Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Ammi na kallonsu duka ta ce,"to bara ta bar muku ɗakin sai inga wa zaku takurawa". ta kamo hannun Fillo suka bar ɗakin suka wuce sashin Lamiɗo ɗakin matarsa Diyam, anan aka zaunar da Fillo don shiryata, simple makeup aka yi ma ta amma tayi masifar kyau, gyaran jikin da akayi ma ta na 4days sai ka rantse an ɗauki watanni ana yi, sai faman shining take yi kamar fatar kifi, fatarta ta zama kamar madara tsabar kyau. riga da skirt na material me tsada cikin lefen da akayi ma ta na gida, sai aka ɗora ma ta alkyabba me mugun kyau red colour. Dadda ta shigo ɗakin, ta shigo tana faɗin,"kaiii Diyam ɓangarenki ai gaba ɗaya ya karaɗe da ƙamshin amarya". ta ƙarasa tana buɗe fuskar Fillo ta ce,"Masha Allah, Tubarkallah. Lallai Muhammad Turaki ya yi da ce da kyakykyawar ƴar mu, ai da na sa ni na ƙayyade masa sabon sadaki". zuciyar Fillo ta buga, tasa hannu ta dafe takardar sakin da ke maƙale acikin brezier ɗinta. Dadda ta ce da ita,"ungo sha wannan". Fillo tasa hannu ta karɓa tana yatsine fuska, zata yi gardamar da ta saba Dadda ta ce,"ke wannan ba magani ba ne ruwan tofi ne Dottijo ya bayar a kawo miki, ma za yi bismillah ki kafa baki ki sha". tayi bismillah a fili ta kafa baki, ba ta sauke ba sai da ta shanye tass da ma tana jin ƙishirwa. "ko ke fa, adu'armu itace Allah ya baku zaman lafiya, Allah yayi muku albarka ya albarkaci rayuwar aurenku, Allah ya baku zuri'a ɗayyiba, ya kauda fitina tsakaninku ya haɗa kanku ke da abokiyar zamanki". kowa da ke ɗakin ya amsa da,"ameen". a lokacin Dada ta shigo, itama ta bata wani ruwan tofin adu'ar ta sha, sannan ta ba ta wani magani na su da kuma wani turare da ta fesheta da shi lungu da saƙo, ta kuma bata wata ƙaramar kwalba itama da ke ɗauke da turare aciki ta ce,"karki yarda taje hannun kowa har ki shiga ɗakinki, ki shafa turaren ciki a lokacin da zai shigo ɗakin, karki yi wasa da duk abin da muka faɗa miki da kuma abubuwan da muka ba ki, so muke kiyi zarra, ki zama tauraruwar da ke haska cikin gidan mijinki". Dadda da Adda Asma su ka kamata a tare suka fita da ita, ɗakin Hajjah aka wuce da ita inda nan Ummi ta ke da zama yanzu ita da su Kaka da sauran ƴan'uwanta, ana shigo da ita Ummi kawai sai ta fashe da kuka, aka ƙaraso da Fillo gabanta ta durƙusa. Ummi ta zura hannunta cikin alkyabbar ta kamo hannunta ta riƙe anata, sai a lokacin Fillo ma ta saki nata kuka da bai zo ba tun ɗazu. "Yanzu kin zama matar aure, kin bar ƙarkashinmu kin koma ƙarkashin wani bawan Allah wanda Allah ya zaɓa miki matsayin mijinki, haka zalika aljannarki ta koma ƙarƙashin mijinki, bauta za kiyi, bautar da za ki saka a ranki cewa ba Muhammad Turaki za ki bautawa ba Allahnki za ki bautawa, biyayyar mijinki a yanzu ita ce gaba da komai a gurinki in banda addininki, in dai har za ki yi ma mijinki biyayya to za ki shiga aljannah, faɗar Allah ce ba tamu ba, ki kula da abincin mijinki ki kula da shimfiɗarsa, karki wasa da tsafta, ki zama me haƙuri, karki ko yi rashin juriya da kawar da kai, in har kin riƙe waɗannan abubuwan riƙo me kyau to kuwa za ki kama mijinki a tafin hannunki, kina da kyau ki ƙara da wanka ƴata, Allah ya yi miki albarka Halima, biyayyar da ki ka yi min Allah yasa kema naki ƴaƴan da za ki haifa su yi miki. Allah ya sa wannan aure da ki ka yi anyi kenan sai mutuwa ce zata raba ku, Allah ya yi riƙo da hannayenki ƴata, Allah ya dasa tsananin tausayinki da ƙaunarki a zuciyar mijinki, Allah ya ba shi ikon yin adalci a tsakanin ke da abokiyar zamanki, don Allah ki zama me haƙuri a gidan aurenki kinji, da auren so da auren ƙiyayya duk sai anyi haƙuri sosai ake jin daɗin zamansa, ki girmama iyayen mijinki wannan zai ƙara ba ki fada a zuciyar mijinki, kar ki zamto me yi masa jayayya da ƙorafi hakan zai sa mijinki yaji kin fita a ransa, ki kula da duk haƙƙoƙin mijinki, ki dage da ibadah da kuma yawaita adu'ar tsari da zaman lafiya tsakanin ke da mijinki da abokiyar zamanki, kin san ba ki da lafiya dan haka ki nesanta idanuwanki da kunnuwanki da dukkan abinda zai zamar miki damuwa balle ki jawa zuciyarki matsala, sannan abu na ƙarshe da zan jaddada miki shi ne ki zama busy akan yawaita karatun ƙur'ani, wannan zai hana zuciyarki samun lokacin biyewa zugar shaidan, Allah ubangiji yayi miki albarka, ya baku zaman lafiya ya kauda fitina a tsakaninku, na yafe miki dukkan abin da kika yi min". rabuwa dai tsakanin mahaifiya da ƴarta sai ya zama abu me wahala, dan ƙam Fillo ta riƙe Umminta tana kuka me taɓa zuciya, kuma da yake itama Ummin tana da raunin zuciya sai su ke ta kukan tare, sai da ƙyar aka samu aka cire Fillo daga jikinta. suka fito aka wuce da ita part ɗin Maudo, shi da Dottijo ne zaune a parlonsa, anan aka zaunar da ita kowa ya fita ya rage daga ita sai su, Maudo ya ɗora hannunsa akanta ya dinƙa kwaranyo adu'a yana tofa ma ta, ya gama nasa Dottijo ma ya yi ma ta, sannan suka shiga yi ma ta faɗa da nasiha me ratsa zuciya, kukanta sai ya ƙaru, kuma lokacin kewar mahaifinta ta kamata, sun jima su na ma ta nasihohi kafin a fito da ita. ko ƙafar gida ba'a fito da ita ba anan ƙaton tsargidan akayi parking da motar Maudo me shegen tsada a gabanta aka shigar da ita, ana ta busa algaita da sarewa kamar wata ƴar sarki, Dadda da Inna Baraka yayyan Hayyo sai wata cousin ɗin Ummi me suna Innah Hajar su ne suka shiga motar amarya, sauran motocin kuma da mutane shida kacal suka bi bayansu, motar amarya tayi airpot sauran biyun kuma suƙa ɗauki hanyar Gombe. a gidan Alƙali aka yada zango, dan su da kansu suka turo motar ɗauko amarya a airpot, su Dadda sun sami tarba me kyau a wajen su Hajiya Madina, sun ga mutunci da karamci tsurarsa, lokacin da su Dadda zasu damƙa Fillo a hannun Mum sai ta girgiza kai tana yi musu nuni da Hajiya Madina ta ce,"ai ga mahaifiyar tasa can". Inna Hajar ta miƙa hannun Fillo akan ƙafafun Hajiya Madina tana faɗa ma ta ga amanar ƴarsu, Maama na murmushi me faɗi da jin daɗi take shaida musu sun karɓa, kuma insha'Allahu ɗan su ba zai bayar da kunya ba, Fillo sai ta rinƙa jin kamar ayau ne ta fara shigowa gidan Alƙali, kuma kamar ayau ne ta fara sanin su Maama dan duk sai take jin su sababbi a wurinta, a cikin hular alkyabbar da ta rufe mata ido banda kuka babu abin da take yi, ƙwayar idonta baƙin rubutun da ke ɗauke da adadin sakin da Turaki ya yi ma ta kawai ta ke haskowa, tana jin muryarsa na ƙara karanta ma ta a kunnenta. sai wajen ƙarfe uku sannan ƴan taraba waɗanda Dada ta zaɓa zasu zo Dinner suka zazzo, ciki kuwa har da ita kanta, tasha wanka na kece raini kamar ba tsohuwa ba, less ɗin jikinta kansa abin kallo ka ƙara kalla ne. sai ƙarfe takwas na dare tukunna aka fara shirin tafiya Dinner, faɗar haɗuwar da amarya tayi ma ɓata lokaci ne, alƙalami ma ba zai iya ba, ta yi kyau iyakar kyan da ƙaryar baki ya ce zai iya faɗa, wata arniyar doguwar riga ce da Maama tasa Samha tayo order ɗin ta daga europe aka taho da ita, kana kallo kasan kuɗi aka sa ba kaɗan ba aka saya rigar, shigar pink aka yi ma ta wanda hasken fatarta yayi bala'in ɗaukar colour ɗin, abin ba'a cewa komai sai dai masha'Allah. sabuwar mota fil wacca Mum ta bawa Turaki a ita zaa ɗauketa, Raudha da Maijidda su kai ma ta rakiya har bakin motar da Bello ne ke zaune a driver seat, aka buɗe ma ta bayan motar ta shiga, san da zamanta ya daidaitu lokacin balaƴaƴƴan ƙamshin turaren da ta san shi kaɗai yake amfani da shi taji ya doki hancinta, ta yi saurin ɗago kai tana kallonsa, ta gan shi yana kallon gefe guda da alama ma bai san da shigowarta cikin motar ba, Fuskar nan kamar an aiko masa da mutuwa, ya fito sak a asalin Turakin da ta fara sani a rayuwarta, sai dai duk da wannan ɗaure fuskar da ya yi hakan bai hana fito da azababben kyan da ya yi ba acikin arniyar suite ɗin da yasa, black da ratsin pink colour irin na jikinta. tuna cewar ita fa ba matarsa ba ce yasa tayi saurin ɗauke idonta akansa, tana me tuna haramcin hakan, idanuwanta suka ciko da ruwan hawaye suna ƙoƙarin zuba, sai dai ba ta basu damar hakan ba dan sam bata so yaga weakness ɗinta a yau balle ya alƙanta hakan da zafin sakin da yay ma ta. ta kafe ƙunshin hannunta da kallo tana jin ƙaguwar su tafi aje ayi ayi a gama taron ta daina ganinsa a kusa da ita. da ga Bello dake driving har su kowa zuciyarsa a cunkushe take, Maijidda ce kawai da bata san damuwar komai ba take jin zuciyarta wasai sai kallon titi takeyi, Bello kuwa bini-bini sai ya daki stearing yana jan dogon tsaki. can da tafiya tayi nisa Fillo taji kallon dake jikinta ya yi yawa ta ɗago ido, karaf ƙwayar idonsu ta tsarƙe ata juna, tasha murr fiye da yanda ya haɗe tasa fuskar, kwatakwata ba ta san lokacin da bakinta ya suɓuce da faɗin,"kana da buƙatar ƙara sanin addini da kyau, domin na lura sam baka san yanda shari'ar musulunci ke tafiya ba". tayi maganar a ƙasa yanda su Bello da ke gaba ba zasu ji ba. Turaki ya dinƙa kallonta da mamaki tsantsa, kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce da ita,"kin fini buƙatar komawa makaranta ke da kika kasa ba da takardar sallamar da aka ba ki". ya faɗa daidai da isowar motarsu event center, suka yi parking a bakin ƙofar shiga gurin sannan suka yi zaman su a mota, Bello bai ko waiga ya kalli Turaki ba balle yay masa magana, ya fita ya tsaya jikin motar sai jera uban tsaki yake yi. sai da duk mutane suka gama shiga cikin hall sannan aka zo aka fito da Turaki da Fillo, Bello ya yi gefe abinsa kamar bai da wata alaƙa da Turaki, aka zagayo da Fillo side ɗin da Turaki yake nan da nan sai ruwan camera akansu, ƙememe suka ƙi riƙe hannun juna duk da ɓata ran da Anty Rahinatu(ƙanwar Mum) ta nuna musu, suka jera kamar ƴan ƙauyen ƙayayau. su Amatullah da suka zama ƙawayen Fillo su ne suka fara shiga a layi na hannun dama da ga nan sai iyayen gayyar a tsakiya, sannan abokan ango da Turaki bai sa a inda Bello ya kawoso su ba suka ja nasu layin a gefen hagu, abin dai gwanin burgewa, ba zaka taɓa kallon fuskar Turaki da Fillo ba kayi zaton ransu a ɓace yake, ko damuwa, hakan yasa duk hoton da aka ɗauke su sai sunyi kyau, ita dai tayi ƴar ƙarama a kusa da shi dan ita kanta sai nauyi take ji. su na ɗora ƙafafunsu akan step na shiga hall ɗin MC ya fara sanar da shigowarsu, kowa ya miƙe tsaye kamar an ce wasu masu mulkin nigeria ne za su shigo. ƙafafun Turaki da na Fillo suka shiga hall ɗin a tare, abokai kuma na take musu baya, cameras suka shiga ɗaukan su ta kowanne angle, me video coverage na ɗauka tun da ga kan takalmansu har zuwa kan fuskarsu. taro dai ya tafi a bisa tsari kamar yanda iyayen ango suka so ya kasance, yanda Bello ya zo ya yi baiograph haka AmaturRahman tazo tayi biograph na Fillo, anci an sha an bar abinci, biki dai kamar da ma an jima ana shirya masa dan sosai sisters ɗin Fillo suka dinƙa rawa, tashin kiɗa a wajenan kace bayyanar dujal, su dai waɗanda ake abin dominsu suna tsaye ƙyam kamar gumaka, gwara Fillon ma na ɗan murmusawa mussaman da ta ga cousin sisters ɗin suna ta shan rawa abin su, ruwan kuɗin liƙi kamar ba'a talauci a nigeria. Dada da Hajiya Madina kuwa watsa kuɗi kawai suke yi kamar babu talakan da ke buƙatarsu a duniya, har hannayensu sai da suka fara ciwo, rawa kuwa ba ka ce da jikinsu su ke yi ba, Dada sanda ta suɓuce zata faɗi akai saurin tarota, amma a haka taci gaba, ita kanta Maama har sai da Khalil yaji haushi yazo ya janyeta, tazo tana rawa ta manta gaban ƴaƴa take da abokan ƴaƴa. sai a ƙarshen taro Fillo ta yanka cake ɗin da Turaki ko kallonsa bai yi ba, kuma babu wanda ya lura da hakan banda Bello da ke kallonsa yana jin kamar ya rufe shi da duka, Hajiya Sajida Yayar Hajiya Ramla ita ta rufe taro da adu'a sannan aka tashi. lokacin da aka tashi ƙarfe goma sha biyu, direct daga nan aka wuce da Fillo gidan mijinta. su na zuwa Dadda tasa tayi wanka sharp sharp aka ƙara shiryata cikin wani ɗinkin atamfa na riga da zani, aka ɗora ma ta sabuwar alkyabba ba irin wacca aka zo da ita ba fara ƙal me arnen kyau, a gurguje suka ƙara yi mata nasiha daga bisani kuma suka yi ma ta sallama suka tafi, tare da shaida ma ta zasu zo gobe kafin su wuce in dai Dada bata hana su zuwa ba. Adda Asma ta kalli su Raudha da suka wani maƙale ma ta ta ce,"sai ku tashi mu tafi ko". kusan duk a tare suka miƙe su na rataya jakunkunansu, Fillo ta kamo hannun Maijidda, ta ɗage hular alkyabbar da aka rufeta da ita, ta kallesu duk su biyar ɗin, Amatullah, Amaturrahman, Raudha, Maijidda, Khairat, da kumburarrun idanunta cikin sanyin murya ta ce,"yanzu tafiya za ku yi ku barni ni kaɗai?, ku zauna tare da ni don Allah". Khairat ta ce,"mu barki ke ɗaya ko mu barki ke da angonki?, gulmammiya rabonki da azababben kukanki tun jiya da kika ji za'a kawo ki gidan miji yau". Raudha ta ce,"bar ƴar ƙaniya za ta wani marairaice mana ba". Maijidda ta ce,"rabu da su zanke zuwa ina ganinki kinji Hussainata". Dadda ta sake ƙwala musu kira dan haka suka fice da sauri su na ƙara yi ma ta sallama da yi ma ta tsiya. tana jiyo takun su a sanda suka sauka daga bene, ta jiyo ƙarar rufe ƙofar parlon ƙasa, sai kuma ta dinƙa jiyo hayaniyarsu a compound suna shiga mota an buɗe musu gate sun fita. ƙarar zuge gate ya haɗe da bayyanar wani bala'in tsoro a ƙirjinta, tayi saurin tashi ta isa window ta leƙa, karaf idonta ya sauka akan Turaki da yake fitowa daga mota, tana kallo ya ɗau wata hanyar ta daban ba nata part ɗin ba, sai kawai taji saukar sabbin hawaye a saman kuncinta masu zafi kamar zasu ƙona fatarta, ta ƙara komawa ɗaya windown ta hangesa ya buɗe part ɗin da yake na Ilham ya shige, tana kallo ya zuge glass door na entrance din parlon, sai taji kamar ya haɗa da zuciyarta wajen rufewa ya datse. a hankali ta sulale a wajen tana rushewa da kukan da zata ce bata taɓa yin irinsa ba, yanzu ita ɗaya zata kwana a wannan ƙaton wajen?, tabi tangamemen bedroom ɗin da kallo, tsoro na masifa ya ƙara kamata, me yasa ma tayi wannan haukar na bari a kawota cikin gidan nan alhalin ba zaman aure zata yi ba zaman iddah zata yi?, ta jima zaune tana ta uban kuka har kusan ƙarfe biyu sannan ta miƙe ta shiga toilet tayi alwala tazo tayi sallah, sai bayan ta idar take jin wani irin loneliness da kuma wani irin tsoro na daban, tayi saurin barin kan dardumar ta haye kan gado ta ƙudundune a waje ɗaya, ƙarshe ɓarawon bacci ne ya ɗauketa. *Comment, Share and Vote.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *47* kirayen sallar asuba ya farkar da Fillo da ga bacci, ta buɗe idanuwanta a hankali, tana miƙewa zaune aka ɗauke wuta, babu shiri ta koma ta ƙara dunƙelewa, har sai da taji masallaci na sallamewa da ga sallah tukunna ta ƙara buɗe fuskarta tana leƙowa, farko duhu ta gani sai kuma ta ga haske ya gauraye ɗakin. da ƙyar ta iya sakkowa kamar me tsoron taka tiles ɗin, alwalar ma kanta ɗaiɗai ta yi saboda tsoron toilet ɗin, ta fito ta isa kan dardumar da ta bari a shimfiɗe tun sallar daren da tayi. zata tayar da sallah taji kamar an buɗe gate, jikin windo ɗin ta isa ta ɗa ga labulen tana hangen bakin gate da mai gadi ke mayar da ƙofa ya rufe, kafin idonta ya manne akan Turaki da yake tafiya zuwa in da taga ya nufa jiya wanda ta tabbatar nan ne part ɗin Ilham ne, dubai jallabiya ce a jikinsa dark blue, sai carbi da yake hannunsa yana ja, a yanzu ma da ya zuge glass door sai taji kamar ya datse da zuciyarta, idonta ya ciko da ruwan hawaye sai dai ba ta basu damar zubowa ba, a hankali ta din ga bin tazarar da ke tsakanin part ɗin na su, cikin kanta tana jin kamar ƙwaƙwalwarta na couting ma ta nisan interval ɗin da ke tsakanin part ɗin na su, tazara ce sosai amma sai take ganin kamar tazarar daidai take da tazarar yatsun hannunta. jikinta taji gaba ɗaya ya saɓule, ta koma kan sallayar ta tayar da sallah, ta jima tana jero adu'oi a san da ta idar, haka kawai taji zuciyarta na raya ma ta kamar Turaki zai mayar da aurensu, ta yi saurin girgiza kanta, it can never be possible ta san da hakan, yanda ya ke da muguwar zuciya ta sa ni ko da wuri ɗaya zasu ke kwana su na tashi ba zai taɓa mai da auren ba, kuma itama ba ta jin ko da ya mayar da auren za ta yar da ta zauna da shi, ai yanzun ma zama kawai take yi da zarar ta gama iddah zata bar masa gidansa, bari kuwa na har gaban abada. ka sa ta shi ta yi ta koma kan gadon, kawai sai ta kwanta nan kan darduma jikinta tana jin duk yana yi ma ta ciwo, hawayen da take ta danne zubarsu taji sun gangaro, muryar Ummi kawai take son ji, ita kawai take son gani. cikin kanta taji na karanta ma ta yanzu ita ɗaya zata yi ta zama haka kamar mayya?, to ai ko wannan bedroom ɗin ya yi ma ta girma da zama ita ɗaya balle wawakeken part ɗin na ta da taji ana ta faɗarsa tun a jiya da su Arɗo su ka dawo daga jere, anya kuwa zata iya ci gaba da wannan zaman da zuciyarta ta tsara ma ta?, ba zata falllasa komai ba kuwa?, kamar fa hauka ne take yi hakan!, ita abin da ba ta so shi ne ƴar ƙaramarta da ita ace wai tana zaman iddah a gidansu, to wanne irin kallo za'a koma yi ma ta?, wanne kalar tunani za su koma yiwa silar rabuwar auren?. sai kawai taji kuka ya taho ma ta sosai, tasa hannu ta toshe bakin kamar akwai wanda ya ke kusa da ita ba ta so ya ji, ita dai ba zata iya wannan zaman ba, gwara ta yi tafiyarta kawai, ko kuma ta kira Ummi ta faɗa ma ta a kawo Sumayya ta tayata zama, Sumayya ƙanwarta ƴar matar Hayyo da har ya mutu da ita ɗaya ce ba su rabu ba, ko kuma ta cewa Maijidda ta dawo nan ɗin?, to ai in har ta faɗawa Maijidda kamar ta kai takardar sakinta ne gaban Dada. da waɗannan lissafin tunanin bacci ya ɗauketa, ƙarfe takwas yunwa ta farkar da ita, hasken ranar da ya ratso ta windon ɗakin yasa hankalinta kwanciya, tsoron ya bar jikinta. tana ta shi ta gyara kan gado, sannan ta shiga toilet tayi wanka, ta daɗe a toilet ɗin kafin ta fito, ɗaya da ga cikin lotions da aka jere ma ta akan dressing mirror ta ɗauka ta shafa, ta shafa farar powder tasa lip balm, sannan ta saka abaya baƙa, ramar da ta yi sai ta ƙara yin kyau sosai acikin kayan. tana sakkowa downstairs sai ta shiga laluben ƙofar kitchen, ƙofofi uku duk sai da ta buɗe, kuma dukansu bedroom ne sai 1 parlo wanda yake shi ne a middle, cikin sanyin jiki ta rufo ƙofar, kenan ita babu kitchen a part ɗin ta?, haɗe musu yay kenan su yi shairing guda ɗaya?, kenan duk wannan uban kayan kitchen ɗin da taga an siya su na can an haɗe su tare da na Ilham?, abun da ake nufi har in zata ci abinci sai taje part ɗin Ilham sannan zata dafa?, ashe kuwa an so yunwa ta kasheta, dan wallahi in har dan sai taje part ɗin Ilham ne zata dafa abin da zata ci, to gwara tayi ta zama a haka har yunwar ta gaji da damƙarta ta kasheta. bakinta ya suɓuce da tsakin da ba ta san dalilin yinsa ba, ta koma upstairs ta buɗe jakar da Dadda ta ce an ajiye ma ta kuɗi, ta zaro 10k, hijab ta ɗauka ta sa ta fito ta sa mu mai gadi, ta durƙusa har ƙasa ta gaisar da shi yana amsawa da fara'a tare da saka ma ta albarka. sai taji nauyinsa, ba ta jin zata iya aikensa dan ya haifeta, idan bai girmi Abbanta ba tabbas za su yi sa'anni, ta yi shiru tana juya kuɗin a hannunta har sai da ya katse shirun na ta da cewa,"da akwai abunda ki ke buƙata ne?". ta ce,"Baba don Allah ko za'a sami almajiri a waje?". ya ce,"aike ne?". ta ce,"ehh Baba". ta faɗa kanta na ƙasa. kamar kuwa yanda zuciyarta ke raya ma ta taji ya ce,"ai kin san layin namu babu almajirai, sai dai ki kawo bari naje na siyo". ta na girgiza kai ta ce,"a'a Baba ka bar shi ba zan iya baka aike ba gaskiya". yay murmushi yana jin har ransa ta burgesa, da kuma yabawa da tarbiyarta da hankalinta, ya tuno san da Ilham tana nan, a rana ba'a aike shi ba a aike shi sau uku, kuma a gadarance da nuna isar mulki. "kawo ƴata babu komai ai sai aje a siyo miki, ai ba aikena kika yi ba, a matsayina na uba zan fita siyo miki abun da ƴata take buƙata saboda kare darajar aurenta". ta ɗago ido tana kallonsa, taji tausayinsa sosai a cikin ranta, ta miƙa masa kuɗin ta ce,"na gode Baba. da ma golden morn za'a siyo min babban ledan, sai madara na gwangwani babba, sai sugar rabin kwano, sai cornflask kwali biyu. za su isa kuɗin ko Baba?". zai ƙirga kuɗin ta ce,"dubu goma ne ban san yanda kuɗin na su yake ba". ya ce,"ehh tou nima gaskiya ban san yanda kuɗin yake ba, amma yanda za'a yi, bara idan naje in akwai ciko sai na karɓo miki lambar akawunt ɗinsa sai ki tura masa tunda da ma mun saba da shi, nima na kan yiwa iyali cefane acan". tayi ɗan jimm kafin ta ce,"bara dai na ƙaro in ya zama da sauran canji ko ma sun kai shikenan". ta faɗa masa hakan tunawa da tayi bata da waya balle wani account. 5k ta ƙaro, ta ba shi ta ce ya yi har na mota, dan indai ba'a tafiyarta ba tasan layin nan nasu kaf babu wani kanti. da ga fitowarta ta farko, da komawar da tayi ta ƙara fitowa duk a idon Turaki da ke tsaye a balcony na sama, hannunsa riƙe da mug da alama tea yake sha, ya bita da kallo san da ta koma ciki yana ji zuciyarsa na ƙirga masa girman laifin da ta aikata. sai bayan ta shiga kuma kawai sai idonta ya sauka acan dining area, adon wurin ya yi bala'in burgeta hakan yasa ta tafi, tana zuwa ta tarar da manyan warmcoolers na abinci guda huɗu da babban tea flask, tana kallonsu ta shaida su, coolers ɗin kitchen ɗin Maama ne da sai

Chapter 52 of 73