Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dasu tamkar ba gobe kafin su tafi mission ɗin. Tin da suka shiga wannan ɗakin horo ba waya, ba komai har sai da suka horu na watanni biyar ɗin nan, aka sabonta masu komai, suka sake fitowa a sabbin yayewa sabbin jini, a lokacin jinin nasu na tafasa. Sai ana saura sati biyu su tafi Mission ɗin aka fito dasu daga ɗakin horo. A tsawon watanni biyar ɗin nan sun sake canzawa sosai, jikinsu ya sake ginuwa tamkar na ƴan wrestling, sun zama zakwakuram jami'ai. Tin da suka dawo mission na biyu bai haɗu da V ba har aka shigar dasu horo, shiyasa ranar da suka fito ita ya fara marmarin ya gani, ana maido masu da wayoyinsu numbeerta ya fara kira, a lokacin dab da mangrib ne, a maimakon y fara kiran daddynsa sai ya tafi ga Juliet ɗinsa, daddy bai san sun fito horo ba, ya dai san a week ɗin nan zasu fita. Yana kiranta ta sanya mashi kuka bayan ta yi picking. To abinku da renon mata a farko, shi ma kukan ya sanya mata na shagwaɓa yana faɗin. "Ni dik yadda za'ayi yau sai na ganki". Wlh Noor ya kware a duniyanci, idan kun gansa a ɗakin horo ba zaku taɓa cewa ya san wani abu wai soyayya ba bare shagwaɓa, babu wasa no nonsense, amma idan yana waya da V, ya ilahi, kunga Leo, V, Aunty's ɗinsa and daddynsa, idan yana waya da waɗan nan gabaɗaya shashasha yake zama, ba zaku taɓa zatan zai iya rike bindiga ba idan kuka gansa a yanayin soyayya, sai in kunga murɗewar jikin ne zai nuna maku alamar da jarumi kuke tare. Jin ya sanya mata kuka yasa ta hakura da nata ta hau cewa. "To ka yi shiru ya isa haka"...... Make kafaɗa ya yi tamkar yana a gabanta, a shagwaɓe ya ce. "Ni in kina son in yi shiru kawai in ganki"...... Cikin zolaya ta ce. "To ka zo gidanmu yanzu". Aikuwa bai sake yin magana ba ya katse kiran ƙid, ita ta zaci ma network ne ko katinsa ne ya kare. Miƙewa ta yi tare da ajiye wayar, ta shiga toilet. Ruwa ta watsa ta fito, nan ta isko su Arya a zazaune kowacce a kan gadonga. Dik suna rike da wayoyinsu, Angelina na kallon fina-finan batsa da ra saba, Manassa na yi wa Vash tsiya, dan ta yi kutse cikin kundin jami'an nasu, a nan ta sato number Vash, ta shigar wayarta tana mashi tsiya, bata faɗa mashi ita bace, ta ce mashi ai ita ba mutum bace, aljana ce, amma a cikin aljanun ma ita ma soja ce. Da farko ya ɗauka wasa take yi, sai ya yi iya yinsa ta faɗa mashi wacece ita amma taki. Yanzu haka diramar da suke yi kenan, ta ce mashi ya yi kokari da ya iya shiga horon watanni biyar ɗin nan tin ciwon kafarsa bata gama warkewa ba. To da yake sau ɗaya kunga suna haɗu da ita a mission ɗinsu na farko, a ranar kuma kunga ta nuna mashi ita ba sa'ar yinsa bace, ƴar GAT take dole ya bata girma, shiyasa bai taɓa kawowa ransa cewa ita ɗin bace, yasan ma bata da numbersa. Ya yi mamakin yadda tasan komai a kansa, ƴar banzar yarinya kuma a cikin kundinsa na form da ya cika lokacin shigarsa aiki ta sato bayanansa, amma take ta wana bawan ALLAH, yanzu tasa ya fara yarda aljanar gaske ce, dan tana faɗa mashi abubuwa na mamaki a kansa, dik abin da yake yi a cikin barrack ɗin sai ta faɗa mashi, kuma wani lokaci drone nasu Arya take turawa ta duba me yake yi, wani lokaci t fake da zuwa office na daddy ya leƙasa, shi kuwa yanzu ya gama saddakarwa da aljana ya yi gamo. Yaran GAT akwai tsiya, ita kuma Angelina tana can tana iskancewarta ga can Unays yana ƙoƙarin macewa da tinaninta. Ita dai Arya hoton Leo take ta faman kallo a wayarta, a ranar da suka dawo sansaninsu ne ta dinga snapping ɗinsa ba tare da ya sani ba,wani lokaci yana zaune a bakin ruwa zata ɗaukesa bai sani ba, shi ne idan bata aikin komai sai ta zauna ta dinga kallo. A kusa da Angelina V ta zauna tana faɗin. "Angelina my Romeo sun fito horo yau da yamma fa". Ta faɗa tana leƙo cikin wayar tata. Nan ta ga abin da take kallo, ai take ta kara matsawa suka fara kallo a tare, kan kace me V ta fara tsuma tana shiga yanayi, ita Angelina dama ta jima da shiga yanayin. A haka Aunty Lisa ta shigo ta samesu, suna ganinta Angelina ta kashe wutar screen ɗin tare da miƙewa zaune tana wani yauƙi. V ce ta ce. "Aunty kayan nan sun maki kyau"..... Irin short jean and crop top ɗin nan ne take sanye da su, sun yi mata kyau ɗin kuwa sosai, sai ma da ta saki coily hairn nan nata irin na Noor, ta haɗu gaskiya iya haɗuwa. Arya dai kallo ɗaya ta yi mata ta ɗauke kai tare da cigaba da abin da take yi. "V come". Aunty Lisa ta faɗa tana kallon Arya. Tana son taga yaran GAT dik sun rungumeta kamar tadda Angelina da Manassa suka yi, amma Arya da Manassa ta gagara samun wannan damar daga garesu, idan ta yi masu magana zasu amsa, baya ga haka basa karawa, idan sun fito bata yi masu magana ba kuma suma basa yi mata, haka suke. Miƙewa V ta yi ta nufeta tana faɗin. "Aunty delirious zaki bani ne?". Hannunta kawai Aunty Lisa ta ja suka fita, kai tsaye main parko suka sauƙo, tana zuwa wajen dining ta ɗauki wani plate dake rufe ta bata. Karɓa V ta yi tana mamakin me a ciki, zata buɗe Aunty ta ce. "No, jeki kaiwa baƙon dake bq". Bata kawo komai a ranta ba, da bathrobe a jikinta ta fito ta nufi bq. Tin a bakin kofa ta ji kirjinta na ɗan bugawa, a ranta ta ce. "Anya ba my Romeo bane wannan baƙo?". Tana tinanin tana shiga ciki. Excuse ta yi a parlon, babu kowa, sai ta nufi cikin room. Nan ma excuse ta yi, ba'ayin magana ba, tura kofar ta yi ta shiga. Tana shiga daga bayanta ta ji an rungumota, sumbata ya mannawa cheek ɗinta kafin ya ce. "Sai da kika sakani zuwa ko?". Ai da sauri ta ajiye plate ɗin a ƙasa ta juyo garesa, da karfi ta rungumesa tare da cewa. "Missed you over my Romeo". Hannunta da ta ɗaura a saman kirjinsa ya kama, wani kyakkyawan diamond ring dake karamin yatsansa ya cire ya sanya mata a babban yatsanta na tsakiya. Ai wani irin kara ta saki tare da kara daka tsalle ta rungumesa. Matseta a jikinsa ya yi, sai ya ɗauketa cak yana juyi da ita a cikin ɗakin, tana murmushi tamkar bakinta ba zai rufu ba. Kun san su idan namiji ya sanyawa mace zobe shikenan tazama matarsa, haka al'adarsu take, shiyasa take murnar tazama tasa, dama ya ce ba zasu tafi next Mission ba sai ya sanya mata zobe, Aunty Lisa ce ma ta bashi wannan shawara saboda tana ganin GAT ba zai yarda Noor ya auri V ba. Saboda ta taɓa kawo mashi maganar a lokacin da suka tafi Second Mission ɗin nan, ta ce zata so ya baiwa brother ɗinta ɗaya daga cikin quadruple ɗinsa ya aura, da buɗar bakinsa sai ya ce dikkansu ya rigada ya masu miji, tin suna jarirai akwai alkawarin wasu a kansu, kuma bil hakki da gaskiya ya faɗa, wlh ya yi wa ƴaƴan ƴan uwansa alkawarinsu Arya. Ita kuma Aunty Lisa ta san da gaske Noor yake son V, ita ma V ɗin da gaske take son shi, dan haka a kan ƙanin nata babu abin ba zata iya ba, shiyasa ta ce ya sanya mata zobe ba tare da sanin daddynta ba, ita ta sayi zoben ma ta ajiye mashi, da ya zo yanzu ne ta bashi. Yanzu da zai zo ya kirata a waya ya ce yana son ganin V, ta ce ya zo bari ta sanar da sojojin dake gate tana da baƙo. Kun ji yadda aka yi ya shigo gidan. So yansu a bisa ƙaidarsu V matarsa ce. E to gaskiya kam musulunci duniya ne nake faɗa maku, ALLAH ka kashemu a cikin Musulunci. Sosai ya yi juyi da ita a cikin ɗakin kafin ya sauketa ƙasa, sannan ya kama hannun nata ya sumbaci ring ɗin. Da sauri ta zumbaci in da ya sumbatar ita ma. Wani ƙaramin kwali ya ciro daga aljihun sportswear ɗin jikinsa ya, miƙa mata ya yi yana faɗin. "Saka mun nawa dan mu kara mallakar juna da kyau". Da sauri ta karɓa, jikinta har yana rawa ta buɗe, da sauri ta ciro zoben sai kyalli yake yi, sanya mashi ta yi tare da sumbatar hannun nasa. Shi ma sumbata ya yi kafin ya jawota jikinsa. Lokaci guda kuma ta ɗan yi shiru, kamar mai tinanin wani abin, sai kuma ta ce. "My Romeo ya zan da daddy idan ya kalli ring ɗin?". Cike da tsoro ta faɗa, jaira time da yake sanya mata soyayya ta rufe mata ido ta manta da wani daddy, sai yanzu da ta san ta zama matarsa shi ne ta tina da daddy. Kun san idan aka ga zobe a hannunta za'a san ta yi aure, tin da kunga zoben shi ne shaidar ita ta wani ce, yanzu GAT na ganin zoben yasan me yake nufi, shiyasa, kuma bata isa cire zoben ba sai da iznin mijin nata, idan ya bata izni zata iya cirewa ta ɓoye. Ɗan rankwafowa kanta kaɗan ya yi, kamar mai raɗa ya ce mata. "Na baki izinin ciresa ki ɓoye har sai mun bar barrack ɗin nan sai ki mayar"....... Ai wani irin daɗin da ta ji bata san lokacin da ta yi tsalle ta ɗalesa ba, tana ta murmushi, shi kuwa yana ta kallonta, daga karshe ya ɗauketa suka koma saman sofa mai zaman mutun ɗaya dake room ɗin. Zama ya yi da ita a jikinsa, ya ce a matsayinsu na masoya da suka mallaki juna yau ta bashi labarin da zai sanya shi kukan farinciki. Ɗago kai ta yi suna fuskantar juna, tasa hannu tana shafa face ɗinsa kafin ta fara bashi labarin yadda zata kula da shi tin da ya zama nata. Ni kam na ce ba'a nan gizo ke saƙa ba, ku bari GAT ya damkeku zaku gane ALLAH da girma yake, dan wlh yai maki miji!. ----------------------------🔥 CRYSTAL PALACE. A bakin kofa ya tsaya tare da zuba mata ido yana kallon yadda take ta faman shan golden morn ɗinta cikin kwanciyar hankali, mamaki ne ya kama shi, wai ba ce mashi ta yi ta yanke da wuƙa ba?. Almost 5 mins yana tsaye kafin ya ɗan yi gyaran murya. Da sauri ta ɗago kai, wani irin ƙayattacen murmushi ta saki kafin ta ce. "Daddy welcome"......... Harara ya dallah mata kafin ya ce. "My cherry bloom kin mai da daddy abin wasa ko? A ina wukar ya yankeki?". Ɗan turo baki ta yi kafin ta nuna mashi hannunta tana faɗin. "Ga wajen nan, zo ka gani"....... Gently ya tako izuwa in da take. A gefen bed ɗin ya zauna tare da cewa. "In ga wajen". Ya faɗa yana miƙa hannu zai riko hannun nata. Da sauri ta janye hannun nata tana murmushi kafin ta ce. "Kawai fa son ganinka nike, na ji ina kewarka ne shiyasa na ce ka zo!"........... Har cikin ransa ya ji daɗin da ta ce son ganinsa take yi, amma yasan ba kalamanta bane wannan, kuma tabbas ba kalaman nata bane, bayan fitarsa ta kira Rimsha ta faɗa mata ta ce tana son daddy amma daddyn ya ce baya sonta, shi ne Rimsha ta bata shawarar yadda zata gane idan yana sonta ko da gaske baya son nata, shi ne ta fara gwada shi ta gani. Yana binta da wani irin kallo kafin ya ce. "Waye ya koya maki karya kuma?"....... "Ni daddy ba wanda ya koya mun, kawai ni na tuna da kaina"...... Wayarsa ya ciro daga aljihu, ya shiga cikin record na wayarta dan ya duba, sai ya ga bayan fitarsa ai ta kira Rimsha, a ransa ya ayyana cewa Rimsha ce ta koya mata, sai ya ji yana son jin me suka tattauna, ga shi bai ɗauko bluetooth ba, dan haka sai ya hakura da jin hirar tasu sai ya koma gida, ya haske hasken screen na wayar ya mai da ita cikin aljuhu kawai ya zuba mata idanu tana shan golden morn ɗinta tana ɗan turo baki. After 2 days. Zaune yake a saman sofar parlonta rike da waya yana dannawa, yau ya tsara gayu cikin wasu tsadaddun three-pieces suit masu shegen kyau ash color, ya yi kyau matuƙa, sai tashin kamshin yake yi. Ya yi nisa cikin abin da yake yi unexpected ya ce an ce. "Hi, well-done sir"......... Da yake kansa na sunkuye ne yana taɓa waya sai ya ɗan ɗago eyes ɗinsa ya kalli yatsun kafafunta, a tinaninsa dama Aisha ce ƴar wajen Madam, amma daga yatsunta ya gane ba ita bace, dan Aisha fara ce sosai ta fi Suhana. Kuna ganin Aryan kamar baya kallon abubuwa ko? To har yatsun kafafun Madam sai ya faɗa maku yadda suke, dik abin dake tare da Seraphina yana sane da shi, kuma yana kula da sanya idanu a kan komai sosai, su ne suke kallon kamar ba ruwansa da su, dan kunga idan ya shigo gidan room na Seraphina kawai yake wucewa, idan ya tashi kuma ya fice abinsa. To ba haka bane, wani lokaci yana shigowa gidan har ya fita babu wanda yake sani har ita Seraphina ɗin, wani lokaci karfe 1 dare suna barci yake shigowa ya sake fita, dan haka ya san komai, tin ma kafin su Aunty Safiyya su zo gidan yasan zasu zo, kuma yana sane da cewa ita Safiyya tana da dalilin zuwanta gidan, watau dan ta fitar da Seraphina daga CP, dama ya yi shirin canzawa Seraphina ɗin school izuwa wanda yake cikin CP dan kada ma ta sake fita CP ɗin, sai kuma sara ta zo a kan gaɓa ya sameta da waɗan can littafan. Kai kafin ya ɗauki Madam aiki ma sai da ya san wacece ita in and out, ba kawai ya ɗauketa bane! Dan haka dik wani motsinsu a tafin hannunsa suke, kawai yana son su kama kansu da kansu ne. Su suke ganin kamar sun mashi wayau bai sani ba, basu san cewa da IRON FIST suke tare ba, kasar da ba kasarsu bama suna iya sanin halin da take ciki in and out, suke aikin sirri a kan wasu abubuwa ma bare a kan family ɗinsu, family ɗin ma wacce Champion ɗinmu yake matuƙar kauna, ai ganinsu kawai yake yi. Ganin bai ɗago ba kuma babu alamar zai amsata ne yasa Suhana ta sake matsawa dab shi, cikin yanga irin nasu na ƴan mata ta sake ce mashi hii. Shiru tamkar babu shi a wajen. Daidai lokacin Seraphina ta fito shirye cikin wani dogon wandon jeans ash color da riga top fari tas, ta yi bala'in kyau. Sai ma da ta gyara ash hair ɗin nan nata yana wani irin sheki, Madam ta ɗaure mata hair ɗin a tsakiya sai ta saki jelar a baya har saman mazaunanta, ga wasu guntu-guntu gashi da suka kwanto ta gaban goshinta. Hannunta rike da wayarta da kuma ƴar siririyar fashion bag ɗan karamin da ko wayarta ba zai iya shiga ba, sai tashin kamshi ita ma take yi. Ganin Suhana a tsaye a gabansa yasa ta ɗan tsaya daga nesa tana faɗin. "Daddy I done". Sai a lokacin ya ɗago eyes ɗinsa a kanta, wani irin cool ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa tsaye. "Super my Cherry bloom". Ya faɗa yana nufota. Da sauri Suhana ta bashi hanya, saboda da ya miƙe kwarjini da cika idonsa ya kara ninkuwa....... Murmushi Seraphina ta yi tare da cewa. "Daddy my birthday date ya kusa zuwa, mammyna bata nan, na kai 2 years bana celebrating, yakamata this year in yi ko?". A gabanta ya tsaya tare da cewa. "Zamu yi celebration mai lasisi this year". Ya faɗa tare da riko hannunta, har wani ɗan lumshe idanu ya yi da ya taɓata, kamshin perfume ɗinta yana mugun tafiya da shi. A cikin ransa yana faɗin a ranar birthday ɗin nan zan mallakeki kowa ma ya huta, aurenmu zai zama special, a fili kuma cewa ya yi su je. Binsa ta yi tana ɗan waigo Suhana dake tsaye, ita ma juyawa ta yi ta bisu da kallo har suka wuce kafin ta juya cike da takaici ta koma cikin ɗakin Madam, tin da ta kalli Aryan a ranar farko ta ji ya kwanta a ranta, tana son ganin full face ɗinsa, amma ta rasa dama, dan su face mask ya zame masu jiki, ko a gidansu su ukun nan ne zaku gansu da shi a fuska, yanzu ta zo ne da yanganrta dan ya ɗan kulata ko da gaisuwa ce su yi, amma ya shareta, abin ya kona mata rai. Kai tsaye elevator suka nufa. Suna tafiya Seraphina sai shagwaɓa take zuba mashi, shi kuwa yana ta faman biye mata. Kai tsaye katafaren shopping dake sama suka nufa dan yin shopping gobe Monday zata fara zuwa schoo nan school dake cikin CP ɗin yai masu registration ita da Rimsha, ya sake haɗasu makaranta ɗaya kenan. Wannan karon ya ɗaura ɗamarar saka masu ido da basu kula ba tare da ya bari sun san yana sanin dik abin da suke yi ba!. Suna shiga ya samu waje ya zauna tare da ce mata ta je ta ɗauki dik abin da take so. Da sauri ta wuce ciki tana murna, har da cewa wai zata sayi breziyya, dan Rimsha ta faɗa mata ita dai tana sakawa, kai waɗan nan yara sai Aryan ya yi da gaske wlh, idan ba haka ba akwai aiki, ita Rimsha yanzu 14 years take, kunga ko ta sa bra ba matsala, amma Seraph 13 ɗin ma da sauran watanni huɗu kafin ta cika, ace ma tana da 13 years, wai dik abin da Rimsha ta yi sai ta yi ita ma, kai wannan yarinya, ita ma Rimshar akwai iya shege da komai ta yi sai ta faɗawa Seraph ɗin. Shi kuma ya fito da wayansa, yana fito da waya sai ga Faryan da Rimsha sun shigo shopping ɗin suma. Ai ba ƙaramin mamaki Aryan ya sha na ganinsu ba, yanzu ya zai yi?. Yasan dole Rimsha zata haɗu da Seraphina, and yasan ƙaramin aikin Seraphina ce ta ce zata kawota ta gaisa da daddynta, dama jiya a wayan da suka yi ya ji Rimsha na ce mata ALLAH yasa daddynki ba mugu bane irin uncle Aryan, ya dakeni babu abin da na yi mashi, ba dan ina son family ɗin daddyna sosai ba da na gudu na bar gidan, kuma ba dan Abba ya ce daddyna ya fi son uncle Aryan a kan kowa ba da wlh na cewa uncle Aryan ALLAH ya isa ban yafe ba, wlh ba dan ina son uncle Aryan kamar yadda nike son daddyna ba da na yi sallah na roki ALLAH ya sakamun a kan abin da ya yi mun, amma ba zan iya yi mashi mugun fata ba, zan dinga yafe mashi kome ya mun dan ALLAH ya yafe mun nima, kuma ina kallonsa kaman daddyna, dan wlh yana kama da daddyn nawa sosai kamar an tsaga kara. Yana jin Seraph ta amsa mata da. "Gaskiya uncle Aryan ɗin nan naki azzalumi ne, ni na ji ma na tsanesa, amma ba komai watarana shi ma zai yi aure ya haifi yara, za'a rama maki, ki kyalesa, kuma ki dinga addu'a, mammy ta ce wai idan ka faɗawa ALLAH damuwarka zai biya maka buƙata". To tin da suka yi wannan hira yasan sai Seraph ta ce Rimsha ta zo ta ga uncle ɗinta ba bugu bane. Aikuwa ya zame mashi dole ya gudu. Miƙewa ya yi da sauri ya fice daga super market ɗin, ya tsaya can nesa da wajen yana kallon kofar shiga. Aikuwa yadda ya yi hasashe ne, sun haɗu kuwa a wajen sayan underwears. Suna saki kara game da rungumar juna, sai dariya suke yi kamar wasu zararru, cike da mamaki Rimsha ta ce. "Dama a CP gidanku yake?"...... Seraphina ta ce. "Sunan wajen nan kenan CP?". Kara rungumeta Rimsha ta yi tana amsa mata da e. Ai Faryan baya ya koma yana kallonsu cike da mamaki, sai dai kuma tin da ya kyalla ido ya ga Seraphina zuciyarsa ta amsa, a ransa yake jin ya samu irin kalar zaɓinsa. Sai da suka gama rungume-rungumen junansu sannan Rimsha ta ce. "Uncle Faryan wannan ita ce Seraphina ɗin da nike faɗa maka". Ta dawo da kallonta a kan Seraph. "My star lady ga uncle ɗina dake kaunata shi kaɗai, wanda nike baki labari". Seraphina tana ɗagowa ta kallesa sai da ta ji faɗuwar gaba, domin kuwa jini ba karya ba, kamannin Aryan ta gani, har kamar zata ce daddy sai ta ga wannan bai kai Aryan tsawo da cika ba, da farko zata ce la mai kama da daddy, sai ta tina yadda suka yi da shi a kan hoto, dan haka sai ta fasa magana game da cewa. "Good evening Uncle Faryan". A natse ya amsa mata, ai sai da ya yi magana ta kara tabbatar da kamannin, dan har voice ɗinsu yana shige. Daurewa ta yi bata nuna komai ba, ta ja Rimsha suka shiga cikin shopping, bayansu Faryan ya bi amma daga ɗan nesa, daga karshe ya samu kujera ya zauna, dan ya lura yawonsu a cikin wajen nan ba zai kare ba. Suna tsaka da yin shopping ne wani haɗaɗɗen guy ya tare masu gaba, matashi ne ɗan kwalisa, yana sanye da wasu shaggun pop dress, gashin kansa sak na Noor ɗinmu. Ba kowa bane kuma face uncle ɗin Noor wannan uncle ɗin nasa guda ɗayan. Kallonsa suka yi, take suka ɗaure fuska, Seraphina ta ce. "Are you out of your mind da zaka tare mun gaba?"..... Ɗan lumshe idanu ya yi kafin ya ce. "Yadda kike haɗaɗɗiya haka voice ɗinki ma yake, kin dagi zuciyata"...... Da alama dik family ɗin su Noor muggan ƴan love ne, family ɗin su Abba kuma sun raba jaha da love, kuna ga yadda uncle ɗin Noor yake neman sace zuciyar Princess Teema taku ta amana, ga ji salon soyayya mai ratsa zuciya. Tsoro ne yakamasu, da sauri Rimsha ta ja hannunta suka raɓa gefensa suka wuce, juyawa ya yi ya bisu da kallo, a ransa ya ce. "Ta haɗu, ko zan salwantar da dik abin da na mallaka sai na mallaketa, ita ce na gani a view na benen kusa damu ranar, kyakkyawan tamkar Seraph". Bai san sunanta Seraphina ba, ma'anar Seraph yana nufin kyakkyawan gaske mai haske kamar malaika mafi haske, shiyasa ya ce tamkar Seraph take, bai san kuwa Seraphina take ba. Da iya gaskiyarsa ya faɗa cewa ko zai rasa dik abin da ya mallaka sai ya mallaketa, kun kuwa san familyn Noor ba dai kuɗi ba, akwai gumurzu, da alama kuma ɗan soyayya ne, zai yi saurin sace zuciyar mace, su IRON FIST kun san basu iya soyayya ba, da sauki gaskiya, gara ma Aryan ɗin ya ɗan fisu, to zamu dai ga yadda wasan zata kaya, ga uncle Faryan ma ya ga ƴar baby Cherry Bloom ɗinmu ya kamu. Kutsawa ciki suka yi, a tare suka yi shopping, komai iri ɗaya suka dinga ɗauka, sun lodi kaya sosai, Seraph ta ce Rimsha ta zo su je ta gaisa da daddy ɗinta, aikuwa ta ce to. Sai dai suna zuwa basu gansa ba, sun turo uban kaya niki-niki a cikin shopping bike. Mamaki ne yakamata, sai ta fito da wayarta ta hau kiransa. Bugu ɗaya ya ɗaga, a shagwaɓe ta ce. "Daddy ina ka je?"........ Nisawa ya yi kafin ya ce. "Kin gama ne?". Da e ta amsa mashi....... "Okey ki bar kayan a wajen ki fito ki koma gida zan zo maki da su da daddare, wani abin ne ya taso mun na tafi"....... Tana turo baki ta ce. "To daddy ga Rimsha na haɗu da ita, tana

Chapter 49 of 95