Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kare fuskarta da tayi. sai lokacin ta ɗago ido ta kalle shi, ita yakewa wani irin kallo da bata son gani a wannan ƙwayar idon nasa da bata kama da ta mutane. muryarta kamar zata yi kuka tace,"Wadu munyal mi anda be min a vondi on". (kayi haƙuri ban san da ni kake ba). ya zabga mata harara ya bar wajen, ya ƙarasa ya buɗe coolers ɗin da Zaytuna ta zuba kayan soye-soyen da tayi, ya zuba chips a plate sannan ya zuba tea a mug ya fice. Fillo tabi bayansa da ido kawai, ita bata tasa ta ke ba, burinta yanzu bai wuce ta sami damar ahiga ɗakinsa ba, ba tare da sanin kowa ba ta gudanar da abinda zata yi. shi yasa ta ƙagu suyi-suyi su fice. *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *12* bayan ta gama jera komai a dining tazo ta tsuguna gaban Hajiya Madina. "Maama ko mai ya kammala". sunan da yaranta ke kiranta da shi itama da shi ta ke kiranta, Hajiya Madinar ta faɗa mata haka a watarana, sanda ta ke ce mata. "Fillo ban taɓa ƴar aikin da nake jinta tamkar ƴar cikina ba irinki, saboda haka daga yau Hajiya ya fita daga bakinki, ki dinga kirana da Maama kamar yanda kika ji ƴaƴana nace min kinji". Hajiya Madina ta shiga kallonta ta wutsiyar idonta ba tare da ta amsawa maganarta ba, Fillo kuma dai har yanzu tana nan durƙushe bata motsa ba, kuma tunaninta bai bata ko Hajiya Madinar bata ji ba ne, a'a tasan taji kawai dai a jininsu ne basa amsa maka nan ta ke sai sun ɗan ɗau lokaci. "oak tom, kije ki zuba naki kici". abinda Hajiya Madina tace da ita kenan. Fillo ta miƙe ta wuce, sannan suma suka nufa dining, by the time Turaki har ya gama nasa, yana zaune wajen yana aikin danna waya. suna cikin yin breakfast ɗin ne wayar Nihal tayi ƙara, ganin sunan dake yawo jikin screen ɗin wayar gabanta ya faɗi, jikinta na rawa ta kai hannu tana gyara zaman medical glass nata, ta cikinsa ta ke kallon Hajiya Madina wacce ta dakata da cin abincin tana yi mata wani duba ta ƙasan ido. duk ta dabarbarce, tsoronta Allah tsoronta kar tace ta miƙa mata wayar. saboda haka tayi saurin kai hannu tai mute na ringing ɗin, sai dai kamin ta ɗauke hannunta daga kan wayar sabon kira ya ƙara shigowa. babu shiri ta haɗiye wani dunƙulallan yawu tare da rufe ido. sai dai kamin ta buɗe maganar Hajiya Madina ta shiga cikin kunnuwanta. "give me the phone". kamar zata yi kuka ta ɗauki wayar hannu na rawa ta miƙa mata. Hajiya Madina ta kashe wayar gaba ɗaya sannan ta miƙawa Khalil, ya karɓa ya saka a aljihunsa. har suka kammala breakfast ɗin babu wani wanda yay motsi na hira ko kuma tsokanar juna kamar yanda suka saba da mahaifiyar tasu, saboda yanayin da ta tashi da shi yau sun kasa gane kanta, ga shi Nihal ta ƙara dagula musu ita. Samha ta ɗaga landline en dake gefensu ta kira wayar ɗakin ma'aikata. bugun da bai wuce 2 ba Fillo dake can ta ɗaga. "ke kizo mun kammala". abinda tace da Fillo kenan ta kashe wayar. wanda a ɓangarenta azamar tashin ta ke yi saboda tana lissafe ne da lokaci, su kan ɗauki 10-15minutes a dining, kuma buƙatarsu da zarar sun kammala da shi ai clearing wurin. tana shigowa parlon Hajiya Madina na shirin hawa upstairs, ta kalleta tace mata. "idan kin gama ki sameni a ɗaki". Fillo ta amsa da,"tou". sannan ta shiga gyara wajen. komai nata cikin sanyin jiki ta ke yinsa amma kuma nan da nan ta ke gama abu, tana gama wanke-wanke bata tsaya ɗora lunch ba tunda tasan basa nan kuma bai wuce suyo takeaway na dinner ba idan sun tashi dawowa. zata wuce ɗakin Hajiya Madina Khalil dake parlon a zaune shi ɗaya ya tsayar da ita. "sojan rana zo nan". ta tsaya daga hawa saman ta juyo da murmushi fuskarta, abunda ke burge shi da ita fara'arta da tsabtarta, bata da wannan cunkus ɗin irin na sauran ƴan aikin da suka yi a baya. har ta ƙaraso ta tsuguna a gefen kujerar da yake zaune bai bar kallonta ba, kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta tace,"Hamma Khalil gani". ta faɗi sunan nasa kamar yanda taji ƙannensa na faɗa masa. yace,"ai nai zaton ko kina ciwon baki ne". ya faɗa da salon zolaya. ta murmusa da cewan,"ciwon baki kuma?". yace,"ehh mana, da na kiraki ai ba ki amsa ba tahowa kawai kika yi". ta saki murmushi me faɗi da cewar,"Hamma Khalil to ai kaine kake faɗin sunan da ba nawa ba, shisa sai nayi zaton ko bada ni kake ba". shima murmusawar yay kafin yace,"yanzu ke tsakani da Allah duk wanda ya ganki ranar nan da kika yi ƙeƙam a tsakiyar rana me zai yi zato?, kinga kam dan na kiraki da sojan rana ai ba laifi ba ne". murmushi kawai tayi bata ce komai ba. "anyway, wanne class kike before ki taho aikatau?". furucin da yay yasa ta ɗagowa ta kalle shi kaɗan sannan ta mayar da kanta ƙasa. "bana zuwa makaranta ai". da mamaki ya kalleta,"gaba ɗaya ba ki taɓa zuwa makarantar boko ba?". ta ɗaga masa kai tabbacin hakan. ya girgiza kansa,"to islamiya fa?". ruwan hawaye ya cika idonta kafin tace,"nayi islamiya kamin Ummi ta rasu, kuma itama tana yi min a gida". yace,"wace Ummi?". sai da tasa hannu ta goge hawaye tukunna tace,"mahaifiyata". lokaci ɗaya tausayinta ya kama shi. "Allah ya jiƙanta". ta amsa da,"amin na gode, Allah yaja da ransu Baffa". shima ya amsa da,"amin na gode. amma kuma idan baki je makarantar boko ba taya akai ranar nan kika karanta saƙon da Maama ta bar miki?". taja yatsanta na tsakiya bata ce komai ba. ya katse shirun,"tambayarki nake". murya a hankali tace,"wanda zan aura ne ya fara koya min yanda zanyi karatu, kuma daga baya sai muka daina saboda ayyuka da suka yi masa yawa". kalmar wanda zan aura ta ba shi mamaki. to amma sai dai aure wa ƙaramar yarinya kamar wannan a wajen ƴan ƙauye ba wani abu bane, wataƙila da ace ba anan suke zaune ba yanzu haka tana da ƴaƴa. ya sauke numfashi yace,"yayi ƙoƙari shi wanda za ki aura ɗin...yanzu yaushe ne bikin?". tace,"ba'a tsayar ba tukunna amma dai da an kusa wani dalili yasa aka ɗaga". ta faɗi hakan idonta na kawo ruwa sosai, kuka ta ke sonyi a lokacin amma saboda Khalil ɗin ta hana kukan samun ƴancin fita daga bakinta, domin bata so ya gano wani ciwo da rayuwarta ke ɗauke da shi. ya ɗaga kafaɗarsa ya ajiye wayarsa sannan ya fuskantota gaba ɗaya. "to kin san menene?, mu a gidan nan idan mutum zai yi aiki dole sai yana karatu, kije ki tambayi duk wanda ya taɓa aiki anan, haka tsarin Baffa yake...and dalilin daya sa ma inaga Maama bata yi miki zancen ba kwana biyu aiki ya sha kanta ne, amma yanzu idan kinje ki tuna mata, akwai Malamin da yake zuwa yana yi muku karatu". ta ɗago ido tana kallonsa, kamar bata fahimci me yake son cewa ba. ya ɗaga mata gira,"ehh idan kinje ki cewa Maama ke ba ki yi karatu ba". ta gyaɗa kai kawai sannan ta miƙe zata wuce. Turaki ya shigo parlon a lokacin yana waya. ta gabansa ta wuce tana ji yana cewa,"me zan yi da yarinyar da bata waye ba, ka bar wannan batun she is not my type...infact ni babu aure ma a lissafin rayuwata". hannuwan Fillo suka murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin ta buɗe, tayi sallama amma ba'a amsa ba. hakan yasa tasa kai zuwa ciki ƙafafuwanta na luntsumewa cikin tattausan carpet ɗin dake malale a duka ɗakin tun daga bakin ƙofa, kai kace cikin auduga kake sanya ƙafa saboda tsabagen taushi. tayi tsaye daga nan bakin ƙofar bayan ta maida ƙofar ta rufe, jikinta take takurewa saboda yanda sanyin ac ke ratsata. ta kusan minti uku tsaye sannan Hajiya Madina ta fito daga wata ƙofa da idan ba sani kai ba ba zaka ce ƙofa bace. da sauri ta durƙusa a ƙasa tana kama gefen zanenta ta riƙe. dalilin wani abu da yayi duka acikin kanta sanadin furucin da taji Hajiya Madina tayi acikin wayar da ta ɗauka yanzu da aka kira. "asiri fa kika ce Lubna, wa ya faɗa miki?". abinda Hajiya Madinan ta fara kenan cikin muryar razani, amma ita a wannan lokacin kalmar asirin ce ke ta maimaituwa acikin kwanyar kanta, lokaci guda kuma hankalinta ya gushe daga cikin ɗakin ta lula wani wurin can daban da tunanin abinda ya danganci asirin. "to shikenan Allah dai ya kyauta...ni ma kinga zamu je gidan Alhaji Babba ne akan lamarin Hammansu, sam yaƙi aure kuma ko zancen auren baya so ayi masa, mun rasa kuma dalilinsa dan ko jiya sun fi awa shi da Baffansa kan ya sanar masa da dalilinsa yace shi babu komai haka ɗaya, sannan babbar matsalar duk wannan nacin ibadar tasa yanzu ba yayi, sai kiga ko sallah ake yana zaune...to shine Boɗejo ke ganin abun kamar ba lafiya ba". Hajiya Madina ta faɗawa ƙawarta Lubna da suke wayar. daga ɓangaren Lubna ɗin tace,"subhanallah, gaskiya kam dai wannan labari ba lafiya ba a tashi a nemi magani, namiji har namiji kamar Turaki ace baya son aure, ai lamarin akwai duba...Allah dai ya kawo komai da sauƙi". Hajiya Madina tace,"amin ya Allah...shikenan sai mun ƙara yin waya, dan Allah karki manta da saƙon nan ki bayar akai musu". daga ɓangaren Lubna ta sake cewa wani abu sannan Hajiya Madina tace,"ina ta ƙoƙarin yin hakan. sai dai ina tsoro Lubna, ban san mutanen dake bibiyar rayuwarsa ba, haka ban san wanne irin shiri suke yi akansa ba, dalilin da yasa na dage akan cewar ya haƙura da kowanne irin aiki zamansa a gida shine kwanciyar hankalinmu, haka kuma shima a nasa ɓangaren wannan ne kaɗai tsaron da zai samu...wallahi ba ki ga munin last accident ɗin da yay ba, Lubna sai dana gama cire rai da shi tukunna ya farfaɗo...amma akan maganar wannan company ɗin da Baffa ke cewa zai buɗe musu wataƙila na yarda ya zama jagoran ciki amma in har bai ɗara daga state ɗin nan ba, amma muddin wani gari ko wata ƙasa ce can daban hakan ba zai yiwu ba". haka suka ci gama da tattaunawa tsawon mintuna kafin suyi sallama. ta ajiye wayar tana mai cewa da Fillo,"buɗe wancan closet ɗin ki ɗauko min wasu takardu daga sama". Fillo ta miƙe dan cika umarninta, tana ɗauko takardun tana mamakin irin jama'ar da Allah ya bawa Hajiya Madina, ko da yaushe acikin yin waya ta ke, inda take gani da itace gaskiya ba zata iya ba, domin idan kunnenta bai ciwo ba to bakinta zai yi. yanzu fa ta gama waya ko minti biyu ba'a ƙara ba amma har an kuma kiranta. "zan bar su a gida, akwai yarinya idan kazo zata baka". abinda ta ke cewa dana wayar kenan, kuma lokacin da Fillon ta ƙaraso ta durƙusa ta bata takardun. "alright sai ka zo". daga haka wayar tasu ta yanke, ta dubi Fillo tace da ita,"gobe za ki fara ɗaukar karatu a gidan nan, ba ke ɗaya bace akwai wata sabuwar ƴar aiki da za'a kawo anjima za kuci gaba da aiki tare. bana son fitina Halima, bana son kuskure, ki kula da hakan. karatun boko da arabiya zai ke yi muku. ki tsaya ki maida hankali, domin akwai aikin da nake so kiyi min, aiki ne na masu ilimin boko, idan kin mayar da hankali, idan har kinyi nasarar samunsa Halima za ki sha mamakin yarda zan mayar da ke, duniyarki zata sauya, za ki zama abar kwantance, bayanki zai zama tarihi, idan kuma akasin hakan, tabbas ina mai tausaya miki da asara mafi girma da za kiyi a rayuwarki". Fillo so ta ke ta ɗago ta kalleta amma ta kasa, jan yatsunta kawai ta ke. "ungo wannan". sai a sannan ta ɗago tasa hannu biyu ta karɓi takardun. "ki adana su, zuwa ƙarfe biyar na yamma akwai wani zaizo ya karɓa, baƙi ne dogo yana da ƙasumba...ba shi kawai nace kiyi, kije masa da fuskar mutumcinki Halima...nasan kin gane lissafina". Kan Fillo a ƙasa tace,"tom Hajiya". "bani lafayata fara". Fillo ta miƙe ta ɗauko ta kawo mata. ta cikin mudubi Hajiya Madina ke ta kallonta, zuciyarta na me jin so da tausayin yarinyar. bata bar kallonta ta cikin madubin ba tace,"zo ki saka min wannam fil ɗin". Fillo ta matso zuwa bayanta ta karɓi fil ɗin a hannunta sannan ta saka mata kamar yanda taga Zaytuna nayi mata a duk sanda ta saka lafaya. ita ta ɗaukar mata jakarta suka fito a ɗakin, suna saukowa ta ke faɗa mata,"akwai key ɗin ɗayan bedroom na Hammansu acikin drower na mirrow, idan mun fita kije ki gyara masa. dan Allah ki gyara me kyau, ki kaɗe duk wata ƙura". "tom Maama, sai kun dawo Allah ya kiyaye hanya ya dawo daku lafiya" har bakin mota tai mata rakiya, Khalil ne zai ja motar dama, ta shiga tana tambayarsu, "ina Hammanku da Nihal?". Sameer yace,"Hamma ba lallai yasan mun fito ba, amma naga Nihal tayi wajensa da nake fitowa". "kira min shi". Sameer ya ɗauki waya ya kira shi, sai dai kamin ta kai ga yin magana ma yace gashi nan fitowa. Fillo kuwa tana komawa key ta ɗauka ta fito ta wuce ɓangaren Turaki, ɓangarensa dake jikin na Baffa. tana shiga parlon taji maganarsa na tashi a parlon. tayi saɗaf ta ɓoye ta wajen wani corrido, dan har ga Allah ita ba so ta ke suke haɗuwa ba saboda bata son wannan tsawar da yake sakar mata, yana sakata tana tunawa da moment ɗin da ba son tunawa da shi ta ke ba. kuma har zuwa wannan lokacin tana ƙyale shi ne kawai saboda darajar mahafiyarsa, banda haka da tuni ta nuna masa tafi ƙarfin ya dinga zaburar da ita dan kawai tana aiki ƙarƙashin arziƙinsu. shi da Nihal ne wadda taji tana roƙonsa akan dan Allah ya bawa Maama haƙuri. maganar ta ke tana karyewa saboda kukan dake fita daga bakinta. ta leƙo taga Turakin na tsaye ne ya harɗe hannayensa ta baya yana fuskantar gabas, kansa a sama kamar me tunani. ita kuma Nihal gwiwoyinta na zube a ƙasa a gabansa. kafin ya juyo gareta yaci gaba da magana bayan shirun da tayi. "arziƙi da talauci duka na Allah ne, idan Allah ya baka arziƙi ba yana nufin kafi kowa bane acikin bayinsa, kuma ba wai an baka dama ba ne dan ka wulaƙanta wanda bai da shi ba, shima idan Allah yaso yana iya ba shi nasa rabon, ko kuma ya ƙwace daga hannun kai da kake wulaƙanta talaka ya bawa wanda ka raina...but kin san me nake so ki fahimta?". Nihal ta ɗago da kanta tana kallonsa, sannan ta girgiza kanta alamar a'a. shi kuma yaci gaba,"Mama uwa ce da yau ba zata so ace ƴarta ta shiga gidan da zata wahala ba, wannan haka yake ga kowacce uwa...burin iyaye ne ace ƴaƴansu sunyi aure sun zauna a inda zasu ji daɗi, dan haka Maama bata hana alaƙarki da shi ba ne saboda yana talaka ba...". tun bai kai ga ƙarasawa ba ta katse maganarsa,"Allah Hammah tace makusarsa a wajenta shine talaucinsa, banda haka babu abinda zai hana ta barina mu'amala da shi...kuma ni wallahi Hammah ina sonsa, shi kaɗai zuciyata ke da muradin aure". ya kai hannu ya shafo wuyansa yana mai lumshe ido ya buɗe. "ba za'a hanaki aurensa ba dan kawai yana talaka, idan har na gari ne to ba shi da wani aibu a idon Baffa...saboda haka ki kwantar da hankalinki, ta shi muje". ta miƙe ya kama hannunta suka fita. Fillo ta sauke ajiyar zuciya, duk yacce ta ke tunanin mutumin nan ba haka yake ba. shi ɗin me kyau ne, kuma ta fahimci yana da kyan zuciya. Da yawan masu business suna so advertisemnt ɗinsu yazo da wani salo da kai kanka zai burge ka. *LOGO* tactics ne na janyo hankalin customer. Now mutane da yawa will think haɗa logo na d wuya but in truth indai mutum zai dage its simple like ABC. android phone kawai kuke buƙata da Knowledge n graphic design. abunda ake samun kuɗi da shi yanzu shine graphics design, kuma the minium abinda ake samu per desgn 500 ne...Imagine idan a kowacce rana zaku yi aikin mutum 5...500×5=2500 to d zaman banza ba gwara ki koyi abinda ko da ₦100 ne kike samu kullum b akan babu. Students da ke zaman ASUU you can leverage on it before resuming school. this 2500 na kullum abinda zai yi making a month is 75k. to ko d wannan 75k b kya ja jari ba? now if ace kina son koya and we are ready to teach u this graphic design a kuɗi ƙalilan? Normal Price is 2k wanda zasu biya da wuri is 1500. Special Class is 5k. lecture wll commence on 27th of this month...start making your payment before loosing this big oppurtunity. contact 08024976578 *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *13* Hakimi wato Alhaji Babba zaune akan royal chair ɗin dake tamfatsetsen parlon da ya gaji da tsaruwa da kayan alatu, duk wani kayan jin daɗi na mo re rayuwa an zuba a wannan parlon, haka idan har kai farin shiga ne a zuwa gidan, to tabbas zaka iya rantsewa ba'a ƙasar nigeria kake ba. farin rawani ne akansa, kana masa kallo ɗaya zaka san jinin sarauta ya gama ratsa shi. kamar yanda tarihi ya gabatar, an kafa Masarautar Gombe a shekarar 1804 a lokacin jihadin Fulani wanda Buba Yero mabiyin Usman ɗan Fodio ne. Buba Yero ya mai da Gombe (Abba) hedikwatarsa ​​domin yaƙin da ake yi da matsugunan Jukun na Pindiga da Kalam, daga nan kuma yayi ta kai hare-hare har zuwa Adamawa da ke gefen kogin Benue. a lokacin sarki Alhaji Bukar Dukku shi ke riƙe da sarautar garin gombe, bayan rasuwarsa ne kuma babban ɗansa Hashim Bukar Dukko ya karɓi sauratar, wanda ya riƙe sarautar tsawon shekaru masu yawa. Sarki Hashim Bukar ya ajiye ƴaƴa a ƙalla guda takwas kuma dukansu maza, kuma duk su takwas ɗin sun fito ne daga tsatson mace guda ɗaya Sarauniya Falmata, wacca a lokacinsu ne aka kafa tarihin sarkin daya zauna da mace ɗaya tal a karagar mulkinsa har rayuwarsa ta ƙare ba tare daya mallaki ko da ƙwarƙwara ba. cikin ƴaƴa takwas daya bari sune Adam, Ishaq, Lateef, Harun, Ibrahim, Yusuf, Isma'il, Shu'aib. akaf cikin yaran babu wanda ya samu kulawa me girma da gata daga wurin mahaifinsa irin babban ɗansa Adam, kasancewar tunda Sarauniya Falmata ta haife shi sai da ta shafe shekaru shida kafin ta ƙara samun wani cikin, lokacin har sun yanke tsammani da samun wani rabon, kuma daga haihuwar Yarima Ishaq shikenan ta shiga jero haihuwar ƴaƴa har sai da ta jera 8 gaba ɗaya. duk da ƙarancin shekaru da Yarima Adam ke da shi a wancan lokacin, hakan bai gaza fahimtar cewar shi wanene ba, ya san daga tsatson daya fito, domin a ko da yaushe mahaifinsa na faɗa masa cewar gaba da bayansa shi ɗan sarauta ne dan ko mahaifiyarsa ma ƴar sarki ce. bayan tarin ƙauna, soyayya, gata da kulawa wadda Yarima Adam ya samu a wurin mahaifinsa da mahaifiyarsa, sai kuma na ɓangaren al'umma. waɗanda suke ƙasƙan da kansu a gare shi matsayinsa na ɗa ɗaya tilo a wurin Mai Martaba da suke jin basu da tamkarsa. hakan kuma ya haifar da aƙida ta girman kai da gadara a wurin Yarima Adam, har ta kai ga yana nuna ƙasƙanci ga na ƙasansa, hatta ga hadiman dake kewaye da Sarki kuwa. tun kamin ayi masa ƙanne ya haddace wani furuci dake fitowa daga bakin al'umma na kirarin da suke yi masa da Yarima Sarkin Gobe, kai ɗaya ne Yariman da akai babu irinsa, bayanka sarauta gabanka sarauta. amma tun daga lokacin da mahaifiyarsa ta ƙara haihuwa sai yaji salon wannan kirarin ya sauya, kuma bai gyaru ba har zuwa lokacin da ta tsaya da haihuwa, kirakiran ya tashi daga kansa shi ɗaya ya koma har ga sauran ƴan'uwansa. dalilin da yasa zuciyarsa tayi baƙi kenan akan ƴan'uwansa, dan yana ganin silarsu zai iya rasa wasu tarin nasarori daya rubuce su a tafin hannunsa. da tafiya tayi tafiya sai ya zamana sam Yarima Adam baya ko da raɓar inda ƴan'uwansa suke, tsakaninsa da su nisantar juna, basa samun fuska a wurinsa matsayinsa na babbansu. tun zuciyarsa na raya masa wani abu wai shi ƙiyayya har hakan ta tabbata akan ɗan'uwansa Yarima Lateef, wanda ya ƙwace duk wata fada da yake da ita a wurin mahaifinsu, wannan soyayyar da gata da dukkan komai da ya samu lokacin da yake shi ɗaya daga wurin mahaifinsa gaba ɗaya sai ta koma kan Yarima Lateef, hatta da soyayya da girmamawar da al'umma suke ba shi. kuma hakan ya samo wuri ne dalilin banbancin halayya, cikin kaf su takwas ɗin da Mai Martaba ya mallaka babu wanda ya ɗauko kyawun halayyarsa da ɗabi'unsa sai Yarima Lateef, shine yasan darajar mutane, saɓanin sauran da suke nuna ƙasƙsanci ga mutane, haka shine kaɗai mai sauƙin kai amma kaf sauran suna da mummunar ɗabi'a ta girman kai, kuma shi ɗaya ne mai son mutane da yi musu fara'a, gaba ɗaya Yarima Lateef kan manta da cewar shi ɗin jinin sarauta ne kasancewar ba'a gabansa take ba, amma ƴan'uwansa sarautar itace abar alfaharinsu da tunƙahonsu, a karan kansu sukan ji tamkar su mutstsuke juna saboda girman izza, kowannensu mulki da muƙami kawai yake wa hari a rayuwarsa amma banda Yarima Lateef. shakarun Yarima Lateef 24 a duniya mahaifinsa ya aura masa ƴar gidan wazirinsa me suna Rumana, itama kuma sai ta samu matsuguni na soyayya a wurin Mai Martaba ta dalilin ɗansa da take aure, dan tunda akayi auren Mai Martaba da Sarauniya Falmata suke kiranta da gimbiya. a wannan lokacin Yarima Lateef yayi auren biyayya ne kawai ba don yana son Rumana ba, sai bayan auren kuma ya gane cewar zaɓin mahaifinsa kyakykyawan zaɓi ne a gare shi, kuma dama abinda yasa baya son auren ganin cewar yayyansa Yarima Adam da Yarima Ishaq basu yi aure ba, sai yake ganin kamar babu dacewar ace shi ya riga su yin aure. wannan aure na Yarima Lateef shi ya ƙara janyo masa baƙin jini a wurin ƴan'uwansa musamman Yarima Adam. kuma auren nasa babu jimawa shima Yarima Adam ɗin ya bijiro da nasa inda ya kawo ƴar gidan gomnan garin gombe a matsayin wacce zai aura, bayan zugo shi da Jakadan Sarki yayi akan cewar muddin yana son kujerar mahaifinsa to yayi aure tun mahaifinsa na raye, idan kuwa ba haka ba wannan burin mulkin nasa da saurautar zasu ta shi a tutar babu ne, dan zai kasance abu me wahala a ba shi saurauta alhalin baida iyali. shi kuwa a sanda Jakada ke ba shi wannan shawarar ji yake da zai iya kashe Lateef ba tare da kowa ya sa ni ba da babu abunda zai hana shi, to tsoronsa ɗaya ne, ya riga ya sa ni abu ne me sauƙi Mai Martaba yasa shima a kashe shi ko kuma ya kashe shi da hannunsa. dan Mai Martaba kan mance da kowa da komai akan Yarima Lateef, kuma yasha tarasu ya faɗa musu cewar zai iya yin komai akan Lateef. kuma bayan rasuwar Sarki Hashim Bukar anyi tata ɓurza wajen naɗa magajinsa, don har sai da ta kai ta kawo duka Yaran sun fito da abunda yake zuciyoyinsu ƙiriƙiri, rigima ta ɓarkewa junansu kowa na ganin ya cancanci a basa wannan sarautar. majaifiyarsu Sarauniya Falmata ta shiga tashin hankali mara misaltuwa akan babban yaƙin dake shirin ɓarkewa, Lateef shi ɗaya ne me ƙoƙarin ganin ya kwantar mata da hankali domin har sai da ta kai ga ya ɗauketa daga ƙasar ya fitar da ita da matarsa me jaririn yaro a lokacin, saboda komai zai iya faruwa hatta ga rasa rayuka kuwa. to amma dai yake Allah ya tsara cewar Lateef shi zai hau kujerar mulki, duk irin yanda Adam ya kai ruwa rana wajen ganin ya hana faruwar hakan shi da muqarrabansa amma Allah bai ba su iko ba. daga ƙarshe haka dole suka haƙura suka zubawa sarautar Lateef ido wadda yake gudanar da ita cikin gaskiya, tausayi gami da jin ƙan al'umma kamar yanda mahaifinsa ya aiwatar a lokacin nasa mulkin. Sarki Lateef ya gaji mahaifinsa ne wajen auren mace ɗaya tun auren da mahaifinsa yayi masa na Rumana, kuma lokacin da Sarauniya Rumana ta haifi ɗa na uku Allah ya yiwa Sarauniya Falmata rasuwa. bayan rasuwartata ne wannan ɗan guntun haɗin kan dake tsakanin ƴaƴanta wanda yake na dole a gare su saboda ganin idonta sai

Chapter 9 of 73