiki dan haka ƙofa kawai ya janyo ya rufe yaja motar a 360 yana jin kamar ya ɗauki motar ya dire a cikin asibitin.
*_Ayi haƙuri jiya banda lafiya wallahi sosai, yau ɗinma ƙarfin hali nayi._
*Vote, share and comments.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_Avoid typing errors._
*36*
Allah kaɗai ya kaisa lafiya zuwa Asibitin Miyetti saboda irin mahaukacin gudun da yake yi, yana isa asibitin direct office ɗin Dr Yusuf ya faɗa, yanda yake a matuƙar rikice haka shima Dr Yusuf ɗin yake.
yana ta aikin sauke numfashin yake kallon Dr Yusuf idonsa tamkar zai faɗo yace,"tana ina Dr?, a wanne hali ta-ke ciki?".
Dr Yusuf yaja dogon numfashi ya sauke, ya rufe idonsa for a while sannan ya buɗe ya sauke su akan Turaki yace,"an shiga da ita situation room, and she is in critical condition, wanda yake da kamar wuya...".
"da kamar wuya me?". Turaki ya faɗa cikin ɗaga murya a sanda Dr Yusuf yay shiru da maganar da yake, ya zagayo ta gabansa a firgice yana daɗa cewa,"kaci gaba da min bayani Dr, da kamar wuya me?".
Dr Yusuf ya kalli gefe guda tsananin damuwarsa da tashin hankalinsa na ƙara bayyanuwa yace,"da kamar wuya ta rayu".
Turaki get in to a state of shocked, looking at Dr Yusuf with anxiety, like he did'nt understand what he said, ya buɗe baki zai yi magana Dr Yusuf ya dafa kafaɗarsa yace,"abinda yake nan shi nake sanar maka, bance ba zata rayu ba, but da kamar wuya tayi rai".
cikin wani bala'in tashin hankalin da yafi na ɓarawon da aka kama Turaki ya damƙe hannun Dr, sai kuma a hankali kuma cikin mutuwar jiki yace,"Dan Allah Dr ta rayu, na roƙe ka dan Allah, ko menene kayi dan ta rayu ni kuma nayi maka alƙawarin duk abinda ka biɗa daga gare ni muddin bai fi ƙarfina ba zan baka, amma dan darajan Allah karka bari ta mutu".
yanda yayi maganar dole yay mugu mugun baka tausayi.
Dr Yusuf yace,"Allah ne kaɗai me rayawa da kashewa, zamu yi iya kar bakin ƙoƙarinmu wajen ganin mun ceto ranta, saboda gaskiya akwai matsala babba ma kuwa".
Jikin Turaki ya ƙara mutuwa, yaji zuciyarsa na wani irin motsawa yana jin kamar ya mutu ya huta. yace,"wacce matsalace da har zata fi ƙarfin ku Dr?".
Dr Yusuf yace,"a binciken da muka yi akwai abinda ya gigitata ya kuma ɗimautata da har yaja a lokaci ɗaya zuciyarta ta taɓu, kuma ta kai ga matakin ƙarshe na stage d, yana zama da wuya akai wannan matakin kaga an rayu sai dai kuma wani iko na ubangiji. yanzu fatan da zamu yi guda ɗaya shine in har Allah yasa ta farka to karta farka da tunanin wannan abin da ya girgizata ya haddasa taɓa zuciyarta a lokaci ɗaya, idan har hakan kuma ta kasance to tabbas farkarkawarta bugawar zuciyarta gaba ɗaya, daga nan kuma shikenan tata ta ƙare".
ƙwayar idon Turaki ta kaɗai, yaja da baya ya tafi yana neman madafa saboda jinsa da yake yana neman yanke jiki ya faɗi, yay saurin dafe bango yana kifa kansa ajikin bangon yana jin jikinsa gaba ɗaya ya ɗau shaking.
bai san me yake ji ba, bai san ta yanda zai kwantata yanda yake ji ba, haka bai san halin da yake ƙoƙarin shiga ba.
Dr Yusuf yayo tattaki yazo kusa da shi ya tsaya tare da dafa kafaɗarsa yace,"yanzu taimako guda ɗaya ta-ke da buƙata a wurin mu shine jini...".
tun bai ƙarasa bayaninsa ba Turaki ya damƙi hannunsa suka nufi hanyar fita, cikin gaggawa suka fito a tare suka nufa situation room ɗin da Fillo ta-ke.
tana kwance kamar gawa, kallo ɗaya Turaki yayi mata ya kasa dauriyar riƙe hawayen dake cikin idonsa, kawai ya sake su suka sauko, kamar ba namiji ba, kamar ba jarumi ba, hawaye yake sosai kuma masu zafin gaske waɗanda yake jin zafinsu tamkar zasu ƙona fatarsa, gwargwadon irin zafin da yake ji a zuciyarsa wadda shima yake jin tana gab da taɓuwa.
yasa hannu kamar ƙaramin yaro ya shiga goge hawayen sannan ya kwanta akan gadon da Dr Yusuf ya nuna masa, muryarsa ta fito da wani amon sauti da ba nasa ba yace,"in har da buƙata a kwashe duka jinina a saka mata".
Dr Yusuf yay guntun murmushi ganin kamar Turaki ya zauce, yaji tausayinsa matuƙa kamar yanda shima yake tausayin kansa. kuma nan da nan akayi connecting jinin Turaki zuwa jikin Fillo.
tun jonawar ya juyar da fuskarsa zuwa kan gadon da ta-ke, lokacin an samu gogge jinin duk da ya ɓata mata jiki, kallonta yake tayi yana mai matuƙar tausayinta a cikin ransa, yana kuma lissafin cewar da zarar ta farka komai na wahalarta yazo ƙarshe, zai zamar mata bango kuma jigo na madafarta.
har tsawon awannin da jinin ya ɗauka yana fita daga jikinsa ya shiga jikinta bai ɗauke idonsa akanta ba.
da ƙyar kuma ya yarda ya fito daga situation room ɗin yabi bayan nurse ɗin da tazo tai disconnecting abin shigar jinin daga jikinsa.
yabi bayanta zuwa office din Dr Yusuf, ya same shi zaune akan kujerarsa ya riƙe kansa da duka hannu biyu, wanda kallo ɗaya zaka yi masa kasan cewar yana cikin matsananciyar damuwa.
Turaki ya ƙaraso ciki jiki a saɓule jiri na ɗibarsa, ya nemi waje ya zauna sannan ya ɗauki maltina ɗin da nurse ta ajiye masa akan table ya fasa ya shanye.
ya ɗora idonsa akan Dr Yusuf yana me cike da taraddin jin abinda zai fito daga bakinsa.
Dr Yusuf ya furzar da iska daga bakinsa sannan yace,"zamu jira nan da 30mints muga abinda Allah zai yi".
"insha'Allahu ma lafiya zata tashi".
daga nan kowannensu sai ya ɗauki wayarsa ya shiga kiran lambar da ya nema a contact list, daga ɓangaren Dr Yusuf matarsa Nuratu ta ɗaga kiran tana sallama acikin muryar bacci.
ya kalla agogon hannunsa yaga ƙarfe biyu da rabi na dare a lokacin, a sanyaye yace da ita,"Farha har tayi bacci ne?". tace,"ban sa ni ba wallahi, na barta tare da Mommi na shigo ɗaki saboda kaina da ke ciwo, your Excellency ni dai gobe zuwa zanyi na nemo mata maganin kuka gaskiya".
yay guntun murmushi yace,"ba wani magani da za'a bata, kowanne jariri ai yana kuka dama". Nuratu na noticing yanayin voice ɗin nasa tace,"ehh amma nata kukan yayi yawa". sannan ta daɗa cewa,"your excellency lafiya kuwa naji muryanka so sad?".
yace,"lafiya lau". ba don ta yarda da cewarsa ba tace,"as early morning zaka dawo ko?".
yace,"ehhh may be". tace,"Inna Wuro ma fa ta dawo, daga saukarta ta biyo ta nan wai anan zata kwana can gidan aljanu sun shiga, sai surutai ta-ke wai Aliyu ya kaɗe aljanu sun tafi da shi zasu ɗauki fansa, fatan ta Allah yasa kar su kashe shi tunda ya kashe ƴar sarkin aljanu, da gaske ne yay accident ɗin?".
yace,"Allah ya gyara Inna Wuro, yanzu kina jina?, zan aiko driver ya ɗauke ku, sai ku shirya ku taho tare da Mommi".
tace,"ni dama from your voice na gane babu lafiya, meke faruwa Dr?, kar dai da gaske Inna Wuro ta ke yi".
jin duk tabi ta rikice yace,"relax, yarinyar bata mutu ba ai. akan maganar da nayi miki kwanaki ne".
tace,"wai Dr nah kana ganin hakanne kuwa?".
yace,"i pray so hakan ta faru, na gwada jinin yarinyar ɗaya yake dana Mommi, Swty sai dai kinzo xaki ga abinda nake faɗa miki, dan Allah kuyi da sauri ina so ku ƙaraso before yarinyar ta farka. kuma karku taho da Inna Wuro tazo ta ishi patients da zance, ki bar mata Farha itama kar taita kuka".
daga haka ya katse wayar yana kallon Turaki dake yiwa Maama bayani.
"ban san ya akai ba Maama, asibiti sun kira ni kawai, yanzu haka har an sanya mata jini likitan kuma yace zata farka nan da 30minutes".
daga ɓangaren Hajiya Madina tayi magana sannan ya ƙara cewa,"ehh naga Dsp nata kirana amma ban ɗaga ba". tace,"tom gamu nan Me Babban suna, plss take care". yace,"Maama kizo da sauri dan Allah".
ya kashe wayar ya saka a aljihu tare da miƙewa ya fita daga office ɗin ba tare da yace da Dr Yusuf komai ba.
Fitar tasa babu jimawa Dr Yusuf ma ya biyo bayansa. inda ya same shi tsaye a bakin ƙofar room ɗin da Fillo ke ciki yana leƙenta ta cikin wani glass.
daidai da ƙarasowar Daddy da Ammi wajen, Yusuf ya isa wajensu yana kallon Aliyu da ce masa,"Malami ka kwantar da hankalinka, kayi adu'a kawai Allah yasa ta farka". Aliyu ya sauke numfashi yana komawa da baya ya zauna kan kujera.
Yusuf yace da su Daddy,"na fito ai tun ɗazu ban ganku ba".
Ammi tace,"gida muka koma, da dukkan alama mutanen acikin tashin hankali suke, dan sai bayan zuwanmu da muka shigo cikin haske naga alamar hakan a tare da mahaifiyar yarinyar, ashe ko ɗankwali ma babu a jikinta, haka ma sarƙa ce ɗaure da hannunta. shine naga babu dacewar mu tsaya da ita a haka tunda mutane kowa na wucewa, dalilin da yasa muka koma gida kenan".
Yusuf yace,"Ammi wannan matar fa ba mahaifiyar yarinyar bace, ni har na fara ɗaukar maganar Inna Wuro fa, saboda ita wannan yarinyar ta taɓa kwanciya a asibitin nan, tana da matsalar aljanu da suke yawan ɗaukarta su kaita wani wajen, shi yasa nafi tunanin nima ko aljanar tata ce ta fito a siffar mutane".
Daddy yace,"a'a wannan matar mutum ce, kun riga kun san baiwar da Allah yay min, da naga aljani na san shine. ta bakin nata dai tace wasu mutanene suka sace su shine suka samu suka gudu".
Yusuf ya sauke nunfashi yace,"ofcourse an kidnapping yarinyar in ban manta ba 1month kenan".
Ammi ta nemi wuri kusa da Aliyu ta zauna, bayan ta dube shi da tausayawa ta kalli Yusuf tace,"ya jikin yarinyar?". yace"da sauƙi, nan da mintuna kaɗan ma zata farka".
Daddy yace,"mun biya ta station sun kwance sarƙar hannun matar, da ƙyar suka yarda da mu akan hakan dan tunanin su ma wai ko me laifi ce ta gudu, to amma duk da haka sun haɗo mu da police ɗaya sannan sun shigar da report wai should incase. yanzu please kasa nurse ko kuma kai da kanka kayi ƙoƙarin mata treating hannunta, tsintsiyar hannun duk ya farfashe yay caɓa-caɓa da jini wallahi, abin tausayi".
ya juya yana kallon Ammi yace,"tana ina?".
tace,"gata can wajen corrido ɗin can tana sallah, naga hankalinta duk yaƙi kwanciya, ni tausayi ma ta-ke ban wallahi".
Dr Yusuf ya kira wata nurse, yayi mata nuni da inda Mum ke zauna yace ta ɗau kayan aiki taje wajenta. ba ɓata lokaci Nurse ɗin kuwa tai treatment duk inda wani ciwo yake ajikin Mum, dauriya irin ta babba shi kaɗai ya hanata yin kuka, dan sosai take jin zafi da raɗaɗi, har aka gama ƙwayar idonta na kallon gefe ɗaya, sai bayan an gama tukunna ta ɗago tana kallon duka hannayen da aka ɗaure wajen bandage kaɗan ba mai yawa ba.
a lokacin Turaki ya bar jikin ƙofar ya shiga kaiwa da komowa a wajen hannayensa sarƙe a bayansa, idonsa ya kai bayan Mum da har yanzu ke zaune bata tashi daga wurin da tayi sallah ba, adu'a kawai take akan Allah ya tashi kafaɗun Fillo, har ga Allah tana so ta nemi ahalinta a wannan lokacin to amma ba zata iya ba har sai Fillo ta farka, yarinyar ta taimaka mata a lokacin da take neman taimako.
duk da bayanta yake kallo haka yayi tsaye sai kallonta yake ya kasa ko da motsi, ya kuma kasa ɗauke idonsa akanta, yana jin wani irin abu na shigarsa, yana jin kamar yana so yaga ko wace, gaba ɗaya bai san dai taƙamemen abinda yake ji a tare da shi ba.
yay ajiyar zuciya ya juya ya koma bakin ƙofar, yaci gaba da kallon Fillo yana ta adu'a cikin ransa, bini-bini sai ya kalli agogo ya duba time, cikar lokacin da likita ya ɗiba kawai yake jira, da dukkan fatansa na in lokaci ya cika ta farka lafiya lau. sai dai haka ɗaya kuma yaji totally ya kasa samun nutsuwa, zuciyarsa na masa wani irin zillo, tunaninsa da hankalinsa ya rabu waje biyu, so yake yaci gaba da tsayuwa anan har sanda Fillo zata farka, haka kuma so yake ya bar wajen yaje wajen waccan matar da bai san wacece ba.
ba tare da sani ba ya bar wajen ya nufa wurin da Mum ke zaune har yanzu, ya tsuguna ta gefenta daga ɗan bayanta, ba tare da sanin taƙaimemen abinda zai yi ba, idan ma magana zai mata shi bai san me zaice mata ba, zuciyarsa ce kawai ta kawo shi.
ya buɗe bakinsa zai furta abinda bai san zaice ba sai ga Ammi ta ƙaraso wajen, bai iya ce mata komai ba ya bita da kallo har ta zagaya ta gaban Mum ta tsuguna agabanta.
Ammi tace,"kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki Hajiya, Ɗana ya tabbatar min da cewar ƴarki zata farka cikin amincewar ubangiji, kuma zata farka lafiya lau insha'Allah".
a sannan Mum ta ɗago da kanta tace,"Allah ya amsa, amma Hajiya lokaci yaja da yawa, har yanzu fa shiru".
tai maganar muryarta ɗauke da sautin damuwa.
Ammi ta ƙara cewa,"adu'a zamu ci gaba da yi". Mum bata iya magana ba illa gyaɗa kanta kawai da tayi. bata san me take ji a tare da ita ba, amma dai tana jin zuciyarta na ƙara matsuwa da zullumin son kasancewa acikin ahalinta, ba abinda idanuwanta ke da muradi yanzu sama da su ga Babanta, taga ƴaƴanta tukunna ta sami kwanciyar hankali.
Umma ta ƙaraso wajen, Ammi ta ɗauke kanta daga kallonta, Umma bata kula hakan ba tace,"Ammin Yara wannan itace mahaifiyar yarinyar da Aliyu ya buge ɗin?". Ammi ta kauda fuska gefe tace,"umm ita ce". ta faɗa tana miƙewa ta bar wajen, Umma ta zagaya ta ɗaya ɓarin ta zauna kusa da Mum, suka gaisa tana yi mata adua da sanar mata cewar itama mahaifiya ce wurin yaron da ya bigesu ɗin.
Mum tace,"Allah sarki, mun gode sosai. kun tsaya mana baku bari mun wahala ba".
Umma tace,"to ai hakan ya zama dole akan wanda yasan hakkin bawa".
ta faɗa idonta na kan Turaki da har sannan yake tsugune daga can gefe, kamar wani mutum mutumi sai bin kowa yake da ido, shi abinda ya ɗaure masa kai tun zuwan Ammi wajen yaji tana batun mahaifiyar Fillo, shi yasa yaji kamar ƙafafunsa ma ba zasu iya ɗagawa ba dan haka kawai yaji jikinsa duk yay sanyi, kuma Allah Allah yake yaga fuskar matar.
ganin tsananin kamar dake tsakanin Turaki da Mum wanda Ammi bata lura da hakan ba yasa Umma ce masa,"sannu fa, ya mai jiki?".
Turaki yaji kamar ba da shi take ba, lura da hakan yasa Umma cewa,"da kai nake". ta faɗa tana murmushi.
yana sauke idonsa a ƙasa yace,"Alhamdulillah".
tace,"to Allah ya bada lafiya, dan Allah ina daɗa bayar da haƙuri a madadin yarona".
shi dai bai iya cewa komai ba, ya zama kamar wani soko ko me neman gafara. kuma Umman na yin shiru ta hango Nuratu da Mommi na nufo su, har da Inna Wuro dake goye da Farha.
itace a gaba ta taho tana cewa da Umma,"Falmata ni dai Amadu ya rantse yace min ba aljanu ba ne mutanene shisa ma na iya shigowa asibitin nan amma da a waje zan tsaya gaskiya, dan ban iya saka kaina a masifa, Aliyun ma ni da wurin ƴan sanda aka kaishi tunda ance har yanzu yarinyar bata farka ba, ko kawai ayi kotu da ɗan banza kowa kuma sai yay ta kansa kar aja kuɗin Amadu ya ƙare".
Umma ta miƙe tana cewa,"sannu da zuwa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 38 Chapter of 73