Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
karta soma ta ambaci sunanta idan Kaka ta nemi ba'asin karɓan kayan Dr Yusuf. ai tasan an hanasu shine yana miƙowa ta amshe. Maijidda na ɗan jin tsoro tace,"to ni ai nai zaton da gaske alluran ne shiyasa na karɓa". Fillo na dariya tace,"kinga ke dai kije kisha faɗanki ke ɗaya, ni na tafi aiki. da nasha faɗan Kaka gwara na sha na Hajiya Madina". tana faɗa ta ƙara saurin tafiyarta tana taiwa Maijidda dariya, ita kuma nata jin shakkar shiga da kayan, ji take kamar ta koma taga idan Dr Yusuf bai tafi ba ta basa kayansa, to amma tasan zuwa yanzu ya tafi kam, dan ko ɓata lokacin da suka yi a wurin duba kayan tasan yaje inda zai je. tun shigowarsu gate Fillo ta dage sai sun wuce inda ake zubar da bolar gidan sun zubar da maganun, wanda zatonsu abinda ya faɗa hakan yake. kuma sai da suka je zasu zubar ne suka tsaya suna kallon uban kayan da mamaki. leda ɗaya tulin kayan ƙwalama ne kamar hauka, madara, snacks da choculates da lemukan kwali, tarkace dai iri-iri. sai ɗayan ledan kuma kayan makeup ne aciki, shower gel manyan roba guda biyu wanda mutum sai yafi wata yana wanka da roba, sai lotions da su powder, duka dai dangin kayan kwalliya, kuma da gani kuɗi ne ba na wasa ba aka kashe wajen sayayyar. Fillo ta shiga parlon da sallama tana tafiya a hankali, kanta a ƙasa sai jan yatsun hannunta take yi, Hajiya Madina na zaune akan kujera, ƙafafunta duka biyu akan tum-tum, Sameer na zaune a gaban ƙafafun nata ya tankwashe ƙafa yana yanke mata farcen ƙafarta. sai Nihal dake ɗaya kujeran a zaune tana duba wata handout, daga dining area kuma Zaytuna ce a zaune tana danna waya. Fillo ta ƙarasa ta durƙusa a gefen kujera tana gaida Hajiya Madina. Hajiya Madina ta ɗauke idonta daga karanta story book ɗin da take yi ta kalli Fillo tana amsa gaisuwar tata. "Halimatu anji sauƙi kenan". tace,"ehh Maama na wartsake gaba ɗaya". "to masha'Allahu, Allah ƙara miki lafiya. kina da ƙwarin dai da zaki iya aiki ko?". Fillo tace,"ehh Maama". Hajiya Madina ta gyaɗa kanta, tai shiru for some seconds sannan tace. "to jiya an kawo miki ƴar'uwa da zaku ke aikin tare, ta kammala komai tun ɗazu, yanzu sai ki tashi kije lesson teacher ɗin ku yazo, idan kuka kammala ke sai kiyi aikin rana". wani daɗi ya mamaye Fillo, ko babu komai burinta na yin karatun boko zai cika, abunda mahaifinsu ya kasa yi musu yau wasu bayin Allah zasu mata shi. tunaninta ya tafi can wani lokaci baya, tana wannan tunanin taji Hajiya Madina na ƙara cewa,"dan Allah ku mayar da hankali kunji ko, abunda za'a muku a makaranta shi zai muku, kuɗi masu yawa aka biyasa, akwai percentage ɗin da za'a ke cirewa a cikin kuɗin aikinku, so idan kun mayar da hankali akan karatun kanku kuka taimaka, idan kuma kunƙi kunwa kanku asara babba". Fillo tace,"insha'Allahu Mama zamu mayar da hankali, insha'Allah ba zan baku kunya ba zanyi abinda kuke so nayi". Hajiya Madina ta jinjina kanta. a lokacin sabuwar maid ɗin da aka kawo ta iso wurin ta tsuguna kusa da inda Fillo take. tace,"Hajiya gani". Maama tace,"yauwa ga ƴar'uwar aikin naki nan. ki bata nata reading materials ɗin da Zaytuna ta baki ɗazu, sai kuyi maza ku wuce me karatun na can na jiranku, awa biyu zaku dinƙa yi, da zarar kun kammala ku yo cikin gida, a kama kai bana son shashashancin banza if not zan sallami yarinya". duka su biyun suka amsa da,"to". sannan Fillo tace,"aina zamu sami Malamin?". Nihal tace,"ku tashi muje let me escort you". ta faɗa tana gyara zaman glasses ɗinta, da gyara dogon wandon dake jikinta. "je ki ɗauko littafan naku". ta faɗa tana nuna Ɗausiyya ɗaya ƴar aikin. da ganinta tana da hanzari akan yin abu, dan cikin sauri ta ɗauko ta dawo, kuma kallo ɗaya zaka mata zaka san she is typical ƴar ƙauye, balle kuma ka kai ka ga kallon the way take abubuwanta, maganarta duka hi da ha ne, jiya ana kawota Hajiya Madina tasa Baba Jummai dake kawo mata ƴan aiki ta kaita saloon aka wanko dattin kanta, kuma suna dawowa tasa tai wanka me kyau da dettol da turaren ƙamshi. haka Hajiya Madina take, bata nuna ƙyama ko ƙyanƙyami ga duk yaran da ake kawo mata, karɓarsu take ta nuna musu hanyar gyara kawai. Nihal na gaba suna biye da ita a baya, zasu fita daga falon Zaytuna ta kira sunan Fillo, ta waigo tana kallonta bayan ta amsa kiran. ta mayarwa da Zaytuna murmushin da take yi mata. "i wish you all the best in your studies dear". abinda Zaytuna tace mata kenan, kuma kamar yanda bata fahimci me tace ba haka itama Zaytunan ta fahimci bata san abinda tace mata ba. Zaytuna ta ƙara mata wani murmushin tace,"ina yi miki fatan alkhairi a karatunki, Allah ya bada sa'a". kan Fillo na ƙasa tace,"amin ya Allah, na gode Adda". da haka tabi bayan su Nihal da suka riga suka fice. awa biyu suka ɗauka suna karatun kafin su gama, kuma sosai Fillo ta gane duk abinda aka koya musu ɗin, karatun ya mata daɗi fiye da yanda ta tsammata, ashe shima karatun boko haka yake da daɗi?, shi kansa teacher ɗin nasu sai da ya mata kyautar biro, har yana tambayarta ko ba yanzu ta fara ɗaukar darasi ba, dan ko da ya basu class work guda biyu ta faɗi a examples ɗin da ya ce su bayar, rubutun ta kuwa baka ce wacce ke koyo ba, Ɗausiyya ce yay ta fama da ita, to itama kuma da yake tana da kishi sai da tai ƙoƙarin iyawar. teacher ɗin nasu ba bahaushe bane, amma yana jin hausa sai dai bata kama bakinsa sosai ba. yay da hausa ya haɗe da turanci, su gane hausar da yake yi su bagarar da turancin nasa, idan ya faɗi wani abin da hausa Fillo har gimtse dariyar dake taho mata take yi. dan da ace ita da Maijidda ne ma sai sun saki kayarsu. suna komawa sallah kawai sukai sannan suka fito suka shiga kitchen, suna aikin Fillo na bitar karatunta, ɗan gutun turancin da brain ɗinta ta haddace sai maimaita shi take a zuciyarta, idan ta faɗesa a fili kuma sai taji maganarta wani banbarakwai sai tayi dariya, haka kawai Amir ya faɗo mata a lokacin, idan yay mata turanci sai yace ta faɗi abinda yace sai ta kasa, yace zata iya tace ita kunya take ji tasan ba zai yi daɗi a bakinta ba irin yanda yake daɗi a nasa bakin, sai kuma ta tuna abinda ya faru tsakaninsu a ɗazu, tai saurin watsi da tunaninsa tana jin zuciyarta na zafi. Zaytuna ce ta taya su Fried rice ɗin da basu iya ba, sun maida hankali sosai wajen ganin yanda ake yi, duk abinda ta ɗauko na vegetable zata faɗa musu sunansa da amfaninsa da kuma yacca ake sawa, babu jimawa suka kammala Fried rice ɗin. suna aikin Ɗausiyya ke tambayarta,"Anty kuma sai ku iya cin abinda muka saka hannu?". Zaytuna tai murmushi tace,"Hammah ne kawai baya cin abinda ƴan aiki suka dafa, amma mu kam muna cin duk abinda ƴar aiki ta dafa muddin ta kula da irin tsaftar da muke so, kema baki ga yau fes dake kika fito ba, kuma ina kallonki duk abinda kike yi cikin tsabta kike yinsa...yanzu ma kalle ki tsab, to tsabta ita ke sawa aci girkin mutum, duk daɗin girkin mutum idan baida tsabta sai dai yaci kayansa shi ɗaya". Zaytuna da Ɗausiyya suka ɗauka tray suka fita da shi, suka bar Fillo da ƙarasa haɗa kunun shinkafar da Samha tace tana so tasha. ta fasa madarar gwangwani ta ruwa kenan sai taji kamar mutum a bayanta, ta waigo ta ga Turaki ne tsaye hannayensa a aljihu yana kallon abinda take preparing, da alama ma ba shigowarsa kenan ba. sai ta nemi ta dirirce, ta durƙusa a gabansa da sauri tana gaishe shi, ita bata san me yasa ba amma duk sanda ta gansa sai ta tsorata. bai amsa mata ba ya wuce ya ɗauki cup ya dawo, tana nan durƙushen har lokacin, da wani irin voice tace da shi. "kana buƙatar wani abu ne?". ya kalleta amma ba ita yake kallo ba hannayenta yake kallo, yace. "tashi". ta miƙe tana ɗan matsawa daga kusa da shi. fuskarsa a ɗaure yace,"what is this?". ta so fahimtar abinda yace, amma hakan bai samu ba, jin tai shiru ya waigo ya dubeta, tana tsaye kamar gunki duk ta cika da tsoronsa, hannun nan sai karkarwa yake, shi kuma abin na basa takaici. yaja guntun tsaki ya ƙara cewa,"i am asking you, what is this that you are making?". yanda yay maganar murya a sama yasa ta fara ƙoƙarin hargitsewa, ta ƙanƙame hannayenta a jikinta tare da kulle idonta, shin har sai yaushe zai fara fahimtar wannan yaren ita kam bata jinsa, ita kuwa ko ba dan komai ba ai dole ta tsaya ta mayar da hankali akan wannan gatan da Hajiya Madina tai musu ta koyi turanci. ji take kamar tayi kuka, bata ko ƙaunar tana aiki a kitchen ya shigo, ko ba'a kitchen ba bata so tana aiki taga giftawarsa, ita haɗuwa ma da shi totally bata so. Turaki ya tsaya yana kallon ikon Allah, shi kam ba dan ba dan ba, da sai yace yarinyar nan bata sahun mutane sai dai wata halittar. karkawarwa take kamar wadda ruwan sanyi yaywa mugun duka, ko kuma wacce iskar fanka ke kaɗawa. sai ya ajiye cup ɗin hannunsa kawai ya rungume hannunsa a ƙirji, ya jingina da jikin drower ɗin yana ta kallon sarautar Allah, ba zai ƙara magana ba balle motsi har sai ta gaji dan kanta ta dawo cikin hayyacinta, sannan zai buɗi baki ya faɗa mata karta ƙara ganinsa ta tsorata tunda shi ba dodo ba ne. lokacin da ya tsareta da tambaya a asibiti ya haska acikin kansa da cikin idonsa, wannan lokacin da ya riƙe hannayenta dan hana su rawar da suke yi, amma still basu daina ba sai ma rawar hannun nata ya haɗe har da nasa, tambayarta yay kawai me ya kaita wannan wajen, amma yanda tabi ta ruɗe ta nemi ta firgice har sai da yasa ɗaya hannunsa ya riƙeta da kyau, dan kamar zata faɗo ne daga kan gadon. _"me ya kai ki wannan wurin a wancan ranar?"_ tambayar da yay mata kenan amma kamar ya tuhumeta ne akan me yasa tai kisan kai. sai da ya matse hannunta da ƙarfi sannan ta buɗe ido ta kalle shi hawaye na sakko mata tace masa,_"ina?"_ harara kawai ya galla mata a lokacin, kafin yace,_"wurin da kika je za ki kashe kanki"._ sai kawai ta shiga girgiza masa kai, cikin rawar murya tace,_"Allah ba kashe kaina naje yi ba, ai babu kyau mutum ya kashe kansa"._ taji yay shiru bai yi magana ba, sai ta buɗe idonta dake rufe ta sauke a kansa, ƙwayar idonta ta shiga nasa, taji wani abu da bata taɓa jinsa ba, taga ya ɗaga mata gira duka biyun yana cewa,_"ummm ina jinki, to wa kika je kashewa?"._, saura kaɗan yay dariya saboda yacca ta ƙara ruɗewa da tambayar tasa, har tana ja da baya wanda inda ba'a kan gadon take ba tsab zata arta da gudu. ƙoƙari take ta zare hannunta a cikin nasa tana girgiza kanta cikin tashin hankalin da ya rufeta farat ɗaya. hawaye ne sosai yake sakko mata a sanda take ce masa,_"Allah babu wanda naje kashewa, me yasa zan kashe wani, akan me?, ko cinnaka bana iya kashewa ka tambayi Kaka kaji, dan Allah kayi haƙuri kar ƴan sanda suji su kamani"._ tai shiru tana fashewa da kuka, har sannan bai ɗauke idonsa daga kanta ba, ganin kallon da yake mata yasa tace,_"na rantse da Allah babu wanda naje kashewa, nima gani na kawai nayi a wajen, ban san ya akayi naje ba, kuma ina ta neman hanyar gida na rasa"._ ya ƙara damƙe hannunta sannan yace,_"har lokacin da ya kaɗeki baki sani ba?"._ ba tare da ta kallesa ba tace,_"na sani, ina ta ɗaga masa hannu bai ganni ba kawai sai ya bige ni"._ numfashi ya sauke yace,_"to kin yafe masa ko kin barsa da Allah?"._ sai da ta ɗago ta ɗan kallesa tukunna tace,_"na yafe masa"._ ya ƙara sauke numfashi sannan yace,_"to aljanun naki da suka kai ki su nawa ne?, dama suna yawo dake ko ranar su ka fara?"_ a wannan lokacin kawai tsaida idonta tayi akan kafaɗunsa, ta girgiza masa kai tace,_"banda aljanu ai, ni banda aljanu, ko Malami za'a kira a tambaya"._ yace,_"wanne Malamin?"._ tace,_"Malamin Ruƙiyya"_. yana kallon yanda take kallon ƙirjinsa kamar me karantar wani abu a wajen, sai da ya kalli wajen yaga babu komai kawai dai ba zata iya kallonsa ba shine take kallon wajen. sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya saki hannayenta ya miƙe ya fita daga ɗakin ba tare da yayi musu sallama ba. a yanzu da yake kallonta sai yake ganin kamar a wancan lokacin, har yanzu yana mamakin me ya kaita wajen, me taje yi?, abu ɗaya kawai zai yarda da shi tana da aljannu kuma su suka kaita, abunda kowa ya faɗa kenan. to ya yarda da wannan, amma wannan tsoron nata fa?, shi jininsa babu tsoro a cikinsa, saboda haka ya kamata wannan tsoron nata ya ragu tunda har jininsa na yawo a jikinta yanzu. ya rumtse ido yana tuna the first abunda likitoci suka faɗa sanda suka isa hospital, _"ta zubar da jini da yawa, jini take buƙata a halin yanzu, cikin gaggawa ba da ƙurewar lokaci ba"._ haka suka faɗa a sannan, kuma ba zai iya cewa ga wanda ya nuna masa hanyar laboratory ba, tsintar kansa kawai yayi a wurin, ba tare da kowa ya sa ni ba. abunda ya tsana a rayuwarsa shine ɓata lokaci da kuma dogon bayani, kuma abinda ya sani jininsa AB+ ne, to don me kuma sai an tsaya wani ɓata lokacin gwadawa?, dan haka dawowa kawai yayi ya kama hannun Zaytuna suka faɗa room ɗin da aka kwantar da Fillo. _"ki saka mata jinina, ko leda nawa ake buƙata, ko da za'a kwashe shi duka"._ kayan aiki a ajiye suke to jiran me za tai?, dan haka kwanciya kawai yay akan gado tayi jone-jonen da zata yi, nan take jininsa ya fara shiga jikin Fillo. daga fara shigar jinin bai kuma sanin me ya faru ba, farkawa kawai yayi yaga wani yayi replacing nasa akan gadon, Dr Yusuf, likitan da shima yay kyautar nasa jinin wa yarinyar. sai daga baya Zaytuna ke masa bayanin ai ance shima yana buƙatar ya huta ne dalilin da yasa aka cire nasa kenan, dama leda 1 da rabi ake buƙata, Dr Yusuf ya bada rabin. Turaki ya numfasa yay tattaki ya ƙarasa gaban Fillo dake tsaye har yanzu bata buɗe idonta ba, wataƙila tana jira ne taji ya fita daga kitchen ɗin sannan sai ta buɗe idon, ko kuma tana jira ne ya bata umarnin buɗewar, tunda ita bata da umarnin kanta sai na wani, ya lura da hakan tun farkon zuwanta. sai dai yana zuwa dab da ita taji gabanta yay mugun faɗuwa, allon ƙirjinta ya girgiza, taji kamar ta arta a guje. so take tasa hannu ta toshe hancinta saboda ƙamshin turarensa da ke shiga hancinta, ba saboda rashin daɗinsa ba, idan tace ƙamshinsa babu daɗi tayi ƙarya, wannan ƙamshin yana ɗaya daga cikin ƙamshin da zata iya cewa da wuya a samu ƙamshi me daɗi irinsa. sai dai da ace tana da iko, da ace tana da iko da Turaki da ta haramta masa sanya wannan turaren, da tasa ya bar ƙasar nan yaje wata ƙasar sun wanke duk wani sauran ƙamshi na irin turaren nan dake jikinsa, ba ta son ƙamshin ta tsane shi, ba don komai ba sai don an haɗa asiri da shi, wannan asirin da yay sanadin zuwanta cikin dajin da ta kusa mutuwa. ranar da Turaki ya tsareta da tambayar me ya kaita wancan wurin yana kama hannunta taji ƙamshin, ƙamshi ne da ba zata manta da shi ba, ta jima tana zuƙar ƙamshin a lokacin dan tabbatar daga inda yake fitowa, tunaninta ko asirinne ya kuma biyota, da ga baya ta ankara da cewa ba ƙamshin kowa ba ne sai nasa, that means ya tabbata kenan asirin nan nasan ne, kuma an haɗa asirin ne da turaren da yake sawa...saboda haka yanzu fatanta guda ɗaya ne, Allah ya bata wata dama da zata hana Turaki saka wannan turaren, ko kuma Allah ya ɓatar da turaren daga duniya gaba ɗaya. jin takalmin Turaki gaba ɗaya akan kafaɗunta tai firgit ta buɗe ido ta sauke kallonta akan ƙafafunsa dake cikin takalmin shigowa kitchen. ta haɗiye wani busashshen yawu sannan ta iya buɗe baki tace,"kayi haƙuri ban san me kake cewa ba". ya fito da hannayensa daga aljihu ya tamke fuska yace,"na miki kama da dodo?". da sauri ta girgiza kanta alamar a'a. yace,"to me yasa duk ranar da kika ganni kike rikicewa ki bi ki firgice, ko ina kama da aljaninki?". nanma ta girgiza kai cikin sauri tace,"a'a". yace,"to ina jinki tsoron na mene?". a hankali tana shirin yin kuka tace,"bana so a ɗaga min murya ko kuma a min tsawa". yace,"ni kuma haka nake miki ko?". bata ce komai ba tayi shiru. sai taji yay ƙasa da muryarsa yace,"mene wancan abun da kike haɗawa?". ta ɗaga ido ta kalli robar da take dama kunun tace,"kunun shinkafa ne, Adda Samha tace na dama mata". ya matsa daga gabanta ya ƙarasa wurin yana faɗin,"an gama?". tace,"a'a zan zuba madara ne". yace,"zo ki ƙarasa". sai tai ɗan jim bata motsa ba, ya juyo ya wurga mata wani kallo da niyyar ya doka mata tsawa sai kuma ya taushi zuciyarsa ya sauke murya ƙasa yace,"nace kizo ki ƙarasa ko". ta taho kamar me ciwon ƙafa, ta fasa madarar ta ɗaga gwangwanin tana zubawa hannunta nata rawa, madarar rabi ce ta shiga rabi duk ta zube a ƙasa, haka har ta juye gwangwani ɗaya sannan ta ƙara fasa wani, zata zuba sai taji ya kama hannunta ya karɓi madarar ya zuba da kansa ya jujjuya. yana gama juyawa ya tura mata cup ɗin da ya ɗauko gabanta, bai magana ba amma ta fahimci me yake nufi. sai tace,"zan zuba siga". ta faɗa tana nufar drowern dake sama, ya bita da kallo yana tunanin ta inda wannan ƴar a bar dake iyakar cikinsa zata iya ɗauko abu a wancan drowern dake luluƙin sama. ya lissafa yaga ko da abu zata taka sai ta ɗora me tsayi tukunna tsayinta zai kai, lissafin nasa ya ƙare a kallon siraran ƙafafunta dake yawo a cikin zani, babu makawa ta taka wani abun ta faɗo sai ƙashinta yay breaking in to pieces. ta ɗauko doguwan kujera zata taka ta hau sai ganinsa tayi ya ɗauko roban ya miƙo mata, tana so ta kalle shi amma tana tsoron idonsa, tasa hannu biyu ta karɓa ya wuce ya bar mata wajen. zata zuba sugar ɗin taji yace,"a little bit". sai ta dakata da zubawan. yana ganin hakan sai yace,"ɗan kaɗan". kaɗan ɗin ta zuba, kuma data zuba sai data ɗago ta kalle shi, ba tai magana ba amma kallon nata ya bayyana masa abinda take nufi, itama kuma shirun nasa ta gane cewar yayi. ta zuba kunun a cup ɗin da ya ijje mata sannan ta ɗauko ƙaramin plate ta ɗora cup ɗin akai ta ɗora spoon, ta ɗauka zata fitar masa da shi taji yace,"give me". da sauri ta miƙa masa ya karɓa dan ta gane me yace, bata manta karatun ɗazu ba da teacher nasu ya faɗa musu ma'anar give me da hausa. yana karɓa ya fice ya bar kitchen ɗin, da fitarsa ta sauke wata wawiyar ajiyar zuciya, ta ɗauki tea flask ta juye kunun aciki ta ɗauka ta fita da shi, tana fatan Allah yasa Turaki baya falon a lokacin. samunsu tayi duk suna dining suna lunch, tace da Samha. "Adda Samha nan zan ajiye ko ɗakinki zan kai miki?". Samha bata kalleta ba tana wani shan ƙamshi tace,"ajiye anan". ta zagaya ta gefen da Nihal ke zaune ta aje, sannan tai tsaye ƙeƙam a wurin. tana jin idon Hajiya Madina akanta, duk sai take jin wani iri da kallon, ta ƙara yin ƙasa da kai. "Idan kin kawo abu kike tafiya bayan kin ajiye ba sai kin jira an miki izinin tafiya ba, kinji ko?". tace,"tom Maama". Hajiya Madina tace,"da sauran abincin a kitchen ko zaku ɗiba anan, ko kuma wani abun zaku dafa?". tace,"akwai saura Maama". tace mata,"to kije ku ci". har zata tafi Zaytuna ta kalli cup ɗin dake gaban Turaki, ya shanye rabin kunun ya bar saura. taga idan an barsa asararsa za'ai, kuma wannan na flask ɗin yanda suke da son kunun shinkafa ba zasu bar ko kaɗan ba, kuma tasan Fillon da ta haɗa bata rage ko kaɗan da zata sha ba, tasan abinda zata iya aikatawa. dan haka tace mata,"zo ki ɗauki wannan". Fillo ta zagayo gefen da take, ta ɗau cup ta riƙe. "ki shanye shi karki zubar". ta wuce ta koma kitchen ɗin, ta tarar Ɗausiyya ta zuba musu abincinsu a wani ƙaton roba, da dukkan alama Ɗausiyyan na da shegen ci, kuma bata saba cin abinci a ƙaramin kwano ba. ta ɗauki wani cup ɗin separately ta juye kunun da Turaki ya rage, bayan ta wanke cup ɗin ta maida shi ma'ajiyarsa tabi bayan Ɗausiyya suka fita. **** Boɗejo na zaune a tamfatsetsen falon na gidan Hakimi, wata maid nayi mata tausa. da sallama aka shigo falon, Boɗejo ta ɗauke kanta ga barin kallon tv ta koma kallon ƙofa. ganin masu shigowa ta buɗe baki cike da jin daɗi tace,"Ilham". ta faɗi sunan tana me cike da mamakin ganinta. Ilham da ƙawarta suka ƙaraso ciki, ita ta ƙarasa inda Boɗejo take ƙawartata kuma ta zauna akan kujera. "bari in samu ladan nima". Ilham ta faɗa sanda ta zauna a ƙasa tana cewa da maid ɗin ta tashi ta tafi zata ƙarasa ma Boɗejo tausar. "rai kan ga rai, ashe da rabon ƴar nan zan ƙara ganinki kamin na mutu". Ilham tace,"bar zancen mutuwa my Only Granny, yanzu ai zaki ke ganina akai-akai tunda dai Allah ya yarda an kammala karatun". Boɗejo da har yanzu daɗi bai saketa ba tace,"ai ko dai naji daɗin kammala karatun nan, haka kawai Hashimu ya wani kwasheki ya kai ki wata uwa can duniya kiyi karatu ke ɗaya, ai ranar nan sai dana masa tatas nace idan baya ƙaunarki ne ya faɗa mana sai muje mu ɗauko ki mu dawo dake, wannan wane irin karatu ne ace shekara biyar anata faman yinsa babu ƙarewa". Ilham tai murmushi tace,"to Boɗejo ba gashi har mun kammala ba". "haka ne dama komai ai lokaci ne, yanzu ai ba tausa zaki ba Ilham jikina zaki taho". Ilham ta bar matsa ƙafar da ta fara tayi jikinta suka rungume juna. duk su biyun suna masu jin daɗi. Ilham ƴar gidan Hashim ce mai martaba na yanzu ɗan Boɗejo, itace ƴarsa mace ta biyu wacce taci sunan Boɗejo Rumana, ta tafi america karatu inda ta karanci business administration, kuma tunda ta tafi bata dawo ba sai yanzu, shekara biyar cif. ba don babu halin dawowar ba sai dan kawai mahaifinta yafi so ta nutsu tai karatunta, ya kanje ya dubata akai-akai shi da mahaifiyarta wacce itace mata ta biyu a wurinsa. Boɗejo ko da yaushe acikin mitar karatun Ilham ɗin takeyi duk sanda taje wajen me martaban, har ta kance ko dai dan yaga an saka mata sunanta ne shiyasa baya ƙaunarta, da ƙyar yake samu ya lallasheta, idan yace ta shirya akaita taje ta ganota sai tace ita ba zata je ƙasar arna ba, dama saudiya ne to anan tafi kauri amma ita kam ba dai ta hau jirgi taje ƙasar arna ta kwasowa kanta zunubi ba. Aisha na gefe tana kallonsu da burgewa, ita bata taso ta sami kakanninta ko ɗaya ba duk sun mutu. shi yasa idan taga tsofaffi sai taji suna burgeta, dalilin da ya sa ta biyo Ilham kenan suka taho tare, amma yau tayi niyyar komawa kano saboda kar mahaifinta me martaba sarkin kano ya dawo bata nan, yana dira wanda zai so ya fara ganawa da shi itace, kasancewarta auta. Hajiya Atika

Chapter 18 of 73