Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
amma yana da hanyoyi da dama da yake bi dan gyarawa manya kuskure idan suka yi cikin sauƙi. Da sauri ta ce. "A'a kada ka kirasa yanzu, please ka bari sai anjuma in na koma zan haɗaku, yanzu yana barci ne"..... Ya gama gano akwai matsala, yadda muryarta ke rawa take ƙoƙarin hanasa kiran....... Kai ya jinjina kafin ya ce. "To yanzu dai an gama dubaki ne?". "Am..... In.... To .... Dama likita ne ya ce yana son yin magana da mijina, kuma yayanka yana barci shi ne na kira ka yi magana da shi matsayin yayanka". Ta faɗa murya na rawa.......... Ɗago idanunsa a kan Angelina dake kallonsa ya yi, mamakin Aunty Ummie yasa ya ji kamar ana kiran sunansa a waje, a ransa ya ce faɗa suka yi da Faisal ɗin ne? Menene yakefaruwa da har take son ya yi magana matsayin mijinta? Me yake damunta? Lallai akwai gagarumin matsala. Jin ya yi shiru ne yasa ta ce. "Ba wani abin bane fa, nasan halinka yanzu zaka ɗauka ko wani abin ne"...... Uhm ita da bata yi karatu bane wai take shirin yi mashi wayau, dik da dai ance babba kam babba ne, amma ai ta kwafsa tin a farko, babu rami me ya kawo batun rami da zata ce babu wani abu dan tasan zai ɗauka akwai wani abin, akwai ɗin kenan. Nisawa ya ɗan yi, ya mai da kallonsa kan laptop na Angelina dan ya ga giftawar wani abin ta gaban drone ɗinsu, hannu ya kai saman mouse ɗinta kafin ya ce da Aunty Ummie. "Babu komai, haɗani da likitan, sannan kafin nan faɗa mun meyakefaruwa da Yah Faisal? Please kada ki ɓoye mun". Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta ce. "Gaskiya zan faɗa maka shi ne matsala muka samu da shi, ya dawo gida tin last week ba jiya ba, ya dawo da makudan dukiya, da na tambayi in da ya samesu sai ya ce a haƙar gold yai nasarar samun wani dutse mai daraja ya kai kasuwa, ban yarda da shi ba, na damu sosai, da na tsananta damunsa da tambayar ya faɗa mun gaskiya ina mashi nasiha shi ne ya fara faɗa, ya ce mu koma sabon gidan da ya saya a GRA, na ce ni ba zan koma gidan da ban san da kuɗin me aka saye shi ba, shi ne ya yi ta faɗa wai ina zarginsa, ya ɗauki amaryarsa suka koma can, ni suka barni a tsohon gida wai idan na ga dama in dawo sabon gida in samesu, shi ne takaicin yasa kirjina ya fara ciwo har dai na ɗan kwanta gajerar jinya, yau naga abin yai yawa na zo asibiti". Tin da ta fara magana ya shiga dogon nazari, gabaɗaya ya ji abin yai mashi some how haka. Sai da ta gama jawabi tas, sannan ya ce. "Haɗani da likitan, sannan kada ki koma sabon gidan, ki jira kira daga gareni tukun nan". A takaice ya faɗa....... Kai ta jinjina alamar to, still ya fahimci akwai abin da take ɓoyewa ba iya maganar kenan ba, amma ya gano bakin zare a iya ɗan wannan bayani da ta mashi, dan haka a haɗa shi da likitan bayan sun gaisa ya ce mashi. "Dr ina son sanin me yake damunta". Likita ya hau mashi bayani sosai. "Ta kamu da ciwon zuciya saboda tsananin damuwar da take ɓoyewa a ranta, sannan hawan jini yana gab da kamata, shekarunta sun yi kankanta da damuwar da take tarawa kanta, dole kullum kirjinta ya dinga ciwo sosai"....... Ni kam na ce ba dole ta damu ba, ga rashin haihuwa, ga kishiya, ga bala'in dangin miji, ga ba uwa, ba uba, uncle ɗinta ɗaya tilo gidansa babu daɗin kai ziyara saboda bala'in matarsa, babu ta in da Aunty Ummie ke juyawa ta samu saukin rayuwa face wajen Zaynish kawai, shi kaɗai take kira ta ji daɗi, kishiya ta balbaleta da masifa, ta daketa ta zubar mata da ciki, mijin dake bin bayanta yanzu ya samu abin duniya true color ɗinsa yana shirin bayyana, ya ALLAH, ina ake son wanna baiwa ta tsoma kanta ta ji daɗi ne? Ta ji da zafin rashin haihuwa ne ko damenene?. Bayan likita ya gama mashi bayani Zaynish ya ce. "Na yi tafiya ina nesa, yanzu kai mata dik abin da ya dace, sannan ina son kai mata scanning, ka dubata sosai, idan ka yi scanning ɗin ka duba yanayin karfin ciwon zuciyar tata ya yake, ina jiran ji daga gareka, dik wani kuɗi da za'a kashe ka haɗa mun bill ɗin ka bata ta turo mun". Yana gama magana ya katse kiran, ya kira mai yi mashi canjin kuɗi ya sanar da shi akwai account da zai turo mashi ya saka mashi kuɗi. Mutumin ya ce ba matsala. Angelina dik da bata jin yaren Hausa ta fahimci lallai Zaynish yana cikin tashin hankali da damuwa. Yana ƙoƙarin bin abin da ya gifta ta gaban drone nasu kenan kiran Aunty Ummie ya sake shigowa. Katsewa ya yi ya kirata yana aikin nasa bai dakata ba. Tana ɗauka ta ce. "To na sallameka ne da zaka katse?"....... "Sorry, na bada damar a duba mun ke sosai ne"....... Kai ta jinjina kafin ta ce. "Dik wani ɓoye-ɓoyenka dai na ganoka, yanzu dai ina kanwar tawa take?"......... Cike da mamaki ya ce. "Aunty ban gane ba". "Ina Angelina?". Ta faɗa kai tsaye. Ɗago da dara-daran eyes ɗinsa a kanta ya yi, mamaki yasa ya ɗan kyafta idanunsa sau biyu a kanta, while ita ma shi take kallo, tin da yake bai taɓa karewa fuskanta kallo ba sai yau, ba shakka ya shaida kyakkyawar gaske ce. Ɗauke kallonsa daga kanta ya yi kafin ya ce. "Aunty a ina kika santa kuma?". "Awwwww baka ɓoye mun ba? ALLAH ya dubi rokona ne ya bayyana mun ita, maza bata waya in ji ko kuna tare"..... Slowly ya saukar da waya daga kunnensa ya miƙawa Angelina bayan ya sanya a H-Free, yana ta kallonta mamaki ya hana shi kwakkwarar motsi. Karɓar wayar Angelie ta yi tana wani sunkuyar da kai. "Hello my Aunty". Angelina ta faɗa. Can ya ji Aunty Ummie na dariya kaɗan-kaɗan kafin ta ce. "Fatan kina kula mun da kanina sosai ko?". Ɗagowa Angelie ta yi, ta ɗan saci kallonsa, taga dai ita yake kallo, yasa hannu ya riko haɓarsa yana mamaki, kasa ta yi da kai kafin ta ce. "Sosai Aunty, ina bashi kulawa na musamman". Zazzaro ido Zaynish yai a kanta, a cikin ransa ya yi salati ya kai sau 10, wai tana kula da shi, ko yaushe hakan dik yake faruwa bashi da labari?........ "To Please ki kara kula mun da shi sosai, ya fi zinari daraja, sannan in yai maki abu kada ki yi fushi dashi kin ji? Ki faɗa mun in ɗau maki fansa"..... Aunty Ummie bata son su rasa Angelina dan ma kada su rasa samun haihuwar ƴan 4, shiyasa kullum take faɗa mata idan Zaynish yai mata abu kada ta yi fushi da shi ko ta daina kulasa, ta faɗa mata zata ɗauki mataki. Ai Zaynish kam yanzu kansa ta gama ɗaurewa.......... "Ba zan yi fushi da shi ba Aunty, zan kula sosai"...... Fara'a Aunty Ummie ya ninku, bata da lafiya amma tana dariya saboda son da take yi wa Angelie, ta dinga zuba mata ruwan albarka kafin su yi sallama, bata sake cewa a baiwa Zaynish waya ba ta katse kiran. A ransa ya ce awww saboda wannan ta sake kiransa kenan, lallai ma Aunty Ummie, watau yanzu kishiya zata yi mashi a cikin zuciyarta, mata kenan. Miƙo mashi wayan Angelina ta yi tana ɗan ɗagowa ta saci kallonsa. Bai karɓa ba sai ya ce. "A ina kika san Aunty Ummie?". Ya yi maganar babu wasa a tattare da shi...... Can ƙasa ta ce. "Maso tsuntsu shi ke binsa da jifa ai". Ya jita sarai, amma yai kamar bai ji ba, ya sake tambayarta ina ta san Aunty Ummie. Ɗan turo baki ta yi wanda ya ƙara mata kyau, tana ƴan kame-kame, sai ta ce. "I took her number from your phone, dana ga hotonta ne naga ta mun kyau shi ne na ji ina sonta sosai, shi ne fa na kirata muka gaisa, daga nan ta zama Auntyta nima". Sosai ya ji daɗin kalamanta, musamman yadda ta ce daga nan ta zama Auntynta, amma bai nuna alamar ya ji daɗin ba, sai ya ɗaure fuska game da cewa. "Waye ya baki izinin taɓa mun waya?". "Sorry sir"....... Cikin faɗa ya ce. "Waye ya baki izinin taɓa mun waya i said?!"............. Muryarta na rawa ta ce. "All because of you ne"...... "Because of me?". Ya faɗa yana pointing kansa da yatsa. Ya tamke fuska tamau, babu wasa a tattare da shi........ Kai ta jinjina. "Yes, because of you sir". "How because of me?"......... Ta ɗago ta kallesa, ido cikin ido, babu tsoro kafin ta ce. "Because I love you, and I love those who are close to you, shi ne yasa na kirata, i like her from the button of my heart"......... Ya rabb, kashe mashi baki ta yi, bai taɓa jin kalmar love daga bakin wata daban ba Aunty Ummie ba sai yau, sai ya ji wani iri. Hannu ya miƙa ya karɓi wayansa, ya ɗauke kallonsa daga kanta, ya rasa amsar da zai bata sai ya jawo laptop ɗinta dan su cigaba da aiki. After like 5mins yana nazarinta a cikin ransa sai ya ce. "Shekarunki nawa da har kika san wani abu wai love?". Ya yi maganar ba tare da ya kalli in da take ba. "16 years now, and nasan komai ne because of you, i love you and i love everything about you"....... Bai ɗago ya kalleta ba ya ce. "Don't say this word out again, bana soyayya kuma ba zan yi ba, kada ki sake cewa kina sona!". Ya kai karshe tare da miƙewa ya fito dan shirin yin sallar la'asar. Ita kam ko a jikinta, gargaɗinsa bai shiga kunnenta ba, ta ɗago ta bisa da kallo har ya kurewa ganinta, murmushi ta ɗan yi kafin ta ce. "Sir baka san wacece Angelina ba, wait and see, zaka fara soyayya ne ma babu wanda ya sani, dani kake magana". Ta cigaba da aikinta, ta dinga kewaye da drone ɗinsu a wajen tana tina kalar abin da zata dinga mashi. After some minutes, around 4:30 ya dawo cikin ɗakin. Normal kayansa jeans and t-shirt ya ɗauka ya fito waje, da kallo ta bisa tana tina in sun fara soyayya ita zata dinga saka mashi kaya, dan tasan wanka zai je ya yi ya shirya, ta ɗan yi tagumi tana tinanin irin kulawar da zata bashi. A haka ya dawo ya sameta, ya ce. "Bani drone ɗinki". Ya faɗa ba tare da ya kalli in da take ba. Da sauri ta fito mashi da su guda 10, dama 12 aka basu, ta tura biyu cikin daji. Drone ɗin ya karɓa, ya duba karami a ciki, ya ce ta mashi connecting da laptop ɗinta, ba musu ta yi, tana gamawa ya miƙa mata hannu kan ta bashi drone ɗin, da sauri ta ɗaura hannunta kan nasa tana kallonsa, ta zaci ya miƙo hannu zai kama nata hannun ya miƙar da ita ne, dan tasan in sun haɗa drone ai sakinsa suke yi ya tashi, shi kuma me zai yi da shi da zai karɓa? Shiyasa ta zaci hannunta zata bashi. Ɗago da kallonsa a kanta ya yi. Da sauri ta ɗauke hannunta, tamke fuska tamau ya yi kafin ya ce. "Bani drone ɗin". A hanzarce ta miƙa mashi tana haɗe natsuwanta waje guda....... "Akwai in da zamu je, so expect my call at anytime". Ya kai karshe tare da ɗan satar kallonta, dan yaga tana ƙoƙarin miƙewa. Miƙewa ta yi, ta haɗe natsuwanta kafin ta ce. "Safe journey, and take good care of yourself". Ta haɗe hannayenta tana ɗan jujjuyawa cikin salon soyayya ta faɗa. Bai kalli in da take ba ya juya da sauri ya nufi fita. Gab zai fita muryarta ta katse shi da cewa. "Sir"........... Cak ya tsaya, ya ɗan juyo da kansa ban da jikinsa, fuskanta ya kalla yana jiran jin me kuma. "Don't forget that I love you, kada ka mana wasa da kanka, ka sani ni da Aunty Ummie kana ranmu, ba zamu iya juran wani abin ya sameka ba, ka kula sosai please, good luck in whatever you go to do, I like you and I love you, I can't change that, because it's not something I chose for myself, I will wait until the day you begin to feel for me the same way I feel for you in my heart". Cikin raunin murya ta kai karshe, da ɗan shagwaɓa mai karawa kalaman soyayya armashi ba romantic shagwaɓa ba. Bai yi magana ba, ya juya kawai ya fice da sauri. Da sauri ta biyo bayansa, ta zubawa tafiyar jarumtarsa idanu har sai da ya kurewa ganinta, ta ɗan jingina da jikin tantin tana tina ina ma ace ya yi accepting soyayyarta, ai da ta bashi kyakkyawar kulawa kafin ya tafi wanda har ya je ya dawo ita zai dinga tunawa. To mu sake ɗan komawa baya kaɗan a side nasu Manassa. Da yake yau suka fara aiki a tare, sun wuni suna ɗaki, suna aiki yana tsokanarta, ya ce mata. "Ba wai bana sonki bane, amma akwai dalilin da yasa dole zai daina sonki". Ta tambayesa meyasa baya kulata sosai ne, kuma ya ce yana sonta. Tana aiki tana ɗan turo baki ta ce. "Wani dalili". Sai da ya ɗan faki idanunta ya saki one side smile kafin ya ce. "Saboda a gida an ban mata, ance dole ita zan aura, bani da zaɓi". Jama'a ba sai ga Manasa da ruwan hawaye ba? Da sauri ta ɗago ta kallesa, idanunta suka cicciko tab da kwallah, kirjinta na bugawa da karfi, ta gagara iya yin magana. Ganin haka yasa ya ja hankalinta a kan aiki, ya nemi mantar da ita maganar, amma a cikin ransa ya yi alkawarin hukuntata ta wannan hanya, ba yanzu zai bayyana mata cewa ita yake so ba, sai ya yi wasa da hankalinta da sunan yana da mata a gida kamar yadda ta yi wasa da hankalinsa a kan iya aljana ce. Ai wunin wannan rana dai wanna aiki ta yisa ne kawai, amma bata san me take yi ba, har lokacin da ya zo tafiya, ya shirya ya zo sallamarta bayan sun yi connecting na drone ɗin. A dake ya ce. "Zan je wani waje, wait for my call". Kai kawai ta jinjina taki yin magana, taki ɗagowa ta kallesa. One side smile ya ɗan saki tare da riko hannayenta. "Baki mun fatan in dawo lafiya ba, ko dai kin fasa sona ne?". Cike da sonta ya faɗa...... Tana gab da fashewa da kuka, tana wani irin huci na zuciya a kusa ta ce. "Ba zan taɓa daina sonka ba, amma ai za'a rabani da kai, kawai ka je". Tausayinta ne ya ɗan kama shi, amma ya basar da cewa. "Ba za'a rabamu ba, zan cigaba da rokan Abba ya barni in aureki, so ki kwantar da hankalinki kin ji?". Kai kawai ta jinjina tare da fashe mashi da kukan da take ƙoƙarin rikewa. Kafin ya yi wani yunkurin rarrashi ta faɗo jikinsa, ta rungumesa tightly, tana cigaba da kuka. Ai wani irin jim ya ɗan yi, sai ya ji dik wasu sassa na jikinsa suna amsawa, wani irin yawu ya haɗiya gwad har sai da maƙogwaransa ta yi sama ta sake yin ƙasa, da kyar ya sanya hannu ya rabata da jikinsa. A gurguje ya ɗan rarrasheta, baya son ya tafi ya barta cikin kunci, da suna tare ne ya dinga janta ta tsokana, saboda yana ganinta, amma baya nan gara ya barta cikin farinciki, sai ya ce mata ai zasu shawo kan Abba zai yarda, da wannan kalaman ya yi amfani wajen shawo kanta ta hakura. Sannan yai mata sallama ya fita bayan tantin, to shi ne suka tsaya jiran Noor. To mu koma kan labarinmu. Dikkansu ƴan matansu sun samu damar kallonsu kafin su tafi, amma Arya bata samu daman ganin Leo ba, Noor na zuwa suka kama hanya, babu wanda yasan basa nan sai ƴan matan nasu, suma matan basu san in da zasu je ba, sun dai san sun tafi wani waje kawai. Suna barin wajen waɗannan duwatsu suka kama hanya sai ga wani soja daga cikin sojojinsu ya fito daga bayan wata dutse, yana rufe da fuskansa da nose mask, ba zaka iya gane wanenen bane. Wayan dake hannunsa ya fara daddannawa, jim kaɗan ya kara a kunnena, baka iya gane muryansa sosai saboda nose mask ɗin, ya ce. "Sir sun fita yanzu". Ba'a iya jin me ake cewa a ɗayan ɓangaren, sai kai da sojan ya jinjina game da cewa. "Okey sir". Daga haka ya katse kiran ya gudu ya koma cikin sansani. Su kuwa suka cigaba da tafiya suna tattauna yadda zasu shawo kan wannan gagarumin aiki na gabansu a kan ƴan ta'addar nan. A tsakiyar dokar daji suka yi sallar magrib da ishai, while Unays ya ja sojojinsu sallar a sansani, amma ya yi mamakin ganin su Leo basu fito sallah ba, ya je room ɗinsu basa nan, ya kirasu basu ɗauka ba. Ya tambayi Arya ta ce mashi sun je zagaye a daji ne, zasu dawo anjuma. Ya yarda, dan haka ya jasu sallar magrib da ishai, su kuwa su Leo sun yi tafi mai mugun nisa, har wuraren 8 na safe suka samu damar isa wajen hayakin, nan suka isko wani irin wearing na wutar lantarki mai mugun ban mamaki da karfin tsaro. Amma abinku da renon AZURE cikin karkashin wasu wayoyin yantarki suka kutsa, kun tuna an koya masu horon rarrafe a cikin laka a barrack?. To yau ga ranar amfanin wannan rarrafe, sai da suka yi wa su Arya message kan su kunna laptop ɗinsu, sannan suka kunna bluetooth ɗinsu da already sun yi connecting da laptop ɗinsu Arya a sansani, sannan suka kwanta a ƙasa cikin ciyayi, suka fara rarrafawa ta ƙasan waɗan nan wayoyi. Tsaro mai matuƙar karfin gaske ne a wajen yasa drones ɗinsu Arya suka gagara ketarawa. Sun yi tafiyar good 30mins a rarrafe cikin ciyayi kafin su samu damar ketarawa cikin wajen, ta wannan hanya da suka shigo cike yake da ciyayi matuƙa, basa iya ganin gabansu, har suka kutsa cikin wajen ciyayi ne dogaye da bishiyoyi. Suna samun damar ƙetarawa ciki suka saki drones dake hannayensu, sannan suka taɓa bluetooth na kunnuwansu game da tambayar su Arya shin komai ya tafi daidai?. Matan dik suka amsa masu da e komai daidai kuma suna iya kallon komai sosai. Leo ya ce da Arya. "Start moving the drone zuwa wasu wurare ki duba mana hanya, ki duba mana tsaronsu, su waye a kan hanyarmu kuma me suke tare da shi, wasu irin makamai ne a hannunsu da sauran bayanai na aiki da kika sani". Da okey sir ta amsa, da yake bata samu damar ganin fitansa ba sai ta juyo da drone ɗin ta samu damar kallon kyakkyawan fuskansa cikin helmet ɗinsu ma soji kafin ta juya kan drone ɗin ta fara ƙoƙarin nema masu hanya kenan sai ta ji Leo ya ce. "Oh s***". Jin haka yasa ta juyo da drone ɗinta, me zata gani? Gabaɗaya su Leo kewaye suke, an masu zobe, wasu riƙaƙun mutane da baka iya ganin komai na daga jikinsu ne suka kewayesu da manyan bindigun da suka fi na su Leo ɗin, da alama already sun san da zuwan su Leo wajen, dan ta ko'ina sun kewayesu, sun ɗaura masu bindugu a kai, zasu kai mutum 15 haka, ashe sun ɓuya a cikin ciyayin ne suna jiran shigowarsu, sun yi kwantan ɓauna. Ya rabb, ya sojojin AZURE zasu yi? Captain ya yi gaskiya, a cikin soja akwai maciya amana, dik yadda aka yi akwai sa hannun wasu manya a kamasu, wani soja ne daga sansaninsu ya ci amanarsu? Waye ya bashi aikin? Ya zasu yi kenan? Suna tsaka mai wuya! Ace cikin abokan aikinka ma maciya amana, cikin manyanku maciya amana, ina ake son su sanya ransu? The game is over but over masu waye? AZURES SOLDIERS OR THE GANGSTER'S?. Let's meet in part 2 to see what's going to happen!. -----------------------🔥 WS-HOSPITAL. Tsaye Dr Kamal and Dr James suke a ɗakin da darling yake kwance, Dr Mark bai dawo ba. Dr James ya zubawa darling idanu yana ta kallonsa, mamaki yasa sun gagara kwakwarar motsi. Darling ɗan tahalikin da bai san komai ba, kwance yake a cikin glass ɗin da suka sanya shi, ya ɗage kafafunsa sama yana ta wasa sosai, alamar kyakkyawar lafiya da kuzari sun wanzu a jikinsa, fatar jikinsa ta canza ta koma ta ainahinta, sai dai kurajen nan ne da suka fito mashi ne suka ke nan, amma lafiya kam ya sameta matuƙa, ƙurajen ma sun fara raguwa, ruwan cikinsu na bushewa. Lamarin da ya gigita 3D kenan, ya rabb, ta ya aka yi darling ya samu lafiya? Dr James ya yi iya dube-dubensa bai samu wani dalili ba, sai dai yana zargin kamar akwai wanda yai mashi alluran maganin cutar NEXAPOX-31 ɗin nan, domin da ya binciki jinin darling ta na'ura ya gano akwai sinadarin da ta keta cikin jininsa kwanaki biyu baya! Dik yadda aka yi akwai abin da ya saɓa. To waye yai mashi alluran maganin? Waye ya kirkiri maganin bayan shi kansa wanda ya kirkiri cutar bai gama haɗa maganinta ba, yanzu ake ƙoƙarin haɗata, wani mai basirar ne ya rigasa haɗa maganinta?. Jama'a waye kuke tinanin ya ceci ran darling? Waye yai mashi alluran maganin cutar nan? How? Ta yaya? Yaushe? Waye kuma a ina? Ni kaina na kiɗime da ganin wannan abin, akwai dai abin da ya saɓa! Ko dai a cikin 3D ɗin ne ɗaya imani ta shigesa ya ga ba zai iya barin darling a cikin wannan cuta ba sai ya bashi maganin? Wani bawan ALLAH ne yai wannan aiki? Ga project na kwarin nan da suka jima suna yi IRON FIST sun kama container, ga kuma darling ya samu sauki, kuna tinanin zasu yi shiru ne?. Jama'a su waye WORLD SYSTEM dake ɗaukar nauyin 3D suna shuka fasadinsu a bayan ƙasa? Su waye ainahin IRON FIST dake ƙoƙarin cetan duniya daga musifun WS, shin WS mutane ne ko kuma dai na'urorin ne dake juya duniya? Idan mutane ne a ina suke? Su waye su? Me makomar DOL? Zasu kwaci kansu ko za'a kashesu? Ga Lazy ga IRON FIST! Shin IRON FIST zasu bayyana wa duniya? Idan suka bayyana me makomarsu? Seraphina, Aryan, Rimsha, ya zata kaya? Me a cikin containers da IRON FIST suka kama? Me ake yi da ɓargon jariran nan? Mun ji abin da ake yi da jininsu, me ake yi da ɓargo da ƙashinsu? Wasu irin magunguna ake mana gaurayensu? Menene maganin cutar NEXAPOX-31? Nasan zaku so ganin yadda 3D zasu haɗa maganin ko dan ku ajiye saboda tsaro.Tambayoyin suna da mugun yawa, amma alƙalamina zai amsa maku komai. Jama'a labarin yanzu zai fara, STEP 1 dik sharar fage ce, yanzu zamu shiga ainayin labarin. Gajeriyar note daga gareni zuwa ga readers masu albarka. Kamar yadda na faɗa a littafina na baya a yanzu ma zan sake maku nasiha. Ƴan mata har ma da matan aure, novel ana karanta shi ne dan a ɗauki ilmin da darasin dake ciki kawai, ba dan ki sanyawa kanki samun irin rayuwar dake ciki ba. Dani daku dik mun san hakan ba abu bane mai yiwuwa, meyasa muke yaudarar kanmu? Dik wani luxury life da nike sanyawa a cikin novel ina sanya shi ne kawai dan ƙawata labarin kuma dan ayi nishaɗi ba dan komai ba, na faɗa maku da babban murya irin wannan masifaffen luxury life ɗin, ayi ta zuba kuɗin masifa ba dai a duniya ba, sai a aljanna idan rabbi ya kaimu, ki yi aiki tukuru ki samu aljanna ninkin ba ninkin rayuwar novel zaki samu a can, kada ki yi karatun novel ki yaudari kanki da samun irin wannan rayuwa su yawon ƙasashe da wannan soyayya, ki yi karatun novel dan ki ɗauki darusan dake ciki, ki mai da hankali kan gina lahira ki samu aljanna. Akwai kyawawan maza a gaske fiye dana

Chapter 94 of 95