Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
jin voice ɗinsa, yana daga kwance saman katafaren bed ɗinsa, ya tada kai da cinyar daddynsa dake mashi tausa, wai kun san yadda daddy yake ji da Noor kuwa? Ɗah namiji ɗaya kamar rai, magajin dik waɗan na kadarori ai kun san dole a ji da shi sosai. Sai wani shagwaɓasa daddy yake yi yana matsa mashi damatsan hannu, wai sun sha tafiya ya gaji. Kawai dai daddy ji dashi yake yi, ba wani gajiya, baya son ko ƙuda ya taɓa mashi ɗan lelensa. Noor wasa-wasa soyayya na son koya mashi wasu ɗabi'u, yana jin kunyar daddy ya jisa yana hira da mace, amma ba zai iya hakura bai kirata ba tin da ta ce ya kirata, shi ne ya ce wa daddy wai abokiyar aikinsa ne, shi kuwa daddy ya ce okey, ya kasa kunne yana jinsu. "Where did you drop your phone na dinga kira baki ɗaga ba?"......... Ɗan shagwaɓe murya ta yi tare da cewa. "Sorry, na barsa a ɗaki ne ni kuma ina waje muna buga snooker"....... Satar kallon daddy ya yi, sai yaga baya kallonsa, ƙasa sosai da murya ya yi kafin ya ce. "You look so beautiful this morning, you melted my heart, since da na shiga plane, I've been thinking about your beauty, your smile, they way you hug my dad, I felt like.......". Kasa karisawa ya yi saboda ɗago ido da ya yi suka haɗa ido da daddy dake kallon ɗan bakinsa, yana magana ne yadda daddy ba zai jisa ba, shi ne daddyn yake karantar ɗan bakin nasa. Turo baki ya ɗan yi tare da cewa. "Daddy stop it nooow, stop looking at me". Ya faɗa yana miƙewa zaune tare da hararan daddyn nasa. Gefe daddy ya koma yana faɗin. "Dole na bar kallonka tin da an samu wacce take melting heart ɗinka"........ Pillow ya ɗauka ya fara kaiwa daddy dukan wasa yana faɗin shi a kyalesa. "Wai ni na kulaka ne? Na kyaleka ai". Daddy ya faɗa. Kwanciya ya koma ya yi tare da ɗaura pillow ɗaya a wajen bakinsa wai dan ma kada daddy ya karanci lips ɗinsa....... Shi dai daddy gefe ya koma yana jiran a gama wayar yau dole a faɗa mashi budurwa ce ko abokiyar aiki?. "My heartbeat daddy kake wa haka ko?". V da gabaɗaya kalamansa na ɗazun suka gama tsumata ne ta faɗi hakan, ta ji daɗin yadda ya ce ta yi kyau yau da safen nan, abin ya yi mugun sanya zuciyarta ya yi fari. Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Daddy ne yake tsokanana dai". Nisawa ta ɗan yi kafin ta ce. "Daddy yana sonka sosai". Tarar numfashinta ya yi da cewa. "Over to over ma kuwa, fiye da kansa"....... Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa. "Mu yi video call?"...... Wurga dara-daran eyes ɗinsa a kan daddy ya yi kafin ya amsa da. "Later after daddy ya fita". "Okey where's my Auntys?". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "They escort Aunty Luna, tana da meeting a ofishin jam'iyyar da suka tsai da ita takara"..... Sosai V ta yi mamakin jin cewa Luna ƴar siyasa ce, da sauri ta ce. "Dama Aunty Luna babba ce?"...... Tambayar ta so bashi dariya, amma sai ya fiske da cewa. "She's 35 years old, Aunty Lusi 30 years old, then my two sisters da suka mutu, sannan Aunty Lisa 25 years, sai ni". Ya kai karshen maganar tare da kin faɗa mata shekarunsa. Gaskiya ne, Aunty Luna gogagiyar ƴar siyasa ce, daddynta ya bata goyon baya ɗari bisa ɗari, kujerar Gwamna take nema, sannan macece mai son jama'a, saukin kai da tausayawa talakawa, ga kyauta kamar me, har shi daddynsu yana da tsananin kyauta wanda daga garesa suka koya, dik Sunday sai sun bi gidan marayu da gajiyayyu sun raba masu kayan abinci da tsabar kuɗi. Ita kuma Auntu Lusi CEO ce ta SLBANK, babban banki ne sosai. Ita kuwa Aunty Lisa yanzu take degreenta na biyu a fannin lafiya. Kun san shi kuma Noor ina ALLAH ya jefasa ai, so dik yaran daddy Noor suna da abin yi, zakaru ne da ƙasa ke alfahari da su, basu tsaya cewa su mata ne kawai babu abin da zasu iya ba, sun tsaya tsayin daka, sun yi aiki tukuru dan gina gobensu dana iyalansu, sun samu uba wanda ya jajirce a kansu dik da babu uwa!. "To kai shekarunka nawa?". V ta tambaya cikin zolaya. "Kamar naki suke". Ya bata amsa yana mai da kallonsa a kan daddy. Kukan shagwaɓa ta sanya mashi kan lallai ya faɗa mata shekarunsa, to yaro yana cikin shauƙin sabuwar soyayya ina zai so ɓacin ranta, sai kawai ya amsa mata da. "23 nike da shi". Tana turo baki ta amsa da. "Wow". Kafin ta sake cewa. "Meyasa ka sumbaceni da safe?"....... Yana satar kallon daddy kaman wani mara gaskiya ya ce. "Bcos you look so beautiful"....... Jujjuya eyes ɗinta ta yi kafin ta ce. "Iya shikenan?". Shiru ya ɗan yi, can ya ce. "No, but zamu yi magana leter"....... Kukan shagwaɓa ta sanya mashi tare da cewa. "Ni ban yarda ba, sai ka faɗa mun yanzu". Da sauri ya amsa mata da. "Okey stop crying, a daina melting heart ɗina da wannan shagwaɓa, faɗa mun meyasa daren jiya kika gudu dan kawai na tare maki hanya kada motoci su haskaki?". Tana turo baki game da shessheƙa ta amsa da. "Saboda ka sanya na kwanta a kirjinka mana, dik ka rikitani"...... Can ƙasa a takaice ya ce. "To kirjina ba naki bane?"......... Ai ji ta yi tamkar ta fasa ihu saboda daɗi, amma ta daure wajen rike kanta, murmushi yasa bakinta yaki rufuwa, sai da ta sanya hannunta ɗaya ta toshe ɗan bakin nata tare da lafewa a jikin kujerar tana sauke ajiyar zuciya. Shi kuwa saboda tsabar daɗin soyayya bai san time da ya zame pillow ɗin ba, ya mirgina ya dawo jikin daddy yana faɗin. "Ya kika yi shiru? Ko ba naki bane?". Ai kara kashe murya da haɗaɗɗen shagwaɓarta ta yi wajen cewa. "Da gaske ka mallaka mun kanka?"..... "Ko baki so ne?". Ai har tana tuntuɓen harshe wajen amsawa da tana so. One side smile ya sake tare da kamo kyawawan yatsun daddy yana murzasu cikin wani irin jin daɗi, take ya shiga romantic mood, ya manta da cewa daddynsa ya rike ba ita ba, da hira ta yi daɗi ma har da zura yatsun daddy a bakinsa yana biyewa V. Kun san yarinyar da iya soyayya, tuni tasa ya susuce mata, ya dinga zuba kalaman da bai san ya iya su bama, idan ta sa mashi wani shagwaɓa gagara rike kansa yake yi, sai ya juya ya kifa a saman bed ɗin, still kansa na saman laps na daddy yana ɗan ciza yatsun daddyn da ya zura a baki. Ai shi dai daddy baki ya sake yana kallon ɗan nasa, gabaɗaya ya gama goge mashi hadda ɗan ƙaniya. Sun ɗauki good 1h suna hiran nan kafin ta katse kiran saboda su Arya dake faɗa, Arya da Angelina ke ta faman faɗa tin na ɗazun, Angelina ta bi Arya wajen pool suka cigaba, shi ne ta ce mashi tana zuwa ya bata 10 mins, dan zuciyarta ba zata iya juran faɗarsu ba, kada ku manta zuciyoyinsu a haɗe yake, tana jin tsananin zafin abin da suke yi, dik hankalinta ya koma kansu. Tana katse kiran ya ɗauki 10 mins kafin ya dawo cikin hayyacinsa da kyau, slowly ya ɗago da kallonsa a kan daddy, sai yanzu ya tuna suna a tare ashe. Da sauri ya zabura ya miƙe zaune yana ɗan rarraba dara-daran European eyes ɗinsa a kan daddyn nasa. Sai kuma ya ce. "Daddy seriously it's not what you're thinking, she's my friend". "Ni na tambayeka ne? Ko ka ji na ce ba friend ɗinka ba ce?"........ Shiru ya ɗan yi tare da fara shafa curly hair ɗinsa yana son tuna kalaman da ya dinga faɗawa V, watau ya gane me ya faɗa ko da ace daddy ya ji ma yasan ta ina zai ɓullowa lamarin. Can ya tuna ya ce mata kayan da ta sanya da safen nan yasa ya ga komai nata yadda yakamata, kuma ta yi daidai da irin zaɓinsa. Da sauri yasa hannu ya toshe ɗan bakinsa, sai kuma ya ɗan ɗaga jera guda, kashe mashi ido ɗaya daddy ya yi tare da cewa. "Dik abin da ka faɗa na ji, okey dama boy kana da irin macen da kake so ko? Har da cewa breast ɗinta sun yi daidai ko? To zo nan ka faɗa mun waye ya koya maka dikka wannan?". Ya kai karshe yana ƙoƙarin kama kunnen Noor. Ai a miliyan Noor ya diro kasan bed ɗin, da gudu ya nufi waje yana faɗin. "Daddy ka iya sa ido, ni kada ka sake dawowa ɗakina, I'm matured now"........ Da gudu shi ma daddy ya diro ya bi bayansa yana faɗin. "Jirani in kamaka sai ka kalli tsabar idona ka faɗa mun kada in sake zuwa ɗakinka saboda ka girma, kuma yau sai ka faɗa mun daga ina ka koyi waɗan nan kalamai kai da kake kullum a ɗaki baka fita sai da ka tafi AZURE! Ko a can ka koyo?". Yana magana yana binsa da gudu. Sama Noor ya yi yana faɗin. "Kada ka wahalar da kanka daddy, ba zaka iya kamani ba, now I am a soja from AZURE, the best army academy in the world"........... "Bari in gwada maka cewa ni kuma tsohon ɗan wrestling ne, kafin ka fara training na rigaka". Daddy ya faɗa yana ɗan haki, while shi Noor ko a jikinsa, da gudun gaske ma ya fito harabar makeken filinsu dake ta sama, a nan garden ɗinsu yake, pool ɗinsu ma a saman yake. Yana shiga garden ɗin ya ɓuya a bayan wasu tsadaddun kujeru yana nunawa Aunty Lisa dake zaune tana waya hannu a kan kada ta bari daddy yasan yana wajen. Tana manne da waya a kunne ta amsa da to, yanzu suka dawo gidan, call ɗin GAT yasa ta zauna a garden ɗin tana amsawa, ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya tana yi mana wasa da hankalin daddy GAT ɗinmu, taki bashi haɗin kai dik da bai fito ya faɗa mata ainahin abin dake ransa ba, ya tambayeta ya school ta ce normal, sai ya ce ya soyayya ta ce ita bata yi, ya ce saboda me, shi ne ta ce mashi ta tsani maza. Hankalinsa ya tashi sosai, ita kuma tana nan tana mashi dariya, dan ta yi alkawarin sai ta wana hankalinsa sosai kafin ta amince mashi dik da cewa ita ma ta fola mashi. Yana zaune a office ɗinsa, ya manna waya a kunne idanunsa a kan tarin takardun zaman da suka yi da result na aikin kowani yanki, dama yana kan dubawa ne ya kirata. A natse ya ce. "Meyasa kika tsani maza kika kuma tsani soyayya?"....... "Saboda ɓata lokaci ne da shirme". Ta bashi amsa cikin halin nuna ko in kula, wai irin ta nuna mashi bata damun nan ba. Ai bai san lokacin da ya ce. "Lallai ina da babban aiki a gaba na". Ba. Sai da ya ji ta ce. "To ka karisar da aikin naka mana daddy, sai mu yi waya wani lokaci". Sarai ta gane nufinsa fa, amma ta yi kamar bata gane ba. "Daughter zaki bani ciwon kai ko?". Ya faɗa yana ciro tissue, gumin dake keto mashi a fuska ya goge tare da jan dogon numfashi, kalamanta suka sanya ya fara haɗa gumi dik da sanyin Ac dake office ɗin. A ransa ya ce bari ki shigo gidana dik zan rama ne, a fili kuma ya tsaya sauraran amsarta....... "Daddy ni kuma zan baka ciwon kai? Me na yi maka my lovely daddy?". Har cikin ransa ya ji daɗin yadda ta ce my lovely daddy, nisawa ya yi tare da furzar da iska mai ɗan ɗumi daga bakinsa, a natse ya ce. "Daughter, soyayya tana da daɗi sosai"....... "Kai daddy ba wani daɗi, dik shirme ne da ɓata lokaci"......... "Da gaske tana da daɗi, ki jarraba". ...... Tana faman guntse dariya ta amsa da. "No daddy, ba wani daɗin, dik wahala ce da ɓata lokaci". "Daughter, ki bani dama zan tabbatar maki da cewa soyayya tana da daɗi, zan koya maki yinta, idan har na koya maki kuma kika ji bata yi maki ba zan yarda da zancenki". Ya faɗa cikin wata iriyar sigar da wane mutum ya iya musawa wannan murya....... Wani irin abu ta ji ya tsaya a zuciyarta, musamman yadda ya yi maganar cikin yanayi na kwantar da hankali, ai sai gabaɗaya ta ji ina, ba zata iya ja ba kuma, da kyar ma ta iya cewa. "Daddy zaka iya jarrabawa, amma ni nasan ba wani daɗin da zan ji". Wani irin daɗi ya ji na wannan amsa tata, a ransa ya ce sai dai in ba hannun soja kika shiga ba, a soyayya ai su ɗin karshe ne, a fili kuma sai ya ce. "For sure zaki ji daɗi, ba dai kin baiwa daddynki dama ba?". Kai ta gyaɗa mashi alamar yeah kafin ta amsa da e. "Zamu yi waya da daddare, daga yau zan fara aikin koyawa babyn daddy soyayya". Ya faɗa yana matso da wasu takardu gabansa. Tana sakin ƙayataccen murmushinta irin na Noor ta amsa da. "To my daddy, ka kula mana da kanka"...... Ya ji daɗin kalamanta, ya amsa da. "Okey babyn daddy"..... Daga haka bata sake cewa komai ba ta katse kiran. A daidai lokacin daddy ya shigo da gudu yana faɗin. "Where's my pleasure?". Kai ta ɗan girgiza game sa cewa. "Bai shigo nan ba". Juyawa daddy ya yi, ya fita da gudu. Yana fita Noor ya fito, zuwa ya yi ya rumgumi Aunty Lisa yana faɗin. "That's my Aunty, the reason why I love you kenan". Ya faɗa tare da manna mata sumbata a kumatu. Ita ma sumbatarsa ta yi, daga nan suka cigaba da hira cike da kulawa game da kaunar juna. -------------------------🔥 SERAPHINA Kwance tashi babu wuya a wajen ALLAH, sun fita daga jss 2 zuwa 3 a yanzu, ta mai da kai kan karatu sosai, bata kula kowa sai Rimsha, a yanzu dik karshen sati Champion yake zuwa wajenta, ya rage daga wata-wata zuwa sati-sati, hakan yasa suka yi mugun sabo, ta saki jiki da shi sosai, idan ma tana da damuwa jira take yi sai ya zo ta faɗa mashi, a yanzu da shi da Rimsha kawai ta yarda, ita ma Rimsha ba koma Seraphina take faɗa mata ba, kuma har yau Rimsha bata san wannan daddyn Seraphina shi ne Uncle Aryan ɗinsu ba. Kamar kullum, sun fito daga room ɗinsu zuwa class, tafe suke a tare cikin natsuwa, Rimsha ita ta rike masu rucksack ɗinsu, saboda Seraphina yau bata jin daɗi, ta tashi da ciwon ciki sosai, dan ma suna Exams ne yasa ta daure zata je class. A tsakanin class ɗinsu da hotel suka haɗu da wani kyakkyawan baturen yaro, yana rike da rucksack ɗinsa zai wuce, ga boys ɗinsa nan a biye da shi, da alama irin yaran nan ne marasa jin magana. Zasu wuce ya ce. "Heyyy come here!". With harsh voice ya yi maganar, hakan yasa ya firgita Seraphina. (Masu cewa Princess dan ALLAH ki dinga saka sunan Seraph complete ya fi daɗi to ga shi ina sakawa, shikenan, kun ji daɗi na saka maku sunan complete? Seraphina.) Da sauri ta riko Rimsha, ita ma Rimsha ɗin tsorata ta yi, hakan yasa cikin ladabi suka je gabansa dan amsa kiran. Cike da gadara yaron ya ce. "Which class are you?". Ya faɗa yana nuna Seraphina da har jikinta ya soma kerma saboda tsoro. "Jss 2". Murya na rawa ta faɗa. Kallon santala-santalan cinyoyinta ya yi kafin ya ce. "You're beautiful". Ya faɗa yana shafa kansa, matashi ne da a ƙallah zai iya kai 18 years haka, ɗan Ss3 ne. Shiru suka yi basu iya amsa mashi ba. Ya ga violet eyes da bai taɓa ganin irinsa ba, gata kamar madara ai dole ya rikice, ba ɗalibai na, Seraphina dik and Rimsha dik da ƙananin shekarunsu harta malamansu sonsu suke yi, kowa yana son abu mai kyau. "Go, I'll come to your class and meet you there". Ya faɗa ba tare da ya jira amsarsu ba ya wuce gaba abinsa. Wucewa suka yi suka nufi assembly hall. In a coll way Seraphina ta ce. "Jiya daddyna bai zo ba, da zan faɗa mashi cewa cikina ya dinga ciwo tin shekaran jiya". A shagwaɓe ta faɗa. Rimsha zata yi magana daga bayansu muryan Madam Rohisha ya katsesu da cewa. "Seraphina, your daddy is here, go and meet him in my office". Wani irin murmushi Seraphina ta saki tare da cewa. "Rimsha my dad is here, let me go and meet him". My people ni Star Lady na fara wani hasashe, anya Seraphina ba kanwar Vash bace kuwa? Kada ku manta Abba ya kafa dokar hana soyayya a gidansa, kuma kada ku manta auren haɗi ya yi wa mahaifin Vash da mahaifiyarsa, to ina ga shi kuma mahaifin Vash yana da wacce yake so shiyasa ya aureta ya kaita wani wajen suna soyayya, ku tuna wani abu ɗaya! Meyasa daddyn Seraphina bai zauna da su ba? Baya yarda a gansa tare da Dr, and dik yadda aka yi kunga Champion ya santa, Dr Aryan kanin daddyn Vash ne, idan kuka buga lissafin zaku ga wani amsa fa, ko shiyasa hankalin Champion ya tashi a lokacin da ta ce ita ƴar Dr ce? Kenan yasan yayansa ya yi auren sirri? Kenan yasan Dr? Kenan shi ne wanda Dr take cewa kanin baban Seraphina wanda shi kaɗai ta yarda da shi? Kunga kenan alama ya nuna tasan sauran danginsa ba zasu karɓeta ba, kila tasan ba'a auren soyayya a family ɗin! Champion kanin daddyn Seraphina ne kenan? Kuma kanin daddyn Rimsha! Kai wannan fa hasashena ne, kowacce ta yi nata, alƙalamina ne kawai yasan me yake ɓoye a duhu, shi kuma zai fito damu haske, dan haka mu je zuwa. Bata jira amsar Rimsha ba ta juya da sauri ta nufi office na madam Rohisha, cikinta na tsananta murɗa mata, amma farincikin jin ya zo yasa bata mai da hankali a kan ciwon cikin nata ba. Da sauri ta shiga office ɗin. Tana ganinsa ta tafi da gudu ta faɗa jikinsa tana sauke ajiyar zuciya. Yana zaune a saman visitor chair, still dai bada ainahin face ɗinsa ya zo ba, kuma yana sanye da nose mask. Rungumeta ya yi, can ƙasa in a cool way ya ce. "I missed you so much my daughter"........ Tamkar zata yi kuka ta ce. "Daddy ina ka je jiya Sunday baka zo ba?".......... "I went to a meeting, that's why i didn't come, is there something wrong?". Ya faɗa ne kawai, amma ba wani meeting, suna can suna tsame gurɓatattu daga cikin masu kyau, kun san sai sun ɗauki shekara suna haɗa bayanai da bincike a kan mutane, idan suka tashi cikin sati guda suke kawar da gurɓatattu a kasashe daban-daban da dama. Kuka ta ɗan sanya mashi tare da rabe jikinta da nasa, ta ɗaga rigar uniform ɗinta tana faɗin. "My stomach hurts to much"........ Da sauri ya ɗaura hannunsa dake fari tas kamar madara a saman cikin nata, yana waro idanunsa a kan face ɗinta sosai ya ce. "What did you eat?". ........ Kai ta fara girgizawa kafin ta ce. "I didn't eat anything apart from our normal food". Take damuwa ya bayyana a tattare da shi, jawota jikinsa gabaɗaya ya yi, ya rungumeta sosai tare da ciro wayansa ya hau kiran Madam Rohisha a kan ta zo ta yi masu jagoranci zuwa hospital na school ɗin, sannan ya gyara mata zama a jikinsa, ta kwantar da kanta a saman buɗaɗɗen kirjinsa dake da faɗi sosai, ya tura hannunsa cikin rigarta saman cikin nata, ya fara karanto mata ya hayyu ya ƙayumu bi rahamatika asta gisu aslili sha'anin kullahu, walatakil illah nafsi ɗarfata aiy, wala ilah hadin minan nas. Idan ya karanta sai ya hura a hannunsa ya shafa mata a ciki. A daidai lokacin........ STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥 ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️ 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A STAR LADY. https://www.facebook.com/share/g/1EUXbqsDjP STEP 1________🔥 2025-11-18.🔥 FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥 E_____________15 Idan ya karanta sai ya hura a hannunsa ya shafa mata a ciki. A daidai lokacin Madam Rohisha ta turo kofar ta shigo. Da sauri ya kalleta, bai san ya iya magana da wuri ba sai da Seraphina bata da lafiya, da sauri ya ce. "Meyasa bata da lafiya baku yi taking ɗinta to the hospital ba?". Da sauri Madam ta kariso cikin tana gyara nose mask na face ɗinta, hannu tasa zata karɓi Seraphina daga jikinsa tana faɗin. "Meyake damunta?"..... Ɗaure fuska sosai Aryan ya yi, with harsh voice ya ce. "Bama ku san abin da yake damunta ba bayan amana aka kawo maku yara, so is that how you're treating our babies?". Ya faɗa yana kankame Seraphina ya hana a ɗauketa. "Sorry sir, ba haka bane, bata faɗa mana bane"........ Tarar numfashinta ya yi da cewa. "Sai ta faɗa maku kenan? Ba aikinku bane kowani lokaci duba lafiya da kula da yara?"....... Shiru Madam ta ɗan yi, sai ta sake cewa. "Sorry sir, we made a big mistake, amma zamu kiyaye gaba, except my apology please". Miƙewa ya yi da Seraphina a jikinsa, ya saɓata a saman shoulder ɗinsa, ba tare da ya sake yin magana ba ya fito daga office ɗin, da sauri Madam ta bi bayansa tana kara bashi hakuri. Bai sake yin magana ba har suka kai wajen motarsa, sannan ya ce ta shiga su je. Ba musu ta shiga, daga nan suka wuce hospital na school ɗin dake a can gefe nesa da side na class ta kusa da hostel. Yana parking ya fito ya ɗauki Seraphina suka wuce ciki. Shi ɗin babban likita ne, amma yana son a gwadata da kyau dan ya tabbatar da abin da yake zargi. Magana Madam ta yi wa malaman asibitin, da gaggawa suka karɓesu tare da basu ɗaki a kan su shiga za'a zo a dubata a ciki, ba musu Aryan ya shiga da ita, Madam ita kaɗai tasan me ta faɗawa malaman asibitin da yasa suka yi saurin karɓansu. A saman bed na majinyata dake ɗakin Aryan ya zauna da ita a jikinsa, ya ɗan sunkuyo da kansa a kanta kaɗan, cikin sanyin murya ya ce. "Har yanzu yana maki ciwo?". Ɗan ɗago face ɗinta ta yi, suka kalli juna ido cikin ido, tamkar zata yi kuka ta ce. "Daddy har yanzu yana mun ciwo"......... Ɗan lumshe idanunsa ya yi tare da sake warosu a kan kyakkyawan face ɗin nata, slowly ya ɗaura hannunsa a saman cikin nata. "Zai daina yanzu In Sha ALLAH". Ya faɗa without removing his hand and he didn't stop looking at her. "Baby kin fara girma fa". Aryan ya faɗa yana ɗan yin ƙasa da eyes ɗinsa daga kallon da yake yi wa face ɗinta izuwa dogon wuyanta........ "No daddy, I'm just 11 years now". ....... "11 years 6 month". Ya faɗa yana mai da kallonsa a kan face ɗinta. "Daddy who told you my real age?". Shiru ya ɗan yi, idanunsa a kan ɗan bakin nan nata mai matuƙar ɗaukar hankali, sai da ya ga ta ɗan motsa lips ɗin nata har gefen kumatunta ya lotsa ne ya ɗan kawar da eyes ɗinsa daga wajen tare da cewa. "I'm the one who give you this name Seraphina, is my choice me and your uncle Zayra'an". Ya faɗa tare da kai ɗayan hannunsa ya ɗan shafi gefen face ɗinta, sai kuma ya tsayar da hannun nasa a saman kumatun nata yana cigaba da kallon face

Chapter 25 of 95