ta amshe da cewa,"ai wallahi jiya na so da ni aka je da sai nayi masa rashin mutunci. ni yanzu Nihal ma aina zan ganta, da ƙyar ma idan bata ƙwace tayi gidan Hammah ba fa".
a lokacin ne dattijiuwar da ta shigo tana laluben Hajiya Ramla ta ƙaraso wajen.
Hajiya Ramla tace da ita,"sannun ku da aiki Maga".
"yauwa Hajiya, wai da ma masu yankan nama ne suka ce Baffa ya kira waya yace a ƙara yanka raƙumi da raguna guda uku, sai akai raƙumin gidan Hakimi".
"sun yanka ne?".
"a'a da ma nace bari na zo na fara shaida miki".
"to kinga garzaya ki faɗawa Madina, ki dubata a ɓangarenta ko ɓangaren yaran nan".
"to shikenan, batun funkason can fa ya za'ai da shi?".
"ai da kun gama ku kai gidan Babana, ɓangaren Fillo za ku kai, nata ne aka yi mata saboda baƙin da ke can".
"to shikenan".
Maga ta juya ta fita a parlon, yayin da Hajiya Ramla ta ƙarasa wurin mutanen da ke zazzaune a parlon, waɗanda mafi yawan su abokan aikinta ne.
"sannunku fa". ta faɗa a sanda take zama akan ɗaya daga cikin kujerun, kusa da wata aminiyarta Hajiya Shamsiyya.
"yo ke uwar amarya haka ake sai ki shige ɗaka ki barmu zazzaune anan".
murmushi ya ƙwace a fuskar Hajiya Ramla tace,"haƙuri zaku yi, ƴar taku ce ta sakani gaba tana kuka".
ta faɗa a lokacin da take bawa wata tsohuwa umarnin inda zata ajiye kulolin soyayyan naman da ta shigo da su.
sannan ta ƙwalla kiran Ɗausiyya da sabuwar ƴar aikin da suka yi bayan auran Fillo, me su na Maraƙisiyya, cikin sauri sai ga su sun zo sun durƙusa a gabanta.
"ku ɗauko farantai ku fara rabon naman nan, kowanne plate ku zuba yanka goma sha biyar".
sai kuma ta kalli tsohuwar tace,"Yaya kun kai ɓangaren Madina kuwa?".
"ehh Hajiya yanzu Yami ta tafi kaiwa".
"to masha'Allah, sannunku da aiki".
sannan ta ƙara cewa da ita,"Yaya don Allah ce da Madina ta bayar da maƙullin store, sai a samu waɗanda za su ɗebo lemuka aciki, a ɗebo katan arba'in, akai katan sha biyar gidan Babana, sai a bar sauran anan".
cikin sauri tsohuwar ta miƙe ta fita, sai da ta fara zuwa ta duba wajen aikin suyar ta su sannan ta wuce ɓangaren Hajiya Madina.
nan ɓangaren ma cike yake da mutane waɗanda mafi yawansu ƴan'uwa ne, duk sai ka kalla fuskokin su zaka shaida ashe Hajiya Madina ƴar dangi ce, saboda kusan duk kamannin su ɗaya.
"Hajiya tana sama ne?". tsohuwar ta tambaya a sanda ta shiga parlon.
"kamar dai ta shiga kitchen". wata acikin mutanen dake zaune akan kujera ta faɗa.
"ta fito ta koma sama fa, yanzu suka wuce ita da Zaytuna".
Tsohuwar ta miƙe cikin hanzari ta hau upstairs, ta tsaya a ƙofar ɗakin Hajiya Madina domin jiran iso bayan tayi sallama.
a sanda babu wanda ma ya jita saboda akwai ƴar hayaniya acikin ɗakin.
Hajiya Madina na tsaye a gaban madubi tana ɗaura sarƙa a wuyanta, a lokaci ɗaya kuma tana bayani ga Maga.
"kinga ba wani nama da za'a kai gidan Hakimi, shi ya siyo mana, ko a gidansa ake taron, mu da aurar da ƴaƴa shi da karɓe nama. wani lokacin ma dai Baffa ya fiya neman suna, ya mayar da Hakimi kamar wani ubansa, to kice su yanka a haɗe gaba ɗaya da na gida, in Baffan ya dawo ace masa mantawa aka yi".
Maga ta miƙe tana ƴar dariya ta fita, Yaya ta shigo ita ma, ta durƙusa tana cewa,"Hajiya wai ki bayar da maƙullin store za'a ɗebo lemuka".
"Zaytuna duba drower ɗin nan ki miƙo mata maƙulli".
sai kuma ta dubi Yayan ta ƙara cewa,"don Allah da an ɗebo a rufe saboda jiya sai da akayi mana ta'adi".
Umman Nadiya ta shigo ɗakin a lokacin.
"ke Madina da ma Turaki aure ya ƙara?".
Hajiya Madina ta kalli fuskarta a cikin madubi tare da yin murmushin takaici sannan ta ce,"wa ya guntsa miki wannan maganar?, to ba sabon aure yayi ba tsohuwar matarsa ya mayar, ita ma kuma don fitinanniyar Kakarsa ta ƙara tayar da rigima ne, yauwa biyayya ya ƙara yi a karo na babu adadi, don Allah a bar ɗana ya huta a daina yawan zancensa ana faɗar masa da gaba, haba tun jiya da akace an ɗaura aure da shi ake ta ƙwala kiran sunansa acikin gidan nan kamar wanda yay sata, to idan ma auran ya ƙara zunubi ya aikata ko me?, ina ruwan wani?, ko ba mata huɗu aka halasta masa ba?, haba mutane da shegen gulma da tsugudidi".
Umman Nadiya tace,"to jarababba Allah ya ba ki haƙuri, ni tambaya nayi ba wani abu ba".
Hajiya Madina dai bata ƙara tanka mata ba, ta haɗe rai ta juya kan Zaytuna tana yi mata faɗan kukan da take tayi tun jiya da aka ɗaura aure.
"ni dai ina ga sai na haɗa miki da duka tukunna, haba kuka yaƙi ci yaƙi cinyewa abu tun jiya, to ki shiga hankalinki da ni".
Umman Nadiya tace,"to ai dole tayi kuka, ita kaɗai ce fa acikin su zata yi nesa".
"yo nesa abu da ba ƙasar zata bari ba, Allah na tuba ina nan ina Abuja, shi ma ɗan banzan Bellon da ya biyewa Baffa ya mayar da shi can abujan, ai sai da na faɗa masa ya dage ya barsa su ci gaba da aikinsu anan. ban ma san munafikin dai da ya bayar da shawarar buɗe wani kamfani ba tare da saninmu ba, ko da yake yanzu ai mu ƴan banza ne a wurin Baffa, duk ya mayar mu ƴan wofi, wannan fitinanniyar tsohuwa duk ta bi ta hargitsa mana zama, Allah ya shiryeta kawai, yanzu tun da dai an mayar da auren sai ta bar hankalin kowa ya kwanta".
ta kamo kunnen Nihal da ke shigowa ta murɗe,"ke, ke, ke, ki kiyaye ni fa".
"Maama wallahi Hammah ɗin ne fa ya koro ni, wai daga nace ba za'a bawa masu jeran kayan Ilham abinci ba".
"mtsww Allah ya sauƙa, to Mum ɗin ku tace ki wuce ki karɓo mana kayanmu tun ranki bai ɓaci ba".
"ehh yanzu zan tafi, Maama to sauran kuɗin ai za ki cika min".
"nawa ne?".
ta ɓoye ƴar dariyarta tana leƙo jakar Hajiya Madina dake saman gado ta ce,"jiya na ƙara kai ɗinki na set uku, su zan saka ranar da za'a kai amare, balance ɗin dai har na ku yace 35k za'a bayar".
"idan kuma babu naki fa?".
"20k".
ta zauna bakin gadon ta ɗauko jakarta, ta ƙirgo kuɗi 20k ta miƙawa Nihal ta ce,"ga namu ɗin, naki kuma bari nayi miki kwatancen ɓangaren Baffa ko kuma na ba ki lambarsa kawai, sa 08065....".
kowa a ɗakin yasa dariya hatta Zaytun da ke kuka tun ɗazu, Nihal ta fara shagwaɓa tana zama kusa da Hajiya Madina ta shiga yi mata kirari da kalallameta.
Umman Nadiya ta ce,"gaskiya ya kamata dai a bawa Auta kuɗi ta karɓo nata ɗinkin ita ma, ba wani sai taje gun Baffa".
Hajiya Madina ta ce,"wannan ƴar fa da kike gani tun da biki ya taho ta fara fashin kuɗi, daga shekaranjiya zuwa jiya kawai tayi min fashin kuɗi sun kai kusan 100k. tsabar rashin sanin darajar kuɗi jiya makeup ɗin 20k akayi mata, ɗaurin aure kawai ba wani event ba. her Excellency kuwa ce tayi sai jiya ta ankare da ATM ɗinta, ta manta shaf ta bawa Nihal tun ranar da aka je jeran kayan ɗakin Samha, ƙarshe dai ta talauta ta babu ko sisi a account ɗin nata, to ni dai na bata shawara nace ta makata a kotun alƙali Dikko kawai, ina dalili yarinya duk ta bi ta yashe mu".
"Allah Maama kina da kuɗi, to ki ban 5k sai Mum ta cika min 10k ɗin".
"yo Nihal ko da Kakar ki Boɗejo uwar masifa kike tafe ai biyar ba zan ba ki ba, don haka ki tashi ki kama gabanki kawai, kije can wajen Uwaki ta ba ki".
Zaytuna ta ce,"ke yarinyar nan wai me kike yi da kuɗi?, Maama ɗa zu ma fa tasa Hammah Bello ya turo ma ta 20k, ina jinta kuma again tana bin Khaleel tana yi masa ƴar murya".
Nihal ta tura baki gaba ta ce,"daga yau ba zan ƙara tambayar mijinki kuɗi ba balle ki zo kina min tonon silili, kina terere da ni mijinki ya ban dubu ashirin. shi ma Hammah Khaleel ɗin da ya ban sai da ya faɗawa duniya ya bani, shiyasa zan mayar masa da kayansa, to wai ma idan baku bani ba waye zai ban? Hammah ne kaɗai a gidan nan zaka tambayrsa kuɗi ya baka kai tsaye babu ƙurewar tambayoyi".
Hajiya Madina tace,"ba kya tambayar na hankali ne shiyasa, tambayar ƴan fashi kike yi, ban san ba kuma ko jari za ki kafa da kuɗaɗen mu".
"Maama to ki ban don Allah, haba Maaman Hamman'mu, Maama me haƙorin maka guda biyu, Maama ƙawar Boɗejo, Maama ta hannun dama na".
Hajiya Madina tayi dariya ta make hannunta dake kan haɓarta,"zan ci gidanku Nihal, naga alama kin mayar da ni Kakarki".
sai kuma ta ɗauko kuɗi a jaka ta bata ta ce,"ga 5k nan daga haka ba zan ƙara ko ficika ba".
Nihal ta rungumeta tana yi mata kiss,"Allah ya bar min ke uwar marayu har ma da masu uba, i love you so much. Allah yaja mana da ranki".
lokacin Samha ta shigo ɗakin, bayanta wasu yara ne su uku ke biye da ita, Hajiya Madina ta bita da kallo, cikin sigar tsokana ta ce,"don Allah Umman Nadiya kin taɓa ganin amarya mara kunya irin wannan?".
ta nuna Samha da ta wuce wadrobe ta buɗe tana ɗebo kaya.
"ina irin ƴar ƙwallar nan da ake yi ta ranar ɗaurin aure, to in faɗa miki yarinyar nan dai bata yi ba, jiya Zaytuna na kuka ita tana wage haƙora talatin da biyu a waje, duk sai ta bani kunya...".
Samha ta katse maganar Hajiya Madina da cewa,"kai Maama, ni yaushe akayi hakan, Allah ma nafi Adda kuka".
"yo camera ai ba zata yi ƙarya ba, za'a kawo bidiyo ko bayan raina Umman Nadiya za kice na faɗa".
Samha tayi murmushi ta ce,"Maama ina tawa atamfar?".
"ki ka bani ajiya?".
"Maama daga wurin Mum ɗin fa nake tace Adda ta taho da kayan nan".
Zaytuna ta ce,"nawa kawai na ɗauko na bar miki naki acan, kiyi sauri kije ki duba in ba haka ba a ɗauke, kin san ɗakin Mum wasarairai take da shi, na nemi sarƙata sama ko ƙasa na rasa".
cikin sauri Samha ta fita bayan ta ce da yaran su biyota da kayan da ta ba su.
Nihal ta matsar da bakinta kusa da kunnen Hajiya Madina tace,"Maama gulma zan miki, kin san me Hammah yaywa Fillo kuwa?".
Hajiya Madina tayi saurin mayar da hankalinta gareta. sai kuma Nihal ɗin ta tashi da sauri tana cewa,"kai ba ruwana, ba za'aji mutuwar sarki a bakina ba".
ta faɗa tana saurin ficewa ta bar ɗakin.
Hajiya Madina tabi bayanta da kallo, kafin ta mayar da hankalinta kan maganar da Mama Bilki ke yi mata.
"Zaytuna za'a fara kaiwa kenan?".
"ehh ita za'a kai gobe, jibi akai Samha sai gata mu karɓo amaryar Khaleel, ita anan zata zauna tare da mu, wancan matar ta me Babban sunan kuma yau za su kawota".
Tana faɗa ta miƙe ta fita ta bar ɗakin, don hankalinta bai kwanta ba da maganar da Nihal ta fara yi mata, duk yanda akayi an sami wani misunderstanding tsakanin Turakin da Fillo, dan ta lura tun jiya da aka mayar da aurensa ya zama wani kalar masifaffe, da asuba ma tana jin Khaleel na complain ɗin faɗan da ya kama yi musu na babu gaira babu dalili, to tsoronta kar ya sauke fushinsa akan baiwar Allah, ita da ba ita tasa aka mayar da auren ba, wacca ita ta ma fi shi takaicin mayar da auren, don ta lura da hakan a tare da Fillo, kawai don dai yarinyar na da haƙuri yasa bata nuna ba, sai ka ɗauka ma ko bata san ciwon kanta ba shiyasa take ta hidimarta ko a gefen yatsarta.
fatan ta ɗaya Allah yasa ba Boɗejo ba ce taje ta kunna musu wuta a gida. ko kuma halin jiya ya maimaita musu, don ance jiya ma kafin ɗaurin aure kusan rufe Fillo da duka yayi.
****
"yauwa bayan kin auna fulawanki sai ki zuba butter, ki kwaɓa yeast ɗin da ruwan ɗumi kuma da shi za ki kwaɓin gaba ɗaya. yauwa to miƙo min gishirin can, if you like you can add sugar".
bayanin da Nuratu ke yiwa Fillo kenan a kitchen ɗinta, a yayin da take koya mata yanda ake alkubus, tun san da suka dawo suka zo gidan taci taji daɗinsa tace zata koyi irin nata.
Fillo ta ɗauko roban sugar da gishirin kamar yanda Nuratun tace, ta ajiye tana ci gaba da kallon yanda take yin kwaɓin da kuma sauraron bayanin da take yi mata.
wucewar wasu mintuna Nuratu ta kalli Fillo jin tayi shiru, ta girgiza kanta kawai tare da jin tausayinta, kafin tace mata,"kin san mene?, wallahi tallahi cutar kanki za kiyi muddin za ki ɗauki damuwa kisa a ranki har haka, ke wa ya faɗa miki yanzu ana nuna damuwa da kishiya?, kina ƴar ƙaramarki haka?, amma...".
ranta a ɓace ta ɗauki tukunyar da ta rufe ta bar kitchen ɗin.
Fillo ta bi bayanta da kallo kafin ita ma ta bar kitchen ɗin, parlo ta wuce ta zauna, ta ɗauko Farha da ke cikin keken wasanta, tana cikin yi mata wasa Yusuf ya shigo, bayan sun gaisa ya ke ce mata.
"jiya sai nake jin zancen an mayar da auren abokiyar zaman ki".
wata ƙwallar ciwo ta tararwa Fillo a ido kafin tace,"ehh Yaya".
"to Allah ya baku zaman lafiya, ayi ta haƙuri kin ji ko".
"insha'Allahu Yaya, na gode".
sai ya ƙara cewa,"amma ba ki da wata matsala ko?".
"babu Yaya".
"to masha'Allahu, kar fa kice za ki sakawa ranki damuwa kinji ko, kinga ba isassar lafiya gare ki ba. ya zancen karatun ki kuma?".
tasa hannu ta goge hawayen da yay nasarar gangaro ma ta kafin tace,"lokacin da muna Ausburg har ya nema min addimission acan, to kuma da muka dawo sai yake cewa wai na haƙura kawai, to ban san me dai yake nufi ba, gaba ɗaya zan haƙura da karatun ko kuma wancan admission ɗin zan haƙura da shi".
Yusuf ya sauke numfashi yay ɗan jim kafin yace,"ki ba shi lokaci tukunna, zuwa gaba sai kiji koma menene dai, amma karatun naki yana da muhimmanci sosai".
ya miƙe daga kan kujerar da yake zai wuce ɗaki Farha tasa kuka, ya dawo ya karɓeta ya tafi da ita.
wayar Fillo dake kan cinyarta tayi ƙara, ta ɗauka ta kara a kunne tare da amsa sallamar Maijidda.
"ke na zo kuma na tarar ba kya nan".
"ehh wallahi naje gidan Yaya Yusuf ne".
"lallai ma ke ɗin nan, kuma kika ce na zo na raka ki ƙunshi, kin san za ki fita za kisa na zo, ko don kawai dai kin raina min hankali, wannan ai rashin mutunci ne".
"Allah ya ba ki haƙuri maida wuƙar, ba jimawa zan yi ba yanzu ma fa nake shirin tahowa. sanin halin ɓata lokacinki yasa nace bari kawai in je in dawo, don Allah ki zauna yanzu gani nan a hanya".
"sai kin dawo, idan da mota kika fita ki yiwa Allah ki samo min mangoro a hanya".
"to uwar biyu".
Maijidda tayi dariya sosai tare da cewa,"rufa min asiri maza su kaini ba mata ba, uban wa na aura da har zan zama uwar biyu, ke ɗin dai".
su kai Sallama Fillo na miƙewa ta nufi ɗakin Nuratu, samunta tayi tana haɗa wasu magunguna a leda da dukkan alama maganin mata ne.
Fillo ta zauna bakin gadon tana cewa,"Anty tafiya fa zan yi...". kuma bata ƙarasa ba ƙarar wayarta ya katseta, ganin sunan Maama yasa tayi saurin ɗagawa.
daga ɓangaren Hajiya Madina tace da ita,"Daughter lafiya ba ki shigo ba?".
"Maama naje gidan Yaya Yusuf ne".
"zuwa yaushe za ki dawo?, ko acan za'a yi miki ƙunshin?".
"a'a wallahi Maama, wadda muka yi zata zo ɗin da safe ta kirani an yi musu rasuwa, wai da zata turo sister ɗinta but tana faɗa min bata ƙwarai sosai kamarta ba, shi ne nace ta bar shi kawai".
"ok to ki taho yanzu, nasa a kira wacca ta yiwa amare tazo tayi miki, bana so ki ƙara zama haka babu lallai, da ɗaurin aure an ga ba kiyi ba mutane sai su fara zaton ko baƙin cikin damuwar kishiyarki yasa".
"to Maama yanzu zan taho".
"to shikenan sai kin dawo, yauwa kar ki manta ki taho min da ajiyar nan da na ba ki, ga dai Nihal nan zata ja da duk alamu ɗinkinki na gobe ma babu".
Fillo tayi ƴar dariya.
Maama ta ƙara cewa,"ga baƙi nan an ƙara yi, su na ta tambayar uwar gidan Turaki, idan kin zo duk zan miki bayaninsu, ƴan uwana ne na Kano, babu wanda ya taɓa zuwar min sai yanzu da bikin ƴaƴansu ya tashi".
bayan sun yi sallama Nuratu tace,"to ke ko anan ma ba sai ki godewa Allah ba, iyayen miji na sonki miji na sonki, danginsa su na sonki to kuma dan me na damuwar don ya mayar da matarsa?, auren nan fa biyayya ce kawai zai yi ba wai don baya sonki ba, ko a haka matsayinki da nata ai ba ɗaya ba, matar so kike, ita kuma matar shige".
"Anty Nuratu wallahi ni abin da nake tsoro raini da wulaƙanci".
ta faɗa cikin rauni da muryan ban tausayi.
Nuratu tayi guntun murmushi me sauti.
"me zai sa ta raina ki?, a wanne dalili Fillo?, wurinki fa daban wurinta daban, ko za ku shekara dubu a gidan nan sai kun so za ku haɗu da juna. kinga look, ni fa ko a yanda na ɗauka ma sai ka yi abin da za'a rainaka ɗin tukunna ake samun damar rainaka, as far as kin kiyaye waɗan nan abubuwan wallah ko da me kishiya ke ji bata isa ta raina ki ba. na farko karki kuskuren saka mata Ido a lamarinta, kar ki ke kai ƙaranta, saurin faɗa da ita shi ne babban abin da ke janyo raini, da kuma ɗaukar zuga, in har kishiya ta fuskanci kina ɗaukar zugar mutane to billahi ta gama rainaki, haka zalika kar ki yi gigin dinga shiga kowanne lamarinta ko da ita da kanta ke cusa ki aciki, baya baya dai...".
Fillo ta tari numfashinta,"Anty Nuratu to ni ina ma nake da lokacin waɗannan abubuwan akanta. ina miki batu ne na tana ganin ita ƴar sarki ce, ta fini ilimi, ta kuma fini wayewa, kuma tana da aikin yi, sannan zata dinƙa min kallon cewar ni ba kowa bace face ƴar aikin da aka tausayawa aka auro, Anty Nuratu dole ta raina ni".
"to ai ƴar aikin ta fita tun da har tausayin ma yasa aka iya auro ki, ita da ba'aji tausayin nata an aurota ɗin ba fa sai cusata da aka yi?, mtsww kin ga don Allah ni kar ki bayar da ni, ko wayewar ma ai bata fiki ba, wayewar shiga jami'a kawai ta fiki, amma ban da ta gidan miji, ko kin manta tsawon watanni da kika shafe a ƙasashe da dama kina durzar amarci ke da mijinki, ita ta sami wannan damar ne?, bata samu ba kuma ba zata samu ba".
sai kuma ta miƙa mata ledar da ta gama zuba kaya aciki,"ga waɗan nan ɗin, ai duk nayi miki bayanin yanda za kiyi amfani da su".
"to na gode sosai, Anty Nuratu sai garin kunun, don Allah a ƙara yi min, naji daɗinsa sosai wallahi, sometimes idan na kalli kaina sai inga kamar ba ni ba, ji fa kumatun da na tara".
ta faɗa tana ƴar dariya me kama da ta ƙarfin hali.
"wai ke zatonki kunu ne kaɗai ya saka ki wannan ƙibar, to har da Babyn mu".
"hmm ni fa banda wani ciki. haka jiya Ammi ma da naje sai adu'a take wai Allah ya raba lafiya, ni dai nayi murmushi kawai. kafin mu taho test nawa aka yi duk ba ciki ba ne, ni kam ma ba yanzu zan haihu ba sai kamar nan da 2years lokacin na ƙara girma".
"yanda za'aji daɗin cewa ke juya ce kenan, ki ma daina wannan kuskuren tunanin, yanda kike da kishiyar nan in har ta rigaki haihuwa sai kin fuskanci ƙalubale, gwarama ki roƙi Allah ya ba ki, in ya so kya huta daga baya".
har bakin mota Nuratu ta rakata, ita kuma sai godiya take yi mata.
"ki daure dai ta bakin Abban Farha ki ƙara zuwa asibiti su duba, don bani da tantama kin ɗauki ciki".
Fillo tayi murmushi me ciwo,"idan cikin ne zai bayyana kansa Anty Nuratu. kin san fa nace masa muje asibitin wallahi ko tanka min bai yi ba, da na ƙara magana ma ce yay bai shirya tara ƴaƴa yanzu ba".
tausayinta ya kama Nuratu, ta kawar da zancen dan ta lura kamar akwai damuwar da take ciki, kamar dai yanzu tana zaman haƙuri ne da Turaki kawai.
"kin ji bikin Raudha an mayar da shi Adamawa ko?".
"haka Ummi ta faɗa min jiya da muka yi waya".
"ni ban so hakan ba wallahi, kawai dan ba yanda aka iya da Maudo ne. yaushe za ki tafi to?".
Fillo tayi murmushi me ciwo tace,"ai babu ni a batun zuwa kam dan yace ba zanje ba, kuma wallahi ba zan ƙara yi masa maganar ba, na lura tun da zai mayar da auren nan ya ɗauko wata bura'uba ya ɗorawa kansa, kuma sai dai komai ya ƙare akansa shi ɗaya ni ba saurarsa zan yi ba, ban iya haɗa hanya da damuwa".
Nuratu tace,"Allah dai ya kyauta, yanzu kam sai kin ta haƙuri, yan da za ki sami mijinki a ke ta ɗaya ba haka za ki same shi ba a ku biyu ba. shawarata kiyi ta adu'a Allah ya kauda fitina tsakanin duk ku ukun, abin da bai da kyau Allah ya mayar maku da shi me kyau. sannan don Allah ba ruwanki da wata fitina, imma daga ɓangarenki ko nata, ki kama mutuncinki ki riƙe, kar ki sake wani hargagi ko cin mutuncin ko fashe fashe da duk danginsu a same su daga gareki, wannan duk kishin marasa ilimi ne. kuma jiya na faɗa miki yau zan ƙara maimaita miki, babu ruwanki da shisshigewa ko tusa kai a wurinta wai ko dan ku zauna lafiya a'a sam, idan har taga kin ja ajinki da mutuncinki za ki ga tana jin shakkarki, idan ma tana tare da tsiya ne to zata sha jinin jikinta.
sai kuma shawarar da zan ƙara ba ki, kafin ya amince kici gaba da karatu to ki fara business, kin san ance darajarka jakarka ko aljihunka, to ki kama kasuwanci kamu me kyau, ta yanda hankalinki zai karkata ɗungurungum akansa, ta yanda za ki zama baki da lissafin wata kishiya da takaicin miji sai na kuɗinki, wallah kasuwanci wani babban abu ne na siyawa kai mutunci wasu matan ne kawai basa ganewa, kuma kar ki yarda ki kama kasuwanci da kuɗinsa, ki kira Dada ki faɗa mata kina buƙatar kuɗi ko kuma kice a buɗe miki shago.
Sannan ko da wasa kar ki sake mijinku ya fara samun tashin hankali ta ɓangaren ki, in ba haka duk san da wani laifi ya afku ko da ba ke bace zai ce ai kece uwar rigima, abu guda biyu ne zuwa uku naki, sanin darajar kai da sanin yadda za ki sarrafa ragamar miji, ki zama kece limamiyar ba wannan limamiyar da ke jan ragamar limancin layu biyu ba. Kissa da kisisina kamar ki lashi takashinsa amma shi ma ina jan kunnenki, mutunciki kar ki sake kiyi wasarairai da shi, domin shi ne limamin rayuwa".
Fillo tasa tissue ta goge hawayenta, kuka ya kubce mata ta ce,"ni kaina na san sai nayi haƙuri yanzu Anty, Turaki ya sauya min fiye da tunani. wallahi Anty da yazo min da batun zai mayar da auren nan sam ban nuna masa ina ƙin dawowarta ba balle kuma na ɗaga masa hankali. amma jiya kafin su tafi ɗaurin aure kar ki ga yan da ya taso min da faɗa, har da zagi fa Anty, kuma wallahi ba wani abu nayi masa ba, cewa kawai nayi zan koma can gidansu sai an gama biki na dawo, wai buɗar bakinsa ce yay tunda ina baƙin ciki da zuwan wata ai dole nace zan bar gida, to babu in da zanje in zauna in kula da ƴan uwanta da suke zaryar shiga da fitar yi mata jere, idan suka buƙaci wani abu wa nake nufin zai ba su, ko shi zai baro wajen aikinsa ne ya kawo musu. to kar inyi kuskuren wulaƙanta masa Mata, don ƴar'uwarsa ce, kuma samun zaman lafiya tsakanina da shi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 65 Chapter of 73