babu yanda Hajiya Ramla ba ta yi da ita ba but ta kasaci kwata-kwata, ciwon kan da taji ma yana damunta sosai sai ta miƙe ta koma ɗakinta, Fillo ta ɗauki flask ta bi ta.
"Daughter ya ba ki zauna cin abincin ba?".
Fillo ta ƙaraso ciki ta ajiye abincin, sannan ta kamo hannun Hajiya Madina ta ce,"don Allah Maama ki sauko kici ko kaɗan ne".
haka ta dinƙa roƙonta har sai da Maama ta sauko, da kanta ta riƙa ba ta abincin tana ci, ba ƙaramin daɗin hakan taji ba, kuma Fillo ta ƙara samun wani gurbi acikin zuciyarta, ta ƙara yin farin ciki da jin alfahari a game da dacen mata da Me Babban suna yayi.
and sosai taji daɗin hirar da Fillo take yi ma ta, sai wajen ƙarfe 9 sai ga Turaki ya shigo ɗakin, kallo ɗaya Fillo tayi masa ta ɗauke kanta, ya shigo ya zauna a gefen Maama yana kama hannunta ya riƙe.
"my happiness ya sauƙin jikin?".
Hajiya Madina ta kalle shi cike da so da ƙauna ta ce,"na ji sauƙi me babban suna, ya office?".
"masha'Allah, Allah ya ƙara miki lafiya, Zaytun ta ce min Bp ɗin ya koma normal".
"ai na faɗa maka na ji sauƙi, ɗa zu ma da kayi ta kira bacci na sa mu".
ya sauke numfashi ya ce,"insha'Allahu za ki rabu da ciwon nan Maama, ciwon nan yana takura ni da yawa".
"to Allah yasa, amma ka san girma ya riga ya kama mu, lafiyar sai a hankali, sai dai ai tayi mana adu'a ciwo ya dinƙa zuwa da sauƙi".
sai kuma ta lura da yanda Turaki ya ƙurawa Fillo ido, ita kuma kanta yana ƙasa tana matsa mata ƙafarta ta ɗaure fuska.
sai tayi murmushi tace,"Daugher ina fatan dai baku da wata matsala ko?".
Fillo tace,"ehh Maama babu".
"to Allah yayi maku albarka, ubangiji ya wanzar da zaman lafiya na har abada a tsakaninku, Allah ya kauda mugun ido akanku".
a tare suka amsa da amin.
sai ta kamo hannayensu duk ta haɗe a waje ɗaya tana cewa da Turaki,"me babban suna ina roƙonka da kar Fillo ta rasa farin ciki ko da na sakan ɗaya daga wurinka, amana na baka ita, ka kula min da ita don Allah kaji, tayi min taimakon da ba zan taɓa iya biyanta ba, thats why nake so ka raineta da zallar soyayyarka, ka mayar da ita tamkar jaririya".
ya shafo wuyansa bai iya cewa komai ba. sai ta dubi Fillo ma tace mata,"Daughter ɗago ki kalle ni karki ji kunyata".
Fillo ta kasa har sai da Hajiya Madina tasa hannu a haɓarta ta ɗago fuskarta ta ce,"yaushe za'a haifa min jika?, a yanzu banda burin da ya wuce naga jikana Daughter, so nake na ga ina wasa da jikokina, ina fatan za ki samar min su da wuri".
kunya ta kama Fillo sosai.
"Allah dai ya kawo mana na gari masu albarka". cewar Hajiya Madina.
cike da zolaya kuma ta ƙara cewa,"kyawawa nake so ki haifa min masu kama da ke fa, kar ki yarda su yi kama da Me Babban suna, shi wani lokacin kamar bai da kyau".
duk suka yi dariya ba tare da sun ce komai ba.
ta ƙara cewa,"Allah Daughter duk ranar da Me Babban suna yayi miki laifi ki zo ki faɗa min wallahi sai na rama miki, kinga haka...". Fillo ta ɗaga ido taga yacca ta kama kunnen Turaki.
"to haka zan murɗe shi wallahi har sai yaji a jikinsa". Fillo tayi ƴar dariya shi kuma ya wurga mata harara fuska a cukule.
kafin nan tace da su,"to ku tashi ku tafi ko, dare yana ƙara yi".
Fillo tayi saurin cewa,"Maama don Allah zan kwana anan".
ta faɗa a marairaice.
Maama tace a'a ta tashi tabi mijinta su tafi, har ƙwalla sai da tayi da suka baro wajenta, sai da suka biya ta wajen Mum suka yi ma ta sallama kafin su tafi.
a compound juyin duniya Fillo taƙi yarda Turaki ya kama hannunta, bata yarda ma sun jera ba ganin babu idon kowa, tayi gefe yay gefe, suka shiga mota ma taƙi kallonsa, sai faman ɓata rai take yi tana cin magana.
da tsokana ya ce,"kika ce ba za ki dawo gidan ba".
ta kalle shi sosai kafin ta ce,"da kayi ignoring message ɗin nawa hakan ai bai sa na damu ba".
tun yana tsokanarta har ya rabu da ita saboda ganin ta ɗauka zafi, a lallai fushi take da shi kan ƙin responding messages na ta.
ya koma sai dai ya kalleta yay murmushi ya shafo wuyansa, shi ba abin da ma yake so irin ta kula shi suyi rigima, tayi kuka ko tayi masa tsiwarta.
motar tayi shiru ba abin da kake ji yana tashi sai busawar ac da kuma sautin waƙar i miss you ta Beverley craven.
_here in a silence i wait, there is nothing else i can do, it feels like my heart gonna break, and all i can think of is you, and how my aching arms long to hold you, and show you how much i care, but i'm couting the hours without you, and i don't know how much i can bear, becox i miss you morethan word can say, all i need you here in my life always, yeah i miss you, till you are back with me._
waƙar ta dinga bin gaɓoɓin jikin Fillo tana ratsata, ta kalle shi ta wutsiyar ido taga ya wani sha murr kaman ba shi ke tsokanarta ɗa zu ba fuskarsa a washe da annuri, wanda ta tabbatar na jin daɗin ganinta ne.
sai ta ɗan murguɗa baki kamar yana kallonta kafin ta kai hannu ta kashe waƙar, tana ɗauke hannu yana ƙara kunnawa, zata ƙara kashewa taji muryarsa a tamke yace,"ranki zai ɓaci".
"to bana son jin waƙar ni".
yay mata wani kallo yace,"motarki ko tawa?".
ta haɗe gira tace,"ba yanzu aka gama baka amanta ba, aka ce kayi min duk abin da nake so".
murmushi ya suɓuce a leɓensa, ya tuna alƙawarin da yaywa Maama na kula da Fillo tun ba'a ranar yau ba, ya tuna girman alƙawari, sai ya kai hannu ya kashe waƙar.
sai ya koma yi da kansa, Fillo taji waƙar tafi daɗi sosai a bakinsa, sai ka rantse shi ya raira, ta lumshe ido tana ta sauraronsa, har su ka zo gida bata sa ni ba sai da ya danna horn da ƙarfi sannan ta buɗe ido.
"a sauka a miƙo kuɗin mota".
ya faɗa a sanda take ƙoƙarin buɗe ƙofa zata fita.
ta juyo ta ɗan kalle shi tace,"in doller or in naira?".
"in doller".
ta gyaɗa kai kafin tace,"to driver you wait for me".
Turaki ya buɗe baki galala, zai kamota tayi saurin ficewa tana dariya, shi ma ya fito ya bi bayanta da sauri don ba ya so ta riga sa hawa upstairs becx akwai suprising ɗinta da yake so yayi.
a parlo ya sameta su na gaisawa da su Sakina, waɗanda suke kallo a parlo, su na yi mata sannu da zuwa, ita kuma tana ba su haƙurin tafiyar da tayi bata sanar musu ba.
bai ko amsa gaisuwar da su Hannatu su ke masa ba ya kama hannun Fillo su ka ɗauki hanyar upstairs, a steps na uku da su ka taka yasa hannu ya rufe ma ta ido.
ta san duk neman hanyar su shirya ne don haka sai taƙi kula shi har sanda taji ya buɗe ƙofar ɗaki sun shiga.
ƙafafunta suka lume cikin marbles, da sanyin ac'n da ke ratsawa ta ko'ina acikin ɗakin, kafin daddaɗan ƙamshin nan nasa dake motsa zuciyarta ya shiga hancinta, taji san da ya maida ƙofar ya rufe, kafin ya sauke hannunsa a hankali daga idonta ya mayar kan ɗan ƙaramin ƙugunta, tare da ɗora haɓarsa a saman ƙafaɗarta.
"suprise". hakan ya faɗa before ta shiga buɗe idanunta a hankali.
ba ta san lokacin da ta buɗe idanuwanta duka ba, laɓɓanta suka tale kafin bakinta ya buɗe, fuskarta kuma ta bayyana wani irin farin ciki da jin daɗi.
ƙananun bulbs ɗin dake haskawa zuwa different colours of light su suka fara shiga idonta, kafin baloons ɗin da akai design da heart shape ta ɗauki hankalinta, zuciyarta kuma taji ta motsa da zafin ƙauna a lokacin da ta ɗora ido akan flowers ɗin da aka baza akan gado.
gaba ɗaya sai ta kasa magana balle motsi saboda yacca abin ya burgeta, sai ta fara bin kowacce kusurwa ta ɗakin da kallo, ta san ɗakin, wan nan ɗakin ne da suke rayuwa ita da Turaki a cikinsa, kuma wan nan lafiyayyan gadon me ɗauke da flowers, gadon su ne me ɗauke da katifar nan me bala'in taushi da suke kwanciya akai manne da juna, but ta ya akayi yau ya sauya?, azababben decoration ɗin da aka yi masa ya mayar da shi tamkar ba wannan ɗakin da suke yini acikinsa ba.
_me hakan yake nufi?._ tambayar da zuciyarta tayi kenan, kuma sai taji hannayen Turaki sun kama fuskarta sun karkartar da ita zuwa gaban body mirrow dake gefe ɗaya, ƙwayar idonta ta tsaya cak akan ballon numbers ɗin da aka jera me ɗauke da 1 and 9 making 19, a hankali kuma idonta ya sauka akan ƙaton cake ɗin dake kewaye da candles.
muryar Turaki tayi whispering acikin kunnenta da faɗin,"Happy Birthday to you Fulani Nah".
she was just astonished, ta juyo ta fuskance shi tana faɗin,"my birthday?".
ya jijjaga ma ta kai alamar ehh. with great joy tace,"but how do you know Turaki?, i don't think there is anyone who knows my birthday date".
ya ce,"har Ummi?".
tayi ɗan shiru tsananin farin cikinta na kasa ɓoyuwa ta ɗaga masa kai.
ya daɗa kama ƙugunta yace,"to Ummi ce ta faɗa min, tace ta haifeki a ranar da Yayarta ta rasu shiyasa ba zata manta da date ɗin ba, you are 19years older now, Kaka ce take lissafi ba daidai ba".
ta juya ta ƙara kallon yanda aka ƙawata kyan ɗakin.
"and all this becouse of my day?".
"yes! domin farin cikinki kawai".
ya faɗa yana sumbatar kumatunta.
hawaye su ka saukowa Fillo ta juyo tayi masa wani irin tight hug.
ruwan hawayen ya ɗiga a bayan Turaki, ɗuminsa ya wanzu acikin fatarsa, yasa nasa hannun wurin kewayeta yana shafa gashin kanta, ya ce,"why the Cry Fulani Nah?, i did everything just to make you happy not to make you cry, please stop crying let us celebrate the day".
ta ƙara fashewa da kuka tana ƙara rungume shi.
"you totally suprised me!, am so blessed and honored to have you, thank so much you for making my birthday so special. You made me feel like a princess and gave me the best gift anyone could ever receive. You are my best friend and I love you more than anything in this world! Thank you for making my day special with your love, care and amazing surprises. i am so lucky to have a wonderful husband like you".
ta sake shi tana haɗe goshinsu wuri ɗaya,"Allah yaja da ran mahaifanka, Allah yasa ka rabu da su lafiya, Allah ya ba ni ikon faranta maka nima".
ji tayi ya ɗagata sama yana hajijiya da ita yayin da suke rera waƙa tare, waƙar da ita bata iya ba sai in yayi sai ta kama, a haka ya dinƙa zagaye da ita acikin ɗakin har sai da ta fashe duk baloons ɗin da aka ɗaura.
kafin ya sauketa ya kama hannunta suka ƙarasa gaban cake, ya zauna a kan ƙaramin carpet ɗin dake shimfiɗe a wajen, sannan ya zaunar da ita akan ƙafafunsa da ya tankwashe.
tare suka yi cutting cake ɗin, ta ciro ta kai bakinsa, har ya buɗe bakin sai ta fasa saka masa ta janye tana ƴar dariya, tasa a bakinta tana faɗin ba zai ci ba.
ta ƙara yanko wani zata kai bakinta sai ya juyar da hannun ya saka a nasa, sai da ya fara taunawa sannan ya kai bakinsa nata ya ɗaga ma ta gira.
tayi ƙasa da idonta sannan ta buɗe bakin, yasa bakinsa cikin nata ya zuba mata taunannan cake ɗin, a lokaci ɗaya tayi differenciating tsakanin daɗin yawunsa da cream na cake din.
ta lumshe ido tana taunawa a hankali, yayin da Turaki ke yawo da hannunsa cikin rigarta, ya kwantar da kansa a kafaɗarta yana faɗin,"Maama tace tana son ganin jikokinta, tana so tayi wasa da su".
ya murza tafin hannunta ya ƙara cewa,"yaushe za mu samar ma ta su?".
Fillo tayi murmushi tare da ɓoye fuskarta a saman sumarsa.
ya mayar da hannunsa fuskarta ya shafo sajenta,"ki amsa min don in san lokacin da zan ƙara ganin farin cikinta ya ƙaru".
"ni ma ban sa ni ba". ta faɗa in a cool voice.
yay murmushi tare da ɗago fuskarta yana kallonta.
"if you are ready we will get them today".
tayi saurin girgiza masa kai,"not today".
"then when?".
tayi shiru ba tare da amsa masa ba.
sai ya sauke numfashi yace,"ba kya tunanin nayi haƙuri da yawa kuma ina kan yi?".
ta marairaice murya cike da tsoron da ya fara kamata tace,"ai kai mai haƙuri ne, ka ƙara yi".
bai yi magana ba ya ɗauko wani card ya bata, ta karɓa ta buɗe ta shiga karanta abin da ke ciki.
_On your birthday, I want to remind you that you are special, not only to me but to all those who are privileged enough to know you for the amazing person you are. People like you are hard to come by, but getting to have a wife like you is indeed a gift.. Happy Birthday Fulanin Turaki, wishing you a long life and prosperity._
wani sanyayyan murmushi ya suɓuce ma ta, ta kai laɓɓanta saman goshinsa tayi kissing, ta ce,"tanx, really appericiate".
martanin murnushin ya mayar mata, sannan suka saka cake ɗin a gaba suka yi masa cin yunwa.
mutumin da baya shan choculate sai ga shi yay damalmala bakinsa da choculate wajen sha.
bayan sun gama cin cake da shan choculate suka miƙe daga wajen, kwatakwata Turaki bai bari ta fahimci rashin jin daɗin da yake ciki ba.
suka shiga toilet tare don yin brush, Fillo tace masa tana so tayi wanka, ya fita ya barta aciki, ɗakinta yaje ya ɗauko ma ta kayan da zata saka.
after 10minutes Fillo ta fito daga wankan, sai dai lokaci ɗaya ƙirjinta yay wani mugun bugawa ganin Turaki duƙe a ƙasa ya riƙe cikinsa yana wani irin nishi.
siraran ƙafarta suka jata cikin sauri ta ƙarasa gabansa, ta tsuguna tare da ɗora hannunta saman sumar kansa sannan ta kira sunansa.
sai dai a wannan lokacin baya jin zai iya amsa ma ta balle ya iya ɗagowa ya kalleta, duk jikinsa rawa yake yi tamkar me jin sanyi, after all ɗakin lulluɓe yake da ɗumi me daɗi.
cikinsa ne ke yi masa ciwo sosai, irin ciwon cikin da bai taɓa yi ba, wani irin ciwon ciki ne da yake jikin tamkar numfashinsa zai tsaya cak.
yanayin nasa yay bala'in gigita Fillo, tuni idonta ya kawo ruwa ganin yacca yake shuri da ƙafafunsa a ƙasa, gaba ɗaya jikinta sai ya ɗauki rawa kwatankwacin yanda nasa ke yi.
duk sai ta nemi dabara da wani tunani acikin kanta ta rasa, ta kasa magana ma ballanta ta tambaye shi me yake damunsa, and bata san me zata yi masa ba.
cikin karkarwar hannu ta ɗago kansa daga duƙen da yake, hawayenta ya ɗiga a saman fuskarsa, ya buɗe idanuwansa da suka sauya kala ya dubeta.
ta fashe da kuka tana tambayarsa me ya faru da shi?.
da ƙyar ya iya buɗe baki yace ma ta,"cikina Fulani".
a hargitse ta ce,"ciwo yake ma?".
kansa kawai ya iya ɗaga ma ta.
"ko cake ɗin da muka ci ne?".
nan ma bai iya cewa da ita komai ba, ta tashi a rikice taje ta buɗe drower ta kwaso drugs ɗinsa, sannan ta fita da gudu ta sauka ƙasa ta ɗauko ruwa ta dawo.
lokacin da ta dawo ya kwanta a ƙasa yana murƙusus, ta dawo ta ɗago shi da ƙyar, jikinsa duk ya jiƙe da gumi, kuka kawai take yi a lokacin ta kasa cewa komai.
"buɗe bakinka kasha magani". ta faɗa cikin muryar da ta dusashe da kuka.
sai ya buɗe idanuwansa ya dubeta a cikin gigitar ciwo da neman fitar hayyaci, ya manna kansa a cikinta gami da cusa fuskarsa a ƙirjinta.
ƙamshin turaren da tayi wanka da shi ya ƙara motsa ciwon nasa, sai ya damƙo hannunta cikin kyarmar jiki ya ɗora a mararsa ya danna.
lokaci ɗaya taji ya kanainayeta ya ƙanƙameta, ƙanƙamar da taji tamkar zai ɓalla ƙasusuwanta, ƙanƙamar da ta hanata motsi ko kaɗan.
hankalin Fillo ya ƙara tashi, cikin firgici ta buɗe baki, murya na rawa ta fara ce masa,"ga maganinka na ɗauko, don Allah ka tashi ka sha, i don't want to lose you".
Wani irin rumtse idanu Turaki yayi saboda azaban murɗawar da mararsa ta ƙara yi, ya daɗa ƙanƙameta tare da ƙara danna hannunta a saman mararsa.
Fillo ta ƙara fashewa da kuka tana faɗin,"in kira Maama?, ban iya driving ba in kira Adda Zaytun?, ko Bello zan kirawo?, in je in faɗawa Baba me gadi?".
tai maganar duk a gigice tana ƙoƙarin zare shi a jikinta taje ta ɗauko wayarsa.
sai ya kai hannunsa zuwa wuyanta, ya sunkuyo da kanta yana ɗago da fuskarsa daga saman boobs ɗinta da ya cusa.
muryarsa a shaƙe tamkar ba tasa ba yace,"Don't call any body Fulani".
"no i have to, you are in critical condition, you have to see a doctor, let me call Ya Yusuf".
ta miƙe taje ta ɗauko wayarsa, already akwai finger print ɗinta akai, hannunta banda kyarma ba abin da yake, tama rasa yanda za'ai tayi operating wayar.
taji ya kamo hannunta yana repeating mata cewa kar ta kira kowa.
"don't call any body Fulani, i don't need to see doctor, you can take care of me, the medicine is with you".
"to me zan maka?".
"i just need you Fulani, i need you very badly, please let me have you today".
ta ƙanƙame hannunsa, hakan ya ba shi tabbacin bata gane nufinsa ba, yana numfashi sosai yace,"ina so in kusance ki, ina so muyi mu'amala ta auratayya, don Allah kar ki hanani kusantarki a yau, idan ba haka ba zan mutu, surely you will lose me".
"to hakan shi zai sa ka sami lafiya?".
idanuwansa a lumshe ya ɗaga mata kansa.
Fillo ta rumtse ido sosai sabon hawaye na sakko ma ta, tare da jan wani irin gwauron numfashi, kana cikin tsananin harbawar da zuciyarta ke yi ta daɗa sunkuyo da kanta, ta haɗe fuskarta da tasa.
numfashinsu ya gauraya, wani dunƙulen yawu ya wuce ta maƙogoronta da ƙyar, cikin bala'in harbawan da zuciyarta ke yi ta ɗaura lips ɗinta saman na shi a hankali.
a hankali ta shiga shan lips ɗinsa kamar yanda ya koyar da ita.
numfashin Fillo ya fara rawa saboda tsoro da ke cikin ranta, tayi ƙoƙarin zare bakinta don dakatarta da abin da takeyi, but sai taji ya ƙanƙameta tabbacin baya so ta katse.
bata ankare ba sai ganinsa tayi ya miƙe zaune still bai raba bakinsu ba, a yanzu kuma shi ya shiga shan lips ɗin nata cikin salon da ya fara aika saƙo cikin ƙwaƙwalwarta.
ta fara kuka a hankali tana so ta zare bakinta, ya damƙeta da kyau yana girgiza ma ta kai,"a'a Fulani".
san da yay pressing lips ɗinsa on her boobs zuciyarta ta ambaci sunan Allah.
tunaninta ya tsaya cak, taji yawun bakinta ya bushe kamar bushewar famfo, sannan taji kamar tana neman ta suma.
"Please Fulani Nah...".
haka taji kamar ya faɗa, but sai ta gaza fahimtar komai balle tayi komai ɗin da yake so.
wucewar daƙiƙa ɗaya taji yana neman ɗauke bakinsa, da sauri tasa hannayenta a gaban rigarsa ta dawo da shi.
jikinsa na rawa kamar mazari ya ɗauketa idanuwansu duk a rufe, amma a haka ya ƙarasa gado ya kwantar da ita yana zare towel ɗin jikinta a zafafe yayi wurgi da shi.
tuni kukanta ya ƙaru, but bata tunanin a yanzu zata iya hana shi duk yanda ya so yayi da ita, domin ita kanta ta fara jin daɗin yanayin na su, abin da yake buƙata ita ma shi take buƙata a yanzu.
Fillo ta lumshe idanu jin skin ɗinsa ya haɗu da nata, haɗuwar da tasa Turaki ƙara burkicewa, gently ya shiga shafa jikinta ya fara yi mata wani salo, wannan salon nasa shi ɗaya, salon da taji yana neman ɗaukarta ya kaita saman gajimare.
a san da taji hannayensa a waji waje da bai taɓa zuwa ba, a lokacin numfashinta ya fara katsewa, tasirin abin da yake aiwatarwa na bin kowacce jijiya ta jikinta. wani abu yake yi mata da bata taɓa experiencing ba tun da ta zo duniya.
cikin wata iriyar murya taji yana faɗin,"help me, Fulani help me please".
a wannan lokacin kuka sosai Fillo ke yi, so take ta hanasa zuwa inda yake ta rawar ɗarin ya shiga amma sai taji ta kasa, roƙo da magiya kawai take yi akan ya ƙyaleta amma sam Turaki bai san tana yi ba.
daga lokacin da taji ya fara adu'ar saduwa da iyali, daga lokacin firgicinta ya ƙaru, ta daina ji ta daina gane komai, domin abin da yake shirin yi ya shallake tunaninta, ba irin wannan abun da yay ma ta bane wancan ranar, duk yadda ta tsammaci abun ya wuce tunaninta, motsi wannan ta kasa balle ta samu ƙarfin ture shi, sunan Ummi da Kaka da Maama da Mum da shi kansa ɗin kawai take aikin kira akan su zo su ceceta.
and cikin abin da bai fi ƙiftawar ido ba Turaki ya rabata da virgin ɗinta, ƙofar da sai da ya sha baƙar wahala kafin ya shigeta, lamarin da yay kacakaca da duk wani lissafi da tunanin Fillo.
abu ɗaya ne ta san da shi, wanannan daren, wannan abun da ya faru, abubuwa ne da za su kasance a cikin ƙwaƙwalwarta, ɓangaren tunaninta, wurin da ba za su taɓa gogewa ba har abada.
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*56*
agogon dake manne a bangon ɗakin, tsintsiyar jikinsa ta kaɗa cikin sautin dake ba da ƙarar ɗil, ɗil, ɗil. sakanni 1,2,3 su ka wuce kafin ya shiga bugawar daƙiƙu 1,2,3 har zuwa biyar.
sautin ƙarar ya shiga cikin kunnuwan Turaki kaɗai, kuma a wannan lokacin komai ya lafa, komai banda sautin kukan Fulani da ke tashi.
dogayen gashin idon Turaki su ka ɗaga, kafin murfin idanuwansa su ka buɗe, ya waiga ya kalli Fillo, ya rungumota tsam a ƙirjinsa, numfashi kawai yake saukewa tamkar wanda yay tseren gudu tun daga china, magana yake so ya yi but sam ya kasa, ji yake tamkar yau ne rana ta farko, kamar today is the first day he knows the virginity of a woman in his life, sai ya lumshe idonsa, abu ɗaya ne yake da akwai, daɗin wannan ya fi wancan.
yana jin yanda hawayenta ke sauka a jikinsa, sautin kukanta na fita ɗauke da tsabar wahala, hawayen da suka wanzar da wani bala'in tausayinta a ransa, ya ɗago hannu da ƙyar zai goge mata hawayen sai yaji ta ture hannun a zuciye.
ya buɗe idonsa ya kalleta sai yaga idonta a rufe yake, sai uban hawaye dake silalowa ta gefen idonta kamar an kunna famfo, da ma ya lafiyar kura balle an taɓota, yay wani irin murmushi da zai iya cewa bai taɓa yin irinsa ba, ƙara tsamketa yay a jikinsa har sanda baccin wahala ya ɗauketa.
kissing lips dinta yay kafin ya zare ta daga jikinsa, ya sauka akan gadon yaje ya kunna fitila don baya jin lamp ɗin dake kusa da gadon iyaka haskenta zai wadatar da shi wajen kallonta.
ya kalli agogo yaga ƙarfe ɗaya da rabi, dawowa yay ya zauna, yay tagumi yana kallon fuskar Fillo da tayi jawur kamar jini zai fito, dogayen gashin idonsa suka ƙifta a hankali, ya kamo hannunta ya riƙe yana kallon fuskarta da tayi looking so innocent.
hawaye duk ya bushe a fuskar, wani irin azababben sonta da ƙaunarta yaji su na fuzgarsa, ya san yana son ta tun a lokacin da bai san ya kamo ba, but a yanzu sai yake jin tamkar wani sabon son nata aka dasa a zuciyarsa, gaba ɗaya ta gama mallake zuciyarsa a yau, he was in a state of indescribable joy.
ya san yayi farin ciki da yawa a rayuwarsa, iyaka adadin farin cikin da ba zai ƙirgu ba, but bai taɓa tunanin cewa akwai wani farin ciki a duniya na daban ba kamar wanda yake ji a yanzu, sai yanzu ya shaida farin cikin duniya daban, haka ma farin cikin aure tare da wadda kake so daban.
kallonta yake yi tamkar yau ya fara ganinta, sai ƙyalli take yi, she looks so gorgeous and affectionate.
ya ɗora yatsansa saman lips ɗin ta da ta turo gaba ta taɓe su, yay murmushi, in ban da bacci take yi ya san dole ma sai tayi masa tsiwa.
ƙarfe uku da rabi hannun Fillo ya miƙe ya sauka akan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 63 Chapter of 73