Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a mota ba, becouse kai ka fini sanin kaya masu kyau, idan ni ɗaya ne za'a iya haɗani da fake one". Turaki ya ɗan ciji leɓensa kaɗan sannan yace,"why not su turo da kayan kawai ba sai anje ba". Bello yace,"yanda ma fake one's ɗin zasu fi zuwa kenan. Maama already ta riga taga hotunan su, dan ko launching nasu ba'ayi ba, shisa tace naje ayi a gabana, so ta re da kai dai zamu tafi". Khalil yace,"shikenan Turaki Flour Mills ya tabbata kenan, dan nasan hakan za'a saka tunda Maama ce ta kawo idean". Bello da sigar tsokana yace,"ah haba dai sai kace shi ɗaya ne ɗa, ai sai dai a haɗa sunan mu duka". Turaki ya taɓe baki ya miƙe tsaye yana faɗin,"i don't think i will go with you, kayi tafiyanka kawai ko kuma kuje da Khalil. beside; Sameer ma na Hong Kong ɗin kana iya samunsa acan". Bello yace,"aiko dole sai kaje, ka zama cikin shiri kawai Malam, coux daga nan ma tictiket ɗinmu zanje amsa". ba tare da Turaki ya ƙara cewa komai ba ya fice daga parlon. direct part ɗin Boɗejo ya nufa, acan ya tarar da sisters nasa duka a zaune sun saka Boɗejo a tsakiya sai hira suke, sai bayan ya zauna kan kujera ya fahimci lissafi suke tayi, lissafin aurensa. Samha cikin zumuɗi da tsananin murna take faɗin,"ai Boɗejo babu zancen wani 1week, biki zamu fara from day 1 to day 10, kuma kowacce rana sai mun zubar da naira, sai doller tayi kuka ita kanta sai ta san ana bikin first born a gidannan". Nihal ta taso a kusa da Boɗejo ta dawo kusa da Turaki, ta kamo hannunsa tana cewa,"please Hammah ka sama mana Anty kaji, Allah mun ƙagu ayi bikinka, Allah duka burinmu na kan wannan ranar Hammah, I feel like your wedding day is the first wedding in the world". shima ya riƙe hannun nata yana kallon innocent face ɗinta yace,"to kun zaɓa min matar ne?". dai-dai nan Samha ta taso itama ta zauna gefensa,"ka yarda mu zaɓa maka Hammah?, akwai friends ena da friends Zaytuna da yawa da suke sonka, duk basa ƙasar nan, gasu kyawawa masu class, sai wacca muka ɗaukar maka". tana kallon Zaytuna tace,"ina wannan balarabiyar ƙawar tawa da mukai vedio call ranar nan?, kin tuna ta?, basu dace da Hammah ba don Allah?". bata jira cewan Zaytuna ba koma garesa tana ƙara cewa,"Hammah ka yarda muyi maka zaɓi?". ya kalleta sai kuma ya kalla Zaytuna wadda ke ta kallonsa da tarin murmushi. kamar ba zai ce komai ba sai kuma yace,"kuyi adu'a Allah ya kawo ta gari, aure ai lokaci ne". Boɗejo tace,"a'a lokacinka fa yayi kai harma ya wuce tuni, dan dai kawai Uwarka da Ubanka sun zuba maka ido ne, sai abinda kake so za'ai, yo wannan gata ai ba gata bane. kai in baka san mutumcin mutum aure ba ai su sun sani, to ni dai ina gajiya sai na haɗaka da duk wadda naga dama, Allah na tuba ƴan mata gasu nan birjik a danki...kuma dai ma ni in faɗa maka yar gida muke so jinin sarauta ba bare ba, ah tou karma lokacin da hankalinka zai dawo jikinka kace zaka ɗauko wata can daban, ina ga Madina ce kawai ta shigo zuri'armu a bare". shi dai bai ce komai ba ya jinginar da kansa jikin kujerar. Nihal ta daɗa riƙe hannunsa sosai tana faɗin,"can't wai to see your wedding day Hammah, wayyo Allah wa ya ganni da Sister inlaw". ta faɗa cikin wani irin expression tana faɗawa jikinsa. ranar a part ɗin Boɗejo suka yi lunching, shi Turakin ma bai iya cin komai ba, yanayinsa kamar dai wanda bai cikin natsuwarsa. after la'asar ma da ya dawo daga masallaci part ɗin Boɗejo ya koma, lokacin da ya shiga bedroom nata tana waya da Inna Falmata. ganin shigowar tasa yasa tace,"to sai anjima Falmata, a dai ci gaba da aiki me kyau don Allah, kinga acikin sati huɗu yau munci kwana biyar, to shi haka lokaci yake sai dai idan ba'a saka shi ba, nan dai nan sai kiga yazo". daga haka ta kashe wayar ta ajiye a kusa da ita, ta kalli kan gadonta da Turaki ya kwanta, he don't know why yake jin jikinsa yayi sanyi, tunda Bello yace masa zasu yi tafiya tare yake jin wani feeling mara daɗi a tare da shi, and for the first time da yake jin kamar zai rasa rabin jikinsa, Boɗejo ta kai hannu ta taɓa ƙafarsa taji zafi like zazzaɓi ne ke shirin kamasa. tai salati tana faɗin,"baka da lafiya ne Turaki?". ba tare da ya buɗe idanuwansa ba yace,"lafiyata lau, kawai ina jin ba daɗin yanayina ne". Boɗejo tayi saurin tashi tsaye,"a'a baka jin daɗi ai yana nufin baka da lafiya, tun ɗazu dama na lura da yanayinka, to da yake kai ɗin me ƙauran baki ne ba zaka fito kace baka da lafiya ba sai dai ciwo yay ta cinka". dai-dai nan Ɗausiyya ta shigo ɗakin riƙe da ƙwaryar fura a hannunta. ta shigo da sallama ta nemi wuri ta ajiye, zata juya Boɗejo tace,"kinga garzaya da gudu ki kira min Zaytuna a, kice tazo da sauri Turaki babu lafiya. bance ki bari Uwassa taji ba balle tazo ta ɗaga min hankali da bala'ƴaƴƴan kukanta anan". in few minutes Zaytuna ta shigo ɗakin hankalinta a tashe, kai tsaye inda yake kwance ta wuce. kamar zata yi kuka ta taɓa jikinsa da yay zafi rau. "Hammah wake up mu tafi asibiti". ya buɗe idonsa da sukai jajir ya kalleta. ahankali yace,"ɗauko drugs ena". yana faɗa ta miƙe cikin sauri ta fita, bata jima ba ta dawo ɗakin jikinta sai rawa yake yi, tuni kuma hawayen dake cikin idonta ya sami nasarar gangarowa, bata ƙaunar wannan ciwon nasa na kidney ya tashi, idan ya tashi sai sun gama fidda rai da shi tukunna lafiya take samuwa. Boɗejo ta fito daga toilet a lokacin, tana kallon Zaytuna tace,"ciwon ne ko? ai tun jiya nake lure da shi tunda naga ƙwayar idonsa da kuma yacca ya ɗan kumbura ɗin nan, to kin sansa da ƙarfin halin jaraba, bai san cutar kansa yake ba". Zaytuna na hawaye tace,"inje in kira Maama?". da sauri Boɗejo ta girgiza kai,"a'a sam bakinki alaikum, da yardar ubangiji yana shan magani zai sami lafiya. ko kin manta itama bata da lafiya ne?, jiya likita da ya aunata yace jininta yayi mugun hawa sama, so kike tazo ta mace mana lokacinta bai yi ba, a'a bari tukunna dai a ɗaura aurensa ta gani tana raye". ta zauna kan kujera tana faɗar,"dan Allah kinga kwaɗa kira ɓangaren masu aikin nan wannan yarinyar Fulani tazo ta matsa min ƙafata, naga ta iya matsa ƙafa, kwanaki da tayi min kyace tausar inji irin wacca Hashim ke biyan uban kuɗaɗe ai min, ni tunda nazo ma ban ganta ba sai wannan baƙar nake ta gani tana suntiri, yanzu ma ita ta kawo min fura kuma ba zan iya sha ba gaskiya, da ganinta ba bafulatana bace irinmu. ni Allah yasa ma ba korar Fulani ɗin kuka yi ba, ni ƴa su aka koreta kuwa ba'a kyauta ba, yarinyar ga natsuwa ga hankali ga kyau da tarbiya, in kuwa an koreta to zama a dawo da ita gaskiya, dan ina son tausarta tayi masifar iyawa". Zaytuna tace,"tana nan ba'a koreta ba. bata jin daɗi ne". Boɗejo tace,"Allah sarki ashe shisa, ni wannan ƴa ma da ƙyar in ba sikila bace, Allah dai ya bata lafiya, anjima sai ki rakani wajensu na dubota, wannan yarinya ai tayi, idan nazo biki ga ladabin da take min ba wallahi, ba irin sauran ƴan aikin ba da sunzo sun waye sai su koma maka kallon ɗan banza, yanzu dai ban ruwa a kofi inyi masa tofi sai ki basa maganin ya sha, wannan ciwon nasa ba ƙaunarsa nake ba". Zaytuna ta ƙurawa Turaki ido sosai, wannan gajeran numfashin ke ɗaga hankalinta, fatanta ɗaya kar akai stage ɗin da kowa zaiji jiki ata dalilin ciwon. ta sauke numfashi sannan ta miƙe ta fita ta ɗauko faro ta dawo, a cup ta zuba ta miƙawa Boɗejo. zata ƙara fita Boɗejo tace,"tsaya ki basa ya sha, kin san ba sanin kan magungunan nayi ba". tace,"ya sami bacci ne, zanje na dawo". Boɗejo tace,"to alhamdulillah indai yay bacci ciwon ma ai da sauƙi". kusan awa ɗaya da rabi Boɗejo na tare da Turaki, yana ta bacci har zuwa lokacin, ita kuma tana gefensa cike da tausayinsa sosai. tana tayi masa adu'a iri iri, lokacin har ƙarfe shida da rabi na yamma tayi. lokacin Fillo ta tura ƙofar ɗakin ta shiga da sallama, Boɗejo ta amsa tana yi mata maraba. ta shigo ta tsuguna tana gaidata, idon Boɗejo akanta tace,"sannu, aiko ga shi nan duk kin ƙara zaftarewa, kina cin abinci kuwa ƴar nan?". kan Fillo a ƙasa tace,"ina ci". "to magani fa?". tace,"shima ina sha Boɗejo". "to Allah ya baki lafiya, kunje asibiti an yi miki tasa-tsai kuwa?". Fillo ta girgiza kanta alamar a'a. Boɗejo tace,"wannan ai sakaci ne, bara Allah ya kaimu gobe Khalil ya kaiki asibiti su gwadaki, amma wannan jiki naki ke kam ai yana buƙatar binciken likita". tace,"to Boɗejo na gode...dama Adda Zaytuna tace kina nemana". "ehh kinga da tausa zaki yi min irin wacca kika min ranar nan, to kuma sai take ce min baki da lafiya". Fillo tace,"ai naji sauƙi, zan iya yi miki". sosai Boɗejo ta tsaya tana kallonta da matuƙar tausayinta, tukunna tace,"a'a bari kya yi min gobe. yanzu dai ɗauko mopper ki goge ruwan nan kafin wannan marar lafiyar ya farka yaƙi sakkowa akan gadon". jin ance mara Lafiya Fillo ta ɗago kai ta kalli kan gadon, gabanta sai da yayi mugun faɗuwa ganin yacca fuskar Turaki ta kumbura kamar wanda yayi mummunan accident. Boɗejo ta ɗau mayafi tana faɗin,"bara naje in dawo, wurin Dikko zanje. in kin goge ki ɗan jira ina dawowa kar a barsa shi ɗaya, in kuma Zaytuna ta dawo shikenan. ni baccin nasa ma ya fara bani tsoro, Allah yasa dai lafiyar ce". tana Fita Fillo ta goge tiles ɗin, ta nemi wuri ta zauna tana ta kallonsa, numfashinsa da ƙyar yake fita, tausayinsa take ji har cikin ranta tana yi masa aduar samun lafiya. Turaki ya buɗe idonsa a hankali yana kallon ɗakin, Fillo ta taso da sauri tazo ta durƙusa a gaban gadon ta saitin da yake. "barka da tashi, Boɗejon ta fita amma tace yanzu zata dawo". ta faɗa tana kallon ƙasa, ta wutsiyar ido ta kalli yanda ya cije fuska ya miƙe zaune da ƙyar, Turaki ya dinga kallonta babu ƙiftawa, tun ranar da ta fasa masa turare rabon da ya ƙara ganinta, yau ɗin kuma kamar ta rame sosai. ta gefenta ya sakko daga kan gadon ya wuce toilet without saying anything to her, kanta na ƙasa har sanda ya fito a toilet yana goge ruwan fuskarsa da towel ɗin hannunsa. ya dawo ya zauna gefen gadon tare da kwantar da kansa a jikin gadon, Fillo dai har sannan tana tsugune a wurin sai jan yatsunta take yi. after some minutes ta miƙe tana ce masa,"zan kirawo Maama". ta faɗa tana juyawa zata fita. sai taji ya riƙo hannunta dake aikin karkarwa, duk sai ta dabarbarce ta juyo a tsorace, idonta na ƙasa ta kasa kallonsa, dan lokaci ɗaya jikinta ya hau rawa. ya janyota ta zauna gefen gadon, tare da kamo ɗaya hannun nata ya riƙe sosai. can ƙasan maƙoshi taji yace,"kina so kiyi kwanan ɗakin daga ni sai ke?". da sauri ta girgiza masa kai tana son ƙwace hannunta daga nasa. bayan ya sauke nunfashi yace,"to saita natsuwarki, bana son wannan tsoron". ba ta ko sake yunƙurin motsi ba, haka shima yana riƙe da hannayenta har sai da yaji jikinta ya daina rawar sannan ya tallabi haɓarta ya ɗago da fuskarta yana kallonta. "me ya ramar da ke acikin 5days?". ta girgiza masa kai kawai bata yi magana ba. ya sake cewa,"in tambaye ki zaki faɗa min gaskiya?". tayi shiru bata ce komai ba, sai da ya ɗan ɗaga muryarsa sama tukunna ta ɗaga masa kai da sauri. yace,"faɗa min dalilin da yasa kika fasa min turare?". tuni ruwa ya kawo idonta tace,"ban sani ba ne, amma zan biyaka in ƙarshen wata yayi". yace,"gaskiya nace ki faɗa min ba ƙarya ba". tai saurin ɗago ido ta kallesa kaɗan, sai taga ya rufe nasa idon ya kauda gefe ɗaya yana girgiza mata kai. "ina fa kallonki sanda kika fasa, intentionally kika jefar da shi a ƙasa har kina toshe hanci, warin me kika ji yana yi?". kawai sai ta fashe da kuka tana cewa,"kayi haƙuri dan Allah zan biyaka nace". yace,"na haƙura kuma na yafe ba sai kin biyani ba, amma idan kin faɗa min reason ɗin da yasa kike toshe hanci akansa". bata san lokacin da ta saka ƙwayar idonta a nasa ba tace,"nawa ne turaren?". yace,"50k". jin ya faɗi kuɗin albashinsu gaba ɗaya tace,"warinsa ne bana so shisa". Turaki ya sauke dogon numfashi tare da sakin hannunta. kansa jingine da jikin gado ya kulle idonsa. Fillo dai nata kallon fuskar tasa, taji yace da ita,"bani ruwa zan sha magani". ta miƙe kamar wadda bata da ƙwarin jiki, ta isa ga inda taga ruwan ta ɗauko na cup ɗin dana jarkar, ta dawo ta ajiye a kan bedside. a hankali tace,"ga ruwan". ya buɗe idonsa tare da miƙewa zaune sosai. ya buɗe ledan magungunan da Zaytuna ta ajiye duka ya ciri iyakar wanda zai sha, Fillo nata kallon kwalayen maganin jikinta yay sanyi saboda hoton kidney da ta gani ajiki. ta ɗan kallesa kaɗan tace,"Adda Zaytuna tace baka ci abinci ba". shima ya kalleta kaɗan sannan yace,"nayi loosing appetite". tana jan yatsanta ɗaya tace,"ka daure kayi ko spoon biyu ne tukunna kasha maganin". idonsa a tsakiyar kanta yace,"akwai abincin anan ko sai kin ɗauko?". tace,"ga shi nan a flask". yace,"kaɗan zaki zuba". ta miƙe ta ɗauko flask ɗin da ta shigo da shi wanda Zaytuna ta bata. tana buɗe flask ɗin tace,"Adda Zaytuna ce ta dafa". hakan da ta faɗa sai yasa shi ɗan murmusa kuncinsa, tunaninta zai yi zaton ita ta girka yaƙi ci, bata san ma ko da ita ɗin ta dafa ba zaici. yana kallo ta zuba kaɗan ta miƙo masa. ya karɓa yayi spoon 3 ya ajiye. tace,"ka ƙara please, babu komai acikinka maganin ba zai maka aiki ba". idonta na kallon gefe tayi maganar, Turaki ya tsaya yana ta kallonta, kamar zaice wani abu sai kuma ya fasa. ya ƙara spoon 5 akan wanda yaci tukunna ya ajiye, ta miƙo masa maganin ya sha sannan ta karɓi cup ɗin hannunsa ta ajiye. daga inda take a tsaye tace,"zanje in faɗawa Boɗejo ka tashi". ta faɗa tana shirin barin wajen, sai ta ƙara jin the same abinda yay ɗazu na kamo hannunta ya zaunar da ita gefensa. haka kawai Turaki ke ƙara jin jkinsa yayi sanyi sosai, still holding Fillo's hand har kusan 3minutes tukunna yay ajiyar zuciya ya saki hannun nata. ita dai ganin baya kallonta yasa ta sami damar kallonsa, da taga ya ɗan motsa kai sai tayi saurin ɗauke idonta. tana kallo within minutes ɗin da yasha magani kumburin jikinsa ya fara sacewa. Turaki ya duba agogon hannunsa, ya ɗauki wayarsa ya riƙe, wata ajiyar zuciyar ya sauke muryarsa a hankali yace,"you take care of yourself, zanyi tafiya but ba zan jima ba zan dawo, ba zan wuce 4days ba. if you need anything meet Zaytuna, be carefull with anything that will put you in trouble please". ita dai Fillo kanta na ƙasa idonta na kallon yatsunta, tana jin duk abinda yake cewa, tana jin maganar kamar da ita yake yi, sai dai tasan ba da itan yake ba, wataƙila kamar wancan ranar ne da yace thank you for saving my life tayi zaton da ita yake ashe waya yake yi. bata san dalili ba amma sai taji jikinta yayi matuƙar yin sanyi da jin zancen nasa, ta ɗago kanta karaf suka haɗa ido, sai taji ƙirjinta ya buga saboda yanayin yacca taga ƙwayar idonsa ta sauya. sai ta sami kanta da kasa ɗauke idonta daga ganinsa, tana kallo ya saki murmushin da ya tsaya a lips ɗinsa, kamar ita shima haka yake jan yatsun hannunsa. da taga ya ƙura mata ido sosai sai ta sauke kanta ƙasa ruwan hawaye na cika idonta without knowing the reason why. taji yace,"jibi zamu tafi, Hong kong zanje. ba zaki yi min adu'a ba?". duk da haka kanta na ƙasa tace,"da ni kake?". yace,"ni da waye a ɗakin?". tace,"to ai kaine mutum baya gane da shi kake magana". yace,"to da ke nake, adu'a nake so kiyi min naje lafiya na dawo lafiya sannan na dawo na tarar da ku lafiya". haka ɗaya sai taji wani iri da furucin nasa, yana maganar kamar wanda ke magana da matarsa, in same ku lafiya!, har da ita kenan?, to wace ita a cikin rayuwarsa?. sai yanzu taji wani bala'in tsoro ya kamata akan tafiyar tasa, voice ɗinta na fallasa kukan da take sonyi tace,"kai da wa zaku tafi?". yace,"ni da Bello". tai shiru kamar me dogon nazari kafin tace,"wannan abokinka ɗin me abin dariya?". ya ware idonsa tarr akanta yana mamakin maganartata yace,"ehh shi". tace,"daga kai sai shi zaku tafi?, zai iya kula da kai sosai?, ina nufin kamar yanda ba zai bari wani abu ya taɓaka ba?". tana tambayar taji tafin hannunsa akan haɓarta ya ɗago kanta, ya ɗago da fuskarta lokacin da hawayen dake cikin idonta ya sami nasarar gangarowa. ba tare da sani ba Turaki ya janyota jikinsa yana ƙarewa fuskarta kallo wacce hawaye ke ta sunturi akan kumatunta idanuwanta a kulle. ƙwacewa take sonyi amma ta kasa saboda wani irin kasala da taji yana neman rufeta dalilin jin kanta a kafaɗarsa tana shaƙar wani ƙamshi me bala'in daɗi. yay taking deep breath yana jin kamar yayi hugging ɗinta, he feels like he doesn't want to move away from her, yana jin kamar ya fasa tafiyar just becouse of her, sai dai he has to go, ko dan gudun kar a haɗa Bello da fake kaya. ƙirjin Fillo na bugawa tace,"zanje in kira Maama". A hankali yace,"to kukan me kike yi?, ko na fasa tafiyar?, ko na kira Bellon ki faɗa masa ya kula da ni?, kuma nima ai zan iya kula da kaina". gaba ɗaya sai take jin yacca yake mata magana kamar cikin mafarki ko kuma dai ba da ita bane wata ce daban irinta yakewa magana. bata san ta yanda bakinta ya buɗe ba ma har take iya magana haka duk da uban tsoronsa dake tare da ita, dan wani irin faɗuwan gaba da take ji. ta ɗan kallesa kaɗan ganin yana kallonta tayi saurin ɗauke idonta, taja yatsanta ɗaya tace,"ba zaka iya kula da kanka ba ai, amma shi naga yana sonka, kuma yana da mutumci, Maama zata basa amanarka...Allah ubangiji ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya, Allah yayi maka katanga kan katanga daga dukkan sharrin me sharri, Allah ya ɗoraka akan maƙiyanka, Allah ya tsareka da tsarewarsa ya kiyayeka da kiyayewarsa, ka kula sosai da kanka Maama zata ji daɗin hakan, karka yi wasa da shan magani". tunda ta fara maganar yake kallonta babu ko ƙifce, da wani kalar tunani da yake akanta. kamar ya buɗe komai a yanzu, but zuciyarsa na faɗa masa not now, this is not the right time da ya kamata ya buɗe komai. yana ji ta zame jikinta a hankali tana miƙewa tsaye, so take yi ta bar ɗakin amma kamar an riƙe mata ƙafa, kuma kamar tana jiran umarninsa ne. tayi dai tsaye ta kasa motsawa balle ta tafi. tsaye shima ya miƙe yana kulle idanuwansa, jikinsa duk babu ƙwari haka yake jinsa, bai taɓa jin zai yi tafiya yana fargabar tafiyar ba ko kuma yana tsoro, amma this time around da zai tafi yayi just 4days ji yake kamar wani mugun abu zai faru kafin dawowarsa, ko kuma wani mugun abu zai faru da shi. bayan ya zuba hannayensa cikin aljihu taji yace,"bana son yawan kuka. when am back you will help me find Mum". kallon da take yi masa bana mamaki bane tunda a yanzu ta riga tasan komai, kallo kawai take yi masa me cike da tausayawa, bata ankara ba sai ganinsa tayi tsaye a gabanta dab da ita, tayi wani ƴar guntuwa a gabansa dan da kaɗan ta wuce cikinsa, magana take so tayi masa amma bata san ta ina zata fara ba, hannunta nata karkarwa taji ya sunkuyo da kansa ya ɗora goshinsa akanta yana kama hannayen nata ya riƙe. muryarsa can ƙasa taji yace,"when will these hands stop shaking?". sai taji kamar numfashinta zai yi seezing, jin an turo ƙofar ɗakin ta firgita taja da baya, ganin Zaytuna duk sai ta rikice, so take ta fice daga ɗakin da gudu before Zaytuna ta ɗago daga sunkuyawar da tayi tana ajiye abu, amma ya riƙe hannunta ta yanda duk abinta ba zata iya ƙwacewa ba, Zaytuna ta ajiye aiken Boɗejo da ta shigo da shi ta fita. tana fita Fillo ta fashe da kuka tana ture hannunsa daga riƙon da yay mata. ƙarar shigowar text a wayarsa yasa ya saketa ya nufi wayar, ita kuma ta buɗe ƙofan ta falle da gudu. Turaki ya buɗe messge ɗin Zaytuna da ya shigo yana karantawa. _Boɗejo and Maama are coming._ yana gama karantawa ya juyo da kallonsa inda ya bar Fillo, sai gani yay babu ko ɓurɓushinta, yasa hannu ya shafo wuyansa yana smiling. _sorry for the late update._ *please vote, share and comment.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _not edited._ *28* washegari da safe Fillo ta gama shiryawa kenan sai ga Yami ta faɗo ɗakin kamar an jefota. fuskarta a haɗe take kallon Fillo, ita kuma tana ganin hakan tasha jinin jikinta. Yami ta miƙa mata wayar hannunta tana faɗin,"ungo nan, idan ta kama ki tafi da ita can, abu ɗaya kawai na sani shine ki tabbatar kin ɗaga kiran Amir kunyi magana da shi, ki kuma basa damar zuwa idan ya buƙaci hakan". idon Fillo suka ƙanƙance tana kallon Yami da ta ɓata rai, ƙirjinta taji yana bugawa da sauri sauri domin bata tunanin zata iya bin umarnin Yami. Yami ta doka mata tsawa,"kin karɓa ko saina hamɓare ki". tuni jikinta ya hau kyarma tayi sauri ta karɓi wayar tana duƙawa a wurin ta fashe da kuka. Kaka tace,"to dama ni dai da naga ba kiyi magana ba yasa nayi shiru, zatona ko baki san komai ba". Yami tace,"ai ina sane, na zuba mata ido ne naga iyakar gudun ruwanta. sai naga rashin hankalin nata da gaske ne, to banda ma dai ɗan Adam butulu ne dan ubanki ina ke ina juyawa Amir baya, duk abinda Amir zai yi miki a rayuwa ai ke me iya shanyewa ce ba wai kiyi zuciya da shi ba, wane irin alkhairi ne yaron nan bai yi miki ba, wane kalar halacci ne bai yi miki ba, ke inda baya sonki da gaskiya har yace yaji ya gani ya aminta zai aureki sanda ake hure masa kunne da cewar ke ƴar gaba da fatiha ce. amma saboda toshewar basira irin taki har ki iya ɗaukar fushi da shi na tsawon wata da watanni, gaskiya kin bani kunya da mamaki". cike da takaici Yami ta ƙarasa maganar. Fillo dai kuka kawai take yi tana jin zuciyarta kamar ta faso ƙirjinta, ita ake bawa laifi?. gaskiya ko Yami da Kaka zasu haɗu su kasheta bata jin zata iya yin abinda suke so akan Amir, in har dan ta ɗaga kiran Amir ne ko ta basa damar zuwa gwara ta mutu, dan ko kaɗan bata son jinsa balle ganinsa. Kaka tace da ita,"ni dai ban taɓa tunanin a ɗan guntun ililimin da kika samu daga wurin Amir ba, ilimin da wanda ya haifeki ya kasa baki shi, zaki iya butulcewa Amir ba, ko da kuwa me zai yi miki, irin faɗi tashin da yaron nan ya dinƙa yi a game da rayuwarki ta inganta da kuma lafiyarki yafi ƙarfin wulaƙanwa daga gareki. amma babu komai iya abinda kika yi ma kin zubar min da mutuncina a idon iyayensa, na kuma gode, domin babu wanda zai yarda cewar bani na saka ki ba". Fillo na kuka sosai ta ɗago ta kalli Kaka tace,"shikenan ko mene ya faru sai a ɗora min laifin?, me yasa ba za'a tambaye ni abinda yayi min ba?". Yami ta galla mata harara tace,"rufewa mutane baki, ba'a haƙuri ma'aikin Allah yay haƙuri?, ko kuma ba'a yafiya muke yiwa Allah laifi mu nemi yafiyarsa kuma ya yafe mana. to wallah tun muna shiri da juna ki sasanta tsakaninku a yau. nace masa yazo, dan haka ki

Chapter 26 of 73