Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya lura yayan nasa ya fita hayyacinsa, ɓacin rai da shaiɗan sunsa ya manta da waye ma yake magana, an kure zuciyansa ne. Babban abin da yai mashi zafi yadda aka dinga gayawa Abban nasu magana dan kawai ya je neman auren da su sun ce basa so, a yau Abba ya sa Aryan ya ƙara tsanan mata, har ita Seraphina ya ji ta fita mashi a rai, ya ji ya tsaneta. Cikin fushi ya kwace kansa daga Faryan, yana huci ya nufi waje, yana wani irin taku na jarumta, jikinsa har wani girgiza yake yi saboda ɓacin rai. Yana fita ba'a fi 2 mins ba Abba ya yanke jiki ya faɗi tsabar balain zuciya, take numfashinsa ta ɗauke. Ammie kam ta rasa bakin magana, abin ya fi karfinta. Sai da ta ga Abba ya faɗi ne ta kurma ihu wanda ya jawo hankalin su Faryan a kansa. Da gudu suka yi kansa suna ambatan sunansa, sai dai ina, baya motsawa, cikin zafin jini suka ɗaukesa izuwa cikin mota, ba tare da ɓata lokaci ba suka yi CRYSTAL PALACE HOSPITAL da shi. Ammi kuwa zarya ta fara yi a parlon tana addu'ar ALLAH ya yayyafawa wannan musifa ruwa, tasan halin zuciyan Abba sarai, addu'a take mashi ALLAH yasa kada zuciyar ta buga, dan hakan tsab zai iya faruwa a irin fushinsa! Suna shiga CP-HOSPITAL suka nemo nurses suka zo da bed domin a ɗaukesa. Da yake asibitin gabaɗaya kewaye yake da Camera, suna fito da Abba suka ɗaura shi a saman bed ɗin gabaɗaya camerorin dake wajen suka fara ɗaukansa. Lokaci guda jiniyar agajin gaggawa na asibitin ta fara ƙara wanda hakan ya janyo hankalin dik wani likita a kan su duba laptop ɗinsu su ga menene. Suna duba cameras ɗin suka ga Abba a kwance a kan gado. Wani nurse ne ya ce da Harleen wanene wannan? Ya faɗa yana nuna Abba. Harleen ya amsa da. "Muhammad Khaiza'an by name, ya yanke jiki ne ya faɗi.........". Bai iya karisar da maganar ba sakamakon amsakuwar da ya ji a asibitin ya amsa da kiran sunan Muhammad Khaiza'an. Ya ALLAH ai tin daga kan Chief medical directors, medical officers, specialist doctors, obstetricians da bama aikinsu bane sai da suka nufi wajen, su specialized doctors, senior nurse, nurse, laboratory technician, receptionist, cleaners ma baa barsu a baya ba, technicians, health assistants, kai harta manyan securitys dake wajen sai da suka yi gudun tseran cetan ran bin gadan! Tin daga kan hawa na goma consultants suke gangarowa da gudun gaske tamkar ba manyan mutane ba, ai wasunsu ma gani suke elevator bata gudu, dan haka suka biyo escalator wanda ita ma tattaka stair ɗinta bibbiyu uku-uku suke yi suna tsallake wasu, suna gudu suna cin karo da wasu ma na gudun nufar wajen, lamarin da yai mugun gigita dik wanda yake a cikin C-P-H a yau, basu taɓa gani irin wannan tashin hankali ba, sai da suka ga consultants dake hawa na goma dik sun diro ƙasa ne ma suka ƙara gigicewa, yau ba ji da kai, ba tsare ma jama'a hanya idan zasu shiga elevator, da kafafunsu yau dai suka sauƙo. Tambayar da kowa yake yi wa kansa shi ne wanene wannan dattijon da ake gudun cetan rai a kansa? Waye shi da har su Chief medical directors dik suka yo ƙasa a dalilinsa?...... Cikin ƙasa da mintuna goma harabar C-P-H ya cika tam da maikatar lafiya, ai jama'a basu tashi sanin C-P-H tana da balain tarin ma'aikata har haka ba sai yau, watau suna nan kenan?. Sosai Harleen yai mamakin ganin yadda daga kiran sunan Abbansu C-P-H ta rikice har haka, duba yadda ma'aikata suka rikice daga jin cewa Muhammad Khaizaan ya ɗauke wuta, to ko su da suke ƴaƴansa ai basu yi wannan birkicewa ba. "To waye Abbanmu?" Harleen ya jefi kansa da tambayar da babu mai amsa mashi. Intently ya maido da kallonsa a kan Faryan da gabaɗaya kansa ya kulle shi ma, tambayar kansa shi ɗin ma yake yi waye Abbanmu? TASHIN SENSE shekarunsu almost 31 a duniya amma wai suke tambayar kansu wanenen ma mahaifinsu tukun nan!. Slowly Faryan ya kallesa, kamar baya son motsa bakinsa ya ce. "Harleen, I am completely confused, don't you think Abba is the owner of this C-P-H? Coz bana jin ko mamallakin wajen ma zasu yi wannan rikicewa a kansa"...... "Faryan, I think more than that, kasan CRYSTAL PALACE HOSPITAL mamallakin CRYSTAL PALACE ne ai, ba yadda za'ayi Abba ya mallaki C-H-P kawai, dole sai in C-P mallakinsa ne". "If that should be the case we have to think more than that". Cewar Faryan ........ Jinjina kai Harleen ya yi. Silent for almost 2 mins ne ya biyo baya kafin Harleen ya ce. "Faryan your words have the scent of truth! Ban taɓa ganin Abba ya biya kuɗin hayan gidanmu ba, in short Abba bashi da C-P note-B, ban taɓa gani ba, dole akwai abin da ya saɓa, Abba has hidden many things from us, and If that's the case, we should start investigating now". Suna nan suna zancen tuhume-tuhumensu an shigar da Muhammad Khaiza'an special ɗakin, bama su san wani ɗaki aka shiga da shi ba, saboda suna can suna tinani. Sai da suka farga babu kowa a wajen ne suka fara neman ina aka kai Abban kuma?. Ni ma na ce ina aka kaisa? Zaku sani ne, ba kuna nan kuna surutan banzanku ba, ga shi an yi gaba da shi. Likes comments and share fisabilillah. STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥 For more information 08161390581 Whatsapp me only. ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️ 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A STAR LADY. For more information 08161390581 Whatsapp me only. STEP 1🔥 2025-12-10.🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E_____________ 46 Afkawa cikin hospital ɗin suka yi suka fara nemansa, Harleen ya ɗaga waya zai kira Aryan Faryan ya dakatar da shi, cike da tashin hankali ya ce. "Yah Aryan ba zai ɗauki kiran kowa ba, a yadda ya bar gida a fusace ba zai waiwayemu yanzu ba, ka kyalesa kawai, kuma Abba yana jin haushinsa, idan ya zo faɗa zasu sake yi, kasan halinsu ai, dik sai zuciyar balai, gara ka kyalesa, dan Abba zai ce sai Yah Aryan ya bashi hakuri, shi kuma kasan abin da ba za taɓa yi ba kenan". Tarar numfashinsa Harleen yai da cewa. "Ban san me ainahin matsalar Abba da Yah Aryan ba, Abba fushi Yah Aryan zuciyar balai da kafiya, Abba ya ce sai Yah Aryan ya ce mashi sorry, shi kuma ya ce da ya ce sorry gwara a kashesa, kai wannan balai dayawa take, ni nama rasa me zan ce da Abba, ka dubi faɗar da suka yi kwanaki, sai da Yah Aryan ya fi 1 year bai tako gida ba, dan kawai Abba ya ce sai ya bashi hakuri, sai da Ammie ta dinga rokon Abba, kai ni wlh wani lokaci suna jefani cikin tashin hankali da kaɗawar zuciya". Faryan ya ce. "Babu ranar sassautuwar al'amurra, dan ni banga ranar ba, ka yi duba da yadda Yah Aryan yake mana, ai exactly yadda Abba yake ne a lokacin da yake matashi kamar yadda Ammie ta faɗa mana, kaga kuwa gyaruwan wannan al'amari sai wani ikon ALLAH". Harleen ya ce. "Ɗan nagada kuma ya fi ɗan na koya ba, ai Yah Aryan ma ya fi Abba zafin zuciya, ALLAH dai ya shirya mana shi, amma ni ina ganin idan ya yi aure zai canza"...... Ɗan zaro ido Faryan ya yi, sai kuma ya ɗan saki one side smiling kafin ya ce. "Kuma kana da gaskiya, Abba da yai aure ai ya canza, auren ya ɗan sassautasa, da a baya kafin ya yi aure ne ai Yah Aryan bai isa ya dinga mashi wasu abubuwan ba, amma yanzu Alhamllh Ammie ta sassauta mana zuciyar Abba". Mood na Harleen ne ya ɗan canza, da kyar ya iya cewa. "Ammie ta canza Abba ko kuma Ummie?"........ Shiru Faryan yai bai sake yin magana ba, da alama an taɓo chapter ɗin da baya so ko kuma chapter da tafi karfinsa. Cigaba da zarya suka yi a kofar da suke tinanin nan aka sanya Abba duba da cikan gomannin nurses da manyan likitoci a wajen, sai kai komo ake yi. Dik wani likita dake asibitin a yau yana wannan ɗakin, sun bar duba kowa, sun tashi daga kan kowa, dik sun gudo izuwa wajen Abba........ Harleen yana tsaye a wajen sai ga wani babban Dr ya fito, cikin girmamawa ya ce. "Who's Faryan and Harleen?". Suna kallonsa suka amsa da su ne. "Sir Muhammad Khaiza'an need you inside"........ Alhamdllh suka furta a tare kafin su wuce su ƙarisa ciki, Harleen ne ya fara wucewa, shi kuma Faryan ya rike hannun Dr game da cewa. "Dr a ina kasan Abba? And me yake damunsa? Ya aka yi ka dubasa ba tare da mun buɗe mashi file ba, ba CP note-B da kowa yake da shi a hospital ɗin nan, bamu zo da nasa ba saboda tashin hankali da muka shiga, mun manta a gida, amma kuka dubasa?". Dr yana murmushi kafin ya ce. "Dik wanda ya kwana ya tashi a wannan hospital ɗin matsayinsa na ma'aikaci hakika yasan waye Muhammad Khaiza'an, ai shi ya wuci sai ya zo da note ɗinsa zamu duba shi, wajibi ne a kanmu mu duba shi, batu na file kuma ina ga tin bai haifeka ba yake da shi a nan".......... Cike da mamaki Faryan ya sake cewa. "Ya kake bani labari kamar Abba ne mamallakin CRYSTAL PALACE HOSPITAL?". Girgiza kai Dr ya yi, cike da girmamawa irin wanda suke baiwa dik wanda ya haɗa jini da Muhammad Khaiza'an ya ce. "CRYSTAL PALACE HOSPITAL MALLAKIN CRYSTAL PALACE ne ai, Muhammad Khaiza'an ba shi bane mamallakin CP, but ka tambayesa yana da alaƙa mai karfin gaske da mamallkin wajen, ka yi magana da shi". Kai kawai Faryan ya jinjina tare da wucewa ciki. A zaune a saman special bed na majinya suka isko Abba, ya farfaɗo, ai yadda suka yi tururowar aiki a kansan nan dole ma ya farfaɗo a take. A kusa da shi Faryan ya zauna yana faɗin. "Abba ya jiki?"...... Shiru bai amsa ba, yana tsoron buɗe baki, dan zai iya haɗiyar zuciya, saboda har yanzu yana kan dokin zuciya bai sauƙo ba. Sai da su Faryan suka shafe 30 mins a zaune bai iya ce masu komai ba, daga karshe yai masu alamar su mayar da shi gida. Harleen ne ya fito ya nemi babban Dr, ya ce ga buƙatar Abba, da sauri suka amsa da cewa dik abin da Abba yake so shi suke yi, dan umarninsa suke bi, dan haka dole a su sallame shi. Abin dik ya ɗaurewa su Harleen kai, amma basu yi gigin tambayar Abba komai a yanzu ba, dan sun san ko sun tambaya ba zasu samu amsa ba, yana kan dokin zuciya, sai ya huce. A taƙaice haka suka koma da shi gida, Abba tamkar zuciyarsa zata fashe, ya sha alwashin sai ya yi maganin Aryan a wannan karon, sau uku kenan yanzu Aryan yana mashi irin wannan tsiya, to daga na yau ba zai sake ba, aure kuma tamkar an yi an gama ko zai mutu!! Dan rantsuwa Abba yai da ALLAH ɗaya a wannan sati mai zuwa zai ɗaurawa Aryan auren nan, kuma ya ce wlh in dai Aryan ya musgunawa yarinyar mutane ko ya ɓata mata sai dai ya nemi wani uban ba dai shi ba!! Tashin sense! Lallai akwai balai!!. A ɓangaren shi kuwa Aryan, yana fita gidan Lion ya koma, ya yi mamakin ganin Lion baya gida, shi dai yasan a wannan lokacin Lion baya fita, mafiya yawan lokutan fitan IRON FIST daga 12 na dare ne zuwa 4 na asuba, kada ku manta su SSO ne, jami'an sirri ne, kunga kuwa ba fita zasu dinga yi kasafai suna zuwa office ba, sai muhimmin abu ya taso. Toilet ya wuce, ruwa mai sanyi sosai ya sakarwa kansa tin daga tsakiyar kai, yana son samun saukin halin da yake a ciki. Ya jima ruwan nan na zuba a kansa kafin ya fito sanye da bathrobe fari kal, a lokacin ya ɗan samu sauki a zuciyarsa. A wajen dispenser ɗinsu ya tsaya, sai da ya sha ruwa mai balain sanyi cup 4 sannan ya samu zuciyar ta ɗan yi sanyi. Gado ya haye ba tare da ya sanya kaya ba, daga shi sai bathrobe, dan wani irin jiri ne mai karfi take ɗibansa, yana son kiran Lion ya ji ina ya je a wannan lokaci, amma wani irin kasala da barci sun turnukesa, kafin ya farga barci ta ci karfinsa. Kafin wani ɗan lokaci ya yi barci. ------------------------🔥 Cike da farinciki suka shiga class, class ɗin ya yi mugun haɗuwa, kowacce ɗaliba da chair and table ɗinta, ga AC, dispenser na ruwa, ga cups a jere cikin glass wa ɗalibai, komai tsab-tsab. Zama suka yi a chair dake kusa da juna, tana dai rungume da teddy ɗinta tana murmushi. Dik wani ɗalibi or ɗalibar da ta shigo cikin class ɗin sai ta kalli Seraphina and Rimsha ta sake kallo, yaran sun haɗu fiye da tunani, kowacce student sai ta fara neman su kulla kawance, har maza suka fara yi masu tururuwan zuwa wajensu kullah abota. Su kuwa basu kula kowa ba, suka zauna suna hira, dan warning ɗin daddy Aryan ya shiga kansu. A wannan lokaci Uncle ya shigo hannunsa rike da books da dama. A saman haɗaɗɗen table da aka tanadawa malami Uncle ya shirge littafan hannun nasa kafin ya ɗago ya kalli ɗalibai. Yana ɗagowa suka yi 4 eyes da Seraphina dake ta faman aikin kallonsa, tabbas ta gane da shi suka haɗu a shopping, kuma ta gane shi ne ya taɓa mata jaka ɗazun, idan ta cinka daidai shi ne ya bata teddyn nan dake hannunta. Kyafta mata idanunsa sau biyu yai ganin yadda ta tsare shi da kallo. Lokaci guda ta saki haɗaɗɗen murmushin da bata san ta sake ba, da sauri ta ɗaga teddyn hannunta ta rufe fuska tana cigaba da murmushi. Ƙayataccen murmushi shi ma ya saki tare da zaro book guda ɗaya daga cikin littafan nasa, ya fara rubutu a board da maker dake gefen board ɗin a ajiye. Topic ɗinsu ya rubuta da date kafin ya juyo da kallonsa a kan ɗaliban, dik sun fito da note books ɗinsu, ajiye dik wata shirme ya yi ya fara koyar dasu yadda yakamata, da yake su a kan abin da suke so babu abin da ha zasu iya ba, sai ga shi ya iya koyarwan, kuma bai taɓa yi ba fa, wannan ne karonsa na farko. Bayan ya gama sai ya ce ya basu 5 mins su yi copying na note zai goge board ɗin, da sauri suka fara rubutawa. Kewaye ya fara yi yana duba handwriting ɗinsu, sai yaba masu yake yi, ba laifi sun iya rubutu sosai. A daidai saitin chair ɗin Seraphina ya tsaya, zubawa rubutunta idanu ya yi, sosai ta iya rubutu wanda yasa ya dinga yaba mata. Juyawa yai zai tafi sai ya ajiye mata wani haɗaɗɗen chocolate a kusa da hannunta, ba tare da ya kalli face ɗinta ba ya wuce gaba, ya koma wajen table ɗinsa. A saman chair na malamai ya zauna kafin ya ɗago da kallonsa a kanta. While shi ita ma take kallo, irin kallon nan na Uncle chocolate kuma?. Kashe mata ido ɗaya ya yi wanda ya sanyata sakin murmushi, ta sunkuyar da kai ta cigaba da rubutunta, after ɗan lokaci sai ta ɗago ta saci kallonsa, dik in zata ɗago sai sun haɗa ido, dan ita ya tsare da kallo kawai babu ko kyaftawa. Kallonta ya ɗauke mashi hankali yasa ya wuce 5 mins da ya ɗeba masu, har 10 mins ta kai, sai da Rimsha ta ce. "Done sir"....... Da sauri ya zare kallonsa daga kan Seraphina tare da miƙewa tsaye, ya ce dik su ɗaga pen ɗinsu sama, zai goge board lokaci ya cika, in ma basu gama ba su suka sani. Tamkar zata yi kuka ta ce. "Please sir ka kara mana five mins, ban ƙarisa ba".... Ya ALLAH, ai wani irin spark da zuciyansa ya yi bai san lokacin da ya amsa mata da okey ba. Murmushin da ta sakar mashi gabaɗaya ya yi melting heart ɗinsa, sai ya zauna saman chair yana sakin murmushin shi ma. Yaki sake ɗagowa ya kalleta dan ma kada ta sanya ya manta lokaci. After 5 mins ya ce kowa ya ɗaga pen ɗinsa sama, da sauri suka ɗaga pen ɗinsu alamar dik sun kammala. Share board ɗin ya yi kafin ya sake fara wani rubutun yana bayani. Bayan ya gama rubutu ya sake yi masu bayani da kyau, sannan ya ce 10 mins su yi copy a notebooks ɗinsu. Ya sake komawa saman chair ya zauna, kaman shi ne master na class ɗin nasu. A wannan karon babu wasa, a gaggauce suka yi copy suka kammala. Bayan sun gama ya ce da Seraphina ta zo ta goge board ɗin yana da ga zaune. Kawai so yake ta miƙe ya kara kallonta da kyau. A natse ta miƙe tazo ta ɗauki doster ta goge board ɗin, tin da ta miƙe ya tsareta da idanu har ta zo ta goge ta koma seat ɗinta. Shiru class ɗin yai, ya ce su karanta abin da ya koya masu zuwa break time, haka kuwa aka yi, dik suka buɗe littafansu suka fara karatu. Shi kuma ta ɗauko wayansa yana dubawa, amma fa Seraphina yake kallo ba wayar ba, dan wayar kam ya riketa ne kawai dan kada ƴan aji su zargi wani abin. A haka suka kasance har lokacin tashi break, ana buga break matasan dik suka fara fita waje. Kowa ya fita ya bar Rimsha da Seraphina. Miƙewa Rimsha ta yi tana faɗin bari ta ɗauko lunch box ɗinta, ita kuma Seraphina bag ɗinta ta ɗauko zata buɗe ta fito da kayan cimarta, dan bata zo da lunch box ba, ta ce wa daddy sai next week zata fara zuwa da shi, wai sai ta zo ta ga yanayin makarantar sai ta yanke shawarar zata dinga zuwa da abinci ne ko dai iya small chop ya isheta! Rimsha na fita zuwa in da aka tanada dan ajiye lunch box ya miƙe ya nufi Seraphina dake ƙoƙarin fito da kayan cimarta. A kan chair ɗin dake gaban nata ya zauna tare da miƙa hannu ya ɗauki chocolate da ya ajiye mata ɗazun, ya ɓare ledar, mai ƴaƴa ne, sai ya ciro ɗaya ya kai saitin ɗan bakinta yana faɗin. "Please don't say no, don't say anything". Cikin muryar shagwaɓa ya ɗan faɗa, ashe Noor gadon shagwaɓa ya yi. Muryan nasa ya daki zuciyanta matuƙa, sai ta tsinci kanta da murmusawa kafin ya buɗe baki ya sanya mata a ciki, siririn murmushin da ta ƙara mashi kyau ya yi kafin ya ce. "You're so cutie, jiya na kwana mafarkinki, can you be my girlfriend please?". Ya kai karshe tare da ɗaukar chocolate ɗaya yasa a bakinsa....... Ai gabaɗaya ya goge mata hadda, ya ALLAH, ya haɗu, ta ko'ina, ga iya zallar madarar soyayya, ga salo mai ɗaukar hankali da shagwaɓa, kalamai masu narka zuciya, ya rabb. Miƙewa ya yi, bai jira amsarta ba, ya ɗan sunkuyo kanta kaɗan, tamkar zai yi kissing ɗinta, ta ɗago kai suka kurawa juna idanu, muryanta na rawa tana ɗan kyafta idanu ta ce. "Yeah, why not?". Wani irin musulmin ajiyar zuciya ya sauke tare da sumbatar forehead ɗinta. "I love you". Ya furta tare da miƙewa, ya juya ya nufi chair ɗinsa, bayansa ta bi da kallo tana jin wani irin daɗi a cikin ranta. A daidai lokacin Aisha da Rimsha suka shigo. Saita natsuwarta ta yi tare da karisa fito da small chop ɗinta. A chair ɗin da uncle ya miƙe a kai Aisha ta zauna, ita kuma Rimsha ta jawo chair ɗinta zuwa kusa da Seraphina, ta hau fito da kular abincinta, tin bata gama fitarwa ba kamshi ya buɗe ko'ina a cikin class ɗin, mandi rice ce da ya ji nama da kayan kamshi, sai drinks da Ammie ta haɗa mata, dama ta ce a sanya mata a babban kula saboda tare da Seraphina zasu ci. A natse suka fara cin abincin, Uncle ya zubawa ɗan bakinta idanu tana kara narka mashi zuciya, ya mace a kaunarta. Ita ma dik bayan minti ɗaya sai ta ɗago ya saci kallonsa, ya ALLAH, dik ya narka zuciyar baby cherry ɗin daddy. Bayan sun kammala cin abincin suka tattare komai, suka gyara komai, Rimsha na ɗagowa ta ga Uncle na kallonsu, cike da kunya ta ce. "Sorry Uncle bamu ce ka zo mu ci ba"....... One side smilling ya saki tare da cewa. "Thank you dear". Dik kunya ya kamasu basu ce mashi ya zo su ci ba, a haka aka dawo class suka cigaba da karatu. 1:30 daidai suka tashi school, fitowa suka yi ita da Rimsha, Aisha dake SS1B ma ta fito, su kuma SS1A suke. A ƙasar wata bishiya dake kusa da gate na garden ɗin makarantar suka tsaya. Rimsha ta ce. "Zamu ga waye za'a riga zuwa ɗauka, nasan Uncle Faryan ɗina yana hanya". Ɗago kai Seraphina ta yi da nufin ta yi magana unexpected idanunta suka sauƙa a kansa, yana tsaye a kofar offince da yakasance mallakinsa, ya rungume hannaye a kirji, kallonta kawai yake yi. Suna haɗa idanu ya sakar mata ƙayataccen murmushi, tsintar kanta ta yi da mayar mashi da martanin murmushin. Daidai lokacin motar Faryan ta shararo kan titin wajen, ya gaji da jiransu a parkin lot ya ce bari ya shigo cikin school ya dubata. Rimsha na hangosa ta yi gaggawar nufo motar, yana ganinta shi ma ya kashe tsayar da motar. Kama hannun Seraphina ta yi tare da cewa. "Zo mu je ki gaisa da uncle ɗina kuma husband to be ɗinki"...... Cike da shirirta ta ce. "Husband biyu zan haɗa kenan? Daddy and Uncle Faryan". Suna nufarsa Rimsha ta ce. "A'a ba wani daddy, ki manta da daddyn nan naki please, ni dama bana son shi tin da kika ce ya cika faɗa da sanya dokoki, idan kika bari ya aureki wahala zaki sha, gara ki manta da shi ki so Uncle ɗina, Uncle Faryan zai baki soyayya, zai kula dake, zai maki dik abin da kike so, ga shi Uncle Faryan kyakkyawa kaman mugun Uncle Aryan ɗina, da uncle Aryan ba mugu bane, da yana kula mata da shi zan yi maki fatan ki aura, amma bakin mugu ne, baya kula mata, ALLAH ki so Uncle Faryan yana kama da uncle Aryan, ki shigo cikin zuri'armu, nasan kema zaki so zama cikin familynmu, idan kika auri Uncle Faryan kullum muna tare". Ta kai karshen maganar daidai lokacin da suka isa wajen motar. Hakika kalaman Rimsha sun fara tasiri a ranta, musamman yadda ta ce idan ta auri Uncle Faryan zasu kasance a tare, tana son Rimsha sosai, tana son zama da ita, ko dan su kasance gida ɗaya zata auri Faryan, zasu zama ƴan uwan gaske. Sauƙe glass na motar Faryan yai, a natse ya ce. "Tauraruwa mai haske, kin kara kyau sosai"....... "Good afternoon Uncle Faryan". Ta faɗa a ɗan shagwaɓe tana turo baki....... Idanunsa a kan nata eyes ɗin ya ce. "Afternoon my princess, ya school? Hope komai daidai?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e kafin ta ja baya, Rimsha ta shiga gidan gaba na motar tana murmushi....... "Uncle daddyn Seraphina bai zo ba, ko zamu yi dropping a gida?". Cewar Rimsha. Da sauri ya ce why not, su shigo ya saukesu. Da sauri ita ma Rimsha ta fito ta koma baya, Aisha ta shiga gidan baya, Seraphina ta shigo gidan gaba. Tada motar ya yi suka nufi side ma benen su Seraphina, suna tafiya yana

Chapter 56 of 95