Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
behind. "kana jina Bello?". ta faɗa a sanda ta ke yiwa Zaytuna nuni da dining area, inda a lokacin Zaytuna ta miƙe ta isa wurin dining ɗin, ta ɗauki cup ta tsiyaya watermelon juice aciki, ta ajiye jug ɗin sannan ta dawo ta miƙawa Maama. "ina jinki Maama". lemun dake hannunta ta kurɓa kamin tace da shi,"application for annual leave, ina ce ka miƙa musu ko?". Yace,"ehh Maama na miƙa tun a washe garin ranar da yay accident ɗin". Tace,"good, how many months kasa?". yace,"munyi waya da shi yace na saka just 1 week". ta ɗago ido ta yiwa Turaki wani kallo na ashe baka da hankali, hakan kuma yasa yay saurin sauke idonsa ƙasa, duk da bai san akan mene kallon ba tunda ba jin abinda Bello yace yake ba, amma wannan kallon yasan ba a banza ba. Ta kalla goshinsa da ƙaton plaster ke manne a wajen, sannan ta tsurawa kafaɗarsa ido, tana hasko yanda wajen ke nannaɗe da bandage kwanaki biyar da suka wuce kamin jiya a kwance, ai har yanzu hannunsa na hagu baya moving sosai, amma shine saboda bai da cikakken saiti, yay wannan mummunan accident ɗin sannan yace wai hutun just 7days ya ɗauka, which means monday zai koma aiki. Tai gajeren tsaki, ta lura Turaki nema yake ya kashe kansa a bautar company kawai, yafi damuwa da aikinsa akan lafiyarsa da rayuwarsa, to ita ba ƴar iskar uwa ba ce. Ko da yake shima Bello ba shi da hankalin ai, yana kallo har kusan fitar da rai sukai da Turaki, basu taɓa zaton zai farka ba saboda mugun ciwukan daya ji, amma shine har yake biye masa da ɗaukan hutu na kwana bakwai kawai. Daga ɓangaren Bello so yake yay magana amma yana gudun faɗan da zai biyo baya, dan shima sai bayan daya kai takardar yaga yayi rashin tunani. ta katse tunaninsa da cewan,"then write a resignation letter ka ƙara kaiwa". Turaki da Zaytuna duka a lokaci guda suka ɗago ido suna kallonta da mamaki tsantsa, hatta Bello daga inda yake bai san lokacin daya miƙe daga zaune ba, yana daɗa tambayarta abunda tace. "ehh resignation letter nace, takardan barin aiki ba, And if you can't tell me sai na saka Khalil ya rubuta ya kai". Bello ya haɗiye wani yawu yace,"amma Maama hakan sai nake ganin will not be the best solution, we should just add him a days more off...idan ya dawo sai a san zaman da za'ai da Manager to let him know what is going on". a fusace tace,"karka rubuta ka bari zan rubuta sai na bawa wanda na isa da shi ya kawo, kuma ai dama ban kira na faɗa maka don neman shawaranka bane, umarni nake baka tunanina cewar na isa matsayin mahaifiyar amininka". In calm voice yace,"kiyi haƙuri Maama". Bata ko ba shi amsa ba ta kashe wayar, tana kallon yanda idanuwan Turaki suke kallonta kamar zasu fito waje, amma sai tayi kamar bata san yana yi ba, taci gaba da shafa wayarta har sanda ta nemo lambar Khalil ta kira shi, ringing biyu ya ɗaga. a taƙaice ta amsa sallamarsa ta ɗora da cewa. "You have Bello Ƙaraye's number right?, Anyway if you don't have i will send it to you now, call him and ask abunda na karanta masa, as early as tomorrow morning ka fara aiwatar da abinda nace before you leave to koma ina ne zaka je". Bai tsaya yin wani tambaya ba, haka itama bata jira cewarsa ba ta katse wayar ta ajiyeta gefenta. Ba tare da ta kalli Turaki ba tace,"mun gama magana da Baffa, shima ya amince da hakan, so i do not want to hear anything different... ina ce dama saboda kuɗi kake musu aikin ko?, to mahaifinka ya tara maka arziƙin da har jikokinka ba zasu yi talauci ba, so no need of any job, ka zauna a gida kamar mace, kaci ka sha ka kwanta...bautar company ta ƙare, dan ba zan yarda kaci gaba da yi musu aiki ba suna neman hanyar da zasu kashe min kai saboda kawai kana da gaskiya, ba zan lamunta ba...i won't let anyone kill my son come what may!, aikin ai ba dole ba ne, ko da ace bamu da cin yau balle na gobe, rayuwarka da lafiyarka ta fiye min wannan tsinannan company ɗin". Ba shi da ta cewa a yanzu, dole ne zai yi shiru har zuwa sanda zata sakko ta huce before yay Comprehending nata. bai san reason ɗin daya sa ta ke tunanin accident ɗinsa yana da alaƙa da wasu ke son ganin bayansa ba. "hannun da sauƙi?". Ta tambaye shi tana kallonsa with so much Sympathising na uwa. Ya amsa,"ehh sosai ma". "Allah ya ƙara maka lafiya...tsakanina da wanda ya nemi ya cutar da kai kuma Allah ya isa ban yafe ba, tunda ba wani ya haifa min kai ba". Shi dai bai ce komai ba, ta kalli dining ta kalli Nihal dake shigowa tace,"ki zubo pepper soup". ta wuce dining ta zubo ta kawo mata, ta karɓa sannan ta miƙe ta isa kujerar da Turaki yake, ta kalli mug ɗin da yake aje kan table ɗin dake gabansa tace,"yaushe kasha wannan?". Yace,"ina gama sha kina shigowa". bata ce komai ba ta ɗebo ppper soup acikin spoon ta kai bakinsa, ba son ci yake ba sam amma babu yanda ya iya haka yay ta karɓa har sai daya cinye tas, tana tambayarsa ko zai ƙara yay saurin cewa,"a'a". kansa ya kwantar jikin kujerar ya lumshe ido, Hajiya Madina na waya da wani Asp akan Case ɗin accident da Turaki yayi har 2times, cikin idanuwan Turaki kuwa hoton yanda yay accident ɗin ke haska masa, abunda ya ɗaure masa kai, the samething da wancan, ko da yake gwara wancan yaga motar dake binsa a baya wadda ya tabbatar da attacking nasa ta ke son yi, Amma wannan kam kawai ji yayi burki ya tsinke masa, kuma before he notice anything stearing ya ƙwace daga hannunsa, kamin ganinsa ya ɗauke gaba ɗaya yana tunawa da motarsa ce ɗaya akan titin sai farar motar da ta duki tashi ya ƙarasa gangarawa bakin bishiya, wanda sanadin buguwar kansa da glass kenan kuma sai farkawa yay ya gansa a hospital. Fatansa ɗaya Allah yasa motar da ta buge shi mutanen ciki basu sami matsala ba, saboda ba laifinsu ba ne, shine wajen yayi ƙoƙarin kama stearing ya shiga gaban motar ita kuma tayi saurin kaucewa. Amma Maama ta dage kan motar na sa ne ta hankaɗa shi. yamma liƙis Boɗejo ta shigo parlon, babu kowa a parlon, tai tsaki ta nufi hanyar stairs tana mita. Akan wanne dalili ne ma su duka zasu yashe su wani haura sama after all sun san hawa saman wahala yake yi ma ta. Ƙofar bedroom nasa a buɗe yake, daga bakin ƙofar ta tsaya tana kallon ikon Allah, sai kace wani gwal ko tauraro, yana zaune kan gado sun wani baibaye shi, basu san da zuwanta bama sai da ta shiga ta zauna kan stool ɗin dake fuskantarsa. tace,"wai baka ji sauƙi ba ne har yanzu?, mutum sai kace mace". murmushi yayi bai ce mata komai ba. ta ɗan harare shi tace,"ashe an kwance maka ƙaton rawanin?". Samha tace,"rawani kuma?". tace,"ehh ko za kice min ba haka bane, wadda ba zan faɗi ra'ayina ba sai dai nata". Samha tace,"yo ni wani abu nace Boɗejo, gyara ne fa kawai nake miki...idan wani yaji sai yay zaton rawanin sarauta kike nufi, alhalin ba haka bane...mene haɗin bandage da rawani fisabilillah?". Boɗejo tace,"to banga damar cewa bandage ɗin ba...ina ce ba dake nake maganata ba". Samha bata ce komai ba, Turaki yace,"wai babu wani maganin da akeyi ne irin wannan ciwon ya warke kusa?". Boɗejo tace,"lokacin da muka sameka a asibiti rai a hannun Allah ban bada shawara ba ne?, kaje ka tambayi ita Madinar, sai da nace a kira Waziri ya saka maka hannu a gocewar ƙashin nan sai ce tai inaa ita ba haka ba, gwara asibiti suyi hoto su gano matsalar, yo ni kuwa me zan ƙara cewa wanda ya wuce nayi shiru tunda bani na haifa ba". Turaki yay shiru, ta ƙara cewa,"ƙarafun da asibitin suka danneka da su ba suyi tasiri ba ne da kake neman wani magani na daban?". Yace,"sunyi mana, naji sauƙi fa kawai dai ba yanda ya kamata ba...kafaɗar ce bana iya motsata". tace,"ba sauƙin kenan, ni ai sai dai nace Allah baka lafiya, amma ba dai bada shawarar inda ya kamata akai ka a sama maka lafiya ba, ko kuma maganin da zaka sha...tunda ita Madinar ta ɗauki dukkan yardarta ta ɗora akan bature, yo bature ko gaibu". Zaytuna tace,"Boɗejo asibiti ai ba gaibu bane, yama fi saurin taimakawa lalura". Boɗejo tace,"to ko na asibitin ko na gidan duk wanda akayi ni dai fatana Allah ya ba shi lafiya". Sai kuma ta kalli Turaki tace,"yo kai me ka yiwa mutane suke neman rayuwarka?, gaka dai da kyan hali kuma ni ban san dalili ba, Muhammadu ka faɗa min gaskiya ko dai kana aikata wani mugun abun a ɓoye bamu sa ni ba?". Ya ɗago ido ya kalleta zai yi magana Hajiya Madina ta shigo ɗakin, acikin wayar dake kare a kunnenta cikin tsawa tace,"just do as i said! thats all, i don't want that your blabaring". ta ƙarasa bedside drower ta zauna tana dire wayar da ta katse a gefen Turaki, tasa hannu ta ɗan matsa kafaɗar Turakin, yay saurin rumtse ido tare da yin,"ashhhh". Ya faɗa cikin dauriyar zafin ciwon da yaji. "still dai?". ta tambaya. Shi kuma ya ɗaga ma ta kai. Hajiya Madina tace da Boɗejo,"babu wani mugun abu da yake aikatawa, gaskiyarsa ce tayi yawa, saboda yaƙi bada haɗin kai akan wani cuta da mutanen dake son haɗa partner ship da company nasu, bcox hakan zai jawa company ɗin asara babba. shine yasa suke so su kashe shi dan samun biyan buƙatarsu". Baki buɗe Boɗejo ke sauraronta, tana yin shiru tace,"yo ina dalili anan, wallahi sai ya bar musu aikinsu babu dole, dama kai ka ɗorawa kanka ba ce akayi dan kayi karatu dole kaci ribarsa ba, an tara an ajiye muku, ba ku kaɗai ba har ƴan gabanku, to mene kuma na cewar sai anyi aiki a ƙarƙashin wani?, ina su waye masu bibiyar rayuwar taka?". "Boɗejo ai zar...". Hajiya Madina ta dakar da shi daga abunda zai ce. tace da Boɗejo,"zasu shigo hannu ne tunda ƴan sanda na kan bincikensu". Boɗejon tace,"dole ma a binciko ko su waye, dan babu wanda zai yi kasadar shiga rayuwar jinin Sarki Sulaiman Dukko bai fuskanci tsatstsauran hukunci ba...ɗan babban alƙali kuma jikan sarki, a nemi aga bayanka sannan a zuba ido, hakan ba mai yiwuwa bane...aiki kuma ka barshi har gaban abadan". Hajiya Madina tace,"abunda nace nima kenan, to matsalar yana jin sauƙi abinda ya faɗawa uban akai za'a zauna". Baɗejo ta muskuta tace,"ina ce ai na isa ko?, to bari Dukkon ya dawo ya sameni...wallahi sai dai idan bana numfashi amma wannan aiki dai ba zaka koma shi ba, can suje su ƙarata da duk irin asaran da zasu yi, ai ma'aikatar bata ubanka bace balle asarar ta shafeka". Hajiya Madina ta jinjina da kai da jin daɗin hukuncin Boɗejon. sai dai jin sabon furucinta shi yay saurin dakatar da ita daga shafa masa magani da ta ke yi. "aure ma zaka yi, ka wartsake kaje ka nemo matar aure ka kawo mana, cikin ƙaramin lokaci ba da daɗewa ba, abun yayi yawa ace kamarka baka da aure, ga mata ds yawa nan a dangi, Allah dai ya baka lafiya". Shirun Boɗejon ya haɗe da walƙiyar wani haske a idon Hajiya Madina, hoton abubuwa da dama suka bayyana acikin hasken. Ta san dai tayi ƙasa da idonta, amma bata san lokacin da murfin idonta ya rufe ya buɗe ba, wucewar sakan 1,2,3, wani abu da ita kaɗai ta barwa kanta sa ni ya dira a tsakiyar zuciyarta. Da daddare Baffa yana dawowa Boɗejo ta same shi da kanta a ɓangarensa, tace zuwa tayi ta faɗa masa Muhammadu ya bar zuwa aikin da yake yi acan Habuja, Baffa da yaso yayi ƙoƙarin fahimtar da ita akan hakan ma dake faruwa da shi hanya ce ta matakin nasara a rayuwa, kuma ai mutanen ba zasu taɓa samun nasara ba tunda Allah na tare da mai gaskiya a ko yaushe. tace ita dai indai ta isa Muhammadu ya daina zuwa aikin can tunda ba aljanna ake rabawa a wurin aikin ba. **** *8:00am.* Fillo na zaune a uwar ɗaki da ƙur'ani a hannunta tana karatun suratul yasin, taji daɗin jikinta sosai tun aduar da Amir yay ma wancan ranar, daya je gida haka ya jido mata ruwan adu'oi daga wurin mahaifinsa ya kawo mata, ruwan adu'ar da suka zama na shanta yanzu, shi yasa yanzu sumul ƙalau ta ke jinta kamar bata yi wani ciwo ba. ta rufe qur'anin a sanda ta kai ƙarshen sura, ta tashi ta koma kan katifarsu ta kwanta, idonta na kallon rufin ɗakin. tasa hannu tana shafa kusa da ita wurin kwanciyar Kaka, ji kawai tayi ruwan hawaye ya cika idanuwanta ba tare da ta san da zuwansu ba. tun ƙarfe shida da rabi Kakan ta fita aiki cikin gida, ita ba wai fitar sassafen bace ke damunta, tunda a nan ɓangaren ma ƙarfe shida suke fita, to amma ai anan tana ganin gimlawarta da jin muryarta, amma can idan ta tafi sai dare zata ƙara ganinta. Yunƙurawa tayi ta tashi ta nufi jakar kayanta ta zuge zip ɗin, sai kawai ta zubawa kayan ido, bata san wanne zata saka ba dan yau Kaka ta manta bata ɗauko mata wanda zata saka ba. Kamar zata yi kuka ta shiga ɗebo kayan tana fito da su, kayan duk sun tsufa da yawa, kwana biyu Amir bai yi mata ɗinki ba kasancewar bashi da kuɗi, kullum haƙuri yake bata. Atamfar ta ɗaya ce me kyan gani ta sallah ƙarama daya ɗinka mata, kuma da so take sai babbar sallah zata kuma sakata. har tayi choosing wata atamfarta leda sai ta tuna da cewar Amir yace zai zo anjima shi da abokinsa. dan haka sai ta ajiyeta ta ɗauko me sabuntar full cotton ta saka. Ɗinkin riga da skirt ne, ya zauna ɗas ajikinta, rigar ta kwanta a shafaffen cikinta, breastcuff ɗinma yay dai-dai da breast ɗinta maidaidaita, ƙafar nan tata ƴar sirit acikin skirt ɗin. kayan ta maida ta ɗauki ɗankwalin ta fita, wurin Maijidda zata je tayi mata ɗauri irin wanda ta taɓa yi mata Amir yay ta santinsa. don ita ba iya ɗaurin ɗankwali tayi ba, tafi gane ta saka hula akanta. Tana fitowa saukai kiciɓis da Kaka ta dawo, da mamaki ta ke kallon Kakan, wadda kana gani kasan cikin ƙarfin hali take. Saurin riƙeta tayi suka shigo ciki, Kaka ta zauna ta riƙe kanta da taji yana sara mata sosai. "sannu Kaka, ni dama tun jiya nake cewa ba kya jin daɗi kika dage min ke lafiya kike". Fillo tayi maganar kukan dake bakinta na shirin fitowa. Kaka tace,"ni ƙalau nake...ciwon kai ne kawai, kuma ina shan magani zai daina". Cikin sauri Fillo ta miƙe ta shiga ɗaki ta ɗauko panadol da ruwan adu'a da take sha ta kawowa Kakan. Kaka ta karɓa tasha sannan ta kwanta ta rufe idonta kamar mai bacci. Fillo dai kallonta kawai take yi, tsoro da fargaba fal ranta, idan mutuwa tayi mata haka ya zata yi?, ina zata kama?, wa zai zama gatanta?, shikenan sai ta dawo ainihin maraniya ta gaske. Hannu tasa ta goge hawayen daya sakko mata, ta kama hannun Kaka ta riƙe gam. Kusan minti goma Kaka ta farka daga baccin daya fara ɗaukanta, ta kalli Fillo da ta rafka uban tagumi alamu na nuna hankalinta ma gaba ɗaya baya jikinta. Sau uku ta kira sunanta ba taji ba, sai da ta bubbugi kafaɗarta. "tunanin ne kike?". "kin farka?". Tamyaryoyin suka fito daga baku nan su a tare, Kaka ce ta fara amsa mata da cewar,"ehh na tashi amma yanzu zan koma". Ita kuma tace,"to ki koma dan Allah, ƙila isassan baccin da ba kya samu ne kwana biyu". Kaka dai kallonta ta ke yi, tunanin da inda zata fara yi mata bayani take, kamar da wuya ta yarda taje tayi aikin nan, ba don komai ba ganin a halin da take ciki, sannan babbar damuwarta ma taya za'a sami jituwa tsakanin Fillo da su Nihal?. Da ace Zaytuna ce kaɗai to ba zata ji wani fargaban aikata ba. "yau ba'a gama abinci da wuri ba, ko na tambayo miki Yami?". Kaka tace,"a'a naci zuwa anjima...yanzu tashi za kiyi kije kici gaba da aikin dana baro". Fillo ta buɗe baki tana duban Kaka da irin kallon mamaki. murya a kumbure tace,"ba ki da lafiyar ma ba za su yi miki uzuri ba Kaka, ni babu inda zanje na barki ke ɗaya ahaka babu lafiya, suyi aikin da kansu ko kuma su nemi wata". Kaka ta kwantar da murya tace,"a'a Halima ba haka za'ai ba, kinga aikin nan ma fa ba wata wuya ne da shi ba, daɗewar ma da kika ga ina yi saboda mara lafiyar gidan ne, hatsari yayi me muni yana buƙatar kulawa, zama kawai za kiyi idan yana da buƙatar wani abu kiyi masa, idan dare yayi Hajiyar ta sami zama shikenan sai ki taso kiyi tahowarki...kina gani fa kula da shi kawai aka ƙara yawan albashina ya koma har dubu ɗari". Fillo ta daɗa ɓata fuska babu alamar zata amince da zuwan tace,"yau ya kula da kansa, gobe naje in Allah ya kaimu". Ta faɗa tana miƙewa ta fita ta wuce ɗakin Yami, babu kowa a falon su, tana ta sallama ba'a amsa ba. ba tayi mamakin jin shirun Yami ba, wataƙila tana can wurin aiki tana lura da masu yi, tunda ita da Kaka ne manya. Maijidda kuwa ta san ba zai wuce ta kaɗa yawonta ba, ta ɗaga labulen zata fito sai ga Yami ta dawo. kular abincin dake hannun Yami ta karɓo ta shigo ma ta da ita, gaisawa suka yi ta ke faɗa mata Kaka bata da lafiya. jin hakan Yami ko zama ba tai ba ta suka fito suka wuce, idanun Kaka na bisa ƙofa suka sameta. Yami tai mata sannu Fillo kuwa ta shige ɗaki dan ma kar Kaka ta ƙara tada maganar zuwanta cikin gida, tayi shiru a ɗakin tana tunanin dake sakata zubar da hawaye, kiran Yami yasa ta fito. Yami ce ta lallamata ta yarda da zuwan, kafin ta wuce sai da ta ƙara komawa ɓangaren Yami tace da Maijidda dan Allah ta kula da Kaka bata lafiya, yanzu zata dawo ba jimawa zata yi ba. A compound ta tsaya ta rasa entrance ɗin da zata nufa, ƙofofi ne suke kallonta na part har guda guɗu, ita bata san ina Kakan ke zuwa ba, ita bama ta taɓa shigowa nan ba, kuma bata ga kowa da zata tambaya ba, kuma ba zata iya zuwa wurin me gadi ta tambaye shi ba. Ta nan tsaye Khalil yazo ya wuceta, fitarsa kenan ya dawo saboda mantuwar da yayi. yafi minti biyar kafin ya kuma fitowa, ya ƙara wuceta. sai da zai shiga mota sannan hankalinsa ya ba shi kamar fa mutum ya gani tsaye har 2 times. *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *9* Khalil ya kalli me gadi daya buɗe masa gate,"waccan fa?". ya tambaye shi yana Indicavit masa Fillo. Me gadin yace,"ehh tou Yallaɓai nima dai bayan fitowata daga banɗaki nan na ganta tsaye, ina ce ma cikin masu aiki". Khalil ya maida kallonsa ga Fillo, ba fuskarta yake kallo ba, side view ɗinta kawai yake iya gani, tsinin hancin nan ya fita ta gefe kamar allura. to ai kaf cikin masu aikin babu fara kamar wannan, infact bama sa gari dukansu, banda tsohuwar da ya gani jiya su Samha suka ce masa ita ke aiki yanzu kamin a sami wasu. to ko dai ba mutum bace?, banda haka ya za'ai bawa yazo cikin rana ya tsaya sama da minti biyar, kuma bai ganta da jakar kaya ba balle yace baƙuwa ce ta shigo, to wannan ƴar ƙauyen ma baƙuwar wa zai ce?, yana da tabbacin ba tasu bace, and cikin yaran gidan babu me yin ƙawance da wannan villager ɗin. ba tare daya dubi me gadin ba yace,"baka ga lokacin da ta shigo ba ne?". "a'a ranka ya daɗe, bata nan ta shigo ba gaskiya, dan ko second ɗaya banyi da shiga ɗaki na ɗakko radio ba na fito, can kuma ina ɗaga kai na hangeta tsaye a wurin". mamaki ya kama Khalil, ya bar motar a buɗe ya nufi inda ta ke, me gadin ya mara masa baya. taji zuwan mutum wurin, taga kuma inuwarsu a ƙasa inda idonta yake kallo, amma sai tayi kamar bata san da zuwan kowa ba. ai yana kallonta ɗazu yazo ya wuceta yay shigewarsa ciki, ya ƙara fitowa ya wuceta ko sannu kamar bai san darajar ɗan adam ba. To yanzu daya dawo ya tsaya gabanta me ya dawo da shi ko kuma me zai mata?, tukunna ma shirun da yay bai yi magana ba yana jiran cewarta ne?, ashe kuwa wannan ranar zata ƙare akansu. Shi kam Khalil tsayawa yayi yana ƙare mata kallo da yanda ta ke wasa da yatsun hannunta, yatsunta sirara dogwaye gwanin sha'awa, farcenta fari ƙal da shi. abunda zuciyarsa ta raya masa shine yarinyar kurma ce ko kuma makauniya, tunda ga shi dai ko yanzu da ya tabbatar tasan da tsayuwarsu a gabanta ko motsi bata yi ba, tana nan kamar wadda aka sassaƙa. yanayinta ne kaɗai zai nuna maka ba'a waye ta ke ba, amma kyawun surarta ba zaka taɓa cewa hakan ba. "lafiya dai?". Ya tambaya idonsa tarr akanta. Ta ɗago kyawawan idanuwanta farare ƙal da babu ko kwalli ta ɗan kalle shi, tukunna ta mayar da idonta ƙasa tace,"aiki nazo yi?". Da mamaki yace,"Wanne irin aiki?". Har yanzu idonta na ƙasa ta bashi amsa da cewa,"ni dai haka aka ce nazo nayi aiki, Kakata ce ke yi, ita kuma yau bata lafiya". Khalil ya gyara tsayuwa tare da cewa,"kuma sai tace miki idan tazo aikin cikin rana ta ke nema ta tsaya?". ta girgiza kai tace,"a'a, ban san inda zan shiga nayi aikin ba ne". yana daɗa ma ta duban tsanaki, a cikin ƴan ƙauyen ma wannan lamba ɗaya ce. yay wani guntun tsaki yace,"shi kuma bakinki wari yake yi da ba za ki iya buɗe shi kiyi tambaya ba?". muryarta tayi sanyi yayin faɗin,"ai banga mutane ba ne". Yay mata wani kallon up and down na ban haushi sannan yace,"shi me gadin da kika gani ai dodo ne". Fillo na ƙifta idanuwa ta ɗago zata dube shi taga har ya bar wajen, tabi bayan nasa da kallo, saurin tafiya yake amma ba zaka gane hakan ba a lokaci ɗaya. Tana jan yatsunta hannunta tace da me gadin,"Baba ina zan shiga?, ginin ne na gansa da yawa". "ko dan gaba in kika je wuri ki dinga tambaya, ai matambayi baya ɓata". Me gadin ya faɗa yana yi mata nuni da part din Hajiya Madina. Cikin sanyin tafiyarta ta wuce, kawai tsayawa tayi a bakin ƙofar dan bata san ta yanda zata buɗe ba, bata taɓa ganin irin wannan ƙofar ba, inda ma ace handle ne irin wanda ta saba gani sai ta murɗa wataƙila ta buɗe, amma wannan ma ai ba ƙofa bace glass ne kawai. Kusan 2minutes tana tunanin ta yanda zata shiga acikin ranta, sai gani tayi an turo ƙofar daga ciki ta buɗe. ta kalli Sameer dake fitowa wanda bai lura da ita ba, ya saki ƙofan ta ƙarasa rufe kanta sannan ya fara taka steps zai sauka. Fillo dai kokawa ta kama yi da ƙofar, ta tura ciki taƙi shiga, ta kuma yi ƙoƙarin kama handle ɗin ta janyota nan ma ƙarfinta ya kasa. kamar zata yi kuka ta juya taga saura steps 2 ya ragewa Sameer ya gama sauka. Cikin saurin murya tace da shi. "don Allah kazo ka buɗe min". Ko da ya juyo ya ganta kamar ba zai dawo ba sai kuma ya dawo ɗin, ta wutsiyar ido yake kallonta. Maama me ƴan aiki, ko aina ta samo wannan kuma oho. Yasa hannu ya janyo glass ɗin da aka rubuta open daga jikin handle ɗinsa, yay ɗan murmushi saboda yanda yaga Fillo ta kafe hannunsa da ido da alama tana so ta koyi yacce zata buɗe ne saboda gaba. Ya bata hanyar shiga yana ce mata,"ki ke shiga ta back door, in ba haka ba ƙasusuwanki akan wannan ƙofar zasu ɓalle". Gyaɗa masa kai kawai tayi tukunna ta shige ciki, ai bama sai ya faɗa mata ba, dan ta gama ayyanawa daga yau ba zata ƙara dawowa ba. Yau ɗin ma saboda bata so Kaka taji babu daɗi ne shi yasa banda haka tuni ta juya,

Chapter 6 of 73