miƙe zata gudu sama dan in baku manta ba bata zama a in da yake. Ai wani irin damka ya yi wa gashin kanta. Yana wuci ya kwashe kafafunta ta faɗi ƙasa.
Kusan a tare su Abba dik suka miƙe, saboda sun san Aryan baya dukan mata, dik tsanar Rimsha da ya yi sai dai tsawa da kora ne yake shiga tsakaninsu ban da batun duka, ko su Faryan dake maza baya dukansu bare mace.
Tana faɗuwa ƙasa yasa kafa ya fara tattaketa. Ihu ta fara yi tana faɗin. "Uncle ka yi hakuri". Baiwar ALLAH dik da bata san laifin da ta yi ba, tana bashi hakuri.
Dik cikin parlon babu wanda ya yi gigin nufarsa bare ya dakatar da shi, sai Abba ne ya yi ta mazan cewa. "Aryan lafiyarka kuwa yau? Ko ka fara shaye-shaye ne?".
Ai ina bai kula kowa ba, kai tsaye ya nufi wajen robar wayar da ta haɗa da switch da ya yi connecting light. Ɓanɓako robar ya yi, da karfi ya fincikosa, ya sanya karfi ya zaro wayar dake ciki, ya tsinkota ya nufo Rimsha. Ai tana ganin ya nufota ta kurma ihu tare da miƙewa, ta watsa da gudu ta yi sama.
Ai da gudun gaske ya bi bayanta, room ɗinta ta shiga har da sanya key. Aikuwa yana zuwa duka ɗaya ya yi wa kofar ya rugujeta. Da gudu ta ruga zata nufi toilet, taku ɗaya ya yi ya damki gashin kanta. Janta ƙasa ya yi, ya take kafafunta yadda ya yiwa Seraphina, tsakaninsa da ALLAH ya fara zuba mata wannan wayar wutan, yadda yake dukanta ma ya ninka na Seraphina sau biyu.
Ba komai yasa ya yi hakan ba kuma face ita Rimsha ai musulma ce, me bata sani ba? Bata san lesbian haramun bane? Bugu da kari ta fi Seraphina shekaru, yakamata ace idan Seraph tana yi ta tsawatar mata ne ma ba ace tare suka san komai ba! Seraph ba musulma bace, amma idan baku manta ba na ce maku Dr Hushaima banbancinta da musulmai rashin sallanta ne kawai, so haka ita ma Seraph, ta iya addu'a, ta iya karanta wasu surorin na Alqur'ani mai girma dik da bata san ma'anarsu ba, kuma tana tsananin kaunar Annabi Muhammad, musamman da mammynta ta faɗa mata cewa Muhammad sunan kakanta ne, ta kara son sunan sosai, kullum tana cewa tana son ganin fiyayyen halitta, saboda mammy ta ce mata sai mutanen kirki masu daraja ne suke ganinsa.
Dan haka Rimsha ta fi Seraphina sanin komai, bai kamata ace ita ta yi wannan abin ba, musamman ita da ta samu tarbiyar uwa watau Ammie, gidan Abba ai gidan tarbiya ce, amma ace ta aikata haka, ai dole ta daku sosai.
Baya ji baya gani dukanta kawai yake yi, unexpected daga bayansa ya ji an rikesa, yau dik rashin imanin Harleen da tsanar da yake yi wa Rimsha sai da ya tausaya mata ya tinkari yayan nasa zai karɓeta, dan shi da yake namiji ma ba iya jure dukan Aryan zai yi ba, suna yara sau ɗaya ya taɓa dukansa har suma ya yi.
Kankame shi Harleen ya yi yana rokonsa da ya kyaleta haka nan ya isa. Ai cikin fushi ya hankaɗe Harleen ya yi baya-baya ya bugu da Abba suka yi baya zasu faɗi Faryan ya tari Abba. A fusace Aryan ya ce. "Dik wanda ya sake matsowa nan sai na kashe shi!". Yana wani irin huci ya faɗa. Ihu Rimsha take yi tamkar maƙoshinta zai fashe, ta daku iya dakuwa ba tare da tasan shin a kan me ma ake jibgarta ba.
Daga bayansa aka rike wayar wutar, a fusace ya juya da sufin kaiwa wanda ya rike ɗin duka. 4 eyes suka yi da Ammie, bata bari ya yi wani motsi ba ta ɗaukesa da wani gigitaccen marin da ya sanya shi ɗan ɗauke wuta....... "Ka haukace ne? Ko wani kwayan kasha? Kasheta zaka yi ne?!"....... Cikin tsawa ta faɗa alamar ranta ya kai kolokuwar ɓaci.
Sake mata wayar ya yi tare da juyawa, cikin fushi ya nufi door, a lokacin Faryan da Harleen sun fita da Abban da numfashinsa yake ƙoƙarin ɗaukewa, su dik a tinaninsu tsanar da Aryan ya yi wa Rimsha yasa yake yi mata wannan duka, shiyasa dik suka tashi hankulansu.
Waje ya fito da sauri har yana haɗawa da gudu tamkar zai tashi sama. Ƙasa ya sauƙo, motarsa ya shiga, da gudu ya tada ya bar gidan, dan in ya tsaya billahil lazi zai iya haɗawa da Ammie ɗin ma.
Kan Rimsha Ammie ta yi, dik ta yi laushi, ko motsin kirki bata yi baiwar ALLAH. Ɗagota Ammie ta yi ta rungume a jikinta, ita ma dik ya farfashe mata jiki da bulala har da jini kamar Seraph. Faryan Ammie ta kira tare da bashi umarnin ya ɗauketa sai hospital da gaggawa. Ai da sauri ya ɗauketa babu ɓata lokaci, dan numfashinta ɗaukewa yake yi ya sake dawowa.
Kai tsaye CPH ya wuce da ita dan a cetota. Ammie kuma ta nufi room ɗin Abba dan su tattauna wannan matsala.
E kam akwai matsala sosai fa. To mu je wajen team DOL, watakila kafin mu dawo su Rimsha sun samu farfaɗowa, ko ita Seraph waye zai kaita asibitin? Ga shi ya rufeta a ɗaki! Ya kuma fita cikin fushi saboda marin da Ammie tai mashi, ko ina ya nufa? Fatana ma kada ya je ya yi haɗari a irin wannan yanayi.
-----------------------------🔥
DOL.
Wasa-wasa kwanaki uku suka shuɗe babu su Lion babu labarinsu, domin kuwa bluetooth da suka sanya ma dan samun infamation ma ya yi disconnected, su Arya sun daina jiyo motsinsu, hakan ba karamin gigitasu ya yi ba, dikkansu sun shiga damuwa, V har da kuka, ita kuwa Arya a fili zaku ga tamkar bata damu ba, amma a cikin zuciyarta da sunan wannan my sterious ɗin nata take wuni take kwana, dik ta damu, ko abinci bata ci, ga wayoginsu a sansanin basu tafi da shi ba.
Arya ce ta fito daga cikin tantinsu sanye cikin uniform ɗinta, fuskarta har ya ɗan rame, bata cin abinci sosai, bata da natsuwa, da daddare kwana take yi manne da laptop ɗinta a kusa da ita, komai ƙanƙantar ƙara ta ji sai ta duba ta ga ko su Leo ne, ga shi a garin musayar wuta sun harbe drone ɗin da ta tura masu. Ta yi ƙoƙarin tura wani amma ta gagara kama ainahin saitin in da suke, yanzu kwanaki uku kenan basu san a wani hali suke a ciki ba.
Dik suna zaune jigum-jigum, Angelina dai ta sanya bluetooth a kunne tana sauraran kiɗa, wani lokaci ta taka rawa, idan ta gaji ta zauna.
Gajiya da zama a cikin ɗaki Arya ta yi, dan tana kara shiga tashin hankali da damuwa ne. Waje ta fito bayan ta ɗauki ɗan karamin pistol da aka basu dan kare kansu. Kai tsaye wajen kogin ranar ta nufa, tana tafiya tana ƴan waige-waige, tana jin kamar alamar motsin wani abin ne a bayanta, tana jin kamar dai ana biyota, idan kuma ta juya sai a ɓuya ne yasa ta fara tafiya slowly.
Sai da ta isa dab kogin, da karfi ta juyo tare da ɗaura hannunta a saman pistol gun ɗin nata, ta yi readyn koma menene ta gani zata harbesa ne. Ga manakinta sai bata ga kowa ba. A matsayinta na jami'a sai ta yi amfani da kwakwalwarta, ta motsa tamkar ta juya tare da rungumo hannayenta a kirji.
Aikuwa tana motsawa kamar ta juya sai ga mai binta a baya ɗin ta bayyana, daga bayan wata bishiya katuwa ta fito. Ai wani irin razana Arya ta yi ganin yarinyar, na faɗa maku yarinyar kyakkyawa ce sosai, ga idanunta manya-manya fafare tas. To yau gashin kanta a watse yake, ya zubo mata ta gaba har baya, kuma gashin nata yana da mugun tsawo, dan ya wuci mazaunanta sosai, kuma yarinya ce ƙarama sosai.
A farko da Arya ta ga motsi a bayan bishiya ana ƙoƙarin fitowa har ta zaro bindigarta, amma ganin yarinyar yasa ta mayar da bindigar bayan ta dawo daidai daga razanar da ta yi. Ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗan kyafta idanunta dan ta tabbatar ba almara bace.
Yau yarinyar yadda kuka san aljana ko mahaukaciya haka ta bayyanar mata. Dik da ta ji tsoron yarinyar, amma hakan bai hanata takawa a hankali ta nufi in da yarinyar take ba. Shiru yarinyar ta tsaya bata motsa ba har Arya ta iso in da take.
Durkusawa a gabanta ta yi tare da riko hannunta, cikin harshen turanci ta tambayeta yau kuma me take so?. Kwace hannunta ta yi tare da nuna mata alamar yunwa take ji, abinci take son ci. Ajiyar zuciya Arya ta sauke, miƙewa ta yi tare da kama hannunta suka nufi wajen sansaninsu.
Ai tana isa da ita wajen da gudu su Angelina suka yi kanta suna faɗin a ina Arya ta samo kyakkyawar yarinya haka? Kamar aljana, V mai kuka tuni ta goge hawayen, a gaban yarinyar ta tsaya, sai kuma ta ce. "Arya wannan yarinyar ta yi kama da commander Nirash, ta wani gefen kuma sai naga kamar Romeo ɗina, kamar suna kama, ko dan ina kewansa ne?".
Angelina ce ta ce. "No da sir Nirash take kama"....... Siririn tsaki Arya ta ja tare da wucewa cikin ɗaki, biscuits da wani ɗan ƙaramin kwalin drink ta ɗauko, bata amsawa kowa ba ta zo ta kama hannun yarinyar, a saman wani dutse da Manassa ta ajiye a wajen kofar tantinsun dan zama ta zauna tare da zaunar da yarinyar a ƙasa.
Biscuits ɗin ta buɗe ta miƙa mata, ai da karfi yarinyar ta kwace biscuit ɗin har sai da Arya ta razana, dannawa a baki ta yi har da laidar tana kara zazzare masu idanu. Dikkansu sun tsorata musamman Manassa da dama bata wani yarda da yarinyar ba. Zuba mata ido suka yi suna kallon yadda take danna biscuit ɗin a baki, da alama yunwa yana neman kasheta ne.
Ganin zata ci har da ledar ne yasa V ta yi gaggawar sanya hannu zata kwace ledar, ja da baya yarinyar ta yi ta hanata tana cigaba da danna shi a baki, ta cika kumatu tap tana kara zaro dara-daran idanunta masu kalar sanyin nan, ita ma jade eyes gareta.
Wani irin damƙa Arya ta kaiwa hannun yarinyar, tana ƙoƙarin kwacewa ta hanata tare da sanya ɗayar hannunta ta zare ledar biscuit ɗin kafin ta saketa. Zabura yarinyar ta yi zata kwace ledar daga hannun Arya, miƙawa V Arya ɗin ta yi tare da cewa ta jefar da shi.
Da sauri V ta miƙe da shi ta je ta jefar ta dawo. Yarinyar tana ƙoƙarin zabura ta bi bayan V sai ta kware ta fara tari. Da sauri Arya ta buɗe drink da ta ɗauko mata, a natse ta kai mata saitin bakinta. Da karfi yarinyar ta kwace ta sanya baki, bata ita sha daidai ba, rabi na zuba a ƙasa rabi na bin bakinta. Ƙoƙarin gyara mata Angelina ta yi, sai dai ina, ta ja da baya dan a tinaninta kwacewa zasu yi.
Arya da bata iya jurar hakan ne ta damketa, ta matseta ta gyara mata. Ai tin da ta kafa baki sai da ta shanye tas sannan ta cire. Mamaki ne ya kamasu, Arya ta ce. "Mu kara maki?". ..... Bata san me suka ce ba, sai kallonsu kawai take yi. Miƙewa V ta yi ta ɗauko mata wani biscuit ɗin.
Yarinyar tana gani ta miƙe ta nufi V zata kwace, ita babu ruwanta da kakin dake jikinsu, bata san wani abu wai soja ba.
Riketa Arya ta yi gam tare da cewa V ta fasa mata biscuit ɗin ta zare ledar........ Wani irin ihu ta kurma saboda rike da Arya ta yi, tana ƙoƙarin kwace kanta, ita dai a barta ta isa ga biscuit ɗin. Arya bata saketa ba sai da V ta fasa mata shi. Ana bata ta hau dannawa a baki.
Ganin haka yasa Arya ta ce su ɗauko mata abincin safenta da bata ci ba, da ruwan sha. Angelina ce ta miƙe ta nufi cikin tantin. Su dai sojojin dake gadinsu suna ta faman kallonsu, suna tsaitsaye tamkar saƙaguna. Angelina ta dawo ɗauke da abincin cikin plate.
Yarinyar tana gani ta zabura ta miƙe, kamata Arya ta yi zata zaunar, ina ai ƙoƙarin kwacewa ta fara yi, ganin haka sai ta saketa dan ta ga gudun ruwanta. Kwace abincin a hannun Angelina ta yi, a tinaninsu zata zauna ta ci ne, sai suka ga akasin haka, domin kuwa tana kwacewa ta juya da gudun gaske ta kutsa cikin daji ta hanyar da suka bi suka zo.
Miƙewa Arya ta yi, da gudu ta rufa mata baya dan ta ga ina zata je, sai dai kuma bata yi taku biyu ba laptop ɗinta dake ɗaki ya fara kara. Ai da gudun gaske ta juyo, su Angelina dik da gudu suka watsa izuwa cikin ɗakin, su kansu sojojin dake tsaronsu da gudu suka nufi cikin ɗakin.
ALLAH sarki abin da suke jira ne kwana uku kenan, watau samun location ɗin su Leo. Da gudu ta isa gaban laptop ɗinta, wani irin zubewa a ƙasa ta yi, hannunta har yana rawa wajen tsayar da alert na laptop ɗin kafin ta shiga kan drone ɗin nata.
Ai tana shiga kai tsaye video ɗin a kan faskan Leo dake tsaye bayan wata katuwar bishiya yana kokarin canza bullet na bindigarsa ta fara nunawa, ga harbin bullet sai sucewa ta gefensa yake yi, da alama musayar wuta suke yi, ALLAH sarki, kwanaki biyar kenan yau da tafiyarsu, sun yi kwana biyu a hanya kafin su kai in da mutanen suke, da isarsu da kwana ɗaya network na wajen ya jagule saboda musayar wuta, a haka Arya ta rasasu har aka harbi drone ɗinta, yanzu wanda ta sake turawa ne suka yi sa'ar ya kama network ɗin.
Ai tsabar farinciki idanun Arya cikowa da kwallah ya yi, su V kuwa rungumar juna da su Angelina suka yi, thank God ba'a kashe masu jami'ai ba dik da basu da tabbaci sauran suna raye ko aa, amma ganin Leo yasa sun ji kamar sauran suna raye.
Da sauri ta shiga drone control ɗin, hannunta har yana kerma sosai. V ce ta ce. "Arya ki bibiyi sauran soldiers ɗinmu muga ko suna raye?". Tamkar zata yi kuka ta faɗa, zuciyarta na harbawa da karfin gaske, tana tsoron wani abu ya sami Noor ɗinta.
Arya na kokarin juya akalar drone ɗin izuwa arear wajen dan ta duba sauran sojijinsu sai gani suka yi Noor ya bayyana a gaban drone ɗin, da karfi ya rungumi Leo suka faɗi ƙasa. Suna faɗuwa bullet ta wuce ta kansu, da gefen wuyan Leo bullet ɗin zata fasa Noor ya cecesa, shi hankalinsa yana can yana ƙoƙarin canza bullet ya zuba sabbi daga waɗan da suke waist ɗinsa a ɗaure.
Ai wani irin yawu da Arya ta haɗiye sai da sautinsa ya bayyana a fili, dikkansu jikinsu tsuma ya fara yi, suna jin ina ma ace suna wajen. Miƙewa Leo ya yi yana faɗin. "Thank you bro". Ya faɗa yana yi wa Noor alamar jinjina da hannunsa.
Noor dake kwance a ƙasa cikin ciyayin dake wajen ne ya miƙawa Leo hannunsa ɗayar da bata rike da bindigarsa, ya shagwaɓe fuska yana faɗin. "Ɗagani"........ Hararansa Leo ya yi tare da cigaba da abin da yake yi na zuba ƴaƴan bullet a cikin bututun bindigarsa. Cigaba da kwanciyarsa Noor ya yi, wai ba zai tashi ba sai Leo ya ɗaga sa.
Watau Noor yana da iya shege, a filin yakin ma sai ya yi. Shagwaɓa ya fara zubawa Leo yana shi dole a ɗagasa.
Leo na ƙoƙarin juyowa zai yi mashi magana sai ganinsa ya yi ya yi wani irin tashi cikin zafa, ya yi tsalle ya taka bishiyar da Leo ke tsaye a jikinta tare da ɗaga hannunsa dake rike da bindiga ya saita ta bayan wuyar Leo ya saki wuta, kan ya faɗi ƙasa ya yi harbi biyar a jere kuma dik sun samu mutanen da ya hara, dan kuwa ƴan ta'adda ne suka ɓuya a cikin ciyayyin wajen, su suka harbo bullet da ya so taɓa Leo Noor ɗin ya cecesa.
A tare suka faɗi ƙasa da waɗan da ya harba ɗin. Sake bajewa ya yi a ƙasa yana mayar da numfashi tare da cewa. "Wayyo my dad, my Juliet, i missed you more". Ya faɗa yana rugumo bindigarsa.
Hararansa Leo ya yi tare da cewa. "Tashi mu bar nan dan ba tsaro, mun shiga sansaninsu dayawa"......... Miƙo mashi hannu Noor ya yi yana faɗin. "Ɗagani, karfina ya kare". A shagwaɓe ya faɗa.
"Zaka tashi ne ko sai na ƙara maka nauyi?". Leo ya faɗa on a serious note. Shagwaɓe fuska ya yi yana turo baki, ya ce sam shi sai dai a ɗagasa bashi da karfi. Leo zai yi magana suka ji motsin a kewayen nasu. Kallon juna suka yi.
V da Arya sun gama haukacewa a zaune gaban laptop ɗin, Arya da yake bata son wasa a wajen aiki sai take jin tamkar ta shaƙo Noor, yana ɓata masu lokaci, a cikin ranta tana cewa in dai wani abin ya samu my sterious to kai ne sila, kuma ba zan barka ba. Ita kuwa V kome Noor zai yi burgeta yake yi, salon yaƙinsu ya gama tsumata, har wani nishaɗi suke bata.
Gera guda Leo ya ɗagawa Noor kafin ya miƙa mashi hannu. Kama hannun nasa Noor ya yi tamkar zai miƙe, Leo ya gama sakin jiki Noor zai miƙe sai ya ji Noor ɗin ya fisgisa da karfin gaske ya tafi gabaɗaya ya faɗo kansa. Take bullet ta wucesu fiw.
Dunkule hannun Leo ya yi ya daki Noor a shoulder, alama ce ta jinjina da sojoji ke wa junansu. A wannan karon a tare suka miƙe cikin zafa, jingina bayansu da jikin juna suka yi, Leo na fuskantar gabas Noor na fuskantar Yamma. Kafin su yi wani yunkuri sai gani suka yi ƴan ta'adda sama da 100 sun yi wa wajen zobe a cikin ciyayyin, kuma kusan dikkansu suna rike da bindigu.
Leo ne ya ce. "Bullet nawa ce a bindigarka?". Can ƙasa ya faɗa yadda babu wanda zai ji. "Jaka ɗaya". Ya bashi amsa. Yana nufin bindigar a cike da bullet ya zo da ita, wanda ya harba guda biyar ɗin nan ne kawai suka fita, dama ya gama sanya bullet ne ya zo wajen. Shi ma Leo kunga yanzu ya zuba sabbin bullet..
"What next?". Noor ya faɗa a hankali. "Fire!!". Leo ya amsa mashi da shi. Haba yana rufe baki suka fara ɓarin wuta, take miyagun suka fara mayar masu da martani, hakan yasa suka rabu suka nemi mafaka, Noor ya ɓuya a bayan wata ƙatuwar bishiyar ɓaure, shi kuma Leo ya kutsa cikin daji. Ɓarin wuta suke babu kama hannun yaro.
Daga bayansa Noor ya ji an saka mashi bindiga a kai, wani ɗan ta'adda ne da fuskansa yake rufe da rawani, ɗana kunamar bindigar ya yi, babu imani ya nufi fasa kan Noor. Sai dai kafin ya harba Leo ya rigasa, wani irin wawan harbi Leo yai mashi a gaban goshi, farat ɗaya tafiya ɗaya kenan. Shege take ya zama mushe.
Ɗago kai Noor ya yi, suka haɗa ido da Leo dake tsaye a bayan wata bishiya da Noor ɗin yake fuskanta. Sara mashi Noor ya yi kafin ya juya suka cigaba da ɓarin wuta. A lokaci guda bullet na bindigarsu ta kare ga ƴan taaddar basu kare ba. Kallon juna suka yi, da ido suka sanarwa da juna bullets ɗinsu ta kare.
Ai su Arya na ganin maganar da suka yi da ido na cewa bullets ɗinsu ya kare dik suka ɗauke wuta, musamman V da ta fashe da kuka ne ma. Ita kuwa Arya dafe saitin kirjinta dake barazanar tarwatsewa ta yi. Ƙoƙarin sanya bullets a bindigar nasu suka yi, sai dai kafin su motsa miyagun sun yi masu zobe, dama sun shigo cikin sansaninsu sosai ne, kwana biyu da suka wuce a waje-waje suke musayar wuta, yau Leo ya ce sai ya matsa gaba, shi ne ya shigo.
Saitasu da bindigu suka yi suna faɗin kada su motsa, sun kewayesu ta ko'ina ba hanyar tsira. Basu da zaɓin da ya wuce dole su ɗaga hannu, kallon juna suka yi, da ido Leo yai wa Noor magana kan ya miƙa kansa. Da farko Noor ya so yin gardama, amma da ya tuna cewa Leo baya abu haka kawai sai ya yarda suka miƙa kansu, suka yi surendar.
Matsawa ƴan ta'addan suka yi, mutum biyu suka kwace bindigun hannun su Leo, sannan suka kwace bullets dake waist ɗinsu, suka haɗesu suka tasa ƙeyarsu kan su wuce izuwa cikin ainahin sansaninsu, sai murna ƴan ta'addan suke yi kan sun kama sojoji, zasu kashesu su ɗauki videon yadda suke kashesu su turawa ƙasa dan a kara tsoronsu.
Arya da V tamkar zasu haɗiyi zuciya, kuka V ta fashe da shi, ita kuwa Arya jikinta har kerma yake yi, idanunta sun kara ciccikowa da kwallah, da sauri ta bar gaban laptop ɗin ta fito waje cikin tsananin tashin hankali. Manassa ce ta biyo bayanta, V kuma ta juya ta faɗo jikin Angelina tare da fashewa da kuka mai tsuna zuciya, tana faɗin shikenan mutuwa zata yi idan aka kashe Romeo ɗinta.
Su kansu sauran sojijin dake wajen suke tsaronsu sun girgiza na ganin an kama su Noor, han kulansu ya tashi. Waje suka yo suma. Ita kuma Angelina ta yi ƙoƙarin control na drone na Arya dan ta duba ina su Zash suke ta ankarar da su an kama su Leo idan hakan zai yiwu, tana rungume da V tana rarrashinta.
----------------------🔥
WS-H.
Dr Kamal ne ya yi wani irin shu'umin murmushi kafin ya ce. "To amma ai in baka son Lazy kana son Zinta kam ko? Kuma nasan kasan tana sonka tin ba yau ba!"......... Wani irin shu'umin one side smilling ya saki kafin ya ce. "Kwarai, shiyasa nike son dawo da ita karkashin office ɗina"........ "Kana son haɗa jini da Muhammad kenan?". Dr Mark ya faɗa.
"Hmmmm". Dr James ya faɗa, like shi kaɗai yasan me yake ransa.
Jama'a bari in ɗan baku ƙaramin surprise a nan kafin mu wuce. Wani abin da baku sani ba a nan shi ne, da Maya da Zinta dik an kyankyashesu ne daga sperm na daddyn Lion, su Dr James suna da sperm ɗinsa da suka mashi tiyata suka ɗeba, kun san ana iya yi wa namiji tiyata a ɗebi sperm ɗinsa ai.
Ana mashi ƙaramar tiyasa a shiga percutaneous epididymal sperm aspiration ɗinsa a ɗebi sperm ɗin. To su Dr James sai da suka san yadda suka yi suka ciro sperm ɗinsa, yanzu haka suna da ragowa sun mashi babban killacewa da matakan tsaro, a cewar Dr James zai kyankyashi matar da zai aura da wannan sperm ɗin, sannan idan ya mallaki matar zai yi mata dashen wannan sperm ɗin da kwayayen haihuwarta domin ta haifo mashi magaji mai kaifin kwakwalwar daddyn Lion wanda zai iya irin aikin da yake yi, shiyasa ya kyankyashi sister Maya and sister Zinta, a cewarsa Zinta matarsa, Maya ma'aikaciyarsa, nan gaba kaɗan zai sauke Lazy, da Maya zai maye gurbinta saboda shi masu basira kawai yake so a kusa da shi. Bai son daƙiƙu!.
Baku yi manakin yadda Maya da Zinta suke da tausayi ba? To daddyn Lion shi ne ubansu, uwarsu kuma sai ALLAH ne kaɗai ya san daga gidan uwar wa Dr James ya kwaso kwayayenta ya haɗa ya kyankyashesu, amma dai koma kwayayen wace mace ya ɗauko ya haɗa da sperm na daddyn Lion tabbas kwayayyen sun kasance special ne, dan tin da ya ce zai kyankyasawa kansa mata da magaji ai kunsan ba zai sanya ordinary eggs ba, dole special zai sanya.
A takaice dai plan na shirta mai karfi yadda zai mallaki Zinta, ya kuma dasa mata sperm na ubanta da eggs ɗinta ta haifa mashi magaji mai basirar daddyn Lion, amma wanna plan ɗin ya ɓoye ko su Dr Mark bai faɗa masu shirinsa ba, ya dai fake masu da cewa zai auri Zinta ne kawai dan tana da kyau, saboda daddyn su Lion kyakkyawa ne, so Zinta da Maya sun fi kiwa kyau a hospital ɗin, bai faɗa masu zai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 45 Chapter of 95