Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yanzu suna bayanin yanketa za'ai, Azima dai na cikin wani hali Ahlan, wannan yarinya sai dai Allah yay mata sakayya da wanda ya zama silar shigarta wannan hali". sosai take kuka sanda take maganar, wanda hakan ya ƙara tsawaita kukan Ilham. Ahlan a razane yace,"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, paralyse Umma?, yanke ƙafa?, rasa ido ɗaya?, kai rayuwa kenan kowanne bawa da kalar ƙaddararsa, ita kuma Yaya ga ta yanda tata tazo mata. hasbunallahu wani'imal wakil". shima bai san lokacin da hawaye ya sakko masa ba, tausayin ƴar'uwar tasa yay matuƙar kama shi. Mai Martaba ya ƙaraso wajen jikinsa a mace, yana zuwa Ilham ta taso a jikin Hajiya Shema'u ta tafi ta faɗa jikinsa. ya rumtse idonsa sosai saboda tsananin tausayinta, ya kalli su Hajiya yace,"Dr yace kuna iya shiga wajenta". da sauri kuwa suka miƙe suka nufi wani dogon corridor hanyar da zai sadaka da room ɗin da aka kwantar da Fulani Azima. Mai Martaba ya zauna akan kujerar da suka tashi, ya kwantar da kan Ilham a cinyarsa, yay dauriya da dakiyar maganar da yake jin kamar da kuka a cikinta. yace,"kina so Maminki ta sami lafiya?". tai saurin ɗaga masa kai, yace,"to adu'a za ki mata ba kuka ba, indai kina kuka ba zata sami lafiya ba, kinga dai a halin da take ciki, halin da ko maƙiyinka ba zaka yi masa fatan ya shiga ba". ta ɗago daga cinyar tasa, yasa hannu yana goge mata hawaye, wani na kuma bin wanda yake gogewar. duk cikinsa ƴaƴa mata yafi son Ilham saboda sunan mahaifiyarsa da taci, ƙari da kuma da kyan halinta, dan duk cikin yaransa mata tafi kowa haƙuri da biyayya da nuna ita ɗin ba ƴar kowa bace. yana riƙe da hannunta ya nunfasa yace,"ya kamata ki koma gida haka Ilham, ba zai yiwu ki baro mijinki kizo ki tare anan ba, karki damu ko every weekend ne sai kizo kike ganinta kina komawa". tai saurin cewa,"Dad ni ba zan koma ba sai Mami taji sauƙi". yace,"a'a Ilham". cikin kuka sosai tace,"to Dad ai shima yayi min uzuri tunda yasan wacce bata da lafiya, ni dai ba zan koma ba, Allah Dad ba zan iya zama a ko'ina ba yanzu in ba kusa da Mami ba". Mai Martaba yay shiru bai ce komai ba, wucewar daƙiƙa ɗaya ya ɗauko waya ya kira Turaki, yana ɗagawa daga ɓangaren Turaki cike da girmamawa da tsantsar ladabi ya gaida shi. bayan sun gama gaisawa Mai Martaba yace da shi,"Muhammad babu damuwa dai ko idan Ilham ta zauna nan?". Turaki yace,"ba damuwa Dad". "ka tabbata Muhammad?, karka ce zaka yi kara ko kuma alkunya". yace,"ko ɗaya Dad, ai abinda ya zama dole shi ake dubawa". Mai Martaba yace,"to shikenan, Allah yayi muku albarka". daga haka suka yi sallama. su kai shiru daga Ilham har Mai martaba kowa yana jin ransa ba daɗi, in ace suna da iko kwana ɗaya tal ba za'a ƙara ba Fulani Azima zata warke, to amma lamarin ba nasu bane na ubangiji ne, sai dai su roƙe shi ya warkar da ita ba tare da tayi doguwar jinya ba. suna zaune kusan minti goma sai ga Sarauniya Mabruka wato matar Mai Martaba ta farko, ita da ƴaƴanta uku suna biye da ita tare da masu kula da su mutum uku. tun a washegarin ranar da Fulani Azima tai accident aka taho da ita Philippines domin ƙwararrun likitoci su dubata, dan Mai Martaba yana ganin kamar likitocin nigeria ba zasu iya ba, duk da cewar asibitin fada ma ba ƙanan likitoci bane acikinsa, kusan duk ɗinsu a ƙasar waje suka yi karatu, amma shi yafi ganin su taho nan ɗin. kuma families da dama sun so su biyo bayansu Mai Martaba yace a'a su ɗan dakata tukunna, ita kanta Ilham sai da aka kwana biyar sannan suka taho ita da su Hajiya Shema'u da Turaki, kuma shi ranar da yazo ranar ya koma bai zauna ba. kuma sai a yau da suka kwan 21days sannan mai martaba ya bar iyalinsa suka taho, don farko duk bai zaton za'aja haka ba, da zarar an mata aiki a ido shikenan zata dawo normal, to kuma likita sai yazo musu da bayanin duk da ya girgiza su. Sarauniya Mabruka ce ta fara sauka sauran biyun duk suna baya suma tare da nasu ƴaƴan. ta zauna kusa da Mai Martaba tana ɗago da Ilham daga jikinsa ta kwantar da ita a nata jikin, hadiman dake tare da ita suka watse suka tsaitsaya daga can gefe, Yarima Abbas da Yarima Lateef da Yarima Bilal suka zauna kusa da mahaifinsu ta ɗayan ɓarin. Sarauniya Mabruka tace da Mai Martaba,"ya jikin nata?". idonsa na tsaye ƙyam akan wata ƙofa cike da nazari a bisa faruwar accident ɗin ya bata amsa da cewar,"da sauƙi irin na malam bahaushe, zuwa anjima zasu ƙara shiga da ita theater za'aiwa ɗaya idon aiki, shima tana kukan bata gani da shi sosai, sai maƙogaronta da akai hoto akaga still akwai glasses na mota da suka farfashe mata aciki". "Allah ya sauƙe ya bata lafiya don nabiyyurrahmati". ta faɗa tana saka hannu ta goge hawayen da ya sauko mata. lamarin duk yasa jikinsu mutuwa, sosai suke tausayin Fulani Azima domin ita ɗin mutum ce a garesu, duk wanda zai buɗi baki ya faɗi aibutunta to sai dai idan maƙiyinta ko kuma wanda basa shiri. duk cikin su huɗun ita ɗaya ce babu ruwanta a yanda take nuna musu, ko irin kishin nan ma na rashin haihuwar ɗa namiji ita bata yi sam bata ɗaga hankalinta ba, hasalima kama nasu ƴaƴan take kamar nata, nan kuwa duk basu san tana bi musu ta ƙarƙashin ƙasa ba ne, fir'auna ce a zuciya Allah a fili. suka miƙe gaba ɗayansu suka wuce zuwa room ɗin da take, duk me cikakken imani kallo ɗaya zai yiwa Fulani Azima yaji saukar hawaye a fuskarsa, kwance take kan gadon kana kallon idonta na dama zaka san bata gani da shi kwatakwata, sai kallon kowa take yi da ɗayan shima kuma dusudusu take gani, ga karaya a hannayenta duka biyun banda ta ƙafarta guda ɗaya, kallon kowa kawai take tana hawaye masu zafi. ita so take ma tayi magana amma ta kasa, tun washegarin ranar da abun ya faru taso ta buɗi baki ta nemi yafiyar Hajiya Ramla a sanda suka je dubata, amma tayi tayi tai magana sam ta kasa, ga shi duk ta yanda taso tayi wata alama da zaisa a fahimci tana so tayi magana da Hajiya Ramla ta kasa, kuma daga yanda taga fuskokin familyn Dikko tasan ko kusa Hajiya Ramla bata tona mata asiri ba, akwai tabbas ɗin bata faɗawa kowa komai ba, wanda hakan ya ƙara haifar da danasani da kuma dama nadama a tare da ita, tana ji tana gani ko da bata mutu ba tata rayuwar dai ta ƙare, ita da matacce marabarsu numfashi kawai, babu abinda take biɗa a yanzu sama da ta kalli Hajiya Ramla a gabanta ta nemi yafiyarta, sannan taga Jakadiyya da Drivern da ta kashe suma tace su yafe mata, to amma ba zata samu duka wannan damar ba, haka zata tafi lahira da tarin zunubi da kuma hakkin waɗanda ta zalunta, shikenan ita kuma tayi biyu babu, babu nan duniyar babu can lahirar, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. sosai take kuka idonta guda ɗaya na hawaye, inama ace a dawo da baya, da tayi amfani da damarmakin da take da su ta gyara lahirarta, to sai dai hakan ba zai kasance ba, lokaci ya riga ya ƙure mata, yanda kowa ke ganin saukar hawayen nata babu wanda ya fahimci me take buƙata, sai tausayinta da kowa yaji yana roƙo mata lafiya a wurin Allah. Ilham ta ƙwace daga hannun Sauraniya Mabruka ta isa gadon ta faɗa jikinta ta fashewa da wani irin kuka, kukan da duk sai da ya saka kowa dake ɗakin hawaye babu shiri. *Dubai Quarters, Gombe State, Nigeria.* daga ɓangaren kudu, gida na tsakiya me lamba 20, flat house ne ɗan tsakiya me ɗauke da milk gate da abuja brown paint, sai flowers dake zagaye da ƙofar gidan, daga yanda wajensa yake da kyau zaka shaida cikinsa ma me kyau ne. daga cikin gidan Fillo ce a ɗakinta kwance akan madaidaicin gadonta, ba bacci takeyi ba idanuwanta a rufe suka kawai hawaye na bin gefen fuskarta. ta tashi zaune tana saukowa akan gadon ta shiga toilet tayi alwala tazo ta tayar da sallah, tana cikin sallar Ummi ta shigo, ganin tana sallar yasa ta ce mata,"idan kin idar ki fito muci abinci". bayan Fillo ta idar ta kalli agogo taga har biyu saura, dan haka bata fita ba sai da ta saka uniform na islamiyarta tukunna, ta ajiye hijab ɗin da jakar akan gadonta ta fito cikin sauri. Kaka da Ummi na zaune a ƙasa kan carpet suna kallon tashar arewa 24 ana maimaicin kwana casa'in, ta zauna gefen Ummi sannan su kai bismillah suka fara cin abincin, bai fi spoon biyar Fillo tayi ba ta miƙe, Kaka da Ummi suka bita da ido har ta shiga ɗakinta. wucewar minti biyu sai gata ta dawo riƙe da jaka da hijab a hannu, ta zauna kan kujera tana kallo tv tana ji tana neman kasa riƙe hawayen dake yunƙurin zubo mata. sai bayan da su Ummi suka kammala cin abincin sannan Kaka na dubanta tace,"kinga, kinga Fillo ki kiyaye ni, na faɗa miki ki cire batun cutarwar da Amir yay miki a ranki amma kinƙi ji ko, haka kawai kina ƴar ƙarama dake kisawa kanki damuwa salon kija mana masifa, ke bama abin farin cikinki bane tunda har aka sami bayin Allahn da suka tsaya miki hukuma tabi miki hakkinki". take kuwa hawayen da take ta riƙewa suka zubo, ta kifa kai da gwiwa tana fashewa da kuka, Ummi na kallon ƴartata da tausayawa tace,"Auta zo nan". ta taso ta dawo kan kujerar da Ummi take ta kwanta a jikinta. Ummi na shafa kanta tace,"kina so na koma inda ba xaki ƙara ganina ba?". da sauri ta girgiza kanta da cewar,"a'a Ummina". tace,"to ki daina kuka haka nan ya isa bana so, ki manta da duk abinda ya zama past ki focusing akan rayuwar gabanki, babu abinda zai fishsheki yanzu sama da ki mayar da hankali akan karatunki shine kawai gatanki har zuwa ranar da Allah zai kawo miki miji na gari kiyi aurenki". bata daina kukan ba tace,"Ummi har yanzu abin yana yi min ciwo sosai". Ummi tace,"sai ki godewa Allah da ya tona asirinsa tun bai aureki ya miki cuta me gaba ɗaya ba, ki kuma gode masa da ya kareki daga sharrinsa a iya zaman da ku kai da shi". tayi shiru bata ce komai ba, idonta na haska mata hoton jiya sanda suka je kotu ita da su Maama akan case ɗin Amir da aka ƙarke a jiyan, tana tsaye a bayan Mum taji Turaki ya kama hannunta ba tare da sanin kowa ba suka bar wajen, kuma duk ta yanda taso ta raba hannunsa da nata ta kasa har suka shiga wani ɗaki inda aka kai Amir shi da tawagarsa, kallo ɗaya tayi masa ta saurin ɗauke kanta gefe dan a duniya idan da mutumin da bata ƙaunar gani bai wuce shi ba. kuma tsabar rashin kunya irin da azzalumin bawa wai har yake zubewa a gaban ƙafafunta yana roƙonta Allah da Annabi akan ta yafe masa abinda yay mata, sannan ta roƙar masa alƙali ya sassauta masa hukuncin da aka yanke masa na zaman prison tsawon shekara goma sha biyar, har da wai in ya fito yayi mata alƙawari zai tuba ya koma mutumin arziƙi ya aureta. wannan maganar kuma ita tayi mata zafi bata san lokacin da ta ɗaga hannu ta wanke shi da maruka har biyu ba, Turaki kuma ya karɓi kulki a hannun police ya bata, ta dinga buga masa a fuska har sai da taga jini yana zuba ta hancinsa tukunna ta ƙyale shi tayi saurin fita daga ɗakin, in ba haka ba tsab zuciya zata iya sata ta rarumi duk abinda zai kai Amir Lahira ta buga masa. Kaka na kallon Ummi tace,"Halimatu kinga duk inda Hamid yake yana nan hankalinsa na kanki da tunanin halin da kike ciki, fushin fa da kike da mahaifinsa ba zai fa shafe shi ba tunda ba shi yay miki laifi ba". fuskar Ummi ta juye zuwa ɓacin rai tace,"Dada zan nemi Hamid amma ba yanzu ba, akwai lokacin da nake jira, dama in ace ma zan ƙara waiwayar gidan Hayyo to ace Auta na hannunsa ne, yanzu kuwa da bata wurinsa banga dalilin da zaisa in taka ƙafata a ƙofar gidansa saboda ina da wata ajiyar a gidansa ba, Hamid namiji ne baya buƙatata kamar yanda Auta ke buƙatata". Kaka tace,"bafa zance ake na ki dawo da shi hannunki ba, kije ya ganki yasan kina raye kuma kina cikin ƙoshin lafiya shine maganar da nake yi miki". Ummi tace,"ba yanzu ba Dada". Kaka ta gyaɗa kai tace,"ai shikenan ban san lissafin da kike yi ba. ni Allah yasa ma ta hanyar arziƙi Hayyo yayi kuɗin da aka ce yayi". Ummi tace,"ni banma yarda da yaron da ya faɗa ba". Fillo tace,"Ummi da gaske ne fa, ai sanda ku ka tafi gidan Inna Azimi munje ni da su Badariyya, da muka shiga matan gidan suka ce ai kusan wata huɗu kenan da suka sayi gidan, masu gidan sunyi kuɗi sun tashi, to ni naso ma na tambayi inda suka koma kawai na fasa". Ummi dai bata ce komai ba tayi shiru, ita ai banda ma dai bata son musawa maganar mahaifiyarta ai bata ga me zai sa su ƙara komawa Taraba ba a rayuwarsu, tunda Allah baisa sunyi dacen dangi ba, ita bata yi dacen miji ba, ƴan'uwan Kaka kaf ba wani kula suke da ita ba, kamar ma ba ciki ɗaya suka fito ba ayanda suke nuna mata, kansu da matansu kawai suka sani, dalilin da ya dawo da Kaka nan gombe kenan ta samarwa kanta mafita na neman aiki a gidan sarki, daga nan kuma ta koma gidan Dikko ga kuma matsayin da Allah ya kawo su ayau. Maijidda ta shigo parlon bakinta ɗauke da sallama, su Kaka suka amsa mata ta nemi wuri ta zauna tana kallon Fillo dake jikin Ummi tana hararta da cewa,"Ummi dan Allah ki daina ɗora wannan ƙatuwar abar a jikinki". Ummi na murmushi tace,"autar guda?". Maijidda ta taso ta taho tazo itama ta ɗora kanta a kafaɗar Ummi tana cewa,"Ummi to nima ai autar ce". Fillo tasa hannu ta tureta tana faɗin,"dilla ɗaga min uwa, da wani ƙaton kanki anan zaki ce zaki kwanta jikinta salon kija kafaɗarta tayi ciwo". Maijidda ta harareta tana mayar da kanta wurin Kaka tace,"Kaka Yami tana gaisheki, wai ki bada wannan saƙon da za'a kawai Baba Huraira zata je gidan gobe". Kaka tace,"aiko gwara da Allah yasa ta tuna min, jeki ɗakina ɗauko wannan baƙar jakar tawa ta gado ki kawo min". Maijidda ta shiga ta ɗauko jakar ta dawo, Kaka ta ɗauko saƙon ta bata tana yi mata bayani. sannan ta ɗora da ce mata,"yauwa kuma ki faɗa mata jiya fa an karɓo kuɗaɗenmu na wajen matsiyacin yaron can, an karɓo miliyan shidan duka wallahi". Maijidda tace,"shege ai ni naso jefe ɗan iska akayi kowa ya huta da annoba". sai kuma cikin tsokana tace,"umm in iya bakina kar Fillo ta ƙullace ni". Fillo ta miƙe a jikin Ummi tana hararta tace,"banza kawai". ta faɗa tana tashi ta wuce ɗaki. Ummi tace da Maijidda,"kin fara zuwa yiwa su Hajiya Madina aikin?". tace,"ehh Ummi tun washe garin ma da ku ka taho ai". Kaka tace,"to Maijidda sai ki kula da Allah, na san ki kema hankali da natsuwa ba daga nan ba, dan haka ki iya zamanki da mutanen nan, ki zama me gaskiya da amana da kula da aikinki, kina ganin dai ta dalilin iya zama da su da Fillo tayi alkhairin da suka yi mana, bacin haka wa zai ɗauki gida sukutun guda ya bamu kyauta?, waye zai tsaya tsayin daka akan a karɓar mana hakkinmu wajen wancan azzalumin bawan?, aini babu abinda zance da Hajiya Madina sai dai ubangiji yayi mata sakayya da gidan aljannah, mutuncin matar nan ya wuce duk mutum yake zato wallahi". ƙarar wayar Kaka ta katse maganartata, ta ɗaga tasa a kunne ba tare da ta san waye me kiran ba dan bata iya karanta sunan ba. sai bayan kuma ta ɗaga ɗin ta ɗau muryar Dr Yusuf daga can ɓangarensa da yay sallama, bayan gama gaisawa ta tambayesa iyalin da mutanen gidan sannan yace ta bawa Ummi. Ummi na murmushi ta amsa sallamarsa tace,"Shikenan kuma sai ɗana ya manta da ni". Dr Yusuf ya sosa ƙeyarsa yace,"na isa na manta dake Mommi, wallahi kullum sai munyi kewarki, Mommi ban san me yasa kika ƙi yarda kici gaba da zama a wurinmu ba, ko mun miki laifi ne Mommi?". Ummi tace,"kul Yusuf naji ka ƙara ambatar kun min laifi, ni dai kawai abinda nake so ku sani shine har duniya ta naɗe ba zan manta daku ba da alkhairin da ku kai min, ina nan zan ƙara zuwa na musamman in ƙara godiya, ina jikata Farha?". Dr Yusuf yace,"tana lafiya Mommi, jiya ma Nuratu ke cewa tana so tazo ta gaida ke, to kuma sai naji kamar Maijidda tace kun bar can gidan Alƙali". Ummi tace,"ehh wallahi, ai sun sallami Kaka daga aikin da sha tara ta arziƙi, sunce taje ta huta haka, wallah kam sun bamu gida anan Dubai Quaters, baka gida ba Yusuf so masha'Allah, dama nace sai munyi waya tukunna sai in sanar muku insha'Allahu, to ashe ma Maijidda ta rigani". yace,"masha'Allahu, Allah ya saka musu da alkhairi". "ameen Yusuf, dan Allah ka gaidar min da su Nuratu da Ammi da Umma, kai da kowa ma musamman Inna Wuro, gaisuwarta tafi ta kowa yawa". yace,"insha'Allah Ummi duk zasu ji, sai munzo gaisuwa". "to Allah ya kawo ku, ina nan ina zuba ido". daga haka suka yi sallama, Maijidda na murmushi tayi tafi tace,"mu dai abinmu sharr". ta faɗa tana kallon Fillo data fito cikin complete shirinta na tafiya makaranta, ta gimtse dariyarta Fillo ƙuma ta galla mata harara tana cewa da Ummi,"na fito Ummi". ta zauna Ummi ta dafa kanta tayi mata adu'a sosai, tana ƙara ce mata ta kula. Kaka da zolaya itama tace,"ke kuma sai da angon naki ya kashe wayar sannan za ki fito, wannan kiran dai ai nasan ba namu bane, naki ne ake wani wayance da Ummi ake nema". Fillo ta turo baki tace,"angon wata dai amma bani ba, me zanyi da wannan". ta faɗa da duk gaskiyarta. Ummi ta waro ido waje tace,"iye! Auta ɗan nawa kike cewa me zaki yi da shi?, ban da shi Auta kin isa yanzu ki sani ki ƙara saka ni a idonki?, ah lallai, wato babu ko kunya a gabana kike faɗin me zaki da ɗana, ba ki san nafi sonsa ba akanki". cike da shagwaɓa kamar zata yi kuka tace,"Ummi ni to ba zan auri me mata ba, dan Allah ku daina haɗa ni da shi". Ummi na ƴar dariya tace,"idan kin kwantar da hankalinki ma nima ba zan yarda ayiwa ƴata Nuratu kishiya ba, ah tou can ki yanka kije ki samo daidai dake ɗin, nima ɗana yafi ƙarfinki dan ba abinda zai yi da ƙwaila irinki". ta miƙe cike kunya tana barin kusa da Ummi tace,"ni bama yanzu ba ai, sai na zama barrister tukunna in zaɓa in dirje, by then Abba nah ya shiryu ya gane gaskiya sai yazo ya ɗaukemu, mu koma can inda muka fito sai mu bar tsohon ɗan naki anan da shi da gwalagwajin matar tasa". ta faɗa tana ƴar dariya, Ummi ta ɗau hula ta jefa mata. "kin ci ƙaniyarki naji kin ƙara kiran Nuratu da wannan sunan, ki kiyayeni wallahi". tana dariya sosai saboda yanda Ummin tayi tace,"nima to a faɗawa mijinta ya kiyayeni ya fita a sabgata, ya bar ganin ya taimakawa Ummina hakan ba zai sa ya kafa gwamnatinsa a zuciyata ba". sai kuma ta harari Maijidda tace,"ke kuma baƙar munafuka kici gaba da min abinda kike, Allah idan baki wasa ba naje na faɗawa Hamisu me gadi kince kin amince ya turo iyayen nasa. kuma wallah ki faɗawa Dr'n da yake wahalar dake kan yi masa campeign, Fillo ba zata auri me mata saboda haka ya kama gabansa". Maijidda tace,"wallah ba zan faɗa ba, insha'Allahu sai kin zama amaryar Dr". Fillo bata ce mata komai ba taiwa su Kaka sallama ta fita tana sai ta dawo. tun satin da suka dawo wannan sabon gidan da Hajiya Madina ta basu kyautarsa ta fara zuwa islamiyya wacca ƴaƴan maƙotansu suke zuwa, makaranta ce me kyau da tsada acan wajen gidan sarki, itama Hajiya Madina ce ta sakata dan har gida tazo ta sameta tana ƙara tambayarta,"Fillo ina sonki, ina tsananin sonki Fillo, gani nake har yanzu ban kyautata miki da rabin alkhairin da kika min ba, dan haka ki faɗa min me kike so na kuma yi miki yanzu?". Fillon na kukan farin ciki tace mata,"Maama ni makarantar Islamiyya nake so in koma, ina so na haddace alƙur'ani". kuma take a wurin Hajiya Madina ta kira Khalil ya gama yi mata komai a washegari kuma ta fara zuwa. yanzu haka kuma ana ma ta processing na zana private wa'ec ne, dan Hajiya Madina na gab da tafiya wani course kuma tana so idan zata tafi su tafi tare da ita kamar yanda tayi mata alƙawari. tana tsaye bakin titi tana jiran abin hawa wata jar mota tayi parking a gabanta, gabanta ya faɗi sanda aka zuge glass ɗin motar, ta ɗan ƙaƙalo murmushi tace,"Adda Samha ina yini". tace,"lafiya lau Fillo, makaranta zaki wuce?". tace,"ehh". "to shigo sai in ajeki a hanya". Fillo kamar ba zata shiga ba, saboda ita har ga Allah tana tsoron mutumin da ko da sau ɗaya ne ya taɓa cutar da wani a rayuwa, balle kuma wanda ya jima yana haddasa abubuwan za zai sa yaga bayan wani duk da Allah ba ya ba shi nasara, gani take tamkar su Samha ba akan Turaki bane kawai suke da wannan mugun hali, wataƙila sun cutar da mutane da yawa ma ba tun yanzu ba. ɗayan ɓari na zuciyarta yace mata,"ki kyautata musu zato a yanzu, ki ɗauki komai da ya faru a matsayin abinda ya jima da wucewa". Fillo ta sauke numfashi ta buɗe motar ta shiga, daga yanda ta kalla Samha na driving ɗin ta san tana cikin nishaɗi sosai. dan kamar ba wannan azababbiyar Samhan da ta sani ba a baya ba, kamar ba wannan Samhan da taji suna haɗa plan ɗin yanda zasu kashe ɗan'uwansu ba, ta saki baki sai labari take yi mata, hirar da ita dai bata cewa komai. Samha tai picking call ɗin Maama da ya shigo wayarta, daga ɓangaren Hajiya Madina tace da ita,"ina kika tafi kuma?". fuskar Samha na bayyana wani irin farin ciki da jin daɗin da bata taɓa jinta ba a ciki tace,"Maama yanzu zan dawo, naje siyo special gift ɗin da zan bawa Mum ne". ta jiyo fitar sautin murmushi a tare da Hajiya Madina wacce tace,"good, but ki dawo da wuri". tace,"tom Maama". sai kuma tace,"muna tare da Fillo ma yanzu haka, na ganta hanya zata wuce school na ɗauketa". da sauri Maama tace,"bani ita". Samha ta miƙawa Fillo wayar, daga ɓangaren Hajiya Madina tace,"Fillo ƴata, Allah yayi miki albarka kinji, ubangiji yasa ki gama da duniya lafiya yarinyar nan, wallahi shigowarki rayuwarmu alkhairi ne. Fillo nayi amfani da shawarar da kika bani akan su Samha kuma naga nasara, domin kuwa Samha da kanta ma tazo tana faɗa min duk abinda suka aikata ita da Sameer, Allah yay miki albarka Fillo yanzu hankalina ya kwanta banda damuwar komai, ƴaƴana sun shiryu". Fillo dai murmushi take bata ce komai ba, daidai sanda suka zo gate na makarantar tasu, tace. "Maama mun kawo makaranta zan sauka". Hajiya Madina tace,"to shikenan, sai kin dawo Allah ya bada ilimi me albarka. a dage sosai kinji, gobe da safe ki shigo ina son ganinki, ko da yake ma zan aiko driver yazo ya ɗaukar min ke". daga haka sukai sallama, Fillo ta fita a motar, har ta bar wajen Samha ta kirata ta bata wani biro me kyau. ta karɓa tayi mata godiya sannan ta wuce, ta tafi tana me jin tausayin Samha a ranta, lallai rashin nunawa ɗa soyayya daga wurin uwa ba ƙaramin ƙalubale bane a rayuwarsa. banda hakan dama me zai kai su Samha ƙudurtar cewa sai sun kashe ɗan uwansu alhalin su babansu ba wata kujerar mulki garesa ba. ta tuna sanda ta zauna ta bawa Umminta labarin duk abinda ya faru ga me

Chapter 41 of 73