Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da cewar ta rasu. dalilin da yasa Hajiya Madina ƙara jan Turaki da Zaytuna a jikinta kenan saboda tausayin maraicin su na uwa, ta rungume su a ƙirjinta tamkar ita tayi naƙudarsu, babu ranar da bata kallonsu bata zubar da hawaye ba har suka girma, ƙarshe ma sai ya zamto tana nuna musu tsantsar so da kulawa fiye da waɗanda ta haifa a cikinta, son su take yi domin Allah ba da wata manufa ba. haka kuma kwata-kwata bata nufar yaran da sharri, abinda zai samesu sai ya ɗaga hankalinta wanda zai sami Khalil ko Samha bai ɗaga mata hankali ba ko kusa, don gani take tamkar in wani abu ya samesu lallai Allah xai tuhumeta domin amana ce da tayi alƙawarin ta ɗauka, ta ɗauki alƙawarin zata riƙe su kamar yanda Ramla zata riƙe su, kuma tayi alƙawarin ba zata kalle su da sunan ƴaƴan miji ko ƴaƴan kishiya ba sai ƴaƴan da ta haifa acikinta. bayan shekara goma a wata rana ta laraba sai ga message a wayar Baffa, saƙon da Hajiya Ramla ta turo musu kan cewar tana nan a raye bata mutu ba, kuma ko da xa'a ɗauki tsawon shekara 100 kar su taɓa sawa a ransu cewa ta mutu, tana nan a raye nesa da su sai dai ba zata taɓa dawowa gare su ba har abada. wannan saƙon ya girgiza kowa, kuma wannan saƙon shi ya haddasa jin haushi a zuciyar Zaytuna, take jin tana tsananin fushi da mahaifiyarta, tana jin yau ko da ace za'a kawo mata gawarta ba lallai ne ta dubeta ba. saɓanin Turaki da saƙon ya ƙara haddasa masa damuwa a ransa, lokacin shekarunsa goma sha shida, yana can europe wurin Kakarsa ta wurin uwa, kuma tun daga lokacin har kullum tunaninsa guda ɗaya ne, a wanne hali Mum take ciki?, ya lafiyarta take?, menene damuwarta?. abu ɗaya har kullum ransa ke basa akan barinta gidan shine, wataƙila tayi fushi da shine, tayi fushi da shi akan tana tunanin cewar shi ya haddasa kamawar wutar ɗakin, alhalin shi bai san da komai ba, bai ma san da cewa wutar ta kama ba sai da tayi magana, time ɗin da ta fito ɗaga toilet tayi wanka tana tsane jikinta da towel, shi kuma yana zaune akan gadonta yana homework ɗin da Hajiya Madina ta basa, sai ji yayi Mum ɗin na tambayarsa aina ya sami ashana har yayi mata ta'adi, ta tambayesa ɗin tana yowa wurin da labulen ya ɗan fara ci zata kashe wutar. yana iya tuna yacca taja tsaki a sanda ta kama labulen da sunan zata watsa ruwan dake hannunta, sai yaga kawai ta tangarar da jug ɗin ya faɗi ya fashe, ta wuce ta isa wadrobe ta ɗauki abaya ta zira ta fita ta barsu a daidai lokacin da wutar ta fara ci sosai, yaji tsoro ya sakko akan gadon yabi bayanta da gudu, sai kawai ta hankaɗosa ciki tana doka masa tsawa bayan ta ambaci ainihin sunansa da bata taɓa faɗa ba tunda ta haife shi, taja ƙofar ta rufe tasa key ta cire ta tafi da shi. wannan ɗalilin ya barwa kansa, kuma har kullum yana roƙon Allah ya haɗa fuskokinsu kamin ya kai ga kushewa ya roƙeta ta yafe musu, ya faɗa mata gaskiyar cewar bai san komai ba akan kamawar wutar. "Hammah Hakimi na magana a waya". maganar Zaytuna ta dawo da shi duniyar tunanin da ya tafi. ya karɓi wayar yana karawa a kunnensa tare da yin sallama. sun ɗau lokaci suna waya Hakimi na tambayarsa yanayin lafiyar tasa, kafin daga bisani suyi sallama. washegari ƙarfe goma na safe akayi discharge nasu suka koma gida. kuma suna komawa inda ya fara dosa bayan sunyi lunch shine ɓangaren ma'aikata, dalilin ganin tun dawowarsu bai ga gimlawar Fillo ba, tun da suka dawo yake ta zuba ido ko zai ga ta wuce amma ko inuwarta bai gani ba, kuma yana ta sauraren yaji wani yayi zancenta har da Maama amma sai yaji ba wanda ya ambaci ko da sunanta. _Dan Allah kuyi haƙuri, jiya naso kuyi breakfast da sabon post sai kuma aka sami akasi, na gana typing ɗin banyi saving ba caji ya ƙare, typing ɗin ya goge gaba ɗaya. sai yanzu na sami damar yin wani, a dai ƙara haƙuri hidimar biki sai a hankali wlh._ *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _Please avoid any mistakes._ *25* "barka da shigowa ranka ya daɗe, Allah ya ƙara maka lafiya magajin me gida". adu'ar da ma'aikatan ke tayi masa kenan tunda ya shigo ɓangaren su. yasa hannu a aljihu ya ɗauko bandir na kuɗi ya bawa shugabar ma'aikatan wato Yami, ta duƙa har can ƙasa tasa hannu biyu ta karɓa suna ƙara yi masa adu'oi na fatan alkhairi. tun da ya nufi ɗakin Kaka aka je aka sanar mata, kamin ya ƙaraso tuni ta daɗa kimtsa wurin ta kunna turaren ƙamshi. Turaki yayi sallama a ƙofar ɗakin idonsa na mannewa akan yagalgalallan labulen ɗakin, Kaka ta taso da sauri tazo ta buɗe labulen tana faɗin,"Barka da zuwa ranka ya daɗe". ta yaye masa labulen shi kuma ya shiga, sai bayan ya zauna sun gaisa da Kaka sannan ya fara tunanin acutual abinda ya kawosa. tun bayan gaisawar su da Kaka ya kafe ƙofar ɗakinta da ido, ta yanda ba zaka taɓa fahimtar ga inda yake kallo ba, sama da mintina goma shiru bai ga alamar Fillo ko inuwar Fillo zata fito daga cikin ɗakin ba, kuma motsi kaɗan zai ji daga waje sai ya juyar da ƙwayar idonsa zuwa bakin ƙofa yaga ko ita ce, but sai yaga babu kowa. ya sauke numfashi a daidai sanda zuciyarsa ke ayyana masa tasirantuwar wani abu, kuma lokacin ne Maijidda ta shigo ɗakin tana ta mita. ganinsa yasa tai saurin zube gwiwoyinta a ƙasa tana gaida shi. bai amsa mata da baki illa kansa kawai da ya ɗaga mata. ya miƙe ya yiwa Kaka sallama ya tafi, Kaka ta bawa Maijidda furar da ta dama ta bisa da ita. daga can ɗakin Hajiya Madina Fillo ce zaune a gabanta, kanta a ƙasa, idanuwanta sun cika da ruwan hawaye, tana jin kanta na mugun sara mata kamar zai faɗo ƙasa, maganganun Hajiya Madina nema suke su juyar mata da dukkan wani tunani nata, a yanda dukkan zancen Hajiya Madina suka ratsa jikinta bata jin zata iya ko da ɗaga ɗan yatsa guda a yanzu dai. Hajiya Madina da idanuwanta ke manne akan Fillo itama nata idanun na zubar da ruwan hawaye tace,"wannan shine dalilin da yasa nace miki ina so ki nutsu kiyi karatu, kuma wannan aikin shine wanda nake faɗa miki zaki yi min Fillo, tun a kallon farko da nayi miki zuciyata ta faɗa min zaki iya, hakan yasa na zaɓe ki, ina fatan kuma zaki warware komai cikin sauƙi ba tare da abunda nake gudu ya faru ba". a wannan karon da Hajiya Madina tayi magana, sai Fillo taji kamar tana neman ta tarwatse gaba ɗayanta ne. manyan idanuwanta suka maƙale a kan ƙafar Hajiya Madina dake cikin wani tsadaddan takalmi, so take ta haɗe dukkan maganganun Hajiya Madina wuri guda sannan ta watsar da su a gefe ɗaya, domin bata tunanin akwai ta yanda zata yarda cewar wannan jarumar matar dake gabanta ba itace mahaifiyar Turaki ba. amma dolenta a yau kuma a yanzu ta yarda da hakan, ta yarda da wannan macen ba ita bace asalin mahaifiya wacce ake kira uwa a wajen su Turaki ba. "ban san me zance miki ba Maama, abu ɗaya kawai da na san ya zama dole shine jinjinawa, dole zan jinjina miki, kamar yanda na jinjinawa masu farautar rayuwar Turaki". ta faɗi hakan tana me ɗagowa ta sanya idanuwanta cikin ƙwayar idon Hajiya Madina, sannan ta iya miƙewa jiki a saɓule tana jin kamar ba zata iya tafiya ba, ta bar ɗakin tana barin Hajiya Madina a cikin tsananin tashin hankalin da ba zai misaltu ba. a parlo ta tarar da Samha zata hau stairs wurin Maama, tana jinta tana yi mata magana tayi mata banza bata ko kalleta ba. ta baro side ɗin cike da mamaki da tunani kala-kala acikin ranta, kuma cike da tsoron ɗan'adam, ko waye shi kuma ko ya kuke da shi. a coumpound ta tarar da Ɗausiyya acan wajen bakin famfo tana wanki, ta ƙarasa wurinta tana ce mata. "idan teacher yazo ki faɗa masa bani da lafiya, ba zan iya karatu ba yau. please ki basa assignment ɗina kar yay zaton ko saboda shi naƙi zuwa". Ɗausiyya na kallonta tace,"tun jiya kike kuka Fillo, kuma na tambaye ki kince ciwon kai ne kawai, ni dai wallahi ban yarda dake ba. dan Allah ki faɗa min ko da wata damuwar, mun riga fa mun zama ɗaya". Fillo tace,"kawai bana jin daɗin jikina ne, zanje nasha magani jiyan ban sha ba dama. nasan Adda Zaytuna zata neme ni kice mata Kaka ce tayi kirana". tana faɗar haka ta juya zata bar wurin, lokacin ne motar Zaytuna tayi parking a compound ɗin tana fitowa daga cikin motar, ta ƙwala mata kita hakan yasa Fillo dakatawa da tafiyar ba don taso ba. taje wajen motar tana yiwa Zaytuna sannu da zuwa, Zaytuna ta tsaya tana kallonta da son karanto matsalar dake damunta. "what is the problem?". Fillo ta girgiza mata kai tana faɗin,"nothing Adda". yanayinta kaɗai shi zai ƙaryarta furucinta, Zaytuna tace,"ki ɗauko leda a backseat ki biyo ni da shi". ta faɗi hakan tana wucewa ta barta a wurin. ta ɗauko ledan kayan dake rinjayar ƙarfinta. ko da ta shiga part ɗin su Zaytuna bata sameta ba don haka ajiye kayan kawai tayi ta fito, don yanzu ita sam bata son abinda zai kaita wannan part ɗin ita ɗaya ba tare da wani ba, tun abunda ya faru a jiya take jin tsoron ƙara shigowarsa. haka ta sakko daga upstairs ɗin zuciyarta cike da tunani kala-kala. ta biyo ta corridor ɗin da zai fitar da kai ta baya, sai dai tana zuwa wajen ƙofa taja tayi turus tayi saurin laɓewa saboda abinda ta gani da kuma abinda take ji. tsabagen girgiza da Al'amarin bata san lokacin da ta zube a ƙasa ba tana saka hannu ta toshe bakinta gudun kar numfashinta dake neman tsarƙewa ya fallasata. ta rumtse ido da kyau cikin ranta tana ta adu'a Allah yasa kar a ganta, tayi shiru tana sauraron dukkan zantukan da ake yi, lokaci ɗaya ta ƙara girgiza taji kamar kunnenta ba daidai yake jiyo mata ba, cikin azama ta miƙe tabar wajen da sauri ta koma ta parlo ta bar side ɗin gaba ɗaya sai haki take yi. ta jima a compound zaune a wajen flowers tana ta mayar da numfashi, kafin ta iya miƙewa ta nufi part ɗin su Turaki, cikin sanɗa kamar wacce ke gudun wani ya ganta. tana shiga ta tarar da Khalil a parlo yana kallo, ta tsuguna ta gaida shi cikin rasa makamar abinda zata ce ya kawota. sai kuma taji Khalil ɗin yace,"ke Maama ta aiko?". da sauri ta ɗaga masa kai tace,"ehh". yace,"to kinga ba wani gyara ne me yawa ba, toilet kawai zaki wanke min kinji, yaron dake mana aiki ne bai da lafiya". ta miƙe tana cewa,"tom Hamma". Khalil ya bita da kallo har ta ɓacewa ganinsa, ganin yacca take tafiya kamar mara gaskiya. bata ɗauki lokaci ba ta kammala wankin toilet ɗin Khalil, tana gamawa kuma ta faɗa bedroom ɗin Turaki, da shigarta shima ta wanke nasa sannan ta kimtsa ɗakin gaba ɗaya, ta saka masa turare me ƙamshin gaske. kwalbar turaren dake kan dressing mirror ta ɗauka ta riƙe a hannunta, design na kwalbar yayi matuƙar burgeta, sai dai ƙamshin har yanzu bata ƙaunarsa, kamar wacca taga kashi haka take aikin yamutsa fuska still tana riƙe da kwalban, can kuma sai ta saki kwalban ya faɗi ya fashe, ya fashe a sanda take ƙara saka ƙasan takalminta ta murje kwalban sai ɓata rai take. ƙarar fashewar ya haɗe da rufe ƙofar ɗakin, ta ɗago kai da sauri tana kallon door ɗin sai ganin Turaki tayi ya jingina jikin ƙofar, ya rungume hannayensa a ƙirji yana kaɗa one leg. tsoro sai ya kamata ta dabarbarce tana ja da baya, duk ta rasa yacca zata yi da kuma abinda ya kamata tayi, taji kamar ta kurma ihu saboda yanda ya kafeta da ido yana kallonta fuskar nan a haɗe, alamar ya harzuƙa da ta'adin datayi masa. sai tai saurin duƙawa ta shiga tattara kwalban da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma tana toshe hancinta da shi, bata ankara ba kwalban ya shige mata cikin fata nan da nan jini ya fara zuba. cikin jin zafin ciwon ta furta,"wayyoo Kaka". ta faɗa tana yarfa hannu jinin na fallatsuwa a wani wurin. ganin yanda jinin ke fita sai kawai ta fashe da kuka tana faɗin,"wayyo jinina, wayyo Kaka, wayyo jinina zai ƙare". Turaki da har lokacin yake tsaye yana kallonta yana kallon jinin dake zuba, yaja tsakin takaici ya bar bakin ƙofar ya ƙaraso ciki. akan bed ya ajiye wayoyinsa sannan ya shige toilet, after 10mints ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa, ƙaramin dake hannunsa kuma yana goge sumar kansa da shi. ya kai idonsa wurin da ya barta yaga bata wajen, sai kwalban sai jinin da yaɓata wajen, ya ci gaba da goge kansa yana ƙarasawa bakin gadon ya zauna. ɗago da idonsa da zai yi ya ganta tsaye bakin ƙofa ta kama handle ta riƙe, sai aikin murɗa shi take yi duk tabi ta ruɗe, har lokacin kuma bata bar kukan ba haka kuma bata daina yarfar da hannun ba. da mamaki kawai ya tsaya yana dubanta, jinsa yake kamar ya tashi ya mammaketa don takaici. ta juyo da kanta a daidai lokacin da yake ƙoƙarin ɗauke kansa daga kanta, karaf suka haɗa ido, Turaki ya ƙara shan murr, ita kuma ganinsa babu riga yasa tayi saurin runtse ido tana ƙara fashewa da kuka. bayan Turaki ya saka kaya, ya dawo ya nemi waje ya zauna bakin gadon, ya ɗauki wayarsa yay dialling numbern Zaytuna. tana ɗagawa yace mata,"ki bada bandage a kawo min". yana faɗar hakan ya kashe. ya ajiye wayar sanda Fillo ta kira sunansa,"Hammah don Allah kayi haƙuri, jinina zai ƙare". tai maganar acikin kuka, ya galla mata harara ta ƙasan ido yana ƙara jin sabon takaicinta acikin ransa. jin ana knocking door ya taso yasa key ya buɗe ƙofar, ya karɓi box ɗin dake a hannun Ɗausiyya ya maida ƙofan ya rufe tare da ƙara sanya key sannan ya dawo ya zauna bakin gado. "zo nan". ya faɗa idonsa akanta. kamar ba zata zo ba sai kuma ta miƙe ta taho kamar me shirin faɗuwa, ganin cewar in taci gaba da tsayuwa a haka jininta duka zai tsiyaye. ta tsuguna a gabansa wurin da ya nuna mata, ta miƙa masa hannun ta runtse ido tana jan numfashi. ya kalli hannun ya kalleta sannan yace,"are you stupid?, kwalban ma da ya shiga ba zaki iya cirewa ba kika barsa a jikinki?, ke shashashan ina ce wai". cikin kuka tace,"to ai ba zan iya ba, jini ne yake fita". "jinine yake fita shine cire guntuwar kwalba ya gagareki?". ita dai bata ce masa komai ba banda kyarmar jiki da take yi, yaja dogon tsakin da yayi duka har cikin kunnenta, ya kamo hannun ya cire kwalbar sannan ya shiga treating mata ciwon, tunda yasa spirit ya goge jinin ta tsala uban ihu tana neman fincike hannun, hakan yasa ya riƙe hannun da kyau yanda ba zata ko iya ja ba balle ta iya fizga har ya ɗaure mata wajen da bandage sannan ya sakar mata hannun. zuwa lokacin tayi kuka ta gode Allah. muryarsa a tamke ba tare da ya duba irin zafin ciwon da take ji ba yace,"tashi ki gyaran waje, saura ki ƙara saka hannu tunda baki da hankali". ta miƙe sai sheƙar kuka takeyi ta ɗauko tsintsiya ta tattare wajen. tana kammalawa ta nufi ƙofa zata fita taji ya ƙara saka key ya kulle. "na gama ai". ta faɗa tana kallonsa a ɗarɗarce. ba tare daya kalleta ba yace,"kin san tsadar turaren da kika fasa?". da sauri ta girgiza kai tace,"a'a, amma don Allah kayi haƙuri bada sani na bane". ya ɗauke idonsa daga kan wayarsa ya ɗora akanta sannan yace,"balle ma da saninki kika fasa ɗin, dan haka abu ɗaya na san da shi sai kin biyani turarena, kuma a yanzun anan wajen ba sai anje ko'ina ba, if kika biyani sai ki sami damar fita daga room ɗin nan". maganarsa yasa ta ruɗe ta shiga ba shi haƙuri tana roƙonsa. tayi mugun basa tausayi amma ya ɗauke kansa kamar baya jinta. wucewar mintina biyar sai yaji shiru ɗakin, kukanta ya ɗauke kamar ɗaukewar ruwan sama, tun before ya juyo da kansa ya kalli bakin ƙofar ya fara tunanin ta yanda akayi ta fita after yasa key, sai dai yana juyowa ɗin sai ya ganta ta ɓingilar da kanta ajikin ƙofa baccin kuka ya ɗauketa kamar jaririya. zai iya cewa bai san lokacin da leɓensa ya tale da murmushi ba, banda yasan abubuwa da dama ba, to tabbas zai rantse wannan rigimammiyar yarinyar ba itace hatsabibiyar dake cusa kanta cikin haɗarin da ba nata ba. ya jima yana kallonta a hakan, matsawar ya barta ta ɗauki tsawon lokaci tana bacci a haka wuyanta sai yayi ciwo sosai saboda yanda ya barƙale, hakan yasa ya sakko a gadon yazo ya ɗauketa ya dawo ya kwantar da ita akan gadonsa, yaja blanket ya rufeta yana jin zuciyarsa na matsewa. for few minutes yana daga kishingiɗe ajikin pillow daga ɗayan side ɗin, tunani kawai yake yi kala-kala acikin ransa, daga bisani ya miƙe ya bar ɗakin, yana fitowa yaci karo da Bello na niyyar shigowa, ganin junansu yasa duk suka ɗaure fuska. Bello na ƙoƙarin ya ture shi ya shiga room ɗin, shima Turaki na ƙoƙarin ya turasa baya ya nuna masa hanyar da ta fi dacewa da shi. "Malami ban hanya". Bello ya faɗa cikin tamkewar fuska yana sa hannu ya ture Turaki gefe, ya murɗa handle ya shiga bed room ɗin. sai dai yana shiga ya fito da sauri yana dakatar da Turaki daga tafiyar da yake yi zai sauka daga benen. "Turaki me nake gani a ɗakinka?". a fusace Turaki ya juyo yace da shi,"uban wa ya kai ka shigar min ɗaki dama?". shima Bellon a fusace yace,"da sai da izininka nake shiga?, ko kuma dama Baffa ce yayi ɗakin naka ne kai ɗaya?...ba wannan ne a gabana ba Muhammad, faɗa min me na gani a ɗakinki?, warware min komai tun ban fara shakku akanka ba". Turaki yaja tsaki ya sauka a benen ba tare daya ce masa komai ba. Bello yayi ajiyar zuciya yana sa hannu a aljihu ya ɗauko wayarsa ya kira lambar Zaytuna. *Masarauta Kaltungo.* "nifa duk bayannan naki a banza nake jinsu, shekaru ba su zasu hanani cimma alwashin dana ɗauka ba Jakadiya, tunda har naga bayan Ramla to babu abinda zai hanani ganin bayan Madina, ki rubuta wannan ki ajiye, ko bayan raina zaki faɗa cewar ni Fulani nace duk wata mace da Dikko zai aura rayuwarta a hannuna take". furucin da Fulani tayi kenan a sanda idanuwanta ke sauka a ƙasa, tana jin zuciyarta na zafi da tafarfasa, tana jin yanda zuciyarta ke kuka, kukan da ta ɗauki tsawon shekaru masu yawa tana yi kuma har yanzu bata daina yinsa ba. ƙafarta kawai take kallo wadda tasha adon sarƙa na gwalagwalai da azurfa, kallon ƙafar tata take yi a zahirance, amma a baɗini ƙafar Alƙali Dikko take kallo, ƙafarsa take kallo tana tuno yanda ta riƙe ƙafafunsa a wancan lokacin tana roƙonsa akan kar ya rabu da ita ya aureta ko da bayan auren zaisa wuƙa ya kasheta, da kuma yadda ya fizge ƙafafunsa ya fita daga ɗakin ya barta ba tare da ya waigo ya kalleta ba, waigen kallon da bai ƙara yi mata ba har yau tsawon shekaru 37, duk da kasancewarta matar Yayansa Mai Martaba Hashim. ta rumtse idonta sosai tana jin zafi a zuciyarta, ganewa ne kawai mutane ba su yi ba, amma zafin so yafi ƙarfin kwatance, ita zata iya cewa zafin so yafi zafin wuta zafi da raɗaɗi, muddin wanda kake so bai bar tasirantuwa a zuciyarka ba. Allah ya sani har duniya ba zata taɓa daina son Alƙali Dikko ba duk da cewar akwai igiyar auren wani akanta, auren ma da har suke da rabon ƴa a tsakani, ƴa me shakaru 21 a duniya, son Alƙali Dikko ba daga gareta bane, so ne daga Allah. taja wani dogon numfashi ta sauke, a sannan ta buɗe ido ta sauke akan ƙaton tray ɗin dake gabanta. Jakadiya Haulat tace,"ranki ya daɗe ki ƙara haƙuri akan wanda kike yi, Allah ya huci zuciyarki uwar gijiyata...yanzu kamata yayi kisha furar nan domin ki samu kiji sanyi a ranki, tun safe babu abinda kika sa a bakinki...batun Hajiya Madina da Ɗan Ramla tamkar tsoma allura ne acikin ruwa, kisa a ranki lokacin kawar da su daga rayuwar Alƙali Dikko yazo ƙarshe, zasu barshi kamar yanda Ramla ta barsa". Fulani tayi murmushin takaici me ciwo, sannan ta ɗago ido ta yiwa Jakadiya kallon tsab kafin nan tace,"ban taɓa yin wani shiri akan Madina ba, kasantuwar nasan Dikko ba sonta yake ba, zatona a lokacin Mai Martaba zai sawwaƙe min daga nan sai na maye gurbin Ramla, ashe duk lissafin da nayi akan hakan da ƙazamin tunani nayi shi...dukkan wani shirina ina yinsa ne akan ɗan Ramla, shirye-shiryen da nayi akan na tarwatsa yaron nan yafi ƙirgen yatsu, sai dai har yanzu na kasa ganewa Jakadiya, na kasa fahimta, na rasa dalilin da yasa cikin tarin ƙullin da nayi akan Turaki babu wanda yay tasiri, amsa ɗaya nake so daga bakinki ba daga bakin boka ba, haka kuma abu ɗaya nake so na sani daga wajenki ba daga wajen boka ba, meke warware aikin Malam?, menene ke warware duk wani ƙulli da nayi?, waye yake lalata min dukkan shirin da nayi?". sai kuma ta miƙe tsaye a fusace, ta ɗaga murya cikin tsawa tana nuna Jakadiya tace mata,"faɗa min gaskiya, kina aiwatar da aikin da na saka ki ko kuma cin amanata kike yi?". cike da tsoro da rawa jiki Jakadiya tace,"wallahi, wallahi Ranki ya daɗe ina sawa a aiwatar da duk abinda kika ce, wallahi kuma ko kaffara ba zanyi ba waɗanda na saka suyi ba zasu ci amanarmu ba, ni kaina ina matuƙar mamakin yanda komai ke warwarewa acikin sauƙi, sai dai ina tunanin ƙarfin adu...". ai tun Jakadiya bata ƙarasa ba Fulani ta ƙara ɗaga murya wajen dakatar da ita acikin tsananin fushi da ɓacin rai,"dakata munafuka, tabbas sai naga bayanki Jakadiya domin babu wanda yake cin amanata na ƙyale shi...karki ƙara buɗe baki kice zaki faɗa min zancen banzan da ba yarda zanyi da shi ba, ƙarya kike yi kice tasirin adu'a zai karya aikin asirin da nake ɓarnatar da kuɗi akai, aikin boka tumbutsu ne ba aikin wani galhonaho ba, bokan da yake aiki tamkar yankan wuƙa, kuma tunda har aikinsa yayi tasiri akan Ramla ƴar Turakin Taraba, bana tunanin aikinsa zai ƙi cin wani tsiyatattan halitta Turaki, don haka kamar yanda na ɗauki alwashin ganin bayan Madina da Turaki a wannan ƙarnin, haka kema sai naga bayanki Jakadiya tunda har kika ci amanta". Jakadiya ta zube gwiyoyinta a ƙasa ta shiga roƙon Fulani cikin tsananin ruɗewa, ana cikin haka Ilham ta turo ƙofar ɗakin ta shigo. cike da shagwaɓa ta faɗa jikin Fulani ta sakin kuka da cewar,"dan Allah Mami ki barni naje, Allah ba zan jima ba zan dawo...sau biyu kenan Hammah Turaki na ciwo bana zuwa na duba shi, kuma yana ta min complain ɗin hakan". Fulani ta tureta daga jikinta, ta fita rai a ɓace daga turakar tata. Ilham ta buta da kallo kafin daga bisani ta zube akan gado tana sakin kuka. tana cikin kukan wayarta ta shiga ringing, ta ɗau wayar tana kallon screen ɗin, ganin sunan Turaki na yawo a jiki yasa ta sakin wani kyakykyawan murmushi sannan ta ɗaga tana cewa hello cike da shagwaɓa. daga ɓangaren Turaki ya sauke ajiyar zuciya sannan yace,"ba ki damu da lafiya ba right?". Ilham ta ƙara narkewa da muryar shagwaɓa tace,"Hammah yau zan zo insha'Allah". Turaki yace,"ba sai kin zo ba, ni gani na zo. ina ɓangaren Abbas...but ba zan jima ki hanzarta". *_Wallahi duk son reader da ƙaguwar ai typing baku kama ƙafar yanda writer ke ƙaguwar tayi typing ba, haka kuma baku kaita ƙaguwar tayi tayi ta kammala book ɗinta ba. amma har yanzu na rasa me yasa some readers kuke kasa yiwa writer uzuri idan bata yi posting

Chapter 23 of 73