Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wushirya mai bala'in kyau a tsakanin hakwaran. "Guys I really like this guy da ya zo ɗaukarmu a school, tun ranar ya shiga raina, kuma yana mun yanayi da pleasure ɗina shiyasa nike son shi". Cike da shaukin soyayya ta faɗa. Dikkansu sai da gabansu ya faɗi jin ta ce tana son Leo, musamman Arya, da sauri ta ɗago ta kalleta, bata san time da ta ce. "Wancan banzan kike so? Shi yake burgeki?"......... Da sauri ya gyaɗa kai alamar e. Manassa ce ta amsa da. "For sure guy ɗin ya haɗu matuƙa, but meyasa zaki ce kina son shi?". Kirjinta na bugawa ta faɗa. Siririn tsaki Arya ta ja tare da cewa. "Kowacce ta ti focusing a kan abin dake gabanta, ni bana son wannan hiran"......... V tana cigaba da rungume Teddy ɗinta cikin shauki ta ce. "Bloody bani da wani abin dake gabana face tinanin yadda zan sake ganin guy ɗin can, I think weekend zan shiga cikin barrack nemansa". Dikkansu kirjinsu ne ya sake bugawa, Arya bata sake tsoma baki a maganar ba, ta yi shiru ta barsu da Manassa suna yi har time da daddynsu ya dawo, da sauri suka diro kasan bed ɗin suka nufi waje. Har Angelina mai kallan wancan abin sai da ya kashe ta diro da gudu. A parlon ƙasa suka ci karo da shi. Yana ganinsu hannunsa ya buɗe masu cike da tsantsar so da kauna. Da gudu suka tafi suka faɗa jikinsa suna mashi oyoyo, haɗesu ya yi ya rungume, yana jinsu har cikin ransa. Jim kaɗan ya ɗan raba jikinsu tare da kakkamasu suka wuce sama, kai tsaye room ɗinsa ya nufa dasu, sai faɗi yake yi ya yi kewansu, suma sai maimaita mashi suke yi sun yi kewansa. A saman bed ɗinsa suka haye suka zazzauna, shi kuma ya wuce toilet, hira suka fara yi jefi-jefi, Angelina gabaɗaya tana cikin shaukin romance na kallon da ta yi, har tsuma yarinyar nan take yi, while V na cikin shaukin soyayya mai ratsa gangar jiki na tina Leo and Noor da ta yi. Arya na cikin yanayin tinanin Leo da take cewa sai ta ɗauki fansa a kansa, ga shi kuma yasa da suka bar bags ɗinsu a wajen washegari a school suka sha bilala bibbiyu, takaicinsa ya kara rufeta. Manassa na cikin yanayin ko oho. A haka daddynsu ya fito sanye da bathrobe milk color ya samesu. Rige-rigen sauƙowa ƙasa suka yi, kowacce ta nufi closet ɗinsa suna faɗin su zasu zaɓa mashi kayan sakawa. Tsayawa ya yi a gaban mirror ya hau shafa STARS BODY LOTION ɗinsa. Dikkansu suka ɗauko sleeping dress kala daban-daban suka kawo mashi, kowacce tana faɗin. "Daddy nawa zaka sanya". Yana murmushi mai ƙayatarwa, ya sauke tiger eyes ɗinsa a kan V dake rike da pjs irin na jikinsu. Hannu ya miƙa ya karɓi nata yana faɗin. "Bari in karɓi na Autata, tin da kune manya ku yi hakuri in saka nata, kunga kuma irin naku ne ai ko?". Da sauri V ta rungumesa tana faɗin. "Love you my dad"....... "Love you all daddys baby's". Ya faɗa cikin shagwaɓa dan ya kwaikwayi muryar V ɗin ne. Murmushi su ukun suka yi amma ban da Arya da ita kafin a ga murmushinta dama sai an shirya. Juyawa dik suka yi suka mayar da kayan hannusu. GAT ya shiga toilet ya shirya cikin kayan da V basa, sannan ya fito suka wuce dinning room. Dinner suka yi cike da kaunar juna, sannan ya bisu room ɗinsu, a kan bed na V ya zauna dan ita ce auta, suka fara hira cike da kulawa, basa samun lokacinsa sai dare, shiyasa da daddare zai ɓata lokacin har karfe 12 yana tare da su a room ɗinsu suna hira, ya ja su a jiki, ya gwada masu kauna. V ta kwanta a jikinsa sai shagwaɓa take zuba mashi yana biye mata, suka ce suna son zuwa yawo a ƙasar waje, ya ce sai sun yi passing out zai kaisu dik ƙasar da suke so su yi sati guda kafin su fara aiki. Sai daɗi suke ji....... A yanzu na fahimci cewa a ɓangaren jami'an computer horon su Arya na tafi ne daidai da team na su Leo, kenan yanzu a tare zasu dinga aiki, misali idan za'a tura su Leo aiki tare da jami'an Computer to da su Arya zasu tafi kenan!........ E to akwai case babba ma kuwa! ALLAH yasa kar garin ɗaukar fansa Arya ta basu wrong information ta ja a kashe kowa! Dan zata aikata wannan yarinya mai ɗan banzan zuciyan!. Ga shi dai GAT mutumin kirki, salihi jajirtaccen namiji, baya bin bayan karya, dik yadda yake son yaran nan nasa in dai sun yi rashin gaskiya tsab zai hukuntasu, baya bin bayan zalunci, ALLAH ya taimakesa yaran nasa dik na gari, Arya ce kawai mai riko da kafiyar bala'i. Sosai suka dinga hira, ba shi ya bar room nasu ba sai da dikkansu suka yi barci, ya bi ya rurrufesu da bargo, kowacce ya bata sumbata a kumatu cike da tsantsar kaunarsu sannan ya wuce nasa room ɗin ya kwanta cike da kewar mahaifiyarsu Arya a ransa! ------------------------🔥 US. CRYSTAL PALACE. Ta sha barcin wahala sosai, a lokacin da ta farka sai ta kalli ko'ina duhu, a gigice ta tashi tana ihu, dan tana tsoron duhu sosai ga shi tana firgice na rashin uwa. Dirowa kasan bed ɗin ta yi ta fara laluɓar hanya tana kukan sunan Mammy ɗinta. Buguwa ta yi da bango, da sauri ta tashi tana murza forehead ɗinta tana kuma kuka. Laluɓe ta fara yi tana sanya hannunta a gaba, gaba ta dinga yi, bata ankara ba ta bugu da jikin wani abu mai kamar glass da bata san menene bane, miƙewa ta yi tana kuka tana sake laluɓe. Ta faɗi ya kai sau biyar kafin ta samu hanyar fitowa parlo. Nan ta ga haske, cikin kuka ta sauke ajiyar zuciya tare da nufar tsakiyar parlon. Dakatar da kukan ta yi tana kallon uban kayayyakin dake tsakiyar parlon, shopping ne na dik wani abin da ɗan adam zai buƙata a room ɗinsa, harta kayan amfani na toilet, ita ma ga kayan kamranin STARS BODY LUSH, har da su shampoo ɗinsu an kawo mata. A gefe guda ga kayan kwalama kala-kala. Kallon jikinta, ba kaya sai towel, a ranta ta ce waye ne kuma ya zo ya rufe light na ɗakinta? Ganin babu mai bata amsa, kuma bata ga alamar motsin mutane a gidan bane yasa ta nufi wajen view na parlon. Jikin wall kusa da wajen akwai curtains control a wajen, da yake suna da irin shi a gidansu sai ta taɓa shi, ta danna open. Take curtains na view ɗin suka buɗe. Da sauri ta fara leƙe-leƙe, glass wall ne a wajen, ƙasa ta fara leƙawa wai ko zata g mammynta, ga gundun hawaye a fuska. Ta yi iya kallonta bata ga kowa ba, gabaɗaya C-P ɗin ma yau shiru ba wata motsi. Danna close ta yi curtains ɗin suka rufe kansu, ta dawo cikin parlon jiki ba kwari. Hannu tasa ta jawo echolac ɗaya cikin ukun dake jere a wajen, buɗesa ta yi, nan taga su rebon ne kawai a cike a ciki kala-kala na kama gashi. Rufewa ta yi ta matsa kusa da manyan, da kyar ta kwantar da guda ɗaya ta buɗe, kayyakin sakawa ne masu bala'in kyau da tsada. Abinku da yarinta, tuni ta fara murna tana jin daɗi tin ma ba'a ce mata nata bane. Wani haɗaɗɗen top white ta ciro, sai ta ɗauko ash jeans. Tuni ta hau shiri a cikinsu, a wajen ta shirya tsab, kayan sun yi mugun yi mata kyau kuma. Sai murna take yi ta ɗauko ɗayar echolac ɗin zata buɗe kekan ta ji wani irin gurnani mai firgitarwa. A miliyan ta ɗago kanta, a daidai lokacin wani ƙosasshen bujumin zaki ya sanyi kansa cikin parlon cikin tafiyar ƙasaita. Ai wani irin ihu da ta kurma tare da zabura ta miƙe tsaye, hakan yasa Zakin juyuwa da gabaɗaya jikinsa da kallonsa a kanta, suka ga juna ido cikin ido. Haba wani irin zunduma ihu ta yi tare da watsawa a guje ta bazama ba tare da tasan in da ta nufa ba. Ai da gudun gaske zakin ya rufa mata baya shi ma. Bata san in da ta nufa ba, bata san ya aka yi na sai tsintar kanta ta yi cikin wani ɗaki. Tsayuwa ta yi a tsakiyan ɗakin tana faman waige-waige, daidai lokacin zakin ya bango door ya shigo ɗakin da gudun gaske shi ma. Ihu ta zunduma, lokaci guda kuma ta ɗauke wuta diff, ta sulale ƙasa a wajen. Da gudu zakin ya yi kanta, daga bayansa ta cikin ɗakin wata murya ta ce. "Hero, come here". Da karfi zakin ya juya, ɗakin irin dogayen ɗakin nan ne, ba faɗi sosai sai tsawo. Cikin zafin jini zakin ya yi kan wanda ya kirasa. Wannan mutumin ne dai da ya ɗauko yarinyar daga hospital, zaune yake a saman sofa, wasu rantsastsun sofa set ne a cikin room ɗin, a kusa da sofar akwai wani curtains masu shegen kyau launin dark ash da kamar sun raba ɗakin biyu. Guys ɗin su biyu ne suke zaune suna fuskantar juna, dikkansu kuma face ɗinsu sanye da nose mask, hoodie baka ce a jikinsu, sun sanya hular kayan, da alama tattaunawa suke yi. Jin motsin shigowarta yasa suka kai kallonsu a kanta. Nasan kuna son sanin su waye waɗan nan mutane! To a taƙaice bari in faɗa maku, waɗan nan shahararrun terrorist kuma gangsters ne da duniya ke haukar nemansu, but babu wanda ya san ainahin fuskansu, sunansu da ɓarnarsu kawai ake ji, su uku ne a team guda, ko muryansu babu wanda ya taɓa ji, IRON FIST shi ne takensu, dik in da suka aikata wani shahararren laifi sai sun bar tambarin IRON FIST mai ɗauke da hoton kan zaki, wannan tambari duniya ta rika makama wajen nemansu, an zana tambarin nan a ƙasashe daban-daban ya fi a kirga da nemansu, amma har yau an kasa fitar da ainahin zanen IRON FIRST na gaskiya, dan akwai wajen da suke covering in zasu bar tambarin. An yi binciken duniyar nan an gagara kamasu, to mutanen da wani lokaci basa zuwa aikata abu da kansu, suna daga ɗaki a gaban computer zasu yi abin da zasu yi. Dik kuma idan zasu fita aikata laifi suna da mask na team ɗinsu da suke sanyawa, mutane ne da basu da tsoro bama su santa ba, tsabar yarda da kai zasu iya shiga waje kai tsaye su aikata laifi ba tare da bindiga ko wuƙa ba! Ga bala'in saiti a fagen harbi, idan suka so kashe mutum tazarar mitoci a tsakaninsu suna iya harbinsa kuma ya same shi, suna iya harbin mutum a cikin mota mai tsananin gudu tsabar kwarewa, mutane ne dake amfani da ƙwaƙwalwa fiye da jami'an gwamnati, shiyasa aka gagara kamasu, tsawon shekaru an gagara gane dalilinsu na aikata manyan laifuka, kuma babu ƙasar da suka bari, dik karfin tsaronku suka yi ra'ayi shiga suke yi, da wayar mutum da ba nasu ba ma suna iya karɓa su datsi tsaron wasu tsabar kwarewa da yarda da kai, haɗarinsu ya zarce yadda ɗan adam zai iya tinani, suna da salon kisan mutum na musamman wanda dik wanda ya ga wannan kisa yasan su suka aikata shi, a shekarun baya su ne suka yi wa shugaban Amurka wani irin mummunar kisa suka kifar da gwamnatinsa, kowa kuma yasan su ne, amma an rasa hanyar kamasu, ku duba tsaro irin na shugaban ƙasa, amma suka shiga ta karkashin ƙasa suka kashesa suka fito, kwarewarsu yasa basa barin makama komai ƙanƙantarta idan suka aikata laifi! Ko a gida suke zaku samesu da nose mask, mutane ne kuma masu fuskoki da dama, saboda kwarewa basa amfani da fuska guda, kazalika yau zaku gansu da ido blue, gobe violet, jibi ash, suna iya canza komai nasu a lokaci guda, ainahin suffansu ne dai baya taɓa bayyana, dik kalar da suke canzawa na boge ne, basu taɓa fita da ainahin face ɗinsu ba, takan iya yiwuwa yanzu da suke cikin gidan ma fuskan boge ce, dan ba'a gane masu! Mutane ne basu da shaukin komai sai kisan kai da tada zaune tsaye! Basu da uwa basu da uba a wannan gida, su uku suke rayuwa! Kuma wani abin mamaki ɗaya daga cikinsu baya wani jimawa a tare da su, yana da yawan tafiye-tafiye, idan ya yi sati ɗaya da su, zai iya tafiya ya je ya yi sati a wani waje, ko suna da iyaye to sun ɓoye iyayen a wani waje ne suke rayuwa su kaɗai a nan, dukiyar da suka mallaka ALLAH ne kaɗai yasan adadinta. A takaice su waye su kenan, saura bayani zaku ji daga baya. Yanzu haka wanda Dr ta taimaka yana kwance a gadon asibiti, wanda ya ɗauko Seraph yarinyar Dr kuma babban amininsa ne, dama na faɗa maku su uku ne, to yanzu su biyun ne a nan, shi wancan yana gadon jinya, dan ya rasa jini na wuce misali. IRON FIRST basa magana, basa bari a ji muryansu sai su da junansu, shiyasa guy ɗin can bai tanka Seraph ba!........ Watau akwai wani cakwakiya dake gaban a book ɗin nan! Hmmm! -------------------🔥 Da gudu Hero ya bar kanta ya isa wajensu. Da hannu ya nuna mashi kusa da shi, kallon juna suka yi, ɗayan ya ce. "Champion who is this girl?". ....... Kallon in da take ta wutsiyar ido ya yi kafin ya amsa da. "I don't know her. It's FT said I should bring her home, treat her well, give her everything she needs, but I must not let her see him again or even know that he is in the house when he recovers and returns, baya son sake ganinta kuma baya son ita ma ta sake ganinsa, kawai in kula da ita". Shiru guy ɗin ya ɗan yi, kamar ba zai sake yin magana ba sai ku ma ya ce. "Amma hakan ba zai ja mana matsala ba?"........ "Na yi tinanin hakan, but yarinyar bata da kowa, amma zan bashi shawarar ya kaita boarding school".... Jinjina kai guy ɗin ya yi alamar shawarar ta yi kenan. Da haka suka cigaba da hiransu cikin yaren da ni na fassara maku, ba turanci suke yi ba, sannan maganarsu sam bata fita sosai bare a iya gane voice ɗinsu saboda nose mask da suka sanya!.......... Ba su sake bin ta kan Seraph ba! Hmmmm akwaita kuwa! Yau kuma ta nan na faɗa ni Princess Teema!. To fatan dai kuna biye dani mu warware komai a tare!. STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥 ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️ 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A STAR LADY. https://www.facebook.com/share/g/1EUXbqsDjP STEP 1________🔥 7-11-2025.🔥 FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥 E_____________8 Sun jima a wajen suna zaune, magana kuwa sai su fi mintina 20 babu wanda ya ce ƙala, can su ɗan yi hira, su sake yin shiru. A haka suka shari awanni uku a wajen, kafin Champion ya miƙe tsaye, dik in da kuke neman dakakkun jaruman maza waɗan nan sun kai, tsananin hora kansu suke yi fiye da yadda ake hora sojoji, dik saboda kwarewarsu, su basa yi wa ƙananan ƙungiyoyin ƴan ta'adda aiki, basu ma karɓar aiki a garaje, sai an yi saa, kuma wani lokaci fa har gwamnati suke yi wa aiki ba tare da gwamnatin tasan su ne IRON FIST ba. Akwai wani lokaci da wani daga cikin gwamna a Avaris ya nemi taimakonsu through wani abokinsa, ya basu kwangilar kashe wani sarki, a wannan ɓangare and sansu ne da fuskan ƴan Korea, dan abokin nasa ma ce mashi ya yi akwai wasu ƴan Korea manyan terrorists zasu yi wannan aiki. Mutun ɗaya ne daga cikinsu ya shiga Avaris ya kashe wannan sarki kuma ya fita ya dawo, tamkar wasu aljanu, dan haka fuskokinsu a duniya yana da yawa matuƙa! Su kaɗai suka san ainahin kamanninsu sai kuma alƙalamina!. Miƙewa ɗayan ma ya yi, kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, ya buɗe curtains dake wajen ya shige. Shi kuma Campaion in da Seraph take ya kariso, yana zuwa yasa hannu ɗaya ya damki wuyan rigarta. Sama ya ɗagata sai kan shoulder ɗinsa. Ya nufi waje da ita. Hero zai biyosa ya nuna mashi hanya ya bi ɗayan guy ɗin, dan yasa idan ya biyota za'a samu matsala in ta farka. Kai tsaye room ɗinta ya nufa. Yana tura door ɗin ya tsaya kaman wani gumki, a cikin duhu ya hau jujjuya ash eyes ɗinsa da bani da tabbacin kwayar idanun gaskiya ce, dan na faɗa maku a baya komai nasu na boge ne!. Takawa ya yi a natse ya isa gaban light control dake manne kusa da bed, wajen da low light. Wutar ɗakin ya kunna, gabaɗaya haske ya gauraye ko'ina, a saman bed ya jefa Seraph tare da nufar toilet ɗinta. Jim kaɗan ya dawo hannunsa ɗauke da bowl, a gaban bed ɗin ya tsaya. A maimakon ya shafa mata ruwan a natse, sai ya kwarara mata shi a kan fuska!. A firgice ta tashi tana kiran sunan Mammy ɗinta. Yana ganin haka ya juya ya nufi toilet, bai yi mata magana ba bai kuma sake kallon in da take ba. Jim kaɗan ya fito, zai nufi waje ta diro ƙasa da gudu, a gabansa ta tsaya tare da riko hannunsa dake cikin terrorist hand gloves, muryanta na rawa, jikinta na kerma sosai saboda tsoronsa, dan dole kowa ya tsorata da ganinsu, bama kaga face ɗinsu complete ba, sai dara-daran idanu jajir, dik yadda aka yi suna shan wasu kwayoyi!. "Uncle, please take me to my mammy, I am scared of this house"...... Tana gama faɗar haka ta fashe da kuka gwanin ban tausayi. Kwace hannunsa ya yi ba tare da ya yi magana ba, ya raɓa gefenta zai wuce abinsa. Da sauri ta sake binsa, ta rikesa tana rokon ya kaita wajen Mammy ɗinta. Sau biyu yana kwace kansa tana sake rikesa, a na uku kam sai ya damko wuyanta da karfi, ya zazzare jajaye idanunsa a kan face ɗinta. Da muryansa da ba zaka iya gane wace iriya bace saboda nose mask ya ce. "Your mother is dead. Calm down, we don't want nonsense here!!". Yana faɗar haka ya ɗagata da wuyar da ya shake mata ɗin ya jefa saman gado daga in da yake tsaye...... Mutanen da kan iya harbin mutum a cikin jirgin kasa mai tsananin gudu ai saiti a kansu kuma ba'a magana. Yana jifa da ita bai sake kallon in da take ba ya yi wucewansa abinsa. Ji ta yi duniya ya tsaya mata cak, wai Mammynta ta mutu, sai ta ji kamar almara, shiru ta yi tana jin kanta a saman iska haka. Nan kuma ta fara tunano abubuwan da suka faru a gidansu, sai yanzu komai ya dawo cikin kanta, lokaci guda wasu zafafan hawaye suka fara wanke mata fuska, da gudu ta diro kasan bed ɗin, dan yanzu ta tuna komai. Bayansa ta bi ta fito waje. Babu kowa a parlon, ta manta da zaki a gidan, yau ko kasheta zai yi sai ya faɗa mata me dalilinsa na zuwa gidansu har ya ja aka kashe nata mammynta? Dan a yanzu tana ɗauka FT ne wannan. Shiga da fita ta fara yi a ɗakunan da ta gani kawai, dik in da zata shiga bata ganin kowa a ciki, daga karshe ta isa wajen staircase ɗan siririn nan, tana goge kwallah tana jan hanci. Ya manta bai naɗe staircase ɗin ba. Haurawa sama ta yi, a nan ta ga ashe wata duniya ce guda a saman. Ɗakin da ta fara cin karo da shi a parlon saman ta shiga. Nan ta ga uban computers da ba zata iya kirgasu ba, dik kuma suna kukkunne, kayayyakin aikinsu ne cike a ciki. Zazzare voilet eyes ɗinta a kan komai dake ciki ta fara yi, tana rarrabe idanunta. Can ta tsayar a kan wall na ɗakin dake gefe, hotuna ne kala-kala a cike a bangon. Tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki haka ta nufi wajen. A gaban hotunan ta tsaya tana kare masu kallo, wasu hotunan an sanya jar mark a kansu, da alama an kashe mutanen kenan. Can idanunta ya tsaya a kan wani hoto wanda aka sanyawa jar mark shi ma! Da sauri ta miƙa hannu zata ciri hoto sai kuma ta gagara. A fili ta ce. "For sure my mammy tana da irin wannan hoto! Tabbas tana da hoton mutumin nan! Waye shi? Meyasa hotonsa yake gidanmu kuma yake nan da jar mark? Kenan an kashesa?". Tana neman waɗan nan amsoshi tin bata samu ba idanunta suka sauƙa a kan hoton mammy ɗinta cikin kayan aikinta, shi ma hoton an zana jar mark a jiki alamar ta mutu kenan! Babbar magana! Kenan dama su ne suka shirya kasheta ko ya ake ciki ne?. Nasan izuwa yanzu jama'a kanku ta kulle, ni ma dai kaina ya kulle, me alaƙarsu da Dr? Me alaƙa hoton wannan mutumi da Seraph ta gani yanzu da Mammy ɗinta? Dik yadda aka yi Dr tasan FT ko kuma shi ya santa, in ba haka ba ya aka yi yasan ita likita ce har ya je ta cecesa?. Kai mu ɗan ji labarin Dr ko da kaɗan ne, kila zamu ɗan samu wani haske. Dr ta jima tana rayuwa a wannan unguwa tare da abokan zamanta watau maƙotanta, daga ita sai ƴarta a gidansu, dik wanda ya san Dr zai ce maku ita kaɗai ya sani bata da mij ko dangii, ta reni Seraph cike da kulawa, tsantsar so da kuma kauna. Ita ke kaita school ta ɗaukota, ita take mata komai, ko wajen aiki idan zata je tare da ita take tafiya in ba school, bata yarda ta barwa kowa yarta ba. Seraph yarinya ce mai natsuwa da kwazo, ta taso cikin shaukin son shuke-suken furanni da kiwon tsuntsaye game da ƙananan kifaye a cikin ruwa. Shiyasa gidansu yake cike da shuke-shuken flowers masu ƙayatarwa, a gefe guda Dr tai mata katon glass tana kiwon ƙananan kifaye, ga tsuntsayenta a gefe suma tana kiwo. Yarinyar akwai son wasa da ruwa, dan tsab zata shige cikin ruwan kifi suna wasa tare, bata da hayaniya kuma bata zama kusa da hayaniya. One thing Dr ba musulma ba ce! Amma ba zaka taɓa gane hakan ba sai in faɗa maka aka yi, ta yi rayuwarta ne a tsakiyan musulmai, musulman ma ƴan Nigeria masu shegen shiga rai da iya mu'amala da mutane, shiyasa babu wani abu da musulmi zai yi wanda bata iya ba, harta Alqur'ani mai girma zata iya karanta kusan rabi, addu'oin musulmai kam babu wanda bata iya ba, kuma abin mamaki dik in ta shiga damuwa addu'ar musulmmai take karantawa, sai dai ALLAH bai nufeta da karɓar shahada ba har ta koma garesa. Haka Seraph ta taso ba musulma ba, yarinyar ta taso bata san waye mahaifinta ba, kuma bata taɓa tambayar mahaifiyarta ina daddynta ba, bata damuwa da son sanin ina yake tin da mahaifiyarta tana ɗauke mata dik wata damuwa, ta cika rayuwarta da ƙauna da kulawa. A haka suke rayuwarsu a wannan gida, Dr tana aiki ta rikesu da albashinta, ta shagwaɓa Seraph sosai. A takaice yadda suka rayu kenan, ainahin su waye su zai zo a gaba!...... My people na fara wani tinani! Ina daddyn Seraph? Meyasa kowa bai san shi ba? Dik daɗewar da ka yi da sanin Dr ba zaka taɓa sanin ina mahaifin yarinyar yake ba, wasu ma a gabansu Dr ta haifi yarinyar amma basu taɓa ganin ubant ba, sai suka ɗauka cikin shige ne kawai, kun san su ba wata matsala bace

Chapter 14 of 95