a bisa wanne dalili Ramla?, wace ke?".
Mum tayi murmushin takaici tace,"wace ni kake tambaya Dikko?, har ka manta shekaru 33 baya da na tsuguna na haifa maka yaron cikin tsananin wahala?, tunda ka manta bari na tuna maka, ni ce wannan matar da ta ɗauki cikinsa tsawon wata tara, na raini cikin da wuya bata daɗi ba, na kuma haife shi acikin mawuyacin halin da kai kanka kake tunanin ba lallai na rayu ba, na shayar da shi tsawon shekaru biyu, na ci kashinsa na sha fitsarinsa, ka tuna wacece ni ko kuma dai still na tuna maka?, to ni ce mahaifiyarsa, ni ce wannan uwar da ubangiji ya faɗeta sau uku kafin ya faɗi uba sai ɗaya tal. ka san kuwa da cewar ni ɗin bata wasa ba ce, ina da ikon sawa ina kuma da ikon hanawa ko ana ko ba'a so muddin ana so a gama da duniya lafiya, so banga dalilin da zai sa abi a takura rayuwar yarona ba, yayi biyayyar amma hakan duk bai yi muku ba, ya kuke so yayi da ransa?, so kuke sai ya faɗi ya mutu tukunna?, tunda har yay biyayya ya auri zaɓinku ku barsa ya auri zaɓinsa mana, amma son rai duk ya hanaku kuyi masa adalci, to ni nasa ya saki amaryarsa zai kuma tare da uwar gidansa kamar yanda zuciyarsa take so, kamar yanda hakanne zai zama farin cikinsa da kwanciyar hankalinsa".
ta ƙara kallon Baffa da kyau tace,"dan Allah ka samawa yaron nan lafiya haka nan, iyakar biyayya yai maka, wadda tun da ka haife shi yake yi maka har kawo yau bai taɓa bijirewa umarninka ba".
Baffa ya ɗaga muryarsa,"shutup Ramla".
ya juya yana kallon Turaki yace,"ban goyi bayan ka rabu da kowacce acikin su ba, amma ka mayar da matarka yanzu anan, idan ba haka ba nayi mugun saɓa maka".
still kan Turaki na ƙasa bai ɗago ba, Mum tace,"wallahi tallahi sai dai idan bana numfashi amma ba zai mayar da ita a yanzu ba, yanda kake bin umarnin mahaifiyarka saboda ka gama da duniya lafiya, shima ka barsa ya bi umarnin tasa mahaifiyar saboda ya gama da duniya lafiya, yanda kake gudun fushin taka mahaifiyar haka shima, yanda kake so ka haɗu da ubangijinka lafiya shima haka yake so, haba Alƙali ka bar yaro ya huta mana ko so kake sai kasa masa ciwon zuciya duk saboda kai baka so ka ɓatawa taka mahaifiyar".
ta mayar da idonta kan Turaki da tsananin tausayinsa tace,"Babana ta shi kaje".
ya miƙe jiki ba ƙwari zai wuce Baffa yace,"daga yau na haramta maka shigowa gidana, kar in sake ganin ƙafarka a ƙofar gidan idan kuma ba haka zaka sha mamakin abinda zan maka, fitaaa a gabana". ya ƙarasa maganar a tsawace wadda har sai da ta tsorata su Maama.
Turaki yay saurin ɗago kai yana dubansa, zai yi magana Mum ta tari numfashinsa da cewa,"je ka Babana, Allah yayi maka albarka".
Turaki ya fice yana jan ƙafafunsa da yake jin kamar ba zasu ɗauke shi ba.
yana fita Hajiya Ramla ta dubi Boejo tace,"ina ƙara baki haƙuri, Allah ya huci zuciyarki". sannan ta kalli Baffa tace da shi,"kayi haƙuri your highness".
bai ko kalleta ba ya durƙusa gaban mahaifiyarsa yana bata haƙuri tare da lallashi.
Hajiya Madina ta ɗauki wayarta ta bar wajen ranta fess, tayi upstairs tana danna kiran lambar Ummi, tana yin picking bayan sun gaisa take shaida mata cewa,"Ummin Fillo insha'Allahu ranar litinin zamu kawo lefe".
Ummi ta amsa da,"Allah ya kaimu".
daga haka suka yi sallama.
ɓangaren Turaki kuwa yana zuwa compound kiran wayar Dada ya shigo wayarsa, kamar ba zai yi picking ba sai kuma ya ɗaga, abinda ya tsammata shi ɗin ne ya faru, dan yana sakawa a dodon kunnensa ya ji ta da masifa tana cewa,"ka sakar min jika ko kuwa?, ka san Allah kar ka bari in muku ɗanyen kai".
muryarsa ta fito kamar ta mara lafiya da cewa,"Dada in tana kusa ki bani ita sai na faɗa mata".
a harzuƙe tace,"ka faɗa mata me?".
yace,"shi abunda kika ce".
tace,"wai sakin?".
yace,"ehh".
tace,"haba yaro aini ba ƴar yau ba ce, kaje ka tambayi tarihina na fi son komai za'ai ayisa da hujja, dan haka furtawa da baki kaɗai ba zai gamsar da ni ba, ba kuma shi tabbatarwa da jama'a kayi ba, saki a rubuce nake so kayi shi cikin farar takarda ka yo min aikensa".
a hankali yace,"shikenan Dada, ina kan hanya yanzu zuwa gida, idan naje zan rubuta insha'Allahu".
tace,"ya dai fi, a sakar min jika dan bazan kawota gidan da za'a ke ma ta kallon banza ba"
ta kashe wayarta tana ta jaraba akan Fillo dake kwance kan gado tana aikin kuka tun ɗazu.
Ilham na kwance a ɗaki hadimanta na matsa mata ƙafa Turaki ya shigo kamar an hankaɗo shi, ɗaya bayan ɗaya hadiman suka miƙe suka fita da azama. yay tsaye bakin ƙofa yana kallon Ilham wacce ganinsa yasa ta ɗauke idonta gefe tamkar bata ga shigowar tasa ba, shiru ya ratsa ɗakin na ƴan sakanni sannan muryarsa na shaida ɓacin rai yace da ita,"ki fito waje ki same ni".
har yay bakin ƙofa zai fita sai yaga kamar bata ji me yace ba, hakan yasa ya maimaita mata amma da mamakinsa sai yaji tace,"in fito in yi maka me?".
yay ƙyam yana ta kallonta from head to toe da son gano wani abu, sai dai hakan ya gagara, ba ya son wata sabuwar damuwar dan haka bai ƙara cewa da ita komai ba ya juya zai fita sai yaji tana cewa,"na faɗa maka zan kuma ƙara nanata maka Turaki, ba damuwata ba ne ka auro duk wacca ka ga dama, but ka san da abu guda ɗaya shine ba zan zauna da kishiya a cikin gida ɗaya ba, in har kuma ka aikata wannan kuskuren to ina mai tabbatar maka da cewa kayi bankwana da zaman lafiya da kwanciyar hankali kenan, sonka da nake ba shi yake nufin ka ɗebo duk yayin da ka ga dama ka watsa min ba, wallahi! wallahi! wallahi! muddin wata tare acikin gidan nan sai dai ko ni ko kuma ita".
sai kuma tayi shiru tana fashewa da kuka tana miƙewa zauna ta kifa kanta da gwiwa, sosai take kuka tana faɗin,"me nayi maka a rayuwa kayi min wannan tsanar, ka rasa da me zaka ƙuntata min sai da kishiya, kishiyar ma aure ko wata biyar ba'ai da yi ba, waɗanna kalar maganganu kake tsammanin kunnuwana zasu dinƙa ji daga bakin mutane, kamata, tsakani da Allah kayi min adalci kenan?, kai ko tausayina ma baka ji, ina cikin tashin hankali na irin mawuyacin halin da mahaifiyata ke ciki, kai baka zauna ka rarrasheni ba kuma kace wai ka auri wata tun kafin ni, wanna kalar rainin hankali ne wannan?, to wallahi duk wacce ta shigo gidan nan sai naga bayanta ka rubuta ka ajiye".
Turaki yay murmushin takaici ya fice ya bar ɗakin, ba tare da yace da ita ƙala ba, bedroom ɗinsa ya wuce kai tsaye, yana shiga yay kiran lambar Bello.
Bello na ɗagawa yace da shi,"kai MT you should have call me ka faɗa min boma boman da suke tashi a gida, kawai kasa na ɗau ƙafa na tafi zance Boss yace kar in ƙara zuwar masa gida in ba haka ba sai ya ɓalla ni, Boɗejo kuwa kamar zata bankawa motata wuta, to ni dai yace in ƙara jadadda maka inuwarka ma kar ya sake gani. you thank God kana da gidanka har da mata, ni yanzu fisabilillah ta ya zan jure rashin ganin Zaytun har tsawon lokacin da zai sauko daga dokin fushinsa?, MT please ban shawara dan wallah jin zuciyata nake kamar ana ɗinketa da zare da allura, AC ce fa a motata amma uban gumi kawai nake haɗawa".
a sanda Turaki ke ɗaura towel a ƙugunsa yace,"kana jina?".
Bello yace,"yo MT ko ban da kunnen jinka ai ya zama dole ma na aro na saurareka, balle kuma akwai, ma za ka faɗi duk wata kalar shawara da kake ganin zata zama way out".
Turaki ya cika bakinsa da iska ya fesar yana kama ƙugu sannan yace da Bello,"plss karka min hauka, i want ask you something and be serious ka bani amsa, ta ya ake gane mace na da ciki?".
Bello ya lailayo wata ashar yace,"dan ubanka dama har haka kayi babban aiki?, shege wooo kace baka sonta?, to da kake tambayata ya ake gane mace na da ciki waka taɓa gani na yiwa?, ni ba ɗan iska ba MT karka ƙara min wannan tambayar, ka ɗauketa kuje asibiti ka tambayi waɗanda suka karanci abun, ka ban shawarar kawai da na tambayeka ta ya zanke ganin Zaytun?".
Turaki yaja tsaki da cewa,"useless". sannan ya kashe wayar. ya ƙara lalubo lambar Dr Hasheer, sai da kiran ya yanke sannan Dr Hasheer ya kira shi, bayan sun gaisa yake ce masa.
"Dr kana gida please?".
Dr Hasheer yace da shi,"ehh lafiya dai?".
Turaki yace,"in ba damuwa don Allah ka leƙo gidana".
Dr Hasheer yace,"ok babu damuwa, on my way right now".
ya dire wayar yana shiga toilet ya sakarwa kansa shower, bai jima ba aciki ya fito yazo ya tayar da sallar azahar don ba ya jin zai iya fita masallaci, duk da already ma an riga an idar. idarwarsa kenan Dr Hasheer ya kira shi yake shaida masa yana ƙofar gida, yace da shi alright ga shi nan fitowa.
jallabiya ya zura ya sauka ya fita ya shigo da Dr Hasheer, suka ɗan zanta a parlo na ƴan mituna sannan Dr Hasheer ya ba shi urine container.
sanda ya shiga ɗakin Ilham nata tana toilet, har zai tsaya jiranta kuma sai kawai ya isa bakin toilet ɗin yay knocking.
ta kashe shower ɗin tana tambayar waye, yace,"ni ne, are you coming out now?".
tai masa shiru bata yi magana ba har tsawon minti uku, bai ji ta amsa mishi ba kuma bai ji ta kunna shower ɗin ba.
ransa ya ɓaci kawai ya murɗa handle ɗin ya faɗa ciki, ya ɗaure fuska ya haɗe girar sama da ƙasa ya miƙa mata robar,"yi fitsari ki ban".
"ban gane ba". ta faɗa tana kallonsa nata ran itama a ɓace tana ɗaure tata fuskar.
da yay mata jan ido ya sakar mata tsawa bata san lokacin da ta miƙa hannu ta karɓa roban ba, zuciyarta kamar zata fito waje dan baƙin ciki ta durƙusa tayi fitsarinta miƙa masa.
ya karɓa yana ƙare mata kallo tsab a naked ɗin da take don gano wasu alamomi da Dr Hasheer ya faɗa masa, ya watsa mata banzan kallo sanda zai fice, ko ƙofar bai rufe ba ya bar ɗakin kamar iskar guguwa.
Dr Hasheer ya miƙe ganin ya fito, Turaki ya bashi container ɗin da yake riƙe da ita kamar ya riƙe kashi, yace,"please Dr kar ya wuce yau".
Dr Hasheer yace,"you just give 1hour, shima saboda ba hospital zan wuce direct ba, amma da zarar mun kammala gwajin i will call you and tell you the result".
Turaki ya basa hannu su kai shaking yana faɗin,"thank you so much".
su kayi sallama ya wuce shi kuma ya haura upstairs ɗakinsa. yana shiga ya buɗe locker ya ɗauko jotter da biro ya hau kan gado ya zauna, baya son tashin hankali ba kuma ya son abunda zai zama silar rugujewar farin ciki a tsakanin iyayensa, dan haka dole yayi abunda yake ganin ya dace, kowa da kowa ma ya huta.
but a sanda ya ɗora biron akan takardar sai yaji ya kasa rubuta abunda yake ganin zai zama mafita ta ƙarshe, yaji zuciyarsa tayi wani irin matsewa, ya jinginar da kansa jikin gadon yana tunani tsawon wucewar daƙiƙu masu yawa.
daga bisani ya ɗauko wayarsa ya kira wayar Mum, ko da ta ɗaga ta tambaye shi lafiya sai yaji ya kasa faɗa mata abunda yake shirin yankewa, hakan yasa yace mata ya kira ta ne kawai.
tace da shi,"Babana karka sake ka sawa kanka damuwa kaji ko, ba komai ya sa Baffa faɗa maka haka ba illa ɓacin rai, kayi haƙuri ka ba shi space zuwa wani lokaci. Allah yayi maka albarka".
bayan sunyi sallama ya kira lambar Hajiya Madina, tana ɗagawa ko amsa sallamar tasa bata yi ba balle taji abunda zai ce mata tace da shi,"ya akai?".
ya kira sunanta kamar yaron dake buƙatar shan nono.
tace,"ka ga me babban suna, in kace zaka biyewa wannan uban naka da shima tsufa ya fara rikitar da shi to zaka dawwamar da kanka acikin damuwa ne, don haka ka rabu da shi ka ba shi space zuwa ranar da zai nemeka da kansa, kai ɗin ai na dabanne mahaifinka ba ya iya fushi da kai mai tsawo, naji fitinanniyar Kakarka na cewa zasu zo su ɗauki kayarsu yanzu, to da zarar sun zo sun ɗauketa ka rufe gidanka ka huta abinka, ko office karka dinƙa zuwa har matarka ta tare, kaji ni ko?".
ya sauke numfashi yace,"tom Maama".
tace,"yauwa Allah yayi maka albarka, zamu kai lefe monday in Allah ya kaimu, zasu fara biki ranar wednesday but Ummi bata faɗa min ranar da zasu gama ba, sunce sai Dada ta dawo ita zata yanke wannan".
magana take tayi ta hana shi faɗar abunda yake so yace, har ta gama sannan tayi masa sallama.
ya kasa sauke wayar daga kunnensa sai sulalewa tayi daga hannunsa.
ya maida hannunsa kan takardar da har yanzu ke hannunsa, ya shiga rubutu a sanda yake jin zuciyarsa na bala'in matsewa, yana rubutun muryar Fillo na amsa kuwa a cikin kansa, kamar yanda hotonta ke haska masa acikin idanuwansa tun daga ranar da ya fara ganinta har zuwa ranar ƙarshe na rabon da ya sanyata a idonsa.
ya rumtse idonsa gam a sanda ya kammala rubutun, kuma ba tare da ya iya buɗe idonsa ba ya nannaɗe takarda ya ɗaga ƙasan pillownsa ya saka.
yaja wata doguwar a jiyar zuciya yana kwanciya ko zai sami sassaucin abinda yake ji a ƙasan ransa.
*Vote, Comment and share.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_14readmore, 14÷4=3.5, so typing ɗin kwana 4 muka yi😖, kar naji ance new update untill wednesday🤐 ._
*46*
*Taraba.*
acikin gidan babu abin da kake ji yana tashi sai hayaniyar mutane masu hadadar biki.
Inna Kareema ta fito daga sashin Kawu Abdullahi hannunta ɗauke da ƙatuwar cooler na abinci, tana nufar sashin Jagarɗo suka yi kiciɓis da baƙuwar da ke shigowa.
ta tsaya da tafiyar fuskarta na washewa da tsurar fara'a, ta ajiye kular a ƙasa tana faɗin,"maraba maraba da mutanen Abuja, wato ku sai yau ku ke tafe?".
ta faɗa tana ƙarasawa ta tarota tare da amsar ƙatuwar jakar hannunta.
Dattijuwar baƙa me suna Yaya Sahura ta ce,"yo ke Kareema ai wannan biki da sai an gama za ku ganmu".
Inna Kareema ta ce,"kai haba dai, lafiya?".
Yaya Sahura tace,"ƙalau, ai mu zatonmu litinin ta sama aka ce za'a kawo lefe, taron biki kuma a fara shi ranar laraba, sai daren jiya da Lamiɗo ya kira waya yake cewa da Baban Yara ai bai ga gimlawarmu ba, shi ne yaufa babu shiri muka bugo sammako".
Inna Kareema ta ɗauki kular abinci suka ci gaba da tafiya tana faɗa ma ta,"to ai kin san auren a yanda yazo, shi Dottijo ma ce ya yi mene na cewa sai anyi wani taron biki tun da dai ɗaurin aure an jima da yinsa, akai yarinya ɗakinta kawai, to kuma kin san lamarin Dada. ita taron ma ce tayi sai anyi sati guda ta yanda Kakar mijin zata gane su ne ƴan iska, da ƙyar Dottijo ya shawo kanta yanzu dai za'a yi shi kwana biyu, to jiya anyi Kamu, yau zamu yi al'adarmu ta fulani da kika sa ni, sai gobe kuma a kaita gidanta".
Yaya Sahura tana dariya suka wuce suna ci gaba da tattaunawar su. "hmmm ai da yake Kakar mijin duk ita taso ta ɓata lamarin, karki ga irin tataɓarzar da aka sha kamin Dada ta yarda amma da tsaye tayi tace ko zai mutu sai ya sakar ma ta jika, da ƙyar su Dottijo dai suka shawo kanta ta haƙura".
a parlon Hajjah suka ya da zango in da babu kowa, Yaya Sahura ta zaro ido waje tana faɗin,"wannan uban akwatunan fa kamar za'a buɗe sabon kanti, kar dai kice min su ne lefen?".
Inna Kareema ta wuce ta ajiye kular hannunta tana faɗin,"hhh aiko dai abin da kowa ke faɗa kenan, Fillo dai ai abun nata sai son barka, ƴa tayi goshi dan kaf jikokin gidan nan albarka, banda haka da yanzu Dada taja ma ta tayi asarar wannan abun arziƙin".
"masha'Allahu, kiga akwatuna kamar ba'a rashin kuɗi a ƙasar nan, kalla fa yacca aka ɗaure su da ribom kyace lefen da ake kaiwa gidan sarki ko gidan shugaban ƙasa". Yaya Sahura ta faɗa tana tattaɓa akwatunan da aka jere su waje ɗaya ɗaiɗai har guda ashirin da takwas.
Inna Kareema ta wuce ta rufe ƙofa, ta dawo tana cewa,"ai buɗe su duk ki gani, gwala-gwalai ne aciki har takwas. lefen nan dai in faɗa miki tun ranar farko ba'a ƙara buɗe su ba kin san ba zuciyar kowa ke da kyau ba, masu ɗan hali ba'a gane musu, zan rantse miki kaf kayan ciki babu na ƙasar nan. kin gansu nan kuma Dada ta ce ko kwalli ba za'a taɓa ba".
su kai dariya tare, sannan su ka shiga buɗe akwatunan na gani na faɗa, Yaya Sahura sai saka albarka take tana yabawa.
daga can ɗakin Dada kuwa waya ce maƙale a kunnenta, magana take yi cikin faɗa tana cewa,"ka ga Arɗo ni bana son wannan magana, su kwashe kayansu kawai, duk wani kaya da suka zuba a kwashe su akai musu gidan su ba ma neman taimakon kowa don muna da shi, haka kawai salon yarinya ta tare azo ana goranta ma ta ana cewa ai kayan ɗakin nata ma iyayen miji ne suka yi ma ta, a'a sam ku kwashe musu kayansu ku jera na ku".
da ga cikin wayar Arɗo yace,"to Dada wallahi duk mun rasa yanda zamu yi da su fa, ita mahaifiyar yaron ta ce gudunmawarta ne, Fillo ai ƴace a wurinta...".
tayi hanzarin katse shi a yayin da ta kulle ido tana girgiza kai,"Arɗo akwai ka da shegen taurin kai, ka faɗa musu gudunmawa bama so ta bawa ƴarta, ni jikata bata buƙata".
Arɗo yace,"tom shikenan Dada yanda kika ce".
ta sa ke cewa,"yanzu an kammala kawo kayan gaba ɗaya?".
yace,"a'a da yake bedroom ɗin guda huɗu ne mu kuma order ɗin biyu aka yo, to amma yanzu Saifullahi ya kira wani abokinsa da ke can ƙasar turkey ya taho da su zuwa gobe idan zai dawo".
Dada tace,"to shikenan ya yi, ina fatan kun faɗa masa kaya masu kyau da tsada ake buƙata ko?".
ya ce,"an sanar masa Dada".
"kuyi maganar kuɗi da shi sai ka kira Maudo ka faɗa masa, akwai wasu kayan ƙyale-ƙyale ma da Amatullahi ta nuna min jiya kuma bamu taho da su ba daga can saudia ɗin, zan sa ta turo maka a waya sai ya duba yaga idan akwai acan ƙasar sai a taho ma ta da su".
ya amsa da,"to Dada, sai ta turo yanzu".
tace,"to naji, Giɗaɗo ma sun taho yanzu da sauran kaya. don Allah ku yiwa ƴar nan jere na kece raini, irin jeren da zai hana wannan figaggiyar tsohuwar kwanciyar hankali. ni ban so ma ya haɗe musu gida ba wallahi, na so ya raba su dan sam bana son abin da zai ɗagawa jikata hankali, ina tsoron haɗe su gida ɗayan nan kar suje su ke cutarta tun da ita Allah bai yi ta da baki ba, shashasha ce banda kuka babu uwar abin da ta iya".
Arɗo yana murmushi ya ce,"Dada ai ko hakan ma kamar ya raba musu gidanne, kowacce da part ɗinta kuma da tazara sosai tsakanin part ɗin na su".
ta taɓe baki bata ce da shi komai ba ta kashe wayar tana ajiyewa a gefenta ta dubi Safara'u ta ce,"ke jiya da ku ka je gidan su angon kun gani da gaske bai da lafiyar ko kuwa iskanci ne da rainin hankali kawai za'ayi mana saboda kar yazo bikin?"
Safara'u ta ce,"ƙwarai kuwa Dada, dan har sai da muka je asibitin ma sannan aka sallame shi lokacin, ba shi da lafiya sosai gaskiya ance yana fama da ciwon ƙoda ne".
Dada ta taɓe baki ta ce,"Allah ya kawo sauƙi, rashin lafiyarsa dai ba ita zata hanamu shagulgulan biki ba".
ta waiga ta kalli Amatullahi da ke charting ta ce,"abun jiya da kika nuna min ki turawa Arɗo yanzu".
sannan ta kalla hadimarta da ke matsa ma ta ƙafa tace,"ki leƙa ɓangaren Gaji ki kirawo min Fillo, idan ba'ai wasa ba tana can tana ɗan banzan halin nata, dan yau ko ganinta banyi ba tun safe, ina kyatata zaton ma ko abinci ba ta ci ba".
tana rufe baki Maijidda ta shigo ɗakin, ta wuce tana ajiye kayan hannunta, Dadan ta dubeta tana cewa,"yauwa ke ina wannan ƴa take?".
Maijidda ta turo baki tana ɓata rai tace,"tana can".
tazo wucewa Dada ta rarumi sandarta ta buga ma ta.
"can ina?, dan ubanki ko sheɗan ya san can ne da zan tambayeki kice min wani can... sai yanzu ma na gane mugun halin da Fillo ta kwaso wajenki ta koya, ai Hausawa basu yi ƙarya ba da suka ce abokin ɓarawo ɓarawo ne, haka ma zama da maɗaukin kanwa...sam sam ba kiyi halin ƙwarai irin na kakarki ba, dole na raba ƙawancenku dan ba za'a kaita gidan miji ba kije ki lalata ma ta aure".
Maijidda ta sosa wurin da ta duketa saboda zafi ta ce,"tana sashin Kawu Musbahu ɗakin Adda Amina". zata fita Dada ta dawo da ita,"ke zo nan".
ta dawo tana rakuɓewa wuri ɗaya kamar mara gaskiya, Dada ta kalleta tsab sannan ta ce,"me aka yi miki da ma?".
Maijidda ta fara hawaye tana cewa,"tun jiya take ta kuka kuma duk na tambayeta abin da aka yi ma ta taƙi faɗa min, ina ta rarrashinta ma taƙi yin shiru, zazzaɓi ya rufeta na bata magani ma taƙi tasha".
"wacece da ma?".
tace,"Hussainata mana".
Dada ta miƙe tana dogara sandarta ta fita a fusace, ta shiga parlon Amina mutane na ta gaida ita babu wanda ta amsawa ta wuce kai tsaye cikin ɗakinta.
tana shiga ta sami Fillo kwance akan gado tayi ruff da ciki, ta taƙarƙare ta buga ma ta sandarta a baya, babu shiri Fillo ta miƙe a tsure tana dafe wajen, idonta na fara zubar da hawayen da suka tsagaita ma ta, sosai zafin dukan ya shigeta dan ƙashin bayanta har sai da ya amsa.
Dada ta dinƙa kallon idanuwanta da suka yi jawur, sun kumbura tsabagen uban kukan da take sha a ƴan kwanakin nan, fuskarta kanta tayi jaa ko tausayin kanta bata ji.
ran Dada a matuƙar ɓace ta ce,"ke wai dan uwar ubanki tare da kuka aka haife ku ko kuma an haifeki ne dan ki yi ta kuka a duniya?".
ta nemi wuri ta zauna tana ta faɗa.
"ƴar banzar yarinya mara tawakkali, idan ba za ki iya jurar rashin uban naki ba ki sha fiya-fiya ki bi shi mana, idan kuma auren ne ba kya so ki buɗe baki ki faɗa mana, ko an gaya miki mu muna kai zuri'armu gidan wanda basa so ne. nan na tayar da jijiyoyin wuya akan sai an sake ki saboda ina so na ƙwatar miki ƴancinki, iyayen yaron nan suka zo su kai ta bani haƙuri naƙi na haƙura har sai dai aka kai ƙarata gaban mahaifina tukunna, shi ma ɗin saboda ban iya ƙetarewa maganarsa ne amma da sai na dage akan bakana saboda ko kaɗan ni bana jurar naga za'a wulaƙanta min jinina, da kika san ba za ki iya zama da shi ba tun ranar da suka kawo lefe ba sai ki faɗa ba ace su juya da abinsu, to wallahi tallahi ki shiga hankalinki da ni tun banyi mugun saɓa miki ba, dan tsab sai in baɗawa idona toka nasa Jagarɗo ya kai ki barikinsu ya ƙulleki, ni bana son halin ƴan iska saboda haka ki kiyaye ni".
Fillo ta ɗaga idanuwanta da take jin sun ma ta nauyi ta kalla Dada ta ce,"banda lafiya ne".
Dada ta zabga ma ta uwar harara ta ce,"da ba ki da lafiya kuma sai aka ce kuka ne zai yi miki magani ko?, mtswww".
ta miƙe ta fita ta bar ɗakin tana ta faɗa, a parlon ta sami Ammi cikin mutane tana raba musu Dakkere(abinci ne na fulani), ta kirata tazo tace ma ta.
"ɗanki ya wuce ko yana nan?".
Ammi ta ce,"wanne a ciki?".
ta harare ta ce,"mutanen ƙwarai ake nema ba ƴan wiwi ba, likitan nake tambayarki ba wannan mara kunyar ba".
ta ce,"yana nan, amma ina jin kamar shi ya wuce kai Maudo airpot ɗa zu".
"to ina waccan yarinyar ƙanwarsa, me aikin asibitin?".
"sun je
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 50 Chapter of 73