shi, da komai da komai ya bashi labari.
Kai jama'a ashe dole Noor ya haɗu ba karya, mahaifinsa European, mahaifiyarsa scandinavian a Mexico, kun san da cewa kabilun scandinavian suna daga cikin top ten kabilu mafiya kyau a duniya? Tushensu a Sweden suke, amma suna iya zama a ko'ina. A top ten ɗin ma su ne na 4 a kyau! Shiyasa ɗan yaron nan ya haɗu, ga kyawawan European eyes masu ɗaukar hankali. Mutane dayawa basa banbanta Europe da Ethiopia na Afirka, to bari in banbanta maku, idan kun ji Ethiopia to nan gida Africa ake nufi, amma idan kun ji Europe yana ɗauke da ƙasashe kamar haka, United Kingdom watau Uk kenan, ko ku ce England, ita ce uwa ga Europe gabaɗaya, sai Ireland, France, Spain, Portugal, Belgium, Netherlands, Luxembourg, Germany, Switzerland, Italy, Austria, Poland, Czech Republic, Slovakia, Hungary, Slovenia, Croatia, Bosnia and Herzegovina, Serbia, Montenegro, Kosovo, Albania, North Macedoni, Greece, Bulgaria, Romania, Moldova, Ukraine, Belarus, Lithuania, Latvia, Estonia, Finland, Sweden, Norway, Denmark, Iceland, Russia ta wani ɓangare sashen turai ne, wani ɓangaren nasu kuma yana sashen Asia, su dai suna tsakiya. Haka Turkey suna tsakiya, Andorra, Monaco, San Marino, Vatican City, waɗan nan su ne Europe, kuma sune ainahin turawa ba Amruka ba, America dik ƴan bariki ne a cikinta bakin haure! Na faɗa maku ne da dayawan lokuta idan na ce Europe sai in ji kuna fassara mun shi da Afrika! To ba ɗaya bane!.
------------------------
Nisawa Leo ya yi jin labarin, a ransa yake mamakin jin sunan Fayruz Zaheeran, tabbas ya taɓa jin wannan suna, amma a ina? Ya mance, gefe guda kuma mamaki yake yi jin cewa Noor ya fi to ne daga CRYSTAL PALACE, like wow, waje ɗaya suke, dan shi ma Leo daga can yake, suna gini guda amma basu san juna ba. Da ya tuna suna gini guda sai ya ce kila a nan ya taɓa jin sunan Fayruz Zaheeran ɗin, lokaci guda kuma ya sake tunawa ashe fa suke da mallakin STARS BODY LUSH, zai iya yiwuwa ma a jikin mansu ya ga sunan.
Jin labarinsa yasa ya ji tausayinsa matuƙa, sai ya guduri niyyar taimaka mashi da gaske, a farko ya fara bashi horo ne saboda kansa ya daina sanyasu ɗaukar last, yanzu kuma zai bashi horo ne a matsayinsa na maraya ya tsaya ya karfafa kansa. Tin daga wannan rana Leo ya fara horar da Noor horo ta musamman, ya ja shi a jiki sosai, su Zaynish sai mamaki suke yi yadda aka yi Leo yake jan Noor a jiki har suna magana, sun kuma yi mamakin yadda aka yi Noor yanzu baya faɗuwa a horo, yana kokari sosai.
Sai ma da Leo ya zaunar da shi, ya nusasshesa cewa lallai ya tsaya tsayin daka ya zama namiji, kada ya biyewa shirme, kada ya manta mahaifinsa shi kaɗai ya mallaka namiji, shi kaɗai ya kwallafa rai a kansa, kada ya zubawa daddynsa ƙasa a ido, ya tsaya ya jajirce ko dan ƴan uwansa mata dake gida. Irin waɗan nan kalamai Leo ya dinga yi mashi, har ya sanya Noor ya ji wani irin karfi da kwarin gwiwa ya lulluɓesa, cikin ƙasa da wata guda gabaɗaya Noor ya canza, ba zaku taɓa cewa shi bane, ya zama jajirtacce, dik in da Leo ya sanya kafafunsa Noor ma zai sanya nasa, sun zama very close brothers!.
-------------------🔥
A yanzu sun kai watanni uku a GIDAN SOJA, sun tsaya tsayin daka suna karɓar horo babu wasa, manyan generals sun yi matuƙar sanya idanunsu a kan room 1 ɗin nan sosai, saboda jajircewa da baiwa irin nasu, yanzu ba iya Noor kawai ba, gabaɗaya ɗakin training ɗin dare suke yi, saboda su bada mamaki! Amma su Zaysh Leo yana basu horon dare ne dan kada su ja team na su ya rinƙa faɗuwa, Noor kuwa a yanzu yana bashi ne a matsayin Brother!. E akwai case.
Yau takama Monday, 5:30 bayan sun yi sallar asuba, tsaye suke a hall da suka saba tsayawa, gabaɗaya matasan idan kuka gansu a yanzu sun canza, dikkansu jikinsu ya karɓi horo wuta-wuta, dik sun murɗe sun fara zama mazajen gaske, musamman team 1 dake satar hanya su yi horon dare, jikinsu ya fi na kowa murɗewa, shi kam Leo baa magana, dama jikinsa da horo ya zo AZURE, yana gym, yanzu ya zo ya kara wuta-wuta, ai idan kuka gansa sai ka sha jinin jikinka.
Yanzu fa sun saba da Captain sosai, yana mugun son waɗan nan matasa, ya hora yara dayawa, bai taɓa jin wasu a ransa irin su ba!.
Cike da takun jarumta ya iso wajen, kamewa suka yi suka sara mashi tamkar yadda suka saba. Saman stage ya haye, ba tare da ɓata lokaci ba ya ce. "1, 2, 3 start!" Cikin ɗaga murya.
Yana cewa start suka buɗi baki game da ɗaga murya suka fara rera taken GIDAN SOJA...... "We march through fire, through storm and rain, with steel in heart, we bear the pain, for land and honor, we stand so tall, United as one, well never fall. Oh, we rise, we fight, we stand as one, through darkest nights, til battle's won. With fearless hearts, our banners wave, We are the strong, we are the brave! Our boots leave echoes on the ground, A thunderous beat, a mighty sound. No chains can break the will we hold, Our spirit fierce, our hearts like gold. Through blood and dust, through fire and war, we march ahead, forevermore. For freedom's call, for justice true, Our oath is strong, we'll see it through. Oh, we rise, we fight, we stand as one, through darkest nights, til battle's won, with fearless hearts, our banners wave, we are the strong, we are the brave!".
Bayan sun kammala rera taken nasu, ƙasa Captain ya sauƙa, jagoranci ya yi masu zuwa gym, dan yanzu kowacce safiyarsu tana farawa ne da gym kafin komai. Yana zuwa ba ɓata lokacin suka fara, a yanzu 500 push-ups suke yi in less than 15 mins, 500 sit-ups 300 burpees, kuma cikin zafin nama ba nuna kasala ko gajiya.
Room 1 suna yi ma suna tafawa da juna, Captain ya ga sabon salo, dan kuwa idan suna yi sai su ce ɗaya ya hau bayan ɗaya, Leo ya ɗauki Noor a gadan bayansa, Zaysh ya ɗau Vash a gadan bayansa, watau yi haka ma ba wata wahala sai sun ɗauki abu mai nauyi. Dik Generals na sojojin nan sun shiga mamaki sosai gaskiya, musamman a kan canzawan Noor lokaci guda, hakan yasa suka tsananta sanya masu ido sosai.
Bayan sun kammala push-up Captain ya sanyasu yin 200 squats da kaya a bayansu, wannan horo ana yi masu ne yadda zasu kware wajen iya ɗaukan ƴan uwansu a lokacin wahala, misali idan an harbi wani soja zasu iya ɗaukansa a bayan wuyan ko a kafaɗa ba tare da sun gaji ba, kun gane ai?
Haka suka kwashi 1 hour ana koya masu yadda zasu gudu da koda gawar ƴan uwansu ne a filin yaki, aka dinga sanyasu ɗaukan kayayyaki masu nauyi, shiyasa zaku ga soja zai iya ɗaukar mutum dik girmansa a kafaɗa ba tare da gajiya ba, to sun saba, su yaku-yakunsu ma ɗaukan juna suke dik girmansu su ɗaura a bayan wuya kamar sun ɗauki kwali tsabar azaban horon ya bi jiki!.
Bayan sun kammala wannan, wajen breakfast suka nufa, kamar kullum aka raba masu abinci, cikin natsuwa suka ci, yanzu an rage masu lokacin cin abinci, daga 30 mins zuwa 15 mins, dole ka kammala a 15 mins in ba haka ba ka ƙoshi, saboda horonsu yanzu ya ninku sosai shiyasa aka rage lokutan da basu da amfani sosai aka kara masu kan horo.
Bayan kammala breakfast Captain ya ɗaukesu zuwa wajen da zasu yi pain endurance test, ko kaɗan babu alamar gajiya a tattare da su, Leo da Noor sun haɗa kai, Vash and Zaysh sun haɗa kai.
A wannan horo an sa su sun zauna a ƙasa ba tare da wani ya motsa ba na tsawon awa ɗaya, suna riƙe da bindigogi masu nauyi. Idan wani ya kuskura ya motsa, sai team nasu su fara daga farko. Ga ruwan da ake watsa masu daga sama dik dan kara masu azaba, ga nauyi bindiga, ba damar motsawa ko kaɗan, ko hannunka zai yanke saboda nauyi dole ka jure. A yau ne su Noor suka ga amfanin push-up da suke yi, dan shi ya karfafa masu hannayensu har suka iya ɗaukar bindigogin nan ba tare da sun motsa ba!
Team nasu ita ce ta farko a fita wannan horo da nasara, sun yi murna, amma fa an ci kwakwa, ɗaukar bindiga mai cike da harsashe ba dik kai ba!. Waɗan da suka faɗi aka sanyasu suka fara daga farko, waɗan da suka yi nasara kuma aka ɗaukesu zuwa wajen da zasu yi JUMPING FROM HEIGHT. Wahala kenan!
Wajen wani katanga mai tsawon mita 20 aka kaisu, Captain ya ce suna da 10 mins dole su ko yi hawa katangar nan da gudu su tsallaka shi su dira ta baya!.
Wai baku mamakin yadda sojoji suka iya dirowa daga wajaje masu tsawo? Shiga gida ta katanga baya basu wahala dik tsawonta, hakazalika zaku ga tun motocinsu bai gama tsayawa ba sun iya dirowa ƙasa da gudu, sun kuma iya hawa bene ta hanyar kakkama gini ba ta staircase ko kofa ba, to ga horon da ya koya masu irin wanna, dole su haye wannan katanga su dira. Dik wanda bai yi a kan lokaci ba kun san zai sake ne!.
Ganin katangar da kyau Leo ya yi, a nan ya fahimci su Noor ba zasu iya ba, dan haka sai ya ce da Noor ya koma baya ya zo da gudu ya taka tafukan hannunsa da ya haɗa waje guda sai ya yi tsalle ya kama saman katangar ya haura sama. Captain dai yana tsaye yana kallonsu, dan a wannan waje basirarsu ta kwacesu ne, dole su koyi kowacce dabara su yi tsallaka kafin 10 mins.
Ɗaure belt ɗin wandonsa da kyau Noor ya yi, baya-baya ya yi, da gudun gaske ya zo, cikin zafin nama Leo ya sanya gwiwansa ɗaya a ƙasa, sannan ya haɗe tafukan hannunsa cikin na juna. Noor yana zuwa ya taka tafukan nasa Leo ya taimaka mashi ta hanyar tayasa ɗaga kafafun nasa, ya yi tsalle ya damki katangar. Cikin zafa ya haye tare da rike waist ɗinsa yana mai da nunfashi, saura sojojin sai faman gwadawa suke yi babu wanda ya iya, Noor shi ne na farko da ya fara hawa.
Miƙewa Leo ya yi tare da komawa baya, cikin zafa ya zo da gudun gaske, ya taka tsakiyar katangar tare da kara karfin tsallensa ya damki sama. Haurawa ya yi ya samu Noor, bai ko kalli in da saura suke ba ya kama hannun Noor suka dira ta baya. Nan fa dayawan sojoji suka fara ɗaukar salon Leo, sai su zo da gudu su taka tsakiyar katangar su kama sama su haye.
Captain yana mamakin irin baiwar Leo, kullum shi yake kawo masu salo na musamman, har ta kai in suka je wajen sabon horo suna jiran Leo ya fara, da ya yi kowa zai ɗauki salonsa. Zaysh, Unays, Vash and Juraiz matashin dake ɗakinsu Unays, su ne suka yi na biyun haye katangar, Juraiz jajirtaccen matashi ne, shi ma ɗan Naija ne, ya fito daga Kano ta dabo tumbin gwiwa, kun san kanawa dik abin da suka yi niyyar yi sai sun yi ne, kowa sai ya jirasu! Dan haka Juraiz ba baya ba!
A yanzu dikka matasan sun haye ginin da salon Leo, Captain ya sanyasu suka dinga maimaitawa har na tsawon awa ɗaya, sai da suka saba sosai, a karshe ma kusan a tare dikkansu suka haye saboda an kware ya bi jiki.
Daga nan aka wuce da su wani ɗaki mai matuƙar duhu dan a masu mental stress training, ɗaki ne da ko yatsanka ba zaka iya gani ba saboda tsananin duhu, haka aka rufesu a ciki na tsawon wannan lokaci, ga ƙara na harbi bindigogin dake tashi kusa da wajen, so ake yi a koya masu natsuwa a lokacin tashin hankali da wahala, su natsu su nemawa kansu mafita mai kyau, da yake kuma dikkansu natsastsun matasa ne sai aka samu abin da ake so, dan dik harbin nan da ake yi suna zaune hankalinsu a kwance, wasu ma hiransu suke yi, to kunnuwa sun saba da harbin bindigar ne ai!.
Bayan awa Captain ya fitar da su aka wuce da su wajen da zasu yi rescue run. A nan ma ana koya musu wata dabara ce na yadda za su ceci abokanansu a lokacin yaƙi. An sanyasu sun sanya kaya masu nauyi a jikinsu, sannan su ɗauki abokin horonsu da suka yi kamar sun ji ciwo ba zasu iya tafiya ba, kamar an harbesu a kafa, Captain ya ce su yi gudu da su a bayansu na tsawon mita 500. Amfanin sanya kaya mai nauyi a jikinsu shine, a lokacin yaki zasu ɗauki bindigunsu, ga tarin alburusan dake waist ɗinsu, suma masu nau yi ne, sannan su ɗauki ƴan uwansu, kunga dole su sanya kaya masu nauyi yayin wannan gwaji.
A wannan karon Leo yaki ɗaukar Noor, dan ya ce ya yi mashi kaɗan, bashi da nauyi! Dan haka sai ya ce Juraiz na ɗakinsu Unays ya zo. Ba musu ya je dan shi ma yana mugun yin Leo ba karya, dik wanda ya ce baya son Leo sai in hasada wlh, Juraiz kuwa bashi da hasada dan haka yana yin Leo!.
A bayan wuya ya ɗaukesa, Vash ya ɗauki Noor, Zaysh ya ɗauki Ameer na ɗakinsu Unays, shi kuma Unays ya ɗauki wani katon matashi a room nasu yake shi ma, shi ne cikon na huɗunsu, suka yi ready, Captain na cewa go suka danna da gudu. Dikkansu su babu wanda ya faɗi, hakan na nufin zasu iya cetan abokansu a wajen yaki. Sosai Captain ya dinga sanyasu maimaita wannan horo, saboda yana da mugun muhimmanci a tattare da su!.
Bayan kammala wannan, suka yi sallah suka yi lunch sannan suka shiga class, a ajinsu na yau an koya masu yadda ake haɗa bindiga cikin ƙanƙanin lokaci, ka shirya shi ka sanya bullets, sannan aka koya masu yadda ake goge bindiga idan ta yi datti, aka karantar da su me bullet! Me karancin gudun da yake yi a second, me karshen gudunsa a second, daga nan aka koya masu yadda ake rike kowacce bindiga. A class yau an sha artabo, dan ba kowa ya iya rike bindiga ya yi harbi ba, wasu idan bullet ya zo fita tafiya suke yi da bindigar gabaɗaya su faɗi kasa. Kun san da cewa in bullet ya zo fita da karfi jan bindigar yake yi? In baku sani ba yau kun sani, sai mutum ya jajirce ya rike da karfi in ba haka ba su wuce tare da bullet ɗin, karfin bala'i ne da fitar bullet, baku ga har wani hayaki yake yi idan ya zo fita ba?.
Captain da kansa yau ya sha dariya yadda aka basu ƙananan bindigu su gwada harbi, sai dai Captain ɗin ya ga sun wuce tare da bindigar sun faɗi ƙasa, bullet ya jasu. Abin mamaki Noor bai faɗi ba, bullet bata ja shi ba, dik da bindigar koyar harbi daban, na yaki daban, amma ko na yakin aka bashi tabbas ba zata jashi ba, dan shi ɗin renon Leo ne!.
Captain ya yi mamaki sosai, wai Noor ne da jarumta haka!....... Bayan sun kammala wannan class suka wuce wajen horon magana da ido, kullum sai an koya masu shi, saboda yana da mugun amfani a wajensu, yakamata ace suna da silent words wa juna!.
A yanzu horar da su yana yi wa Captain mugun daɗi, saboda babu ragwaye babu mai sanya shi ciwon kai!...... Basu suka tashi horon yau ba sai karfe 7 kamar da aka saba. Suka yi sallar mangarin and Isha'i, suka yi dinner sannan kowannensu ya koma room ɗinsa.
Suna shiga suka hau yin wanka. Bayan sun yi shirin kwanciya kowa ya hau neman gida. Shi kuma Leo ya kwanta ya ɗauko book ɗinsa yana bitan karatun da suka yi ɗazun, yana jinsu suna ta hira da gida ko a jikinsa. Da suka ishe shi sai ya ce dik su kashe wayoyinsu ko ya karɓa ya fasa! Daga magana ɗaya bai sake ba dik suka kashe wayoyin nasu saboda tsoronsa da suke ji.
A takaice ya ce dik su fito da littafansu su fara karatu! Wani irin harara Zaysh ya dallah mashi kafin ya fito da book ɗinsa, a ransa yana faɗin. "Sai ya dinga yi mana magana kamar shi ne ubanmu, ba za'ayi karatun ba tin da kai ka haifemu". A fili kuma dole ya fito da book ɗin ya fara karatu, dan yasan Leo baya ɗaukar wasa ko shirme, yanzu jikinsu zai gaya masu, ba duka ba zagi amma akwai horarwa! Ganshi da ɗan banzan kwarjinin da yasa suke shakkarsa.
Haka ɗakin ya natsu tsit suka fara karatu, suna jiran 11 ya cika su saci hanya zuwa wajen horon dare da suka saba!.
------------------------🔥
Sanye suke da sleeping dress mai zubin pj's launin maroon, sun yi matuƙar kyau, dikkansu kwance suke a saman beds ɗinsu, sun saki gashin kan nan nasu har ƙugunsu. Arya tana practical a kan karatunsu na yau, amma gabaɗaya zuciyanta yana kan tinanin Leo da yau tsawon wata kenan da haɗuwarsu, basu sake haɗuwa ba, amma ya tsaya a dikka zuƙatan yaran GAT, da tinaninsa suke kwana suke kuma tashi! Su kansu basu san dalilin tinanin nasa ba!.
Ta yi nisa cikin aikin da take yi na ƙoƙarin bin diddigi da kuma datsar wata camerar, shi ne karatun da aka yi masu yau. While ita kuma V tana can tana karance-karance labaran soyayya, a maimakon ta yi practical na abin da aka koya masu, ta tsaya biyewa soyayya.
Manassa tana nata aikin ita ma na fannin likitanci, while Angelina ta kashe laptop ɗinta, ta ajiye shi a gefe, ta shiga bargo tamkar mai yin barci, wayarta ta kunna tana kallon film ɗin batsa a wayar, ita kuma tata bala'in kenan, tin bata kai ko'ina ba akwai ta da son sharholiya, ta iya kallon film ɗin batsa sosai, yanzu ba abin da bata sani ba, shiyasa ta matsu take son saurayi, ta ce sex zai yi daɗi tin bata ɗanɗana ba, wai a haka ma GAT yana mugun sa ido a kan yaran fa, amma ya yi sake idanunsu ya buɗe, wayayyu ne sosai, shiyasa uwa daban take, haka tarbiyarta ma daban yake, da uwar tana raye wasu abubuwan ba zasu yi shi ba.
Batu na gaskiya Angelina ta fisu buɗewar ido a ɓangaren maza da son romance, ita kuma V soyayya da shagwaɓa, har da cewa ita namiji ɗan shagwaɓa zata aura, wanda zai dinga yi mata kuka idan suna romancing juna, ita kuwa Arya cewa ta yi bata ga namijin da zata so ba, suma masu zancen mazan basu da hankali ne, dan haka tana hana su V zancen soyayya, while ita kuwa Manassa komai ma daidai ne, idan anga dama ayi soyayya, idan ba'a yi bama matsalar mutum ne, ita dai karatu ne a gabanta.
V dake ta faman sakin kyakkyawan murmushi ne ta ce. "Bloody i wish in samu masoyi like me yanzu, ku kashe juna da love and romance"........ Manassa dake aikinta ne ta amsa da. "Aikuwa da an yi shirme, saurayi irinki to waye zai rarrashi wani idan ɗaya yana kuka? Nan in kika fara kuka sai daddy ya zo! Ai ke sai irin gangsters da basa dariyar nan ne zasu gyara maki zama".
Arya ce amsa da cewa. "Ke baki da wani aiki sai labaran soyayya ne? Ba zaki yi abin da zai amfani rayuwarki ba ko?"...... Turo baki ta yi kafin ta ce. "Aikinku kenan ai, ku baku san soyayya da shegen daɗi bane, ina zan ga jarumina, Angelie please ku nemo mun shi, zan faɗa mashi ina son shi! Ya zo in yi hugging ɗinsa, in yi kissing ɗinsa, huuuuuuu, I really like love and romance". A shagwaɓe sosai ta faɗa.
Siririn tsaki Arya ta ja tare da cewa. "For sure watarana wannan shauki ne zai gamasar dake! Ni sai na rasa a ina ma kike koyan wasu abubuwa"...... Manassa ce ta amsa da. "Arya, love fa akwai daɗi, there was a time da na kalli wani love film, they way suke son juna, I felt like ace ni ce".
Shiru Arya bata sake tankasu ba, saboda gabaɗaya gani take basu da aikin yi ne yasa, ita bata ga dalilin da zai sanya ta so wani namiji ba......... V ce ta katsesu da cewa. "Oh my God, bloody please ku ce masoyina a dik in da yake ya zo gareni". Ta faɗa idanunta a kan laptop ɗinta tana rungumar Teddyn dake manne da kirjinta.
"Ga masoyin naki ai a jikin roba". A cewar Manassa. Wani irin haɗaɗɗen murmushi ta saki kafin ta amsa da. "Shi wannan ai special ne, nasan ba zan taɓa ganinsa ba bare har ya so yi, shiyasa ban saka a raina zan same shi ba, amma ba zan taɓa son wani kaman yadda nake son shi ba, hoooo look at his soft lips and his big-big sharp eyes, his hair, karshe ne shi ɗin".
Arya ce ta amsa da. "Dama ya za'ayi ki so wani kamar yadda kike son shi tin da har zanen tattoo na face ɗinsa kika je aka yi maki a baya, V you're totally crazy a kan guy da bama a nan yake ba, check they're product very well daga US suke, a ina zaki gansa, amma kin tashi kin je an zana maki face ɗinsa a baya saboda baki da hankali, yanzu idan kika samu boyfriend zaku yi aure ya gani fa? Me zaki ce mashi?".
Tana turo baki ta amsa da. "Dik boyfriend da zan yi sai na faɗa mashi ni fa ina son wani! Dan haka kada ya ji haushin zanen bayana"........ Da sauri Manassa ta ce. "Ba lallai ma akwai wannan guy ɗin a zahiri ba, na fi tinanin zana shi kawai suka yi saboda ya dace da products ɗinsu, amma ke kinsan daga ganin wannan kyau ba na zahiri bane, kalli eyes ɗinsa fa, kamar na wancan guy da ya zo ɗaukarmu a school (Leo), they have sharp eyes mai rikitar da mutane, seriously babu wannan guy a zahiri, dan haka stop wahala your self and focus on what is very important in your life, in ba haka ba in faɗawa daddy, ni ko wancan Nirash ɗin ban gama yarda mutum bane!". On a serious note ta yi maganar!.
Wai kun san dik a kan waye ake wannan zance har ake cewa babu shi a zahiri? A kan hoton jikin STARS BODY LUSH, watau hoton Noor namu na amana, yaran nan a lokacin da suka fara ganin Noor a jikin man shafawan daddynsu sun yi hauka a kansa, V har mafarkinsa take yi kullum, su sauran da suka ce babu shi a zahiri sai suka cire son shi a ransu, ita kuwa V tsabar haukan son shi da take yi har da zuwa a zana mata hoton nasa ɗan karami a bayanta, ga shi ko sunansa bata sani ba, kawai tsantsar kauna ce, har ce mata su Arya suke yi bata da hankali tana son abin da babu shi a zahiri, ita dai bata sanya a ranta zata same shi ba, amma taki yarda babu shi a zahiri, ta ce tin da yana zuwa mafarkinta to akwai shi a zahiri!.
"Ni Manassa ki kyaleni, ko babu shi a zahiri ni ina son shi har cikin raina, ina fatan samun babys irinsa, amma kun san me?". Ta faɗa tana hura kumatu, ranta ya ɓaci an zagi jaruminta.
Arya dai bata sake yin magana ba, ta cigaba da abin da take yi dan bata cika biyewa zancen da ya shafi soyayya ba idan suna yi, gani take shirme ne. Manassa ce ta ce. "A'a bamu sani ba sai kin faɗa"........ Ɗan murmusawa ta yi har kyawawan fararen tas ɗin hakwaranta bayyana, ga giɓin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 95