dai kamar matacciya, baccinta kawai take yi. Turaki still holding her hands da ɗayan hannun kuma yana shafa lips ɗinta yake ta kallon lumsassun idanunta, zai iya rantsewa bai san time ɗin da wani fitinannan murmushi ya ƙwace masa a fuska ba, ya lumshe idanu tare da ƙoƙarin kai lips ɗinsa saman nata trying to kiss her sai kawai yaji zuciyarsa na faɗa masa,"not now, not today, but one day, in that special night, the night that will come not once, but for your entire life".
ya rumtse idonsa sosai tare da jan wani wawiyan ajiyar zuciya ya sauke, ya ɗago kansa yana kwantar kansa a pillow, ita kuma ya daɗa gyara mata kwaciyarta ajikinsa tare da jan blanket ya rufesu, sai shafa gashin kanta yake yi, duk shafa ɗaya sai yaji zuciyarsa ta buga, haka har ɓarawon bacci ya ɗauke shi.
sai gab da asuba Turaki ya farka, yana tashi yay alwala yay raka'atanil fajr sannan ya wuce masallaci saboda ya makara, ko da ya dawo masallaci side ɗin Maama ya wuce, ya shiga bedroom nata ya sameta ta idar da sallah tana lazimi, anan ya zauna har ta idar suka shafa aduan tare, lokacin 6 har tayi.
gabanta ya zauna ta ɗora hannunta saman kansa, ta dinƙa jero adu'oi tana tofa masa tana hawaye, har sanda ta ɗauki kusan minti 7 a haka sannan ta ƙarashe da faɗin,"Allah ya kai mun ku lafiya ya dawo da ku lafiya, Allah ya tsare min kai, dan Allah ka riƙe ibadarka, kar kayi wasa da azkar da adu'a. Bello yace ƙilan zaku iya kaiwa har 7days, but bana jin hakan zai yiwu, in ya wuce 4days ɗin ko ka taho ko na biyoku, Allah ya tsareku".
Turaki ya amsa da amin yana me ɗago da kansa, ganinta tana hawaye hankalinsa yay mugun tashi. "Maama lafiya?, menene?, in ba kya so naje na haƙura kawai, Bello zai iya komai shi ɗaya and beside zai sami Sameer acan".
ta girgiza masa kai da cewar,"a'a ku tafi tare, Sameer ai ya dawo jiya, yace yaje room ɗinka time kayi bacci".
Turaki ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya rungumo Maama shima hawayen na sakko masa, ya tsani tafiyar nan da zai yi sam baya son yaje, dan ba shi da yanda zai yi tunda Maama tace yaje ɗin, amma ji yake kamar in yafi wani abun zai faru, kamar tafiyar tasa zai sa ya rasa ɓarin jikinsa.
Fillo dai da asuban bayan fitar Turaki masallaci ba daɗewa ta tashi, taga ita kaɗai ce a ɗakin, cikin ranta ta ƙara yabon kyan hali irin na Turaki, watakam bai ma iya kwana the same room da ita ba, ta sauko a gadon tana tafiya a hankali saɗaf saɗaf saboda har sannan tsoron daren jiya bai barta ba, abinda ta fara tunawa ma kenan da ta buɗe idonta, maciji a compound da kuma bakin gate, yo ita kuwa me zai sake tsayar da ita a wannan wurin, ai har mutuwa.
a rufe taji ƙofan sanda taje buɗewa, ta ɓata fuska ta dawo ciki ta shiga toilet tayi alwala ta fito, tana idar da sallah ana ɗauke wuta, hakan yasa a sukwane ta koma kan gadon ta kwanta tana ƙudundunewa tana adu'a a fili, har bacci ya ɗauketa.
Turaki ya turo ƙofan ɗakin ya shigo, darduman sallah kawai ya kalla ya shaida tayi sallah ta koma ta kwanta, a yanayin kwanciyar kuma yasan tsoron jiya dai har yanzu bai barta ba.
kayansa ya cire ya shiga yay wanka, komai a hankali yake yinsa gudun kar ya tasheta, 7:30am ya gama shiryawa cikin ƙananun kaya da bai cika sasu ba, ya ɗauka brief case daidai nan Zaytuna ta shigo ɗakin.
duk da ita tasan Fillo matar Turaki ce hakan bai hanata jin kunya ba da ta shigo ta tarar da shi yana kissing forehead ɗinta. sai ta tsaya ɗaga bakin ƙofan tace,"B Ƙaraye yazo". ta faɗa tana murmushi.
ya ƙaraso gabanta ya kama kumatunta yace,"ki zage ki dinƙa faɗar sunansa Bello, dan shi gatsal yake faɗar Zaytun a gabana". tasa hannu ta rufe fuska tace,"ai ni baya faɗa a gabana".
Turaki yay murmushi yay mata side hug yace,"ki kula min da kanku, mussaman waccen fitinanniyar, dan Allah kisa ido akanta sosai kin riga dai kin san bata ji, sanya kai a hatsari shi yafi komai sauƙi a wurinta. ki faɗawa Kaka zata dawo wajenki da zama for some days dan na riga na tsoratata ba lallai ne take iya zaryan zuwa side ɗinsu da nan ba. ki sa ido akan fitarta, bata son cin abinci, bata son shan magani, na baki amanarta na baki amanar Maama na kuma baki amanar kanki, just 4days zanyi in dawo".
ya ƙarasa faɗa Zaytuna ta rungume shi.
cikin kukan da take yi tace masa,"jiya nayi mafarki Mum ta dawo, ta dawo hannunta da ƙafarta duk ciwo". ya kwantar da kanta a ƙirjinsa yana shafa bayanta yace,"ta kusa dawowa da izinin Allah, ina dawowa zamu nemota ni da Fulani". a sanyaye tace,"Hammah bana tunanin Mum na raye". yace,"yaro ma na riga babba mutuwa, so shekaru ba sune mutuwar mutum ba, gamu da Maama har yanzu a raye, kisa a ranki Mum ta kusa dawowa garemu da ranta da lafiyarta, zan faɗawa Fulani issue ɗin da zarar na dawo".
kiran wayar Bello da ya shigo a karo na kusan huɗu yasa shi sakinta yana waiga yana daɗa kallon Fillo. ji yake kamar kar ya tafi, ya kama hannun Zaytun suka fita yana faɗa mata,"idan kinje wurin Kaka ki ɗauko cream ɗin da ta ke shafawa ki jefar, i don't think wanda kika saya ranar nan take shafawa".
Zaytuna tace,"tayi haske sosai ko?, nayi zaton ma wanda na sayo mata ne so after na tambayeta tace min bata fara using da shi ba, tana shafa wani da aka kawo musu, Kaka ta hanata buɗe sabon wai almubazzaranci, but zanje ɗin sai na ɗauke".
suka fito compound ɗin Bello dai na tsaye sai hararsa yake, Turaki ma ya hararesa ya ƙarasa wurin Maama, sallama dai kamar kar ai tafiyar, kuma kamar wannan ne karo na farko da zai fara tafiya, Nihal ma ta dage cewar ita dai zata bisa, yace sunyi late ai da tun jiya ta faɗa masa sai a anso tictiket har ita, Samha ma ta riƙesa tana faɗin kawai ba sai ya tafi ba ita bata so yana nisa da su, Hajiya Madina ta zabga mata harara tana me jin wani ɗaci da baƙin ciki na kasancewar Samha ƴarta.
Ilham kam da ta kwana a gidan tana riƙe da hannun Boɗejo tana goge hawaye. Boɗejo tace,"ni wallahi duk kun saka jikina yayi sanyi, tafiya sai kace yau zai fara, ko saboda kawai ya jima bai yi nesa daku ba?. fisabilillahi irin wannan sallamar da kuke yi ai ta masu bankwana da juna ce, irin fa wannan sallamar akeyi idan mutum zai mutu. to ni dai gaskiya idan tafiyar nan bata zama dole ba ke Madina sai kisa shi ya haƙura".
ta kalla Hajiya Madina taga tana goge hawaye tace,"ka ga wani ƙarin tsinkar da zuciya kuma".
Turaki dai yana tsaye jikinsa duk yay sanyi, shima ji yake kamar idan ya tafi ba zai dawo ba, sai kallon side ɗinsu yake yi, kamar zai ga Fillo ta leƙo ta window, kamar zata leƙo suyi sallama. ya sauke ajiyar zuciya ya kira sunan Ilham, ta ɗago tana goge hawaye ta tafi zuwa gabansa, ya ɗauke hannunta daga fuskarta yana sa handky ɗinsa ya goge mata fuskar, a hankali yace,"kukan mene?".
tace,"nace zan bika tun jiya". yay murmushi yace,"4days fa kawai zanyi na dawo". ya faɗa yana ɗago kai ya kalla Nihal yace,"auta zo". tazo itama nata hawayen na sauka a lokacin.
yace,"ku shiga kuyi min rakiya to".
Boɗejo tace,"kaga in ɗaukowa Ilham mayafinta ku tafi tare kawai, ni bana son kuka yana ɗaga min hankali".
Khalil wanda zai driving nasu yace,"Allah babu da wadda zan tafi da ita, ina sauke su nima da inda zanje".
Boɗejo na hararsa tace,"kana kama da mutanen kirki amma ba haka kake ba, in motar kai ka saya sai ka hanasu shiga ai".
Khalil dai ya tubure babu me binsa, har sai da Hajiya Madina tasa baki, amma hakan bai sa ya yarda sun tafi da kowa ba.
ƙarfe tara Fillo ta tashi, ta tashi a firgice tana bin ɗakin da kallo, ta sauko daga kan gadon da sauri tana rarrabawa idanuwa. har yanzu babu alamar ya shigo, to taya zata fita daga ɗakin alhalin yasa key?.
tana ta ɓata rai ta shiga gyara ɗakin, tana gyaran gado taci karo da farar takarda a ninke, ta ɗauke ta aje kan side drower sai kuma taji tana buƙatar buɗewa, bata san ba ko yana da alaƙa da mugwayen mutanencen.
ta zauna gefen gadon ta warware takardan, farkon abinda ya fara burgeta handwritting ɗin jiki, sai kuma zanen heart da peppern ke ɗauke da shi. sannan tabi rubutun da kallo tana karantawa acikin yaran fulatancin da aka rubuta.
_Nisa tsakanin zuƙata biyu ba ya nufin shinge fa ce tuna kyakykyawar alaƙa dake tsakani...ƙwarai akwai wanda yake ƙaunarki kwatankwacin yadda makaho ke buƙatar ido, fiye da yadda kurma ke buƙatar ji, fiye da yadda gurgu ke buƙatar ƙafa, Dai-dai da yadda mara lafiya ke buƙatar lafiya, cikin ƙanƙanen lokaci yana jin kin zama rayuwarsa gaba ɗaya, kula da kanki shine mafi abinda yafi so daga gareki kiyi masa a sanda yay nisa dake, amana!, amana!, amanar kanki a tafin hannunki daga gare shi._
haka siddan Ilham ta faɗo cikin zuciyarta a sanda ta gama karantawa, ba wai don ta santa ba ko tasan matsayinta, tana hasko hoton yanda ta same su jiya a ɗakin Boɗejo. ta taɓe baki ta miƙe tana jefar da takardar a ƙasa, tabi ta kanta ta wuce ta gyara kan table ɗin dake hargitse da takardunsa, tana gyaran ɗakin tana kumbura ba tare da sanin dalili ba, kuma har ta gama gyaran bata bi ta kan gadon da ta soma gyarawa ba, saboda haka ɗaya taji gyarasa baida wani amfani duk da ita ta kwanta akai.
tana riƙe da kwanukan abinci a hannunta taji an turo ƙofar ɗakin an shigo, idonta ya manne akan Ilham dake shigowa kamar wacca ƙwai ya fashe mata a ciki, fuskarta duk hawaye, ta shigo ba ko sallama ta wuce ta gaban Fillo ta faɗa kan gado tana ɗauko pillow ta rungume a ƙirjinta.
wani abu da Fillo bata san ko menene ba ya tokare mata a maƙoshi, tasa kai ta fice a ɗakin da sauri.
_ba fa kwa yin comment, kar kusa nai zuciya na dire typing ɗin._
*vote, comment and share.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_Avoid error mistakes._
*31*
wani abu da Fillo ke ji akan Ilham ya tsaya mata a ƙirji kamar ƙurji, har ta baro upstairs ɗin wani irin ɗaci take ji a tare da ita da bata san dalilinsa ba.
lokacin da ta fito compound zata wuce ɓangarensu ta tarar ana rage flowers ɗin gidan, wajen duk yay kaca-kaca, tausayin masu aikin cirewar da gyara wurin ya kamata, neman halal da wuya, kuma a haka namiji ke fita yasha wahala ya kawo macen da bata arziƙi ba tayi masa ɗiban albarka, ta girgiza kai tana me jin tausayin kowanne namiji acikin ranta amma banda Hayyo mahaifinta.
sai da taje gab da shiga gate ɗin nasu kawai maganar macijin jiya ta dawo sabuwa acikin kanta, take kuma tsananin tsoro ya rufeta ganin wani reshe na flower da aka sare wada yay kama da jikin macijin, ba shiri ta kurma uban ihu tana duƙewa a wajen sai kururuwa take, da sauri masu aikin suka yo kanta suna tambayar lafiya, dai-dai nan Khalil ya ƙaraso wajen shima yana duƙawa gabanta da tambayar lafiya.
cikin kukan da take tace,"maciji ne". with suprise kowa ya ƙara maimaita abinda tace,"maciji kuma?". ta ɗaga kanta jikinta sai rawa yake yi. nan da nan masu aikin suka shiga laluben wajen, Khalil kuma yace ta tashi sai ta girgiza masa kanta tace,"ba zan iya ba".
yace,"kin gurɗe ne?". ta ƙara girgiza masa kai ba tare da tace komai ba.
yana murmushi yace,"daure ki tashi babu komai anan, macijin ai ya tafi ga shi can sun kashe shi".
tun ɗazu da ta duƙe sai a yanzu ta ɗago da kanta tana rarraba idanuwa, yacca take yi ɗin ba ƙaramin bawa Khalil dariya tayi ba. bai kasa riƙe dariyarsa ba ya saki yana ce mata,"tashi na raka ki". ya faɗa saboda yanda yaga duk ta firgice, firgicewar da ba zata iya tafiya ita ɗaya ba.
ta miƙe da ƙyar sai ƙanƙame ƙafarta da jikinta takeyi, ya wuce gaba yana cewa,"muje".
idonta ya sauka cikin compound ɗin nasu, maganar Turaki ta cewar ai wadda ma macijin ya maƙale mata mutuwa tayi, sai taji inaa ba zata taɓa iya shiga ɓangarensu ba, tana jin ma kamar sai dai Kaka ta dawo nan itama. ba shiri taja da baya tace da Khalil,"Hammah Khalil ba nan zani ba ɗakinmu zan wuce".
tana tafe tana ɗage ƙafafu haka ya rakata har ƙofar ɗakinsu, zaune ta sami Ɗausiyya na gyaran zogale, ganin Fillo yasa Ɗausiyyan ƙyalƙyalewa da dariya tace,"matsoraciyar kawai". Fillo na hararta tace,"tsoro ai halal ne, kuma tsoron me kika kalla nayi".
Ɗausiyya tace,"ai ina kallonki sanda kika zube, har nayo wajen naji ana batun maciji babu shiri nayo reverse".
Fillo na ƙara harararta sanda take zama kan gadonsu tace,"ashe kema matsoraciyar ce".
Ɗausiyya tayi dariya tukunna tace,"2days kina makarar shigowa".
Fillo na kwanciya kan gadon tace,"wani lalataccen barci nake fama da shi 2days ɗin, in kuma kina da magani sammani".
tai maganar tana jin jikinta a saɓule, yanayinta duk babu daɗi kamar wani abu na shirin faruwa mara kyau.
Ɗausiyya tace,"aiko dai ki nemi magani. ɗazu da Hammah Babba zai wuce yana cewa da Adda Zaytuna wai in yaje can wurin da zai je zai sayo mata maganin daina bacci, da kina nan kema da kin faɗa masa tunda naga yana da kirki, kawai dai baida sakin fuska, jiya ma 2k ya ban".
lokaci ɗaya Fillo taji allon ƙirjinta ya girgiza, Turaki ya tafi?, when is he coming back?, tare da Bello suka tafi, ta ya zai iya kula da kansa?, ya tafi da maganinsa?.
tarin tambayoyin da suka zowa cikin kanta kenan a lokacin, ga shi babu ɗaya da take da amsarta, dan haka ido kawai ta lumshe kamar me bacci, tana jin Ɗausiyya nata magana amma bata jin zata iya buɗe baki ta amsa mata saboda faɗuwar gaban da take ji, wani irin yanayi da bata taɓa jin kanta aciki ba, like kamar dai something bad will happen soon.
bayan kwana biyu aka kawo akwatin sa ranar auren Fillo daga gidan su Amir, Innarsa da wasu Anties nasa guda biyu na ɓangaren mahaifi sune suka kawo, akwaiti guda ɗaya da atamfa 4 aciki sai less da zai kai 6k guda biyu, shadda ɗaya da material guda ɗaya, da fashion na yari da sarƙa guda biyu sai takalmi da jaka duk guda ɗaya, sai kuma hijabs har ƙasa guda biyar da 5k a haɗe, akasa ranar aure wata biyu masu zuwa.
kaya dai masha'Allah sunyi kyau sosai gwanin san barka, kowa ya gani sai ya yaba, haka akaita zuwa ana gani ana tafiya da masha'Allah, su Yami kam baki har kunne jikarsu tayi goshi.
sai dai fa duk wannan bidiri da akeyi Fillo bata ko ga tayar akwatin ba balle kayan da suke ciki, dan ƙememe tun ranar da Turaki ya tafi ta kasa zuwa ɓangarensu tsaboda bala'in tsoron dake ranta, kayan sawarta ma sai Maijidda ce ta kawo mata tace musu wai jarabawa za'ai musu, kwana suke suna karatu ita da Ɗausiyya shisa.
farko dai a tsorace take da zuwan, to amma da aka kawo kayan sai tsoro ya haɗe da kunya shisa ta kasa ko da zuwa, idan taje bata san taya zata fara haɗa ido da mutane ba, tasan kuma halin Maijidda zata sata a gaba ne da aikin zolaya, dama tun washe gari ma tazo tana mata lissafin abubuwan da zasu yi da biki, ita dai har ta ƙaraci surutunta bata ce mata ƙala ba, Maijidda ma da haushi ya cikata ta karɓi wayar Yami da ta zo amsa tai wucewarta da cewar bata ƙara zuwa, ita zata je tayi nata shirin ita ɗaya.
tun ranar da aka kawo kayan Amir ke ta doka mata kira akan zai zo, tai masa godiyar kaya har yake tambayarta ko sunyi, tace masa sunyi tunda har Maijidda ta faɗa dan ita bata je ta gani ba. Amir dai juyin duniya yazo yaga Fillo sam taƙi, idan tayi kamar tace masa yazo sai taji inaa a dai yi auren tukunna, ai haka taji Turaki yace duk masu yin zance a gidan, shisa ga ƙannensa nan cikinsu babu wadda ke yin zance ashe dalilin kenan, Amir tun yana lallashi da roƙo da ƴar murya Fillo dai taƙi yarda da zuwansa, har yay fushi ma washe garin ranar gaba ɗaya bai kirata ba, kuma sai sauƙi yazo mata ranar Yami ta aiko Maijidda ta karɓar mata wayarta.
kuma da Hajiya Madina tayi mata batun me yasa bata zuwa wurin Kaka sai tai mata ƙaryar ai tayi tafiya ne, sai dai fa a wannan kwanaki biyun Fillo tayi muguwar rama, tun daga kan fuskarta har jikinta, na farko tsoro ya hanata sukuni, na biyu kuma kewar Kaka duk ta addabeta.
ɓangaren Amir dai da yaga ba zai iya da azabtuwar rashin ganin Fillo ba ya kwaso ƙafa yazo gidan, ya sanarwa me gadi cewar wurin Hajiya Madina yazo saboda ya sami damar shiga cikin gidan kai tsaye, ta yanda zai zaƙulo Fillo a duk inda take ya fito da ita, shi ba zai iya da rashin ganinta ba, yana ƙara kwana bai sata a idonsa ba tsab zai iya rasa ransa. Mai gadi ya sanar ma da Hajiya Madina, akayi masa iso zuwa parlon baƙi, taje ta same shi suka gaisa, zatonta ma ko masu buƙatar taimako ne amma sai taji yana mata bayanin wurin Halima yazo.
kusan minti guda Hajiya Madina ta ɗauka tana kallonsa cike da nazarinsa, tare da kuma mamaki matuƙa akan batun wurin wacca yazo, ashe yanda take tunanin Fillo ba haka take ba?. tashi tai tana ce masa ya jira yanzu zata zo, aka kawo masa ruwa da snacks da kuma juice na pineapple, kayan dai na aje kan table ɗin dake gabansa yana kallonsu amma ya kasa ko taɓa ruwan, bini bini sai ya duba agogon hannunsa, shiru shiru Fillo bata fito ba wucewar mintina goma da tafiyar Hajiya Madina, a ransa sai ya fara tunanin kamar ko ba zata zo ba ne, kuma kamar Hajiyar ce ba zata barta ba, sai yaji ransa yay mugun ɓaci.
ɓangaren Fillo kuwa suna can suna aikin suyar wainar shinkafa Baffa zai yi baƙi, suna faɗansu ita da Ɗausiyya kan ita Ɗausiyya na cika mai a suyar, ita kuma Fillo na zuba kaɗan, faɗan dai ya tashi akan kowacce ta sakawa ƴar uwarta ido, Zaytuna da Nihal kuma na gefe suna haɗa miyar agusi da ganda, suna jinsu suna yi musu dariya.
Nihal ta waigo ɗauke da dariya a fuskarta tana kallon Ɗausiyya tace,"ke fa kece aikinki baya kyau, mai idan yay yawa a abinci baya daɗi Ɗausiyya kuma kin san dai akwai masu ulcer".
Fillo na kallon Ɗausiyya tai dariya tace,"ah tou kin dai ji, in kuma man kike so ai sai ki bari in tazo ƙarshe ki soya taki da duka galand ɗin, lafiyarki ai ba lafiyar wani ba".
Ɗausiyya ta galla mata harara ta ɗauki waina guda ɗaya acikin wacca Fillon ta soya ta wuce wurin Nihal tana faɗin,"Adda Nihal kalla fa ki gani, abu ƙamas ai sai taja mana magana ace muna da maƙon mai alhalin akwai wadatarsa". ta buɗe cikin wainar tana ƙara faɗin,"ji fa aba a bushe kamar ba'a saka komai ba, yanzu dan Allah cikin abokan Baffa wani ya kai bakinsa ai direta zai yi dan wannan dai ba zata ciyu ba Allah".
Nihal na taɓa wainar tace,"gaskiya kuma fa haka ne, mutane da basa rasa abin faɗa sai su tafi suna cewa Baffa baya wadata gidansa da isassan man abinci".
Ɗausiyya ta kalla yanda Fillo ta cika tai fam tace,"ah tou, dan haka ki zuba mai isashshe kiyi suya Malama, in yaso kyayi tsumulmularsa a gidanki babu ruwan koya, ƙarƙari kijawa mijinki magana wurin abokai da dangina a tafi ana yi da ke biki iya girki ba".
tai ƙarashen maganar tana dariya. Fillo tace,"ko ba komai dai mijina yace ina da tattali, ke kuwa kullum sai kinsha masifa akan haukar almubazzaranci da kike masa".
Zaytuna tai dariya sosai. Nihal da bata fiya shigowa kitchen ɗin ba tace,"haka kuke aikin dama kamar kaji?".
har sannan dariya bai ɗauke akan fuskar Zaytuna ba tace,"kika biye su ba abinda zai hana bakinki yagewa, dan kamin barinki kitchen ɗinn sai kin ji wani complain ɗin na daban".
dai-dai nan Hajiya Madina ta shigo, duk suka yi shiru, ta dubi Zaytuna da Nihal tace,"sannunku da aiki". suka amsa da yauwa, tace da su,"where is Samha?". Nihal tace,"na ga ƙawarta tazo ɗazu sun fita".
Maama bata tace komai ba ta maida kallonta ga Fillo tace,"meet me in my room". ta faɗi hakan tana juyawa ta fita.
Fillo ta miƙe tana wanke hannu a sink, taiwa Ɗausiyya gwalo tace,"kuma ai aiki me kyau in ba haka ba ran mutum ya ɓaci". ta faɗa tana mata gwalo sannan ta fice daga room ɗin.
tun da ta shiga room ɗin Hajiya Madina taga yanayin fuskarta sai jikinta yay sanyi, ta ƙarasa shigowa ta zauna a ƙasa tana fuskantarta, duk lokacin da taga fuskar Maama ahaka tasan to da matsala,so farkon abinda yazo cikin kanta shine Turaki, 4days dama taji Zaytuna na faɗin zai yi, ga shi yau har kwana 5, lafiya?, meke faruwa?, ko kuma yana kan hanya?.
rashin sanin amsa yasa ta ɗago kai da sauri ta kalli Hajiya Madina da ke ta kallonta ta kasa cewa komai. murya a hankali tace,"Maama lafiya?, Hamman har yau bai dawo ba".
Hajiya Madina ta sauke numfashi tace,"zasu taho jiya sai Baffa ya tura su El-Salvador zasu yi signing wani contract da wani kamfanin fulawa acan, jibi insha'Allahu zasu sauka".
Fillo tace,"Allah ya kaimu ya dawo da su lafiya".
ta faɗa kanta na ƙasa. Hajiya Madina na studying nata tace,"kunyi da wani zai zo wurinki ne?".
tambayar taji ta a wani iri, hakan yasa tai saurin ɗago kai tana kallon Maaman, kan tai magana Hajiya Madina ta jefa mata tambayar,"Amir yazo wajena yace min yana son ganinki. waye shi?, aina ku ka haɗu?, dama can ya sanki ne?, da yaushe kika fita har ya ganki ya biyo sawunki?".
Fillo ta sadda kanta ƙasa tana wasa da fingers dinta tace,"wanda zan aura ne, amma wallahi ba muyi da shi cewar zai zo ba yau".
with Astonishment Maama tace,"wanda za ki aura Fillo, asin how?".
Fillo ta kwashe duk bayanin komai har kayan sa ranar da aka kawo ta faɗawa Hajiya Madina. ita dai kallonta kawai take tana ganin kamar yarinyar ƙarya take yi, ƙarama da ita haka age of 17 going to 18 ace za'ai mata aure?, tasan cewar su ƴan ƙauye ne da basu fiya bawa rayuwar ƴa mace muhimmanci akan yanda zamanin yanzu ke tafiya ba, amma bata taɓa tsammanin za'a iya aurar da yarinyar nan kusa ba kasancewarta me ƙaramin jiki sosai, in ba sani ma kayi ba zaka iya rantsewa ba 18 zata shiga ba.
dalilin da yasa tun a ranar da yarinyar ta kwanta mata a rai ba tayi hanzarin shigar da tata buƙatar garesu ba kenan, kiwon Fillo da take yi tanadi ne take taiwa ɗanta Muhammad Turaki, ashe har wasu sun mata shigar sauri, wani ya riga ɗanta, wani daban zai mallaki kamilar yarinya me natsuwa da hankalin da irinta ke da wuyar samu, ba ɗanta Muhammad Turaki ba, wani daban can. yanzu wa zata ƙara kama masa?, har cikin ranta bata ji daɗin wannan batun ba sam, to amma ya zata yi, shirinta da lissafinta daban ne, hakama yanda ubangiji ya shirya lamarinsa daban, kuma na ubangiji shine dai-dai, kuma dama ita kullum adu'arta alkhairi take nema.
dan haka yanzu adu'a ta rage mata akan Allah yaywa Turaki da Khalil zaɓin mace mafi alkhairi a gare su. ta sauke numfashi tana daɗa kallon Fillo tace,"amma Fillo me yasa baki faɗan ansa ranar aurenki ba na fara shiri?, ko haka kike so na kaiki?, ko kin manta nace ke ƴata ce?". ta faɗa cike da zolaya, Fillo kanta na ƙasa bata iya cewa komai ba saboda kunyar da ta kamata.
Hajiya Madina ta miƙe ta isa wadrobe ta buɗe ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 30 Chapter of 73