Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ɗin suka nufa. Ɗaki ne wanda kun sani, cike yake da glasses dayawa, sannan kamar chemical lap haka wajen yake, dik ta in da ka juya manyan chemical ne masu mugun haɗarin gaske a wajen. Sister Zinta and sister Maya suna sanye da chemical care gown, hand gloves a hannu, socks a ƙafa, eyes care a idanu, sun dukufa gaban computers sai aiki tuƙuru suke yi. 3D na shigowa suka miƙe tsaye dan girmamawa a garesu, yanzu almost 4 months kenan suna wannan aikin, tin ranar da suka sanya hannu, barci wannan rabi da rabi suke yi. Abin da zai baku mamaki kuma basu taɓa sanin aikin me suke yi ba, kawai suna tsamo wasu chemicals ɗin ne su sanya a wasu, amma kowanne sai sun tacesa sun ciri mai karfin cikinsa, idan kun fahimta su Maya ilimin chemical kawai suke da shi. Duba aikin nasu 3D suka yi, komai na tafiya yadda yakamata, jinjina masu Dr Kamal ya yi, da alama ya fi su Dr James sauƙin kai, fitowa suka yi daga cikin room ɗin izuwa side na dabbobi watau section B. Yau wajen a cike yake da kukan dabbobi kala-kala, ga waɗan nan jiga-jigan guards ɗin suna ta aikin kai komo. Sanya gabaɗaya guards ɗin suke da kayan kariya a jikinsu, da alama aiki tuƙuru suke yi. Gaban wasu manyan guards biyu 3D suka tsaya, matasan nan suna rike da zabga-zabgan macizai guda biyu, sun mace kan macizan jikin wani kwalba, sun ɗaura hakwaran macizan a bakin kwalbar, sannan sun matse tsakiya wajen cikin macizan, macizan sai fito da wani green ruwa daga bakinsu suke yi yana zuba a cikin kwalbar. Wannan green ruwa shi ake kira da neurotoxic, hemotoxin, sinadarai ne masu matuƙar haɗari da illah, dan suna hana jini gudana a jiki, and yana lalata jijiyoyin jini, a hankali ya lalata tsokoki jikin mutum, to wannan sinadaran suke matsowa daga jikin macizan. Jinjina kai 3D suka yi alamar aiki na tafiya da kyau, sai suka matsa kusa da wasu guards dake mace sinadaran corpion mai suna chlorotoxin, watau wani sinadari ne dake shafar jijiyoyi, yana haddasa raunin jijiya daga nan shanyewar jiki, shi ma sinadarin da yanayin yadda suke tatsansa a jikin dabobbin, kowacce dabba tana da sinadari mai cutarwa kuma tana da mai amfani, dan haka kowanne da yanayin yadda ake fitar da shi, kunga maciji tana da sinadarin da ake iya yin maganin ciwon zuciyaa da shi, kunga wannan ba mai cutarwa bane, amma su a nan mai cutarwa suke fitarwa. A nan ma sun tabbatar komai ma tafiya daidai sai suka wuce gaba. Nan ma wasu guards ne ke ta faman matse sinadarin dart frog mai suna batrachotoxin, sinadari ne da idan ya shiga jikin mutum yana toshe sodium channels, yana haddasa bugun zuciya ta tsaya cak, amma a hankali yake aiki na likitoci guda ba...... Nan ma duba aikin na tafiya daidai. Gaba suka ƙara wajen masu tatsan dafin pufferfish mai suna tetrodotoxin, watau sinadari ne da idan ya shiga jikin mutim yana toshe jijiyoyin jini, yana sanya numfashi ta dinga ɗaukewa tana sama-sama kamar mutum zai mutu. A nan ma komai na tafiya daidai. Wucewa gaba suka yi wajen guards dake tatso tsinadarin cone snail mai suna conotoxins, shi wannan sinadarin idan ya shiga jiki yana hana jijiyoyi aiki, yana haddasa shanyewar gaɓoɓi ya baka sassaiɓar mutuwa ba mutuwa da gaggawa ba, sai ya gana maka azaba a jiki. Oh ni Princess Teema na shiga uku, ko me suke yi da wannan sinadaran? A tinaninku me suke yi da shi?. Kai idan kana raye babu abin da ba zaka gani ba, ALLAH ka kawo mana agaji, ka dubemu da idanun rahama ka dafa mana, ALLAH ka jiƙanmu ka jiɓancin al'amurranmu. Sai da suka tabbatar komai na tafiya daidai kafin su fito daga wannan ɓangare, kai tsaye suka koma wannan ɗaki na meeting ɗin nasu da suke zama. Dr Mark ya ɗauko glass cup da wani tangamemem drink ya nufi saman sofa. Dikkansu zama suka yi a kan sofas ɗinsu, Dr Mark ya tsiyaya drink ɗinsa a cup, dan shi karatu ta fi shigansa idan yana yi yana sipping drink mai sanyi, kuma ɗan banza kullum Americano yake sha. Dr James ne ya miƙe tsaye tare da kunna light na tangamemen touchscreen computer dake gabansu sofas ɗin nasu, ya ɗauki wani sanda siriri dake wajen ya rike da hannu dan ya ji daɗin bayani. Hannu ya ɗaura kan screen na computer, pressing ɗinta ya shiga yi cikin kwarewa for like 5 mins, sannan ya ɗauke hannu. Take wani rubutu ya bayyana a kan screen ɗin, P-C shi ne sunan project ɗin, idan baku manta ba project da suke yi da su Maya kenan, sai yau zasu mana bayanin wani irin project ne. NEXAPOX-31 shi ne ainahin sunan da suka sanyawa wannan aiki, a jikin folder na aikin ma sunan dake rubuce kenan. Cikin folder ya shiga kai tsaye. Take wani dogon jawabi ya bayyana. Kara natsuwa su Dr Kamal suka yi dan sauraran wannan aiki, gagarumin aiki ne da sun jima suna yinsa, ba tin yau bane, ya haura shekaru 5 suna shiryasa, yanzu ne da aka hura masu wuta daga can WORLD SYSTEM shi ne suke son kaddamar da aikin cikin gaggawa su fito da shi, dakon jiransu ake kamar hauka, hakan zai tabbatar maku makudan biliyoyin daloli ne a kan wannan project ɗin. A natse ya ce. "Menene NEXAPOX-31?". Ya faɗa yana mai da kallonsa a kan su Dr Mark da suka kara natsuwa, one thing, dikkansu 3D ɗin nan Dr James kamar malaminsu yake, ya fisu kwarewa a kan komai, bugu da kari shi yake yin dik wasu manyan project irin NEXAPOX-31 da sauransu, sai ya kammala shirya manyan abubuwa game da project ɗin, sannan yake zama kamar dai yanda suka zauna yanzu ya zayyana masu irin project ɗin, amma a tare suke yin komai, sai dai ba lallai su san kai tsaye ga abin da suke shiryawa ba, sai an yi tafiya mai nisa yake zama yai masu bayani, daga nan su karisa a tare! Fatan kun fahimceni?. "NEXAPOX-31 wata.......... Likes comments and share fisabilillah. STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥 For more information 08161390581 Whatsapp me only. ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️ 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A STAR LADY. STEP 1🔥 2025-12-1.🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E_____________ 32 & 33 "NEXAPOX-31 wata cuta ce mai ƙwayoyin virus, tin da nike project a kan cututtuka ban taɓa yin makamancin wannan ba, ya sha bamban da dik wata cuta da ya wanzu a baya, wannan cuta na ciro kwayoyin cuta da dama daga jikin dabbobi masu haɗari kamar su bats, rodents, and reptiles da sauran dabbobi, na jima ina shirya wannan project ɗin"...... Ya ɗan nisa kafin ya cigaba da cewa. "Na faɗa maku ta zarce cututtukan da suka wanzu a baya irin COVID-19, HIV, Ebola da dai sauran manyan cututtuka masu haɗari da suka gigita duniya, to wannan ya damesu ya shanye, domin kuwa shi ne cuta na farko da yake ƙunshe da DNA da RNA a lokaci guda, wadda ke ba ta damar canzawa da wuri da tserewa immune system watau garkuwar jikin ƴan adam". Ya sake ɗan dakatawa ya nisa kafin ya cigaba da cewa. "Wannan cuta zata yi balain girgiza duniy fiye da yadda su COVID-19 suka girgiza duniya a baya, chemicals da na ruɓar tsawon shekaru uku a wannan cuta ba karamin abu bane, dole wannan cuta ta gigita duniya, hankula zasu tashi, asibitoti zasu cika, rayuka zasu salwanta, tattalin arzikin duniya zata girgiza, manyan ƙasashen da cutar zata fi shafa zasu shiga wahala, tattalin arzikinsu zai ruguje, za'a rufe ƙasashen ba shiga ba fita, kuɗi ba zasu shiga ba kuma ba zasu fita ba, zasu cinye abin da suka tara, wahalar zata zarce yadda ake zato". Ya dakata yana mai da numfashi. Dr Mark ne ya ce. "Good job, gaskiya wannan cuta da alama da zafinta take tafe, amma a wannan karon ta yaya (WS) World system suk shirya baza cutar ta isa ga in da ake so?". Shiru Dr James ya ɗan yi na ɗan lokaci kafin ya ce. "Ta kasuwannin nama masu ɓoyayyen tsari watau wet markets, kasan na tsara cutar ta yadda zata iya ɗaukar makonni biyu a jikin mutum bata nuna ba, so zata iy makonni uku a jikin dabobbi bata nuna ba, dan haka zamu yi amfani da kasuwannin dabbobi, zamu samo kosassun dabbobi mu yi masu alluran cutan sai mu kaisu kasuwannin, mutane zasu sayesu, dik wanda ya ci namansu ya kamu kenan, idan aka yanka dabbar masu saya suka sayi nama shikenan kuma! Dole cutar zata bazu". Ya nisa kafin ya cigaba da cewa. "Wani abin birgewa kuma a nan shi ne cutar zata bazu a cikin mutane ne ta hanyar airtight aerosol droplets, zata shiga ta hanci ko baki, ta dai hanyar iskar da mai ɗauke da cutar yake fitarwa kamar numfashinsa kenan, dik wanda ya ci namar dabbar a gida idan ya yi numfashi kusa da wani shikenan shi ma zai ɗauki cutar, daga nan cutar zata ratsa jikinsa har ta shiga huhu, a ƙasa da sati biyu zata fara tarwatsa dik wasu kariyar jikinsa". "Hanya ta biyu da cutar zata shiga shi me ocular membrane, idan mai ɗauke da kwayar cutar ya taɓa idanun wanda bai da shi yakan iya kamuwa shi ma, ta hakan ma ta fi haɗari, dan zata shiga cikin jini ne kai tsaye daga ido". "Hanya ta uku shi ne cin abinci mai ɗauke da cutar, kamar namar dabbobin da zamu yi wa alluran, ko kayan lambun da zamu yi wa dajuka feshin cutar, muddin mutane basu wanke kayan lambun da gishiri sosai ba tabbas zasu kamu". Ya kai karshen jawabin yana binsu da kallo. Dr Kamal ne ya ce. "Nice work, amma kuma wani irin illah zasu yi wa ɗan adam baka faɗa mana ba"........ Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da taɓa screen na computer, ya shiga cikin folder ɗin cutar da kyau, take bayanai suka bayana rututu, ƴar sandar dake hannunsa ya gyara tare da fara yi masu nuni da jikin screen ɗin before ya fara bayani. "Na faɗa maku wannan cutar ta fi COVID-19 haɗari nesa ba kusa ba, cuta ce dake ƙunshe da DNA da RNA a lokaci guda, shi ne illar farko, illa ta biyu cutar tana lalata lungs, tana sa huhu ya cika da ruwa mai guba, wanda ke janyo mutuwa cikin awanni 72, amma kada ku manta na faɗa maku cutar tana ɓuya a jiki ba'a ganeta da wuri, tana kai 2 weeks kafin ta bayyana, a wannan 2 weeks ɗin cutar zata yi yawo a cikin jinin mutum, ta bi ko'ina ta kashe garkuwar jiki a saiɓaɓe, so zata kashe dik wani garkuwar jiki ta yadda idan ta bayyana jikin mutum ba zai karɓi maganin kowani iri ba sai maganin da na kirkiran wa cutar, sannan sai ta bayyana ne take kashewa a awanni 72". Ya ja numfashi kafin ya cigaba da cewa. "Illah ta biyu da zata yi wa mutum shi ne acute respiratory collapse, ciwon ɗaukewar numfashi mai karfi, sannan ya haifar da zazzaɓi mai zafin gaske, ciwon kai mai tsanani, da ciwuka a fata irin na bullae kuma irin na monkeypox dake fashewa suna zubar da jini, and za'a su haifar da karancin jini da platelets, wanda ke haifar da zubar jini daga hanci, kunne, idanu, da al'aura, dik zasu faru ne idan cutar ta bayyana a jiki, kuma dik zasu faru da mutum ne a ƙasa da waɗan nan 72 hours ɗin". "Idan mutum yana da sauran kwana a gaba bai mutu a cikin 72 hours ɗin nan ba to fa zai kamu da cerebral infiltration, dan karfinta zai sanya ta shiga blood brain barrier, watau jinin kwakwalwa ta janyo hauka, da kurmancewa". Ya sake sauke ajiyar zuciya kafin ya cigaba da cewa. "Mortality wannan cuta ta fi COVID-19 da yawa, saboda zata kashe mutane 40 cikin ɗari 100 na duniya a cikin kwanaki 5 zuwa 7 da bayyanarta idan ba ayi maganinta da gaggawa ba, wanda kuma kun san da cewa maganinta babu wanda ya isa ya yi ta a duniya! Babu mai maganinta sai makirkirinta". Ya kai karshen maganar tare da sakin wani irin one side smiling na zallar mugunta yana wani ɗaure fuska at the same time kaman wani shaiɗani. Hannu suka ɗaga suka jinjina mashi, sannan Dr Mark ya ce. "Amma kai tsaye me zai sa wannan cuta ta fi COVID-19 da sauran cutukan baya ban tsoro da firgitarwa?". Bottle water ya wuce cikin freezer ɗinsu ya ɗauko tare da glass cup, wajen ya dawo, saman sofa ya zauna tare da ɓalle bakin robar ruwan, ya daddala a cup, a natse ya kai ɗan bakinsa. Mai ɗan yawa ya sha tare da ajiye cup ɗin, sannan ya miƙe ya koma gaban computer bayan ya ajiye cup ɗin a saman glasa table dake gabansu. A natse ya ɗaura hannunsa kan screen na computer, ƙasa ya yi da bayanan izuwa kan amsar tambayar Dr Mark. Cikin natsuwa ya fara bayani kamar haka. "Abin da yasa ya fi COVID-19 ban tsoro shi ne yana ɓoyewa a jiki har tsawon sati biyu ba tare da wata alama ba, sannan yana yaɗuwa ne ta cikin iska, ruwa, goganyar fata, ya fi COVID kamuwa da sauri, bugu da kari shi yana kaucewa rigakafi, wato da wuya allurar rigakafi ta yi aiki da sauri saboda canjin DNA na wuce misali da yake da shi, wannan sati biyu da yake yi a ɓoye a jikin mutum yana sanyawa ya lalata garkuwan jiki ta yadda babu wani maganin da jikin zata karɓa face maganin da na basu da kaina, haɗarinta ya zarce tinaninku". Dr Kamal ne ya katse shi da cewa. "Hope ka shirya maganinta?"...... Jinjina kai ya yi tare da cewa. "Ka san bama ƙirƙirar cuta haka ba tare da mun shirya mataninta ba"....... Kai 2D suka jinjina mashi kafin su hau zuba mashi jinjinar ban girma da kwarara mashi gwiwa. A dake ya ce. "Sai duniya ta gigita zamu fitar da even rigakafin cutar, da rigakafin kawai nike son mu tara billiyoyin daloli kafin mu je kan maganin, dan a wannan karon kamar yadda cutar take special haka maganinta yake special, maganin zamu zuba mashi maƙudan kuɗi na wuce misali ta yadda zai sa a rasa rayuka dan ba kowa zai iya mallakar maganin ba". Cike da zallar rashin imani ya kai karshen maganar. Watau duniya ta zarce yadda dik ɗan adam yake tinani, zasu kirkiri cuta dan raje yawan al'umma kuma dan kasuwanci, domin kuwa suke da riba, ko rigakafin cutar kawai suka fitar a guje za'a bi maganin dan ana tsaka mai wuya, a rigakafin kawai ba karamin kuɗi zasu samu ba, kun ji sun ce sai duniya ta jigata ta rasa madafa zasu saki maganin cutar, hakan ma da mugun tsada zasu saki maganin ta yadda ba kowa zai iya saya ba. A nan ina da tambaya! Kun taɓa tambayar kanku cewa waɗan nan cututtuka da suke ɓullowa duniya daga ina suke ɓullowa?...... Bayan na gama jin bayanan Dr James na yi wani tinani fa my people, amma bari in barwa zuciyata wannan tinani, ALLAH yasa shiruna ya zame mun alkhairi! Wai ko dai in faɗa ne kawai?........🤔 Amma ku kuma ku faɗa mun bayan kun gama jin wannan bayani na Dr wani tinani kuka yi? Ko dai har yanzu kuna nan jiya iyau? Ba cigaba? Sai jinjina mashi su Dr Kamal suke yi suna yaba muguntarsa, suna kuma kara mashi kwarin gwiwa. Shi kuwa sai kara jin kansa na kara girma yake yi. Cikin wani irin murya mai amo ya ce. "A yanzu duniya a tafin hannuna take! Sai yadda na yi da ita! Ni ne Devil wanda da zai yi wa mai gida Dujjal tarba ta ban girma a lokacin da zai iso! Wannan project yakamata na canza mashi suna daga PC izuwa Death is inevitable! Ko kuma a death that wipes out an entire family!!"........ Dr Mark ne ya ce. "Ka barsa a PC ɗin ma ya yi". (PC yana nufin Population Control, na ji wasunku suna cewa CRYSTAL PALACE ne PC da yake nufi, to ba haka bane, CRYSTAL PALACE fa CP ne ba PC ba kusan ɗaya suke yasa kuka ruɗe) Dr Mark ne ya ce. "Amma meyasa WS ta hura mana wuta kan mu saki project ɗin nan yanzu? Mun yi da ita ai sai shekaru uku zuwa huɗu gaba, meyasa suka ce lallai mu saketa yazu?". Nisawa ya ɗan yi kafin ya ce. "Kasan a wasu ƙasashen za'a kafa sabuwar gwamnati, ma'ana zaɓe ta ƙarato saura shekara ɗaya da ƴan watanni, sannan kasan akwai manyan ƙasashen da suka gwadawa WS taurin kai, kuma da alama ƙasashen sun tsaya da ƙafafuwansu, suna da karfin tattalin arziki da karfin faɗa aji, sannan da alama suna da power da WS take shakkarsu shiyasa suka buƙaci project ɗin nan dan su gigita kowa, a taƙaice dai gargaɗi mai karfi suke son yi wa duniya, a karkashin ƙasa kuma akwai plan na ruguje ƙasashen da suka kawo karfi suke ganin suna da murya mai karfi, sannan a gefen ƙasashen dake biyayya ga WS kuma su za'a haɗasu da wannan cuta ne domin sabuwar gwamnatin da zasu kafa, a hargitsa ƴan ƙasa ta yadda gwamnatin da ta hau sabuwa ba za'a ga laifinta a farko ba, za'a ce duniya ta shiga rikici, so ko gwamnatin ta yi shekarun mulkinta bata yi wa ƴan ƙasa komai ba za'a ce ai dama wannan balain da ta faru na wannan cuta gwamnatin ba zata iya shawo kan matsalar lokaci guda ba, so kunga a nan dik badakalar da gwamnatin zata yi babu wanda zai mai da hankali ko ya zargesu, daga nan WS zata cinwa abin da take so". Wannan bayani nasa ya mugun gamsar da su, watau WS basa sakar cuta sai idan za'a samu sabbin gwamnatin dake masu mubaya'a, watau a kowani gwamnati sau ɗaya suke sake cuta ko da wannan gwamnatin zata sake maimaita shekarunta a mulki ba zasu saki wata cuta ba sai idan sabuwar gwamnatin ce zata hau, sannan suna yin hakan kuma dan su ruguje ƙasashen dake ƙoƙarin tasowa! Tab akwai matsala. Dr Mark zai yi magana suka ji alamar motsi a office na Dr James, Dr Kamal ne ya ce. "Ko su Maya ne?"....... Kai Dr James girgiza kafin ya ce. "Sai dai Lazy"....... Wani irin shu'umin murmushi Dr Mark ya saki kafin ya ce. "Ce mun zaka yi mutuniyarka, James Lazy fa sonka take yi"...... Wani irin ɗaure fuska ya yi kafin ya ce. "Me zan yi da tsohuwar da komanta ya kare? Kada ka manta Lazy ta haura 47 years, surgery ne da magunguna yasa take haka, da kaina in mata surgery ɗin sannan in dawo in kwashi ragowa? Are you out of your sense?!". Wani irin dariyar mugunta Dr Kamal ya yi kafin ya ce. "Zakuwa ku dace, tana sonka sosai fa, kada ka manta ta yi maka abubuwa da dama a rayuwa, ita ta taimaka maka wajen kawo ƙarshen Muhammad Haiza'an, kada ka manta idan ba da sa hannunta ba baka isa shiga CRYSTAL PALACE har ka sace Muhammad mu yi nasarar cire ƙwaƙwalwansa ba, dan haka Lazy bata cancanci ka ki ta ba". Ya kai karshe yana dariyar shakiyanci da iskanci. Kara ɗaure fuska Dr James ya yi tare da cewa. "Stop it! Dik abin da Lazy ta yi she did it because of money, na biyata hakkinta sai kuma ta ce zata yi aiki tare damu, tana sha'awar kasancewa tare da mu, na mata adalci na ɗauketa aiki, sai kuma me? Ta ce tana son ai mata surgery a canza mata kamanni kada ƴaƴanta su gane fuskanta zasu kasheta, haka nai mata surgery na canza mata kamanni, daga karshe ma ta gudu ta baro Washington ta dawo nan da zama, dik na karɓeta saboda girman aikin da ta yi mana, kunsan kwakwalwar Muhammad ba wasa ba, na bata aiki a ƙarƙashin office ɗina dik dan in yabawa ƙoƙarinta, dik ban mata adalci ba?". Hararansa Dr Mark ya yi kafin ya ce. "Ka dai faɗi gaskiya, ba wani dan kayi mata adalci yasa ka ajiyeta a ƙarƙashin office ɗinka, kawai ka ɗauketa ne saboda nufinka a kan ƴaƴa Muhammad, kana son sperm and brain ɗinsu, kuma kasan ita kaɗai zata iya wannan aiki, saboda ita kaɗai tasan ainahin jininsu!". Hararansu shi ma ya yi kafin ya ce. "Dik da haka dai na yi mata adalci"..... "Kai ku bar tuna mana baya, bamu taɓa aiki mai tsananin wahaka ba irin waɗan nan ayyuka guda biyu". Cewar Dr Kamal. "Wani aiki kenan?". Dr James ya tambaya. Dr Kamal ya ce. "Aikin ƙwaƙwalwar Muhammad da kuma aikin ƙwaƙwalwa Namjoon, mun wahala a kan ayyuka biyun nan"....... Kai kawai Dr James ya girgiza alamar wahalar ta zarce ayi magana. WAYE NAMJOON? WANI IRIN AIKIN ƘWAƘWALWA AKA YI MASHI? NASAN KUN GANE WAYE MUHAMMAD KAM AI! WATAU MAHAIFIN SU LION! KENAN A WANNAN HOSPITAL ƊIN AKA CIRE ƘWAƘWALWARSA? LALLAI AKWAI GAGARUMIN MATSALA NA KIN ƘARAWA KUWA!. Kamar yadda suke zaune suke wannan hira cikin nishaɗi da tsokanar juna haka suma su Maya suke zaune suke hira. Bayin ALLAH kansu ya shiga ruɗani ne, sun shiga tsananin tashin hankali na ganin irin aikin da aka sanyasu, wannan document da aka basu su karanta, jerin sunayen chemicals da ake son su zaƙulo su haɗe masu ne, wani chemical ɗin idan sun haɗa shi da wani sai an barsa ya yi sati biyu ya gama tsumuwa sai a sake suba wani. Da farko da suka fara aiki ba su damu sosai ba, sai yanzu da aikin ya yi nisa, suna isa kan manya-manyan chemicals masu haɗari kuma masu tsanani a guba shi ne fa hankulansu ya tashi, sun san idan aka haɗa kaza da kaza ga abin da zai haifar, nan fa suka yi mugun gigita, dik sun sha jinin jikinsi. Sister Maya ta fi tausayi da saurin karaya, cike da tashin hankali ta ce. "Sister Zinta kina ganin me nike gani kuwa? Me kike tinanin zasu yi da wannan abin?"...... Sister Zinta da ta gama shan jinin jikinta ne ta amsa da. "Sister Maya na fara fita a hayyacina ne ko kuwa dai mafarki nike yi? An taɓa haɗa waɗan nan sinadaran waje ɗaya ne? Kisan kai zasu yi ne?". Dogon numfashi sister Maya ta ja kafin ta ce. "Babban tashin hankalina shi ne waɗan nan sinadaran da muƙa haɗa waje guda, kamar Dimethylmercury CHH, kin sani, sinadari ne dake shiga jiki a hankali ba tare da nuna alamu ba, sai daga baya ya haifar da matsalolin fata, kumburi, da raunuka masu wari, kuraje masu fashewa su fitar da jini, amfani da shi yana da matuƙar hatsari!" Ta ja numfashi kafin ta cigaba da cewa. "Ga kuma sinadarin cantharidin CHO, sinadarin da ake samu daga wasu kwari masu haɗari, yana sa kuraje su kumbura su fashe su fitar da ruwa wani lokaci kuma har jini suna yi. Ga kuma sinadarin ricin CHNO, sinadarin dake haddasa kumburi da kuraje masu zafi sosai. Hallau ga arsenic trioxide AsO, sinadarin dake sa mutum jin daɗi rayuwa a farko, amma daga baya yana haddasa cututtuka na fata, kumburi, da kuraje masu wari. Dik da wanna suka sake cewa mu zuba thallium sulfate TlSO a ciki, mugun sinadarin dake haddasa matsalolin fata da kumburi ba tare da an yi saurin gano shi ba". Ta kai karshe tamkar zata yi kuka, dik da basu san me za'ayi da waɗan nan sinadaran ba tabbas sun gigita da haɗawa, suna jin kuma tamkar ba zasu iya cigaba da haɗawa ba. Na ce kun tuna cewa da Dr James

Chapter 42 of 95