ƙofa sai kace dutsen duniya, ai da taci gaba da gwada ƙarfinta wajen buɗewa kaf ɗinta zata kakkarye.
Tana tsaye tana ƙarewa haɗuwar parlon kallo tare da saƙe-saƙe cikin ranta Samha ta fito daga wani room dake parlon, ganinta ƙatuwa yasa Fillo saurin durƙusawa tana gaisheta a tunaninta itace Hajiya Madina.
Murya can ƙasa Samha ta amsa gaisuwatata ba tare da ta ko kalli inda ta ke ba, ta wuce ta zauna kan kujera tana ɗaukan remote ta sauya channel.
Wani abu ya tuƙe a wuyan Fillo, kenan haka Hajiyan ke wulaƙanta mata Kaka?. tausayin Kakar ya kamata, cikin ranta tana adu'ar Allah ya horewa Amir dai suyi aurensu ko sa huta da wannan bautar a ƙasan wasu balle a dinga wulaƙanta su.
"gadin ƙofa aka saka ki ne?". Samha ta tambayeta bayan wucewar daƙiƙu biyar.
Fillo tace,"a'a Hajiya, ban san aikin da zanyi ba ne".
Samha ta ɗago ido tana ƙare mata kallo, garin kwashe-kwashen Maama yau kuma me ƙanjamau ta ɗebo musu, halitta babu kyan gani jiki sam babu tsokar arziƙi, kai da gani kasan ba'aci an ƙoshi ba.
baki ta taɓe sannan ta ƙara ce mata,"Maama bata karanta miki aikin da za ki ke yi ba?".
Sai a sannan Fillo ta ɗago ido tana kallonta, ashe ɗazu kallon tsoro tayi mata, yarinya ce da girman jiki dalilin daya sa tai zaton matar gidan ce. A hankali tace,"ba'a nuna min ba". ta faɗa tana tura baki gaba.
Da hannu Samha tayi mata nuni, ita kuma ta shige sum sum kamar munafuka ta nufi kitchen ɗin, sai faman takure ƙafafuwanta ta ke yi saboda sanyin AC da yay yawa a tiles ɗin, ga shi takalminta ta barsu acan waje.
Turaki na tsaye a bakin friedge, ya ɗauko maltina ya buɗe ya tsiyaya a cup, ta tsuguna tana gaishe shi, zaton ta ko me gidan ne, amma bai amsa mata ba kasancewar da earpod a kunnensa duka biyun, har ranta taji babu daɗi, a yau ta ƙara yarda da cewar talaka wulaƙantacce ne indai yana ƙasan me kuɗi.
Turaki kam bai ma san da shigowanta ba, ganin ya juyo daga inda yake facing tayi saurin matsawa daga bakin ƙofa ta ba shi hanya, yay ficewarsa still bai lura da ita ba dan hankalinsa ba wajen yake ba.
tafi ƙarfin minti biyar a tsaye daga gefe ɗaya, haɗuwa da tsaruwar kitchen ɗin kawai ta ke ƙarewa kallo, ita dai badan-badan ba sai ta rantse gidan ƴan yan kan kai ne nan, ko kuma tace ba'a duniyar take ba gaba ɗaya.
Fitowa tai daga kitchen ɗin dan sanin abunyi, bai zai yiwu Kaka na can kwance ba lafiya ba tazo ta tsaya anan babu aikin fari balle na baƙi.
tana fitowa sukai kiciɓis da Hajiya Madina, tana kallonta ta shaida itane matar gidan, tai saurin durƙusawa ƙasa ta gaisheta, Hajiya Madina ta amsa fuskarta da fara'a tana ce mata ta miƙe tsaye.
Fillo ta miƙe kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, Hajiya Madina tasa hannu ta ɗago fuskarta tana mata wani kallo, wani kwarjini yarinyar tayi mata, itama Fillon hakan ta ke a wurinta, shi yasa tun kallon farko bata bari sun ƙara haɗa ido ba.
Allah ma ya sa ni Hajiya Madina ta girgiza da ganin yarinyar nan wanda ta rasa dalilin hakan, tsintar kanta tayi da jin wanzuwar sabon yanayi, babu shakka yarinyar zata zamar mata jigon wani abu, ta san da wannan.
ta kawar da mamakin ganinta a gefe guda, Kafin ta buɗi baki tayi magana Fillo ta rigata.
"Kaka Rabi ce ta turo ni na ƙarasa aiki, bata jin daɗin ne yasa ta tafi". Tayi maganar idanuwanta na kan tafin hannun Hajiya Madina dake tallafe da haɓarta.
Hajiya Madina ta faɗaɗa fuskarta da murmushi tace,"masha'Allahu sannunki, ya sunanki?".
"sunana Halima". "sannu Halima, Allah miki albarka...ke jikar Kaka Rabin ce?".
Ta ɗaga kanta,"ehh jikarta ce, a wurinta nake da zama". "to sannunki kinji, amma jikin nata ba tsanani yayi can ba ko?".
Ruwa ya kawo idon Fillo sanda tace,"ehh na dai baro ta zata yi bacci, tace kanta ke ciwo".
Hajiya Madina tace,"to Allah ya bata lafiya...kin ƙarasa aikin?".
ta girgiza kanta alamar a'a. "ai yanzu na shigo kuma ban san aikin da zanyi ba".
Hajiya Madina ta sauke hannunta daga haɓarta, bata san me yasa zuciyarta ke wani irin zillo ba. ta kalla kujerar da Turaki ke zaune, bai ci komai ba ta sani, kuma ba zai ci girkin kowa ba idan ba nata ba, ƙannensa ma sai an kai ruwa rana yake iya cin abincinsu balle na wata ƴar aiki, ita kuma tana so ta fita cikin gaggawa, suna da meeting na friends ɗinsu da suka saba duk ƙarshen wata.
"mu shiga kitchen ɗin". ta faɗawa Fillo. Tayi gaba ita kuma ta bita a baya. tai mata nuni da wata drower tace,"buɗe ciki ki bani ƙwai guda 10".
cikin sauri Fillo ta ɗauko ta kawo mata, ita kuma ta ɓare ledar indomie super pack guda biyu ta jefa acikin ruwan zafi, sannan tasa Fillo ta yanka albasa ta kuma yi greating taruhu.
In few minutes Hajiya Madina ta gama soya indomie da ƙwai ta zuba a plate, sannan ta dafa tea daya ji kayan haɗin Sahaz Special Spices, lokaci ɗaya kitchen ɗin ya kaure da ƙamshin spices ɗin, Fillo sai shaƙe ƙamshin ta ke.
Ita dai Fillo na tsaye a gefe tana kallon duk abinda ta ke yi, da kuma bin umarnin duk abinda ta sakata, tana kuma yiwa mata bayanin abubuwan da zata yi, ba wani aiki ne me wuya ba, Kula da buƙatun Turaki ne kawai.
"miƙo min wancan tray ɗin na tsakiyan". Hajiya Madina ta faɗa tana ma Fillo nuni da inda zata ɗauko tray ɗin. ta jere kayan break fast ɗin akai ta bawa Fillo tace ta wuce da shi kan dining.
"Hajiya ina ne dining ɗin?". Allah ya taimaketa bata da ƙauyancin faɗin abu, Hajiya Madina tai murmushi bata ce da ita komai ba.
Sai da ta gama wanke hannunta a sink tukunna tace da ita,"muje na nuna miki...in kin kai akwai ɗaki idan kika fita ƙofar kitchen daga baya, sai ki zauna in yana buƙatar wani abu zaki ga kira ya shigo ta wayar ɗakin, landline ce, ɗagawa kawai zaki yi ba sai kin danna wani wuri ba...please karki yi delay wajen amsa kiransa, becouse bai da lafiya isashshe".
Fillo ta biyota a baya suka fito, tayi mata nuni da dining area ta wuce taje ta aje akai. "if ya gama sai ki kwashe kayan ki wanke...karki ce za ki ɗora abinci, baya cin abincin kowa sai nawa". tana faɗa mata hakan tace taje tace masa his breakfast is ready. da faɗin hakan ta haura upastairs cikin sauri.
Fillo dai bata gane guntun turancin da Hajiya Madina tayi mata ba, tai shiru tana nazari da son gano abinda tace ɗin amma ta kasa.
Ta ɗaga kai ta kalli inda Turaki ke zaune kan kujera ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya, cikin ranta tana mamakin isa da jin kai irin nasa, wato bama iyaka masu aiki yake walaƙantawa ba harda matarsa.
komai da take rayawa cikin ranta ya katse lokacin da Zaytuna ta shigo parlon, ƙananun kaya ne ajikinta sunyi mata kyau sose, kamar balarabiya ta watso gashinta ta baya, ta saka head band akan gashin.
Wurin Turaki ta wuce tana smiling ɗin dake fiddo da asalin kyan fuskarta, ta zauna kusa da shi kamar zata shige jikinsa, ta kamo hannunsa guda ɗaya sukai shaking. "Hamma nah yau ka tashi da wuri haka".
yasa yatsa ya lakuce mata hanci,"aka ce miki irinki ne ni, bacci babu sauƙi".
Dariya tayi tana kwantar da kanta a kafaɗarsa tace,"Hamma nah na fa rage, tunda ka dawo ai baka kalla na kai 10am ban tashi ba ko".
Idonsa na manne kan news ɗin da ake a aljazeer ya ɗaga mata kai kawai.
Conversation ɗin nasu shi ya warwarewa Fillo komai, kenan wannan shine Hammansu da Hajiya Madina ke ta faɗa mata ɗazu, ba me gidan ba kamar yanda ta zata. Kenan shine mara lafiyan da Kaka ke bata labari?, ta ƙara kallonsa da kyau tana jinjina wani lamari dake cikin kanta.
tana jin Zaytuna na tambayarsa,"Maama bata sakko ba?".
"yes". Ya amsa mata before ya kalleta yace,"wa akai ma kwalliyan?".
Ya tambaya da salon tsokana. Ta maƙale hannunsa tana cewa,"kai Hammah nah ni kam wa zanma kwalliya banda kai". leɓensa na talewa da murmushi yace,"ummm to kinyi kyau sosai...kinyi break fast?".
Ta gyaɗa masa kai,"tare zamu yi da kai".
Ya hurar da iska daga bakinsa,"to ai Maama bata sakko ba har yanzu, ni kuma bana so ki zauna da yunwa. ko muje kitchen ɗin mu dafa tare kinga mun hutar da ita?".
ta ɗaga masa kai alamar ehhh, hannunsa na riƙe da nata suka miƙe tare, kai tsaye kitchen suka wuce, suna shiga ƙamshin egg ya shiga hancinsu, idonsu kuma ya kai kan wanke-wanken dake cikin sink, Zaytuna ta dube shi, shima ita ɗin yake kallo idonsa na haskawa da irin abinda nata ke haskawa.
"but yaushe Maama ta sauko har tayi girki ban sa ni ba?".
"may be bata san ka shigo ba, ko ka shiga ɗakinta?".
"nop, time ɗin dana shigo bata tashi ba ai".
Fitowa suka yi daga kitchen ɗin, Zaytuna ce ta kula da Fillo bayan da Turaki ya haye upstairs, ta kalleta da murmushi a fuskarta tace,"sannunki".
Da yake Fillo ta shaidata ta duƙa har ƙasa ta gaisheta, Zaytuna ta amsa tana tambayarta lafiya tayi tsaye anan.
"Kaka ce bata da lafiya shine na amsheta".
"ohh kece jikartata dama?".
ta gyaɗa kai,"eh ni ce".
Zaytuna ta sakko daga step na farko data hau, ta dafa kafaɗar Fillo tana kallon fuskarta, haka kawai taji yarinyar ta burgeta.
"sannunki, kina da kyau sosai...amma jikin Kakar da sauƙi ko?".
"ehh na dai barta tana bacci".
"Allah ya bata lafiya". Zaytuna ta faɗa tare da kai kallonta kan dining ɗin, tana buɗe plate tace,"ke kika girka?".
"a'a Hajiya ce, babu jimawa ta hau sama. tana ta yi min bayanin wanda zaici abincin to ban gane ba ne".
Zaytuna na murmushi ta ƙara dafa shoulders ɗinta tace,"na Hammah ne, ba ki lura da shi ba ne a zaune?".
Fillo tace,"nayi zaton Alhajin gidan ne".
Zaytuna da Nihal wadda ta shigo yanzu taji abinda Fillo tace suka saki dariya tare.
"Lallai kuwa Alhajin gidan, yau an maida Hammah tsoho...ke sai kace mara gani sosai ki kasa banbance dattijo da matashi".
Nihal ke faɗa.
zata hau upstairs ta ke cewa da Zaytuna.
"Adda kije Baffa na kiranki".
"oak, to kice da Hammah ya sakko ga breakfast ɗin nasa".
Nihal ta haye upstairs ita kuma Zaytuna ta fita, suka bar Fillo tsaye a wurin. da jikin bango ta jingina har sanda Hajiya Madina suka sakko ita da Nihal da Turaki, da shirin fitarta ta sakko hakan yasa tayi mata adawo lafiya, babu jimawa Turaki ya dawo daga rakiyan da suka tafi yi mata.
yana waya da Bello Ƙaraye ya shigo, ya zauna kan dining ɗin ba tare daya taɓa abu guda na abincin ba. har sanda ya gama wayar Fillo dai na nan tsaye kamar soja, wasa kawai take da yatsun hannunta, hanakalin na can wurin Kaka, tana ta zullumin wannan bawan da har yanzu bata sami kallon fuskarsa ba ya samu ya sallameta tayi tafiyarta.
Turaki na danna waya ya ɗago ido ya kalleta suka haɗa ido, tayi saurin ɗauke nata, shi kuma ya kalli kayan abincin sannan ya ƙara kallonta ta gefen ido. maganar Maama na dawo masa cikin kansa, wai ita tayi helping nata da greating taruhu da yankan albasa, to taya ma zai soma cin abicin da wannan yarinyar ta saka hannu?.
wani ɓacin rai ya ziyarce shi, ai ko abincin restaurant ba kowanne yake ci ba, balle kuma na wannan abar. yau bai san me ya sami Maama ba, ita da ta ke haƙura da ko menene akan buƙatarsa kawai, amma yau akan wani meeting har tana haɗa dafuwar abincinsa da ƴar aiki.
murya a tamke yace da Fillo,"ja kujera ki zauna".
Ba dan tasan su biyu ne kawai ba da sai tayi zaton ko da wani yake, tunda babu wata alama da ta nuna da itan yake. kuma duk da hakan dai sai ta tsaya, domin tasan kujerar da yake magana tafi ƙarfin zamanta.
Ita duk rayuwarta ma bata taɓa ganin irin kujerun ba ma.
kusan 2minutes da maganar tasa ya ƙara ɗago ido yana mata wani duban yatsine, yay saurin kauda kansa a tsawace yace,"do you want me to repeat my self before you sit?".
Saurin rufe ido tayi tare da ƙanƙame jikinta, sai rawar jiki ta ke yi kamar me jin sanyi. A rayuwarta ta tsani tsawa, bata sonta ko kaɗan, tsawa na firgitata, tsawa na sakawa ta kusa fita a hayyacinta, tsawa na sakawa ta tuna wani moment da bata son tuno shi a rayuwarta, tsawa na sawa har suma tayi, dalilin da yasa a ko yaushe ta ke guje duk abinda zai sa ayi mata tsawa.
tafi minti uku kafin ta dawo normal, da ƙyar ta iya haɗiye yawun bakinta, a hankali ta buɗe ido ta sauke su akansa, irin kallon da yake yi mata gani ta ke kamar zai duke ta...idonta ya ciko da ruwan hawaye, ta shiga ƙiftasu gudun kar su zubo, ta kama jan yatsun hannunta tana danasanin zuwanta, da wannan abun da yayi mata ai gwara tayiwa Kaka gardamar ba zata zo ba.
ta kalle shi suka haɗa ido, ta yi saurin ɗaukewa tana jin faɗuwar gaba.
Muryarsa har cikin kanta ya ƙara cewa,"Do I look like someone who would talk to you and ignore?".
Da ƙyar ta iya buɗe ido tana kallon yatsunta, shi wai bai san bata jin wannan yaren ba ne da yake ta ɗaga mata murya da shi. ita bata san ba ma ko abincin ma baya ci da kansa sai an bashi, ƙilan shi yasa yake tayi mata wannan ihun, to ai ba laifinta bane laifin babarsa ne da bata yi mata wannan bayanin ba, kuma ma ya za'ai ace wannan ƙaton ba zai iya cin abinci da kansa ba, banda dai lalacewa.
in cool voice dake rawa tace masa,"kayi haƙuri ka daina ɗaga muryar, ni ban san me kake cewa ba shi yasa, bana jin wannan yaren".
Yay ma ta wani uban kallo kafin yace,"na farkon ma ba ki ji ba?".
tace,"wanne?".
Ya galla mata harara bai ce komai ba, haka kawai taji tana tsoronsa, yanda taga ya jijjiga kai bata san me zai aikata ba, saboda haka hannunta na shaking taja kujeran ta zauna a ɗarare.
"na zauna". ta faɗa tana kusan ƙwarewa.
ta wutsiyar ido yake kallon hannunta dake rawa akan plate, yana da tabbacin yarinyar nan bata da isashshiyar lafiya.
Muryarsa a kausashe yace,"buɗe abincin kici".
ta wani waro ido waje ta kalle shi, cin sanyin jiki tace,"na ƙoshi".
rufe bakinta ya haɗe da wani mugun kallo daya watso mata, bata san lokacin da ta damƙe plate ɗin abincin ba.
Turaki kuwa kallon ƙasusuwan jikinta kawai yake, ina alamar ƙoshi anan?, kamu ɗaya zai yi mata ta ɓalle gaba ɗayanta, idan kuwa yace zai yi mata kallon tsab sai ya ƙirge duka ƙashin jikin nata, kuma a hakan ta ke ikirarin ta ƙoshi.
ya karkato kanta murya a ɗage yace,"kin ci abincin nan ko sai na miƙe kinga asalin tsayina?".
babu shiri Fillo ta kai hannu cikin plate ɗin zata fara ci, ya dakatar da ita cikin tsawa da cewan,"ɗau spoon".
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*10*
wannan tsawar da Turaki ya sakar mata ita tasa ta rikicewa gaba ɗaya, she was completely out of her mind, spoon ɗin da ta ɗauka ya faɗi ƙasa ya bada sautin wata ƙara wadda sai da Turaki yasa hannu ya toshe kunuwansa.
haushin hakan yasa shi damƙo hanunta cikin zafin nama, wanda bai san lokacin da yay hakan ba. ɓacin rai ne kawai, jin mugun riƙon da yayi mata sai kawai ta fashe da kuka tana ƙara rumtse idanuwanta da kyau, ta shiga girgiza kanta a hankali cikin zubar hawaye masu zafi.
muryarta tayi can ƙasa, amma hakan bai hana lafuzan bakinta shiga kunnansa ba, thats why he focuse attention on something she is saying. "dan Allah kar kiyi mata komai". ya so yaji dukkan abunda tace sai dai hakan ya gagara, sai wanda kawai ya tsinta, kuma daga shi ɗin tayi shiru, bata sake cewa komai ba sai shashsheƙar kuka da ta ke yi.
ya ƙura mata ido kawai yana dubanta da kyau da kuma mamakin fitar hayyacin da tai a lokaci ɗaya, ba sai an faɗa masa ba da ganin yarinyar yasan bata da isashshiyar lafiya. lokacin da ta dawo cikin natsuwarta ta shiga buɗe idanuwanta a hankali ta sauke su akan hannunsa da har yanzu ke riƙe da nata gam.
ƙirjinta banda up and down babu abinda yake, idonsa na kan dining table ɗin da alama wani abu yake tunawa, hakan yasa bai san da buɗe idanuwan nata ba sai jin maganarta yayi.
"Hannuna". ta faɗa muryarta na fitowa a hankali. ya ɗago ido ya kalli hannunsu dake haɗe, sai kawai yasha mur sannan ya kalleta yace,"ba ki da hankali da za ki sakarwa mutane cokali yayi wannan uwar ƙarar, kuma kukan na uban mene?".
bata ce da shi komai ba tayi shiru, ƙoƙarin ta janye hannunta ta ke amma yaƙi sakinta, ta matse ido kaɗan ta buɗe tare da cewan,"ka matse min fata". sai a lokacin ya ankare ya sakar mata hannu, ta wutsiyar ido ya kalli yanda fatar wurin tayi jawur.
ita dai tunda ya sakar mata hannun sai ta kama wajen tana shafawa a hankali saboda zafi, so take ta gama hucewa ta miƙe ta tafi inda tafi kauri, tafiyar da ba zata ƙara dawo da ita nan ba, wannan zuwan nata shine na farko kuma shine na ƙarshe ba za'a kuma wani ba.
ta miƙe zata bar kujerar ya ɗaga kai ya kalleta, murya a tamke, fuska a ɗaure yace,"koma ki zauna, in kinga kin tashi a wurin nan to kin cinye wannan ƙazantar taki".
ta kalli abincin ta kalle shi, ta ɗan haɗe fuska sannan tace,"Hajiya ce ta girka bani ba ai".
yanda muryarta ta kumbura wajen faɗa sai ya zamana kamar da rashin kunya ta faɗa, hakan yasa yay saurin ɗagowa, da miƙewarsa tsaye da kai hannu fuskarta zai mareta duk bai san lokacin da yay ba. banda Allah ya taimaka tayi saurin yin ƙasa da fuskarta da sai ya sharara mata marika.
ya yiwa dining table ɗin wani mugun duka hannunsa na dunƙulewa akai. "saboda nace kici ƙazantarki shine za ki buɗe ba ki kice min Hajiya ce ta girka, what do yo mean by saying that?".
ta ƙanƙame jikinta saboda ganin kamar zai saka ma ta hannu, ya hankaɗa kujerar baya ya fito yay tsaye gabanta, tana jin yanda hucin isakar hancinsa ke sauka a jikinta. kallonsa ta ke ta ƙasan ido, zata iya rantsewa wannan mutumin ko me jinnu ko kuma me ƙarancin lafiyar ƙwaƙwalwa.
yana shirin kai hannu ya shaƙi wuyanta don ta fassara masa abinda ta ke nufi da maganarta, sai ga Zaytuna ta shigo parlon, tun daga bakin door da ta hangesa tai saurin ƙarasowa ta riƙe hannunsa tana dubansa a rikice.
"matsa baya". tace da Fillo wadda ke duƙe har lokacin, kuma jin hakan yasa tayi saurin matsawa da baya ta raɓe daga bango tana sauke numfashin kamar wacca tayi tseren gudu, zuciyarta cike fal da tsoronsa.
Zaytuna ta juya ta ƙara kallonta sannan ta ƙara maido da kallonta kansa. "please Hamma nah sorry".
idan da zata zauna zaman lissafi zata iya lissafa wucewar kusan rabin shakara rabon da taga ya shiga cikin wannan mood ɗin, mai sauya shi ya fita daga Turakinsa ya koma wata halittar ta daban. zata faɗa ko aina ne he is very simple Man, abu biyu ne kawai a duniya masu rikiɗar da shi, su saka ya fusata har ya aikata wani mummunan abun ba'a cikin hayyacinsa ba.
sai dai mamakin da ta ke taya Fillo ta fama masa ciwon dake zuciyarsa, ko kuma garin ya ta taɓa abunda zai iya aikata kisan kai akansa?.
tana kallon Fillo tace,"me kika yi masa?".
tana girgiza kanta tace,"ni ban masa komai ba. abinci yace sai na cinye kuma ni na ƙoshi".
"an kira shi a waya ne?".
"ni ban sa ni ba".
Zaytuna tayi shiru, dole cikin biyun abunda ke haddasa masa ƙunci zuci ya faru. tasan ko menene baida alaƙa da mahaifiyarsu tunda Fillo bata san komai ba akai, amma duk yanda akai bisa kuskure ta taɓa Maama, shi kuma ɓangaren da baya ɗauka kenan.
idon Fillo na kan Turaki, tsab zata iya lissafa adadin jijiyoyin da suka fito raɗau ajikinsa, tun daga kansa har hannayensa da wuyansa. fahimtar da tayi masa mutum ne shi da ba'a sanya mahaifiyarsa acikin kowanne lamari saboda muhimmancinta. kuma ita sai a yanzu take ganin rashin kyautarwarta, bai kamata dan yace taci ƙazantarta ba ta buɗi baki tace ai Hajiyarsa ce ta dafa, kenan jagwalgwalon ba nata bane na uwarsa ne, matsayinsa na wanda tasan ya bata shekaru da yawa bai kamaci irin wannan maganar daga gareta ba.
ko babu wannan ma yaci ace ta darajarta shi duk da jin kai da ta fahimci yana da shi, tunda ita da Kakarta a ƙarƙashinsu suke rayuwa sama da shekaru biyar, ba'a taɓa haɗasu da mara kyau sunci ba matsayin su na ƴan aiki, haka kuma ba'a basu makwanci mara kyau ba. idan ba zata manta ba me gidan da kansa na shiga ɓangarensu ya gaida tsofaffi, Hajiya Madina ce ma bata taɓa gani amma ta taɓa ji ance ta shiga sau ɗaya.
kawai sai tayi ƙasa da idonta tana jan yatsun hannunta, maganar Kaka na dawowa cikin kunnenta na wani lokaci can baya da ta taɓa faɗa mata.
"Halima dan Allah ki rage jin kai domin ke ba ɗiyar kowa bace, ki rage zafin zuciya, ki zama me haƙuri, ki zama mai sadda kai ga wanda duk kika san ya shiga ɓacin rai ta sanadiyarki, karki ce ba za ki bada haƙuri ba domin tsugunawa wada ba gajiyawa bane, ka zama me haƙuri ma da iya bada haƙuri wani babban arziƙi ne gare ka...bada haƙuri babu abinda zai rageki da shi sai dai ma ya ƙareki da abubuwa da dama...zai iya sawa aga mutumcinki, zai iya zama silar ɗaga darajarki".
Fillo ta rufe ido ta haɗiye wani busashshen yawu, a hankali ta shiga sauke gwiwoyinta har ta kaisu kan ƙasan tiles ɗin. muryarta ta fito da amon rashin jin daɗi tace,"dan Allah kayi haƙuri".
hannunsa na cikin na Zaytuna ya damƙe da kyau, ya waigo yana mata wani irin kallo kamin yace,"cinye abincin nan shine zai wanke ki".
itama sai ta ɗago ido ta kalle shi,"to idan na cinye zaka haƙura?".
"kurma ce ke da ba kiji me nace ba".
faɗin hakan yasa ta miƙe ta zauna kan kujerar, har yanzu hannunta bai bar rawa ba ta ɗauki spoon ta fara tura abincin bisa dole. kuma har lokacin suna tsaye shida Zaytuna idanunsu duk akanta, daga yanda ta ke ci yasan cin dole kawai takeyi, sai dai shi babu ruwansa ko zata amayar sai ta cinye.
sai da tacinye tass tukunna ta ɗago da kanta ta kalle shi idonta na zubar da hawaye, yay saurin rumtse idonsa yana kauda kai gefe, idan da abinda baya son gani a rayuwarsa shine hawayen mace.
yana jin zata miƙe ba tare daya kalleta ba yace,"wa zai shanye miki tea ɗin?".
jin hakan yasa tasa hannu ta ƙara goge wani hawayen, sannan ta kalli Zaytuna tace,"Anty na ƙoshi idan na kuma cin wani abu amai zanyi".
Zaytuna tace da shi,"Hammah ai mata afuwa".
ya wurgawa Zaytuna wani kallo sannan yace da Fillo,"kin zuba kinsha ko sai na barki da Allah akan zagar min Uwata da kika yi".
tai saurin girgiza masa kai.
yace,"to zuba rabin kofi ki shanye".
tana zuba tea ɗin tana hawaye haka ma har ta shanye bata bar kuka ba. sai a sannan yay ƙasa da murya yace,"aikin da aka kawoki shi kawai za ki dinga yi, duk ranar da kika ƙara gigin saka hannu a abinda zanci sai kin cinye shi ta hanci".
yana faɗar hakan ya bar wurin, yana fiddo waya daga aljihunsa yay picking call ɗin Bello Ƙaraye dake shigowa. a bakin ƙofar parlo ya tsaya yana cewa,"bana part ɗina ina part ɗin Maama".
da faɗin hakan ya katse wayar ya maida aljihu sannan ya nufi kujera ya zauna.
Zaytuna ta wuce upstairs bayan tace da Fillo idan baƙo ya shigo ta kai masa ruwa da lemu. ta amsa da tou, sannan ta miƙe ta kwashe kwanukan abincin da aka tursasa mata ci ta kai su kitchen, ta dawo ta gyara wurin ta goge ya zama fess sai ƙyalli glass ɗin yake.
a kitchen ma kusan duk wani abu da ake cin abinci acikinsa sai da ta fito da shi ta wanke,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 73