tana faɗar Allah ya kyauta raki irin na Fillo, bata san ya za'ai ba idan tazo haihuwa.
kuma sai bayan minti goma sai ga Maijidda ta shigo ɗakin neman Fillo, Kaka wadda har ta kwanta a lokacin tace mata,"yo aini nayi zaton wurinku ta nufa, ta shigo tana kukan ciwon ƙafa to nama zaci banɗaki taje, dana ji shiru kuma nace ƙila tayi wajenku".
Maijidda ta zauna tace,"bata je ba Kaka". ta faɗa muryarta na nuna rashin jin daɗi. Kaka tace,"ƙila can cikin gidan ta koma, yanzu ai zaki ganta tunda ba can dai zata kwan ba, yanzu haka tayi mantuwar wani abu ne shi yasa ta koma".
Maijidda dai tayi shiru bata ce komai sai ɓata rai ta ke, Kaka na kallonta dai bata tambayi ba'asi ba, saboda tasan kwanan zancen, akan dai Fillo ne da basa zama tare yanzu shine take ta yin wannan kumburin.
shiru-shiru Fillo bata dawo ba sama da kusan rabin awa, Maijidda lokacin itama har ta fara hamma. ta fara masifar ita wannan aikin bata sonsa sam, zata sa Yami ta nemi wata yarinyar akai musu a ƙyale mata ƙawarta.
Kaka tace,"to wai ke Maijidda iyaka akayi miki da shiga cikin gidan da ba za ki dinga binta ba ko me?, ba sai ma ku dinga yin aikin tare ba".
Maijidda tace,"ni bana son shiga wurin da za'ake min gani gani Kaka, tunda sun san basu ɗaukeni aiki ba ina zuwa za'a fara min tambayar yanda Uwata ta haifeni".
Kaka tace,"aiko dai kin yiwa Hajiya sharri dan ba haka halinta yake ba...zaman jira ne kuma sai kita zama karki yi bacci har sai ta dawo, waya san ma ko acan zata kwana tunda har ta kai wannan lokacin...to ni dai na kwanta sai da safe".
Maijidda dai tai zaune jugum tana sauraron radion Kaka dake kunne, har lokacin da gidan radion suka tashi a aiki. daga ƙarshe dai data gaji da jira ta tabbatar Fillo ba dawowa zata yi ba ta tashi ta rufe ƙofar ɗakin sannan tabi Kaka ɗakin ta kwanta itama a inda Fillo ke kwanciya.
ƙarfe sha biyu da minti goma sha biyar na dare a lokacin, motar Turaki akan hanyar da bai san ya akai ya biyo cikinta ba. hanyar tayi duhu dulum sai haushin karnuka dake tashi. gefe da gefen hanyar shukoki ne na masara da shinkafa da alama dai gonaki ne a wajen.
ya rasa me yake damunsa gaba ɗaya, shi dai yana zaune yaji kawai yana so ya fito yasha iskar gari, kuma da har ya wuce Lambu sai ya koma ya ɗauki key ɗin motarsa ya fito.
da farko gidan Mai Martaba yaso ya nufa, sai kuma zuciyarsa ta sauya masa ra'ayi, ya dinga bin titina yana sauka daga wannan zuwa wannan. tuƙin kawai ba dan ya san inda hankalinsa da tunaninsa yake ba, shine har ya shigo wannan layin da bai san ina motar ta kawosa ba, dan ba shi ya kawo kansa ba..
wuri ya samu yayi parking ya fito ya jingina da jikin motar yana fuskantar inda shukar shinkafar take, idonsa akan Shukar yake amma ba ita yake kallo ba, ba kuma tunani yake yi akanta ba, wucewar minti goma ya kalli agogon wayarsa yaga ƙarfe sha biyu da rabi a lokacin.
sai kawai ya buɗe motar ya koma ciki, ya kuma nausawa cikin gonar ba tare da tsoron daren ba.
driving ɗin yake with high speed kamar me shirin barin gari, ba ganin gabansa yake da kyau ba a lokacin duk da fitilar motar daya kunna. yasa hannu a rigar kujera zai ɗauki glasses ɗinsa sai ya tuna ɗazu da zai karanta jarida yasa Nihal ta ɗauko masa.
yay guntun tsaki kawai, jin komai yake babu daɗi, cikin kansa kamar babu komai, kamar ma ba'a cikin duniyar yake ba.
da hakan yasa hannu ya daki stearing da ƙarfi, horn ya kama nan wani Kare dake gefen wata bishiya ya tashi da gudu ya tsaya a tsakiyar hanya, ganin hakan yasa Turaki ƙara danna horn da ƙarfi, nan karen ya bar wajen da gudu. tsaki kawai yake jerawa, ya jera yafi ƙarfin ƙirgen yatsu, bai san meke damunsa ba, bai san meke masa daɗi ba, bai san me zaiyi ya samu salama ba.
kawai sai ya tsinci idonsa da haska masa wasu shafuka acikin al-qur'ani, da haka kuma zuciyarsa ta fara karanta abunda ƙwayar idonsa ke haska masa.
sannu a hankali yaji yana samun relief, nan ya kai hannu ya kunna alqur'ani, ƙira'ar Shuraim ta fara tashi acikin motar.
ba tare da ya sani ba, haka kuma ba tare daya ankare ba yaji ya daki abu. gabansa ya faɗi, bakinsa ya furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, duhun idanunsa ya washe lokaci ɗaya, yayi mugun taka burki babu shiri ganin yana neman bi ta kan abinda ya buge wanda bai san mene ba a lokacin, ƙarar taka burgin ya bada wani ƙara ƙuuuu, tunaninsa ɗaya ne wata dabbar ya kaɗe.
sai dai me zai faru?, a lokacin daya fito daga motar cikin hanzari sai kawai yaga mutum yashe a ƙasa cikin jini, macece, amma kamar ba mutum ba haka zuciyarsa ta faɗa masa.
saboda haka kamin ya kai ga tsugunawa gaban wadda yake da tabbacin ta riga ta zama gawa sai daya kalli ko'ina da ina, yaga babu kowa kuma babu alamun kowa, sannan ya tsuguna yana mai jin fargabar kai hannu ya taɓata.
bakinsa ɗauke da tarin adu'oi yasa hannu ya juyo da ita daga kifen da take, jini duk ya wanke mata fuskarta, babu ta yanda za'a ganeta. ya janye gashin kanta daya baje akan fuskar. ya ƙara furta innalillahi sannan ya kama hannunta wanda yake a damƙe kamar ta riƙe wani abu, ya taɓa yaji artery ɗin wurin na motsi.
ya sauke ajiyar zuciya, ji yayi kamar yayi hamdala a lokacin.
kansa ya ƙulle da tunanin ma me zai yi, kuma tana ina zai fara, kuma me ya kamata yayi.
yana riƙe da hannun tsawon wucewar wasu daƙiƙu sannan ya miƙe da sassarfa ya buɗe bayan motarsa, ya kunna fitilar motar sannan ya dawo ya ɗauketa ya sakata a motar, yarinya ce ba wai babba ba, hannunta guda ɗaya ya sauka akan kafaɗarsa, ya ɗauke yana kallon hannun nata da yake a damƙe.
ƙwayar idonsa ya tsaya cak a kanta, wacece?, me ta fito yi a irin wannan lokacin?, daga ina ta ke?. zuciyarsa ta ƙara ɗarsa masa anya kuwa mutum ce?, sai yayi saurin ɗauke idonsa daga kanta ya sauke ajiyar zuciya. ya rufe bayan ya dawo mazauninsa yana ƙara volume na karatun daya kunna.
yana kunna motar ya ɗauki wayarsa ya kira lambar Hajiya Madina, dai-dai lokacin daya hau kan titi ta ɗaga wayar. muryarta tattare da tarin bacci ta kira sunansa tana mai mamakin kiran nasa a irin wannan lokacin ƙarfe ɗaya na dare.
daga ɓangaren da take ta miƙe zaune akan gadonta cikin faɗuwar gaba ta kunna bedside lamp. "Hammansu". ta kira sunansa cikin wani amon sauti da bata san tana da shi ba.
a wannan lokacin Turaki kamar zai yi kuka, ya juya baya ya kalli yarinyar sannan muryarsa dake ɗauke da tashin hankali yace,"Maama na kashe rai".
"what?, ban ji da kyau ba Hammansu". tayi maganar a ɗage tana durowa daga saman gado babu shiri.
"Maama ban san ya akai ta shigo gabana ba, its like kamar jefota akai". a rikice yay maganar kamar yanda yake a rikice.
Hajiya Madina da ta faɗa toilet tana wanke fuska don ta wartsake daga mafarkin da take tunanin tayi tace,"kana ina Hammansu?".
yace,"ban san inda nake ba Maama, ina dai kan wani titi. har yanzu banga wani wuri dana sa ni ba, banga asibiti ba ko ɗaya Maama...kamar da sauran ranta ina tsoron karta ƙarasa mutuwa".
muryar Hajiya Madina a ɗage tace,"wai wacece ne? kuma me kake so ka faɗa min?".
ya ƙara juyawa ya kalli bayansa sannan yace,"accident nayi Maama, kuma ban san wa na kaɗe ba".
tace,"na shiga ukuna, to da yaushe ka fita daga gida ban sa ni ba?, daka fita ma ina zaka je me Babban suna?".
ya kulle idonsa sannan yace,"Maama duk ba wannan ba, bana so ta mutu ta sanadina, bana cikin hankalina wallahi ban san lokacin dana kaɗeta ba, na kasa fita daga inda nake, kamar ma na bar garin gombe gaba ɗaya".
Hajiya Madina ta zube a gefen gadon da ta ke ta fashe da kuka. wucewar daƙiƙa biyu ta sauke numfashi tace,"ka nemi wuri kayi parking, ka kunna datarka...zamu bi location ɗinka yanzun nan...kai ta biya innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, zaka samu mafita kamin ƙarasowarmu insha'Allahu, take care kaji, kama kashe motarka kawai".
yayi shiru bai ce komai ba. ta katse shirun da cewar,"Hammansu kana jina?". idanuwansa a rufe yace,"Maama idan ta mutu fa?". yay maganar da tsananin rauni. tace,"i beg you stop negative thinking, ba zata mutu ba da yardar Allah, gamu nan tahowawa".
tana faɗar hakan ta kashe wayar, tabi layin Khalil da kira, kira na farko dana biyu duk bai ɗaga ba sai ana uku, cikin bacci ya kira sunanta. tunma bai ƙarasa faɗar sunan ba tace,"Khalil ta shi a barcin nan muna cikin tashin hankali, tayar da mota gani nan".
Allah ya taimaka Khalil baida saurin bacci, yana jin haka ko tambayar ba'asi bai jira yi ba ya diro ya zira jallabiyarsa ya fita. Hajiya Madina ma zani ta ɗaura akan kayan baccinta sannan ta zura hijabi ta fito da warikan takalma, sai salati ta ke yi.
*Please Vote, Comment and Share*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_avoid any mistake plss🙏._
*16*
*Shongom LGA, Gwandum, Yabayo village.* rubutun da map location ɗin ya zana kenan ajikin wayar dake riƙe a hannun Khalil. with high speed yake drving motar kamar zai tashi sama. adu'a yake cikin ransa Allah ya kaisu lafiya, idan ba haka ba za'a iya samun gagarumar matsala a wannan tuƙin nasa, saboda kukan mahaifiyarsa dake gigita hankalinsa da tunaninsa, da kuma tunanin halin da ɗan'uwansa, Yayansa mafi soyuwa a gare shi yake ciki.
tunda suka taho kuka kawai takeyi, duk wata magana ta kwantar da hankali ya faɗeta amma taƙi tasiri a gareta, ya rasa me kuma zaiyi, yasan dai ba zata taɓa natsuwa ba har sai sun isa inda take da buri, to amma atleast yana so ta tsayar da wannan kukan nata ko dan ya samu yayi tuƙin nan lafiya.
ya ƙara kallonta a karo na babu adadi yana jin zuciyarsa na tsinkewa, ya cine fuska ya wani daki stearing da mugun ƙarfi, kamar ya fasa ihu haka yake ji. shi amsar ma da yake so ya sani wai me ma ya fitar Hammansu a wannan salasainin daren?, shin ba ya shiga bedroom ɗinsa yayi masa gud night ba, ya tarar kuma lokacin har ya fara bacci.
ya sauke numfashi yana barin kallonsa ga tuƙin da yake, a hankali yace da ita. "Maama dan zatin Allah kiyi shiru ki daina wannan kukan, wallahi yana ɗaga min hankali, stearing nan nema yake fa ya ƙwace a hannuna".
tasa gefen hinabinta ta goge hawayent tana so ta tsayar da kukan. ta ɗago ta kalle shi idanuwanta duk sunyi jawur sun yi girma. cikin sanyin murya kuma a raunane tace da shi,"to ka kira min Baffan naku".
ya rufe idonsa ya buɗe ya sauke agabansa, da zafin nama ya kaucewa bishiryar daya kusa duka. ya furta subhanalla sannan yace,"Maama na faɗa miki insha'Allahu babu wani abu da zai sami Hammah, shima nasan bige mutum ɗin da yay ne yasa ya rikice har yake faɗa miki bai san a inda yake ba...".
ta katse shi da cewar,"ni dai idan ba zaka kira min Baffan ba to ka faɗa min, sai na sauka na nemi masu waya su ara min".
yace,"to me za kice masa?".
ta ɗan kalle shi yana mata abu kamar ba ɗanta ba, sai tayi shiru bata ce masa komai ba. shima shirun yayi, can ta ƙara cewar,"yanzu dai ba zanci arziƙin wayar taka ba Khalill?".
buɗar bakinsa yace mata,"kina so ki rasa mijinki ne?". ta girgiza kai da sauri. "to ki haƙura da wannan kiran dan baida amfani, kin san dai Baffa ya fiki shiga tashin hankalin akan lamarin daya shafi ƴaƴansa, yanzu idan kika faɗa masa ya yanke jiki ya faɗi a inda yake fa?, kin san dai yanda ba kya kusa da shi ɗin nan anything can happen. so kiyi haƙuri har mu ƙarasa ai mun kusa zuwa, na kira mijin Inna Falmata yace ga police nan da ambulance zasu biyo mu a baya, dan Allah Maama kiyi haƙuri kita adu'a kawai kinji uwa ta gari".
ta gyaɗa masa kai kawai tukunna tace,"to amma baka sauri ka ƙara speed". yace,"to Hajiya Maama yanzu kam za kiga mun isa...ai wurin ba wata tafiya me nisa bane".
tana kallonsa tace,"Yabayo fa Khalil". yace,"can ɗin fa, yanzu za kiga munje Maamancy, situation ɗin da kike ciki ne fa yasa ki ganin nisa".
ta kuma gyaɗa kai bata ce komai ba, taci gaba da tasbihin da take yi.
a wannan lokacin idanuwan Turaki a kulle suke ya kwantar da kansa jikin kujerar, abinda zai iya faruwa da shi dalilin accident ɗin nan ba shine damuwarsa ba, ran yarinyar kawai yake ji, baya so ta mutu, idan ta mutu bai san wanne hali iyayenta zasu shiga ba.
ya buɗe idanuwansa a hankali ya sauke su akan titin da duhun dare yasa ba'a iya hangen komai. yaji wani abu da bai san menene shi ba ya tsarga masa. ya juya baya yana kallon yarinyar, har yanzu zuciyarsa faɗa masa take da gawa yake tare, ta riga ta mutu, irin jinin da ta zubar ba zai barta ta rayu ba.
ya miƙa hannu ya ruƙo nata wanda yayi sanyi kamar ƙanƙanra, hakan ya wanzar da wani abu wai shi tsoro a zuciyar Turaki da bai taɓa ji ba tunda ya girma, babu wata shakka ta riga ta mutu yasan da wannan, shikenan haƙƙin rai ya hau kansa.
idanunsa ya kulle ya bawa kujerar duka yana jin kamar ya saka kuka. me ya yiwa rayuwa ne da take neman tayi masa ɗaurin goro, yana ƙoƙarin buɗe nauyayyun idanuwansa yaji an buɗe ƙofar motar, mamakinsa ɗaya ne ta ya aka buɗe ƙofar bayan yasa lock?, wa ya buɗe?, yasan dai 10minutes bata isa ta kawo su Maama wurin nan ba, duk da he dont have comfirmation of where he is, amma yasan ko ina ne nan da nisa yake.
kuma kafin yay wani yunƙurin juyo da kansa ga ƙofar sai yaji an daki wuyansa, duka bana wasa ba, irin dukan nan da zai yiwa jijiyar wuya lahani, ya rumtse ido saboda tsananin azabar daya ratsa dukka ilahirin jikinsa.
tabbas no any doubt wani ne zai yi attacking nasa, but wanene wannan?, and how comes aka san da wanzuwarsa a wannan dajin?.
Allah ya sa ni a situation ɗin nan da yake ciki ba shi da courage ɗin da zai iya encountering ko waye da faɗa don ganin ya ƙwaci kansa.
inda ace ba'a irin wannan halin yake ciki ba, da ace baya cikin fargaba da taraddadin mutuwar wadda ya kaɗe, to zai yi fighting da koma waye dan ganin ba'a cutar da shi ba, zai ƙwaci kansa ta ƙarfi even if ace 1% chance yake da shi, and he most win saboda ba zai taɓa bari yayi failing ba wajen kuɓutar da rayuwarsa, not becouse of burin da yake so ya cimma a rayuwa ko kuma saboda baya son mutuwa da wuri, no!, its just becouse of his Mom, Maama na buƙatarsa a raye, idan ya mutu ya barta bai san ina zata saka kanta ba, ya riga ya sani her only hope and wish is su rayu tare da shi.
but still bai karaya ba haka yasa hannuwansa biyu ya riƙe hannun wanda ke son shaƙe masa wuya, sai dai inaaa girman mutumin ya shallake tunaninsa, ko ace da kuzarinsa ba zai iya gwada jiki da shi ba.
haka yana ji ƙaton mutumin ya shaƙesa da iyaka ƙarfin da numfashinsa zai ɗauke gaba ɗaya, kuma take yaji yana neman shaƙar iska ya rasa, saboda haka kawai sai ya sare ya sallama.
yana jin mutumin na magana da wasu ta waje amma bai san me suke cewa ba, sama-sama yake jinsu. so yake yaji muryoyinsu, so yake yaji ko da kalma ɗaya ce tak ta abinda suke faɗa, ta yanda ko da Allah yasa yayi surviving zai iya samun hanyar da zai kama su.
daƙiƙa 1,2,3 ta wuce mutanen suna magana, kuma har lokacin jibgegen mutumin na shaƙe da wuyan turaki da hannu ɗaya, ɗayan kuma ya toshe masa baki da hanci, a taƙaice dai babu ta inda iska ke samun shiga lungs na Turaki.
yana ji aka buɗe ƙofar baya, ya hangi siririn mutum ta cikin mirrow ya duƙa akan yarinyar, bai san waye ba dan baiga fuskarsa ba. har yanzu mutanen magana suke da junansu, kuma har yanzu ya kasa jin komai da suke cewa, ya rufe idonsa yana kokawa da cikinsa dake so ya fitar da iska. ƙirjinsa yake jin yana yi masa zafi, ji yake kamar zai mutu, fatansa ɗaya ne a lokacin, kar ya mutu a lokacin sai a hannun Maama, so yake ya mutu yana kallon fuskarta.
wasu adadin sakanni suka wuce ta cikin kansa, a lokacin da ya gama saddaƙar da tafiyarsa lahira, a lokacin ne yaji words guda 22 sun shiga cikin kunnensa, kalmomin da suka fito daga bakin siririn mutumin dake riƙe da hannun yarinyar da ya kaɗe.
_"yarinyar nan zata yi mana amfani, da sauran ranta. ni ko da ta mutu ma ina sonta a hakan, dole ne zan moreta saboda na kwaɗaitu da ita"._
furucin da mutumin yayi kenan, kuma furucin da ya sami nasarar shiga cikin kunnen Turaki har ya zarce zuwa cikin zuciyarsa ya dunƙule a waje ɗaya.
ƙarfi da kuzarin da Turaki yake jin ya rasa na ƙwatar kansa shine yazo masa acikin giftawar sakan ɗaya, wasu manyan jijiyo suka bayyana a hannayensa da goshinsa, tamkar idonsa akan siririn mutumin yake, kuma kamar yasan abinda yake shirin aikatawa, dan haka kawai zura hannunsa yayi ta baya ya damƙi hannun mutumin wanda yake shirin ɗaukar yarinyar, sannan yasa ɗaya hannun nasa yana ƙoƙarin ya cire hannun ƙaton daga bakinsa.
damƙar da Turaki ya yiwa siririn mutumin ta shiga ratsa jikinsa, mutumin ya ɗaga murya wajen cewa wanda ke riƙe da Turaki"gayen nan fa bai suma ba, ya riƙe min hannu kuma kamar ba zan iya ƙwacewa ba, bugawa shege bindiga akai".
da maganar da yay, da ɗauko bindigar da ƙaton yayi, da samun nasarar da Turaki yay na cire hannun mutumin daga bakinsa, suka haɗe lokaci ɗaya da ƙarar jiniyar motar ƴan sanda dake tashi daga can nesa.
babu shiri ƙaton mutumin ya saki Turaki ya falla da gudu zuwa motarsu, shima siririn ya fizge daga hannun Turaki ya falla zuwa motar, ashe basu biyu bane kawai, suna da yawa, kamin Turaki ya zuro ƙafarsa daga cikin motar ya fito tuni sun bar wajen sai tashin ƙurar motarsu.
tsayawa yayi yana bin bayan motar da kallo, so yake yaga lambar motar ko zai samu wata shaida amma duhun dake cikin idonsa ya hana. can kuma tunaninsa ya dawo kan yarinyar, dan haka da sauri ya buɗe bayan motar, ganinta yasa shi sauke ajiyar zuciya. ya shiga tattaɓata yana jin kamar ko sunyi mata wani abu ne.
ji yake ba zai iya cigaba da jira ba, barin wajen zai yi, idan shi ya cutu ba komai ba ne, amma baya so wani abu makamancin wanda sheɗanin can ke faɗa ya faru da yarinyar, dan haka cikin azama ya koma seat ɗin driver zai tashi motar, dai-dai nan kuma motar Khalil ta ƙaraso wajen, motar police na biye da su a baya, yayin da abulance ke bin bayan ta police ɗin.
Khalil na yin parking Hajiya Madina ta fito daga cikin motar, ƙafarta ma ko takalman babu ta barsu a mota, a guje ta tsallaka side ɗin da motar Turaki take har tana bigewa da dutse, ko gabanta bata gani da kyau, burinta ɗaya ne a lokacin taga lafiyarsa, hawayen nata ma nema suke su tsaya da zuba saboda kamar sun ƙare.
tunda ta fito daga motar ƙwayar idon Turaki ta tsaya cak akanta, kamar wanda aka sassaƙa haka ya kasa ko da motsawa, kallonta kawai yake, kallonta yake tana tahowa gare shi da irin tashin hankalin da bai taɓa ganinta aciki ba, da wannan tausayin na uwa shimfiɗe a fuskarta, da wannan tsoron na mahaifiyar da bata son rasa ɗanta acikin ƙwayar idonta, yana gani tayi tuntuɓen amma ya kasa motsin da zai fita ya tareta daga faɗuwar, alhalin kuma so yake ya fita ya rungumeta, amma ya kasa, ƙafafunsa sunyi nauyin da ba zai iya ɗagasu ba, sai kawai ya rufe ido wani hoto na can lokacin baya yana haska masa.
Hajiya Madina na ƙarasowa ta buɗe motar hannunta sai karkarwa yake. "me babban suna". sunan da ta kirasa kenan a sanda ta buɗe motar ta gansa kamar gunki. kuma ganinsa a hakan sai idanuwanta suka haska mata hoton wani abu da ba zata iya jurar gani ba, haka ma zuciyarta ta ɗarsa mata faruwar wani lamari da ba zata iya ɗaukarsa ba. a hankali ta shiga sauke ƙafafuwanta har gwiwarta ta kai ƙasa, sai kawai ta kifa kanta akan ƙafafunsa ta fashe da wani gunjin kuka me taɓa zuciyar duk wani me sauraro, irin kukan da duk wani me rauni yaji shima sai yayi.
sai a wannan lokacin ne Turaki ya iya motsa hannunsa ya kamata ya ɗagata, sannan ya fito daga cikin motar, ya kasa magana haka itama ta kasa, kuka takeyi shima hawayen yake, ya jata zuwa jikinsa yayi mata wata runguma, itama wata runguma tayi masa wadda take daban da tasa, har tsakiyar babban yatsansa yaji rungumartata, irin rungumar da rabon da tai masa ita tun yana yaro.
likitocin dake cikin ambulance ɗin suka fito cikin hanzari, da gadonsu suka iso wajen motar Turaki, Khalil ne ya buɗe bayan motar, yayin da nurses suka janyo yarinyar suka ɗorata akan gadon suka yi ambulance da ita.
cikin sanin makamar aikinsu wasu nurses ɗin suka shiga goge jinin da yake kan fuskarta, yayinda wasu daga cikinsu kuma suka shiga ƙoƙarin ganin sun saita numfashinta ganin cewar da ranta.
duk aikin da suke gudanarwa akan idon Khalil dake tsaye hannayensa acikin aljihunsa, kuma tsananin mamaki ya wanzu a fuskarsa lokacin da suka gama goge fuskarta tayi tas, wa zai gani?, yana gani dai-dai kuwa?, ba yarinyar daya kai asibiti bace ɗazu, Fillo ce fa me aikinsu. sai kawai ya fuskanci wurin da Hajiya Madina da Turaki ke tsaye har yanzu, tana ta aikin tattaɓa shi da kallon ko'ina a jikinsa kamar wadda ta ɗauki tsawon lokaci bata gansa ba.
Turaki yake kallo ba Maama ba, kallonsa yake yana recalling back wani moment da Fillo tace masa,"tsoronsa nake ji". haka ta faɗa masa jikinta na kyarma, sanda ya shigo kitchen zai ɗauki abu. tambayarta yayi kawai menene ya faru yaga kamar a tsorace ta ke, shine ta faɗa masa hakan, kuma ko da ya tambayeta me ta ke tsoro sai ta kalli ƙofar kitchen ɗin sannan tasa hannu ta goge hawayenta tukunna tace masa,"Hammah".
"me yasa to?, yayi miki wani abunne?". tambayar da yayi mata kenan. amma amsar da ta ba shi ita ta ɗaure masa kai,"babu abinda yayi min amma yace zan cutu idan har ban bar inda yake da rayuwa ba, wai haka yaji zuciyarsa tana faɗa masa...kuma ni bana so mu daina wannan aikin saboda da kuɗin muke rufawa kanmu asiri, kuma ni wallahi Hammah Khalil banda mugun nufi, bana cutar da kowa sai ƙoƙarin ganin na kare wanda za'a cutar".
abunda ta faɗa masa kenan tana hawaye, bai ce mata komai ba a lokacin, kawai ya ɗauki abinda zai ɗauka ya fice daga kitchen ɗin.
kuma yana zuwa ɗakin Turaki ya maimaita masa abunda ta faɗa, Turaki bai mu sa masa ba, hasalima ce yayi masa. "Khalil haka jikina yake bani, haka zuciyata take faɗa min...kamar yanda nake jin Granny zata iya cutuwa idan muna rayuwa a wuri ɗaya, haka nake ji akan wannan yarinyar itama".
Khalil ya sauke ajiyar zuciya sanda tunanin nasa ya katse, sukai magana da wani police sannan yayi tattaki ya ƙarasa wurin su Hajiya Madina. yana zuwa ya sanar mata cewar,"Maama DPO yace zamu wuce".
ta haɗiye wani yawu sannan tace,"pack anything that is very important daga cikin motar nan ka kaisu cikin taka...sai a bar wannan anan, ko ta zama rabon wani ko kuma in Allah yayi azo a ɗauketa daga baya, tunda babu me drving ɗinta yanzu".
Khalil na kallonta da tsananin tausayi yace,"wani police ɗin yay driving ɗinta, ko kuma ni
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 73