mintuna ƙasa da biyar su kuma sauƙo.
Ai zazzaro idanu Noor ya yi, cike da damuwa ya matsa kusa da VASH tare da cewa. "Bro I'm tied wlh, ba zan iya ba, hawa sama fa, no, my legs done tied over". Bawan ALLAH fushinsa na ɗan lokaci ne, har ya manta ya ce kada su sake yi mashi magana ma.
Ganin ya nuna manta da kalamansa na ɗazun ne yasa suma suka manta, Vash ya ce mashi. "Noor this is just the beginning for our training, saboda yau ranarmu ta farko na karɓar horone ma yasa kake ga ake mana ƙananan abubuwa, i promised you in the next one week dik wannan tafiya for two mil zai canza zuwa 10 mil to up, dik horo zai ninka kansa, kawai abin da zance shi ne, kada ka kunyata daddynka, kaga ni na shiga soja ne for my dad, kafin ya mutu kullum maganansa ɗanya in zama soja, shiyasa granny ɗina ya horar da zuciyata da kaunar aikin, i will do all my best dan ganin na cika burin daddyna, i wish yana raye a lokacin da zai ganni da kaki, amma ba komai".
Tin da ya fara magana idanun Noor suka cika da kwallah. "Sorry for the rashin dad bro". Jinjina kai kawai ya yi kafin ya rike hannun Noor da kyau..... "Be strong, zaka iya my brother".
Noor da yasan ba zai iya jurewa bane ya ce. "I will try, but not sure zan iya". Jansa ya yi suka fara tattaka steps ɗin da sauri yana faɗin. "By the grace of God zamu fito da good result mai kyau and a rukuni guda zamu fito, zamu yi aiki a tare".
"I wish that". Noor ya faɗa tare da zaro idanunsa waje, dan yaga NIRASH har ya hau yana saukowa su yanzu suka yi rabi, mamaki ne ya kamasu daga shi har VASH, yanzu ya kara tabbatarwa da gaske NIRASH yake wannan aiki ba wasa ba.
Haka suka sha faman hayewa sama da kyar suka sauko, suna saukowa Noor ya durkushe kasa a waje yana wani irin haki da ɗan karfi-karfi.
Hutun five mins Captain dake tsaye yana kallonsu ya basu kafin ya sake umartansu da su yi gudu sosai zuwa wajen waɗan nan duwatsu da tsaunuka, ba musu suka dallah da gudu suka nufi wajen, amma fa a wannan karon ma Noor ne na karshen zuwa, dan shi wlh bai huta bama Captain ya sake tashinsu, ga shi idan baka tashi ba wasu zaratan sojojin huɗu dake binku a baya da manyan bulalu su baka a jikinka.
Da suka isa sai da suka ɗan jira Captain, hakan ya kara basu damar hutawa kaɗan.
Yana zuwa ya umarcesu da su fara tsallaka ƙananan tsaunika da duwatsun nan. Nan fa Noor ya ce shi ba zai iya bafa, dan kafafunsa zafi suke yi mashi, abinku da renon madara and ice cream.
Hannunsa VASH ya ja yana faɗin. "Wlh a wannan gida babu tausayi babu tausayawa, shiyasa idan soja yakama mutum babu imani yake jibgar bawa, a wannan horo dakake ganin mun fara ake cire masu dik wata tausayi da imani, saboda bakin azaban da suke sha, in har baka tashi ba, wlh Captain na iya sanya wannan shegiyar takalmar tasa ya tattakaka, ko kaɗan ba zasu tausaya maka ba, so is better for you to stand up".
Tabbas Noor yasan gaskiya VASH yake faɗa mashi, saboda yasan dokokin gidan soja, yakaranta komai ya kuma cika komai, dan haka babu uwa, babu uba, babu ƴan uwa, wlh ya yi gardama mugun azaba da bakin duka zai ci, kuma a banza ya daku in an dakesa, babu mai tausaya mashi daga cikin manyan sojojin nan, su gama dukansa su haɗa shi da horo mai azaba, a haka zai goge, ya fi mashi sauƙi ya miƙe ya bi umarni kawai.
Idanunsa sun cicciko da kwallah haka ya miƙe ya nufi waɗan nan duwatsu ƙanana dake gefen manya-manyan, da kyar Noor yake iya tsallakasu. A wannan waje good 20 mins Captain ya basu suka yi wannan aiki kafin ya wuce da su wajen wasu igiyoyi dake ɗaɗɗaure, kasansu ruwan taɓone mai ɗan zurfi.
Cikin kakkausar murya ya ce. "Zaku rarrafa cikin ruwan nan ne a kasa da minti biyu ku fita ta gefen can, kada wanda ya bari kansa ya taɓa igoyiyin nan, idan kanka ya taɓasu tabbas zaka sako ne daga farko, kuma kada wanda ya bari kansa ya taɓa ruwan!!". TOH FAH!
Ai dukkansu bin ruwan da kallo suka yi, yana da tsawon taku 30, sannan suka ga igiyoyin da aka ce kada kansu ya taɓa, lallai aiki ne babba. UHM BASU SAN AIKI BABBA MA YANA GABA BA, AI YANZU MATAKIN PRIMARY SUKE, SAI GABA.
Wasu kuma takaici suke yi na fararen t-shirt dake jikinsu, yanzu shikenan rigarsu ya tashi a aiki kenan? Ga shi basu ga alamar fuska a wajen Captain ba bare su ce ya yi hakuri ya bari sai gobe zasu shiga kada kayansu ya ɓaci, gobe sai su sako bakaken kaya, ba hali, dole suka ɗaura ɗamara, sun fi su 100 a wajen, amma mutane uku ne suka fara faɗawa cikin ruwan kai tsaye, ciki harda NIRASH wanda shi ne farkon faɗawa bayan ya ajiye littafin da yake karantawa ɗazun da watch dake ɗaure a hannunsa a gefe kusa da Captain, ya faɗa cikin ruwa ya fara rarrrafawa da gwiwowinsa.
Zaysh ya rufa mashi baya, sai wani kyakkyawan chocolate guy dake tsaye a kusa da su shi ma ya faɗa.
Shi kansa VASH a wannan karon tsayawa ya yi yana kallon Noor cike da tashin hankali, dan wlh bai kawo a ransa zasu shiga ruwa ba, ga balain sanyi da ake yi.
Muryar Captain ce ta karaɗe kunnuwansu da cewa. "Mintuna biyu gareku, dik wanda minti biyu ta gota bai fito ba sai ya sake farowa, zai yi ta farowa har sai ya fito a mintuna biyu ko ƙasa da hakan"...... Ai tin kafin ya rufe baki mutasa sun kai 30 suka faffaɗa, still dai Noor and VASH suna tsaye, saboda sun gaji.
Ɗaya bayan ɗaya matasan nan kaf suka faɗa saura su biyu, suka ci minti ɗaya a tsaye a wajen, sai da sukaga babu wani sarki sai ALLAH sannan suka faɗa cikin ruwan suna aikin haɗe rai. Sai dai ko tsakiya basu kai ba mintuna biyu suka cika, Captain ya yi wa waɗan da suka fito kafin mintuna biyu alama da su ja baya, su sun tsira.
Waɗan da basu fito ba har mintuna biyu ya cika suna fitowa aka ce su sake farawa, tamkar zasu yi kuka haka suka sake komawa, a karo na biyu ma Noor and VASH basu fito a mintina biyun ba, kun ga rarrafe ba kamar tafiya a ƙafa bane.
Hakan yasa aka sake mayar da su, da dai VASH yaga babu mai iya kwatarsa a wannan gida, Mama no dey baba no dey fa sai ya zage a karo na uku ya fito a ƙasa da mintina biyu. Shi kuma Noor tin yana da sauran karfi har ya gaza, amma bai iya fita a kasa da mintuna biyu ba.
A tinaninsa taimaka mashi za'ayi idan ya gaza, ina ai sai ya ga akasin haka, dan a horon soja ba'a taimako, shiyasa zaku ga suna tashi a marasa tausayi, to ba'a gwada masu tausayi da imani ba a yayin horo, ubansu suke ci har zuƙatansu su bushe ba kaɗan ba.
Ai Noor bai tashi sanin a GIDAN SOJA GIDAN WUTA yake ba sai da ya ji saukar wannan uwar kwandorom ɗin takalman Captain a tsakiyar bayansa, ya takashi da karfi a cikin ruwan yana daka mashi tsawan ya yi sauri, dan kowa ya fita saura shi kaɗai, yana ɓata masu lokaci.
Dole tasa Noor ya cije, yana zafafan hawaye ya fara iyo a cikin ruwan nan, da kyar da suɗin goshi, ya maimaita sama da sau biyar, sannan ya iya fitowa a mintuna biyu daidai.
Da ya fito a tinaninsa barinsa zasu yi ya huta, sai fa ya ga akasin haka, domin kuwa sake zangon tafiya suka fara yi dan komawa ainahin cikin Barrack in da suka fito kenan, a lokacin karfe 7 daidai ta buga, sun ɗauki awa ɗaya da rabi a wannan waje kenan suna horo.
Da kyar Noor ya iya kai labari, ya ja kafafunsa suka karisa wajen, suna zuwa suka tsaitsaya a wannan katan fili da suka tsaya bayan fitowarsu daga ɗakunansu, a nan ne Captain ya ce. "Mintuna 30 gareku na yin wanka da canza kaya, 7:30 daidai zaku fara breakfast, zuwa 8 dole kun gama, 30 mins na ɗan hutawa dan kuna sabbin zuwa, 8:30 zaku fara gwada horon hannun zuwa 11 zaku shiga class! Lokacinku ya fara daga yanzu!". With harsh voice ya faɗa.
Ai da gudu suka fara watsewa, ji kake dam! Dam! Dam! Suna taka kasa, dik suka watse ya rage Noor da baya iya tafiya da kafafunsa sosai. Da gudu VASH ya dawo baya ya zo ya taimaka mashi suka koma room ɗinsu.
Da yake suna girmama lokacin, dayawansu cikin kasa da mintuna 15 suka kammala shiri except Noor da suna shiga ɗaki ma bajewa ya yi a kasa yana jan doguwar numfashi game da saukewa a hankali-hankali, har su VASH suka gama wanka, dik suka shirya cikin wandunan jeans and t-shirts masu balain kyau shi yana zaune.
Vash ne ya ce. "Noor 30 mins garemu fa, kasan dokoki da tsare-tsaren gidan nan, ba'a kauce lokaci!".... Yana kwaɓe fuska ya ce. "Ni babu in da zan sake zuwa!"........ "Noor baka son lafiyar jikinka na lura, gara maka fa ka tashi, dan wlh in muka gama breakfast ko baka yi ba lokacin horo dole Captain ya fito da kai da duka".
Noor zai sake yin magana, Leo ya riga shi da cewa. "Make sure you clean this floor before I come back". Maganansa ta farko a garesu keman. A natse ya yi magana, yana da murya mai sanyi da kaifi ga balain daɗin saurara, yana gama faɗa bai jira amsarsu ba, infact bai ɗaga ido ya kalli in da suke ba ya sa kai ya wuce da sauri abinsa, dan ya kammala shirinsa cikin wasu zafafan kayan dake nuna shi ɗan royal family ne, kansa sanye da army p-cap........ Yana yawan sanya p-cap ne saboda baya son kallo, in dai zai bar gashin kansa a buɗe sai an dinga kallonsa ko ina ya juya, shiyasa yake yawan rufewa, bugu da kari p-cap ɗin na ɗan hana ganin face ɗinsa sosai, ya huta da idanun jama'a a kansa, ga kuma kitso a kansa da ya yi, ai dole ayi ta kallonsa, kyan gashi kyan kitso da kyan halitta. Say Masha ALLAH.
Bayansa suka bi da kallo. ZAYSH ne ya ce. "This guy acting like he's our parents, ji yadda yake bamu umarni". ......... VASH ne ya ce. "I don't know why I like his character".......... "Same to me bro, and I like his sharp voice, ji yadda ya yi magana yanzu fa, like wow". Noor ya faɗa yana cigaba da kwaɓe fuska.
"Yeah, yana da tsari mai kyau for his life, but why baya mana magana bayan we're together in the same room?". Cewar ZAYSH da abin ke bawa haushi..... "That's why a like his style, he don't want to talk, and hakan girmama kai ne, amma dai yakamata ace yana yi mana magana like friends tinda we're the same now, and kuma ba wani finmu shekaru ya yi ba fa". Cewar VASH.
"We lost 5 mins again, ba lokacin wasa bane yanzu, let's go guys". Zaysh ne ya faɗa. Da sauri Vash ya ce. "Noor I don't want to see you in this situation, please tashi ka yi wanka, kaga dattin jikinka ya ɓata mana floor har wannan mai fuska irin na gangsters ɗin yana baka command na ka gyara masa waje ko?".
"Ai ba zan gyara ba, da wani nuna isa da iyayin nan nasa". Noor ya faɗa yana ɗaure fuska kafin ya daure ya miƙe, da kyar yana tangaɗi ya afka cikin toilet.
"Bari in taimaka mashi in gyara wajen". Cewar Vash yaro mai saukin kai, kuma iyayensa manyan kai ne, amma yana da sauki sosai. Da sauri Zaysh ya ce. "Don't do that, ku bar wajen haka in ga uban me wancan ɗan rainin hankalin zai yi idan ya dawo, ba ya wani ce mu gyara mashi waje ba? To ku bari mu ga me zai iya".
Ɗan zazzaro idanu Vash ya yi. "But not for him kawai ai, cleaning the place is for our healthy all"........ "I know that, but for now ka bari mu ga gudun ruwan shi, me zai iya yi mana, kasan fa idan bamu gwada mashi muma guraye bane ba zamu zauna lafiya da shi ba, yana wani ɗaga mana kai like ya fimu ne, idan ya yi wasa ma muka gama horon nan result ya fito a karkashinmu zai yi aiki".
Noor da ya fito yanzu ɗaure da towel ne ya jingina da jikin bangon wajen toilet ɗin tare da cewa. "Da kuwa ya gane kuransa, ni dan in bashi wahala har takalmata zai rinƙa wankewa".
"Zaysh, Noor kuna da matsala, idan aka biye ta ku zamu ɓata breakfast time ɗinmu a nan". Vash ya faɗa....... Karisowa ciki Noor ya yi, da sauri ya hau shiryawa yana tinanin yadda zai rinƙa gujewa horon nan. Waje Zaynash ya nufa yana jin haushin Leo a ransa, saboda yadda yake nuna masu shariya.
Hall na cin abincinsu ya nufa, yadda tsarin hall ɗin yake wajen cin abinci ne da kowani table yake ɗauƙe da four chairs, kuma kowani table da number ɗakin mutane a jiki, kamar su Leo da ɗakinsu yake room number 1, to haka table ɗinsu ma yake da number 1 a jiki, su huɗu ne a ɗakin kazalika chairs huɗu ne a wajen.
Zaune Zaynash ya isko Leo yana cin abincinsa cikin natsuwa da tsari yana kuma ɗan naɗe yatsun hannunsa kamar yana tasbihi, ya duƙar da kai ƙasa, dikkan sauran matasan ma suna zazzaune suna cin nasu abincin cikin tsari da natsuwa. Saman chair Zaynash ya zauna tare da jawo plate ɗinsa dake rufe ya buɗe.Wake ne da ƙwai dafaffa domin ƙarfafa jikinsu da ƙara masu kuzari, sai black tea mara madara, dan madara tana sanya kasala, su kuma ba'a buƙatarsu da kasala, ga bread a gefe, sannan ga lemu guda ɗaya domin kuzari da rage gajiya. Waken Zaysh ya fara ci yana ɗan satar kallon yadda Leo yake cin abincinsa tamkar baya son motsa baki, shi da yake namiji ma sai da abin ta burgesa bare mace.
A lokacin cin abincinsu fa ba a yarda a yi magana ba. Kowa yana ci da gaggawa, saboda su gama cikin 30 zuwa kasa kacal! Idan soja ya yi kuskure ko ya kasa gama cin abincinsa a cikin waɗan nan ƴan mintocin, to za a tura shi ya yi tsalle kwaɗo guda 100 ko gudu na musamman kafin a bar shi ya tafi, kuma ba zai cinye sauran abincinsa ba.
A haka su Noor suka kariso suka sami su Leo, zama suka yi suka hau cin abincin suma a cikin gaggawa, dan saura 5 mins 30 mins da aka ɗeba masu ya cika. Kafin 8 ya cika sun kammala cin abincin nasu, a nan Captain ya umarcesu da su tashi su nufi wajen da aka tanada dan ɗan miƙe kafafunsu kafin 8:30 ya cika. Da sauri suka miƙe suka nufi wajen.
Zama suka yi Zaysh and Vash suna ta gulmar Leo, kai Vash har da cewa. "Tun da ya zo yana wani naɗe yatsu ko me yake yi haka oho?".......... Zaysh ya ce. "Ni ban yarda da shi ba, daga gani daga familyn gangsters ya fito, ji wani kitso dake kansa ta bayan wuya fa". Da sauri Noor da Vash suka kai kallonsu kan bayan wuyansa ta ƙasan p-cap ɗin, a nan suka lura yana da wani abu a wajen dab gashin kansa tamkar wani zanen fuskar wani abu haka, kurawa wajen idanu Vash ya yi.
Shi kuma Noor da ɗan ba ruwana ne sai ya ɗauke kallonsa daga wajen tare da cewa. "Kuma kyakkyawa ne sosai wlh guys"........ "Ana cin kyau ne?". Zaysh ya faɗa a kufule. Murmushi kaɗan Noor ya yi wacce ta kara fito da kyansa. "To ai kaima Zaysh kyakkyawa ne, ni wlh suna mun kama da Vash ma wani zubin"...... Vash ɗin ne ne ya yi sauri cewa. "Noor banda kalaman yaudara, ta ina muke kama?".
"Seriously kun mun kama". Cewar Noor. Da sauri Vash ya sake cewa. "Baka son gaskiya dai"........ Zaysh ne ya ce. "Ku daina wannan zancen muyi focusing akan abin dake gabanmu na horo".
Kun san wani abu? Shi fa Zaynash so yake yi ya zama na ɗaya, yana jajircewa ne sosai dan ya tsallake horo lafiya ya fita da result mai kayu da karfi, ya fita a babban soja, to ya ga kuma dik ƙoƙarinsa Leo yana wucesa, ya yi iya yinsa ya isa waje sai ya samu Leo ya rigasa, to wannan abin ne yasa yake jin haushin Leo ba komai ba, yana son idan suka kammala horon nan ya zamana shi zai fito da matsayin shugaban rukuninsu, dik matasan sojijin nan su zama a karkashin ikonsa, amma yaga Leo na ƙoƙarin kawo mashi cikas.
Kuma a cikin wannan rukuni na horon shekarar nan, su uku ne zakwaƙurai wanɗan da tin a horon farkon nan manyan sojojin suka gane hakan, da Leo, Zaynash sai wani ɗan Nigeria mai suna Unays a room number 2 yake, suna da jajircewa matuƙa, dan dik horon da suka yi yau su ukun nan ne a gaba, sai dai da alama za'ayi zazzafan gasa a tsakanin su ukun nan wajen tsai da goni ɗaya, saboda yadda suke jin haushin juna, Zaynash yana jin haushin Unays da Leo, while Leo baka gane ainahin ina ma ya dosa, yana jin haushinsu ko baya ji dik ba'a gane mashi, shi ma Unays haushin Zaynash and Leo yake ji, saboda suna zuwa daidai da shi, ya so ace ya fi kowa, ga shi ɗakinsu makwabtan juna ne. KAI AKWAI KALLO FA A GIDAN SOJA WLH, ZAZZAFAR GASA, KU DAI MU JE ZUWA.
8:30 daidai Captain ya dawo hannunsa rike da wata sharɓeɓiyar bulala wacce ganinta kawai tashin hankali ne. A saman stage dake wajen ya tsaya yana faɗin. "Ready! Zaku fara horon daidaito a yanzu, zaku koyi yadda za ku tsaya da ƙafafunku ba tare da fargaba ba a lokacin harbi ko farmaki ƴan ta'adda".
Mimmiƙewa tsaye suka yi, sai suka fara kallon juna. Muryan Captain ɗin ne ya katse masu kallon da suke yi da cewa. "Kowannenku ya kama abonkin matsaya a tare"........ Basu gane nufinsa ba, hakan yasa suka sake binsa da kallo.
Ɗan gyara murya ya yi tare da sake cewa. "Ku shiga rukuni guda, dik ƴan ɗaki ɗaya su kasance a tare waje guda, zaku tsaya ne da kafafunku ɗaya a kasa, ɗaya zaku ɗangalesa a sama, dik wanda ya saki kafansa ɗayan kafin lokaci ta cika, to dikka saura mutane ukun da suke ɗaki guda zasu je da gudun gaske su taɓa wancan post dake can, wanda ya yi karshen dawowa kuma zai karɓi bulalu guda biyu masu kyau".
A miliyan suka juya suka kalli post ɗin da yake magana a kai, mugun nisa ne da shi, suka sake juyowa suka kalli bulala dake hannunsa, lallai fa babban aiki, kuma dikka wannan ace farko ne ake masu kaɗan-kaɗan? Tab gaba sai yaya kenan? Kallon juna suka sake yi, a fili Noor ya ce. "Wani kaddara ya kawoni aikin soja ne wai?". Yana kwaɓe fuska ya faɗa. Sai kuma ya juyo da kallonsa a kan Vash, Zaynash da kuma oga Leo.
Wani irin kallo Leo ya wurga mashi har sai da ya ji maƙoshinsa ta bushe yana buƙatar ruwa, in a cool way sosai Leo ya ce. "If you people cause us to fail, then what?". Then he went silent as if they already knew what would come next.
"Ready". Captain ya faɗa yana kallonsu. "Start"....... Da sauri dik suka ɗaɗɗage kafafunsu ɗaya sama suna bubbuɗe hannaye tamkar zasu tashi sama. Zubawa lokacin ido Captain ya yi a agogon dake hannunsa, lokacinsu ya fara daga yanzu kenan.
Unexpected from nowhere suka ji karar harbi da bindiga, ai kusan rabi da kwatan waɗan dake wajen sai da suka sauke kafafunsu, wasu ma har ƙoƙarin gudu suka yi, su da ake koyawa yadda zasu saita natsuwarsu a lokacin yaki, amma sune suka razana har haka daga jin karar bindiga, tab da aiki kenan, da gangan aka buga bindigar dan a gwadasu dama.
Nan fa Captain ya sanyasu gudu zuwa taɓa post, bayan sun dawo waɗan da suka yi last a kowani team suka sha bulalu bibbiyu a gadan baya, haka ya sake cewa su ɗage kafafunsu, Leo and Zaynash da Unays makocinsu sun jajirce sosai, ko da wasa basu sauke kafafunsu a lokacin karar bindigar ba, dik da cewa sun ɗan razana.
A karo na biyu suna ɗage kafafu da ƴan mintuna aka sake buga bindigar da karfi, a yanzu ma dai su dayawa suka sauke ƙafafuwa suka kuma razana, haka suka sha gudu suka kuma sha bulala. Sai a karo na uku ne suka fahimci lallai wannan bindigar saboda su ake bugawa, dan haka sai basu sake razana ba, suka tsaya, a karo na huɗu aka sake buga bindigar, nan ma dai suka tsaya cak, abin ya yi mugun burge Captain, lallai ya shaida suna da kaifin ƙwaƙwalwa da saurin gane abu, sun fahimci saboda su ake buga gun ɗin har sun ɗauki mataki, lallai suna da jajircewa da zafi nama, ya jinjina masu.
Lokacin da suka saba da karar bindigar suka gano saboda su ake yi, sai suka tsaya kyam tamkar saƙaguguna, ana buga bindigar ko a jikinsu, sai dai kuma basu fi minti uku da fara tsayawa cak ko da karar bindigar ba Noor ya sake ɗayan kafansa yana faɗin. "Wlh na gaji"........ Zaysh and Leo a tare suka haɗiyi wani irin yawun takaici, dan dikkansu burinsu team nasu ya zo na ɗaya, ransu ya sosu. Vash ma ya ji haushin sake kafa da Noor ya yi.
A tare dikkansu suka sauke kafafunsu suna ɗaure fuska, juyawa suka yi da gudu su ukun, suka nufi wannan post ɗin, shi kuma Noor ya sake ɗaga kafansa ɗaya sama bisa umarnin Captain.
Leo ne ya fara dawowa da gudu sai Zaysh ke take mashi baya, Vash ne last ɗin dawowa, ya karɓi bulalu biyu masu lafiya a gadan bayansa. Sake komawa suka yi suka tsaya suna kwaɓe fuska, Zaysh ne yake faɗi a ransa dole a canzawa Noor ɗaki, a raba shi da su tin da rago ne, su kuma ɗakinsu dikka jarumai ne!.
A karo na biyu Noor ya sake sauke kafafunsa har da durkushewa kasa yana numfashi sama-sama. Ai tamkar Zaysh ya rufe shi da duka haka suke ji. Ajiyar zuciya Leo ya sauke tare da kai hannu yana ɗan shafa kirjinsa kafin ya sauke kafafunsa ya juya da gudu ya nufi wajen post ɗin, Zaysh ya rufa mashi baya, sannan Vash.
Kamar ɗazun yanzu ma Vash ne ya sha bulala guda biyu, tamkar zai cinye Noor da harara haka suka sake komawa suka tsaya. Ina short kafin a tashi wannan horon sau uku Noor yana sasu gudu, yasa Vash karɓar bulala.
Da suka kammala sai faɗa Vash yake yi mashi, yana ta zaginsa wai ya cika ragonta, shi dai ban da ALLAH wadarai da aikin soja babu abin da yake faɗi. Shi kuwa Unays wannan faɗuwa ta Noor ta yi mashi daɗi, koba komai a yanzu team ɗinsu ta zo na farko tin da su ko ɗaya babu nasu da ya faɗi, abin ya yi mashi daɗi sosai, ji yake tamkar ya baiwa Noor kyauta.
----------------------------TIME🔥
Karfe 11 daidai suka hallara a katafaren class ɗinsu, class ɗin ya tsaru sosai, tamkar secondary set haka, suna da Ac, tables ɗinsu mai shegen kyau da loca, chairs ɗinsu mai kyau, kowa da kujerarsa. Captain Onbish ne ya hallara
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 95