Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yana gabar da project ɗinsa, a abubuwan da ya kirga cutar take haifarwa har da kuraje masu fashewa su yi jini? Nasan yanzu kun gane daga wani sinadari aka samu wannan, sannan ya ce ciwon yana shiga ne a hankali, yana ɓuya na sati biyu kafin ya bayyana a jiki, kenan kunga irin sinadaran da aka zuba mashi yasa zai ɓuya a jiki na tsawon sati biyu, lallai akwai matsala, mu leƙa CRYSTAL PALACE mu dawo. CRYSTAL PALACE. Shirye suke cikin tsadaddun tail coat masu bala'in kyau launin dark blue watau navy da ya yi masifar fito da tsantsar kyansu, ku hasko fararen fata a cikin navy blue ya zasu kasance?. Musamman Aryan and Lion da suka cire face mask ɗin fuskansu a yau suna karisa shiryawa, barema Lion da ya fito daga Pamira blood, hasken irin pure white ɗin nan ne mai balain kyau. Ya ilahi, tamkar ka samu waje ka zauna ne ka yi ta faman kallonsu kawai kada ka ɗauke idanu, idan kuka kalli lips ɗin Lion oooooo, ya ALLAH, zaku zaci ya sanya pink janbaki ne, ya ciza kala sosai yana wani irin kyalli, hakama lips na Aryan, bakin Lion irin round lips ɗin na ne mai masifar kyau, ga shi ɗan karami, lipa ɗinsa suna da ɗan cika daidai masha ALLAH. This two guy complete face ɗinsu ya haɗu, ga sexy gorgeous body, a gaskiya Lion yana kama da Leo sosai, kamar an tsaga kara, hatta hair ɗinsu golden white dake ta faman sheƙi kamar gold idan ya ji gyara, ya ALLAH, na sake cewa ya ALLAH. Na Lion ya sha kitso kalba a wajen Aryan, ya ɗaure mashi gashin nasa yai mashi tuntu da jelar, kitson tai masifar kara mashi kyau na gasken-gaske. Shi kuwa Aryan arabs hair garesa, kada ku manta shi bakuraishe ne, gashinsa irin dark blue ɗin nan mai sheki wanda zaku zaci ma baki ne in baku kallah sosai ba, gashin ɗan daidai ne a kan nasa, bata wuci zuwa bayan wuyansa ba, yadda dai gashin larabawa yake, yana kwance luff yana wani irin sheƙi, ga wasu gajeru guda biyu da suka zubo mashi ta gaban goshi sun yi nannaɗa sosai, while na bayan kuma suna kwance kuff sun yi bayan wuyansa. Ya ALLAH idan kuka ga Aryan ko, yadda yai gyaran gashinsa tamkar shararren ɗan soyayya, ga dikkan alamu yana cikin soyayya!. Shi kuwa guru ba zan ce komai a kansa ba saboda yana sanye da nose mask, yana zaune gefen bed rike da waya yana latsawa.......... Bayan Aryan ya bar wajen Seraphina ya fita ne ya wuce office ɗinsu bai je wajen Abba ba, daga office ya dawo gida, ya rufe sim ɗinsa da su Abba suka sani ya buɗe na iya nasa da su Lion, shiyasa Seraphina ke ta faman kiransa number a kashe. Bayan sun kammala shiryawa suka ɗauko haɗaɗɗun nose mask ɗinsu suka sanya, irin nose mask masu rufe har saman hancinsu ɗin nan ne, iya kwayar ido zaku gani, and dikkansu hat suka sanya a kansu dan shi ne ya dace da shigar tail coat. Wani irin diamond watch mai bala'in tsadar gaske suka ɗauko iri ɗaya, a tare suka fara sanyawa a hannunsu, sai dai su sun kammala sanyawa na Lion kuma ya zame ya faɗi ƙasa a ƙoƙarinsa na gyara botirin tail coat ɗinsa na wajen hannu dake ƙoƙarin fita. Duƙawa Aryan ya yi ya ɗauko agogon, sai wani irin kyalli take yi. Tamkar jiya basu doka faɗa kamar zasu kashe juna ba, haka ya kama hannun Lion ya zura mashi agogon tare da sanya mashi maɓallanta, sun yi masifar kyau, suka ɗauko half covers shoes suka sanya a kafafunsu launin baki kalar hat ɗin kansu. Sai tashin daddaɗar kamshin perfume na kamfanin su Noor suke yi. A jere suka tsaya a tsakiyar ɗakin kamar wasu guards, guru dake zaune a gefen bed ne ya kwaso masu wayoyinsu wanda dik bala'in mutum ba'a iya bin diddiginsu. A tare suka jera zuwa waje, cikin zafin nama suke taku dake nuna tsantsar jarumta a tattare da su. Cikin tsadadden motar Aryan suka shiga, dan basu cika fita da motar Lion or na guru ba, dayawan lokuta dana Aryan suke fita. Suna fitowa harabar side ɗinsu sai ga wasu jiga-jigan jami'ai guda biyar sun biyo elevator sun sauko zuwa in da suke, ashe a hawan dake ƙasan nasu benen jami'ansu na SSO ne, suna tare da su dan basu tsaro na musamman, sun ki yarda su zauna gida ɗaya da jami'an ne saboda su ne IRON FIST, idan suna tare da su za'a iya samun ɓacin rana saboda jami'an SSO akwai basira. Da yake sune manya cikin hukumar SSO ba ta yadda za'ayi a barsu babu masu basu tsaro shiyasa suka kama masu benen ƙasan nasu dan kada gwamnati ta zargesu. Abin da yasa yanzu ma ba'a zargansu saboda an san su jami'ai ne dake buƙatar sirri na musamman, shiyasa idan suka yi wani abin ba'a zargansu. Dukkansu gidan baya na motar suka shiga, jami'i ɗaya ya shiga driving seat, sauran jami'ai huɗu suka tada mota guda wanda ya kasance nasu ne dama, already suna da motoci guda 3 kasancewar su 12 ne ke tare da su. Yanzu Aryan ne ya ce jami'ai 5 su zo su tafi, shiyasa basu sauƙo su dikka ba, and dikka jami'an suna sanye da black suit, sun saje da guards dan ɓadda kama. Aryan ya umarcesu da su wuce da su wuce kai tsaye izuwa airport dan ba zasu ta fi da jet ɗinsu dake saman benensu ba, kun san kowani bene a CRYSTAL PALACE a sama kololuwa akwai wajen saukar karamar jet wanda yadawa daga cikin manya a CP ɗin suna da jirgin kansu wanda yake sama a fake, daddyn Noor ma yana da shi, su Lion suna da shi. Kai tsaye airport aka wuce da su, jirgi suka hau sai Washington. Suna dira a Washington jiga-jigan motocin jami'an SSO dake wajen already sun yi wa airport ɗin diran mikiya, ta ko'ina kaki ne ke shawagi, an turo masu sojoji, ƴan sanda, har da fighter jet ta sama dan tabbatar masu da tsaro. Ƴan jaridu sun cike airport ɗin tab, ta ko'ina sai snapping ɗinsu pic's ake yi. Dik kansu kansu a ƙasa a lokacin da suka fito daga cikin jirgin, kowa yana burin samun damar ganin faskokinsu, amma sunki bada dama. Da gudun gaske jami'an SSO suka zo suka yi masu zobe suna sara masu, ga wasu jami'an da suka jera layi tin daga wajen bakin marfin jirgin har izuwa wajen motar da aka tanada masu, rike suke da manya-manyan bindigu waɗan da basa saɓa saiti. Wargima waje yake samu, domin kuwa babu ɗan jaridan da ya iya keto tsakanin jami'an SSO ya isa wajensu Aryan wai ya ce zai masu tambayoyi, sun dai ja gefe suka masu hotuna har suka shige cikin motocin da aka tanada masu. Da gudun gaske jami'an SSO suka shiga nasu motocin suma, a tare aka tada motocin, a jere suka fita airport ɗin suka nufi white house da su, watau fadar shugaban ƙasa. Yau suna da wani zazzafar meeting ne da manya-manyan kakin dake faɗin ƙasar. Sunan wannan meeting ɗin ma National security high command meeting. A secure intelligence & defense operations room na white house za'ayi meeting ɗin. Meeting ɗin zai fara ne da misalin karfe 12:00 AM na dare kenan, zasu kammala karfe 4:00 AM, gab asuba kenan, yanzu kuma 11:30 suka isa airport, daga airport zuwa fadar shugaban ƙasa zai ɗaukesu 20 mins, zasu shiga a kan lokaci kenan. Waɗan da za'ayi meeting ɗin nan da su sun haɗa da shugaban ƙasa, ministan tsaro na ƙasa, CDS watau Chief of Defence Staff, COAS, CNS, CAS, NSA, DG, GOC, FOC, AOC da sauran manya dik zasu hallara. Kowa yasan yadda gidan gwamnatin ke da tsaro da tsari ga haɗuwa, ba sai na tsaya ɓata lokacina wajen yi maki bayani ba. An ƙawata ɗakin taron nan sosai da sosai dan ɗakin yana cikin wani ɓangare na Presidential Villa ne, wall na ɗakin mai tsawon gaske ne, CCTV ta ko'ina, rundunar tsaro ta musamman dake kai komo a arear yadda kuka san cewa idan an barsu zasu iya hana mala'ikan mutuwa ketawa ciki ya ɗauki rai! Babu alamar imani ko wasa a tattare da dik jami'an dake wajen!. Wurin yana da drone surveillance sama da counter sniper system a ko’ina. Ba a amfani da wayoyi ko internet na jama'a, dik hanyar sadarwan wajen tana military grade encrypted satellite line. Su kansu jami'an da za'ayi zaman da su kafin su shiga cikin ɗakin sai da scan na farko, na biyu voice ID da aka shiryawa na'urar already, na uku badge code da ake basu ana saura minti ɗaya meeting. Yanayin tsarin ɗakin meeting ɗin ba'a magana, dan ɗakin round ne ba kamar sauran ɗakuna ba, an yi haka ne kuma dan kowa ya dinga kallon juna. Ga wani haɗaɗɗen tangamemen table launin black oak a tsakiya, an zagaye shi da kujerun masu laushi launin baƙi, kowacce tambarin rundunar ko in ce maku kowacce hukuma kamar soja da Air Force kunga ba ɗaya bane, to kowacce kaki da chair ɗin babban General ɗinta da zai wakilcesu a wajen an manna tambarin kakinsu a jikin kujerar da zai zauna, ga sunan hukumarsu a jikin ɗan karamin signpost a gaban kujerar tasa a saman table ɗin. Sannan a gaban kowani babba na kowani kaki akwai LED screen panel dan nuna bayanan sirri, bayanan sirri suna fitowa daga secure satellite intelligence feeds mafi aka sari. Sannan akwai babban smart board mai 80 inch a ta gaban ɗakin dake ɗauke da taswirar gabaɗaya ƙasar, daga kudancin kasar har arewacin ƙasar. Sannan ga hologram table a tsakiyar table ɗin nasu, wanda ke iya nuna tsarin harin 3D simulation. CCTV da ke ɗakin an saita shi ta yadda ba zai ɗauki sautin komai ba sai dai hoto, an haɗesa da jammer system. His excellency yana da matsayi na farko a kan kujerar farko da aka tanada na musamman, dik da tsananin tsaron dake wajen hakan bai hana kasancewa yana tare da security aide ɗinsa dake tsaye a bayan kujerarsa tamkar sassaken gunki ba. Daga jujerarsa sai na Ministan tsaro, dan haka komai ya kammala, su Aryan na shigowa ɗakin his Excellency ya shigo shi ma, yana shigowa kuma aka kulle kofar babu wanda zai sake shigowa. Wani irin musulmin natsuwa ɗakin taron ya yi, daga nan zaku fahimci manyan kai ne a wajen, kuma zaratan maza ba ƙananan kwari ba. Bayan kowa ya ɗan natsu ya sauke numfashi, masu buƙatar shan ruwa sun sha daga cikin ruwan da aka jera a gaban kowannensu, hankalin kowa ya natsu, sai Ministar ɗin tsaro ya miƙe tsaye tare da gyara mic dake saitin gabansa, a natse ya gabatar da dalilin wannan zama da suke yi dik karshen wata, ya kuma gabatar da buƙata daga office ɗinsa, ya shinfiɗe dikkan rahotonnin da ya tattara daga hannun wasu manyan jami'an ƙasa da kuma wasu ƴan majalisu da dai sauransu. Bayan ya kammala gabatar da komai da shaida ne. Chief of Defence Staff watau CDS wanda shi ne general security strategy, ya miƙe ya kora nasa jawabin, baya ga shi dik Chiefs na Runduna kama daga COAS watau Army, CAS Airforce, CNS Navy, SSO da dai sauransu sai da suka yi nasu jawabin, a jawabin su Lion guru ne ya yi, dan Lion da Aryan basu motsa ba saboda ransu dake jagule, kun san IRON FIST da kaifin ƙwaƙwalwa, tuni sun gano maƙaryatan cikinsu, shi ne nan ransy tai mummunar ɓaci, idan suka ce zasu buɗe baki ko zasu motsa a wajen zasu iya tarwatsa komai, shiyasa shirunsu ya fi masu alkhairi. Bayan kowa ya gama bayanan dake a bayyane kowa yasan da su, masu karya sun shararo nasu, sai His Excellency ya buƙaci jami'an sirri na musamman da su bada nasu bayanan, watau irinsu SSO CIA da sauransu, misali kamar a Nigeria ace NSA da DG DSS, kun gane ai?. A wannan karon sai da kowa ya gama gabatar da nasa, sannan SSO sune na karshe, guru zai sake miƙewa ya wakilcesu Lion ya ɗan dakatar da shi ta hanyar ɗaga mashi hannu, sannan ya miƙe tsaye shi da kansa. Ƙara ɗaure fuskar nan tamau ya yi, babu alamar annuri a tattare da shi, gyara mic ɗin gabansa ya yi kafin ya kunnata, a natse ya fara magana kamar haka. "Bisa ga bincike na sirri ya nuna cewa akwai manya daga cikin manyan jami'anmu dake taimakawa ƴan ta'adda, akwai masu basu makamai kuma akwai masu gwada masu hanyar guduwa". Ya ɗan ɗakata ba tare da ya ɗago ya kalli kowa ba, dik a cikinsu babu wanda ya kawo batun cewa akwai masu baiwa ƴan ta'adda makamai da sauransu sai SSO, shiyasa ya miƙe da kansa dan su gansa da kyau, kowa yana jin labarin halinsa dama, sun san ko a cikin SSO ɗin ma su basa ɗaukar raini ko wargi. "Akwai manya dake ɗaukar nauyin ta'addanci ba iya kasar nan kawai ba, harda ketare! Sannan akwai sabbin hare-hare da aka shirya dan ƙaratowar zaɓe saboda maguɗin da kuka shirya, an kuma bada damar shigo da muggan miyagun kwayoyi masu haɗari dan ƴan ta'addan su bugu a ranar zaɓe su yi aiki cikin fitar hayyaci yadda zasu yi kan mai uwa da wabi ga kowa ba tare da tausayi ko tunani ba"........ Kai tsaye ba tare da shakkar kowa ba ya ce. "Harin ma ya shafi harda His Excellency saboda sanin cewa kujerar mulki ba zata kwace daga hannunsa ba saboda adalcinsa! A bisa binciken sirri ya nuna an hayo sabbin ƴan ta'adda bakin haure daga kasashe da dama, kuma dik wannan abin yana faruwa ne a tsakanin manyan jami'ai zuwa ministoci". Babban GAT na sojojin kasar. (Bafa GAT namu na AVARIS ba, kada ku manta to) GAT ɗinsu ne ya ce. "Shaida zaka bada a bayyane ba wai ka tsaya ce mana binciken sirri ba!"....... Yana rufe baki conol lieutenant na Navy ɗinsu ya ce. "Shaida muke son gani, ka bamu shaida.........". Dukkansu cike da shakkarsa suka yi magana, saboda IRON FIST akwai balain kwarjini da cika ido, ga sawa mutane zarra da tsoro, sai ma idan sun kalleka da waɗan nan shaggun idanun nasu masu rikitarwa. Kasa ƙarisa magana Conol ya yi saboda ido da Lion ya wurga mashi, bai san time ɗin da ya haɗiye maganar ba..... "I am speaking, yet the soldiers and the navy officers keep interrupting me! I talk and they talk over me! What kind of disrespect is this?!". Lion ya faɗa yana sauke idanunsa ƙasa saboda ya ga gabaɗaya ya rikita conol yasa sai zufa yake ta faman haɗawa na tsaresa da kallo da ya yi, yasa bawan ALLAH shiga ruɗu da tashin hankali tamkar ba jami'i ba, kun san su fa SSO kowani kaki shakkansu suke ji, ai na faɗa maku matsayinsu da kuma horonsu, musamman su da suka matsayin admirals ai sama suke da sojoji da sauran kaki. Cikin zafin nama GAT and CONOL suka miƙe, at the same time suka sara mashi game da cewa. "Sorry sir"......... Shiru bai yi magana ba, dan yana son zuciyarsa ta ɗan sauƙa ne kafin ya yi magana, watau Lion shi irin mutanen nan ne masu balain saurin fusata, dan dai baya son hargitsa taron nan ne, akwai wani saƙon da yake son isarwa, ba dan haka ba yadda yake da saurin fushin nan da ya jima da kai masu duka sai dai su ji hakwaransu a ƙasa lokacin da suka shiga maganarsa, amma ya daure yana dannar zuciyar kada ya sumar da mutum. Hasbiyallahu waniimal wakil kafa 10 ya maimaita a cikin ransa, take zuciyar ta sanyayya, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cigaba da cewa........ "Dik wasu jami'ai dake da sa hannu a kan ta'addanci, da waɗan da suke tallafawa masu tada zaune tsaye, harda masu sai da makamansu ga ƴan ta'adda dik ku kwana da shirin cewa SSO idanunta na kanku, kuma aikinmu tamkar iska yake, babu wanda yake iya sanin lokacin da aikinmu zai biyo ta kansa, kamar yadda babu wanda yake da sanin lokacin zuwan iska ko guguwa waje!". Ya ɗan dakata saboda baya iya juran dogon magana. Zazzaro idanu sosai suka yi a kansa, Conol a cikin ransa ya ce kai kaga yadda yake magana yasa na ji tamkar naga mutuwa a gabana ne take mun magana!. Sai da ya nisa kafin ya cigaba da cewa. "SSO bata magana biyu, kowa kuma ya shaida!". Yana kai karshe ya koma ya zauna tare da ɗan yin ƙasa da kai tamkar mai tinanin wani abin. Ai kusan duk jami'an dake wajen sun yi mugun shan jinin jikinsu, dayawansu tsoro ya bayyana a kan fuskokinsu, dan kamar yadda ya faɗa ne SSO basu taɓa magana biyu ba, tarihi ma ta shaida. Wani irin daɗi His Excellency ya ji na jin abin da Lion ya faɗa, watau shirin kifar da gwamnatinsa suke yi ta ƙarkashin ƙasa kenan? Lallai kuwa da matsala. Karin wani haske, kunga da His Excellency da su Lion suna da kusanci sosai, Mr President yana mugun kaunarsu sosai da sosai. Wannan tsakanina da ku ne masu karatu, zan faɗa maku abin da su Lion basu sani ba, sun ɗauka kawai Mr President yana sonsu ne saboda jajircewansu a kan aiki kuma suna taimakawa gwamnatinsa, amma a gaskiya ba haka bane, shi ɗin jininsu ne, amma daga su har shi basu san da hakan ba, sun ɗauka shakuwa ce kawai take a tsakaninsu, amma gaba zaku ji wani irin alaƙace a tsakaninsu, shin ɗan uwan waye daga cikinsu, guru ne? Ko Lion? Ko dai Aryan? Mu je dai zuwa. Wani irin musulmin shiru ɗakin taron ya kara yi, sai da Mr President ya yi gyaran murya tare da cewa su cigaba da jawabinsu. COAS ya fara bada rahoton ayyukan sojojin ƙasa a yankunan da ake fama da ƴan ta'adda. CNS ya bada bayanan ragin fashin teku, musamman dilolin kwaya, ya bada rahoton irin jajircewar da suka yi wajen ganin an daina shigo masu da kwaya. Sai dai yana magana yana kallon Lion da ya yi ƙasa da kansa, su Aryan dik sun yi ƙasa da kai, IRON FIST basa son ana kallonsu, saboda kada ma wasu su haddace wani daga cikin halittar fuskansu, kun san su ɗin ruwa biyu ne, sai da ɓoye kai, so sun tsani kallo matuƙa, shiyasa dik in da zasu je kansu a ƙasa. Bayan sun kammala jawabinsu ne aka fito da sabon tsarin zone enforcement protocol dan ƙara inganta tsaron ƙasar. Mr president ya ce a tsananta tsaro sosai, sannan dik jami'an a sabonta masu kayan aiki na zamani da sabbin makamai, aka rubuta takarda, suka tsara komai. Sai da aka gama Mr President ya kalli SSO, a natse ya ce. "Baku bamu naku tsarin ba? Kuma muna buƙatar shawarinku amma baku ce komai ba". Shiru wajen ya yi suna jiran jin ta bakinsu. Amma babu alamar Aryan da Lion zasu motsa, saboda karairayin da wasu daga cikin jami'an nan suka sake shirgawa ya matuƙar kona masu rai, shi ne suke cooling down na temper ɗinsu kada su sanya lahira tai baƙo. Haka dik jami'an nan suka bada ra'ayoyinsu da shawarinsu game da dabarun da suke ganin ya dace abi, amma su dai SSO shiru babu wanda ya ce word. Dole aka kyalesu dan shi Mr President ya san su waye su, dan haka shirunsu shi ne mafi alkhairi ga kowa dake hall ɗin. Bayan gama jin shawarin kowa Mr President ya yanke shawarin da ta dace, sannan ya umarci sabbin matakai. Karfe 4 na asuba daidai suka gama wannan zama, Mr President ya yi wa kowa godiya game da gargaɗi mai karfin gaske, musamman ga ministan tsaro, sannan daga karshe guru ya rufe masu taron da addu'a, dan su Lion kam har yanzu sunƙi ɗago kai bare su sake yin magana. Mr president ne ya fara fita, then su Lion suka rufa mashi baya, kai tsaye cikin gidan suka shiga, dan sun saba, in sun shigo Washington a nan ma suke sauƙa, ba yadda His Excellency bai yi da su ba kan su dawo Washington da zama amma suka ƙi, a New York aka haifesu har suka girma ba zasu iya ƙaura ba. Already suna da room ɗinsu a gidan, dan haka shiryar suka yi tsab bayan sun yi wanka, suka fito zuwa masallacin shigaban kasa dake cikin fadar. Bayan sun yi sallah suka hau hanyar komawa New York, basu sake zama da Mr President ba dik da cewa ya so hakan, ya so su yi zama kan bincken nasu amma ba dama sai kawai ya hakura suka wuce. Tin da suka kama hanyar airport Lion ya kifa kansa da jikin kujerar mota yana wani irin sauke numfashi mai ɗumi. Da farko Aryan ya so sharesa, amma ya ji ba zai iya ba, sai ya matso ya dafa shi tare da tambayansa me yake faruwa?. Tamkar zai haɗiyi zuciya ya mutu, sai da ya yi shirun good 5 mins, har sun fidda ran zai yi magana, sannan in a harsh way ya ce. "Ta ya za'ayi duniya ta gyaru? Ta ko'ina gurɓatattu ne! Son kai, zalunci, cin amana, son duniya, son abin duniya, dik ya cika zuƙatan kowa! A haka ta ya za'ayi duniyar ta gyaru?". Shiru dik suka yi, saboda sun san gaskiya yake faɗe, shegen son duniya ya mayar da kowa azzalumi mara imani. Gudun kada ta kwaɓe masu yasa suka yi shiru suka kyalesa, shi ma shirun ya yi, can kuma ya dunkule hannu ya daki glass na kofar motar sai da ta tarwatse saboda ba dukan wasa yai mata ba, gabaɗaya glass ɗin kuma ta farfasa mashi hannu sai jini jajir ta fara malala, takaici tamkar zai mutu, dik ta in da ya juya azzalumai ne masu son kai, su sha wahala su yi aiki tukuru amma tamkar basa yi saboda yadda zalunci ya cika ko'ina, dole ya fusata, dole ransa ta ɓaci, dole ya daki abin da ya fi glass. Cikin zafa Aryan da guru suka damki hannun nasa, har suna rige-rigen damƙa. Sai dai ina, kwace hannun ya yi tare da sake dunkuleta ya daki jikin marfin motar har sai da ta girgiza, take glass ɗin suka sake natsawa cikin hannunsa, yana wani irin huci tamkar zai kama da wuta, with harsh voice ya ce. "Is better for me to die a kan irin wannan murɗaɗɗen rayuwa, kowa burinsa ya sami duniya, kowa ya manta da ALLAH da ranar tashin alkiyama, kana ƙoƙarin gyara gabas laanannun nan na kwance maka da lalata maka yamma!". Ya kai karshe tare da daddagewa ya buga kansa da jikin marfin motar ta wajen glass da ya fashe ya bar sauran guntu-guntu. Cikin fusata ya sake ɗaga kan nasa zai buga Aryan ya rikesa da karfi yana ƙoƙarin dannansa. Dik glass ɗin ta fashe mashi goshi, abin akwai mugun cin rai da kayan takaici ne, ace jami'an da yakamata ku haɗa kai ku gyara kasar suke da alhakin wasu kaifukan? Dole ya shiga wannan mood ɗin. Wani irin jiri ne ta fara ɗibansa a lokacin da yake ƙoƙarin kwace kansa daga damkar da Aryan ya yi mashi. Rikesa gam Aryan ɗin ya yi jini na ketowa daga gaban goshinsa in da ya buga kan izuwa kan tongue ɗinsa da ya ciza da hakwaransa tamkar zai fasa harshen nasa saboda tsananin takaici. Guru ne ya cewa driver ɗin nasu ya taka motar da gudu sosai tin da sun kusa isa cikin airport. Basu ƙara wani tafiya sosai ba Lion ya ɗauke wuta a jikin Aryan saboda zafin da zuciyansa ta ɗauka, sumewa ya yi, ga zafin da kansa take mashi tamkar zata fashe. Godiya suka yi wa ALLAH da ya sanya ya suma, zasu samu sauki. Shi ma Aryan ɗin dauriyar ce kawai, amma ji yake tamkar yai ta buga kansa a bango kada ya dakata, wannan musifa dame tai kama. To a haka dai suka dawo CRYSTAL PALACE, kai tsaye gida suka koma, Aryan da kansa ya yi treating Lion yadda yakamata, ya gyara mashi gaban goshinsa da hannun nasa, sannan ya bisa da alluran barci na good 5 hours dan ya samu barci, hakan zai sanya ya samu natsuwa kuma zuciyar ta sassauto. Bayan sun tabbatar yana cikin aminci da kariyar UBANGIJI sai suka nufi room dake kusa da

Chapter 43 of 95