Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 FIVE LIONS🦁🦁🦁🦁🦁 MALLAKIN FATEEMA ZAHRA MUSA. A-K-A PRINCESS TEEMA STAR LADY. 31-10-2025.🔥 THE STORY OF DEATH OR LIFE🔥🧠 E_____________1 DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI. *Wannan littafi na ZAKUNA BIYAR tin daga page 1 na step 1 har zuwa karshen step 1 sadaukarwa ne ga mutanena na ƙasar Niger, ƴan Niger ƴan amana, ƴan Niger sun mun abin da ba zan taɓa mantawa da shi ba, Niger gidan karaminci da mutunci, gidan amana da kyautatawa, kai ƴan Niger baki na ya yi kaɗan wajen iya faɗan alkhairanku, kun mun na gani! Ban san da me zan biyaku ba shiyasa na yi maku wannan sadaukarwan, ALLAH ya kara maku lafiya da zaman lafiya, kwanciyar hankali da farinciki, jin daɗi da walwala mara yankewa har illarh Masha ALLAH, hakika ina kaunar mutanen ƙasar Niger kauna sosai mara misiltuwa, much love.*🌹♥️ _________________🔥 U.S New York City. New York tana daga cikin birni mafi girma a cikin Amurka, wanda ke ɗauke da manyan cibiyoyi na kasuwanci, kuɗi, da al'adun kasar Amurka. Tana daga cikin jahohin da suka fi kowanne daraja a fannin kuɗi da al'adu. Unguwar upper east side, manhattan kenan. Wuri ne da ya shahara da manya-manyan gidaje na alatu, gine-ginen tarihi, da tarin art galleries. Yana kusa da central park, fifth avenue, da manyan kasuwanni kamar bloomingdale's. Unguwa ce ta manya-manyan kai, irinsu manyan lauyoyi, ƴan siyasa, da masu nasara a wall street!. 02:00AM. Agogon birnin YEW YORK ta buga. Dare ya yi sosai, dik wata halitta mai rai da natsuwa tana barci dan kara samun natsuwa. Kwance take a saman katafaren bed ɗinta, ta yi lamo cikin lallausan bargonta, da alama tana jin daɗin wannan barcin da take yi. Tamkar a mafarki haka ta fara jin alamar ana dukan gate ɗin gidanta, lamarin da yasa ta ɗan motsa daga yadda ta kwanta kenan. Lokaci guda ta zabura ta miƙe zaune sakamakon dukan gate ɗin da aka yi da karfi tamkar za'a rugujesa. Zazzare ido irin na mai barci a cikin duhu ta fara yi, take ta fara ƙoƙarin saita natsuwarta dan ta fahimci da gaske dukan gate ɗin ake yi ne ko mafarki?. Jin tabbas da gaske ne yasa ta kai hannunta saman phone set dake jikin bedside drawer tana laluɓar wayarta, jikinta take ya hau kerma tana cigaba da zazzare ido. Tsabar ta shiga tashin hankali rawar da hannunta yake yi yasa ta gagara iya ɗauko wayar. Wani irin duka da aka sake kaiwa gate ɗin ne yasa bata san lokacin da ta diro kasan bed ɗin ba, sai gata ta ɗauko wayar. A razane ta nufi waje tana ƙoƙarin kunna light na wayar, amma ina abin ya ci tura, dan hannunta ya gagara tsayawa bare ta iya kunna wutar. Fitowa ta yi cikin duhu tana laluɓar hanya, hankalinta ne yake kara tashi jin irin yadda ake dukan gate ɗinta tamkar za'a rugujesa, har wani irin zufa ne yake keto mata, saboda tasan dukan gate karfe 2 na dare kam sai in wani ikon ALLAH amma ba alkhairi bane. Wani siririn corridor ta nufa tana ƙoƙarin kamo dik adduar da azo bakinta, sai dai kuma ta gagara iya kama kwakkwara guda ɗaya. Tana cikin laluɓe ta damko handle na wata kofa, a hanzarce ta turo kofar ta shiga ciki. Da kyar ta iya jan kafafunta ta isa gaban switch saboda wani irin rauni da jikinta ya yi. Wutar ɗakin ta kunna, lokaci guda ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, a hankali ta tako izuwa gaban bed dake a cikin ɗakin. Irin babys bedroom ɗin nan ne da ya ji komai na more rayuwa, and komai na cikin ɗakin sky blue ne, harta curtains dasu furniture's. Ɗakin ya yi balain haɗuwa matuƙa. Hannunta na rawa ta sa ta yaye sky blue lallausan bargo dake kan bed ɗin. A karo na biyu ta sake sauke ajiyar zuciya. Wata yar yarinya karama ce kwance a saman bed ɗin, ta baje abinta tana zuba barci, sanye take da wando guntun zuwa gwiwa da yar riga mai siririn hannu launin pink color. Gashin kanta very silky ne zube a kan face ɗinta wanda yasa ba'a iya ganinta, dan tsawonsa har saman cikinta. Wani irin duka da aka yi wa gate ɗin ne yasa wannan kyakkyawar mata ta zabura, jikinta ne ya tsananta kerma, a gaggauce ta mayarwa da yarinyar bargon ta lulluɓa mata kafin ta yi saurin juyawa ta nufi switch. Kashe wutar ɗakin ta yi sannan ta fito. Tsabar ruɗewa sai ta rasa ina zata nufa, ta dafe kirjinta dake barazanar tarwatse mata da hannu ɗaya. Da kyar ta iya gano staircase ta sauko down. Gudu-gudu sauri-sauri ta nufo tsakiyar main parlo. A nan ta tsaya tana ƙoƙarin kunna light na wayarta. Sai dai abin ya ci tura, wlh screen na wayar gabaɗaya yaki dannuwa. Jin mai dukan wannan gate ɗin bashi da hakuri ne yasa ta fahimci koma wanene a zaƙe yake da son shigowa, dan haka sai ta nufi switch na parlon. Da kyar ta iya laluɓarsa ta kunna wutar. Katafaren parlo ne wanda ya ji komai na more rayuwa irin na masu hannu da shuni, ga shi tsab-tsab sai kamshi dake tashi. A gaggauce ta nufi kofar parlo. Saboda yadda jikinta yake rawa yasa da kyar ta iya ɓalle dik wasu keys na jikin door ɗin ta nufo waje. A harabar gidan ta ɗan tsaya tana kokarin kamo kwakkwarar addu'a ta yi kafin ta karisa bakin gate ɗin. Wani duka da aka yi wa gate ɗin ne sai da ya yi wani irin jijjiga, ai bata san lokacin da ta karisa wajen ba sai ganinta ta yi a dab gate ɗin. Muryarta na rawa kirjinta na bugawa sosai ta ce. "Waye....... Ne?". Daga ta waje wata muryar da bazata iya gane wanene bane ya amsa mata da. "Open the gate now". Yadda aka yi maganar akwai alamar galabaita da wahala a tattare da mai wannan murya!. "Ban gane in buɗe gate a wannan lokaci ba, karfe 2 dare fa? Wanene first, ina son sani kafin in buɗ.........". Bata iya karisa maganar ba ta dakata sakamakon wata mahaukaciyar dukan da aka yi wa gate ɗin, sai da ta yi baya a miliyan, dan a tinaninta ma ruguzowa kanta gate ɗin zai yi. Da wannan galabaitattar murya aka yi ƙoƙarin daka tsawa. "Open the gate now I said!". Da gudu ta matso jikin gate ɗin ta hau ciccire locks na jiki tana faɗin innalillahi wa inna ilaihir rajiun, hasbunallahu waniimal wakil. Da kyar ta iya buɗewa. Ai tana zare locks ɗin aka banko gate ɗin ciki aka shigo, ana shigowa aka ɗaura mata silent pistol gun a daidai saitin kanta. Cikin wannan galabaitaccan murya aka sake cewa. "Close the gate". Ko kaɗan bata tsorata dan ya ɗaura mata bindiga a kai ba, hasalima tausayi ya bata ganin yadda yake wani irin numfashi mai nauyin gaske, alamar yana cikin azaba, and ganin haka ganin kuma shi kaɗai ne yasa ba musu ta kulle gate ɗin kamar yadda ya buƙata. Tana rufewa ya nuna mata cikin gida da hannu dake rike da gun ɗin alamar ta wuce su tafi ciki. Bata yi gardama ba ta wuce gaba ya rufa mata baya suka shige cikin parlo. A nan ne fa ta tsaya tsakiyar parlon tare da juyowa wai ko zata samu damar ganin face ɗinsa, dan sun shigo haske. Sai dai ko kusa ko alama bata ga alamar hakan ba, dan yana sanye da puffer jacket mai katan hula da ta rufe kansa har gaban goshinsa, sannan yana sanye da p-cap daga ta cikin hular jacket ɗin, ga shi kansa a sunkuye kasa, da alamar nose mask ma a face ɗinsa. Nuna mata upstairs ɗin da gun ya sake yi alamar su je, sai dai kuma bata cigaba da tafiya ba, ta tsaya tana yi mashi kallon tsab ne, lokaci guda idanunta suka sauka a kan jinin dake zuba daga yatsun hannunsa, ziiiiiirrrrrr haka jinin yake zuba kamar an buɗe tap a low gudu. Da sauri ta ɗan zaro dara-daran idanunta a kan face ɗinsa da bata iya gani. "Bawan ALLAH meyasameka? Waye kai? And me kake nema da ni?". Cikin raunin murya ta yi maganar. Ko kaɗan bai yi magana ba ya cigaba da nuna mata sama da bindigar cikin yanayi na galabaita da kasawa, da alama dik sauran karfinsa ta karewa dauriya ce kawai yake yi. Ganin hakan yasa kawai ta wuce gaba ya rufa mata baya suka yi sama. Ba shi ya ce mata ba, kai tsaye ta nufi wani ɗaki da aka rubuta OPERATING ROOM (O-R) a jikin door na kofar aka yi wannan rubutu. Handle na door ɗin ta murza ta tura, kofar ta buɗe, ciki ta shiga ya rufa mata baya. Ɗaki ne tamkar hospital, ga gadan majinyata mai ɗauke da bedsheet blue, curtains na ɗakin dik blue, ɗakin yana da girma sosai, ko'ina tsab yake sosai, sannan akwai katan AC dan hana ma'aikata gumi, yadda kuka san katafaren hospital dai. Daga jikin bangon dake fuskantar kofar shigowa hoton matar ce sanye da surgical gown, da alama babbar likita ce, dan tin daga kan yanayin hotunanta dake a manne a bangon zaka gane babban ce, jikin wannan bango dai dikka frames na hotunanta kala-kala ne, wani hoton tana aikin tiyata aka yi mata, wani ana bata kyautar karramawa, wani kuma tana rike da jariri sabon haihuwar da ko cibi ba'a yanke mashi ba! Gasu nan dai hotuna kala-kala. Da alama Surgeon ce. Ai suna shiga ya cire gun ɗin daga kanta ya karisa wajen bed ɗin da kyar, yana zuwa ya faɗa saman bed ɗin ya kwanta hannunsa rike da bindigar. Ganin hakan yasa ta yi gaggawar karisowa in da yake, dik tausayinsa ya yi mugun jiƙata, da sauri ta zo ta rike hannunsa da yatsun ke zubar da jini, a nan ta fahimci jinin daga sama yake zubowa izuwa kan yatsunsa, ga kuma alamar harbi da bindiga a damatsansa. Hakan yasa ta yi gaggawar sakin hannun nasa ta nufi wasu drawers dake gefe guda. Cikin ƙanƙanin lokacin wannan mata ta shirya cikin kayan kariya kamarsu surgical gown, gloves, face mask, face shield, surgical cap. Sannan ta kwaso kayan aikin irinsu scalpel, forceps, tissue & hemostat, retractor, suction machine, bullet extractor, irrigation syringe, suture needle da thread, surgical drapes, sterile daga cikin drawer ta kawosu saman table dake kusa da bed ɗin, jikinta har wani irin rawa yake yi mata, burinta ta yi gaggawar kammala shiryawa ta taimaki rayuwarsa, dan ta gano harbinsa da bindiga aka yi, jikin rigarsa wajen damatsan hannunsa a fashe. Take ta hau preparation dan yin tiyata. Bayan ta gama tsab sai ta haɗa alluran kashe zafi, ta so yi mashi alluran barci ne, dan shi ne ma a ƙaida, amma sai ta ta ce bari ta yi mashi na kashe zafi, dan daga yadda zuciyarsa take bugawa out of control ta fahimci akwai abin da yake son cinmawa, yi mashi alluran barci a yanzu babban kuskure ne sosai, dan bata san waye shi ba? Bata san daga ina yake ba? Mutumin kirki ne ko na banza dik bata sani ba, bata san me zai iya zuwa ya dawo ba, so gara mata idanunsa biyu iya wuya. A gaggauce ta ajiye alluran a gefe bayan ta yi mashi, sannan ta ɗauko almakashi ta fara yanka hannun jacket ɗin tasa daga wajen yatsunsa har zuwa damatsan hannunsa, ta cire hannun rigar gabaɗaya, a gefe ta ajiya game da mayar da almakashin cikin try na kayan aikinta. Sai ta ɗauko antiseptic dan ta tsaftace in da bullet ɗin ke ciki. Ta yi matuƙar tausaya mashi baiwar ALLAH, ta ga ya rasa jini sosai, kuma still zubar da jini yake yi, tamkar bullet ɗin ta gota hanya, ta nufi kusa da kashi ko jijiya haka. Da sauri ta ɗauko X-ray machine, na'urar ce da ake amfani da ita kafin cire bullet dan gano wurin da bullet ɗin ya tsaya sosai. Idanunta ta kura a kan na'urar tana kallon yadda bullet ɗin ta fasa namar damatsan hannunsa ta shiga ciki. Sosai tausayinsa ya kara kamata, ganin ta gano in da bullet ɗin yake ne yasa ta ajiye machine ɗin a gefe ta ɗauko scalpel, wukar duba ta asibiti, ana amfani da ita dan buɗe fata ko nama a inda bullet ɗin ya shiga. Ganin tsokar nama ta yi yawa a damatsan nasa ne yasa ta ɗauko x-c dan reɗe namar ta rage. A natse take aikin cikin tsari da tausasawa, amma cikin zafin jini babu kasala a tattare da ita. Dik abin da take yi mashi yana ganinta, idanunsa biyu amma bai motsa ba, da yake ma ta yi mashi alluran kashe zafi!. Bayan ta reɗe namar wajen ta ajiye a gefe ne sai taga jini ya tsananta zuba sosai, hakan yasa ta ɗauko suction machine, na'urar da ake amfani da ita dan tsotse jinin, bayan ta rage mashi jinin wajen sai ta ɗauko antiseptic solution, magani ne irin chlorhexidine da ake amfani da shi dan tsabtace wurin harbin, a natse ta tsabtace wajen tsab kafin ta ɗauko retractors, wannan da ake amfani da shi ne dan riƙe nama da buɗe wajen aikin dan ganin bullet ɗin sosai. Yanzu ta samu ganin bullet ɗin yadda yakamata, dan haka sai ta rike retractor ɗin da hannu ɗaya, ta sa ɗayan hannunta kuma ta ɗauko forceps, wannan abin ne mai kama da almakashi, ana amfani da shi dan kama bullet ɗin cikin sauƙi. A hankali ta riko bullet ɗin ta cirosa, kai tsaye ta jefasa cikin ruwa mai sanyi sosai dake cikin bowl da ta ɗauko before. Wani irin jini jajir ne ya fallatsa ya biyo bayan wannan bullet da ta cire, hakan yasa ta yi saurin ajiye su retractor ɗin ta ɗauko sterile gauze pads, da shi ta yi amfani dan tsotse jini dake ɓulɓula a wajen!. Sannan ta ɗauko irrigation syringe, sirinji mai girma da ake amfani da shi dan wanke wurin da ruwa mai tsabta ko maganin kashe kwayoyin cuta, so ita ma da maganin ta wanke mashi wajen. Bayan ta kammala ta ɗauko sutures, Igiyoyin likitoci da ake amfani da su dan ɗinki wurin da aka yi aikin. A natse cikin tausayawa sosai ta ɗinke wajen tsab sakamakon yanka naman wajen da ta yi da kara buɗa wajen harbin, sannan ta sanya sterile gauze pads da bandage ta rufe tsab, dan kare wurin kada wata cuta ta samu hanyar shiga. Bayan ta kammala komai ta tattare tsab, ta gyare wajen ta kuma goggoge jininsa da ya zuba har saman mattress na bed ɗin. Ko'ina ya zama tsab-tsab tamkar ba'ayi aikin komai ba, sai dai bata lura da uban jinin da ya malala ta kasan bed ɗin ba, dan a lokacin da ya kwanta ya saki hannun nasa jini ya zuba sosai har ya malala, hankalinta ya tafi wajen ƙoƙarin ceto ransa yasa bata kula da jinin ba. Kurawa wajen da ta yi mashi aikin idanu ta yi na ƴan mintoci kafin ta dawo da kallonta a kan fuskarsa. A ranta ta ce. "Yana buƙatar magunguna irinsu antibiotics dan hana kamuwa da cuta, e.g. ceftriaxone, da kuma painkillers dan rage zafi, da e.g. paracetamol, tramadol, sai anti-inflammatory drugs, dan hana kumburi wajen da kumburin jiki, da tetanus injection, lastly sai wound dressing set, dan canza bandage akai-akai, ga shi bani da su a gidan nan". A saman wani sofa set mai zaman mutum biyu dake cikin ɗakin ta zauna tana mayar da numfashi, ta yi aiki matuƙa, dan har 4 na asuba ta yi. -------------------------🔥 4:30AM. Daidai agogon jikin bangon ɗakin ya buga. Barci ɓarawo ya ɗan fara ɗaukarta, tamkar a mafarki a hankali ta fara jiyo sautin alamar tafiyan mutane a cikin gidan wanda hakan ya yi mugun ɗaga mata hankali yasa ta farka a firgice, ji ta yi tamkar buɗe parlo door ake ƙoƙarin yi. A zabure ta kai kallonta kan patience ɗinta dake kwance saman gado, taga dai ko alamar motsi bai yi ba. Miƙewa tsaye ta yi tana dafe saitin zuciyarta. Da sauri ta nufi kofar fita har kamar zata kifa, a ranta take faɗin yau kuma wace iriyar kaddara ce wannan? A fili kuma ta ce. "Hasbiyallahu wani'imal wakil". Kamar ɗazun a guje ta nufi ɗakin ƴarta, still dai yarinyar tana ta zuba barcinta cikin kwanciyar hankali. Addu'a ta yi ta tofa mata kafin ta nufi waje, ta jawo door ta rufe mata sannan ta nufi down da gudun gaske. Ɗai-ɗai bibbiyu take tsallake steps ɗin nan. Tana isa tsakiyar parlo sai gani ta yi an banko door ɗin an shigo. Gabanta ne ya buga da karfi ganin kartin maza majiya karfi kuma madaka katti har guda biyar sun afko cikin parlon. Gabaɗayansu sanye suke da bakaken kaya tamkar waɗan da zasu tafi taron ƴan wuta, ga wata uwar rigan sanyi mai zubin puffer jacket da ta kai masu har kasa sosai, sun sanya hular rigar a kansu wanda ya sanya fuskokinsu bata fita ba, ga nose mask daga ta ciki da suka gargame fuska da shi. Irin waterproof boot ɗin nan ne a kafansu, ga wasu maka-makan hand gloves a hannayensu, a takaice dai baka iya ganin komai nasu, iya jajayen idanunsu ne kawai a waje shi ma idan ba ka leƙa cikin hular rigar sanyin nan ba baka iya ganinsu. Salati ta fara yi jikinta na tsananta kerma. Cikin harshen turanci ta fara tambayarsu. "Who........are...... You". Da kyar ta iya faɗin hakan. Dik cikinsu babu wanda ya yi magana, suka nufo cikin parlon, suka jero har in da take tsaye. Kasancewar su biyarne yazamana ɗaya yana tsakiyarsu kenan, hakan yasa na tsakiyar ya ɗaga hannu sama ya kyasta yatsunsa, take suka yi wa matar zobe, ko bata ga fuskokinsu ba tasan waɗan nan babu alamar imani a tattare da su. "Ina mutumin da ya shigo gidan nan?". Wannan da ya kyasta hannu shi ya yi maganar, ba zaka taɓa iya tantance voice ɗinsa wace iriya ce bace saboda nose mask ɗin ta hana fitar muryar da kyau. "Ba..... Babu wanda ya shigo gidan nan!". Da kyar ta basu amsa saboda tsoro........ Shiru gabaɗaya suka yi, tamkar ba zasu tanka mata ba, har ta ɗan saki jiki unexpected ta ji wani irin gigitaccen marin da yasa ta yi baya-baya kamar zata faɗi. Wanda ya yi maganar ne ya dallah mata wannan marin, lokaci guda ta ji kunnuwanta sun ɗauke ji na ɗan lokaci kafin ta sake dawowa daidai. A karo na biyu ya sake cewa. "Ina mutumin da ya shigo cikin gidan nan? Bana magana sau biyu, a kanki na fara, kada ki bari hannuna ya sake motsawa! Dan innai duka na biyu sabauta ake yi". Zazzare idanu ta yi a kansa ko zata iya rike komai kankantar makama da zata iya ganesu ko a gaba ne, sai dai babu wani abin da take iya hangowa. Tana cikin tinanin neman makama a tattare da su ta ji wani irin azaba ya ziyarci gaban goshinta, kan kace me jini ya fara wanke mata fuska, duka ya yi mata da gindin bindigar da ya fitar daga aljihunsa, irin police pistol gun ɗin nan ne. Wani irin jiri ne ta ji ya kwasheta, tana ƙoƙarin faɗuwa ɗaya daga cikinsu ya damki gashin kanta ta baya, hakan yasa ta tsaya a kan kafafunta. Da hannun wannan na tsakiyar ya yi masu nuni da upstairs a kan su haura sama. Tsabar rashin imanin da gashin kanta suka jata da karfin gaske suka yi sama da ita, suna wani irin taku dake nuna koma su waye su lallai gurayene ba ragwaye ba, sannan basu da tausayi. Sai da suka fara hawa upstairs ɗin suka lura da blood da ya yi ta ɗiga a ƙasa, na mutumin da ta yi treating kenan. Blood ɗin suka fara bibiya suna haurawa har zuwa bakin wanna room ɗin. A nan eagle ɗin nasu ya dakata tare da ɗan matsawa gefe, ɗaya daga cikin yaransa ne ya yi gaggawar shigowa gabansa ya sanya kafarsa ɗaya ya take door ɗin da karfi sai gata ta wagale gabaɗaya. Biyu daga cikin yaran dake bayansa ne suka yi gaggawar wucewa gaba suka shige ciki. Sai da suka shiga eagle ya tako cikin ƙatsaita. A tsakiyar ɗakin suka dakata suna muzurai, zazzare idanu suka hau yi a cikin room ɗin ko zasu hango wani abin. Sai dai kuma ɗakin wayam babu kowa. INA MUTUMIN YAKE?. Eagle ne ya fara wuwwurga idanunsa ta ko'ina yana bin ɗakin da kallo, can ya tsaida kallonsa a kan bullet dake cikin silver bowl da ta ajiye saman table, sai kuma alamar jini-jini dake jikin bedsheet da bata gama gogewa da kyau ba, saboda mutumin na kwance. Kasa da idanu eagle ya yi sai ya ga alot of blood a kasa ya malala har karkashin gadan. Cikin natsuwa eagle ya taka zuwa gaban bed ɗin, hannu yasa cikin bowl ɗin ya tsamo wannan bullet ɗin, kura mashi idanu ya yi na ƴan sakanni kafin ya juyo da kallonsa a kan sauran yaran nasa. "This bullet is mine, daga gun ɗina ya fita, dan

Chapter 1 of 95